Duniya ta yiwa Gimbiya Binta zafi, ba ta san sanda ta
durkushe kasa ta na mai sakin kuka mai tsanani. Gimbiya K’amariyya ce ta fito
hannun ta ruk’e da sakon Bintu, gani Gimbiya Binta cikin tashin hankali ya sa
ta sakin sak’on na Bintu bisa kujera, ta k'arasa gare ta da sauri ta na mai
waige waige cikin fargaban sharrin masu tsirku.
d’ago ta yi ta na fad’in
‘’haba ‘yar uwa, ba yanzu mu ka gama rarrashin ki ba, me
yayi zafi Binta shi ba wuta ba? Maza tashi mu yi ciki kar bayi su gani su sami
abin yad’awa’’
Kanta ta d’aura bisa kafad’ar Gimbiya K’amariyya ta na mai
fad’in
‘’na shiga uku Didi, duniya na neman juya min baya, hatta
d’an uwa na ya fi kaunar d’iyar bayi akai na ni da na ke cikin umman sa’’
Gimbiya K’amariyya na mai buga bayan Gimbiya Binta a hankali
cikin rarrashi, ta ja ta su ka yi ciki. Sai da su ka shiga d’akin Gimbiya
K'amariyya, ta sallami baiwar da ke cikin d’akin sannan ta zaunar da Gimbiya
Binta bisa gado ta nemi ba'asi akan tsakanin Yarima Nuhu da Bintu. Nan Gimbiya
ta fad’a mata yanda ta kasance tsakanin ta da Yarima Nuhu, jin haka ba ta yi
mamaki ba, sai ma tsaki da ta ja ta ce
‘’shiga shigila gand’e ma shiga rawar takai! Har kya ma damu
da Yarima Nuhu, in dai wajan shiga shirgin da ba na shi ba ne in aka gan shi
kowa ya shafa fatiha, ya manta ba kauna ba, ciki d’aya su ka hito da Bintu! kar
ki wani damu, zancen komawar ki k'asar Nigeria kuwa InshaAllahu zance ne, kuma
in dai Aisar ne ya ma zama na ki an gama’’
Gimbiya Binta na mai kwantar da kan ta bisa gwiwar Gimbiya K’amariyya
ta ce
‘’ina godiya Didi, dan Allah kar ki bari Takawa ya raba ni
da farin cikin rai na’’
Ta na shafa kan ta ta ce
‘’in dai wannan ne kar ki damu, bayan auren d’iyar bayi na
miki alk'awarin shedawa Hajja Kilishi lamarin ki da Aisar, sai a san yanda za a
bullowa lamarin, ko?’’
Ta k’arasa maganar ne ta na mai d'ago fuskar yar uwar ta ta,
cike da farinciki Gimbiya Binta ta tsinci kan ta ta na mai washe hakora, ashe
dai da rabo. Haka dai su ka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali har
Gimbiya Binta ta mance da maganar Yarima Nuhu bare ma ya dame ta.
Bintu kuwa ko da ta samu ta ganta d'akin Hajja Kilishi, nan
ta yi zaune abun ta, da Hajja Kilishi ta tambayi sak’on na ta, sai cewa ta yi
ba ta ga Gimbiya K’amariyya ba. Hajja na k'orafin dama ba ta ce Bintu ta je da
kan ta ba, ta sake aika wata baiwar ta karb’o sak’on, sannan ta bawa Jakadiya
da ta zo tafiya da Bintu.
Sak’onni ne na kayan gyra jiki wanda ya had’a da su dilka,
halawa, kalta, kurkum dadai duk sauran kayan gyaran jiki wanda musammam Hajja
Kilishi ta sa aka mata sautin su daga Agadez.
A daren ranar Bintu ta fara shiga hannu, mai gyaran jiki na
yi, mai koya mata kissa da dabarun zaman fada na yi, mai mata jawabi yanda
sabuwar rayuwar ta za ta kasance na yi. Telar babban gida ma ba a barta a baya
ba, haka ta yi tattaki ta zo ta gwada Bintu tare da tafiya da damin siturun da
Hajja Kilishi ta zab’arwa Bintu. Hatta gashin Bintu da Marry ta yanke sai da
Jakadiya ta saita almakashi ta daidaitasu, ta na mai tambayar ya aka yi gashi
rabi dogo rabi gajere. A lalle sai an wayar da Bintu ta fito fes kamar d’iyar
saraki. Ita kuwa Bintu ba ta fasa kuka da kewar Innar ta ba.
Daga ranar zuwa washagari sai ga Bintu an fara wasai.
Washagari da safe, Bintu da Jakadiya tare su ka zauna karin kumallo, cin abinci
ma sai Jakadiya ta koya mata dan kar ta je ta bada su a masarautar abokan gaba.
Abinci ne kala kala na alfarma irin na gidan saraki, kai ka ce ba fari ake a
masarautar ba. Bintu na gani Innar ta ce ta fad’o mata a rai, ba makawa ta san
yanzu ta na nan ta na fama da hatsi da dusa, amma ita nan ga abinci har da na
b’arna a gaban ta.
Da kyar ta iya cin kad’an daga abinci, hakan ma sai da
Jakadiya ta sab’ar ma ta, ta na mai tuhumar ta da tsabar mugunta ne ya sa Bintu
k'in cin abinci, dan a ganta ramammiya ta sa ace tsabar yunwar da ke addabar
Masarautar su ne, ko kuwa cutar yunwa ya kama ta.
Kan wannan jaraba na Jakadiya ne ya sa ta bi yanda Jakadiya
ta ce, ta na mai gwada mata yanda za ta yi haka har dai ta ta6a wanda za ta
iya, a dole Jakadiya ta hakura ta rabu da ita.
***** ******
Sai da ya rage saura sati guda auren Bintu sannan Innar ta
ta yarda ta zo wajan Jakadiya ganin Bintu, hakan ma sai da Jakadiya ta matsa
tukunna. Ganin yanda Bintu ta canza ta yi wasai fatar ta har shek’I ya ke, duk
da dai ta yi wani irin rama sai da ta ji dad’i. Sun dad’e suna hira, nan ta ke
sheda mata sarki ya ‘yan ta ta. Sam Inna ba ta yi wani murna ba, a fad’an ta da
hatsarin da aka jefa d’iyar ta har gwara a bar ta d’iyar bayi har abada. Da
Inna ta zo tafiya da kyar Bintu ta sake ta, nan fa taita sana'ar ta ta, wato
kuka babu kuma mai rarrashin ta bare ace mata ya isa.
Bayin da aka amince da su, wanda su aka yarda su shiga wajan
Jakadiya kuwa kishi su ke da Bintu, musammam da su ka ji ashe ita ce za a aurawa sarki ba Binta ba,
ga gyara da hidima da ake mata sai kace wata d’iyar saraki. Baiwa ta zama ‘yan
tacciya. Da yawan su kan ce kukan munafurci Bintu ta ke, wasu kuwa fad’i suke
ina ma su an Bintu, da kakarsu ta yanke sak’a.
Babban gida kuwa Gimbiya Binta Hajja Kilishi ta sa a gaba ta
na mata gyaran jikin bogi, a lalle ayi basaja gudun ‘yan tsirku na fada. Amma a
zahirin gaskiya Sarki ya sa a duba makaranta mai kyau da tsada k’asar Nigeria
domin mayar da ita can. Har ila yau daga Gimbiya Binta har K'amariyya ba su
fasa k’ulle k’ulle da shige da fice ba dan neman yanda za a yi Takawa ya sauya
shawara, amma dai abin ya ci tira. Har kar gaban ta ya sa ko ta kan Bintu ba ta
bi, bare ta sa ta a idanun ta.
Haka ma Yarima Nuhu, wanda ya rame a ‘yan kwanaki kad’an
tsabagen fargaba auren Bintu da ke gabatowa bilhakki. Gashi gaba d’aya an 6oye
Bintu cikin fada, raban da ya sa ta a ido tun randa ya zo ya tadda ita da
Gimbiya Binta ta na mata cin kashi, duk yanda zai yi ya gan ta yayi amma babu
Bintu babu alamar Bintu. Daga bisani ya yanke hukuncin tarar aradu da daka,
bayan sun dawo daga shawagi, ko sauka daga dokin sa be yi ba, yayi tattaki zuwa
wajan Jakadiya da buk’atar sa na ganin Bintu
Kan ya k’arasa ga 6angaran na ta su ka yi kaci6us a hanya,
ta fito za ta turakar sarki. Ganin ta yayi saurin jan linzamin dokin domin
tsayawa, har sai da dokin ya fara dara da nagarta (tsalle da rawa) cikin
yanayin tada kura, Yarima Nuhu na mai damk’e linzamin gudun kar ya ji shi k’asa
ya shiga k’ok’arin tsayar da dokin. Jakadiya na mai d’aga hannun ta na dama da
ta d’unkule sama ta ce
‘’kiwo sannu Yarima, ba sake ba manko, kamazuru abokin
dabara, amincin ka ya fi ga linzaminka’’
(ta na fahimtar da Yarima Nuhu ya nutsu, hankalin sa ya tafi
kan linzamin dokin kada ya kada Shie’’
Ko da ta ga dokin ya tsaya, sai ta sa kai za ta yi gaba,
Yarima ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar fad’in
‘’ba ki ji ba Jakadiya, wannan zuwan na ki ne’’
Jin haka Jakadiya ta ja ta tsaya, ta na bashi amsa da
‘’anya kuwa ba na ce ah ah ga Yarima ba yayinda na ke kan
hanyar da zata sada ni da Babban Bijimi ba?’’
Da sauri Yarima Nuhu ya sauko daga bisa dokin, ya na mai jan
linzamin dokin ya dawo daga gefan Jakadiya, wani irin iska mai zafi da k’asa ke
busawa duk da dadai la’asar ce sakaliya.
‘’wa ya isa tsayar da Jakadiya a hanyar da zata sada ta da
Takawa?’’
Jakadiya na gyad’a kai ta ce
‘’barka da siddi masu duniya’’
‘’barka dai Jakadiya, gani na zo gare ki da buk’atar ganin
Bintun arziki ko da kuwa na ‘yan dak’ikai ne’’
cewar Yarima Nuhu ya na duban Jakadiya. Ko da ta d’aga ido
ta kalle shi sai ta ga ya mata kwarjini. Sanye ya ke cikin dokakkiyar shadda
koriya d’in ‘yan fakistan. Ya d’aura falmaran ruwan zuma bisa, ga farar hular
sa irin ta larabawa wacce ba ta da nauyi bisa kan sa, kafar sa kuwa takalmin
fata ne sau ciki, shima kore an yi masa ado da d’igon ruwan zuma.
Ganin idan sa ya sa ta kasa yi masa musu kamar yanda ta saba
yi masa akan duk abin da ya jib’anci Bintu. Kana ta tsinci kan ta ta na mai
fad’in
‘’yo to Yarima ka san abun ga ba haka ake ba, Babban Bijimi
ya ce a killace d’iyar bayin nan, amma tin da ka zo da kan ka yi tsimayi cikin
lambu, zan sa a rako ta, amma kada ka ruk’e ta, kasan amare ba a san ana ganin
su hakan nan sakaka saboda.....’’
‘’ina godiya Jakadiya, ba zan manta da wannan alfarma da ki
ka yi a gare ni ba’’
Yarima Nuhu yayi saurin katse ta dan ba ya san jin maganar
da Jakadiya ke masa game da auren Bintu, ya na mai jan linzamin dokin sa yayi
hanya da za ta sada shi da lambun ba tare da ya jira amsar Jakadiya ba.
Kasancewar ruwa be sauka ba, yawanci shuke shuken da ke
cikin lambun duk a bushe su ke, sai kukan tsuntsaye da kwari ne ke tashi sama
sama. Dokin sa ya saka ya na shawagi cikin lambun, yayin da ya sami wata
shifid’a da ke k’ark’ashi bishiyar mangwaro, ya cire takalmin shi, ya zauna
sannan ya kuma kishingid’a kan tintin da
ke jere bisa shimfid’ar.
Be dad’e da zama ba ya hangi wata da ya kasa gane ko wacece
ta shigo lambun ta na mai waige waige da alama akwai wanda ta ke dubawa. Daga
in da ya ke zaune ya k’ura ma ta ido cikin kokanton abun da kwakwalwar sa ke
fad’a masa.
Sanye ta ke cikin doguwar riga ruwan zuma, an mata aikin
hannu irin na sarauta tun daga sama har izuwa k'asan rigar da jan zare. Kan ta
nad’e da jan kallabi, haka ma talkamin da ke sanye k’afar ta ja ne. Ganin ta
nufu in da ya ke sai da ya tashi zaune daga kishingid'ar da yayi, ya na mai
gyara zama, tafiyar ta ya dad’a gasgata masa abin da ya ke gani, babu shakka
ita ce d’in ce.
Tin da ta hango shi gaban ta ya shiga fad’uwa, ba a san ran
ta ta fito ba, dan ko da Jakadiya ta zo
ta tadda tela ta sa ta gaba ta na gwada
kayan da aka sa tela ta d’in ka mata, ta na kan na k'arshe Jakadiya ta ce
Yarima Nuhu na da buk’atar ganin ta.Ta so cire kayan da ke jikin ta dan ta fi
gane shigar su na bayi, amma Jakadiya ta ce ah ah, kada ta 6ata lokaci ta yi
maza ta je ta same shi yanzu yanzu cikin Sirri.
Gaba d’aya ta kasa sakewa, dan ta kwana biyu ba ta saka
k'afar ta waje ba,gashi kayan da ke sanye jikin ta da ma takalmin da ke k’afar
ta duk sun saka ta na jin kan ta daban, abun da ba a saba ba, gashi a dole ta
na ji ta na gani an sa ta gaba da gyara,
lalle sai ta yi kama d’iyar saraki, ita dai wannan masifa ba ta ta6a
ganin irin shi ba.
Da wanan tunani ta k’arasa gaban sa, amma ko da ta masa
sallama ta na mai zubewa a k’asa kamar yanda ta saba duk sanda ya bayyana gaban
ta, sai ta ji shiru be amsa ba. Ba ta gusheba kan ta sunkuye ta sake masa
sallamar a karo na biyu, shi ma shiru, na ukun da ta sake ne ta d’aga ido da
niyar kallan in da ya ke zaune, sai tsintar idanun ta tayi cikin na sa, ya taso
izuwa gaban ta ya durk'usa ya na kallan ta kamar zai had'ye ta. Cikin fad’uwar
gaba ta yi saurin yin k’asa da nata idanun ta tana mai fad’in tuba
‘’tuba na ke Yarima’’
Niamey
‘Bangaran Aisar kuwa, yau take kwana uku da dawowar su Nijar
daga k’asar Ingila, in da aka duba mai girma shugaban k’asa Gaddafi Nur. Zaune
Shugaba Gaddafi ya ke a k'awataccin falon sa, tare da babban d’an sa wanda ake
kira Junaid da kuma Aisar. Jikin na sa Alhamdulillahi yayi kyau kwaran gaske,
wanda hakan ya bashi dama zantawa da 'ya'yan na sa akan abubuwan yau da kullum.
Aisar kuwa kamar kullum, yanzun haka ma gangan jikan sa
kad’ai ke wajan, amma zuciyar sa na ga Bintu, tunanin Bintu ya hana shi sakat,
ya jagula tunanin sa har ya na da yak'inin cewa muddun ba zuwa yayi gare ta ba
zai iya shiga wani hali.
Cikin wannan hali ne kamar daga sama ya ji Shugaba Gaddafi
ya ambato sunan Masarautar ta su Bintu, wato Sa’ayrasa. Wanda haka ya sa yayi
saurin dawowa cikin hankalin sa, ya na mai san jin ainihin maganar da shugaba
ya ke.
Nan ya sami amsar da ya ke buk’ata, takardu guda biyu
Shugaba ya mik'awa Junaidu ya na mai fad’in
‘’gashi nan Junaidu wasik’ar gayyata ce daga Masarautar
Fabarusa da Sa'ayrasa, wanda za su gudanar da auratayya tsakanin junan su nan
da mako guda’’
Cike da farin ciki, kafin ma Junaidu ya kar6a Aisar yayi
saurin sa hannu ya kar6e ya na mai fad’in
‘’mashaAllahu, wato Bintu ta yi gaskiya auratayya ce zai
kawo silar k'arshen gaba tsakanin wannan Masarautun, wannnan yarinya ba dai
kwakwalwa ba’’
Ya na magana ne ya na k’ok’arin bud'e ma'jin waasikar, be
san daga Shugabn k’asa har Junaidu kallan sa su ke cike da mamaki ba, musammam
Junaidu da be ta6a jin zance wata mace daga bakin Aisar ba, ya ce
‘’Bintu? Wacece Bintu?’’
Sai a sannan Aisar ya tuna ashe fa a zahiri ya yi maganar,
ya na mai duban Junaidu hannun sa rike da wasikar da ya bud’e ya ce
‘’wata d’aliba ta ce a makaranta da na koyar mai kwazo da
hazak’a, bakin ta na fara jin auratayya na iya kawo k’arshen gaba, yar
Masarautar Sa’ayrasa ce’’
‘’yar wani hakimi ce a Masarautar?’’ Shugaba Gaddafi ya
tambaya cike da farin cikin ko dai ya kusa samin sirika ne. Ga mamakin sa sai
ji yayi Aisar ya amsa masa da
‘’d’iyar bayi ce.....’’
Shiru ne ya biyo baya, yayinda Aisar ya duk’ufa kan karanta
wasik’ar gayyata na musammam da aka aiko daga Masarautar Sa’ayrasa, cike da
mamaki ya ce
‘’gide Sarkin Fabarusa da kan sa zai auri d’iyar Sarkin
Sa’ayrasa? Na yi zatan tsakanin ‘ya ‘yan su ne? ko da shi ke harkar manya ba a
cewa komai’’
‘’ai auren dama za a yi ne ba hakan nan bak’atatan ba, za su
yi ne saboda taimako da Sarki Sule na Sa'ayrasa ya nema daga Sarki Abdulraman
na Fabarusa akan fari da ya addabi Masarautar ta su, ka na Ingila shi ya ba ka
da labari"
Aisar na mai duban sunan Fatima da ya bayyana bisa wasik’ar
ya ce
‘’dama ya na da d’iya Fatima ne? Na san dai akwai wata
d’iyar sa Binta wacce na koyar a makarantar Sovereign’’
‘’ni ma dai Gimbiya K’amariyya kawai na sani da ita aka fi
fita damawa a masarautar ta su, in dai akwai Fatima sai dai ta kasance kanwa a
gare ta, yo to ai Binta Fatima ta ke, ko shakka babu d’alibar ta ka ce ma"
Junaidu ne ya amsa masa.
Aisar na mai d’aga kafad’a cike da nuna an yi ba daidai ba
ya ce
'’kai amma yarinya ce sosai, gaskiya auren nan be dace ba
bata fi shekara goma shabiyar ba, ina zancen makarantar ta kuma fa? Wannan ai
tauye hakki ne, me zai hana a aurar da yayarta ta tunda ita ta kai munzali?'’
Duk abun nan ya na yi ne ba dan kowa ba sai dan Bintu, ta na
yawan fad’o masa a rai tun sanda ya ji batun farin da ya addabi k’asar su,
rashin lafiya Shugaba Gaddafi shi ya hana shi sakat, yo to ana ta kai wake ta
kaya, amma idan ya tuna rayuwar fada ta ke, sai hankalin sa ya kwanta dan ya
tabbatar ba za ta6a kwana da yunwa ba. Amma jin za a aurar da Gimbiya Binta ya
sa hankalin shi tashi, dan babu mamaki k’arshen karatun Bintu kenan, kila ma ta
na cikin bayin da za tura Fabarusa domin kula da Gimbiya Binta. Ya kai duban sa
ga Shugaban Gaddafi wanda tun da su ka fara magana be tanka ba, ya ce
‘’Baba na ka duba wannan lamarin saboda Allah, wannan nauyin
na Gwamnati ne, ceto rayukan al’umma, ba na Masarautu ba, mun san kana yi, kuma
kai me yi ne’’
Maimakon Shugaba Gaddafi ya bashi amsa sai murmushi ya
sakarwa d’an na sa. Junaidu ne ya bashi amsa da toh
‘’toh d’an k’asa mai kishin k’asa, kana ina san da Baba ya
sa aka hannu za a fitar da damin kud'i dan aika abinci ga Masarautar’’
‘’to me ake jira ba a aika ba? Me ya kawo jinkirin? In dai
rashin lafiyar Baba ne, Baba ya ji sauki,
a yi maza a aika dan a taimaki bayain Allah’’
Cewar Aisar cike da damuwa. Shugaba Gaddafi na masa nuni ga
takardar hannun sa ya ce
‘’ga amsar nan bisa hannun ka, jin Masautar Fabarusa za ta
taimakawa S’ayrasa, da kuma niyar su na auratayya ya sa mu ka dakata, muddin
hakan zai kawo k’arshen gaban da ke tsakanin su toh fa babu ruwan Gwamnati da
shiga lamarin, sai dai mu bada gudunmawa ta hanyar amsa gayyata da kuma k’ara
mu su k’arfin gwiwa, kud’in da mu ka ware dan ciyar da masarautar kuma ya tafi
ga wani aiki wanda zai amfane su ta wani fannin’’
Aisar na mai girgiza kai ya ce
‘’na fahimta, Baba na san saboda yanayin jikin ka ba za ka
sami halartar d’aurin auren ba, in zan sami dama ina so na zama d’aya daga
cikin wanda za su wakilce ka’’
Jin haka Junaidu ya san hakan nan yanda Aisar ba ya san duk
wani abu da zai had’a shi da siyasa, ya san banza ba ta kai zomo kasuwa, ya ce
‘’ah ah ka manta ranar za ku koma Ingila domin duba jikin
Baba? Ka bari an hutasshe ka ni na je’’
Duk da yayi maganar ne cike da zolaya, sai da Aisar ya tsuke
fuska, dan kuwa gani ya ke yanda ya ci burin ganin Bintu, duk wanda zai hana
shi ganin Bintu shi an mak’iyin shi, jin za a je Masarautar su ya san tun da
d’iyar bayi ce ko shakka babu zai gan ta, ko dan ya sami daman ganin iyayen ta,
ya ji ya za su yi da karatun Bintu tun
da dai ita Gimbiya Binta aure za a mata, kuma ya rok’e su da kada su cire ta
daga makaranta, idan ya kama ne ya d’au nauyin ta, zai yi.
Ya na mai tsuke fuska ya ce
‘’zai fi kyau dai kai ka koma Ingila, tun da Baba ya ji
sauki, duba shi kawai za a yi ina ga babu amfanin zuwa da ni’’
Shugaba Gaddafi ya ce
‘’to tsakanin ku, idan dukan ku biyun ne ma za su d’aurin
auren daidai ne, ina jin sauki sosai, ba na buk’atar rakiyar ku’’
Murmushin jin dad’i Aisar ya saka, cikin ran sa ya na mai
fad’in
‘’Bintu na ina nan tafe, ki kwantar da hankalin ki babu mai
cire ki daga karatun ki’’

rashin lafiyar Baba ne, Baba ya ji
sauki, a yi maza a aika dan a taimaki bayain Allah’’

Kallon Bintu Yarima Nuhu ya ke cike da so da k’auna, murya
can k’asa ya kira sunan ta
‘’Bintun arzki, dama haka ki ke da kyau? Anya kuwa Bintu zan
juri rashin ki?’’
Kanta a k’asa ta d’an ja da baya, dan kuwa ganin Yarima Nuhu
durkushe gabanta ba k’aramin takura ta yi ba, dad’in dad’awa yau kuma ya zo
mata da saban salo na magana. Ai kuwa sai ta yi kamar ba ta ji ba. Kana ta ce
‘’Allah shi taimaki Yarima, Barka da yammaci, Jakadiya ce ta
ce Yarima na da buk’atar gani na’’
Hannunta da ke rawa ya bi da kallo, in da idanunsa suka sauka bisa zoben hannunta, sai kyalli da
shek’i ya ke, ba tare da wani tunani ba ya d'aura hannunsa bisa hannun lta mai
d’auke da zoben. Jin sabon salo hannun Yarima Nuhu bisa na ta ya sa Bintu janye
hannunta a firgice cikin sauri kamar wacce aka d'aurawa garwashi, nan ta shiga
yarce hannun tana ka6ewa kamar wanda wani abu ya mak’ale. Gaba d’aya ta firgice
idanunta na shirin kawo ruwa.
Cike da mamaki Yarima Nuhu ya ke dubanta, kana ya ce
‘’Haka ki ke k’yank’yamina Bintu? Duk wannan d’aga hankalin
da yarfe hannun dan na ta6a ki ne?’’
Sai a sannan ta farga da abun da ta ke, tuni ta zube
hannayen nata a k'asa, idanunta na fidda kwallar da dama su ke mak’ale cikin
kwayar idanunta, fad’i ta ke.
‘’Na tuba, kamin rai, na tuba, ba na so na mutu Yarima,
aradu ba na san na rasa raina.’’
Ya na mai jinjina maganar cikin ransa, cike da mamaki ya ce
da Bintu
‘’Wa ya ce za ki mutu?’’
Zuciyarta d’aya, har ila yau ba ta fasa hawaye ba ta ce
‘’Iya Dije ce’’
‘’Iya Dije?’’
Yarima Nuhu ya
maimaita. Bintu na mai gyad’a kai ta ce
‘’Eh Iya Dije, ta ce idan har na sake na bari namiji ya ta6a
ni mutuwa zan yi, kwankwatsi ma kuwa.’’
Ga mamakinta sai gani ta yi Yarima Nuhu ya jefa kansa baya
ya na mai saka dariya mai sauti. Cikin rashin fahimta Bintu ta duk’ar da kai
jiki na rawa.
Tashi ya yi, ya koma wajan zamansa na fari, yayinda ya zauna ya na mai kishingid’a bisa tintin
cike da mulki da sarauta. Har a lokacin idanunsa kanta ya ke, fuskarsa kunshe
da murmushi bayan wasu d’an dakik’ai ya ce
‘’Bintu d’ago ki kalle ni.'’
A hankali ta d’ago kanta, cikin bin umarni ta kai kallonta
gareshi, fuskarta cike da hawaye. Gefansa ya mata nuni da shi sannan ya ce
‘’Dawo nan ki zauna.’’
Ta na fidda kwayen idanu ta ce
‘’Iye?’’
Kai ya gyad’a mata cikin jaddadawa, bai kuma fasa mata
murmushi wanda ke k'ara masa kyau ba. Cike da shakku Bintu ta tashi a hankali,
inda ya mata nuni nan ta je ta zauna, amma can nesa da shi.
Ya na mai jin dad’in maganar Bintu, duk da yayi mamaki ace baiwa
kamar Bintu batasan komai ba har haka, sakamakon shaidar rashin kamun kai da
ake yiwa matasan bayi irinta. Kana ya nisa tare da fad’in
‘’Iya Dije ki ka ce kowa? Ko shakka babu ta yi gaskiya’’
A tsorace Bintu ta d’ago ta kalleshi ta na mai fad’in
‘’Shikenan ni Bintu mutuwa zan yi, na shiga uku na lalace.’’
Dakyar Yarima ya iya kunshe dariyar da ta kusa cin
k’arfinsa, ya na mai k'ok’arin d’aure fuska ya ce
‘’Banda yanzu, ba za ki mutu ba tunda ni ba ta6a ki, hallo
na yi ba gangan ba, zoben hannunki na ta6a, amma kar ki yarda wani ya ta6a ki
muddin ki na so ki yi tsayin rai, musamman idan aka kai ki wannan Masarauta na
Fabarusa, ko da kuwa Sarki Abdulrahman ne da kansa.’’
Ta na mai tunani yo dama me zai sa Sarki Abdulrahman ya ta6a
ta, ta yi saurin amsawa da
‘’Aeadun Allah ba zan bari ba, hallo ni ma ba na zuwa kusa
da maza, Inna ta ta hana’’
Yarima na mai duban zoben hannun ta wanda hakan nan ya ji ya
tsole masa ido, ya ce
‘’Wagga zobe na hannunki, wa ya baki?”
Zuciyar Bintu d’aya ta amsa masa da
‘’Monsieur Aisar ne ya bani ajiya.’’
Wani bakin kishi ne ya ta so masa jin sunan namiji bakin
Bintu, nan da nan ya sha mur ya na mai kausasa murya ya ce
‘’Akan wani dalili zai baki zobe ajiya? Shi waye d’in ki?
Ashe dama ki na soyayya?’’
Cikin k’ok’arin kare kai ta ce
‘’Wallahi ba na soyayya, ban ta6a yi ba, idan k’arya na ke
aratta kashe ni, Monsieur ne a École ya
ce na ajiye masa.’’
‘’Ciro zoben ki bani’’
Ya ba ta umarni. Har ga Allah ba ta son cire zoben, idanunta
na fidda kwalla yayinda ta ciro zoben daga yatsanta, maimakon ta bashi sai ta
dunk’ule shi cikin tafin hannunta. Ganin bata da niyar mik’a masa, ya mik’o
hannunsa gare ta, a hankali ta d’aga ido ta kalle shi, ya na mai gyad'a mata
kai ya mata nuni da hannunshi. Hannunta na rawa, ta aje zoben bisa tafin
hannunsa, ba ta ankara ba sai gani ta yi yayi wulgi da shi gefe. Da sauri ta bi
inda ya jefa da kallo yayinda ta ji zuciyarta na mata rad’ad’i, sai a
sannan tasan ashe zafin da zuciyarta ke
mata ba na rabata da iyayen ta kad’ai ba ne, har da na rashin Aisar har abada,
gashi idan aka d’auke turarukan da ya bata, zobenshi ne kad’ai ya rage mallakin
sa a gunta, ta na ji ta na gani Yarima Nuhu ya raba ta da shi kamar yarda ‘yar
uwarsa ta rabata da shi, idan ita dan ta na son Aisar ne, shi kuwa Yarima Nuhu
menene na shi azancin? Tambayar da ta yiwa kanta kenan, wanda nan ta ke kuwa ta
ji amsarta, Yarima Nuhu na mai duban ta ya kira sunan ta da kakkausar murya
‘’Bintu’’
Hakan yasa Bintu dawowa da kallonta gareshi. Bai gushe ba ya
cigaba
‘’Soyayya gaskiya ce, soyayya halal ce muddin ba a tsallake
iyakokin Ubangiji ba, ba laifi ba ne don kinyi soyayya, amma ki sani duk
duniyar nan da ni ya dace ki yi, Bintu ni mai kaunarki ne, ni Nuhu ni masoyinki
ne da ni ya dace ki yi soyayya ba da wani tsoho da ake shirin amra mi ki ba, ko
kuwa wancan sokon Monsieur da ya bawa d’alibarsa ajiyar zobe!’’
A tsorace Bintu ta fara ja da baya, ta na mai girgiza masa
kai, tsabagen firgici ta kasa magana. Da sauri ya rik’o hannunta, ya na fad’in
‘’Karki guje ni Bintu, ni mai k’aunarki ne, kimin alkawarin
za ki aje min kanki amana, ah ah kawai ki shirya mu gudu, duk k’asar da ki ke
so aradu zan kai ki Bintu, kar ki yarda a amra mi ki wannan tsohon.’’
Cikin sauri Bintu ta fizge hannunta daga nashi, har lokacin
ba ta fasa girgiza kanta ba, yayinda ta ke hawaye d’aya na bin d’aya, tunda ta
ke a rayuwarta babu wanda ya ta6a furta kalmar so a gareta, kuma ba ta ta6a
zaton zata ji shi daga bakin ko da ‘yantaccan d’an adam ba ne, bare kuma
Yarima, Yariman ma na Sa'ayrasa. Hankalin Bintu bai dad’a tashi ba, sai da ta
ga kwalla cikin idanun Yarima Nuhu na gangara a hankali bisa kuncinsa, nan ta
mik’e tsaye da sauri yayinda kuka ya ci k'arfinta tana mai tattare kasan
doguwar rigarta, ta juya da niyyar tafiya, hakan yasa Yarima Nuhu tashi da
sauri, ya na mai rik’o kallabinta ya ke fad’in.
‘’Karki tafi ki barni Bintu, aradu zan iya rasa raina, ki
tausayamin.’’
Sakar masa kallabin ta yi, gashin kan ta lub lub ya sauko
har bisa wuyanta maimakon gadon bayanta da ya saba saukar sakamakon askin da ta
sha gun Marry, tana mai tafiya cikin gudu gudu, sauri sauri, ta d’au hanyar
fita daga lambun.
Yarima Nuhu rik’e da kallabinta ya shiga doka mata kira
‘’Bintu! Bintu!! Bintu!!!’’
Ina ko waige ba ta yi ba bare ta tsaya har ta fice daga
cikin lambu, in da ta bar Yarima Nuhu rungume da kallabin na ta bisa k’irjin
sa, ya zube gwiwowi biyu k’asa zuciyarsa na bugawa kamar za ta tsage ta fito.
0 comments:
Post a Comment