Wani wahalallen
miyau ne ta haɗe da k'yar,
tayi tsuru-tsuru da ita kamar wadda aka dasa, buɗe baki tayi zatai magana ta kasa ta bar bakin buɗe tana kallon Aunty Zainabu,
Jikinta bai tashi
kyarma ba saida Aunty Zainabu ta doso inda suke, tana tafiya tana kallonsu
fuskarta babu annuri, bata ankara ba sai dai taji ta fara jik'ewa da zufa ta ko
ina,
"Aunty wallahi
zan miki bayani, don Allah ki dakata, abinda kikaji ba haka bane"
Bata tankata ba
harta k'araso inda take, tuni taa gama
sandarewa, sai dai taga ta duk'a inda take, ta ɗaga filo ta zaro wayarta, sannan ta juya tabar ɗakin, ba tare data tanka musu
ba
Wata munafukar
ajiyar zuciyah ta saki sannan ta juyo inda hafsatul kiram take itama duk taa haɗa zufa, tama fita ruɗewa, (wanda suka karanta
littafin hafsatul kiram sun santa da saurin ruɗewa, abu kaɗan
ke sakata kuka), tuni hawaye suka wanke mata fuska, harta so ba Majeeda dariya,
"Akwai
matsala fa" inji Majeeda,
"Matsalan me
kina ga batace komi ba, da alama bataji mu ba"
"Zanyi fatan
hakan hafsat, anma nifa hankalina bai kwanta ba da irin kallon da take
mana" duk sukai shiru kowa ya rasa abun cewa,
Sun daɗe a haka babu wanda ya iya
cewa komi, k'arar shigowar text ne ya katsesu a wayar Majeeda, duk saida suka
firgita, sannan ta daure ta duba, kamar wata marar lafiya,
"I don't say
it enough, but wanted to let you know that I love you."
"luv uh too i
swear, ina ka shige?"
"cikin
zuciyarki...lol ina hanya hope kowa dai ya gama tafiya, ina kewar matata da
yawa"
Ta sauke ajiyar
zuciyah, addu'ah ta shiga yi Allah ya kawoshi gidan da wuri, tare da Addu'an
Allah yasa Aunty Zainabu bataji su ba.
Firarma kasawa
sukai ita da hafsat, da gudu ta tafi toilet ta zazzagar da fitsarin data kusan
saki shigowar Aunty, tana dawowa ta zari jikkarta,
"Tohh
Aminiyah, nidai zan tafi"
ta tashi da sauri
tana gyara ɗaurin zane, "ina kuma
zaki tafi ki barni cikin wannan bala'i?"
"Haba, ki
kwantar da hankalinki mana komai zai dai-daita insha Allah, zamuyi waya Ya Umar
yana waje"
"kema fa
hankalinki tashe yake taya zan kwantar da nawa?" dafa kafaɗarta hafsat tayi, suka fito
tana kwantar mata da hankali,
Sai dai me? Falonta
wayam babu furnitures nata, komai an kwashe kamar sabon gini, duk suka saki
baki suna kallo har Aunty Zainabu tazo ta bangajesu ta wuce bedroom ɗin nata tana sauri,
Kayan sawarta ta
dinga kwashesa tana juye mata a akwatunanta, hafsat na ganin haka ta mata
sallama ta tafi, bata samu maa ta amsa mata ba,
Tafiya tayi da
sauri inda Aunty take ta rik'e mata hannu,
"Aunty ina
za'a kaimin kayan kike kwasarsu?"
Bata tankata ba taci gaba da kwashewa, sai da ta gama kwashe
komai, ko k'yalle bata bari ba ta jasu tayi waje dasu, Majeeda ta k'ara shan
gabanta,
"Aunty don Allah ki faɗamun ina zaki kaimun kaya?" k'ara shareta tayi
taci gaba da jan kayan,
Duk ta ruɗe kuka kawai take kamar wacce
ake zare ma rai, ta kwanta nan k'asa kamar k'aramar yarinya tana gunjin kuka,
"Don Allah
ki rufamun Asiri Aunty yanda naki ya rufu, ki taimakeni karku rabani da Yaya
Majeed, shine rayuwatah, don Allah Aunty ki tausayamun" idan Aunty Zainabu
ta tankata ku da kuke karatunnan kun tanka, haka taci gaba da kuka har muryarta
ta soma sik'ewa,
Tana ji tana gani
suka kwashe komai na ɓangarenta, harta Abdallah goyeshi tayi a bayanta, ta
wurga mata mayafi,
"ki tashi mu
tafi nace"
Da tafiyar gwiwa ta
gangaro inda Aunty take ta rik'e k'afafunta,
"ki kasheni ma
kawai Aunty, zaifimun sauk'i da rayuwa babushi, don Allah karki Rabani da Yaya
Majeed Aunty, ina sonshi" ta k'ara fashewa da kuka hannuwanta rik'e da
k'afafun Aunty Zainabu,
Ji tayi Aunty ta
k'yalk'yale da daria,
"lallai
Majeeda bansan sanda soyayya ta rufe miki ido ba haka, ranar da za'a kawoki kin
cika ma mutane kunne, 'don Allah karku kaini, bazan iya rayuwa dashi ba,' yau
kuma kece da cewa bazaki iya rayuwah babushi ba, Sabon gidan da Dadd ya baku
zaku koma, ko wani kike ba ajiyar kuɗin
da za'a sake miki wasu kayan?"
Wata doguwar ajiyar
zuciyah ta saki tana jan numfashi, ta ɗago
kanta tana kallon Aunty cikin shakkun maganar data faɗa, murmushi taga tana mata,
"Aunty dgsk
sabon gidan zaki kaini?"
"da gaske
mana, idan ba can ba ina zan kaiki?" shiru tayi sannan hankalinta ya fara
kwanciya,
"da tunanin
me kikeyi?"
"ba komi Aunty,
mu tafi" tana maida mata murmushinta, suka fito suka tafi, sai jan Aunty
take da labari don ta tabbatar ba haushinta takeji ba, ita kuma taci gaba da
biye mata,
Bata ankara ba ta
gansu hanyar gidansu Majeed, ta ɗago
fuskarta cikin wani hargitsin tana kallon Aunty, tun kafin ta mata magana ta
rigata,
"Zamu biya ki
musu ban kwana ne" sannan ta saki ranta, hankalinta kwance suka shiga
gidan, kai tsaye ɗakin Abba
suka wuce
Kowah ya haɗu a ɗakin kamar ana wani taro, Daddynta da Momie, Umman
Majeed da Abbanshi, harda Zahra ma, Majeed ta hango shima zaune, anma bata ga
alaman damuwa a fuskarshi ba don shima ba'a mishi maganar ba, kuma bai taɓa kawowa a ranshi zasu san da
maganar ba,
Ganin haka itama
bata damu da ganinsu ba, don bataga alamar Aunty taji maganar da tayi ba, suka
samu wuri saman carpet ita da Aunty suka zauna, suna satar kallo ita da Majeed,
Abban Majeed ne ya
fara magana "bamu zauna nan don ku mana k'arya ba, ko mu saurari wani
shirme naku, kun riga da kun gama kaimu k'arshe, ku faɗa mana tsakaninku da Allah wanne irin zama kuke
tsakaninku"
Ba wani shakku a ran
Majeed yace "irin zaman da kukeso muyi Abba, mun daina faɗa, ina bata duk wani hakk'inta na aure, ka tambayeta
kaji" tun kafin a tambayeta ta amshe
"sosae ma kuwa
Abba, yana kulawa dani, muna zaman mu lafiya"
Daddy ya jefa musu da tambayar da duk saida ta kusan katse
musu en hanji,
"Bayan kun
raba auren naku kenan?" duk suka fara muzurai irinna mararsa gaskiya,
dak'yar Majeed ya iya k'arfin hali,
"Raba Aure
kuma daddy kamar wasu mararsa hankali, mema zaija mana raba aure?"
"Wa kake
tambaya cikinmu?" inji Abba,
"daman ina
hankalin yake? Ban taɓa tunanin
zaku iya aikata hakan ba, kun munafunce mu, kuma kun cuci kanku..." Majeed
da har yanzu baisan yanda akai ba, yayi saurin cewa
"Abba mufa ba
abinda muka aikata, idan ma wani ne yakeso ya haɗamu daku wallahi sharri ne"
"waye zai
muku sharrin cikinmu? Koda yake, daman kun daɗe
da maidamu shashashai tunda har kuke tunanin bazamu gano zaman da kuke ba"
Abba ya mik'a hannu ya ansa wayar Aunty Zainabu data ɗauka kusa dasu, ta kunno recordn ɗin maganar Majeeda da hafsa yanda kowa zaiji,
Majeeda kamar ta
zunduma da gudu, tama kasa zama kamar wacce zafi ya kama, hawaye ne kawai ke
kwararo mata ta ko ina, tunda take bata taɓa
shiga tashin hankali haka a rayuwarta ba, tama kasa ɗaga kai ta kalli kowa, Majeed ma tunda ya ɗukar da kanshi bai k'ara ɗagowa ba, zufa kam rigarshi
harta jik'e,
Ɗakin yayi shiru, sai sautin kukan Majeeda dake fita
a hankali,
"Shima wannan ɗin sharri ne?" Abba ya
tambayesu,
"Anma na rantse
Abba babu abinda ya shiga tsakanina dashi..."
Wani irin k'wallo
Daddy yayi da ita,
“shi cikin Abdallahn a ruwa kikasha cikinshi? Ko har
yawon iskanci kike fita?" tai saurin rik'e bakinta, tana dafe inda daddy
ya sa mata k'afa saboda zafin da yake mata, idanunshi sunyi jajir da ɓacin rai,
Sai lokacin takai
kallonta ga Momie, ta duk'arda fuskarta tana share hawaye da alama kuka take,
wannan wane irin tashin hankali ne yau take gani?
Abban Majeed ma
cikin rawar murya da alama dauriya yace,
"kun cucemu,
kun karya duk yarda da mukai daku, Alk'awari ne mukai ma mahaifinmu, Anma a
sanadiyyarku mun kasa cikawa, Allah ya gani munyi iyakar k'ok'arinmu, anma kun
nuna mana baku isa ba, HARAMTACCEN ZAMA?, bansan a ina kuka samo wannan
tarbiyyar ba, kuma kunyi kaɗan kuce mune
muka baku ita, me kukeso jama'a suce a kanmu? Mun muku auren dolene kuka maida
kanku haka? Wlhy k'arya kuke duniya ta zagemu a kanku, bazamu taɓa yafe muku...."
Umma tace "duk
meya kawo hakan Alhaji? Yanzu kuma inka musu baki ya kakeso su zama?"
"harna yaushe
kuma? ZAMAN DADIRO fa, wallahi zaifimin daɗi
ace mutuwa sukai da inga wannan rana" duk k'arfin halin da Abba yake da kuka ya k'arasa maganar,
Can ciki Majeed
shima Yace "Ayi hak'uri Abba, kuskure...." wani irin Mazga da Abba
yakai mishi a baki har saida yayi jini,
cikin tashin hankali ya buɗe bakin sai
gashi har hak'ori ya fita,
Hakan baisa Abba ya
saurara mishi ba, saima ya tashi ya rufeshi da duka ta ko ina, daddy na
rik'eshi anma kamar yana k'ara mishi k'arfi, shiko Majeed ko motsawa baiyi ba,
yana zaune yanda yake Abba na jibgarshi, dak'yar daddy ya k'waceshi ya matsa
sai huci yake,
"ka k'yaleni
in kasheshi in huta da wannan bak'in cikin nashi, ai duk laifinshine, shine
babba kuma sakaran banza, inama amfanin haihuwarshi?"
"A'ah Yaya,
idan har akwai laifinshi tohh nata yafi yawa"
"laifinta
data buɗa baki ta sakeshi? Idan har ya
daraja maganarmu bai saketa ba zata saki kanta ne? Ko zata ma kanta ciki ne?
Shine lalataccen ɗan iskan da
yayi sanadin komi, ita tana da raunanniyar zuciya, da kalamai en kaɗan zai iya galaba a
kanta" yana gama faɗi ya shige
bedroom ɗinshi, Umma ta tashi ta bishi,
Haka su Daddy suma
suka fita, Aunty Zainabu taja Hannun Majeeda suka tafi anan kowa ya watse
akabar Majeed kamar wani zararre,
Saida Zahra ta dawo
ta mishi magana sannan ya mik'e ya tafi yana tangaɗi ko kallon gabanshi baiyi harya shige ɗakinshi
Har sukaje gida
Majeeda kuka take, babu wanda yayi k'ok'arin rarrashinta, kamar ranta zai fita
haka take wannan kuka,
Suna zuwa Aunty
ta rakata tsohon ɗakinta,
kayanta komi sunanan, ta kwance mata goyon Abdallah ta ajjeshi sannan ta juya
ta barta nan,
Jawoshi tayi ta ɗaura saman jinyarta ta tsura
mishi ido, kowanne hali babanshi yake ciki? Shikenan fa kamar k'iftawar ido
komai ya gama faruwa, rungumeshi tayi a jikinta taci gaban da kuka,
Bayan kwana biyu,
Majeeda babuci, babusha, saita kama dole, tayi wata uwar
rama tayi bak'i sosae, kullum cikin kuka take, daga Momie har daddy babu wanda
ya kula da halin da take ciki, Abdallah kanshi yayi ramar dole saboda bai samun
isasshen abinci, sai dai da madara ake kaɗa
mishi,
Kullum cikin kiran
layin Majeed take bai shiga, babbar damuwarta kenan da batasan halin da yake
ciki ba, rayuwar gaba ɗaya taa
burkice mata da babu Majeed a tare da ita,
Sai a kwana na Uku
ne Momie ta fara gajia da halin da take ciki, tunda ta shiga ɗakin bata fito ba, abinci yanda aka kai mata haka
za'a ɗaukeshi, ruwa kawai take ɗura ma cikinta,
Tana kwance ta saka waya a gabanta tana kuka, bayan ta gama
kiran layin Majeed,
Momie tace
"tashi Zaune" babu gardama ta mik'e zaune tana share hawaye, momie ta
jawo kwanon Abinci ta ajje mata gabanta,
"banson
gardama, ki maza ki cinye abincinnan idan baso kike muci gaba da sanya miki ido
ba" kuka ta fashe dashi sosai ta faɗa
jikin momie,
"Don Allah
momie kuyi hak'uri"
"naji tashi
kici abinci nace" ta tallabota, sai da ta tabbatar taci mai yawa sannan ta
k'yaleta bayan tasha ruwa, da kanta ta fita da kwanonin sannan ta dawo zauna
tana fuskantar Majeeda,
"Damuwar me
kike?" tayi shiru ta kasa ɗago
kanta, momie ta zare wayarta dake sak'ale a hannunta,
"bamu isa mu
rabaki dashi ba Majeeda? Yanzu kiran menene kike mishi?" shiru ba amsa,
"ke ba
k'aramar yarinya ba da basai an zauna ana miki faɗa ba, yanzu duk bayan wannan neman wata alak'a kike
a tsakaninku? Ki zauna kiyi tunani kanki ne kike cuta, kece mace, daga inda ya
samu wata macen zai manta dake, kekau kina nan kullum kina cutar zuciyarki da
tunaninshi, kiyi tunani idan har yana sonki me yasa ya sakeki? Da yake kanki
rashin hankali ya k'are kika zauna kikaci gaba da zama dashi, kullum kuna cikin
saɓon ubangiji, kuna tara ma
kanku zunubai, me zakuce da ɗanku idan ya
girma ya gano ta hanyar da kuka sameshi? Ki godema Allah da abun ya tsaya a
haka, damarkice da zaki zauna kita rok'ar yafiyar ubangiji, ki manta da Majeed
da rayuwar da kukayi a baya,"
"Momie wallahi
na kasa ne, kullum ina k'ok'arin mantawa dashi, don Allah ki tayani da
Addu'ah"
"ki k'ara
dagewa kam, don babu wani sauran zama a tsakaninku, babu inda kika taɓajin anyi saki Uku an koma,
kema kina tashi kina addu'ah Allah ya yafe miki, ya kuma yaye miki sonshi,
namiji ne da ba'asha mishi alwashi, duk yanda yakai da sonki wata rana shida
kanshi zai goranta miki,......" nasiha dai sosae Momie ta shiga yi mata,
gaba ɗata jikinta yayi sanyi, har
momie ta barta tana zubar da hawaye,
"Taya zan fara
koyama kaina rayuwa babu Majeed?"
Majeed,
Shima tun daga ranar duk wani farin ciki ya k'aurace mishi,
yana raye anma yafi kama da matacce, ko kukan ya kasa yi, idan ya fara kallon
wuri ɗaya sai ya daɗe a haka, ko magana baiyi, tunsu Umma na ganin abun
wasa harya fara damunsu, ada Zahra ce kawai ke kula dashi,
Umma har sanyashi
gaba take taita kukan kodai ya haukacene, gashinan dai har asibiti anje babu
wani ci gaba, ko abinci aka ɗura sai anbi
da ruwa zai haɗe,
Wata rana Zahra taje take bamasu Momie labarin halin da yake
ciki, sai a sannanne majeeda na laɓe
ta jiyo, taci kukanta harta gode ma Allah,
Abdallah ne ta goya
ta tafi dashi su Umma nata jajenshi, daga can ɗaki ya dinga jiyo kukanshi, takenan duk abubuwan da
suka faru suka dunga dawo mishi, baisan sanda ya k'walla k'ara ba, sai a
sannanne yayita kuka,
Wani lokacinshi
kanshi kukan yana maganin damuwa, sukaita murna jin ya dawo hankalinshi,
Aisha tana yawan zuwa ganinshi, duk da ba wata fira ke shiga
tsakaninsu ba, anma tana k'ok'arin debe mishi kewa
A gurguje plz
Bayan shekara ɗaya
Abubuwa da yawa sun faru cikin, ɓangaren Majeeda ta gama makarantarta, hankalinta
kwance ta fara mantawa da Majeed duk da abu mai wahala ne ta iya cire
tunaninshi a ranta, anma tana k'ok'arin hakan,
Abdallah yayi
wayau, yana ɗan jagwalgwala magana, babu
inda bai zuwa yawo koda gudu ne, kakanninshi kowanne ɓangare ji suke dashi, duk da ba'a yayeshi ba anma
kusan kullum a gidansu Umma yake yini, ba k'aramin tausayin yaron sukeji ba,
Aunty zainabu ma ta haifi ɗanta namiji,
Abdul k'adir,
***
Anata shirye-shiryen bikin Majeed da Aisha, anyi hidima
sosae duk da angon ba wani nutsuwa gareshi ba, mahaifinta ne ma ya matsa akayi
saboda yanda ta guji auren kowa ita dai sai Majeed kullum tana gidansu, duk
yanda Majeeda taso ta danne zuciyarta ta halarci bikin kasawa tayi, sai dai ta
kulle kanta a ɗaki tayi ta
kuka,
An ɗaura aure, can kaduna state
aka kai mishi amaryar don yanaso yayi nesa da gida,
Dare yayi Amarya na
can bedroom ansha lulluɓi ana jiran
ango, kamar daren farkonshi da Majeeda shi kaɗai
ya shigo da ledar kaji da drinks a hannu, ya tura k'ofar ɗakin zai shiga,
Daren farkonshi da
Majeeda ya faɗo mishi, yanda suka dinga faɗa kamar sun cinye junansu,
baisan sanda ya saki laidar ba ya dawo da baya, kujera ya samu a falo ya zauna
yana sharar hawaye, ba kaɗan ba yake
kewar Majeeda,
Shiru-shiru Aisha
ba ango, tun tana tunanin yana hanya ya
kusan zuwa harta daina ta fara tunanin abinda ya tsaidashi,
Har k'arfe ɗaya babu Ango, hankalinta fa
ya tashi ta fara tunanin ko ina ya shige, shawarar kiranshi a wayane tazo mata,
ta ɗauko wayarta ta kirashi, can
falo ta dinga jiyo ringing ɗin wayar
anma ba'a ɗauka ba, haka ta dinga kira
tana katsewa, ta fara tsorata, cikin sadaukarwa ta lallaɓa ta fito falon,
Can ta hangoshi saman kujera yayi tagumi da alama tunani
yake, ta daurema zuciyarta ta k'arasa inda yake, sai da ta ɗan taɓoshi
sannan yasan da zuwanta,
"Majeeda
ko?" ta tambayeshi tana kallonshi da raunanniyar murya,
"bazan miki
k'arya ba Aisha, naa kasa mantawa da Majeeda, wlhy komai nake ita nake
tunawa" cikin sigar lallashi tace,
"ba abune mai
sauk'i haka ba hniee, anma insha Allah nayi maka alk'awarin maye maka gurbinta,
zan zame maka mace ta gari, zan maka dun abinda zai faranta maka in guji wanda
zai ɓata maka, zan nuna maka
soyayya fiye da wacce kake tsammani, ina sonka da yawa hniee"
"ngde Aisha,
kiyi hak'uri kinji, insha Allah zanyi k'ok'arin daina tunaninta"
"ba komai fa
hniee, taso muje ka kwanta, tunanin ya isa haka," haka taci gaba da
lallashinshi da kalamai masu daɗi
har sai da ta tabbatar hankalinshi ya kwanta,
A daren ranar
Majeeda tayi kukanda bata taɓayi ba tunda
tazo duniya, yanzu ne ta k'ara tabbatar ma kanta da taa rasa Majeed, daman
Momie ta faɗa mata namiji ba'asha mishi
alwashi, shknan har yayi aurenshi,
Ga wani ciwon kai
daya matsa mata ko barcin ta kasa, ita kaɗai
a ɗaki Abdallah na wurin momie
yayi barci tace a barshi tunda ba tashi yake ba, sai faman shafa confo take a
kai,
Abubuwa sun mata
yawa kamar ita kaɗai damuwa ta
k'are mawa, ga faɗan Abba
kullum maganarshi ta fiddo miji tayi aure, kamar tana zaune a saman kansu,
Tohh ita wama zata
aura? Ita da ba fita take ba ballantana wani yace yana sonta, inma fitar dole
ta kama mata da dogon hijabinta da nik'ab take tafiya, ta saɓa Abdallah a kafaɗa
kamar matar aure, dole aji shakkar mata magana,
Yanzu haka sauran
sati ɗaya lokacin da daddy ya bata
ya cika, koya aura mata duk wanda yaga dama, ta riga ta hak'ura da koma wanene,
tunda ta rasa Majeed bata da wani sauran zaɓi,
Kwana Uku da bikin
Majeed har lokacin bata da wani natsuwa a tare da ita, zata fito dai ta taya
Momie en aikace-aikacen da suka kamata, sai Momie tana janta da fira duk don
taga hankalinta ya kwanta, anma data koma ɗaki
sai wata sabuwar damuwar kuma,
Yauma kamar kullum
ta gama duk abinda take, ta shiga da Abdallah toilet ta sake mishi wanka, tun
kafin ta shiryashi yaketa son ya fita, tana saka mishi kaya kam yabar ɗakin,
Ta ɗauka ɗakin Momie ya tafi, ta shareshi tayi kwanciyarta har
barci ya fara ɗaukarta ta
jiyo muryar Momie tana tambayarta "Ina Abdallah" da ta ɗauka cikin barci ne, sai kuma
ta tashi firgigit,
"Momie ba
wurinku yaje ba?"
"A'ah tunda ya
biyoki rabona dashi" ba shiri Majeeda ta sauko daga kan gadon,
"ni wannan
hegen yawon na Abdallah, yanzu haka yana can yana ɓarna"
"Aikam k'ara
ki nemoshi, don yau yaimun ɓarna kujera
zanyi dashi" tana dariya ta zira
hijabinta,
"Momie ana zauna
mai gida?"
"ni bani miji
da wannan maɓarnacin, na barma Umma
dai" dariya kawai tayi ta wuce, kullum cikin bata dariya suke, Momie da
Abdallah,
Gidan ta shiga zagayewa, lunguna da sak'o da duk inda take
tunanin Abdallah babushi, duk faɗin
gidan babu inda bata duba ba, harta fito tsakar gida, inda ake ajje motoci ma
taa dudduba babu shi, ta k'arasa tana tambayar mai gadi ko yaa ganshi,
"wallahi hajia
da yake na zagaya bayan gida ban lura ba koya fice, kuma saina manta da gidan a
buɗe, duk an duba gidan
bainan?" bata tsaya bashi amsa ba ta saka k'afa zata fice, kuma saita tuna
bata da nik'ab ɗin, da
gudu-gudu, sauri-sauri ta koma ciki sannan ta ɗauko ta dawo,
Momie cikin tashin
hankali take tambayarta,
"Momie ban
ganshi ba bari in duba cikin unguwa"
Abinka da unguwarda babu mutane, yaransu ma basu cika fita
ba, sai en tsararun mutanen data gani take tambaya, anma kowa amsar ɗaya ce bai ganshi ba, tsananin
tashin hankali harta fara hawaye ta cikin nik'abinta,
Harta yanke shawarar
komawa gida ta fasa, tasha kwanar layin bayansu, tana shiga ta hangoshi hannun
wani handsome zaune saman bayan mota yana mishi wasa, sai dariya yake abinshi,
Saida ta saukar da
ajiyar zuciya, sannan ta k'arasa inda suke,
"Ina
wuni" ta gaishe dashi, cikin rashin fahimta yake dudduba kusa dashi,
sannan ya dawo da kallonshi gareta ya tsura mata ido cikin nik'abin data rufe
fuska dashi, yana son garin fuskar mamallakiyar zazzak'ar muryarnan, shikau
Abdallah sai wasanshi yake a jikinshi,
"Yaron dake
hannunka nawa ne, ya fito daga gida" majeeda ta faɗa cikin k'osawa da kallon da yake mata,
"ta yaya zan
gane ba satarshi zaki ba, kina cikin wannan bak'in Abun"
"na maka kama
da mai sata ne? K'ila dai kaike shirin hakan" ta mik'a hannu zata ɗaukoshi aiko ya k'ara mak'alk'ale
mutumin,
"Abdallah" ta k'wala mishi kira cikin ɓacin rai,
"Ayam" ya
amsa da gwarancinshi,
"Zo muje gida
Momie na kira"
"um-um,
uncle" ya faɗa yana k'ara
rik'e mutumin, takai hannu zata ɗaukeshi
da tsiya, ya rirrik'eshi gashi bataso ta haɗa
jiki dashi,
"Don Allah ka
bani yarona in tafi"
"kingama
tsoranki yake, alamar bai sanki ba, ki buɗe
fuskarki idan da gaske kin sanshi" ganin tana k'ara ɓata ma kanta lokaci ya sanyata ɗaga nik'ab din, tsaida komi yayi ya tsaya yana
kallonta, duk yanda yake hasaso kyawunta a zuciyarshi ta wuce nan,
Abdallah na haɗa ido da ita ya k'ara lafewa
jikin mutumin yana daria,
"Auntieee,
wannan ne"
"wannan ne me?
Kazo muje nace" ta jawoshi ya koma da baya yana dariya,
"Don Allah
malam ni Matar aure ce ka bani yarona in tafi"
"Ni naa
tambayeki ne? Ai gashinan saiku tafi, nima da kika ganninan mijin aure ne,
kawai yaronne bani da, kuma ina matuk'ar son yara da saurin shak'uwa dasu"
"nima duk ban
tambayeka wannan ba" sai lokacin yayi dariya sosae harya fara bata haushi,
"wai matar
aure, don kuna kama dashi shine zai zama ɗanki?
Matar aure ma kama ne da ita"
"tunda kaa
gane ina kama dashi, kasan ba satar shi zanba kenan? Ka saukeminshi in ɗauka" ya sauko daga samar
motar ya saukeshi anma yaqi sauka,
"gashinan masu
ɗa"
Yaro fa yak'i sauka, sai daria yake yana rik'eshi,
"ban juwa,
didan"
Duk yanda taso anma
yak'i yarda da ita
"hajia ki
rok'eni kawai in kai miki yaronki gida" bata saurareshi ba taci gaba da
lallashin Abdallah yazo su tafi, anma yak'i yama maida ita kamar k'awar
wasanshi,
"Abdallah
bazaka je gida ba?", ya tambayeshi, shikau harda saurin ɗaga kai,
"Meyasa?"
yayi shiru da yake maganarshi ba k'wari tayi ba,
"mu tafi can
muyi wasan ko"
"eeh janje
didan"
"Yauwah tohh
mu tafi yaron kirki" ya ɗaurashi a
kafaɗa sukai gaba don yaga hanyar
da Majeeda ta biyo,
"Auntie mu
tafi ko? Nima zan wuce gidane yanzu, ko an barmun shi?" batace mishi komi
ba dai tabi bayanshi, suka tafi, sai da sukaje dai-dai gidan tace "tohh
sauke minshi anan" ana saukeshi kau yayi cikin gidan da gudu,
"na gode"
tace mishi kawai, sannan tabi bayan Abdallah, yayi tsaye a k'ofar yana kallonta
harta shige,
Mai gadin ya taso
rufe k'ofa ya ganshi nan tsaye, ya fasa rufewar bayan ya lek'o da kanshi,
"Barka dai
yallaɓai"
"Yauwah baba,
sannu da aiki" ya juya zai bar wurin,
"Aiki da
godia, wurin Alhaji kazo ne?"
"A'ah yaron
Matar gidan dai na maido"
"matar gidan
kuma? Ɗiyar Alhaji dai" harya
fara tafiya ya dawo jin haka, baba mai gadi harda gyara tsayuwa zai fara
tsegumi,
"Shifa
yaron?"
"ɗanta ne, anma yanzu shekara ɗaya kenan da en watanni basu
tare da mijin"
Gaskiya mai gadinnan
akwai surutu, mutumin ya faɗa a ranshi,
"Allah sarki,
nagode sosai baba" ya zaro dubu biyu ya mik'a mishi, ya amsa yana washe
baki, don akwaishi da son kuɗi
"ni keda godia
yaro," sai kuma ya kasa tafiya, yayi shiru yana so yayi ma baba magana,
"numberta zan
baka?" da sauri ya ɗaga kai,
"yauwah baba
za'a samu ko"
"eeh yaro, anma
ka k'aro dubu biyar", yana kallon tudun Aljihunshi, ikon Allah wannan
wanne irin mai gadi ne? Gashi dai tsoho sai tsurku da son gulma, ga shegen son
kuɗi,
Ya kwaso duk kuɗin Aljihunshu dubu uku,
"gashi baba,
daman su kaɗai suka rage"
"tohh shknan
yaro nima rabi zan baka tunda rabi ka bada" baza'ayi haka ba baba ina
zuwa,
Ya koma inda ya aje
motarshi, ya jawota k'ofar gidan, ya dawo ya mik'a mishi dubu biyar cas sannan
yace yana zuwa, ya shiga ɗakin da yake
ya ɗauko wayar bala driver daya
bari chaji ya kawo mishi,
"Gashinan
Alhaji duba, ko hajia Majeeda, ko Majeeda, ko er gatan Alhaji duk yanda kaga an
rubuta"
"Sunanta
majeeda kenan" ya faɗa yana
murmushi, "suna mai daɗi, kuma ya
dace da ita,
Ya maida mishi wayar
yana godia bayan ya ɗauka number,
Abdallah da gudu ya
shige gidan, Majeeda na mishi magana bai tsaya ba saida yaje inda momie take ya
faɗa jikinta yana daria, sannan
taja ta tsaya tana kallonshi,
"Abdallah ina
ka tafine muna ta nemanka?"
"wuyin
uncle" ya fara lallaben Aljihunshi ya ciro chocolates yana bata,
"shine ya baka
wannan" ya ɗaga mata
kai,
"ka daina fita
yawo kaji" nanma ɗaga kan
yayi, sannan ya sauko kuma ya tafi wurin Majeeda ta ɗaukeshi, suka tafi ɗaki,
Faɗa sosae ta mishi harya fara kuka, ta rungumeshi don
batason ɓacin ranshi, ta share hawayen
daya zubo mata,
"ka daina
rashin ji kaaji yaro nah"
"baran kala
fita ba"
"yauwah nima
naa daina maka faɗa" taci
gaba da lallashinshi har yayi barci,
Da dare harta
kwanta, taji wayarta na ringing, ta jawo da duba bata gane number ba ta maida
ta aje, mai kiran dai ya nace da kira gashi barci takeson yi, ta ɗauka kawai batayi magana ba,
Ɗayan bangarenma shirun akayi, harta gaji da saurare
ta kashe ta maida ta ajje, aka sake kira ta kashe wayar ma gaba ɗaya,
0 comments:
Post a Comment