Suna shiga mota kamar ya mata magana kuma
ya fasa, sai da suka shiga gida ya bita har cikin ɗakinta, ko a lokacin jikinta a sanyaye yake.
Ya tsuguna inda take ya ɗaura
hannunshi a saman gwiwoyinta, ta zuba mishi ido tana k'ok'arin kauda damuwarta.
"kina tsoran za'a iya gano HARAMTACCEN ZAMAn da muke ko?" ta ɗaga mishi kai,
"toh waya sani bayanmu dazai iya faɗa musu har su gane? Wannan tsoran naki ne da shakku
kawai matsala na, plz ki daina kinji" tayi murmushi saboda yanayin daya
k'arasa maganar,
"na daina masoyi, kawai gabana ne
yake ta faɗuwa"
"ki manta komai a ranki mana, banason abinda zai rabani dake"
"nima hakan"
Bayan wani lokaci...
SO DA SHAK'UWAne (Amrah A msh)
kullum ke k'aruwa a tsakaninsu, wani kulawan sai tsakanin Majeed da Majeeda,
komai a tare sukeyi, tarairayarta yake sosae kamar k'wai ɗaya a cikin miya, baya shakkar nuna mata soyayyah a
gaban kowa, soyayya suke irin babu irinta a duniya,
Majeed ne ya fito da shirin fita, yasha
kyau cikin farar shadda, yana tsaye yana saka agogo itama ta fito da mayafinta,
"tohh saina dawo masoyiyah, mezan zo miki dashi?" ta mak'ale kafaɗa kamar wata k'aramar yarinya,
"nifa da gske bazaka barni ni kaɗai
ba"
"haba tawan, ya za'ai naje wurin ɗaurin
aure dake?"
"tohh ka fasa zuwa mana"
"Ɗaurin Auren Abbakar ɗin?" ya faɗa yana zaro ido,
"inkin yarda dai na kaima Aunty zainabu Ajiyanki" ta ɗan saki fuskarta,
"Anma bazaka daɗe ba?"
"da an ɗaura aure
zan dawo"
"tohh shkenan muje"
Suka fito tare, a hanya suna tafiya tana tsaidashi, komai ta gani tanaso
ya sai mata, kwaɗayi dai
kala-kala shi kuma ya dinga biye mata,
A k'ofar gidan Aunty zainab ya ajeta, ta
sauka sannan ta lek'o tagar da yake,
"saika dawo," ta mishi kiss a gefen kumatu
"tohh babe, saina dawo" ya ɗaga
mata hannu yana fara'a, saida ta shiga gidan sannan ya tafi,
Tana shiga Aunty ta taso da fara'arta tana mata oyoyo, ta zube saman
kujera, Aunty ta kalleta da mamaki,
"Halan a gajiye kike?"
"A'ah aunty, yunwah dai"
Aunty ta zauna kusa da ita,
"ya gidan naku?"
"lafiya lau Aunty" sannan ta gaisheta, duk ba yanda Aunty ta
saba ganinta ba,
Ta jawo ledanta ta fiddo Apple ta faraci, sai dafe kanta take,
"Aunty nace inajin yunwa, ko saina nema abincin?"
"Tohh ay naga daga gidanki kike, kuma baki sanar dani zaki zo
ba"
"ni ban tsaya na k'oshi ba, ganin zan fito"
"tohh ay yanzu zan ɗaura
na dare" ta mik'e tana dafe da kanta,
"nidai bazan jira ba Aunty, bara na dafa ko cous-cous ne"
"sai dai indomie"
"tohh yana iya" ta nufi kitchen ɗin, indomie ɗinma
saida ta rumurmutsi wata taci hakanan kafin ta dafa, ko dahuwa bata k'arasa ba
ta juyeta ta fito,
Aunty nanan inda ta barta, ta fito tana tafiya tana rik'e kanta, ga wani
irin tashin zuciyah da takeji idanta shak'i k'anshin indomie ɗin, ta daure dai ta zauna, Aunty tace,
"wai lafiyanki?"
"wlhy Aunty ciwon kai nake fama dashi kwanannan, da jiri" taje
zata zauna, jiri ya kwasheta ta kusan faɗuwa
da sauri Aunty ta taso zata rik'eta, ta daure ta ajje indomie ɗin,
"Wai yadai majeeda" sai dai kawai gani tayi majeeda ta sulale
a wurin,
Aiko duk ta rikice, ta shiga kiran layin mai gidanta muhd anma yak'i
shiga, ta kira layin majeed, taa kusan katsewa ya ɗauka,
"kayi sauri kazo yanzu majeeda ba lafiya, kayi sauri plz" bata
jira me zaice ba ta katse,
Shima jin muryarta a rikice, duk hankalinshi ya tashi, bai tsaya sallama
ta kowa ba ya shiga motanshi ya nufi gidan Aunty, tafiyar mintuna kaɗan ya kaishi gidan,
Ganin halin da Majeeda take ya sakashi k'ara ruɗewa, baisan
sanda ya saka hannu ya ɗauketa ba,
Aunty ta biyosu a baya suka wuce Asiti sai kwarara gudu yake, ikon Allah ne
kawai ya kaisu,
Aunty na zaune bayan an shiga da Majeeda, Majeed kam sai zagaye wurin
yake yaje ya dawo, har Aunty zainabu ta gaji tace mishi,
"wai bazaka zauna ba Majeed?"
"Aunty yazan zauna bayan ita tana can
tana shan wahala"
"tohh ci gaba da zagayen ku raba wahalan"
Nurse ce ta fito,
"likita yace zaku iya shiga" tun
kafin Aunty zainabu ta mik'e ya rigata shiga ɗakin,
Abokinsa Mukhtar ne ya hango, ana ce mishi Dr. Shaheed, ya taho da fara'arshi
yana bashi hannu,
"ka ce mana Amaryar da aka hanamu rakiyar ango don karmu ganota ne
aka kawomin har inda nake"
Majeed yayi daria sosae
"kasan dai yanda abun yake, anma ay har gida naso muzo da ita"
"har yanzu na biyo bashi kenan?"
"yanzu dai Aboki ya jikin nata?"
Dr. Shaheed, Ya washe baki tare da k'ara mik'a mishi hannu,
"ina tayaka murna"
"banson iskanci fa, matata na kwance asibiti kace kana tayani
murna, meke damunta plz?"
"Koma menene ai aikinka ne mutuminah"
"ni kuma? Kaifa ɗan iskane
rashin lafiyar matar tawa ma saika jamun rai?" Dr. Shaheed sai dariya yake
mishi ganin ya damu sosai yace,
"Amaryarmu tana ɗauke da juna
biyune, na tsawon sati shida"
Ya fiddo duka idanunshi cikin
tashin hankali ne koko mamaki? K'ila kuma duk tsantsar farin ciki ne,
"ciki shaheed?"
"k'warai kuwa Aboki, idanta farka zaku
iya tafiya, anma bayan ka bani goron Albishir ɗina" ya faɗa
cikin zolaya,
Aunty Zainabu dake tsaye a k'ofan tace, "Ai wannan babbar Albishir
ne Dr, ni da kaina zan kawo maka"
"Tohh Aunty godia nake,"
Duk majeed yayi sukuku har Dr.
Shaheed ya fita, Aunty ta wuceshi taje inda Majeeda take kwance, idanuwanta a
buɗe ta farka, anma hawayene
kawai ke zuba a idanunta,
"Miye haka Majeeda? Keda zanga murna da farin ciki a fuskarki, miye
na kuka kuma?
Shiru tayi ta kasa koda k'ifta idanunta ne, sai dai hawayenda takeyi
kawai, Aunty Zainabu tayi maganar harta gaji,
"Aunty Zainabu ina ganin fa murna ce
taima Majeeda yawa, wannan kyautah ce Allah ya bamu da ba kowa yake bama
ba"
"hakane, ayni namayi tunanin ko ciwonne"
"A'ah da akwai matsala daya
faɗamun"
"hakane fa" ta zunguri Majeeda,
"Tashi mu tafi tohh, tun yau kin fara tunanin ciwon nak'uda"
saida Majeed yayi dariyar dole,
A hanya ta dinga kiransu momie tana musu Albishir, Abdul-Majeed yana
driving ya juyo,
"wai ya kike faɗa musu tun
yanzu Aunty?"
"tohh sai yaushe zan faɗa
musu? Kaga kuwa yanda suke murna" shiru bai ce mata komi ba, har gidanta
suka ajjeta, tana k'ara nanata musu shawarar likita yanda za'ana kula da
Majeeda,
Saida ta fita sannan Majeeda ta samu damar fashewa da kuka, baiyi
k'ok'arin lallashinta ba har suka isa gidansu, tun kafin ya gama parking ta
fito daga motan har tana shirin faɗuwa,
ta ruga ta shige ɗakinta,
sulalewa k'asa tayi ta ɗaura kanta
saman gefen gadon tana kuka,
Ya daɗe a tsaye jikinshi a sanyaye,
sannan ya matsa inda take, ya mik'a hannu zai jawota ta buge hannu, ya k'ara
mik'a hannu ta tureshi tana ci gaba da kukanta, cikin sanyin jiki ya zauna
gefen gadon, sai kuma ta maida kanta samanshi sannan taci gaba da kukan,
Hannunshi yasa yaci gaba da shafar gashin kanta,
"Ya isa hakanan tohh, meye na kuka" ta k'ara k'arfin kukan
nata,
"Miye na kuka? Idan banyi kuka ba dariya zanyi saboda ina murna da
wannan abun dake jikina?"
"kenan baki murna saboda ɗana
yana a jikinki?" tayi tsit tana share hawaye,
"Anma bata wannan hanyar ba Yaya majeed"
"saita wacce hanya? Kenan kuwa har abada bazamu ga ɗanmu ba, kina nufin har yanzu
baki kallona a matsayin mijinki?" ta shiga girgiza kai,
"abunda ya kamata muyi murna da farin ciki ne, ki daina kallon
cikin dake jikinki a matsayin wanda muka samu a HARAMTACCEN ZAMA, ki kalleshi a
yanda kowa ke kallonshi, kema kina sonshi ko?" ta daga mishi kai,
"nima inason duk wani abu dazai fito a jikinki, ina sonki sosae Majeeda"
Ta tashi taɗan rage
tsawonta, ta kwantar da kanta jikinshi tana wasu hawayen, ya ɗago da fuskarta
"bazan taɓa bari kiyi
kuka ba Majeeda indai ina tare dake" ta juya bayan hannunta tana murmushi
zata share hawayenta, ya rik'e hannun,
"na miki alk'awarin share hawayenki,
a duk halin da kika tsinci kanki, na farin ciki kona damuwa, ina tare
dake"
Ya saka harshe yana share mata hawayen, sai kukan natama ya koma na
farin ciki, ya haɗa bakinshi
da nata yana kissing ɗinta, har
saida yaga hankalinta ya kwanta, sannan ya saketa,
Tun daga ranar Majeed ya k'ara ninninka kulawan da yake bama Majeeda,
tana ɗauke da cikin ne kawai anma
komai yi mata yake, su Umma ma kullum cikin aiko mata ciye-ciye suke, ba'a ɗaukar lokaci zatazo ganinta,
Cikin nada wata bakwai momie tace zata maida ita gida, ya marairaicema
Aunty Zainabu,
"Aunty Zainabu yanzu mena gaza wurin yima majeeda? Ynzu kun tafi da
ita wata nawa kenan bazan ganta ba? Plx Aunty don Allah ku barmun matata"
"Aiken momie ne fa ya zance mata knan? Haihuwar farko ce yama za'ay
ka iya kula da majeeda"
"Tohh Aunty idan na samo mata mai aiki fa?"
"har k'ara hakan, anma dai ka barta
ta koma gida gsky" duk ya rasa yanda zaiyi da Aunty Zainabu kamar ya fasa
mata kuka, ya kalli majeeda,
"kinason kije gida ki barni anan?" kallon Aunty Zainabu tayi
sannan ta maida kallonta ga Majeed,
"Idan kace A'ah bazan je
ba" Aunty Zainabu ta kalli Majeed
tana ɗaukar jikkarta,
"Nasan ma A'ahn zakace, ni naa daina zuwa gidanku inga rashin
kunyarnan"
"Hak'uri za'ai Aunty"
"oho, ku kuka sani dai"
Majeeda ta fara k'ok'arin tashi saboda yanda cikin yayi girma, "Aunty bara in rakaki
"yi zamanki, Allah dai ya raba
lafiya" su duka amsa da "Ameen",
Ya dawo kusa da ita bayan Aunty ta tafi,
"Ban kyautah ba ko Majeeda?"
"A'ah itama Aunty ai taga kana kula dani sosai"
"Bazan iya jurar rashinki ba koda na kwana ɗaya ne"
"nida babynmu ma bamuso muyi nisa dakai"
"Yauwah tawan" ya kwantotah
jikinshi, ya fara shafar cikinta,
"babyna nason hutu, muje ku kwanta" ya fara k'ok'arin ɗaukarta, ta rik'o hannunshi,
"nifa na gaji da kwanciyarnan, yanzunnan fa ka taso ni zuwan
Aunty"
"Tohh ay nafison kina kwanciya ku
huta"
"nidai hakanan, likita ma yace ina motsa jiki ai"
"tohh naji kuɗan
zauna"
Ta kamo hannunshi ta rik'e cikin sanyin murya tace "Yauma bazaka
kaini wankin kan ba?" ya k'ara damk'e hannunta cikin nashi,
"ki gane mana, nifa banso ku wahala ne"
"nidai gsky yayi datti sosae"
"tohh zan wanke miki, shknan?" ta rik'e bakinta tana daria,
"ina ka taɓajin namiji da wanke kai?"
"A gidan Majeed da Majeeda" ya bata amsa yana murmushi,
"meye a ciki? Nima fa ina wanke nawa"
"hakane tohh muje toilet ɗin"
"toh ina zuwa" ya tafi da sauri ya kai mata doguwar kujera a
toilet ɗin, ya haɗa ruwa mai ɗumi
sannan ya taho ɗaukarta,
Harta k'ok'arta ta mik'e, tana tafiya dak'yar,
"Yanzu sai dai kin tashi kin bama babynmu wahala?" ya taho zai
kamata,
"nidai ka barni plz, nan da toilet ɗin"
"naji taho in rik'e ki tohm" dak'yar ya barta ta tafi ita kaɗai, ya gyara mata kujera ta
zauna,"
Hannunshi ya ciko da shampoo ya lafta mata, sannan ya fara gogawa a
hankali kamar wanda baison taɓa kan, ta
saka hannuwanta duka biyun a kumatu tana kallon ikon Allah ta mirrow,
Kusan 15mnts kumfa bai gama haɗewa
ko ina ba, ta saka hannu ta shafi kan,
"Yaya majeed a haka yaushe zai wanku?"
"zai wanku mna, bazan dai miki yanda zakiji zafi ba"
"wankin kai ma har zafi ne dashi? Nidai bara inyi da kaina,
"in barki kisha wahala kenan, indai kin gaji a bari sai gobe"
haka tana ji tana gani ya dinga lallaɓawa
a hankali yana wanke mata, daya murza sau ɗaya
sai ya kwaraya ruwa, dak'yar ta mishi dubara tana wankewa yana zuba mata ruwa,
Babu inda bai jik'e ba a jikinsu kafin ya gama wanke mata kan, sai da
duk suka sake wanka sannan suka fito,
Akazo wurin drying, da hand dryer yake busar mata da kan yana sharcewa,
haka ya dinga soka comb ɗin yana
zarewa, ba don ya shartu ba ya tattara mata abinta ya k'ulle,
Yau taa rigashi farkawa, a hankali ta janye hannunshi daga jikinta, ta
kara mishi pillow, sannan ta taho a hankali zata sauka daga saman gadon, sai
dai taji ya kwanto jikinta ta baya, yana shak'ar qamshin gashinta, ta sauke
ajiyar zuciya tana dariya,
"yau na makara ko? Har kina shirinmin wayau"
"A'ah da sauran lokaci fa, ni ɗinma
na fasa fita, kai kwanciyarka"
"nak'i wayon naki, kingama tashi na" idonshi cike da barci ya
sauka daga gadon, daman basu daɗe
da komawa ba bayan sunyi sallah, ba don tanaso ba ta koma ta kwanta,
Kamar kullum saida ya tabbatar ta cika cikinta, sannan shima yaci, ya
gyara mata kwanciya bayan ya aje mata duk abinda zata buk'ata sannan ya fita
office,
Duk bayan mintuna kaɗan zai
kirata yaji ya take, kafin lokacin tashi yayi zuwanshi uku yaga koda abunda
take buk'ata, ko kaɗan baison ta
nema abu ta rasa,
Da marece ya taimaka mata ta shirya tsaf, shima da shirinshi ya rik'o
hannunta suka fito,
"Yaya Majeed baka faɗamun inda zamuje bafa"
"kedai kizo muje"
"plz ka faɗamin Yayanah"
"babynmu zamu k'arasa ma
sayayya" saida ta tsayar da tafiyarta tana mishi kallon mamaki,
"Yanzu siyayyar baby har akwai abinda ya rage mana?"
"Shine zamuje mu gano ai, idan an kawo wanda bamu siya ba"
mamaki daya mata yawa ma kasa cewa komi tayi,
Sun kwaso siyayya sosae na baby da nata itama, ɗinkuna harta fara gajiya da yinsu, kayan babynma
babu abinda basu siya ba anma duk saida ya k'aro, da ɗan gadonshi mai shegen kyau, shima kala biyu kenan
suka siya, duk wani abun da zasu buk'ata sun siya sun aje tun kafin watan
haihuwar yayi,
Watan haihuwarta ya kama, momie da kanta ta sake mishi maganar komawar
Majeeda gida, anma ya rufe ido ya bata ha'kuri kawai, haka Umma ma taso ta koma
wurinta anma ya hana, sai dai ta tura mata Zahra tana taimaka mata, sunajin daɗin canjawarsu,
****
Tun cikin dare ta fara jin cikinta
na juyawa, ana zungurinta, haka ta daure tayi sallahn Asubah tana ta k'arfin
halin kar Majeed ya gane batajin daɗi,
duk da Zahra nanan saida ya tabbatar ta cika cikinta, da duk wani abunda ya
saba mata, sannan ya fita office,
Haka ta takure wuri ɗaya tanajin ciwon na k'aruwa, ko Zahra ta shigo sai
dai ta daure kawai tana murmushin yak'e, harta gama duk abinda take ta dawo ta
zauna tayata fira,
Sai haɗa zufa take ciwo na cinta ita
kaɗai, tun tana iya maida ma
Zahra harta kasa, ta fara k'ara tana rik'e cikinta,
Zahra duk ta ruɗe ta kira layin Majeed, yana dai dai kiran Majeedar
sai gashi ta kirashi, yayi saurin ɗauka
tun kafin tayi magana ya rigata,
"Zahra Abun yaazo ne?"
"eeh Yaya kayi sauri kazo tana wahala
sosae"
"ganinan yanzu" tun kafin su gama waya ya fito daga office ɗinshi, cikin hanzari ya shige
motarshi ya nufi gidan,
Kafin suje Asibitin Umma ta rigasu, kusan tare sukaje da Aunty Zainabu,
haka aka shigar da Majeeda, idanunshi duk sunyi jajir saboda tausayinta, kamar
ya tayata kukannan yakeji,
Ya kasa zama, ya kasa tsayuwa, yana jiyo kukanta har cikin ranshi, duk
yanda Umma taso ya Zauna ya nutsu ya kasa, saima ya matsa nesa dasu yaci gaba
da safa da marwanshi,
Tasha wahala sosai har kusan la'asar bata sauka ba, har ana niyar ai
mata aiki, cikin ikon Allah sai ga kai ya fara fitowa, dak'yar bayan tasha
wahala, ta silalo k'aton jaririnta namiji,
Kyakkyawan gaske dana kasa tantance da
wanda yake kama a cikinsu, dogon hancinshi da gashin girarshi duk na Majeed ne,
sai ɗan k'aramin bakinshi da
fararen idanuwanshi na Majeeda, gashin kanshi mai sulbi ya kwanta, kamar na
babanshi,
Bayan ankai Majeeda inda zata huta akace su shiga, tunda Majeed ya ɗaukeshi sau ɗaya ya gani ya maida ma su Umma, ya koma wurin matarshi
don duk damuwarshi tana a kanta
Awa shidda tayi aka sallameta, Asibitin cike da family ɗinsu, haka suka cika motoci suka nufi gidan Majeeda
da Majeed,
Anan ma saida Umma taso ta tafi da ita
gidanta tayi wankan Arba'in, anma Majeed yak'i amincewa, shida kanshi ma yayi
driving don kar Umma tace dole sai an kaita can,
Murna sosae su Abba sukai da jaririnnan kasancewarshi jikansu na farko,
duk da a yanzuma aunty Zainabu na ɗauke
da juna biyu,
Kyautar tsantsararren gida Abba ya musu, zasu koma bayan suna,
Kullum gidan cike da Mutane kamar a ranar
ne suna, su Majeeda ba zama sai hidima da jama'a kullum Majeed cikin k'orafi
yake bata bashi lokaci,
Zahra takai mishi abinci yace ta turo mishi da Majeeda, fitowarta wanka
kenan, saida ta ɓata lokaci
wurin shiryawa, nanma dak'yar k'awayenta suka barta ta tafi, jaririn na kukata ɗaukeshi kawai suka tafi ɗakin babanshi,
Tana shiga ya maida k'ofar ya kulle, da dubara ta ajje babyn, tun kafin
tayi magana ya haɗa bakinshi
da nata, sun daɗe a haka tun
suna a tsaye har suka zauna gefen gado, kukan babyn ya saka suka tsagaita, ya
zauna yana kallonsu ta saka mishi abincinshi a baki,
"ko kewata bakiyi ko?"
"Fiye da kaima Yaya Majeed"
"ban yarda ba, tun haihuwar yaronnan
kika daina kula dani, baki damu da cina ba, baki damu da kizo kiga yanda na
tashi ba, idan bana kiraki a waya ba bazaki kirani ba"
"ka yarda dani Yaya Majeed komai nake kana cikin Raina, ni kaina na
k'agara a gama hidimarnan" ya mik'a hannu ya ansheshi bayan yaa gama sha,
"Na kaasa koyon barci ba tare dake ba"
"nima haka dear, yanzu ai na kwana
biyu ne kawai"
"Yayimin yawa fa,"
"kaaci abinci?" kai ya girgiza mata, da sauri ta tafi ta zubo
mishi, ta zauna ta bashi saida ta tabbatar ya k'oshi sannan ta k'yaleshi, taa
daɗe har saida aka mata waya tayi
bak'i sannan ta koma ɓangarenta,
Tana ganinsu ta saki fara'a,
"laah! Asiyah kardai ku cemun kune sai yau"
"donma kin ganmu kenan, mu da ba'a faɗa nawa ba?"
Fatima tace "ke kike maganarmu, yanda suke da hafsatul kiram ma ko
ita bata faɗa mata ba" sai da gabanta
ya faɗi da suka ambaci hafsatul
kiram, na'urorin jikinta ne suka dakata da aiki na wani lokaci suna magana ma
anma ko saurarensu ba tayi,
Sai da Asiya ta taɓota, sannan
ta dawo daga tunaninta duk ta rikice, ta fara murmushin yak'e,
"Wa? hafsatul kiram? Kema kinsan bata k'asarne, kuma na rasa
numberta tunda ta canja sim"
"itama haka tace sanda na faɗa mata haihuwarki, halan tunda
ta tafi bakuyi waya ba?" kai Majeeda ta ɗaga
ma Fatima, sai kuma ta zaro ido da taji abinda tace,
"kika faɗa mata na
haihu, ya akai kika faɗa
mata?" duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda duk ta rikice lokaci ɗaya, Aunty Zainabu dake
tattara wankin baby ta kalleta shek'ek'e,
"miye don An faɗa
mata?" ta k'ara washe hak'oran yak'e,
"Ba komi Aunty kawai dai naso in bata mamaki ne"
Fatima tace "kinga barama na mata waya ta fara miki k'orafin rashin
kiranta tun yanzu" Majeeda sai k'ok'arin dai daita nutsuwarta take, ita
tsakaninta da Allah ko tunawa da hafsat bata sonyi, tana cikin tunani Fatima ta
mik'o mata wayar,
"Aminiyatah!!" inji hafsat,
"Na'am, Amaryar Umar shikenan an manta da mutane babu wani
zumunci"
"Haba! Ni zance miki haka, har ki
sake aure bazaki sanarmin ba?"
"Wai Aure? Ni ɗin?"
"tohh daa wa?"
"kinga besty zan kiraki, kinsan hidimar jama'a, yaushe zaki
dawo?"
"nan kusa, amma bazan faɗa
miki ba nima, ki gaishemin da baby" a sanyaye tace "zaiji"
sannan ta saki ajiyar zuciyah bayan ta kashe wayar,
Basaina faɗa muku ba,
kunsan nutsuwa taa k'are ma Majeeda a wannan rana, haka ta yini da tunani
sosae, duk taa shiga damuwa,
Ranar suna yaro yaci suna
Abdallah, ba k'aramin shagali akai ba a wannan rana, gida yaa cika da mutane,
Anyi abinciccika kala-kala, nama ko ko shi kaɗai
kakeso sai kaci ka k'oshi, ga gassasun kaji da soyayyun ma,
Kayan barka ma Majeeda ta samesu harta rasa wurin ajjewa, banda kudaɗen data samu, gida cike da
jama'a babu masaka tsinke, muryarta harta soma shak'ewa saboda hidima da
jama'a,
Tana cikin canja kaya text ɗin
Majeed ya shigo mata,
"Hey babe, i cant stop thinking about uh koma me nake ke nake gani,
ina kewarki plz bzan ganki ba?" sai da ta ɗanyi murmushi sannan ta maida mishi,
"miss uh more dear, hidimar jama'a sai a hankali, zaima zama abun
magana idan nace zanzo"
"plz babe, kwalliyan kawai zan gani" sai da ta ɗauka lokaci sannan ta maida
mishi amsa, saboda yanda mutane keta shigowa,
"ka duba pics a whatsapp yanzu"
"nidai ban yarda ba, ga frnds ɗina
ma zaku gaisa, sunata so su ganki"
"Wlhy babu damar barin ɗakinnan
fa, muyi waya dasu mana?"
"Shikenan bazaki zo ba"
"M srry nawan"
"owk ki samamin lokaci da dare plz"
Bata mishi reply ba wata frnd ɗinta
ta anshe wayar, suka ci gaba da fira, haka a gajiye ta k'are hidimar, bata samu
zuwa ba sai dai suka sha waya da dare,
Washe gari su Aunty Zainabu suka dawo gyara mata gida saboda yanda aka ɓata ko ina, tare da wasu
mutanenta da Zahra suka shiga gyaran,
Tana can cikin bedroom ɗinta ta fara jiyo magana kamar ta hafsatul kiram
sama-sama, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa,
ta tashi a hankali take tafiya zata lek'a taga kowacece, sukai kociɓus da ita tana shirin shiga
bedroom ɗin,
Sai da taja ta baya kamar wacce taga Abun tsoro,
"Amaryar jego"
"ke kuma haka ake dawowa babu labari?"
"daman ayna faɗa miki
mamaki zan baki" ta k'arasa inda Abdallah yake kwance ta ɗaukeshi,
"Masha Allah, wannan kyakkyawan
babe"
Ita dai Majeeda binta kawai take da murmushin yak'e ko zama ma taa kasa
yi, hafsat ɗinma ganinta take kamar wata
mutum daban,
"Ki zauna mana, kinsan ina da tarin tambayoyi sosae a baki na"
duk taa ruɗe take magana,
"tambayoyi kuma? Ay kya bari dai kisha ko lemu ne"
"Haba gidanki nazo fa, kamar dai wata bak'uwa"
"saiki zama bak'uwar mana tunda zuwanki na farko ne, kedai bara na
kawo miki"
"nidai ki barshi ki zauna" bata
saurareta ba ta nufi hanyar fita, tana mata magana anma saida ta fita,
Zahra ta rok'a Alfarma, ta kai mata drinks ɗin, sannan ta samu wuri inda su Aunty Zainabu suke
ta Zauna, don ganin hafsatul kiram take kamar wata surukarta,
Saida ta aiko kiranta ba don taso ba ta tashi ta tafi,
"kin ganmu nan aiki muke ta fama dashi"
"Shine kuma zaki barni ni kaɗai
zuru"
"kizo mu tafi falon mana kamar wata
bak'uwa" ta mike zata tafi, hafsatul kiram ta kamo hannunta ta zaunar da
ita, kanta ta dafe daya fara sara mata,
"Daga ganin yanda kike kauce-kaucennan ya tabbatarmun da baki da
gaskia, plz majeeda karki tabbatarmun da zargin da nake miki na HARAMTACCEN
ZAMA kuke da Majeed"
"kinga wannan ba lokacin da zamuyi maganar nan bane,"
"sai yaushe zamu yita? Ko kina nufin wani auren kikai kika fito
sannan kuka maida aurenku?"
"keni babu wani auren da nayi, daman can wasa nake miki babu wani
raba auren da mukai da Majeed" ta faɗa
kanta a k'asa,
"da gaske kike?" hafsat ta
tambayeta tanason haɗa ido da
ita,
"da gaske mana"
"k'arya kike Majeeda, akwai yanayin da mutum zaiyi wasa da kuma
yanayin da mutum zaiyi magana a gane gaske ne, yanda kukai aure da Majeed babu
abinda bazaku iya yi ba"
Kuka ta fashe dashi, don kalmomin da zata kare kanta sun k'are mata,
Hafsatul kiram ce kawai tasan matsalarta, kuma itace rufin asirinta, tasan zata
bata shawara mai kyau,
"ina sonshi hafsa, ina matuk'ar sonshi, bansan ta yanda akai na
fara sonshi ba, anma bazan iya rayuwah babushi ba, ke kaɗai kikasan sirrinmu, shiyasa muka yanke shawaran
muci gaba da rayuwanmu a haka, koda mun faɗa
a gida tsinuwa ne kawai, Bama zanso abinda zai rabani dashi ba" hafsatul
kiram hannunta har kyarma yake,
"kina nufin bayan ya miki saki Ukun kuke zaune a tare?"
"eeh don Allah ki taimaki rayuwatah karki faɗa ma kowa, wlhy bazan iya rayuwa babushi ba"
duk ta rikice mata, tana kuka tana rok'arta, sai rirrik'eta take,
"plz hafsa kicemun bazaki faɗa ma kowa ba"
"Abunda naketa faɗa miki kenan Majeeda, anma ko sauraratah bakiyi ba,
Yanzu idan kuka mutu a haka me zakuce da Allah? A haka zaku zauna kuna tara
yara? Wata k'ila ni kaɗai nasan
sirrinku a yanzu, kuna tunanin harku mutu Allah bazai to na asirinki ba? Duk
son da kuke yima junanku bai kamata kuyi irin wannan zaman ba, kiyi tunani
wannan ba soyayyah bace da zaku kai kanku da halaka, in banda abunki....."
"Plz hakanan nidai, naji shawaranki,
nidai kicemun bazaki faɗa ma kowa
ba"
"Abinda ya dameki kenan? Naji bazan faɗa ba Majeeda, sirrinki da yafi wannan ma ni mai rik'e
miki ce, wannan Alk'awari ne tsakaninmu"
Cikin farin ciki Majeeda ta rungumeta tana murna,
"Na gode sosae Aminiyatah"
"babu godia tsakaninmu"
Sannan ta ɗago
fuskarta tana ci gaba da murmushi,
Cak, fara'ar fuskarta ta ɗauke
kamar wacce aka faɗa ma sak'on
mutuwa, jikinta yahau rawa, hango Aunty Zainabu da tayi tsaye a k'ofa ta tsura
musu ido,
0 comments:
Post a Comment