Da safe tana kunna wayarta kiranshi ne ya fara shigowa, ba
tare data duba bama ta ɗauka,
"Assalamu
Alaiki" ya faɗa da daddaɗar muryarshi cikin nutsuwa,
"Wa'alaikas
salam," ta amsa mishi,
"Hajja Majeeda
ina fatan kin tashi lafiya" mamaki ne ya kamata sosae yanda har yasan
sunanta,
"Yi hak'uri
don Allah ban gane mai magana ba"
"wanda kike
tsammanin kiranshi ne, ko kuma nace wanda kike tunani a halin yanzu"
"Banfa gane
mai magana ba"
"kina neman
k'arin bayani dai, anma daɗewarmu a
jiya, bai kamata ki sauri mantawa dani haka ba, kamar yanda nima na kasa daina
ganin kyakkyawar fuskarki"
"Shine kuma
akace dole sai nayi tunaninka? Don Allah malam na faɗa maka fa ni matar aurece" ta faɗa da alama ya fara ɓata mata rai
"Ajiyan fa
kamar naa yarda, kafin in gano gaskia, don Allah majeeda mu duka ba k'ananun
yara bane, ki bani dama in faɗa miki
abinda ke tafe dani" shiru ta mishi, hakan ya bashi damar ci gaba da
magana,
"Sunana
Shaheed, anma family namu sunfi kirana da sarki"
"sarki?"
ta maimaita, ba tare da taa sani bama,
Yayi er dariya
"da ina yaro kuka ne dani, shine mama na ta samun sarkin kuka"
Dariya ya bata, ta
rik'a abinta ciki-ciki tana saurarenshi,
"ina rik'e da
kamfanin mahaifina ne a halin yanzu, bana aikin gomnati, naayi karatun gaba da
secondry har zuwa master's, sannan kuma kamar yanda na faɗa miki ina da Mata shekararmu biyar kenan da aure,
Allah bai bamu haihuwa ba, ban taɓa
tunanin auren MATA BIYU ba, sai jiya da na ganki, kallo ɗaya kika kwanta min a rai, Allah ya jarabceni da
soyayyarki, don Allah Majeeda ki bani dama, ki shigo rayuwarmu nida iyalina,
ina matuk'ar k'aunarki,
Shiru tayi kamar
mai nazari, hakanan taji hawaye nason zubo mata,
"Don Allah
kice wani abu Majeed, kice kin yarda, a shirye nake dana miye miki gurbin
tsohon mijinki, na zame ma Abdallah tamkar mahaifinshi, ki amince dani, ni
masoyinki ne na gaskia"
Kasa rik'e kukanta
tayi, ta kashe wayar kawai ta jefar da ita, taci gaba da kukanta da ita kanta
bata san dalilinshi ba, sai da tayi mai isarta, sannan ta shiga toilet ta wanke
fuskarta, ta fita daga ɗakin tana
jinshi yana sake kira ko kallon wayar batayi ba,
Kamar mai tsoron
wayar ta kasa komawa ɗakin duk da
taa gama abinda take, ta nemi wuri a falo ta fara kallon dole har marece yayi,
sannan ta koma ɗakin,
Miss calls ɗinshi 99, ta kashe ta gaba ɗaya ta tura ta jikka ta ajje,
wani irin nauyinshi takeji, don yaa wuce saurayi tunda harda Mata, zai kai irin
35 haka, wani irin yanayi takeji a kanshi, anma ta rasa ta yanda zata fassara
yanayin, bata ɗauka bayan
Majeed ba akwai namijin dazai iya tsaya mata a rai haka, ita tayaya ma zata
fara soyayya,
Kwananta biyu
bata kunna wayar ba, sai ana uku, gobe kenan lokacin da Daddy ya bata zai cika,
tana gyara ma Abdallah kayanshi ya shigo da gudu,
"Auntie,
Momie na kiya" ya koma da gudu yana faɗa
mata, tana tambayarshi 'ina Momien' ko tsayawa baiyi ba,
Tana zuwa momie ta
faɗa mata bak'one tayi, ta koma
ta sako mayafi sannan ta fita,
Can ta hangoshi
da Abdallah saman cinya sai surutu yake zuba mishi, hannunshi choculate har
babu hannun rik'ewa, yana hango ta ya kasa daina kallonta, har tana harɗewa ta samu dai ta k'arasa,
taja kujera ta zauna, sannan ta ɗan
zamo ta gaidashi,
Ya amsa yana ta
fara'a, har lokacin idonshi na kanta,
"ke kuma kalan
naki salon horan kenan Majeeda?" ta k'ara k'asa da kanta tana wasa da
yatsunta,
"Anan ɗinma babu amsa? Yau kwana nawa
kin kashe waya da sai dai ki jini asibiti, kasa daure wa nayi yau nazo da
k'afafuna sauraren Amsa"
"hhm"
tace da alama duk ta takura da zaman, haka amsarta ta kasance, sai kuma
"eeh" da "A'ah" shi kaɗai
yake zuba surutunshi harya lura da yanayinta,
"Da alama yau
baki cikin yanayin kodai sai a waya zaki bani amsar" da sauri tace,
"toh shiknan" sai da ya murmusa, "in kuma naji a kashe gobe ki
k'ara ganina" murmushi kawai tayi, ta mik'e ta tafi,
"ba
bankwana?" ta kasa juyowa,
"Allah ya
kiyaye hanya"
"Ameen"
ya faɗa yana sauke Abdallah, bayan
ya cika mashi aljihu da kuɗi,
Ya juya zai shiga
motarshi saiga Daddy ya shigo, ya tsaya harya fito sannan yaje ya gaisheshi har
k'asa cikin ladabi, ya tashi zai tafi ya tsayar dashi,
A gurguje,,,,,,,,,
Daddy yace
"sai dai ban ganeka bane" cikin ladabi yace,
"Sunana Shaheed
ibraheem imamu Abba, nazo wurin Majeeda"
"tohhhh,
Alhaji ibraheem dai wanda na sani?"
"eeh
Abba"
"tohh masha
Allah, idan ka koma gida saika turo iyayen naka, nan da wani ɗan lokaci sai a...."
Don tsabar jin daɗi ma baisan sanda ya katse Daddy
ba, "Da gaske Abba" wani irin
kallo ya mishi na rashin ganewa sannan ya gane bai kyauta ba, daya saka
k'ok'onto a maganar, yaci gaba da washe baki ba kunya Shaheed kema Daddy godia,
Washe gari lokacin
daya ɗibarma Majeeda ya cika, tunda
safe data shigo gaisheshi ya tsayar da ita,
"kina sane da
yau ne lokacin dana ɗibar miki ya
cika"
"eeh Abba,
bani da wani zaɓi, Insha
Allah zanyi biyayya ga duk mijin daka zaɓamun"
"Tohh tashi
kije, Allah ya miki Albarka, daga yau ki fara shirye-shiryen bikinki nan da
wani ɗan lokaci" wani irin faɗuwar gaba taji,
"Ameen
Daddy" ta mik'e jiki ba k'wari tabar ɗakin,
tohh anma meyasa bata faɗa ma Daddy
Shaheed ne zaɓinta ba? Kuma dai gani take
kamar yaa fasa don tun bayan tafiyarshi, bai nemeta a waya ba, koba wannan ma
yanzu tafiso Daddy ya sake mata wani zaɓin
da kanshi, don ta samu ta mishi biyayyar data kasa a baya,
••• ••• •••
An kusa bikin
Zahra, sai aka saka lokaci ɗaya, Duka
bangarorin sai shirye-shiryen biki suke, su Majeed anzo biki, shi yanzu
hankalinshi kwance, soyayya da kulawa babu wanda bai samu a wurin Aisha, tuni
ya manta da komai ya rungumo matarshi don ba k'aramin so take mishi ba,
Majeeda ma tunda
hidimar bikin ta kama, ta kwantar da hankalinta, bama kamar da taasan Shaheed ne
zata aura, ta kasa yarda ne, anma wani ɓangare
na zuciyarta faɗa mata yake
ta fara kamuwa da soyayyar Shaheed,
Ansha shagalin
biki, garin Mashi aka kawo mana Zahra😉, Majeeda kuma Aka ajeta Katsina
Layout, taci kuka sosai, kamar shine aurenta na farko,
Da dare ya kirasu
ita da uwargida domin musu nasihar zaman lafiya, tana zaune kafin uwar gidan ta
fito taa tsura ma wani hotanta dashi ido, sunyi kyau sosae tana tsaye ya
rungumota daga baya suna dariya, kyakkyawahce anma bata da haske sosae da ɗan k'aramin jikinta mai kyau,
Jin tafiyarta ne
yasa Majeeda ta daina kallon hotan ta maida kanta k'ansa, ta zauna kujera mai
kallon wacce suke sai k'amshi take zubawa, da yake Maryam akwai tsafta,
Sai da ta ɗago ta kalleta ne, kamar ba
itace a hotonnan ba, tayi wata uwar k'iba sosae, irin hajiyoyinnan, cif ta cika
kujera mai zaman mutum ɗaya, babbar
mace mai halin dattako, bai ɗauki wani
lokaci yana musu bayani ba, ya sallamesu kowa ta koma ɗakinta,
Zaman su da Maryam
sosai takejin daɗinshi, tana
janta a jiki, har dangin shaheed take janta kasancewarta mace mai zumunci, da
fahimta, ɓangaren Shaheed ma bata da
wata matsala, yana bata kulawa sosai yakeji da iyalanshi, bata da wata damuwa
yanzu,
Sai dai kewar
Abdallah da yanzu yake hannun Umma, kowa yaso a bar mishi shi, sai daga k'arshe
suka hak'ura aka barma Umma,
Watansu Uku da
aure Allah ya albarkaceta da juna biyu, ba k'aramin farin ciki Shaheed da
Maryam sukayi ba, kusan ma Maryam duk ta fisu Murna, tun daga lokacin ta ɗaukema Majeeda duk wata
hidimar gida, ita take kula da ita, sai abinda takeso za'a girka, Maryam mace
ta gari ce sosae, kusan tare suke rainon cikin,
Har mamakin Maryam
take, mace mai kawaici da k'ok'arin danne kishi, irinsu kaɗanne a duniyar nan, ko godiya take mata sai dai tace
"banson haka
fa Majeeda, ni ban taɓa kallonki a
matsayin kishiya ba sai dai er uwa, abinda muka daɗe muna Addu'ar nema ne da Shaheed, Allah bai bamu
ba, kuma yaa nufeki da samu, ina tayashi son duk abunda yakeso, wallahi ji nake
duk ɗayane"
"Gaskiyarki
Auntyna, ina yima kowacce mace Addu'ar samun kishiya ta gari kamarki"
Maryam tayi daria,
"da kuma
macce ta gari kamar ki ba" sukai dariya gaba ɗaya, kamar ba kishiyoyi ba,
Cikin Majeeda nada
wata hudu, k'awar Maryam tazo ta iskesu suna fira da Majeeda, sai dariya suke
bazaka taɓa cewa kishiyoyi bane, ko
gaisuwar Majeeda dak'yar ta amsa taja Maryam suka shige ɗakinta, tun kafinsu zauna tayi k'asa da Murya,
"Me nake faɗa miki Maryam? Ke har yanzu
kin kasa gane inda ke miki ciwo"
"ko kuma kece
kika kasa fahimtata Asiya, nifa babu abunda yarinyarnan ta tsaremun"
"Aikam baki
shirya ganin aibun kishiya ba, wallahi karki ga yanzu da cikinnan yana miki
kawaici, tana ajje ɗa a cikin
gidannan keda babu duk ɗaya, a hakan
ma ya aka k'are? Wallahi duk yanda kikeson Shaheed tana haihuwa zata rabaki
dashi"
Anzo wurin, don babu
abinda Maryam tafi tsana a rayuwarta kamar ace zata rasa Shaheed, "Tohh
anma Asiya, nima fa inason inga yaro a cikin gidannan, shekara nawa bamu samu
ba?
"Zaki ga yaro
a cikin gidannan, anma kina da iko dashi? Wata da tazo cikin ɗan lokaci zata rabaki da gidanki, idan kuma so kike
sai lokaci yayi ki bani labari tohh in saka miki ido"
"inaaa zan
zauna? Nidai yanzu ya za'ayi?"
"kuɗi kaɗan zaki bada, yanzu daganan wurin wani malamin zaure
zanje a lalata abinda ke cikinta, daganan kema in anso miki maganin
haihuwan"
"da gaske nima
zan samu haihuwan?"
"indai kinyi
yanda akace, kuma saikin yarda da malamin sannan zaki ga aiki",
"gaskia wannan
ba k'aramin Albishir bane, anma don Allah kar ayma Majeeda wani mugun abu"
tsoki Asiyah taja,
"hajia idan
kinason aiki, ki tashi ki ɗauko yanzu
in dawo miki da magani, da zafi-zafi ake dukan k'arfe"
"inaso mana,
yanzu kuwa"
Ta tashi ta lalubo mata kuɗi
ta bata, har bakin gate ta raka ta sannan ta dawo,
Ranar Majeeda keda
Shaheed, Anma Maryam ita tayi komai kamar yanda ta saba, babu wani canji a tare
da ita, bayan sunyi dinner yaja matarshi suka wuce ɗaki,
Ta fito daga wanka
tana ɗaure da towel, ta isa gaban
mirrow ta zauna zata fara shafe-shafe, suka haɗa ido ta cikin madubin yana kwance ya k'ura mata
ido, suka sakar ma juna murmushi,
"banson kallo
fa"
"laifine don
mutum ya kalla matarshi? kawai tunani nake"
"tunanin me
kuma?"
"Da wanne irin
farin ciki zan kasance a ciki? Idan ya kasance dake na fara rayuwa"
"hhm zaka fara
ko"
"wallahi da
gaske nake Majeeda, ban taɓa farin ciki
ba kamar ranar dana fara ganinki, kowanne dak'ik'a ɗaya da nayi tare dake, ina alfahri dasu, ji nake
kamar donke kaɗai akayi
zuciyatah, kece farin cikina"
"nima ina
farin ciki dakai sosae, inajin daɗin
kasancewa dakai, ina sonka fiye da kowacce halitta dake doron k'asa" ita
kanta batasan sanda maganar ta fito mata ba, anma tasan tabbas k'aryane ta faɗa,bata da kamar Majeed a
zuciyarta,
Cikin farin ciki ya
tashi ya tare ta zata saka kaya,
"da gaske
kike kina sona fiye da kowa" cikin son subar maganar tace "da gaske
mana, har kana k'ok'onton soyayyar da nake maka?"
"A'ah wlhy,
kina nufin har daddyn Abdallah kenan?"
"wake Maganar
daddyn Abdallah kuma yanzu?"
"nidai inason
sani plz, nasan kinso Majeed sosae Majeeda, kina nufin son da kikemun yanzu
yafi nashi?"
Rasa yanda zatayi
tayi, duk ya tsareta da tambaya, gashi batason ɓata mishi rai,
"Soyayyar
Majeed daban take a zuciyatah, ban taɓa
tunanin zan iya koda kallon wani namiji a matsayin namiji ba bayanshi, anma a
yanzu da nake tare dakai, banama tunawa dashi, nikam soyayyar da kake nunamin
ma ta isa, ban buk'atar sanin tsakanin Ni da Aunty Maryam wakafi so, wannan
sirrin zuciyarka ne"
"ke ta dabance
Majeeda, kalamanki suna matuk'ar tasiri a zuciyatah, kece wannan sirrin na
zuciyatah, kinason sanin wa nafi so?....."
Girgiza mishi kai tayi, ba magana, ya jawota ya haɗa da jikinshi, ya fara aika
mata da sak'onni cikin wani irin yanayi, m sai da aka turo k'ofa sannan sukai
sauri suka saki juna,
Maryam ce saida ta
shigo tsakiyar ɗakin sannan
ta fahimci halin da suke ciki, sai da ranta ya sosu, anma ta kanne kawai,
"kuyi hak'uri
na shigo muku kawai, bansan oga na ciki ba"
"haba, Aunty
keda ɗakinki kuma"
"uhm,
maganinki na kawo miki, nasanki da wasa dasha"
Ta mik'a mata ruwa a
cup da maganin, ko kaɗan bata kula
da yanayin canjawar ruwanba, sai da ta kwankwaɗeshi tass, sannan ta mik'a mata cup ɗin,
"nagode sosae
Aunty"
Ta ɓata rai "banson haka fa, sai da safenku"
ta fita ta rufo musu k'ofa
Ta juyo wurin Majeed tana mishi murmushi,
"Auntynah
tana ji dani sosai"
"gaskia ne,
nayi sa'a sosai da samun mata na gari"
"Muma munyi
sa'a da samun miji na gari, da kowacce mace zatayi alfahrin samu"
Ya jawota bayan ta
gama saka rigar barcinta,
"hajia nifa na
gaji da wannan jan lokacin" ya kashe musu fitila, saboda yau cikin
tsananin buk'atarta yake,
Tun lokacin daya
fara da shasshafa jikinta ta fara jin wani yanayi a jikinta, can cikinta
takejin kamar wani abu na motsi anma ba sosae ba yana ɗan tsira, bata ɗauka
wani abune daban ba, anma ciwon har tsakiyar kanta take ji, kasa taɓuka komi tayi, wani irin azaba
ta dingaji bayan ya tashi ya shiga wanka, kamar tafiyar tsutsotsi haka ta dinga
ji a cikinta duk yaa yamutse kamar ana cin kayan cikinta, ga wani irin zafi
kamar ana dahuwa a ciki,
A haka ya dawo ya
iske majeeda,
"wankan fa
dear?" shaheed ya tambayeta,
Dak'yar ta iya buɗa baki tana cije leɓe,
"zan tashi
inyi" baima lura da yanayin da take ciki ba, yaja bargo ya kwanta,
Haka ta dinga
juye-juye, hannuwanta biyu ta dinga sawa tana matse cikin ko zataji sassauci,
kamar ruɓaɓɓen abu haka takejin cikin, ta sauko qasa komai ta
samu ɗaura ma cikin take ta dinga
juye-juye, da taji dai abun bamai k'arewa bane, ko nak'udar Abdallah bataji
azaba haka ba, a kwance ta dinga jan jiki har inda Shaheed yake, ta dinga
tashinshi, baimasan tanayi ba barcinshi yayi nisa,
Hawaye ta dinga
zubarwa masu zafi, ko ina jikinta ciwo yake kamar ba nata ba, ko hannunta bata
son motsawa maganar ma ciwon buɗa
baki takeji, haka ta dinga daurewa tana kiranshi, ta saka hannu tana
bubbugashi, wani masifaffen ciwon nema idan jikinta ya haɗu da nashi,
Jinta tayi taa
jik'e kamar wacce tayi fitsari, a ruɗe
ta saka hannu ta shafa k'asanta, jinine ta gani a malale, ba k'aramin ruɗewa tayi ba, ta fara wani irin
kuka,
"Na shiga Uku,
ya Allah ka taimakeni kar in rasa wannan farin cikin na shaheed, don Allah ka
tashi shaheed, karmu rasa abunnan da
muke matuk'ar so, ka tashi shaheed karka rasa mu" haka ta dinga kuka, tana
sambatun da azabarma bata bari tasan tana yi ba,
Maryam na jiyota
daga inda take laɓe, ta koma ɗaki cikin farin ciki bama
kamar da taji Shaheed baisan tanayi ba, anma kuma a yanda take jin tana magana
dak'yar tausayinta take ji sosae, da kuma tausayin shaheed idan ya rasa wannan
cikin na Majeeda daya k'wallafa rai a kanshi,
Sai da ta
galabaita sosae, harta suma a wuri sannan shaheed ya farka, da sauri ya buɗe idanunshi ganin halin da
Majeeda take ciki kwance a gabanshi bata ko motsi, cikin tashin hankali ya
shiga girgizata anma ko motsi ba tayi, ga jini malale a jikinta daya qara tayar
mishi da hankali,
Fridge ya ɗauko robar ruwa ya dawo inda
take ya fara kwara mata, ta saki wata doguwar ajiyar zuciyar, idanunta sun
k'ank'ance saboda azaba ta shiga hawaye,
"Cikina
Shaheed, mutuwa zanyi, mutuwa zamuyi nida babynmu"
"bazaki mutu
ba Majeeda, rayuwatah tana buk'atarki, don Allah kicemun babu abinda ya samu
babynmu" girgiza kan zafin ciwo kawai take, tana hawaye, duk ya fita
hayyacinshi,
Ganin yanda take
dafe da cikinta, da alama tana cikin azabar ciwo, ya ɗauko robar ruwan ya shiga tofa mata addu'ah, wadda
RAZ suka kawo a littafin dodon jatau, da kuma ayatul kursiyyu, suratul ikhlas,
falaq da nas, kowanne sau Uku, ya dawo fuskarta ya bata tasha, sannan ya
kwantar da ita, ya shafe mata fuskarta da cikin, da hannuwanta da k'afafuwanta,
ta kwantar da kanta kawai jikinshi, tayi shiru tanajin ciwon na lafawa kaɗan-kaɗan,
A haka barci ya ɗauketa jikinshi, ya gyara mata
kwanciyar, bai koma barci ba, sai dai ya ɗauko
Al-Qur'ani yana karanta mata har aka kira sallah, kallon tausayi kawai yake
mata, kamar ya cire ciwon ya maida a jikinshi, rok'on Allah ya shiga yi daya
kare mishi abunda ke cikinta, yasa babu abinda ya sameshi,
Sai da aka kira
sallahr asubah ya lallaɓa ya sauketa
daga jikinshi, yana tashi itama ta buɗe
ido, da k'arfinta ta yunqura zata tashi, ya dawo zai rik'ota
"ina
zakije?"
"wanka
zanyi"
"tohh
kwanta bara in haɗa miki
ruwan"
"Zan iya
fa"
"kedai ki kwanta
nace"
"tohm ranka
shi daɗe"
Ta koma ta kwanta ba
don tanajin daɗin kwanciyar
ba, don ko ina jikinta a ɓace yake,
sai dai jinin ya daina zuba,
Shiya taimaka mata
ya mata wankan, dak'yar ya barta ta gyara wurin duk da tace mishi ta warke, sannan
ta koma ta kwanta bayan tayi sallah jinta take kamar bata taɓa ciwo ba,
"tashi fa
zakiyi mu tafi asibiti"
"Ba buk'atar
wani asibiti fa, na warke"
"kinason min
wasa da baby ko? Da lafiyanki ma, jini kika zubar fa, na damu da sanin matsayin
da babynmu yake ciki plz ki tashi mana" sai kuma yayi shiru muryarshi ta
canja damuwa ne fal a ciki,
"Duk laifinane
Majeeda, da nasan zaku cutu jiya duk buk'atar da nake da wlhy dana hak'ura,
baki kyautamun ba da baki faɗamun ba tun
wuri"
"Nima fa ban sani
ba, anma fa tun kafinnan ne nakejin ciwon, karka zargi kanka shaheed, bara in
shirya ɗin"
"tohm"
ya faɗa kawai yayi zurfi cikin
tunani, duk damuwah ce a ranshi,
Tare suka fito
bayan sun shirya, karo sukaci da Maryam da kayan abinci a hannunta, ta tare su
da murmushi,
"Yanzu nake
shirin kawo muku break fast ashe harkun fito, bara in kai muku dinning" ta
juya tana ci gaba da magana, wani irin farin ciki take ciki,
"inanan ina
aiki, anma hankalina na wurinki, ya jikin naki?" sai da Majeeda tayi shiru
cikin mamaki sannan ta bata amsa,
"Yayi sauk'i
auntie, Kin tashi lafiya?"
"lafiya lau
Majeeda," sannan ta juya wurin shaheed ta duk'a har k'asa cikin ladabi ta
gaisheshi, ya amsa mata kamar shi yayi ciwon ba Majeeda ba, duk ya shiga damuwa,
Abincinma kaɗan yaci, ya tashi bayan yacema
Majeeda ta sameshi a waje, harya juya zai tafi kuma ya dawo da kallonshi kan
Maryam, cikin wani yanayin da har saida ta tsorata,
"Ya akai
kikasan Majeeda bata lafiya?" kame-kame ta shiga yi, tama rasa amsar da
zata bashi, Majeeda ce tayi murmushi,
"Ba daɗewa fa ka faɗa mata zamuje asibiti" da sauri Maryam ta ɗago tana yak'e,
"eeh mana,
kaine ka faɗa"
Har lokacin
kallonta yake, don yasan kishi babu abinda bai saka mata, kuma bai manta da
maganin data kawo mata ba, don ranar ne kawai ta taɓa bata magani da kanta, shi yamayi tunanin k'wayar
maganinne tunda a hannu tazo dashi,
"tunda muka
fito bamui maganar asibiti ba,"
"Miye haka
Shaheed?" majeeda ta tambayeshi, hannu ya ɗaga mata yana kallon Maryam, can dubara tazo mata,
"Wai Yau nice
kake tsarewa da tambaya saboda na nuna kulawa a kan matarka? Jiya kukan data
dinga yi tana wayyo cikina waye baiji ba? Ban taɓa tunanin hakan daga gareka ba Shaheed" sauke
ajiyar zuciyah yayi sai kuma baiji daɗi
ba,
"Kinsan na
yarda dake da yawa Maryam, kiyi hak'uri, na fara tsorone kada ko kishi ya saka
kin fara canja halaye, ina tsoran halin Matan yanzu"
"Duk k'ok'arin
da nake akan matarka anma abunda zakamun kenan don yanzu ka samu ɗa? Ni kake zargi Shaheed?
Ni....?" ta kasa magana ma saboda kuka,
"ba haka bane
Maryam kiyi hak'uri don Allah" tashi tayi ta ruga da gudu ɗakinta, dak'yar take gudunma
saboda kib'a, yabi bayanta, Majeeda ta samu wuri ta zauna duk taa damu itama,
Sun daɗe yana rarrashinta kafin su
fito, tana dariya kamar ba itace ta gama kuka ba,
"Tohh Majeeda
a dawo lafiya"
"Ameen Auntie,
ban gajia kullum da gode miki, inama kowacce mace addu'ar samun kishiya
kamarki, kici gaba da hak'uri damu plz"
"ba komi
Majeeda, anma zai addu'arnan taki....,ba kowacce mace keson kishiya ba"
"indai irinki
ce Auntie kowah ma zai so" murmushi Maryam tayi ita kaɗai tasan fassaranshi,
"Tohh shknan
saikun dawo, Allah ya baki lafiya"
"Ameen"
Sannan ta koma ciki,
su kuma suka tafi asibiti,
Tsadajjen Asibiti
sukaje, ba ɓata lokaci sukaga likita, aka
mata scanning da duk sauran abubuwa, likita ya tabbatar musu da babu wani abun
daya samu cikinta, anma tana k'ara samun hutu sosae, (bed rest) saboda jinin
data zubar, sunyi farin ciki sosae, ba kamar Shaheed saida yayi sujjadar godiya
ga ubangiji, lallai Addu'ah bata faɗuwa
k'asa banza,
Sun fito tare suna
tafiya taji yaro ya rirrik'e mata k'afafuwa,
"Mamanah" muryar Abdallah taji da mamakinta, ta juya shiɗin
dai ne, ta ɗagoshi dak'yar zata ɗauka, Shaheed ya ansheshi,
"Yanzunnan fa
likita yace ki daina ɗaukar Abu
mai nauyi"
"Uncle"Abdallah ya faɗa,
Shaheed ya harareshi da wasa,
"bana hana
Uncle ɗinnan ba" Abdallah yayi
dariya,
"Na daina
Daddyna" Majeeda dai kallonshi kawai take baki buɗe,
"kai dawa
kukazo Asibiti?"
"Nida Umma ne,
ni kuma na fito" Majeeda ta kamo kunnenshi zata murɗe,
"Yanzu
yawonnan bazaka daina ba Abdallah?"
"in zaki mishi
faɗa kuma sai kinji mar ciwo? Zo
muje kaji Abdallah Umma na can na nemanka" ya juya sukai gaba ta bishi a
baya, duk nisan da yayi kau tsaf ya gane inda ya baro Umma, suka shiga batasan
ma bainan ba,
Suka gaisa da Umma,
ashe Aisha ce batajin daɗi,
"Umma Ashe
Aisha bata lafiya kuma banji ba"
"jikinne
nata kullum ba daɗi Majeeda,
Shiyasa ma bama faɗa"
"Allah sarki,
meke damunta"
"har yau dai
basu faɗa mana ba, anma jikin nata da
sauk'i ma"
"Allah ya
k'aro sauk'i Umma" ta k'ara kallonta, barcinta takesha, ita har manta
kamanninta ma take, rabon data ganta tun tana gidan Majeed, hannunta ta duba,
"Aikam na
baro jikkata inda na zauna" Shaheed da keta shan surutu wurin Abdallah
yace "bara in ɗauko miki
tohh"
"A'ah yi
zamanka bara inje" ta fice da sauri tana tunano inda take ganin ta barota,
cikin sa'a ta ganta, tana ɗauka ta juya
zata tafi, ta jiyo maganarshi a kunnanta, bazata taɓa mantawa da muryarba, bazata taɓa manta yanayin da takeji idanta saurari muryar ba,
shiru tayi ta kasa motsawa daga inda take, ko kallanshi ma batayi ba, wani irin
yanayi da bazata iya fassarawa ba ta shiga, ganin haka ya canja akalar zancen,
"ke haryau
baki iya gaisuwa bane?" murmushi tayi jin ya tuno da lokacin da suke faɗa, kafin aurensu kenan,
"Ayni banga
Abinda zan gaisar ba anan"
"lallaima
yarinyar nan, yauma rashin kunyar zakimun?"
"babu yarinya
anan" ta bashi amsa,
"idan nazo na
murɗe wannan masifaffen bakin naki
kinmu bayani"
"Zan zauna ne
ka murɗemun baki? Kaima kasan ba
tsoranka...." sai kuma tayi shiru tana k'ok'arin maida hawayenta, su duka
suka yi daria,
"Gaskiya da
munyi yarinta" ta faɗa tana juyowa, shima dariyar
yake, sai kuma yayi shiru, shima da damuwa a fuskarshi
"lokacin da
muka fara gane gaskiya kuma k'addara tayi halinta" sai yanzu ta ɗago suka haɗa ido, tun bayan rabuwarsu bata k'ara ganinshi ba,
shekara kusan Uku, yayi fari ya k'ara kyau sosae, sai dai rama da yayi da
alaman bai cikin kwanciyar hankali,
"Yaya Majeed
dukka rame" ita kanta batasan sanda ta faɗa ba,
"kekam Matatah
na kwance Asibiti, kullum ciwo, idan ban rame ba ya za'a gane nine mijin?"
ya faɗa da zolaya, sosae ya bata
daria,
"Allah ya
bata lafiya"
"Ameen, kwana
da yawa, faɗamun ya rayuwanki?"
"ba daɗi, tun bayan rabuwar mu, Munyi
aure da shaheed, matsalan dangin miji, ga kishiya kullum saita zaneni, miji
babu ruwanshi dani, babu ci babu sha, babu wanda zan faɗama matsalana, kaifa?" yaɗan murmusa, irin yanda yake idan taa gama burgeshi,
"Munyi aure da
Aisha, Masifa harta linka taki, safe daban rana daban, ba ruwanta damun girki,
kullum tayi ficewarta bata tambayata, ta rainani batajin magana ta
kuma..." yayi shiru yana tunani, suka k'arayin daria a tare,
"ina cikin
farin ciki yaya Majeed, bani da matsala da kowah"
"nima haka
Majeeda, Aisha macece ta gari, banda damuwa yanzu saita ciwonta kawai, sai muna
tunanin taji sauk'i kuma abun ya dawo"
"Insha Allahu
zata samu lafia"
"Ameen
fa"
"Yanzu dai mu
manta da rayuwarmu ta baya, ko babu komai mu en uwanah ne, kina kallona a
matsayin yayanki, komai ya wuce"
"komai yaa
wuce fa," ta faɗa tana share
hawayenta cikin dubara, "bara inje yanzu zamu tafi"
Ta juya ta tafi,
shima bai iya ce mata komi ba, soyayyar gaskiya kenan, kowannensu k'ok'arin ɓoye damuwarshi yake da
murmushi, anma a zuciyoyinsu sunajin ciwo sosae,
Tana zuwa sallama
sukayi da Umma, bayan ta k'ara duba Aisha, sosae ta bata tausayi,
0 comments:
Post a Comment