Lokacinda Maryam ta
fahimci cikin Majeeda nanan bai fita ba, ba k'aramin kad'uwa tayi ba, ba shiri
ta nemo Asiyah har ita suka koma wurin Malam, sai dai sunyi rashin sa'a ya
tabbatar musu babu makawa sai an haife cikin, sai dai daga baya zaisan yanda
yayi da yaron harma ita Majeedar tabar gidan,
Bayan wata biyar
Majeeda ta haifo santaleliyar yarinyarta Mace, ko ban fad'a ba kunsan ba
k'aramin farin ciki iyalannan sukayi ba, har Maryam taji dad'in zuwan yarinyar,
tun haihuwarta ita take hidima da ita, wani irin soyayyarta take ji,
Ranar suna yarinya
taci suna Maryam, shawarar Majeeda kenan, ta dage sai anyima Maryam takwara,
ansha shagali sosae, tun ranar haihuwarta har washe garin suna, babu wanda bai
shaida da haihuwar Maryam ba, harta da Aisha matar Majeed kullum tana gidan,
don yanzu sun zama kamar en uwah,
Kullum Maryam
k'arama tana wurin Maryam, tsakaninta da Mamanta sai in tana rigimar yunwa,
Shaheed ma acan ya tare b'angarenta wurin d'iyarshi, ita dai Majeeda ta zama er
kallo,
Tun tana da
shekara guda suka yayeta, sai dai madara, ganin haka Maryam ta koma wurin
Malam, da maganarsu ta baya kar Majeeda ta samu wuri tayita haifa ma Shaheed
yara, ita kuma ta zama hoto, shima abu
ya bada da zata zuba mishi a abinsha, tace "shi yafi komai sauk'i
malam" sannan tayi godia ta tafi,
Majeeda na kwance,
Shaheed ya shigo d'akin da Marece ne, tayi mamaki sosae don da wuya ya shigo
idan ba dare ne ba,
"Sannu da
dawowa" baice komai ba yaci gaba da k'are ma d'akin kallo, duk da daman
yanzu yaa daina kulata, sannan ya zura hannu Aljihu ya ciro takarda, ta
kalleshi da mamaki,
"takardar
miye?" cikin yanayin da bai tab'a mata magana ba yace "in faɗa miki da baki mana, idan ni
yaronki ne, Ansa ki duba" jikinta ba k'wari ta mik'a hannu ta amsa ta buɗa, Saki Uku ne reras, tana
ganin haka ta kulle takardar idanunta cike da hawaye, ita kuma k'addarar da
Allah ya ɗaura mata kenan,
"Mena maka
shaheed?"
"kawai na gaji
da zama dake, babu laifin da kikamun, ki tattara kawai ki tafi, sannan kuma
karma ki sakaran tafiya da Maryam, tuntuni na barma Maryam ita" wani irin
takaicine ya taso ma zuciyarta, wani irin kallon tsana take mishi,
"Sai yanzu
ne na fahimceka, lallai yau na yarda ka cika namiji, watau aurena kayi in haifa
maka ɗiya ka cimun mutunci? Lallai
idan ance maza DUK HAKA SUKE (littafina mai zuwa), bazanyi gardama ba, saika
zauna dasu halayensu da baka taɓa
tunani ba zasuna bayyana, ka rusa duk
wata yardar dana maka Shaheed, kaci amanatah, bazan taɓa yafe ma cutar dani da kayi ba, kuma Maryam nina
haifeta babu inda zan tafi in barta"
"Da ita
kikazo? Zaifi miki ma daki manta da ita, don keda ita har abada, kuma kici gaba
da zama har in dawo in sameki" ya fita fuuu yabar ɗakin, anan ta zube k'asa tasha kuka sosae kamar
ranta zai fita, da kanta kuma ta rarrashi zuciyarta tayi shiru, jikkarta kawai
ta ɗauka tabar gidan,
Mai napep ya
ajeta k'ofar gidansu, ta fito dak'yar take haɗa
hanya ta shiga gida,
Momie da Umma ne a ɗakin tazo gidan, Abdallah ma
ya koma gidan babanshi a can ya sakashi makaranta, dak'yar har tana ganin jiri
ta faɗa falon, wurin zama a kujera
harta kusa faɗuwa, ta jinginar da kanta
kawai tana dafe kanta dake mata ciwo sosae, duk suka taso sukayo inda take,
Kasa basu amsoshin
tambayoyinsu tayi, sai dai ta mik'a musu takardar dake hannunta, duk tare suka
saki salati, sunyi matuk'ar tausaya mata, Umma kamar karta bar gidan don
tausayin Majeeda, babu wanda zaiga halin da take ciki bai tausaya mata ba,
A gurguje dai....
Bayan shekara Uku...
Majeeda ta kwantar da hankalinta, Yanzu ta zama lecturer a
makarantar Umyu katsina, tsakaninta da Majeed sai dai mutunci kawai na en uwah,
gida ma ganin halin da take ciki ya saka ko maganar aure basu mata, kullum dai
suka mata Addu'ar zaɓi mafi
Alkhairi,
Aisha ne da Majeed
kwance ya juya mata baya, ba barci yake ba, anma kuma yayi shiru kamar mai
barcin,
"Kayi shiru
hniee inata magana ni kaɗai, kuma
nasan ba barci kake ba" shirun ya k'ara mata,
"kana jina
fa" baice komi ba, ta kamo k'afarshi ta fara mishi susar k'adangaruwa,ba
shiri ya fara dariya, ya kamota ya rungume, tureshi tayi suka fuskanci juna,
"Wai hniee Meyasa
kullum nake maka maganar dawo da Majeeda kake shareni? Wlhy na faɗa maka banda Matsala da hakan,
kuma kunason junanku, ga Abdallah kullum k'ara girma yake, zaiso ya ganshi a
tsakiyar iyayenshi"
"ke ba
mahaifiyarshi bace?"
"Duk da haka
nidai ka dawo da ita don Allah"
Fuskarta ya jawo
ya haɗa da tashi suna shak'ar
numfashin juna "Hakan kikeso" ta ɗaga
mishi kai,
"Zanyi komai
saboda farin cikinki, Anma nidai ki dainamun maganar zanyi tunani akan
hakan"
"naji anma
baza'a ɗauka lokaci ba?" ya gyaɗa mata kai, duk wannan maganar
da take k'arfin hali ne kawai, yana rungume da ita, ɗagotan da zaiyi yaga jinine ke fita ta hancinta, ta
tafi luuu ta faɗa gefe,
cikin tashin hankali ya rink'a jijjigata, ciwon nata nayau yafi na kullum ɗaga mishi rai, doguwar riga
kawai ya ɗaura mata saman kayan barcin
jikinta, ya ɗauketa a ruɗe ya saka mota, dak'yar ya iya driving zuwa asibiti,
Har gari ya waye
bata dawo hayyacinta ba, likitoci na iyakar k'ok'arinsu a kanta, en uwanta cike
a asibitin, wata nurse ta lek'o tace "Waye Majeed?" da sauri ya matsa
inda take yana cewa shine, yabi bayanta suka shiga Maryam na kwance ta farka,
idanunya tsaye kanshi tana murmushi, ta mik'a mishi hannunta ya rik'e yana
hawaye, ta ɗan ɓata rai da wasa,
"Miye na kuka
kuma hniee? Ka kwantar da hankalinka kaci gaba damun addu'a kamar yanda ka
saba, wlhy koda mutuwa nayi ina cikin farin ciki sosae, burinah ya cika, na
rayu na wani lokaci kuma zan mutu a matsayin matarka, kada ka manta da maganar
da mukayi jiya da dare, kada ka manta dani Majeed" k'ara rirrik'e hannunta
yayi,
"bazaki barni
ba Aisha, zamu rayu a tare insha Allah"
Girgiza kai tayi
"ban taɓajin ciwon da nakeji ba a yau,
ni nasan wannan ciwon shine ajali na" ta k'ara lumshe ido dak'yar take
magana, tashi yayi yana k'wala ma likita kira,
tak'i sakin hannunshi, ya juyo yana kallonta, murmushi ta k'ara mishi,
"kada ka
manta da alk'awarinmu na dawo da Majeeda" sannan ta sakeshi, ya tafi duk
jikinshi yayi sanyi, suna dawowa da likita har rai yayi halinshi, anan Majeed
ya faɗi sumamme, yasha jinya sosae
Asibiti kafin ya ɗan samu,
Bayan shekara ɗaya,
Da mutuwar Aisha,
Abdallah yanada shekara 10, ya zama ɗan
saurayi, Maryam nada shekara 4, Majeeda ta zama babbar mace, 'yar gayu da ita,
kullum k'ara kyau take, idan ka ganta bazaka ce tayi shekarunta ba, har Gida
Maryam ɗin Shaheed tazo neman
yafiyarta, Shaheed ma har kuka yayi na zafin rabuwa da ita, bata rik'esu da
komai ba ta yafe musu, sannan ta barma Maryam, Maryam k'arama don har lokacin
Allah bai bata haihuwa ba,
Majeeda ce tafe
cikin Mota, tana tuk'i cikin natsuwa, duk da saurin da take zuwa gidansu Umman
shaheed saboda kiran gaggawar da aka mata, mintoci kaɗan ta isa gidan, mai gadi ya wangale mata gate ta
shiga, daga makaranta take duk ta shawo gajia, kai tsaye falon bak'i ta wuce,
Kamar yanda suka
saba idan zasuyi meeting, kowa ya hallara, zahra ce kawai babu, ta gaishesu
sannan ta samu wuri ta zauna, kallo ɗaya
data ma Majeed ta k'ara hango ramar da yayi sosae,
Bayan ta samu wuri
taa zauna, Abban Majeed yayi gyaran murya ya fara Magana,
"Wannan
karon ba Umarni bane muke baku, shawara ce muka yanke kuma duk saida
amincewarku, abinda ya faru mu ɗauka
k'addara ne, yanzu kuma dama ce garemu, mu cika Alk'awarin da mukai ma
mahaifinmu, muna fatan wannan karan bazaku bamu kunya ba"
Momie ce ta nisa,
tun kafin kowah ya fara magana "Gaskia ni ban yarda da wannan hukuncin
ba" su duka suka juyo suna kallonta, taci gaba da magana cikin fahimta,
"Su duka
yanzu ba k'ananun yara bane, kun manta abunda wancan haɗin ya haifar? Shiyasa ni ban cika magana ba, anma
gaskia wannan lokacin bazan yarda a k'ara musu dole ba, su koma halin da suka shiga wancan lokacin
ba" Daddy ya katseta
"Waye yace
dole za'a musu? Suna da damar da zasu faɗi
ra'ayoyinsu, karki manta da Alk'awari ne muka ma Mahaifinmu, ba don haka ba
koda kansu suke so bazamu taɓa k'ara
amincewa ba, kuma yanzunma idan har basu so bazamu k'ara tilasta su ba"
shiru tayi bata k'ara magana ba,
Abbah yace "ku
muke saurare", Majeeda kanta a k'asa tun tana kuka a hankali harta fara
shesshek'a, Majeed ma sai dai tashi yayi ya fita, fuskokin iyayen nasu duk ta
nuna rashin jin daɗi, sunyi
jugum kowa ya kasa motsawa, message ya shigo wayar Aunty zainabu, ta ciro ta
tana ganin daga Majeed ne ta buɗe
da sauri, da k'arfi ta karanta yanda kowah zaiji,
"Ki tayani
godia Auntynmu, kunyarsu ta hanani furta komai, sun nuna mana soyayyar da babu
abinda zamu biyasu da ita, Allah ya saka musu da mafificin Alkhairi, ya k'ara
musu tsawon kwana" kowa a ɗakin
saida ya murmusa, sunyi farin ciki sosae, Majeeda ma murmushin jin daɗi take, ta mik'e da gudu ta
fita, kunya bata barta ta jira kowah ba, ta shige motarta ta wuce gida,
Cikin lokaci kaɗan aka fara hidimar biki,
shagali sosae akayi wanda ko bikinsu na farko ba'ayi ba, cikin sati biyu aka
gama komai aka kai Amarya ɗakinta,
Bayan en rakiyarta
sun gama tafiya, ta shek'a wankanta, tayi kwalliya ta fitar hankali, ko ina
jikinta k'anshi yake, ga wata doguwar riga data saka ta daifi babu, irin
shigarda tasan Majeed yafiso, sai dai ta ɗaura
zani daga sama,
Yana shigowa
tsaye yayi a k'ofa yana kallonta, duk'arda kanta tayi sannan wata irin kunya ta
saukar mata, ya ware mata hannuwa alaman tazo ya rungumeta, cikin zolaya tace
"yau kuma ina laidan da za'a jefeni da ita?" daria yayi,
"rufamun
asiri zaki jamun ɗauri,"
itama tayi dariya,
"nayi alwala
fa, kai kawai nake jira"
"tohm ranki
shi daɗe"
Ya shiga yayo
alwala, ya fito, Sallah sukayi raka'a biyu kamar yanda manzon Allah ya koyar
damu, ya daɗe yana kwararo musu addu'ar
zaman lafiya, sannan sukai godia ga ubangiji,
Ya rausayar da
kanshi yana kallonta, rayuwarsu ta bayace ta dinga dawo mishi, wata irin
soyayyarta na k'ara ratsashi, itama kamar hakan takeji, ta hure mishi idanu,
"ka faɗa mana"
"na rasa mezan
faɗa ne, kullum k'ara kyau kike,
bazaki taɓa tsufa ba"
"kaima
hakanne, babu wanda zaice kana da kaman Abdallah"
"bazan iya
bayyana miki farin cikin da nakeji ba da dawowarki gareni, wallahi ban taɓa sanin ina sonki da yawa haka
ba saida na rasa ki, HARAMTACCEN ZAMA, ya k'are, Allah ya bamu ikon farantama
juna har k'arshen rayuwarmu"
"Ameen"
ta faɗa
GODIYA
Ta tabbata Ga Allah
daya bani ikon kammala littafinnan lafiya, tsira da Aminci su k'ara tabbata ga
annabinmu Muhammad (S.A.W), kuraren da suke ciki Allah ya yafe mana, Ameen,
Bani da bakin godia gareku Masoyana nesa da kusa, inajin daɗin yanda kuke nuna soyayyarku
ma littafinnan, Allah yabar k'auna, sai kunjini a sabon littafina K'IYAYYA,
anma bayan na dawo daga jigawa wurin kishia labarin A HANYAR JIGAWA,
yananan tafe ba daɗewa domin
nishaɗinku,
domin gyara ko
shawarwari
SADAUKARWA
wannan littafin
sadaukarwa ne ga dukkan jikokin Alhaji sani katibu, duk sunayensu ne a ciki
Manyan gobe,
Allah ya raya mana ku ta farkin addinin musulunci, ya zaɓa muku abokan zama na gari, Ameen
IYAYENA
Allah yaji k'anshi mahaifinmu da rahma ya gafarta mishi,
Allah ya k'ara tsawon kwana momienah, Allah ya saka miki da gidan Aljannah,
hak'ik'a Uwah ce ta gari, ina sonta fiye da rayuwatah!
NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION
Ina Alfahri daku,
Allah ya k'ara ɗaukaka, ya
k'ara mana haɗin kai,
Godiya ta musanman,
Da taimakonka ne na
fara littafinnan harna k'areshi, ILILEE, nama rasa ta yanda zan gode maka,
Allah ya k'ara basira, Ameen
AMINAN JUNA
K'awaye na gari,
babu kamarku a zuciyatah, RAZ, k'aunarku dabance a cikin zuciyatah, kalmomi
bazasu iya bayyana farin cikin da nakeji kasancewarku cikin rayuwatah ba, Amrah
A msh and Zahra bb, Allah ya bar tare.
Beelybadaru, kina
raina a koda yaushe
En uwanah writer,
gaisuwa mai yawa a gareku, Allah ya k'ara basira ya k'ara mana haɗin kai baki ɗaya,
Duk group ɗin da nake ciki da wanda suke
samun littafina, ina mik'a gaisuwa mai yawa gareku, Ma'assalam
Taku har kullum
Rabiatu sani
katibu mashi
0 comments:
Post a Comment