Tafiya muke nida Hanee ko waige bama yi, da abn yayI nisa ma
har gudu muka koma yi duk dan muga mun tarar da wannan hamshaqiyar yarinyar,
bamu muka tsaya ba sai bakun wani qayataccen gida wanda da ka ganshi gasan na
wani mai muqami ne, a daidai vakin gate yarinyar ta tsaya da motarta qirar
range rover ash colour, horn tayi amma shiru ba'a bud'e gate ba, sai bayan
kamar minti biyu ta qara wani horn d'in amma shiru gate man bai bud'e gate d'in
ba. A fusace ta fito daga mota ko jakarta bata d'auka ba ta bar motar bud'e ta
shiga gidan. Koda shigarta ta samu gate man d'in kwance yana rawar sanyi alamar
baida lafiya, bata ko duba yanayinshi ba ta d'aga hannunta ta wanke shi da
mari, dafe kumatunshi yayi wani zazzafan hawaye na saukar mishi, kafin ya
ankara ta qara d'auke shi da wani marin, sai a lokacin tace "kai uban waye
da zanyi maka horn har sau biyu amma ka kasa bud'e min gate? Bayan kuma kasan
bisa ga d'abi'ata horn daya kawai nakeyi ko sallah kake dole kabarta kazo ka
bud'en gate in shigo gida, mtswww wawan banza!".
Fita tayi bata
koma takan motar ta dake waje ba, tayi
tafiya mai nisa kafin ta isa inda farfajiyar gidansu take, shiga tayi kai tsaye
babu ko sallamah. Ta samu momy kishingide ana mata matsar qafa, fad'awa tayi
jikinta tana mayar da numfashi, a firgice momy ta miqe zaune tana fad'in
"na shiga uku, auta me ya faru dake na ganki kamar ba'a hayyacinki
ba?". Kyakkyawar budurwar tace "momy wai waye ta kawo mana wancan
wawan a gidan nan?", momy tace "wa kenan?", a shagwa'be tace
"gate man d'in can mana". Momy tace "ai! Wai baba faruku? Dady
da kanshi ya kawo shi wai yana tausayinshi ne, me ya miki ne auta ta?",
"momy wai har sau uku ina horn amma yaqi bud'en gate, motar ma tana can na
bari a waje har da key d'in yana jiki ban cire ba tsabar takaici", miqewa
tsaye momy tayi tace "auta! Baki da hankali ne? Baki gudun a sace ta ne?
Kin san fa jiya aka kawo ta, waccan d'ayar ma ajiyeta kikayi fa aka sace miki a
gidan biki". Kamar tana jira momy ta gama maganar aikuwa ta fashe da kuka tana
fad'in "momy! Yau nice kike yiwa fad'a har da nuna min yatsa? Momy tunda
nake baki ta'ba yi min haka ba, a dalilin wancan wawan tsohon gate man d'in?
Tou barin je inda yake, wlh sai yabar gidan nan, ko uban wa ya tsaya
mashi".
Fita tayi ko dan kwali babu a kanta, bata ko nemi takalmi ba
ta kama hanyar d'akin me gadi, ta same shi still yana rawar sanyi wadda tafi
yanda tabarshi d'azu. Bara jira komai ba ta fad'a d'akinshi, finciko shi tayi
ta jefar waje, ta duba bakin katifar shi taga wata qaramar Ghana most go, dauko
ta tayi ta jefa mashi a daidai isowar momy wurin, fitowa tayi daga dakin tace
"a dalilinka momy na tayi man fad'a harda nuna ni da yatsa tayi, wlh yau
sai kabar gidan nan, tsohon banza zaka nemi takurawa rayuwata, sai ka koma
qauye aci gaba da cin tuwon dawa ai, mtsww" taja tsaki tare da barin
wurin.
Abn haushi wai
momy ta kasa ce mata komai, har tayi nisa da qyar tsohon nan me gadi yace
"SAFNA!!! Ni kika wulaqanta haka? Ni kike kira da tsohon banza? Ko da yake
banga laifinki ba, laifina ne da na qasqantar da kaina nake bauta a gidanku,
hmmm!! Neman halak kenan, insha Allahu yanda na nema gareku kina wulaqanta ni
bayan kuma nayi jika dake, ina roqon Allah ya kawo ranar da kema zaki nema a
wuri na...." ya qarasa maganar cikin kuka da ban tausayi.
Da sauri ta dawo wurinshi ta sake wanke shi da mari tace
"ba amin ba tsohon NAJADU!! Allah ya fika, kuma ni bazan ta'ba nema a
wurinka ba, babana yana da kud'in da ko bayan ranshi zanci har in kyautar wa
mabarata irinka" ta tofar da yawu qasa tace "tir! Da MUMMUNAN
FURUCINKA".
Barin wurin
tayi da gudu saboda qunar da zuciyarta ke mata. Momy bata ce komai ba sai bin
bayan 'yarta da tayi tabar me gadi nata goge hawaye. Bayan kamar minti biyu
yaja Ghana most go d'inshi ya fita. A hankali yake tafiya dan yana tsananin jin
zazza'bi.
Da qyar ya
samu yaje tasha ya hau motar qauyensu BAGARUWA,
d'an chanjinshi ya biya kud'in mota ya isa. Ya samu Nawwaf na zaune
qofar gida ya buga tagumi, koda yaga
babanshi tuni ya tashi ya nufI wurinshi ya kar'bi jakar suka qarasa ciki yana
mashi sannu da zuwa.
Da shigar shi gida bai jira komai ba ya kwanta kan wata
tabarma dake shimfide a bakin qofar d'aki, NAWWAF dai sai bin babanshi yake da
kallo ganinshi da yayi sukuku, "Abba sannu da zuwa", ya ansa da
"yauwa NAWWAF, ina umman taka?",,,,," tana daga ciki ina jin,
Ummah!", "ga ni nan, zuwa fa, aahhh lale marhaba da mutan birni,
sannu da hanya" ummah ta fada tare da fitowa daga daki.
Wasu irin
zafafan hawaye suka fara ambaliya a fuskar Abbah, duk hankalunsu ya tashi ganin
abbah na kuka, a rude NAWWAF yace "abba wai me ya faru ne? Tunda kazo naga
kana da damuwa a zuciyarka, ka fada mn matsalarka wlh na dauki alqawari indai
ina da maganinta".
Ummah tace
"malan meke faruwa da kai, kuka fa kakeyi, tunda nake dakai ban taba ji ko
ganin kayi kuka ba, amma da mamaki sai gashi yau kana yi har idonka yayi
jaa".
Sun d'auki
tsawon lokaci shiru basu samu ansa daga Abbah ba, jin bashi da niyar basu ansa
ne yasa Ummah tayi qarfin halin cewa "ka watsa ruwa malan ka kwaso rana
sai kaci abinci". Baice mata komai ba ya miqe jikinshi na rawa ya nufi
toilet. Da gamawarshi ya fito, abinci
kawai yaci ya kwanta bacci yayi gaba dashi.
NAWWAF duk abn
duniya yabi ya dame shi, sai zaman tagumi yake har abba ya farka yaga Ummah
zaune kusa dashi tana hawaye, ga NAWWAF
ma zaune a gefen Ummah, ganin su cikin wannan halin yasa shi cewa "kuyi
haquri, bana son na fada maku abnda zai saku bacin rai ne shi yasa naqi fada
maku, amma tunda kuna son ji yanzu zan fada",,,,,,,,,,nan ya hau basu
labarin duk abnda ya faru tun farko har qarshe.
Zumbur NAWWAF
ya miqe tsaye yace "Abbah ka bar naje Katsina na samu jakar yarinyar nan, wlh
sai naci mutuncin ta kamar yanda taci naka mutuncin, kawai qaramar yarinya ta kiraka da tsohon
banza, munafuki, Subhanallah! Abbah yau yau din nan zan tafi". Bai jira
komai ba ya tafi dakinshi da nufin canza dressing.
Tsawa daya abbah
ya mashi dole ya tsaya, abba yace "na saka ne? Wau kai NAWWAF yaushe zaka
rage wannan ZAFIN zuciyar taka ne? Ya kamata fa kasan ka girma, kuma nace
kabarta da duniya, duniya zata bida ta, ai laifi na ne da naje gidansu da aiki,
kaga inda ace banje ba ai da bazata ci min mutunci ba, amma yanxu da nabar
gidan ba shikenan ba? Sai kuma tayiwa wani ai".
Ummah tace
"hakane malan, tou amma yanxu idan ka dawo gida ka zauna ya zamuyi da
abincin da zamuci? Shi NAWWAF bai iya ko wace sana'a ba, shidai karatun boko kawai
ya tasa a gaba, ni fa yanxu kusan shekarar shi biyu kenan da gama degree
dinshi, har service ya gama amma babu wani aikinyi kullun sai zaman qofar gida
yake, sai matacciyar zuciya kawai".
NAWWAF da
hawaye ya wankeea fuska yace "Ummah indai hakane zan nemi kudi insha
Allahu, neman kudi kuma ta tsaftatacciyar hanya, zan nemi halal insha Allahu ko
ta hanya mafi wahala ne".
Koda sukaje kuwa sun samu Mal. Shazali anyi layi a gidanshi
kowa da abnda ya kawo shi, Hamza yace "sai kabi bayan wannan na
qarshen",
Nawwaf yace
"yanzu wannan uban layin duk sai na bishi?",
Hamza yace
"qwarai kuwa sai ka bishi, da haka kowa ya fara har aka kaiga na farko,
yanxu za'azo kanka ai tunda naga duk masu bada balance ne",
Nawwaf yace "tou".
Layin yaita
bi har akazo kanshi, mal. Shazalin da kanshi ya bashi kurar amma fa yasha
gargadi kafin a bashi, da alqawarin zai ringa kai balance kullun yabar wurin
cikin farin ciki da zumud'I, harda jarkokin aka bashi yaja suka kama hanyar
gidan hayar da hamza yakeda daki a ciki.
TUSHEN LABARI.
Alhaji Marwan d'ane ga malan Sani mai gilashi, ya taso cikin
tsananin talaucin iyaye, tun yana dan shekara biyar aka sakashi makarantar
primary, daqyar da wahala suke samun
kudin breakfast ma dan su kansu wanda zasuci wahala yake basu, mal. Sani kuwa
baida wata sana'a kullun yana zaune a gida, baki daya xuciyarshi ta mutu, baya
da wani burin tashi ya nemi na kanshi, Rabi itace matarshi, mata mai kokarin
neman na kanta, kullun naseeharta daya ce wadda bata wuce mal. Sani ya nemi
halak ba, amma sam baya daukar maganarta, wani lokaci ma sai yace wai gori take
mashi dan taga itace ke ciyar dasu, har kuka takeyi idan ya fada mata haka.
Bayan shekara
biyu a lokacin Marwan yana da shekaru bakwai a duniya kwatsam Rabi ta samu juna
biyu, tayi godiya ga Allah amma sam abn bayyi mata dadi ba, saboda abincin da
zasuci ma wahala yake masu, tun suna su uku kenan ina ga sun qara yawa, mal.
Sani yaji dadi sosai data sanar dashi tana dauke da juna biyu,
Bayan kamar kwana
uku da sanar dashi da tayi tace "mal. Kaga dai yanxu ina da ciki wata uku
ya kamata ka fara qoqarin neman na kanka tun kafin lokacin yayi kuma aita
daddafe daddafe a rasa yanda za'ayi",
Mal. Sani yace
"sata kike so nayi ko yaya? Ko kuma ke zaki bani jarin?",
A zuciye Rabi
tace "nifa malan ba haka nake nufi ba, me zaisa nace kayi sata? Amma kuma
ai akwai hanyoyin neman kudi da dama wanda akeyi, kai kenan kullun kwanxe a
gida, ni kwance kaima kwance babu mai tada wani",
Yace "kyayi
kya gama Rabi, ni banda Inda zanje idan kin matsu ki fita kiyi dako", yaja
tsaki ya shiga dakinshi.
Haka Rabi taita jan cikinta cikin rashin kulawa har yakai
wata bakwai, alokacin ne ta yanke shawarar tsaida duk wani aiki da takeyi
kamar; dakau, wanki da guga na kudi da sauransu. Bayan cikinta ya cika wata
tara Ta samu da qyar da wahala ta tattar
dubu sha daya harda tsohuwar ajiya, taba mal. Sani tace "mal. Ga wannan, a
siyo ko qaramar tunkiyace wadda za'ayi yanka, idan kudin sun samu chanji sai a
yo mana cefane. Ni kuma akwai dubu biyu hannu na sai in siyo kayan jinjiri
dasu",
Mal. Sani da
murmushi yace "yauwa uwar gida, wlh kina burgeni, zuciyar maza ne
dake", bata bashi amsar komai ba da qyar ta shiga makotansu gurin A'I me
kayan koli, irin kayan nan masu hangan roba ta siya wasu na mata wasu na maza
ta hada kala takwas dasu sannan ta koma gida.
Ta samu mal. Sani
bayanan a tunanin ta ya tafi siyo tunkiya dan ta fada mashi ta fara jin naquda.
Bayan kamar minti arba'in mal. Sani yazo yana kuka,
"Me ya faru
ne malan?"
Yana goge hawayen
yace "dama na siyo tunkiyar ne na hadu da wasu mugaye a hanya suka qwace
suka min duka a hanya", ido bude Rabi tace "tunkiyar? INNA LILLAHI WA
INNAA ILAIHI RAJI'UUN" ji kake tiiiiii ta fadi qasa, hankalinshi bai ko
wurin yaci gaba da "kuma fa uwar gida da sauqi aka samu tunkiyar, naira
dubu tara aka bar min ita, baki ga girmanta ba qatuwa da ita",
Jin shiru ba
amsa ne yasa shi cire hannunshi daga Ido da yake murzar qwallan qarya, ganin
jini nata malala daga jikin Rabi yasa shi fasa ihu a daidai shigowar Marwan,
"Abba me
ya samu mamana? Jifa jini na fita, mama ki tashi dan Allah", kuka yake
sosai abn tausayi yace "abba kaine ka duki mama ko?",
Mal. Sani yace
"wlh ban duketa ba Marwan",
"Ka duke
ta mana Abbah! Ga jini na fita, ai idan ba'a duki mutun ba jini baya
fita",
Bai kuma bashi
ansa ba ya samu ya ciccibi Rabi ya saka a baro ya kama hannun marwan da hannu
daya, dayan kuma yana tura baron.
Basu zarce ko ina ba sai qaramar asibitin dake cikin qaramar
hukumar Kaita, da hanzari aka kar6eta domin ceto rayuwarta, sun dauki kimanin
awa biyar akanta,
Wata nurs ce ta fito tace "wa keda Rabi'atu
Sani?",
Da sauri mal. Sani yace "ni nazo da Ita,
ina fatan ta sauka lafiya",
Saida ta jinjina
kai sannan tace "ina son ka sani da rayuwa da mutuwa duka a hannun Allah
suke, ka dauka dama rai arone aka bamu kuma a ko wane lokaci wanda ya ara mana
zai iya zuwa karvar abnshi, Allah baya barin wani dan....." bata gama fadi
ba sakamakon tsawa da mal. Sani ya daka mata yace "me kike nufi? Kina
nufin matata ta mutu ko kuwa danda ta haifa? Karki mayar dani sha3 mana",
Qaramin likitan
ya fito duk yayi xufa yace "malan daga fadan gaskiya sai ka mata wannan
tsawar? Matarka ta samu zubar jinu sosai tare da mummnar faduwar gaba kafin ta
fara naquda, babu wanda ya isa ya qetare lokacin da allah ya tsara mashi.
Matarka ta rasu munyi iya qoqarin mu dan ganin mun ceto rayuwarta amma da yake
iyakar rayuwar kenan bamu iyaba, kayi haquri amma an ceto jinjirin namiji ne
kuma lafiyayye",
Wata irin nadama
tazowa mal. Sani, kuka yake sosai ya shiga dakin ya rungume gawar matarshi yana
fadin "ki yafe mn Rabi'atu, na soki sobda bazan taba iya yiwa wata mata
shiba, nine na kashe ki Rabi'atu kuma a shirye nake da kai kaina ga hukuma tun
kafin naje ga bbar hukuma", ya miqe tsaye yace "yalla6ai ku kira 'yan
sanda su tafi danI a yanke min hukuncin kisa, wlh nune na kashe ta, likita bani
da wata sauran rayuwa data rage min a doron qasa, don allah ka kaini a yanke
minhukuncin kisa".
Babu musu kuwa
likita ya kira 'yan sanda tare da shaida masu duk abnda mal. Sani ya fada da
bakinshi, su kuma basuyi wani bincike ba kawai suka tura kotu, jin gamsasshiyar
hujja daga bakin mal. Sani yasa aka yanke mashi hukuncin daurin rai da rai babu
wani bincike, basu tambayeshi ta wace hanya yabi ya kashe matarshi ba kawai aka
tafi dashi prison.
Marwan kuwa
yana zaune ya hada kai da guiwa yana tunanin hakun daya tarar da mamanshi ciki
har zuwa asibiti da sukayi tare, duk baisan an tafi da babanshi ba, gajiya da
yayi ga kuma yunwa yasa ya miqe tsaye yana ta kuka yana kiran "Abbah!
Abbah" amma shiru, sosai yaqara fashewa da wani kukan.
Dr. Nasir na
bakin gawar Rabi ya rasa ya da zayyi da Ita, a hankali yake jiyo kukan Marwan,
da sauri ya fita dan ganin wanda yake kuka, ganin Marwan yayi har ya galabaita,
likita yace "yaro me ya faru kake kuka?",
Marwan yace
"babana nake nema, kima gashi mamana bata da lafia, can naga an shiga da
ita har yanxu bata fito ba", jin hakan ya tabbatar wa Dr. Nasir cewa
marwan dan mutumin nan ne, jan hannunshi yayi cikin tausayi ya kaishi gaban
gawar mamanshin.
Cikin natsuwa Dr. Nasir ke magana yace "ya
sunanka?",
"Sunana
marwan",
"Gud, Marwan
an saka a islamiyya kuwa?",
"Ehh an
saka ni harda tahfiz ma inayi",
"Yauwa
Marwan, an taba baku labari akan mutuwa?",
"Ehh ana
fada mana, kuma har malamin mu yace duk kan mai rai sai ya dandani mutuwa, kuma
komai sonka da mutun Allah bazai barshi dankai ba, komai girma komai qarantar
mutun idan lokacinshi yayi sai ya mutu",
Sosai maganar
marwan ta ratsa dr. Nasir. Cikin mamaki yace "marwan shekarunka
nawa?",
"Am 8years old",
Da dabara yace
"tou marwan indai ka tabbatar da cewa Allah shine yake bayarwa kuma yake
qwacewa ka fada mn",
"Ehh na
yarda",
"Yanxu idan
ka arawa wani pencil dinka na makaranta zaka koma ka karbi abnka?"
"Ehh zan koma"
"Tou
Marwan, Allahn daya raya mamanka ya bata aron rai tou yau ya karbi abarsa, ina
so kayi mata addu'ah ka fawwalawa Allah komai dan daman shine ya ara
mata",
Marwan yace
"tou unle na yarda kuma Allah yani kan mamana",
"Ameen"
dr. Yace. Tare da miqawa marwan jinjirin data haifa.
Ya karba yana
ta kallonshi yaro mai kyau mai irin fuskar mamansu, saI daya kalli jinjirin
yaji wani irin kuka mara control yaxo mashi tausayin qaninshi na matuqar
addabarshi, bayan ya gama kukan ne yace "uncle ina babana?",
Bai boye masa
komai ba ya fada mashi, wani irin haushi yaji gashi bai san kowa a danginsu ba.
A babbar
masallaci dr. Nasir ya sanar da mutuwar Rabi, anan aka dauko gawarta aka kawo,
ta samu masallata sosaI tare da yan rakiya, aka kaita kushewarta.
Dr. Nasir kuma
yayi alqawarin daukar su marwan tare da riqesu tsakaninshi da Allah. Yayiwa
jinjirin huduba da sunan babanshi "SANI".
Haka sukaci gaba da
rayuwa gidan Dr. Nasir, baya nuna masu komai face tsantsar soyayya, matarshI
Saude kuwa ta tsane su, kullun sai tsana da tsangwama, Sani da ake bawa madara
bata kula dashi sai dai me aikinta Zulai
ce ke bashi madara aduk lokacin daya dace, Marwan kuwa kullun da kalar
azabar da take gana mashi, danta Shahid ma har dukan marwan yakeyi idan
babanshi baya nan.
Kwatsam wata rana
Dr. Nasir baya nan Saude ta aiki Marwan da kudi yaje shago, a hanyarshi ta zuwa
ne ya yarda kudin, ya neme su ya rasa, yaita kuka dan yana tsabar tsoron
masifar Saude.
Kawai ya yanke
shawarar yaqi komawa gidan, haka yaita tafiya bai san inda zaije ba. Tun daga
nan nima na tafi na barshi dan karmu 6ata tare, har iwa yanxu ban san inda
Marwan yake ba.
A 6angaren
gidan su kuwa jin Marwan shuru bai dawo ba yasa Saude tace danta Shahid ya tafi
ya nemoshi, yaita nema amma bai ganshi ba ya dawo gida. Tuni Saude ta tsure dan
bata san abnda zatace wa mijinta ba. Har bayan isha Babu Marwan babu alamanshi,
Zulai tafi kowa rudewa saboda tana son marwan amma gashi uwar gijiyanta ta kasa
daukar wani mataki akan 6atan yaron.
Dr. Nasir ne
ya dawo shahid ya fara bashi labari, yace "dady mamy ce ta aiki Marwan
shine har yanxu bai dawo ba",
Cikin kidima Dr.
Nasir yace "Marwan din? INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN", da
sauri ya qarasa cikin gidan yana kwalawa Saude kira.
"Ina kika
aiki Marwan da har yanxu bai dawo ba? Saude tun yaushe na hanaki aiken Marwan?
Idan gaskiya ne me yasa bakya aiken Shahid tunda yama girmi Marwan?",
Da in ina Saude
ta kasa bashi ansa, "d d...dm..ma..naa ras..."
"Yi mn shiru
Saude! Tunda abn naki hakane zan nemo wanda zata ci gaba da kula mn da Sani,
Zulai ta ringa taimaka mata, na kula ke kam bazaki iyaba, ina nufin zan qaro
aure dan Sani kawai",
Da sauri ta zabura
tace "aure alhj.?! Aure fa kace? Saboda wannan shegen yaron da baida asali
zaka qara aure?"
" Ke kikaga
shegun yara Saude, nikam ban hada kowa dasu ba, na daukarwa kaina alqawari a
idanuwan mutane a cikin babban masallaci tun kafin a dauki gawar mamansu, kina
so inci alqawarin ne? Tou ni ban iya wannan ba, da hankalI na da komai bazaki
sani jin kunya a idanuwan mutane ba, kuma yanxu zan fita neman Marwan, matuqar
ban ganshi ba tou kema sai kin kwana a seil",
Sosai Saude ke
kuka tana fadin "wato alhj. Ni kake so ka tozarta ko?" Taci gaba da
kuka ko kulata Dr. Nasir bayyi ba ya nufi bakin motarshi.
Tunda ya fita
yake neman Marwan lungu da saqo amma babu ko alamunshi, har saida ya jigatu
sannan ya nufi police station, harda hotonshi ya gwada masu (wanda ya dauke shi
a waya yana riqe da Sani), ya basu wadatattin kudi sannan ya tafi gida daka
ganshi zaka gane yana cikin damuwa mara adadi.
Ya shiga gida
kanshi a dafe bai kula kowa ba sai zulai daya gani yace "ina Sanin yake?
Ko shima an barshi ya tafi?",
Cikin tsoro tace
"yana daki yallabai, na gama bashi madara ne yayi bacci",
Bai gama jinta ba
ya isa dakinta, ya samu shi cikin net dinshi kwance yana bacci, a hankali ya
bude gidan sauron ya sumbaci Sani a goshi tare da fadin "insha Allahu zan
riqeka fiye da yanda iyayenka zasu riqeka, zanyi bakin kokari na ganin ka samu
farin ciki har qarshen rayuwarka, dan uwanka daya 6ata ma insha Allahu zan bada
kudi ko nawa ne indai za'a ganoshi",
Rifewa yayi yana
share 'yar kwallar data fito mashi yabar dakin.
'Dakin shi ya shiga baiko bi ta dakin Saude ba, wai shi a
nufin shi yana gwadata ne yaga ko zata shiga dakinshi ta tambayeshi labarin
Marwan saboda taga sanda ya shigo amma ta koma dakinta wai ita a dole mai
kishi, shiru shiru bata fitoba har bacci ya daukeshi. Qarfe ukun dare ya farka
da tunanin rashin ganin Marwan, tashi yayi ya dauro alwala, ya hau sallar da
koshi bai san adadin wadda yayi ba, ya hau adduah "yaa Allah ka bayyana
mana wannan yaron, idan kuma 6atanshi alkhairi ne Allah ka kaishi wuri mafi
alkhairi, Allah ka kareshi da kariyarka ya Allah" kuka yaci qarfinshi ya
tsaya da addu'an.
Washe gari da sassafe
baiko nufi aikiba saida ya fara zuwa gidan momma (mamanshi) ya gaishe ta tace
"Nasiru ya kwanan yaran dasu saude?",
"Lafiya ba
lafiya ba momma",
"Me ya
faru?" Cikin kidima ta fadi haka tana mai son jin abnda ya faru,
"Momma
marwan ne Saude ta barshi ya fita tin jiya bai dawo ba, har police station naje
amma sam babu wani labari, sai daga baya Shahid yake bani labarin kalar azabtar
dashi da sukeyi shida Saude",
Miqewa momma tayi
tace "na shiga uku! Marwan din?! Amma kuwa Saude bata kyauta ba, dama
kalar riqon da takewa marayun Allah kenan? Tou shi kuma Sani ya maganarshi?
Tana dai feeding dinshi yanda ya kamata ko?",
Jin tambayoyin
momma bazasu qare ba yasa a taqaice yace "Sani ma zulai me aiki ta barma
shi wai ita ke kula dashi, tou ni a gani na kawai in qara aure ko zan samu mai kula dashi tunda ita bazata
iya ba",
"Shawara me
kyau kenan Nasiru, dama akwai Maryam 'yar qanwa ta, kamilalliyar yarinya ce
mahaddaciyar Qur'ani, wannan shekarar ta gama makaranta, insha Allahu yau zan
tinkari mahaifiyarta da maganar, kome kenan zan kiraka",
"Tou momma
nah, shiyasa bana gudun kI da duk shawarar dana ke nema, Allah yasa hakan shine
mafi alkhairi".
Cikin sati bayu aka gama maganar auren Dr. Nasir da Maryam.
Ba'ayi wani abu ba sai walima.
Saude tasha kuka
ita a dole mai kishi, ganin bata da yanda zatayi yasa ta dangana. Gida daban
aka kai Maryam, saboda Dr. Nasir yasan baza su ta'ba zaman lafiya ba matu'kar
ya had'e Saude masifaffiya da Maryam nitsatstsiyar yarinya.
Kwananta uku a
gidan shi ya kar'bo Sani, sai da ya sai mashi komai sabo kafin ya kaishi, har
da madarar da ake bashi mai kyau da tsada.
Sosai Maryam taji
dad'in Sani, saboda ita dama can maI son yara ce, musamman Sani da Dr. Ya aure
ta musamman saboda shi.
Kula sosai yake
samu wurin Maryam, ko kukan shi bata son ji. Tsakanin ta da Saude kuwa ko ta
kai mata ziyara bata ko kallon inda take, magana ma bata ansawa idan tayi mata.
Sai harare harare. Da zarar Sani yayi rarrafe ya nufi inda take kamar taga kura
take mashi. Ta kai da tsoron ta ma yake ji, ko gidan sukaje baya nufanta.
Marwan kam
babu ko labarin shi, anyi nema har an gaji, Dr. Nasir yace ma Maryam "ni
har ma na fawwakawa Allah komai, fata na dai Allah yasa yana lafiya a duk inda
yake",
Maryam tace
"Ameen ya Allah".
Kwance tashi babu
wita wurin Allah har Sani ya shekara hud'u ya shiga makaranta, yana da haza'ka
sosai dan duk class d'in su babu mai 'ko'karin shi. Har Dr. Yana yawan mamakin
Sani, bai ta'ba ganin yaro kamar shi mai sharp brain ba.
A haka har ya gama
Secondary School, a lokacin Maryam nada yara uku duka mata, babbar itace Zarah,
mai bi mata kuma Futha, sai autar ta Khairat. Duk a cikin yaran Sani yafi
sha'kuwa da Futha, suna shiri sosai har idan bata ganshi ba bata jin dad'I.
Kwatsam da gamawar shi gwamnati ta d'auki nauyin fitar dashi UK karatu. Futha
tasha kuka kafin su rabu, sai da yaita bata baki kafin ta amince.
to marubuta yau zan fara karan ta littafin ku mai suna 'zafin so'. ina fatan ALLAH yasa mu qaru da illimin da ya qunsa.
ReplyDelete