Hajiya ce ta katse maganar zucin Haroun,ta hanyar fad'in " lalle ka tabbata tantiri,bara na kira uban ka in ya so sai ka sheda ma sa,amma ina mai tabbatar maka ba in da Habeebti za ta bi ka,mara kunya fitsararre!" Ta na magana ne ta na danna wayar ta dan kiran Alhaji.
Habeebti da ke tsaye,zafin ruwan tea din da ya subuce daga hannun ta sam be dame ta ba,tsabar zafin sa Haroun a ido da ta ji. Juyawa ta yi bayan ta gama aika ma sa da sakon tsana da ta tabbatar ya je gare shi ta cikin kwayar idanun ta, d'aki ta nufa ta na ji Hajiya na magana da Alhaji a waya cike da bacin rai. Shi kuwa Haroun bin Habeebti yayi da kallo har ta shige ciki,sannan ya sami waje ya kame kan kujera,Haroun junior bisa cinyar sa.
Hajiya da ta lura da kallan da ya bi Habeebti da shi tuni ta dad'a tsorata,wannan sai ka ce kura ya ga nama?aje wayar ta yi ta na huci ta ke duban Haroun,shi kuwa sam hankalin sa ba ma wajan ta ya ke ba,lissafin rayuwar sa da Habeebti ya ke,dan tabbas tun da aka d'aura ma sa ita ba wanda ya isa ya hana shi tafiya da matar sa. Daga bisani har da dan sunkuyawar sa ya ce "Hajiya barka da dare,an wuni lafiya?" A fusace Hajiya ta amsa ma sa da ban wuni ba da ka ganin? Mara kunya kawai,kai dai wlh albasa ba ta yi halin ruwa ba,da haihuwar irin ka gwara barin sa" murmushi kawai ya yi,ya ma gyara zama abun sa.
Sallama su ka ji,maimakon Alhaji da ta kira Alhaji Hamisu ne ya zo. Ganin shi Hajiya ko amsa sallamar ba ta yi ba sai Haroun ne ya amsa,yayinda ya aje Junior ya sauko ya durkusa k'asa,shi kuwa Junior jikin sa ya dawo ya jingina."Na ce Alhaji ba ya kusa ne?" Hajiya ta tambaya a fusace. Idanun Alhaji Hamisu kan Haroun da ya sunkuyar da kai kamar mutumin kwarai ya ce "Hajiya ai abun da ya yi Alhaji Shamsu shi ya yi ni ko ba haka ba? Kai Haroun lafiyar ka da tsohon daren nan haka ka zo ka ce ka zo d'aukan iyalin ka?duk watannin da su ka shud'e ba ka zo ba sai yau hakannan san ka d'agawa jama'a hankali ko?toh ka d'auke su ka tafi da su ina?" Gaishe shi Haroun ya yi cikin ladabi da biyayya,kafin ya kada baki ya ce " Dama na gama shirya komai Abba,da ke a can Kaduna an ba ni apartment nan cikin Army barrack za mu zauna....." "Ka na nufin Kaduna za ka tafi da su yanzu haka?" Alhaji Hamisu ya katse shi ta hanyar jefa ma sa wata tambayar. Haroun na shafa kan sa da ya ke kwal babu gashi ko tsili d'aya ya ce "da wai haka na ke nufi,idan da hali kuma da yardar ku....." Alhaji ya na mai gyara tsayuwa ya ce "ba hali ba kuma za mu yarda ba!" Da sauri Haroun ya d'aga ido ya kalli Alhaji Hamisu,wanda ganin haka ya ce "kalle ni da kyau....." Hajiy da maganar ke yiwa dad'i ta jinjina kai ta na fad'in "madallah,gwara ma a raba auren kowa ya huta" Haroun ya yi k'asa da idanun sa.
.
Alhaji Hamisu be gushe ba ya cigaba" abun da ya sa kuwa na ce haka mu ba mu da hurumin yanke hukunci akan Aliya ta bi ka ko kar ta bika,ka shirya ka je k sami Kawun ta Alhaji Umar,abun da ya yanke da shi za ka yi amfani.." sam ba haka Haroun ya so ba,amma ba yanda zai yi haka ya godewa Alhaji Hamisu,tare da fad'in "Zai ziyarci Alhaji Umar,duk yanda su ka yi zai zo ta fad'a ma sa" Alhaji Hamisu ya ce "Toh Allah ya tabbatar da alkhairi" Hajiya da ke da tabbacin auren nan raba shi za a yi tace " alkhairin shi ne a raba auran..."
Alhaji Hamisu ne ya fara tafiya,an ci sa'a Junior ya yi
bacci jikin Haroun dan haka salin alin ya kwantar da shi kan doguwar
kujera,ya na mai adduar sake ganin fitowar Habeebti,idanun sa kan hanyar
d'akin,Hajiya ta lura da hakan ta ce "idan ka aje kayan tsiyar na ka ka
san inda dare ya ma ka!" Maganar na Hajiya kusan dariya ma ta sa
shi,fuskar sa cike da fara'a ya ce toh " Hajiya ta kuma sirika ta,mu
kwana lafiya...." Da sauri ya fice ya na dariya jin Hajiya ta shiga
zazzaga masifa,ta na fad'in "dole dai a ce da mijin iya baba,ba yanda
zan yi tun da ina auren uban ka,amma kam ba zan tab'a zama surikar ka
ba!!! Can da su gada!! Auren nan dole a raba"
Ya na fita kai tsaye b'angaran Mama ya wuce. Ita kuwa Habeebti tun da ta shiga d'aki ba ta k'ara fitowa ba. Haroun junior ma sai biyo ta aka yi da dashi. Kwana ta yi ta na lissafa irin gurasar da za ta gasawa Haroun d'anya a hannu muddun tsautsayi ya sa Allah ya k'addara zaman su gida d'aya.
Ya na fita kai tsaye b'angaran Mama ya wuce. Ita kuwa Habeebti tun da ta shiga d'aki ba ta k'ara fitowa ba. Haroun junior ma sai biyo ta aka yi da dashi. Kwana ta yi ta na lissafa irin gurasar da za ta gasawa Haroun d'anya a hannu muddun tsautsayi ya sa Allah ya k'addara zaman su gida d'aya.
Kwana d'aya kacal ta k'ara a gidan Hajiya kan ta koma
Bichi,ko gidan amare ba ta lek'a ba. Komawar ta Bichi ko da wasa ba ta
yiwa Yakumbo zancen Haroun ba,gudun abun da Yakumbo za ta ce dan ta ita
kamar ta mance da abun da ya mata,ko da yake ai mai d'aki shi ya san in
da ya ke masa yoyo.
Bayan kwana uku sai ga Alhaji Umar ya zo da batun
Haroun,ace war sa "Yaro ya zo ya same ni da maganar tarewar iyalin
sa,toh abun da ya faru dai ya faru. Ya sheda min ya na da gida ne can
cikin barikin sojoji da ke garin Kaduna in da ya ke aiki,nan ya ke so su
tare" Yakumbo da ke zaune a tsakar gida tare da Alhaji Umar ba k'aramin
dad'i maganar ta yi ma ta ba,ko ba komai ta huta da gulmar yan unguwa.
Ta ce "toh kai me ka ce masa? Alhaji Umar ya ce "Ce ma sa na yi yarinya
dai matar ka ce,amma hakan nan ba za mu ba shi ita ba sai mun je mun ga
in da ya ke ikirarin zai aje ta,idan ya ma na,kuma yarinya ta shirya
fani'iman sai a ba shi iyalin sa su tafi,dama kyan d'iya mace d'akin
mijin ta. Dan haka cikin satin nan za aje a ga gidan na shi,ita kuma za
ta shirya nan da sati biyu,idan mazaunin na sa wanda za a iya zama ne za
ta bi mijin ta.." Yakumbo ta gyad'a kai,kana tace "Amma ya ka ga
yanayin yaron?anya kuwa zai iya ruk'e aure K'arami?" Mumushi Alhaji Umar
yayi."Eh toh na ga ya dad'a girma da wata sabuwar kammala da ban san
shi da ita ba ada,toh amma maganar zai iya ruk'e aure ko ba zai iya ba
wannan abu ne na Allah,ba kwarya ba ne bare a kwankwasa a ji Kwarin
sa,sai dai ayi fatan alkhairi kawai" "kwaran gaske,toh Allah ya fishe mu
alkhairi,bara na kira ta ka fad'a ma ta da kan ka,ka san halin ta,shiru
shiru da ita amma sai bori da taurin kai kamar mutanen farko" Yakumbo
ta shiga kwalla mata kira,yayinda Alhaji Umar ke tsimayen fitowar ta.
.
Ai kuwa taurin kannan da bori sai da Habeebti ta
tab'a shi. Dan ba rabuwar arziki su ka yi da Alhaji Umar ba,wanda ya bar
ta tana kuka sakomakon jadda mata nan da sati biyu dole ta bi mijin ta.
Cikin satin har gidan Alhaji Umar Hajiya ta je kan rashin amincewar ta
na tariyar Habeebti. In da ya yi watsi da al'amarin,ya sheda ma ta sun
je sun ga inda Haroun zai aje Habeebti,saboda haka ta sa a ran ta tarewa
ba fashi.
Hatta Hajja Fadi ta na mai bakin cikin tarewar Habeebti,ita kuwa Anty Salmah farin ciki ta yi,Maman Zahra har da ba da gudunmawar daka da gumbar mata a kaiwa Habeebti,wanda karshen su a masai n Yakumbo su ka k'are. Haka duk wani kayan mata da ake had'awa Habeebti zubarwa ta ke,gani ta ke tsabagen an rai na ta ma shi ya sa ake ba ta. Musammam Yakumbo da ta tsufa amma kwashe kwashe gun ta kamar maman bola,tun ta na bawa Habeebti haushi har ta koma ba ta dariya.
Satin da za kai Habeebti ne aka nemi Haroun da batun jera,in da ya ke sheda mu su Habeebti kad'ai gidan ke buk'ata sai kayan sawar ta dan komai na zaman rayuwa ya aje a gidan sai abun da ba za a rasa ba.
Ana gobe za a kai Habeebti mutan Abuja su ka zo,Bichi su ka kwana saboda su sami komawa Abuja ranar da za a kai amarya. Da sassafe aka dau hanyar Kaduna,daga Kano Anty Salmah da Maman Zahra ne su ka wakilci dangin Haroun. Bayan Habeebti ta sha nasiha daga wajan su Yakumbo da Alhaji Umar da ba su san ta inda ya ke shiga ta nan ya ke fita,in dai Habeebti ce da na ta shirin na zuwa gidan Haroun,musammam yanda Anty Maijidda ta jadada ma ta kar ta sake ta yarda Haroun ya cimma burin sa kan ta,ta tabbatar ya yi danasanin kassara mata rayuwa da ya yi.
Karfe goma sha d'aya daidai a Kaduna ta mu su. Gidan da aka bawa Haroun ba yabo ba fallasa,gida ne mai dauke da d'akuna biyu madaidai ta dukkan su akwai toilet ciki,sai falo wanda shi ma madaidaici ne,,da kuma kitchen mai hade da store. Sai dan baranda daga waje. Haka kuma duka sauran gidajen barrack din su ke,banbanci d'akuna ne,wasu d'aya,wasu biyu ne,wasu uku,har da ma mai hud'u ko biyar ya dangan ta da rank din mutum.
.Hatta Hajja Fadi ta na mai bakin cikin tarewar Habeebti,ita kuwa Anty Salmah farin ciki ta yi,Maman Zahra har da ba da gudunmawar daka da gumbar mata a kaiwa Habeebti,wanda karshen su a masai n Yakumbo su ka k'are. Haka duk wani kayan mata da ake had'awa Habeebti zubarwa ta ke,gani ta ke tsabagen an rai na ta ma shi ya sa ake ba ta. Musammam Yakumbo da ta tsufa amma kwashe kwashe gun ta kamar maman bola,tun ta na bawa Habeebti haushi har ta koma ba ta dariya.
Satin da za kai Habeebti ne aka nemi Haroun da batun jera,in da ya ke sheda mu su Habeebti kad'ai gidan ke buk'ata sai kayan sawar ta dan komai na zaman rayuwa ya aje a gidan sai abun da ba za a rasa ba.
Ana gobe za a kai Habeebti mutan Abuja su ka zo,Bichi su ka kwana saboda su sami komawa Abuja ranar da za a kai amarya. Da sassafe aka dau hanyar Kaduna,daga Kano Anty Salmah da Maman Zahra ne su ka wakilci dangin Haroun. Bayan Habeebti ta sha nasiha daga wajan su Yakumbo da Alhaji Umar da ba su san ta inda ya ke shiga ta nan ya ke fita,in dai Habeebti ce da na ta shirin na zuwa gidan Haroun,musammam yanda Anty Maijidda ta jadada ma ta kar ta sake ta yarda Haroun ya cimma burin sa kan ta,ta tabbatar ya yi danasanin kassara mata rayuwa da ya yi.
Karfe goma sha d'aya daidai a Kaduna ta mu su. Gidan da aka bawa Haroun ba yabo ba fallasa,gida ne mai dauke da d'akuna biyu madaidai ta dukkan su akwai toilet ciki,sai falo wanda shi ma madaidaici ne,,da kuma kitchen mai hade da store. Sai dan baranda daga waje. Haka kuma duka sauran gidajen barrack din su ke,banbanci d'akuna ne,wasu d'aya,wasu biyu ne,wasu uku,har da ma mai hud'u ko biyar ya dangan ta da rank din mutum.
Ba laifi su Yakumbu sun yiwa Habeebti gata,dan kuwa da garan ta aka had’o ta. Hatta jan miya sai da aka soya mata wanda za ta kwana biyu ta na amfani da shi. Bare kuma su daddawar ta,kuka,kub’ewa dadai sauran su. Tun azahar mutan Abuja su ka yi gaba. Su Anty Salma ne su kai mata har yamma,sai da Haroun ya dawo sannan su ka tafi su ka bar junior da Maman sa cikin kuka da kad’aici. Dan shi ma Haroun aiki ya ke ya baro saboda su Anty Salma,suna tafiya ko ganin Habeebti be yi ya ba ya koma aikin sa,ganin Habeebti na mu samman ne dan haka sai ya shirya ma sa.
Bayan ta sha kukan bak’in ciki ta k’oshi ta tashi
d"auke da Junior ta bi koina na gida tana kallo. Falon ta ba wani
tarkace aka cika ba,an masa ado da black and ash colour. Kitchen din ta
ma well polished abun sha’awa. Bayan ta gama duba ko ina,d’aki d’aya ne
ba ta duba ba,wanda ta ke tunanin na Mai junior ne,gudun kar ya na ciki
ba ta yi shirin ganin sa ba tukunna. Bayan sallar ishai ta yi wanka ta
yiwa Junior wanka,sanye cikin kayan bacci riga da wando ta shiyar Junior
ta sa ma sa diaper, sannan ta sawa dakin ta mukulli ta kulli saboda
gudun attack din dare,"Ba a aure ta ba aka far ma ta bare kuma an
aure",ta fad’a cikin ran ta yayin da ta ke bin lafiyar gado har da
guzirin yar wukar ta duk d ta kulle kofar dan ba mamaki ya na da spare
key. Ba su dade da kwanciya ba bacci ya d'auke su dan daga ita har dan
na ta sun tara gajiya. Haroun kuwa be dawo ba sai wajan goman dare,ko da
ya ji gidan shiru,ya kuma murd’a kofar d’akin ya ji an sa key sai ya
dara,duk da ya na da spare key kawai ya juya abun sa ya ci gaba da
harkokin sa,after all gobe ma rana ce.
Washagari tun bayan da ta yi sallar asuba,ta
cirewa Junior diaper ta d'aura sa kan fo kamar yanda ta saba ma sa
kullin,dan kuwa Junior mai tutun asuba ne,bayan ya gama ta gyara shi su
ka koma bacci ba ta tashi ba sai da ta ci baccin ta ta k’oshi,wajan
karfe tara bacci ya ishi Junior shi ya tada ta da kukan yunwa. Ta na
hamma da salati ta tashi,duk in da ta sa kafa ya na biye da ita,haka su
ka shiga toilet inda ta yi brush ta ma sa gami da wanke fuska dan ta yi
niyar su fara yin wanka amma yanda yake ma ta kuka ta san ba za a yi
abun arziki ba dan haka ya na biye da ita ta sanya hijabin ta su ka nufi
kitchen. Indomie ta samu ta dafa musu kasancewar kitchen din akwai
komai da ta ke buk’ata. Allah Allah ta ke su gama su koma ciken kafin
Haroun ya fito,amma shirun da ta ji har ta gama su ka ci ta wanke abun
da ta bata be fito ba ya tabbaatar ma ta bayanan.
.
Ko da ta tashi yin wanka tare ta yi da yaron ta dan babu yanda za ta yi ta aje shi ta shi wanka,Junior yaro mai kiriniya kafin ta fito sai ya sa ta aikin da za ta kwana ba ta gam aba. Kwalliayar ta tayi cikin material pink mai laushi,ta yi kyau sosai. Sannan junior ma ta shirya shi cikin riga da wando brown,ta taje ma sa kai sai kamshi ya ke abun sha’awa. Kallan sa ta ke yayinda ta yi tsaye kan sallaya,da hijabi sanye a jikin ta tana shirin yin sallar walha.’’zan yi salla ne Junior,be a good boi ka zauna gu daya owk?"junior da be gama fahimtar abun da take fad’a ba ya washe ma ta baki,ganin haka ta ce ‘’dax my boi’’ sannan ta kalli gabas ta tada salla.
Sam ba ta lura da fitar shi ba har sai da ta idar da
sallah ta yi sallama. Ko da ta waiga ta wayam sai ta tashi da sauri ta
na fad’in ‘’ai sai dai ba Junior ba’’ Fitowa ta yi ta na waige waige,ba
yaro ba alamar sa,hatta kitchen da store sai da ta lek'a amma wayam.
Tuni hanjin cikin ta ya kad’a,ta na shirin komawa d'aki ta d'auko
takalmi ta fita waje neman sa ta jiyo dariya na tashi daga d'akin
Haroun. A hankali ta k’arasa kofar d’akin,ta jingina tare da manna
kunnan jikin kofa, ko Allah ya sa ta ji murya Junior. Ta gama sakin
jikin ta cikin rashin sa’a Haroun da ke ruke da hannun Junior ta cikin
d’akin ya sa hannu ya j kofar da niyar budewa. Nan kuwa Habeebti da ta
saki jikin ta jikin kofar ta bi kofa sai gata nan kamar wacce aka
hank’ado d’akin saura kiris ta kifa Haroun yayi saurin rik’ota yayinda
Junior da ya yi tunanin wasa ake ma sa ya kyakayce da dariya. Sai da ta
nutsu ta dawo daga shock din da ta shiga sannan ta lura da positon din
da ta ke da kuma hannayen Haroun biyu ruke da kafad'ar ta wanda kiris ya
rage ta fad'a kan sa,yayin da ya tsura ma ta ido kamar zai had’iye ta.
Da sauri ta yi kokarin buge hannun sa daga jikin ta,amma ta kasa,ganin haka ta watsa masa harara gami da fad’in ‘’dallah Mallam sake ni’’ maimakon ya sake ta,sai ma dad’a ruke ta da yayi tare da fad’in ‘’is dat a way of sayin thank you a garin ku?….ko ba ki san taimakon ki na yi ba?…..’’ ganin yanda ya ke kallan ta da wannan manyan idanun na sa ya sa gaban ta ya fara fad’uwa,bugun zuciyar ta ya k’aru har ta kai sai da Haroun ya gane musammam yanda ta dan d'auki lokaci kan ta bashi amsa,sannan ta ce’’Ina gargad’in ka da ka gaggauta saki na….’’ dad’a matso da ita jikin sa yayi,Habeebti ta runtse idanun ta,ta na jin shi har da yar dariyar sa irin you are now in my control woman. Sannan ya ce " Idan na ki fa?…umm my Habeebti ?my wife?….idan na ki me za ki yi?…me za ki iya yi?…’’ Ya na magana ne ya na dad’a motso da fuskarsa zuwa na ta har ta kai ga ta na jin saukar numfashin sa bisa fuskarta…’’sanyayyar ajiyar zuciya Habeebti ta saka wanda hakan ya k’ara bawa Haroun k’arfin gwiwar kokarin hade fuskar sa da na Habeebti,toh amma me zai biyo baya….Dagewa ta yi ta d'aga kafar ta gwiwar ta be sauka koina ba sai tsakiyar cinyar Haroun. Tuni ya saki wani k’ara gami da sakin Habeebti ta yi tangal tangal za ta fad’i Allah ya sa ta yi saurin rik’o kofa…shi kan shi junior kuka ya sa dan tsoratar da yayi jin ihun baban na sa da yayi baya hannun sa biyu ruk’e da in da Habeebti ta aikasa injuriy.k’asa ya zube idanun sa sun kad’a sun yi jajur sai zufa ya ke dan azaba iya azaba ya ke ji. Habeebti na murmushin mugunta ta sunkuya daidai fuskar sa ta ce’’ Ta ce kallo ni nan mugu,wannan kad'an daga cikin aiki na kenan Mai junior,ka k’ara kai hannu jiki na i will make sure i kill you……’’dan rad’ad’i ya ma kasa magana,ya na kallan ta ta sa hannu ta d'auki Junior da ke faman kuka….sai da ta je bakin kofa ta sake juyowa ta ce ‘’I dare you…..’’sannan ta watsa ma sa kallan tsana ta fice gami da buga ma sa kofa….ya na juye juye cikin azaba.
.Da sauri ta yi kokarin buge hannun sa daga jikin ta,amma ta kasa,ganin haka ta watsa masa harara gami da fad’in ‘’dallah Mallam sake ni’’ maimakon ya sake ta,sai ma dad’a ruke ta da yayi tare da fad’in ‘’is dat a way of sayin thank you a garin ku?….ko ba ki san taimakon ki na yi ba?…..’’ ganin yanda ya ke kallan ta da wannan manyan idanun na sa ya sa gaban ta ya fara fad’uwa,bugun zuciyar ta ya k’aru har ta kai sai da Haroun ya gane musammam yanda ta dan d'auki lokaci kan ta bashi amsa,sannan ta ce’’Ina gargad’in ka da ka gaggauta saki na….’’ dad’a matso da ita jikin sa yayi,Habeebti ta runtse idanun ta,ta na jin shi har da yar dariyar sa irin you are now in my control woman. Sannan ya ce " Idan na ki fa?…umm my Habeebti ?my wife?….idan na ki me za ki yi?…me za ki iya yi?…’’ Ya na magana ne ya na dad’a motso da fuskarsa zuwa na ta har ta kai ga ta na jin saukar numfashin sa bisa fuskarta…’’sanyayyar ajiyar zuciya Habeebti ta saka wanda hakan ya k’ara bawa Haroun k’arfin gwiwar kokarin hade fuskar sa da na Habeebti,toh amma me zai biyo baya….Dagewa ta yi ta d'aga kafar ta gwiwar ta be sauka koina ba sai tsakiyar cinyar Haroun. Tuni ya saki wani k’ara gami da sakin Habeebti ta yi tangal tangal za ta fad’i Allah ya sa ta yi saurin rik’o kofa…shi kan shi junior kuka ya sa dan tsoratar da yayi jin ihun baban na sa da yayi baya hannun sa biyu ruk’e da in da Habeebti ta aikasa injuriy.k’asa ya zube idanun sa sun kad’a sun yi jajur sai zufa ya ke dan azaba iya azaba ya ke ji. Habeebti na murmushin mugunta ta sunkuya daidai fuskar sa ta ce’’ Ta ce kallo ni nan mugu,wannan kad'an daga cikin aiki na kenan Mai junior,ka k’ara kai hannu jiki na i will make sure i kill you……’’dan rad’ad’i ya ma kasa magana,ya na kallan ta ta sa hannu ta d'auki Junior da ke faman kuka….sai da ta je bakin kofa ta sake juyowa ta ce ‘’I dare you…..’’sannan ta watsa ma sa kallan tsana ta fice gami da buga ma sa kofa….ya na juye juye cikin azaba.
Ya kai kusan minti talatin ba cikin hayyacin sa ba,ko da azabar ta lafa ya kuma tabbatar ba ta ji ma sa ciwo ba,nan yayi kwanciyar sa ya na tunanin ina Habeebti ta koyo mugunta har haka? "Lalle an daura min aure da yardaba.." abun da ya ta jaddadawa cikin ran sa kenan.
Habeebti kuwa ko da ta kai Junior d'aki baccin dole ta
sa shi. Ita kad'ai tai ta nishad'i duk sanda ta tuna yanda ta yiwa
Haroun,ba za ta mance yanda fuskar sa ta koma ja ba tsabar azaba,fatan
ta Allah ya sa ta ji masa ciwo yanda ya na ji ya na gani zai zama
fanfanfayo. Kunna wayar ta ke da wuya wayar Yakumbo ta shigo,bayan sun
gaisa sosai ta tambayi Junior Habeebti ta fad'a ma ta ya na bacci,su ka
tab'a hirar su sannan su ka yi sallama. Sai kuma wayar Hajiya wacce ita
tsoran ta kar dai Haroun ya k'ara aikatawa Habeebti na rannan,amma jin
ta garau ta san ko ma an aikata na hankali aka yi,da za su yi sallama
Hajiya ta ce "Aliya tun da Allah ya had'a ki da jarababban miji sai ki
yi hakuri ki na yawan shiga ruwan zafi akai akai" da har za ta ce sai
dai Haroun ya shiga ruwan zafi yau dai,amma sai ta fasa ta amsa mata da
"umhum" su ka yi sallama. Haka dai tai ta amsa waya kamar dama jira ake
ta kunna wayar.
Haka kuma wanda su ke kusa ta ita sun shigo mata,amma duk yawancin su ba musulmai ba ne,ko kuma musulmai ne amma ba hausa saboda ba yaren su ba ne. Mai Junior kuma tunda Habeebti ta yi maganin sa be iya fita ko nan da kofar gida ba,d'aki ya yi kwanciyar sa dan gani ya ke ba ma zai iya takawa sosai ba,dan ma Allah ya taimake shi weekend,Sunday so aiki sai gobe. Habeebti da d'ari d'ari ta wuni ranar dan ta san ta aikata aikatacciya,da ta ji motsi sai ta fara raba idanu,ta na jiran ganin Haroun.
.Haka kuma wanda su ke kusa ta ita sun shigo mata,amma duk yawancin su ba musulmai ba ne,ko kuma musulmai ne amma ba hausa saboda ba yaren su ba ne. Mai Junior kuma tunda Habeebti ta yi maganin sa be iya fita ko nan da kofar gida ba,d'aki ya yi kwanciyar sa dan gani ya ke ba ma zai iya takawa sosai ba,dan ma Allah ya taimake shi weekend,Sunday so aiki sai gobe. Habeebti da d'ari d'ari ta wuni ranar dan ta san ta aikata aikatacciya,da ta ji motsi sai ta fara raba idanu,ta na jiran ganin Haroun.
Zuwan sa aiki ba k'aramin sakewa Habeebti ke samu ba. Kafin ya dawo ta dafa duk abun da za ta dafa,kuma sai ta tabbatar na daidai cikin ta ne,kafin kuma ya dawo ta gama komai ta gyara kitchen yanda ba ma wanda zai ce an yi wani hidima cikin kitchen din in dai ba wai fad'a ma aka yi ba. Shi kan shi ya na mamakin haka,kullum ya kwaso yunwar sa sai dai ya zo ya ga wayam,idan ya tambaya ta ce "ka aje kuku ne agidan ka?" Dan haka sai ma ya daina tsammanin abuncin daga gare ta,kafin ya dawo sai ya tabbata ya cika timbin sa,dan kuwa ya na dan shakkar ganganci Habeebti tun da ta gwada ma sa hauka.
Satin Habeebti d'aya a barracks ta saba da wata mace mai
matsaikaicin shekaru,wacce ake kira mama Eze. Mijin ta Emeka direban
sojoji ne wanda ya ke kurtu. Amma mutumin Haroun ne sosai,kuma apartment
din su be da nisa da na Haroun. Kullum safiya gun ta Habeebti ke zuwa
siyanwa Junior k'osai ta haka su ka saba,sai dai matsalar Mama Eze
gulma,gulma da zancen mutane cikin ta har da na siyarwa. Kullum in dai
Habeebti ta je gun ta sai ta sha gulmar yan barracks,hakan be hana mutum
ya zo wucewa ba ta yi shunan sa da baki kafin ya wuce ta sa faifaisa.
Ita dai Habeebti ba ta tanka mata ba,dan ta san ita ma haka ta ke yiwa
mutane na ta.
Ranar wata talata ne Habeebti ta tashi da matsanancin ciwan jiki ga kuma d'aci da bakin ta ke mata,dan ko siyan k'osan ma ba ta iya fita ba,sai Maman Eze ce ta kawo mata har gida bayan ta tashi daga suyan. Ranar haka ta wuni a daddafe. Ana yin magarib kuwa zazzab'i ya rufe ta. Da kyar ta samu ta iya yin sallar isha,ko shafa'i da wutiri ba ta iya yi ba. Junior be ya dame ta da kukan yunwa a dole ta fita kitchen nemo masa abunci dan kuwa yau be samu abuncin arziki ba.
Miya ta zubo tare da bread,nan falo ta zauna da niyar bashi yanda ya na gama ci za ta mik'a plate din kitchen. Amma yaro da rigima wai alalle sai dai ta bari yaci da kan sa. Da ke dama ba k'arfi gare ta ba sai ta sakar ma sa ta yi kwanciyar ta kan doguwar kujera.
Ranar wata talata ne Habeebti ta tashi da matsanancin ciwan jiki ga kuma d'aci da bakin ta ke mata,dan ko siyan k'osan ma ba ta iya fita ba,sai Maman Eze ce ta kawo mata har gida bayan ta tashi daga suyan. Ranar haka ta wuni a daddafe. Ana yin magarib kuwa zazzab'i ya rufe ta. Da kyar ta samu ta iya yin sallar isha,ko shafa'i da wutiri ba ta iya yi ba. Junior be ya dame ta da kukan yunwa a dole ta fita kitchen nemo masa abunci dan kuwa yau be samu abuncin arziki ba.
Miya ta zubo tare da bread,nan falo ta zauna da niyar bashi yanda ya na gama ci za ta mik'a plate din kitchen. Amma yaro da rigima wai alalle sai dai ta bari yaci da kan sa. Da ke dama ba k'arfi gare ta ba sai ta sakar ma sa ta yi kwanciyar ta kan doguwar kujera.
.
Ba junior ba,hatta carpet din falon sai da ya sami rabon sa,gaba d'aya yayi dumu dumu da miya ga kuma barbad'in bread ko ina. Sai da ya gama bawa cikin sa hakkin sa yayi dam sai kuma ya fara mata kukan wai lalle sai ta goya sa.
Daga kwance ta ke kallan sa har rawan sanyi ta ke,ta ce
"na bacci ka ke nema,za kuma ka samu wallahi" takowa yayi wajan ta,ya
na k'ok'arin goga mata hannun sa da yayi dumu dumu da miya,Habeebti ta
yi saurin tura shi gefe ba da niya ba sai ga yaro a k'asa ya sa kuka
wanda hakan yayi dadai da shigowar Haroun,sanye da kaki.
Da sauri ya aje jakar hannun sa ya na fad'in " Yaa Salam! Ke muguntar ki ba ga yaro ba ba ga babba ba,yanzu da ki ka hankad'a sa da kin ji masa ciwo sai ki ce fa kin fi kowa idanun kuka..." Ya na magana ne yayinda ya k'arsa ya d'auki Haroun Junior,wanda tuni ya bi ya goge miyar hannun sa jikin kakin Haroun,wanda ganin haka ya dan ja da baya sai ji yayi k'afar sa ta sauka ciki plate mai dauke da rogowar miya. Da sauri ya cire k'afar ta sa da ta riga ta kwaso miya,sai a sannan ya lura da da yanayin datti da falon ya ke ciki.
Cikin bacin rai ya ce
Da sauri ya aje jakar hannun sa ya na fad'in " Yaa Salam! Ke muguntar ki ba ga yaro ba ba ga babba ba,yanzu da ki ka hankad'a sa da kin ji masa ciwo sai ki ce fa kin fi kowa idanun kuka..." Ya na magana ne yayinda ya k'arsa ya d'auki Haroun Junior,wanda tuni ya bi ya goge miyar hannun sa jikin kakin Haroun,wanda ganin haka ya dan ja da baya sai ji yayi k'afar sa ta sauka ciki plate mai dauke da rogowar miya. Da sauri ya cire k'afar ta sa da ta riga ta kwaso miya,sai a sannan ya lura da da yanayin datti da falon ya ke ciki.
Cikin bacin rai ya ce
"No wonder kullum ki ke cikin d'aki kamar daddawar
d'aka,dare d'aya da ki zauna a falo ji environment din da ki ke kwance,i
can't blv you can be dis dirty" ya zuya a fusace,Junior a hannun shi,ya
na dingishi saboda kar ya taka kafar da ya kwaso miya ya dad'a b'ata
wajan wai shi mai tsafta ya shige d'akin sa.
Bin shi da ido Habeebti ta yi,cikin ran ta kuwa murmushi kawai ta yi,maza kenan,sarakan kyamkyami amma sai k'azanta. Kai tsaye toilet ya kai Junior,har da masa wanka,shi ma yayi,sanye da farar jallabiya ya zo ya wuce Habeebti da sam be lura da rawan sanyin da ta ke ba,ya shige d'akin ta,ganin ba ta biyo shi ba jikin sa ya fara ba shi ba lafiya. Cikin d'aya daga akwatinan ta ya d'auko kayan Junior,har da diaper sannan ya fito. Har ya wuce ta ya dawo ya tsaya gaban ta ya na duban,sai a sannan ya lura da rawan sanyin da ta ke. Sun kuyowa ya yi da niyar tab'a goshin ta,Habeebti ta buge hannun. Zafin da ya ji daga hannun ta da ta sa ta buge na shi ya sa shi dad'a rikicewa,ya kara kai hannu goshin ta,ta sa hannu ta buge. Kusan sau uku suna haka kafin ya hakura ya ce "taurin kan tsiya,ina zuwa i will get back to you"
A gurguje ya koma wajan Junior da tuni ya fara bacci. Cikin sauri ya sa ma sa kaya in da ya kasa sa ma diaper,kawai sai ya sa ma sa wando ya na mai fatan baya fitsarin kwance,dan hankalin sa ya yi kan Habeebti ko addua be yiwa Junior ba ya koma gun ta.
Bin shi da ido Habeebti ta yi,cikin ran ta kuwa murmushi kawai ta yi,maza kenan,sarakan kyamkyami amma sai k'azanta. Kai tsaye toilet ya kai Junior,har da masa wanka,shi ma yayi,sanye da farar jallabiya ya zo ya wuce Habeebti da sam be lura da rawan sanyin da ta ke ba,ya shige d'akin ta,ganin ba ta biyo shi ba jikin sa ya fara ba shi ba lafiya. Cikin d'aya daga akwatinan ta ya d'auko kayan Junior,har da diaper sannan ya fito. Har ya wuce ta ya dawo ya tsaya gaban ta ya na duban,sai a sannan ya lura da rawan sanyin da ta ke. Sun kuyowa ya yi da niyar tab'a goshin ta,Habeebti ta buge hannun. Zafin da ya ji daga hannun ta da ta sa ta buge na shi ya sa shi dad'a rikicewa,ya kara kai hannu goshin ta,ta sa hannu ta buge. Kusan sau uku suna haka kafin ya hakura ya ce "taurin kan tsiya,ina zuwa i will get back to you"
A gurguje ya koma wajan Junior da tuni ya fara bacci. Cikin sauri ya sa ma sa kaya in da ya kasa sa ma diaper,kawai sai ya sa ma sa wando ya na mai fatan baya fitsarin kwance,dan hankalin sa ya yi kan Habeebti ko addua be yiwa Junior ba ya koma gun ta.
.
Wannan karan da ya zo tab'a goshin ta ba ta hana shi ba. Da sauri ya janye hannun sa daga jikin ta da yayi zafi kamar wuta. Da sauri ya d'auke ta da niyar kai ta asibiti,sai kuma ya yi wani tunani dan a gaskiya taimakon gaggawa Habeebti ta ke nema. Dan haka sai ya wuce da ita d'akin ta gudun kar ya kai ta na shi su tada Junior. Kan gadon ta ya kwantar da ita,ya shiga band'aki ya debo ruwan sanyi cikin wani dan roba da dan k'aramin towel din ta. Da ke riga da zani ne jikin ta,sai yayi kok'arin rage mata kayan jikin ta,wanda hakan ya sa ya sami ladan duka ba adadi,amma be hana shi ba. Cikin undies din ta ya barta,zuciyar shi d'aya ya shiga tsamo towel din,duk sanda ya d'ora jikin Habeebti sai ta yi dan k'ara kuma ba ta fasa buge hannun sa tana kok'arin rufe kan ta...ya na" Sannu Habeebti,sannu my Habeebti"
Kusan minti goma Allah ya sa jikin Habeebti ya rage
zafi,zazzabin ya sauka,amma rawan sanyin da ta ke yi ya ma fi na
d'azu,sai a sannan ya lura da AC din d'akin kunne ya ke,ya tashi da
niyar zai je ya kashe Habeebti ta rik'o hannun sa. Cikin rarrashi ya ce "
ba tafiya zan yi ba my Habeebti,ina tare da ke,AC kawai zan kashe...." A
hankali ya zare hannun sa daga na ta sannan ya je ya kashe,ya dawo.
Ganin yanda ta ke rawan sanyi ya yanke hukunci kwanciya da ita,may b ta
sami body contact zai ragu sai su tafi asibiti. Dan haka sai ya cire
jallabiyar shi,gajeran wando ya rage ma sa,ya hau gadon gami da jawo
Habeebti da ke k'udundune cikin bargo,yayi hugn din ta sosai tare da
rufa mu su bargo. Rawan sanyin da ta ke ya ragu sosai,har ta kai bacci
ya na dan d'ibar ta. Ba ita ba,hatta Haroun da dama ya kwaso gajiya nan
bacci ya kwashe shi. Tym to tym jikin na ta na dad'a zafi,yana farkawa
ya na goge mata. Sai wajan biyun dare su ka sami bacci ishasshe.
Bacci yayiwa Haroun dad'i,ba shi ya tashi ba sai da aka idar da sallar asuba. Ganin Habeebti kanannad'e jikin sa har da murmushin shi mai k'ayatarwa,"ina ma ace haka ya ke bacci kullum da sai ya fi sarki jin dad'i" abun da ya ke fad'a cikin ran sa kenan,yayinda ya zame jikin sa daga na Habeebti,ya tashi a hankali. Jikin ta ba zafi sosai amma har yanzu akwai zazzabi,da tunanin gari na wayewa zai kai ta asibiti ya shiga toilet d'in ta ya d'auro alwala. Nan cikin d'akin ta ya yi sallah. Amma be tada ita ba ganin yanda ta sha wuya kafin ta samu bacci jiya.
Da ke Haroun be iya cin kwan makauniya ba,ko da ya idar da sallah maimakon ya tafi d'akin sa,sai ma dad'a kwanciyar sa yayi har da wani jawo Habeebti jikin sa,ita kuwa cikin bacci har da gyara kwanciya da kyau. Cikin jin dad'i Haroun yayi kasadar k'ara gyara mata kwanciyar.
.Bacci yayiwa Haroun dad'i,ba shi ya tashi ba sai da aka idar da sallar asuba. Ganin Habeebti kanannad'e jikin sa har da murmushin shi mai k'ayatarwa,"ina ma ace haka ya ke bacci kullum da sai ya fi sarki jin dad'i" abun da ya ke fad'a cikin ran sa kenan,yayinda ya zame jikin sa daga na Habeebti,ya tashi a hankali. Jikin ta ba zafi sosai amma har yanzu akwai zazzabi,da tunanin gari na wayewa zai kai ta asibiti ya shiga toilet d'in ta ya d'auro alwala. Nan cikin d'akin ta ya yi sallah. Amma be tada ita ba ganin yanda ta sha wuya kafin ta samu bacci jiya.
Da ke Haroun be iya cin kwan makauniya ba,ko da ya idar da sallah maimakon ya tafi d'akin sa,sai ma dad'a kwanciyar sa yayi har da wani jawo Habeebti jikin sa,ita kuwa cikin bacci har da gyara kwanciya da kyau. Cikin jin dad'i Haroun yayi kasadar k'ara gyara mata kwanciyar.
Ya kai kusan minti talatin ya na duban ta,shi ne har da dan kissing idanun ta da hakan ya sanya ta bud'e idanun a hankali,dama naturally sleepy eyes gare ta,ga kuma bacci ya zame mata biyu,fuskar ta d'auke da murmushin da ya kusa tsaida bugun zuciyar Haroun ta dad'a lumshe idanun ta. Haroun be san sanda ya dad'a hugn din ta ba har ta kai ga Habeebti wacce ke mafarkin gata kwance da Mahaifiyar ta margayiya farkawa gaba d'aya.
Da fari sam kasa gane yanayin da ta ke ta yi,ita dai ta ji ta
rungume jikin mutum tsabar yanda ya matse ta da kyar ta ke kwakkwarar
numfashi.....kuma..sai a sannan ta shafa jikin ta,ta gane ashe undies
din ta ne kawai sanye da ita....ihu ta kurma wanda hakan ya sa Haroun
sakin ta da sauri...ita ma din da sauri ta ja gefe ta na me rarubar
bargo don rufe jikin ta. Fad'i "ta ke me ka min? Mugu me ka min!!"
Cikin lallami ya ce "Dan Allah ki yi k'asa da muryar ki my Habeebti,akwai mak'Oya fa kar ki manta ba nisa gare mu ba,za su ji" ina idanun Habeebti ya rufe ga wani sarawa da kan ta ya ke,ta ce " an ki a yi a hankalli d'in,answer me dallah,me ka min na ce?" Cikin lallami ya ce " gode min ya kamata ki yi,ba ki da lafiya,kula na yi da ke..." Ya na magana ne ya na k'ok'arin rik'o ta. Da sauri ta yi baya ta na mai buge hannun sa,ta ce "Mara tsoran Allah,dama kiris ka ke jira ka k'ara samin dama cimma burin ka,you can't wait na zama unconscious ka yi taking advantage d'ina,ka samu ka yi raping d'ina..."
Cikin lallami ya ce "Dan Allah ki yi k'asa da muryar ki my Habeebti,akwai mak'Oya fa kar ki manta ba nisa gare mu ba,za su ji" ina idanun Habeebti ya rufe ga wani sarawa da kan ta ya ke,ta ce " an ki a yi a hankalli d'in,answer me dallah,me ka min na ce?" Cikin lallami ya ce " gode min ya kamata ki yi,ba ki da lafiya,kula na yi da ke..." Ya na magana ne ya na k'ok'arin rik'o ta. Da sauri ta yi baya ta na mai buge hannun sa,ta ce "Mara tsoran Allah,dama kiris ka ke jira ka k'ara samin dama cimma burin ka,you can't wait na zama unconscious ka yi taking advantage d'ina,ka samu ka yi raping d'ina..."
Fusata Haroun ya yi jin kalaman Habeebti,ya ce " dallah
kar ki zama sokuwa da gangan mana,me na mi ki toh? Kin duba jikin ki
kinga na tab'a ki ne? Ko ko jiyan ma kin sha kwaya ne?in akwai ma wanda
ya kamata ya yi fad'a ni ne,because you tried to seduce me woman!"
Kalaman sa ne ya sa Habeebti sakin baki,kafin daga bisani ta d'auki filo ta jefi Haroun da shi,yayi saurin kaucewa,nan ta shiga jifan sa da duk abun da ya zo hannun ta,tana fad'in "fitar mun daga d'aki,na tsane ka!na tsani ganin ka mugu kawai...." Ganin haka Haroun ya tashi da sauri kan ya fita sai da ya ji saukar wayar ta a gadan bayan shi,kafin ta fad'i k'asa ta tarwatse.
Ya na fita d'akin sa ya nufa,ran sa idan ya yi dubu ya b'aci. Tura kofar sa da wuya wani wari ya bugi hancin sa,sai da yayi baya da sauri,hunnun sa bisa hancin sa ya daure ya tura k'ofar a hankali ya na mai raba idanu....nan bisa kan gadon sa ya ga abun da ya haddasa warin. Wato Junior ne ya dank'ara tutun sa cikin wando,sannan ya cire wandon ya damalmala kashin jikin sa da ma kan bed sheet din gaba d'aya. Ganin Haroun tsaye kan sa da gaba d'aya ma ya manta da rayuwar Junior,Junior ya kyalkyale da dariya.
Kalaman sa ne ya sa Habeebti sakin baki,kafin daga bisani ta d'auki filo ta jefi Haroun da shi,yayi saurin kaucewa,nan ta shiga jifan sa da duk abun da ya zo hannun ta,tana fad'in "fitar mun daga d'aki,na tsane ka!na tsani ganin ka mugu kawai...." Ganin haka Haroun ya tashi da sauri kan ya fita sai da ya ji saukar wayar ta a gadan bayan shi,kafin ta fad'i k'asa ta tarwatse.
Ya na fita d'akin sa ya nufa,ran sa idan ya yi dubu ya b'aci. Tura kofar sa da wuya wani wari ya bugi hancin sa,sai da yayi baya da sauri,hunnun sa bisa hancin sa ya daure ya tura k'ofar a hankali ya na mai raba idanu....nan bisa kan gadon sa ya ga abun da ya haddasa warin. Wato Junior ne ya dank'ara tutun sa cikin wando,sannan ya cire wandon ya damalmala kashin jikin sa da ma kan bed sheet din gaba d'aya. Ganin Haroun tsaye kan sa da gaba d'aya ma ya manta da rayuwar Junior,Junior ya kyalkyale da dariya.
A fusace kamar mai shirin kuka Haroun ya kada baki ya ce
" Wato ita ta na can ta na masife ni ladan jinyar ta da na yi,kai kuma
ka nan ka na jik'a min aiki,ko shakka babu wannan yaron da uwar sa sune
ajalina....!!!"
.
Rasa yanda zai yi da Junior ya yi,ga warin da ya
addabe shi, jiya an b'ata waje da miya ya kira matar shi k'azama,shi
kuma gashi da kashi aka masa ado. Sai a sannan ya gane duk macen da ka
gan ta da d'an ta sai dai ka kalle ta kawai,Allah kadai ya san yanda ta
ke fama( Allah ya sakawa iyayen mu mata da alkhairi,amen).
Fuskar nan ba fara'a da hannun d'aya ya d'auki Junior
cike da kyamkyami ya kai shi toilet ya dire shi ciken bath tube. Da kyar
ya iya cire ma sa rigar ya shiga kuzawa yaro ruwa,tun junior na dariya
har ya fara dan shid'ewa sannan ya iya wanke ma sa kashin tare da masa
wanka.
Hakannan d'in sa tik ya wuce da shi d'akin Habeebti.
Ya tadda ta kan dadduma ta idar da sallah,gaban ta ya dire junior ba
tare da ya tanka ba ya juya ya fita. Ganin yanda Haroun ya ke cika ya na
batsewa,ga Junior tik d'in sa ruwa na d'isa daga jikin sa ya sa
Habeebti murmusawa dan tabbasa Junior ya yi tsiya kenan,asuba ta yi ba a
sa shi kan fur ba ko dai yayi fitsari ko kashin kwance. Ba ta san sanda
dariya ta kwace ma ta ba,haka ta tashi ta na shirya Junior ta na
dariya, Junior na taimaka mata da na shi dariyar,lalle Junior ya sa Mai
junior aiki.
Shi kuwa mai Junior gaba d'aya bed sheet d'in ya cire ya had'a har wandon Junior ya fita ya wulgar, fad'i ya ke "d'an yaro sai shege warin kashi kamar na manya!ba ka k'ara kwana d'aki na" daga kofa har window na d'akin wangale su ya yi,ga fanka da ya saki.
Sai da Junior ya ci abunci sannan ta iya shiga wanka a daddafe,dan ita abuncin ma kasa ci ta yi. Daga cikin toilet ta ke jiwo Haroun Junior ya na d'an wasannin sa. Tin ya na jiyo Junior,har ta ji shiru. Sai ta yi tunanin bacci ne ya d'auke shi.
.Shi kuwa mai Junior gaba d'aya bed sheet d'in ya cire ya had'a har wandon Junior ya fita ya wulgar, fad'i ya ke "d'an yaro sai shege warin kashi kamar na manya!ba ka k'ara kwana d'aki na" daga kofa har window na d'akin wangale su ya yi,ga fanka da ya saki.
Sai da Junior ya ci abunci sannan ta iya shiga wanka a daddafe,dan ita abuncin ma kasa ci ta yi. Daga cikin toilet ta ke jiwo Haroun Junior ya na d'an wasannin sa. Tin ya na jiyo Junior,har ta ji shiru. Sai ta yi tunanin bacci ne ya d'auke shi.
Ga mamakin ta da ta fito ba Junior babu alamar sa. A hanzarce ta yafa mayafi,ta bazama neman Junior ta na kwalla ma sa kira,amma shiru, ganin d'akin mai Junior a bud'e ya sa ta lek'awa,wani d'an wari wari ta ji ya na tashi,gadon ko bed sheet babu bare a yi batun gyara. Ba Junior babu mai Junior. Har band'aki ta duba amma sai rigar Junior ta tsinta.
Hankali tashe ta koma d'akin ta,wayar da tun da ta jefi
mai Junior ta tarwatse ta shiga had'awa hannu na rawa..sai a sannan ta
lura da jakar kayan Junior ba ya inda ya ke aje. Wannan ya sa ta
rud'ewa,ta ringa kok'arin kunna waya amma ya k'i kunnuwa. Hawaye ta ke
ta na buga hannayen ta bisa cinyar ta,fad'i ta ke "shikenan ni Aliya
wannan mutumin ya kassara ni!ina ya kai min d'a!" A wannan yanayin ta ji
ana buga mata gida,da sauri har da sassarfa ta je ta bud'e,Mama eze ce
ta zo,ganin yanayin da Habeebti ta ke ciki ya sa tunanin jikin ne,ta ce
"Ayya Mrs Haroun,ya jiki?dama Oga Haroun ya ce na zo na raka ki
hospital..." Habeebti da tuni ta fita daga hayyacin ta ce " Maman
Eze,ina ya ke?ina Oga Haroun din ya ke?" Cike da mamaki Maman Eze ta ce "
him don travel na! Shi da Papa Eze,shi ne ya ce na zo na kai ki
hospital.." kawai sai ta sawa Mama Eze kuka. Cikin tausayawa Mama Eze ta
ja ta su ka zauna,tai ta rarrashin ta kafin ta samu ta yi shiru. Sannan
ta ke tambayar ta dalilin kukan ta. Har za ta fad'a mata sai ta tuna
wacece Mama Eze,uwar gulma kenan,bare kuma ba kowa ake budewa sirrin
gidan ka ba. Dan haka ta sake shawara ta ce tsabar ciwo ne. Duk da ba ta
gamsu ba,sai cewa ta yi " toh ta shirya su tafi ma na"
Habeebti na share hawaye ta tashi,sai da ta shiga ciki ta ruke k'ugu," "Shin shi wannan mutumin ina ya kai mata d'a?" Cike da masifa ta ke tambayar kan ta," lalle mutumin nan ba k'aramin fitina ya ke nema ba,amma bari na je hospital d'in,sai da lafiya ake iya komai,i need d strength" da wannan tunanin ta shirya ta su ka tafi.
Habeebti na share hawaye ta tashi,sai da ta shiga ciki ta ruke k'ugu," "Shin shi wannan mutumin ina ya kai mata d'a?" Cike da masifa ta ke tambayar kan ta," lalle mutumin nan ba k'aramin fitina ya ke nema ba,amma bari na je hospital d'in,sai da lafiya ake iya komai,i need d strength" da wannan tunanin ta shirya ta su ka tafi.
Sai da aka ma test aka ga maleria ke damun ta. Aka ba ta
magani da allurai sannan su ka dawo gida. Har su ka je su ka dawo
hankalin Habeebti ba ya gare ta. Tym to tym sai Mama Eze ta dan tab'a ta
sannan ta ke iya bata amsa.
.Ranar dai haka ta wuni ta na jinya ta na farautar Mai Junior. Bashi ya dawo ba sai wajan bayan isha'i ta ji motsin shi. Riga da siket ne a jikin ta,english wears. Dan masifa yau ko mayafi bare hijabi ba ta tsaya d'auka ba,kanta ba kitso ta dai yi parkn gashin ta a k'eya. Kai tsaye d'akin sa ta fad'a ba ba tare da ta yi sallama ba. Ganin Haroun tsaye ya na cire kaya,be hana ta saurara ma sa ba ta je ta sha gaban sa hannun ta ruk'e da k'ugu ta ce "Malam ina ka kai min d'a?" Ko kallan ta be yi ba,bare ya nuna ya san da shi ta ke,ya ci gaba da cire kayan sa. Ta k'ara da "ka na ji na fa....." Ganin ya na k'ok'arin cire belt ya sa ta juyawa baya da saurin da har sai da ya murmusa tare da fad'in "mara kunyar karya..." Sai da ta d'au kusan minti goma yanda ta tabbatar ya gama ko ma me ya ke ta juyo,amma sai ta ga wayam,sai kuma ta ji k'arar ruwa na sauka a toilet,ga shi dai k'ofar a bud'e ya bari. Tsaki ta ja ",Mtsw dan iskan mutum dai be ji dad'in rayuwar sa ba!" Ta fad'a cikin ran ta,yayinda sim sim ta kwashe k'afar ta ta yi waje da karfi ta ce " za ka fito ka same ni,sai ka fito min da d'ana!"
Falo ta je ta kame jiki na rawa dan masifa. Ya kai
kusan awa d'aya kafin ya fito cikin shigar kananan kaya,wando wanda be
kai har k'asa ba da riga mara hannu duka bak'ak'e,ya yi kyau kwarai ga
kamshi sai tashi ya ke. Ta na ganin sa ta tashi tana fad'in "Tambayar ka
fa na ke fa Mallam!" Hannun sa biyu cikin aljihun wandan sa ya nufo kai
tsaye,wanda hakan ya sa bugun zuciyar ta k'aruwa,ganin ya kusa dabda
ita,ya sa ta fara ja da baya,har ta ji ta daram ta zauna kan kujera.
Haroun kuwa ya kawo in da take,sun kuyowa yayi,kamshin sa ya dad'a
mamiye ta,kallan ta ya tsaya yi ganin yanda ta takure kan ta,ta kasa ko
motsi idanun ta runtse.
Murmushi ya saka yayinda ya kai hannu ga goshin ta,ya
danyi sakanni sannan ya ce " well nt bad compare to fever din jiya"
sannan ya sauke hannu ya mayar cikin aljihu ya juya zai fice....jin ya
matsa daga kusa da ita ya sa ta sakin ajiyar zuciya,sannan ta tashi da
sauri ta ce " Haroun ina ka kai min d'a?" Ya na sa takalmi ba tare da ya
juyo ba ya ce da ita " ashe kin san sunana My Habeebti" shiru ta yi ta
na sauraran sa,dan wulak'anci irin na Mai Junior,sai da ya bari ya je
bakin kofa,sannan ya juyo ya ce "ya na gidan marayu.." sannan ya sakar
mata dariyar mugunta ya fice.
Wani irin kuka ta saki,ta zube k'asa har da burgima. Dama ta san rashin arziki irin na Haroun,yanzu shi dan zaman da yayi na k'ank'anin lokaci ya tsani Junior har ya kai ga kai ma ta d'a gidan marayu!ita da ta raini cikin da ba na dan halas ba, har tsawan wata tara,ta haife,ta shayar ta goya ta mutu kenan?ga shi ba ta da waya bare ta kai k'ara gida. Ai Kaduna ba bak'onta ba ne,da ta kwana rumfa d'aya da Haroun gwara ta yi kwanan titi. Da wannan tunanin ta tashi ta had'e kayan ta tsaf,da kud'in ta dubu biyar a haka ta zura hijabi hannun ta d'auke da jakar kayan ta,ta rufo gidan ta yi fitowar ta.
.Wani irin kuka ta saki,ta zube k'asa har da burgima. Dama ta san rashin arziki irin na Haroun,yanzu shi dan zaman da yayi na k'ank'anin lokaci ya tsani Junior har ya kai ga kai ma ta d'a gidan marayu!ita da ta raini cikin da ba na dan halas ba, har tsawan wata tara,ta haife,ta shayar ta goya ta mutu kenan?ga shi ba ta da waya bare ta kai k'ara gida. Ai Kaduna ba bak'onta ba ne,da ta kwana rumfa d'aya da Haroun gwara ta yi kwanan titi. Da wannan tunanin ta tashi ta had'e kayan ta tsaf,da kud'in ta dubu biyar a haka ta zura hijabi hannun ta d'auke da jakar kayan ta,ta rufo gidan ta yi fitowar ta.
Ta na tafe sam ba ta lura ba ta wuce Mama Eze da Emaka. Ganin ta Mama Eze za ta mata magana Emeka ya hana ta,ta hanyar fad'in " no no don't call her,can't you see she is crying nd even carrying a bag,ba lafiya ai!" Tab'e baki Mama Eze ta yi tare da fad'in" dat woman?ai she dai cry tun safe...." Cikin kwab'a Emeka ya ce "chai Mama Eze na amebo go kill una,sha make i call her husband" cikin nuna bacin rai Mama Eze ta yi gaba abun ta.
Haroun na cikin yan uwan sa sojoji suna shek'a ayar su,sai ga kiran
Emeka. Ya na d'agawa Emeka ya ce "Oga Haroun no b your wife i jst saw?"
Cikin wasa Haroun ya ce "in your dreams?" Cikin jaddawa dan ya ga Haroun
wasa ya d'au maganar ya ce "i swear i jst saw your wife,crying she dey
walka commot frm dis barracks" a nutse cikin ba da umarni ya ce " Emaka
make sure she don't go far,gani nan zuwa" ya aje wayar tare da mu su
sallama,har da masu mai tsiya wai tsoran matar shi ya sa be iya yin dare
a waje.
Da sauri ya ke tafiya,Allah da ya taimake shi ma Habeebti ba sanin kan hanyar barracks din ta yi ba. Ta na ta dibi dibi a hanya,ga dare ga bishiyoyi ya sa garin k'ara dubu,gashi ko hasken wata babu,dake k'arshen sha'aban ake,ana sa ran kamawar ramdan sati mai zuwa.
Kacibus su ka yi da juna,ko da Habeebti ta gwale ido ta ga shi din ne dai ba wani ba,sai ta saki jakar kayan ta juya za ta sa gudu. Taku uku ya k'ara caraf ya kamo kayan sa,ya d'aga ta sai ga ta a kafad'ar sa,ta na ihu ta na dukan bayan sa amma ko a jikin sa,ya durk'usa ya dau jakar,sannan ya mike gida.
.Da sauri ya ke tafiya,Allah da ya taimake shi ma Habeebti ba sanin kan hanyar barracks din ta yi ba. Ta na ta dibi dibi a hanya,ga dare ga bishiyoyi ya sa garin k'ara dubu,gashi ko hasken wata babu,dake k'arshen sha'aban ake,ana sa ran kamawar ramdan sati mai zuwa.
Kacibus su ka yi da juna,ko da Habeebti ta gwale ido ta ga shi din ne dai ba wani ba,sai ta saki jakar kayan ta juya za ta sa gudu. Taku uku ya k'ara caraf ya kamo kayan sa,ya d'aga ta sai ga ta a kafad'ar sa,ta na ihu ta na dukan bayan sa amma ko a jikin sa,ya durk'usa ya dau jakar,sannan ya mike gida.
Habeebti ba ta gushe ba sai dukan gadon bayan sa ta ke tana kiran sa " Mugu,dallah ka sauke ni Mugu! Mugu! Mugu kawai!..." Sai ga Emeka a gaban su yana haki,ganin su sai ya biyo bayan su har su kai gida. Haroun zai shiga gida ya ji Emeka ya ce" Oga she keep calling you mugu,y na?" Ya aje jakar ya na k'ok'arin bud'e k'ofa da mukulli ya ce "It is my wife way of saying swthrt" jin haka ya sa Habeebti k'ara kai ma sa duka...ya na dariya ya bud'e kofa,ya d'auki jakar,har ya shiga ya juyo ya ce " And Emeka tnx for today..." sannan ya tura k'ofa ya rufe.
Emeka da ya saki baki ya na kallan ikon Allah ya ce " en eh my
pleasure Sir" ya tafi ya na soshe soshe. Shigar su parlour kan kujera ya
zauna tare da aje Habeebti kan cinyar sa. Yunkurawa ta yi za ta
tashi,ya yi saurin maidota,ya sa hannun sa d'aya ya ruk'e duka hannayen
ta biyu. Sannan ya ce "wai menene ne Aliya? Shin da ki ka fita ina za
ki?ko tsoran dare ba kya ji? Um my Habeebti?" Cike da taikaici fuska fal
hawaye ta ce " ina ruwan ka da ni Malam! D'a zan je na nemo!" Ya na
murmushi ya ce " gidan marayu za ki je?ai da sai ki tambaye ni na wani
garin,amma dai bara na kira mi ki shugabar wajan" wayar sa ya kira wata
number,jin an d'aga ya kara kunnan Habeebti,sai ji ta yi an ce " Mai
Junior wato ka biyo sahun d'an ka ko?ai gobe gobe zan aika shi Bichi dan
ya bi yara na da na mak'ota duk ya cije abun sa!" Anty Salmah ce ke
magana cikin zolaya. Jin haka ya sa Habeebti jin kunya,da k'yar ta iya
magana,jin ita ce ba mai Junior ba su ka gaisa da Aunty Salmah,har ta
mata ya jiki,Haroun ya ce mata ba ta da lafiya d'azu da ya kawo mata
Haroun Junior. Bayan sun gama waya ne dan kunya sai ta kasa d'aga ido ta
kalle shi.
Hannun ya sa ya d'ago fuskar ta sannan ya ce " My
Habeebti,yanzu hankali ya kwanta?" Ta yi masa shiru,ya k'ara da "yanda
na ga kina san My Junior ya tabbatar min da ki na so na tunda d'a na
ne,kya so d'a ki k'i uban sa..?" Cikin tsiwa ta d'aga ido ta kalle shi
ta ce " no na tsane ka,na tsane ka Haroun,na tsani ganin ka!"
A hankali ya shafa fuskar ta kafin ya ce " ni kuma san
ki na ke Aliya,ina san ki,undiluted love,so was it randa na fara d'ora
idanuna kan ki,so it is yanzu da ki ke mallaki na,so be it Aliya....or
let me die.." ido ta k'ura ma sa na tsawan wani lokaci,yayinda zazzafan
hawaye ya gangaro daga idanun ta ta ce "You shouldn't hav raped me.."
yatsa ya sa ya bi hawayen ta da ya gangaro ya na gogewa sannan ya ce "
Am sorry for dat Aliya,believe me i am...."
0 comments:
Post a Comment