Kamar saukar aradu haka ya yi kan Haroun,ji ka ke tas.!! ya dauke kumatun sa da marin da sai da Haroun yayi baya zai fad'i,Dawud yayi saurin cin kwalar sa ya had'a shi da bango,ko kok'arin kare kan sa Haroun be yi ba bare ya kai ga azancin ramawa,Mama ta fashe da kuka ta na fad'in "jama'a ku taimaka ku shiga tsakanin su dan Allah,Dawud kan ka daya kuwa...." Ummi kuwa sai tafa hannu ta ke ta na sallallami,Yayinda sauran jama'ar gun su ka kawowa Haroun d'oki,amma ina ba karamin duka ya ke karba gun Dawud ba,abun da ya dad'a d'agawa Mama hankali ganin jama'a sun kasa kwatar sa daga hannun Dawud.
Kuka take ta na fadin "ku bari ya kashe shi ma
kawai,wannan masifa da mai ta yi kama idan ba ka kashe shi ba baka isa
dan halal ba Dawud"
"Dawud!!!!!" Jin muryar da ta kirasa da kakkausar sauti
ya sa Dawud tsayawa cak ba tare da ya saki Haroun ba wanda ya sha bugu
kwaran gaske ..."you ar stupid!!!"Alhaji ya daka ma sa tsawa,ya k'ara
da" You ar very stupid indeed! Let go of him....ryt now!!!"
A sanyaye ya na huci kamar zaki ya saki Haroun,nan ya zube yana goge jinin da ke zuba daga bakin sa..Mama da Ummi su ka yi kan sa da sauri,Mama na kuka ta na fad'in "wannan ai rashin mutunci ne,wannan ai rainin arziki ne sannu Haroun,wai kai me ka ma sa haka ya ke wannan cin fuskar,Alhaji dubi yanda ya canza ma sa halitta dan Allah"
Nan fa kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa daga mai fad'in kar Mama ta yarda ta d'au mataki,sai mai fad'in ai a tsaye Haroun ya fi Dawud karfi,me ya sa ba zai rama ba ya tsaya har ya ma sa wannan bugu......
,A sanyaye ya na huci kamar zaki ya saki Haroun,nan ya zube yana goge jinin da ke zuba daga bakin sa..Mama da Ummi su ka yi kan sa da sauri,Mama na kuka ta na fad'in "wannan ai rashin mutunci ne,wannan ai rainin arziki ne sannu Haroun,wai kai me ka ma sa haka ya ke wannan cin fuskar,Alhaji dubi yanda ya canza ma sa halitta dan Allah"
Nan fa kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa daga mai fad'in kar Mama ta yarda ta d'au mataki,sai mai fad'in ai a tsaye Haroun ya fi Dawud karfi,me ya sa ba zai rama ba ya tsaya har ya ma sa wannan bugu......
Rai bace kamar mai shirin yin kwalla Alhaji ya ce " ka wuce office ka jira mu" kai a sunkuye ya wuce ciki dan kuwa be gama da Haroun ba. Bayan tafiyar sa Alhaji ya dubi Hajiya ya na fadin " Hajja Fadi ku ma ku zo ku same mu a office din" ya juya ba tare da ya kalli Haroun ba,dan gwara Dawud,shi ko ganin sa ba ya san yi. Ya na ji Hajiya na Alhaji ai da ka tsaya ka taimaka ma sa..."
Cikin Office d'in Doctor kuwa Doctor ne ya yayyafa ma
Hajiya ruwa,da taimakon Allah sai ga ta ta farfado wanda hakan yayi
daidai da shigowar Dawud,Alhaji biye da shi. Sai da ta dan yi Jim su
Ayub suna ma ta sannu,dan sai a sannan Dawud ya san ta ma sume. Sai
daga bisani kuma ta farga abun da ke faruwa ya kara dawo ma ta. Kuka ta
sa ta na fad'in "shikenan ni Mairo an kashe ni an gama da ni,Alhaji ya
zan yi da yar amana?Alhaji Haroun ya cuci Aliya"
Furucin ta karaf a kunnan Mama da sa k'afar ta kenan cikin office din biye da Ita Haroun da Ummi....
Tsaywa ta yi cak ta na mai zare ido,ta na magana ne cikin lame lame "Alhaji ahhh na ce Hajiya Mario wai waye ya yiwa waye umm fyad'e na ji an ce....?"
. Furucin ta karaf a kunnan Mama da sa k'afar ta kenan cikin office din biye da Ita Haroun da Ummi....
Tsaywa ta yi cak ta na mai zare ido,ta na magana ne cikin lame lame "Alhaji ahhh na ce Hajiya Mario wai waye ya yiwa waye umm fyad'e na ji an ce....?"
Budar bakin Hajiya sai cewa ta yi ."d'an ki Haroun ya yiwa d'iya ta
fyad'e....." "Innalillahi wainna ilaihi rajiun!" Fad'in Mama ta na mai
tafa hannayen ta,tambaya ta ke "wai wani d'an nawa ki ke magana? Wannan
ai ya sasheshshen zance ne! Hajiya Mario yanzu kiyayyar ta mu ta kai har
haka?
Kan Hajiya Mario ta kai ga bata amsa Alhaji ya katse ta
cikin tsawatarwa "Haba da Allah ku yiwa mutane shiru,wai da me za mu
ji?da aika aikan da aka yiwa yarinya ko kuwa da halin da ta ke ciki na
ita ba a mace ba ita ba a raye ba,ko da mutanen da yaran nan su ka tara
min waje ko kuwa yanzun ma jama'ar za ku tara min eh Hajiya Mario? Hajja
Fadi?" Tsit ka je,in ban da kukan Hajiya ba abunda ke tashi,sai Mama da
ta ke ta harare harare an yi wa d'an ta sharri.
Sai da wani dan lokaci ya shud'e ba wanda ya sake tankawa dan kuwa tunanin kowa ya tsaya. Kowa da abun da ya ke sak'awa cikin ran sa,musammam Haroun da ya kasa gasgatawa aikata ko u yi ashin aikata abun da ake zargin sa da shi.

.
Doctor da ke zaune tun d'azu ya na nazartar maganin da
Ayub ya ba shi,ya d'ago kan sa ya na mai duban Ayub cikin zurfin
tunani,daga bisani ya ce "kai da ka zo ka same su kwance,ka tabbatar
Haroun din a buge ya ke?
Ayub ya amsa ma sa da "eh dan be ma iya tashi ba sai da na kwara ma sa ruwa mai sanyi k'arara....." Doctor ya dawo da hankalin sa ga Haroun,duban sa ya ke da kyau ya na nazartar sa. Ya k'ara duban Ayub tare da fad'in ka tabbata a buge ya ke? Ayub ya jinjina kai. Hannu biyu Mama ta daura aka ta girgiza jiki kamar mai shirin tashi sama...
Doctor be gushe ba ya ce " Alhaji wannan ba hurumi na ba ne,amma gaskiya akwai abun da ya d'ore min kai,sannan kowa ne duk mutumin da ya ke a buge zai iya aikata komai,toh amma yanda Ayub ya ce Yayan sa ba ya cikin hankalin sa tsabar buguwa har takai sai da aka watsa ma sa ruwan sanyi k'arara,anawa hasashen ya bugu to d extreme level kenan,shin ba kwa mamakin ina ya sami karfi har ya iya yiwa mace fyad'e a wannan yanayin da ya ke ciki?duk da kuwa yarinyar ita ma a buge ta ke. Bayan haka mafi yawan hasashen mu ya nuna da wuya ka ga mutumin da ya bugu har haka ya tsinci kan sa cikin sha'awar da har zai iya aikata hakan,toh ina ma hankalin da nutsuwar gun dan Adam din da ba ya iya bambamce fari da baki? ya kamata a nutsu a duba abun nan logically musammam fmly case ne,kar ku yanke hukunci da gaggawa ku jira Allah ya tashi yarinyar nan ta fad'a mu ku da bakin ta....."

"Doctor ban tari numfashin ka ba.." Hajiya ce ta katse
shi dan d more ya ke magana d more ya ke dad'a kuntata ma ta ."me ka ke
nufi da ka ce wanda ya ke buge ba zai iya aikata wannan laifi ba...in ba
bugagge ba wazai afkawa yar mutane da rana tsaka ba kunya bare tsoran
Allah....." "Wanda yake da k'arfin aika ta hakan ya ke nufi ba bugaggen
da be ma san in da hankalin sa ya ke ba bare ya sami karfin aikata
hakan" Hajja Fadi ce ta ara ta yafa,ta k'ara da " ai ba Haroun kadai mu
ka tadda a gidan ba,eh in ma zargin ne ai har da d'an ki za a zarga,ba
mamaki ma shi yayi aika aikan ku ke san mak'alawa d'ana,ko ya gan shi ne
ya na aikatawa?kai Ayub ka ga Haroun da idanun ka ?toh wlh aniyar ku ta
biku....."
.
Hankalin kowa ya ga Ayub jin maganar Mama. Zufa ne ya
lullube shi dan magana ma kasawa ya yi. Hajiya ce ta ce lalle "Hajja
Fadi yau na tabbatar da rashin tunanin ki......." "Dan Allah Hajiya ku saurare ni" Doctor ne ya katse su
ganin maganar sa na shirin tada husuma,dan shi kan sa Alhaji shiru yayi
kawai kan sa sunkuye kamar ma hankalin sa ba ya office din.
"Me kuma za ka ce Doctor?ai ka gama magana!" Fadin
Hajiya kenan ta na mai hararar Mama. Doctor ya girgiza kai" ba ku
fahimce ni ba,abun da na ke nufi shi ne kar ku yi saurin yanke
hukunc......." "Gwara a hada har da wanda be ji ba be gani ba?"Hajiya ta
kara katse shi a hasale.
Kai kawai Doctor ke girgizawa,Alhaji ne ya ce "na fahimce ka Doctor,ni ma din ba wai na gama yanke hukunci ba ne,Allah ya tashi kafad'ar yarinyar nan,ni kuma na yi alkawarin daukan hukunci tsattsaura ga duk wanda ya aikata wannan rashin mutumcin a k'ark'ashin inuwa ta.."
Ya na magana ne ya na duban Haroun da Ayub,ya k'ara da "kun wulak'anta ni,kun tozarta ni,kun maishe ni mutum Mara daraja,ina mai tabbatar mu ku koma waye wannan sai ya fuskanci fushi na,sai an bi hakkin yarinyar nan ko da kuwa hakan ya na nufin fitar da wanda ya aikata hakan daga cikin jerin 'ya'ya na,wallahi sai na sallama shi...." ya na gama magana a fusace ya tashi ya fice. Ya bar Hajiya ta na saban kuka,Ummi da yau ta ga ta kan ta tana ba ta baki.
Ita kuwa Mama hannun Haroun wanda ke tsaye kamar mutum mutumin ta ja su ka yi waje,dan gani da ke da Dawud ya sami dama kashe shi zai yi.
Shi kuwa Dawud abun duniya ne ya masa yawa,tabbas akwai hikima a maganar Doctor,toh amma ya zai yi da rayuwar sa?ya rayuwar Habeebti za ta kansance?tabbas in dai masifa ta sami dan musulmi ba abun fad'i face Innalillahi wainnailaihi rajiun.
.Kai kawai Doctor ke girgizawa,Alhaji ne ya ce "na fahimce ka Doctor,ni ma din ba wai na gama yanke hukunci ba ne,Allah ya tashi kafad'ar yarinyar nan,ni kuma na yi alkawarin daukan hukunci tsattsaura ga duk wanda ya aikata wannan rashin mutumcin a k'ark'ashin inuwa ta.."
Ya na magana ne ya na duban Haroun da Ayub,ya k'ara da "kun wulak'anta ni,kun tozarta ni,kun maishe ni mutum Mara daraja,ina mai tabbatar mu ku koma waye wannan sai ya fuskanci fushi na,sai an bi hakkin yarinyar nan ko da kuwa hakan ya na nufin fitar da wanda ya aikata hakan daga cikin jerin 'ya'ya na,wallahi sai na sallama shi...." ya na gama magana a fusace ya tashi ya fice. Ya bar Hajiya ta na saban kuka,Ummi da yau ta ga ta kan ta tana ba ta baki.
Ita kuwa Mama hannun Haroun wanda ke tsaye kamar mutum mutumin ta ja su ka yi waje,dan gani da ke da Dawud ya sami dama kashe shi zai yi.
Shi kuwa Dawud abun duniya ne ya masa yawa,tabbas akwai hikima a maganar Doctor,toh amma ya zai yi da rayuwar sa?ya rayuwar Habeebti za ta kansance?tabbas in dai masifa ta sami dan musulmi ba abun fad'i face Innalillahi wainnailaihi rajiun.
Jin maganar Doctor ya na kiran sunan sa ya yi firgit ya dawo daga cikin kogin tunanin da ya tsinci kan sa. A hankali ya amsa da "Doctor ya halin da Habeebti ke ciki?za mu iya ganin ta?"
Cike da tausayawa Doctor ke duban Dawud,dan tabbas ya san akwai
dangantakar zuci tsakanin Dawud da Habeebti shi ya sa ya shiga
matsananciyar damuwa,ya ce "ta na gynea emergency saboda comma d'in da
ta shiga,ana ba ta gudunmawar gaggawa dan mu samu ta yi regainin
conciousness din ta, kan a mata dinki,dan a sanadiyar rape din anji ma
ta rauni,ta sami tear...." Shiru Doctor yayi ganin yanda Dawud ya runtse
idanun sa.....a hankali ya taba hannun sa yana fad'in "kar ka
damu,Allah zai ba ta lafiya.."
Hajiya ce ke kuka ta na surutai jin kalamin Doctor "wai kar mu damu,an yiwa yarinya budurwa fyad'e har da dinki za a mata wai amma kar mu damu,kin ji fa Ummi,wai kar ya damu...Allah ya idan ta,wlh sai Allah ya saka ma ta,yanzu ni Mario me zance da su Yakumbu?Allah ya isa wlh!!!!"

Wata Nurse ce ta leko,ta d'agawa Doctor kai ba tare da
ta yi magana ba,shi ma jinjina ma ta kai ya yi,yayinda ta koma ta rufe
mu su kofa.
.Cikin nutsuwa ya ce da Ayub "za ku iya ganin ta........" "Ta farfad'o ne?" Dawud ya tambaya da sauri. Kai Doctor ya girgiza ma sa," for now sai dai addua,za ku same ta gynea emergency room 8 amma...."ai ba su jira ya k'arasa magana ba gaba daya su ka fice da sauri,hannun Hajiya aka. Bin su yayi da kallo cikin tausayawa ya na fadin Allah ya kyauta.
K'ofar room 8 su ka tura da sauri kamar wanda aka watso,ganin
Habeebti kwance,ga oxygen cylinder bisa hancin ta, hannun ta na dama
daure da robar ruwa ya ya na d'ga d'is d'is. ga catheter da aka sa ma ta
biye da kafar ta. Idanun ta rufe,fuskar ta cike da layin hawayen ta da
ya bushe a fuskar ta ya yi fari.
Bakin k'ofa Dawud ya tsaya,k'afafuwan sa ne su ka ma sa nauyi,ya kasa d'aga su ya k'arasa ciki. Hajiya ce mai k'arfin halin karasawa ta na "Aliya,wayyo Aliya,Aliya"Ayub da Ummi da ke bayan ta sai hakuri su ke ba ta.
Ba Hajiya ba,Hatta Ummi sai da ta zibda hawaye,dan ba shakka cuta dai an cuci Habeebti. Dawud kuwa kallo daya ya ma ta,ya juya da sauri ya fice.

Sai da su ka isa falo sannan ta sake shi,gami da zuba
ma sa mari kwarara har uku,nan ya zube gwiwowin sa biyu a
k'asa,hannayen sa biyu ruke da kafafun ta,sai a sannan ya bud'i baki
murya na rawa ya ke fadin "wannan ya yi kad'an Mama,na cika d'a Mara
daraja,na cika Mara albarka,na cika d'an da ake Allah wadar da irin
shi,d'an da ke sa mahaifiyar sa kuka,dan Allah Mama ki kauda ni ki
huta,rayuwa ta ba ta da amfani......"
Nan Maman ta zube ita ma ta na kuka,ta ma rasa yanda za
ta yi da Haroun. Suna cikin haka Anty Salma wacce su Halima su ka sanar
da ita halin da su ka tadda Habeebti,ta shigo.
Tirus ta tsaya dan ganin Mama da Haroun din da aka ce ma ta su na asibiti zube a falo,daga d'a har uwa kuka su ke.
Da sauri ta k'arasa ta na salati,ta na fad'in me zan gani ni Salma" Mama ta fara ruk'owa ta na kok'aron goge hawayen da su ke zuwa daga idanun ta, ita kan ta Salma kukan ta sa dan ganin Haroun na kuka ta san ba k'aramin abu ke sa shi kuka ba,bare kuma ganin hawayen mahaifiyar su ba karamin tashin hankalin ba be a gare su ba.........
.Tirus ta tsaya dan ganin Mama da Haroun din da aka ce ma ta su na asibiti zube a falo,daga d'a har uwa kuka su ke.
Da sauri ta k'arasa ta na salati,ta na fad'in me zan gani ni Salma" Mama ta fara ruk'owa ta na kok'aron goge hawayen da su ke zuwa daga idanun ta, ita kan ta Salma kukan ta sa dan ganin Haroun na kuka ta san ba k'aramin abu ke sa shi kuka ba,bare kuma ganin hawayen mahaifiyar su ba karamin tashin hankalin ba be a gare su ba.........
Sai da su ka ci kukan su ka koshi sannan Hajiya ta iya fad'awa Anty Salma halin da ake ciki. Anty Salma ta yi tambayar duniyanan akan Haroun ya fad'a ma ta gaskiya alamarin,amma y ace sam ba zai iya tuna komai ba. Anty Salma ta ce wannan ba Magana ba ne,in har kuwa haka ne ya sa kan sa a matsalar da babu mai fidda shi sai Allah,danko ita ba za ta iya shaidan sa ba,danmaye ai komai shi ka iya aikatawa.
Ranar dai kowa haka ya wuni ya kwana ba dadi kamar gidan
mutuwa. Huda kuwa sam kin gasgata alamarin ta yi,ita a lalle sharri aka
yiwa Haroun,har ta kai ta kawo sai da Ummi ta buge ta jin ta na so ta
tada ma ta da husuma,kwana ta yi ta na kuka.
Daga Ayub har Dawud babu wanda ya runtsa bare kuma
Hajiya da Mama da uwa uba Haroun. Haka kuma haka wayar Habeebti da ke
d'akin ta,kwana ya yi ya na kada kararrawan shigowar wayar Alamin,amma
ina ko ta kan sa ba a yi ba,har wayar ta gaji charji ya kare.
Washagari aka d'auko Yakumbo ba tare da an fad'a mata abun da ya faru ba,sai zuwa ta yi ta tadda Aliya kwance. Nan ta sa musu buri wai an cuce ta an d'auko marainiyar Allah an bata ma ta rayuwa,Mairo ta cuce ta,da ta sani Karami ta bawa ruk'on Habeebti. Da kyar da mak'yark'yata aka samu aka shawo kanta. Dama ga gigin tsufa. Ai kuwa nan gaban Habeebti ta ke kwana ta wuni,a na ta duk wanda ya yiwa Habeebti wannan cin zarafi ka iya dawowa ya karasa ta har lahira. Haka ma Dawud,idan ba aiki ne ya tsare shi ba ya na wajan Hajiya da Yakumbu da ke jinyar ta.

Gidan Alhaji kuwa zaman lafiya ne ya k'are. Alhaji kullum cikin fada yake na ba gyara ba dalili,ga kuma wani sabon gaba da Hajiya da Mama su ka kulla,kullum ana cikin gayawa juna magana. Ga shi daga Haroun har Ayub an hana su fita ko da kuwa kofar gida ne,sai Habeebti ta farfad'o. Da wannan kuncin dukkannin su su ke fama. Haroun Kullum da Habeebti yake kwana ya na wuni cikin ran sa,kuma har ga Allah ya na san zuwa ya duba ta,amma ina ko da yayiwa Mama zancen sai rufe shi da fada da ta yi, ya rufaa ma ta asiri dan Allah.
Kwanan Habeebti uku kwance tamkar gawa,a cikin na hud'u ne Dawud
da ke zaune da Hajiya da Yakumbu,ya zuba matai do yayinda su Hajiya suna
can suna dan hirarrakin su. Me zai faru….sai ganin hannun Habeebti yayi
ya na motsawa. Da fari yayi zatan gizo ta ke masa dan kuwa hakan ta ke
ma sa lately,dan haka sai basar kawai.
Can ya ga ta kara,ai kuwa da sauri ya ta shi ya na fad'in ‘’ Hajiya motsi ta ke,motsi ta ke wallah’’ lokaci guda su ka yi kan ta,yayin da Dawud ya yi waje da dan gudun sa,ya na surutai kamar wanda ya zare.
Kuka su ke suna hamdala ganin manyan idanun Habeebti bud'e,yayin da ta ke kare mu su kallo kamar a sannan ta fara ganin su. Dawud ne ya shigo tare da Dactor d'in da ya azallazalo biye da su kuma wata Nurse ce d'auke da wani dan tire.

Habebti dai ta na kwance sai idanu,Hajiya da Yakumbu na
ta kiran sunan ta suna jera mata sannu,amma ina idan Habeebti ta tanka
dutse ma ya tanka. Sai da ya fara cire roban hancin ta jin numfashin ta
ya dan daidai ta kafin ty fara duba sauran lafiyan cikin ta.....
.Sai da ya gama duba ta ya ce "Alhamdulillah ta na samin sauki,thou har yanzu ta na cikin shock ne,amma nan da dan loakaci kadan bakin ta zai bude inshaAllah’’ ya na magana ne ya na kokarin sokawa Habebtin allurer jijiya a hannanun ta na dama. Har Doctor ya karaci budurin sa ya fice Habeebti ba ta tank ba.
Kafin ka ce me tuni Hajiya ta shedawa Alhaji cewa
Habeebti ta ta shi. Ba a jima ba sai gashi ya zo tare da danuwan sa
Alhaji Hamisu,wanda zuwan su ya yi daidai da zuwan k'anin baban Habeebti
wato Alhaji Umar. haka ma su Mama, Ummi da su Akib,Ayu,Anty Salma
Halima,Aysha,Maryam,Bilkusu gidan dai gaba d'aya idan aka d'auke Haroun
da ke can cikin zulumi da fargaban abun da zai je ya dawo,hatta Huda da
ba ta tab'a zuwa ta duba ta ba sai ga ta ta biyo su dan jin Habeebti ta
farka,dan ta na mai tabbacin cewa gaskiya dai a yau za ta yi halin ta,za
ta fad'i wanda ya ma ta fyade wanda ta san ba zai taba zama Haroun ba.
Sabon d'akin da aka kai Habeebti kasancewar ta farfad'o
ba karamin girma gare shi ba,dan haka su ka cika shi tab jama’a da ba su
san abun da ke wakana ba sai fadi su ke ‘’umm wannan yarinyar yar dangi
ce’’ ‘’yarainyar nan ba dai gata ba’’ ‘’kai yarinyar nan akwai dangi’’.
Duk wannan dandazo da aka yi kan Habeebti duk da kuwa Daoctor ya ce a bar ta ta huta,ba ta tanka mu su ba,sai ma runtse idanun ta da ta yi tamkar mai bacci. Su ma d'in tunanin su baccin ta ke,dan hirarrar su su ke sama sama. Bini bini wayar Ayub ke k'ara,amma sai ya duba ya kashe. Har sai da Yakumbo ta tanka cikin zolaya ta ke fad'in ‘’ka dauka ka ce ka na tare da ta karfen mana’’ murmushi mai kama da yak'e ya ma ta dan kuwa shi Haroun ne ke kiran sa,ko me yake so ya ce ma sa oho. Ganin hawaye na gangarowa daga idanun Habeebti ya sa hankalin kowa ya yi kan ta hankali tashe,dan tun tanayi ciki ciki har ta fara kukan sosai tana kok'arin tashi yayinda Hajiya ta ruke hannayen ta na fadin "yi hakuri Aliya….yi hakuri" Dawud da Ayub ne su ka fita a tare dan kiran Doctor.
.Duk wannan dandazo da aka yi kan Habeebti duk da kuwa Daoctor ya ce a bar ta ta huta,ba ta tanka mu su ba,sai ma runtse idanun ta da ta yi tamkar mai bacci. Su ma d'in tunanin su baccin ta ke,dan hirarrar su su ke sama sama. Bini bini wayar Ayub ke k'ara,amma sai ya duba ya kashe. Har sai da Yakumbo ta tanka cikin zolaya ta ke fad'in ‘’ka dauka ka ce ka na tare da ta karfen mana’’ murmushi mai kama da yak'e ya ma ta dan kuwa shi Haroun ne ke kiran sa,ko me yake so ya ce ma sa oho. Ganin hawaye na gangarowa daga idanun Habeebti ya sa hankalin kowa ya yi kan ta hankali tashe,dan tun tanayi ciki ciki har ta fara kukan sosai tana kok'arin tashi yayinda Hajiya ta ruke hannayen ta na fadin "yi hakuri Aliya….yi hakuri" Dawud da Ayub ne su ka fita a tare dan kiran Doctor.
Ba komai ne ya k'ara d'aga mu su hankali ba face jin sunan Haroun da ta ke ta nanatawa cikin kukan na ta,cikin kuka ta ke fad'in ‘’Haroun ka taimake ni….Haroun kar ka raba ni da mutunci na….Haroun menene haka…..Haroun ka ji tsoran Allah..Haroun….Haroun…….’’ Gaba daya d'akin idan aka d'auke mazan da ke ciki kuka su ke…kowa da abunda yake yiwa kuka. Mama halin da dan ta ya sa ta shi ya sa ta ke kuka, Ummi,Halima,Aysha da Maryam da Anty Salma kuwa daga Haroun din har halin da Habeebti ke ciki ya sa su zubda hawaye. Huda kuwa kukan ana shirin raba ta da masoyin ta ta ke,duk da kuwa be taba furta ma ta Kalmar soyayya ba. Ba a maganar Mama da Yakumbo da ta ci danmara,ta na kuka ta na wallahi sai na d'aure Haroun,wallahi sai an bi hakkin marainiyar Allah.
Doctor na shigowa be ko b'ata lokaci ba ya yiwa Habeebti allurer barci,nan aka samu ta yi bacci. D
'akin in ban da kuka babu abun da ke ta shi. Alhaji Hamisu
wanda su ke kira da Abba ne ya dubi Yakumbo kana ya ce Yakumbo ban san
da wani ido za mu kalle ki ba,amma ina so yanzu ki biyo mu mu tafi gida.
Ai kuwa Yakumbo ta cake,ai ko sama da kasa za ta had'e ba in da za ta
sai an damk'a ma ta Haroun a hannun ta. Alhaji ya fice ya na jin Alhaji
Hamisu na ba ta hakuri na da ta bari a je gida,kar jamaa su ji mutunci
da daraja ya zube….’’Toh kai dama ina darajar ta ke?…’’fadin yakumbo
Kenan ta na mai duban Mama da ta kasa fadin komai sai kuka….
Yakumbo ta kara da ‘’ai batun wani daraja ya kare tun da ba a ji kunyar cin zarafin marainiya ba ni kuma bazan ji kunyar daukan fansa ba……
Yakumbo ta kara da ‘’ai batun wani daraja ya kare tun da ba a ji kunyar cin zarafin marainiya ba ni kuma bazan ji kunyar daukan fansa ba……
"
Da kyar su Dawud su ka lallaba da taimakon Alhaji
Umar aka samu Yakumbo ta yarda za ta bi su gida a yi ta can,dan sun san
Yakumbo tun ta na da jinni a jika irin jarababban tsofaffin nan ne,bare
yanzu da ta tsufa. Gaba d'aya aka dunguma zuwa gida. hajiya kadai aka
bari gun jinyar Habeebti.
Alhaji na fita shi ma gidan ya wuce. Farfajiyar gidan
ya tadda Haroun zaune yayi jigum kamar wanda aka aikowa sakon
mutuwa,sanye yake da gajeran wando da ya dan wuce ma sa gwiwa kalar
khaki,sai kuma bakar riga mara hannu. Ganin shigowar Alhaji a fusace ya
san zaman lafiya dai kam ya kare a yau. Da sauri ya mi ke tsaye ganin
Alhaji ya yo kan sa, ya na karasawa kusa da shi jikake tas!….tas!..ya
wanke shi da mari kwarara har uku ya na fadin mutumin banza mutumin
hofi…….hakan yayi daidai da isowar su Yakumbo da tun kan Dawud ya gama
parking ta leko da kanna ta ta window ta na fad'in "wannan ya ma sa
kadan Alhaji,bari na fito,wallahi sai ya yi kwanan chaji ofis……."ganin
kowa ya fito,Mama wacce idanun ta ya yi jajur,Ummi wacce it ace ta ke
tallafe da hannun Mama ita da Anty Salma dan kiris ya rage ta yanke jiki
ta fad'i. Halima,Aysha,Maryam,Akib,Ayub ….su Alhaji duka dai hatta
maigadi be fasa lekowa da ga can gefe ba.
Alhaji ya fizgo hannun Haroun da ya kasa d'aga ido ya
kalli kowa,sai da ya je gaban Yakumbo ya tura ma ta shi a wulakance,kan
ka ce me sai gashi a k'asa dan kuwa kafafun sa ba za su iya d'aukan sa
ba…nan da nan Huda ta yi kasa da sauri sai gata tsugunne gaban sa ta na
kuka…yayinda Halima,Maryam da Aysha tare da Bilkisu rungume juna su ka
yi suna kuka..Mama ta kauda kai gefe tamkar ba ta wajan….ba tare da ya
damu da halin da su ke ciki ba Alhaji ya ce da Yakumbo’’gashi nan
Yakumbo,ki ma sa duk abun da ran ki ya so kafin police d'in da na kira
su zo su tafi dashi…….’’
0 comments:
Post a Comment