Tafiya ta ke yi mai cike da nutsuwa, cikin jerin likitoci
da malaman lafiya, yadda ta ke tafiya a jerin y'an sahun gaba shine zai
tabbatar maka da ita din ma babba ce, hakazalika duk inda ta gifta zaka
ga mutane suna gaisheta manyansu da yaransu.
Matashiya ce wanda shekarunta ba za su gaza talatin da
biyar (35) ba aduniya, ba fara ba ce sol haka kuma baza a kirata bak'a
ba, ta na da idanu madai-daita had'e da dogon hanci wanda ya dai-daita
da kyakykyawan fuskarta, karamin bakinta shi ya dad'a kawata kyawun
fuskarta, tanada yalwataccen gashin gira da na ido ga kuma kwantattacen
saje wanda shine zai nuna maka ta na da yawan gashi, baza kuma a kirata
doguwa ba haka baza kuma a kirata gajera ba, sannan kuma ita ba siririya
ba ce sai dai za'a iya saka ta a cikin jerin matan nan da aka fi sa ni
da y'an duma-duma, komi dai na jikinta abin burgewa ne.
Sanye ta ke da atamfa samfurin holand mai kalan fari da
kwalliyan blue, ta yane kanta da karamin gyale mai kalan blue, sannan
takalmin da ke kafanta shi d'inma kalan blue ne mara tudu, sanye ta ke
da farin gilashi mai kara karfin ido wanda ya amshi fuskarta.
Kai tsaye d'akin mata suka shiga wanda sukaci gaba da duba marasa lafiya cikin gwanan cewa da aikin.
Yadda ta ke mu'amala da marasa lafiya cikin wasa da dariya
sukuma suna bata ansan duk abinda ta tambayesu ba tare da wata matsala
ba abun ya dinga ba manyan likitoci fararen fatan da suke tare mamaki,
kuma suka k'ara yaba kwazonta.
Ba wai sabon abu bane a wurin su, sai dai ganin cewan
mafiya yawan likitoci a nahiyar africa basu fiye janyo marasa lafiyansu a
jikinsu ba, hasalima sai kaga wasu sun d'au girman kai sun sawa kansu
wannan yasa suka dinga ya ba mata.
Mamakinsu bai k'aru ba sai lokacin da suka kammala duba
marasa lafiya, akan hanyarsu ta koma wa, inda mutane suketa gaisheta
tamkar wata tauraruwa, wani daga cikin manyan likitocin ne wanda shi din
ma farin fata ne ya kasa hakuri ya ce cikin harshen turanci
"Dr Farida tabbas kin cancanci a yaba miki, sai dai kuma fa
ya kamata fa nima kibani wannan sirrin" ya k'arashe cikin sigar
tsokana, sauran likitocin ma suka mata caa kowa da abinda yake fad'i ita
kuwa badda murmushi ba abinda ta ke yi.
Isowarshi wurin shi yayi sanadiyar d'aukewa murmushin da ke
kan fuskanta, kallo d'aya ta mai gami da sunkuyar da kanta, gabanta ne
yaci gaba da fad'uwa had'e da shiga yanayin da ta saba tsintar kanta a
duk lokacin da ta yi tozali da shi.
Hannu ya ba sauran likitocin suka gaggaisa ko kallon inda
ta ke baiyi ba, bayan kammala gaishe-gaishe a tsakaninsu da kuma ta6a
hira akan abin da ya shafi aikinsu ne d'aya da ga cikin likitocin ya ce
cikin sigar wasa " Dr Umar kai ma ya kamata ka rok'a mana Dr Farida ta
ba mu wannan sirrin da ta ke anfani da shi wanda ya sa marasa lafiya
suke kaunarta haka" ya fad'a cikin harcen nasara.
"Akwai wani mara lafiya da zan duba sai mun had'u a wurin
review meeting" ya fad'a cikin basar da waccan maganar ba tare da ya
basu ansa ba, bai jira me za su ce ba ya bar wurin cikin tafiyarsa ta
kasaita.
Cikin wani irin yanayi tabar wurin baza ta iya cigaba da
aikin ba saboda yadda ta ke jin zuciyarta, kai tsaye inda suka saba
ajiye motocinsu ta nufa, don cigaba da zamanta a wurin zai iya haifar
mata da bugawan zuciya.
Ta na shiga motarta ta fashe da wani irin kuka mai ta6a
zuciyar duk wani mai sauraro, ita to mai zata yi wanda zai sa Dr Umar ya
daina nuna mata wannan tsanar, sai da ta yi kuka kuka mai isarta kafin
daga bisani ta yi ma motarta key ba dan kukan ya tsaya ba, haka tacigaba
da kuka had'e da figar motar kai tsaye wani unguwa ta shige gamin da
yin hon a kofar wani madai-daicin gida mai kyau, ba da jimawa ba wani
dattijo yazo ya wangale kofar, wanda da alama shi ne maigadin wannan
gidan, ba tare da ta ansa gaisuwar da ya mata ba, ta samawa motarta
wurin parking.
****************
Dattijuwar mace ce wacce a shekaru ba zata gaza shekaru
arba'in da biyar (45) ba a duniya, ta na da d'an kiba sanna bak'a ce mai
cikakken kamala.
Zaune ta ke akan kujera ta zaman mutum uku, labarai ta ke kallo a gidan talabijin din aljazira.
Yanayin yadda ta shigo falon shi ya janyo hankali wannan
dattijuwar cikin tashin hankali ta kalle ta had'e da bud'e hannayenta
duka biyu alamar tazo gareta, ba tare da 6ata lokaci ba Farida ta
k'araso da gudu ta fad'a jikin dattijuwar, tunda dama ta na bukatar
wanda zai rarrasheta.
Rungumota a jikinta ta yi ta kuma cigaba da shafa bayanta
ba tare da ta yi magana ba haka nan kuma ba ta hanata kukan ba, idan da
sabo ta saba da irin wannan yanayin da d'iyarta ta saba shugo mata a duk
lokacin da suka had'u da Dr Umar dan haka yau d'in ma ba ta bukatar
tambaya tasan shi d'in ne, sai da ta bari ta yi kukan sosai sannan ta
goge mata hawaye had'e da ce wa.
"nasan ko baki fad'a min ba nasan Dr Umar ne ko" sake janyo
ta jikinta ta yi ta cigaba da shafa bayanta alamar rarrashi, kafin daga
bisani ta cigaba da cewa
"Anya Farida rayuwa zata yuwu a haka kuwa, bakya tunanin
wani ciwo ya kama ki, ni na fad'a miki ki kwantar da hankalinki ki kuma
bi shawarar da nake baki nasan zakiji dad'inshi amma kinki yarda ya
kikeso na yi ne my dota?"
Sai a sannan Farida ta tsagaita da kukan, cikin dashewar
murya ta ce " Aunty bawai nak'i bin shawararki bane amma ni nasan cewa
Dr Umar ya tsane ni ko kallona ba ya son yi, Aunty ki fad'a min ya
zanyi, mai zanyiwa Dr ya daina nuna min tsana afili ya na hantarata,
Aunty why mai yasa bazai gane k'addara ba?" Kukan ne ya dad'a kwace mata
sosai.
Yatsa Aunty ta samata a baki alamar ta yi shuru, sannan ta
kamo hannunta duka biyu ta had'a da nata sannan ta ce cikin tausayawa "
banaso ki dinga fad'an wannan kalamain dotana ni dai abin da na keso da
ke shine ki kwantar da hankalinki sannan kisawa ranki Dr Umar bai
tsaneki ba ya ma fi kowa sonki"
Cire hannunta ta yi daga na Aunty had'e da tashi ba tare da
ta yi magana ba har sai da taje bakin kofar da zai sada ta da d'akinta
kafin ta tsaya ba tare da ta juya ba ta ce
" Aunty karki manta babu abinda Dr Umar bai sani ba a game
da ni, wannan dalilin ne yasa ya tsane ni na kuma tabbatar da ba zai
ta6a sona ba, tabbas na cuci kaina"
0 comments:
Post a Comment