Jini na gani yana fita ta baki da hancin Mama ta na gogewa a
hankali, fad'awa na yi kan kafarta ina kuka, rik'emin hannu ta yi
sannan ta ce "kinsan dai bana son kukan nan, magana nakiraki muyi fa"
Cikin kuka na ce "Mama nasan kina jin jiki kuma nasan ni ce sila, Mama wallahi banyi ba a rayuwa, banyi ba mamaaaaa"
Na k'arashe cikin kuka, gogemin hawaye Mama ta yi kafin
kuma ta ce " ba kece sila ba Farida abubuwa da dama sun faru dani wanda
sunyiwa zuciyata girma, baki da laifi mune masu lefi, munyi *SAKACI*
wurin baku tarbiya"
"Mahaifinku bai so na haifeku ba, amma na dage sai na haifeku, ashe bazan iya baku tarbiyan da ya dace ba, ku yafemin yarana"
"Don Allah Mama kidaina fad'an haka, ba laifinki ba ne,
tabbas nauyi ne ya miki yawa Mama, Allah yafi kowa sanin nauyi ya miki
yawa"
"Wani tsarin iyali kukayi, inaso ki fad'amin gaskiya" Mama ta tambaye ni.
na ce "wallahi ni ban ta6a zuwa asibiti anyimin komai ba"
Mama ta ce "bai ta6a baki magani ko wani abun ba?" Na ce "nidai nasan yana yimin allura duk bayan watanni kad'an"
Girgiza kai Mama ta yi cikin takaici ta ce "Hassan ya cuceki Farida, amma ba komi kanshi yayiwa"
Ta d'anyi shuru sannan ta ce "nasan za ki fuskanci tsanani
arayuwarki zuwa gaba, gashi bazan kasance dake ba balle na rungumeki na
rarrasheki, amma zan baki shawara d'iyata, duk halin da kika tsinci
kanki ki koma ga Allah shi ne gatanki"
Tari ta yi wanda ya fito da Jini, ni nasa hannu ina goge ma ta had'e da cewa
"Mamana ba za ki tafi ki barni ba, wallahi duniya zata
yimin zafi idan na rasaki, babu Ya Hamid, babu Ya Abdallah sannan kema
kidinga irin wannan maganar Mama"
Shafa min kai Mama ta yi sannan ta ce "ki rik'e Ummi tamkar
uwa nasan itama zata rik'eki tamkar ita ta haifeki, sannan ki rik'e
Umar ya zama abokinki kuma abokin shawar ki, Farida inaso ki rik'e Umar
domin shi d'in masoyinmu ne, karki sake yarda da duk wani rud'in d'a
namiji kuma karki damu kanki akan aure mijinki zaizo gareki lokacin da
Allah ya tsara zai soki a yadda kike kinji"
"Sannan ki yimin alkhawari bazaki sa ke aikata sa6o irin wannan ba" na ce na yi alkhawari Mama"
Tace "toh jeki ki turomin Umar Allah ya miki albarka, Allah ya zama gatanki d'iyata"
Har na fita Mamana ta na anbaton kalmar albarka a gareni, ta kuma kasa d'auke idonta akaina.
Na tura ma ta Ya Umar bansan mai ta ce mishi ba, sannan su Baba da Ummi ma duk sun shiga.
Washegari da safe komi ya auku, wannan ranar ita na kira da
bak'ar ranar, wannan ranar itace sanadin d'aukewar duk wani jin dadina,
domin a ranar Allah ya amshi ran Mama.
Bazan iya kwatanta muku halin da na shiga ba, sai dai komi
ya tsayamin na wasu lokuta, sannan na jima ina ciwo, Baba ya aikawa
dangin mahaifiyata da dangin shi, duk kuwa sunzo, kakata ta yi kuka
sosai, haka ma Innayo.
Bayan anyi kwana bakwai da rasuwar lokacin da kakata tazo
tafiya taso ta tafi dani amma Ummi ta rok'eta akan ta barmata ni har
zuwa lokacin da zan k'are makaranta ta, ba yadda ta iya domin tasan irin
ruk'on da tayiwa Mama.
Baba ma yaso tafiya dani Bauchi amma Ummi ta ce yabari yayi
aure tukunnan don barina ni kad'ai a gida ganganci ne duba da yadda
nasa damuwa a raina, shima haka ya hakura ya barni amma duk ranar juma'a
sai yazo ganina.
Lokacin da Mama ta cika wata d'aya da rasuwa lokacin kuma
na samu saukin jiki saura na zuciya, Ummi ta umarceni da na fara zuwa
school da islamiyya, a wannan lokacin rayuwa ta yi min zafi ban isa fita
ba.
ko school naje ko Islamiya andinga cewa ga wacce bak'in
cikinta ya kashe uwarta rayuwa ta yimin zafi har takai bana fita, sai
kuma abun yaso ya ta6a k'wak'walwata na fara wasu irin abubuwa, wanda
duk tsangwamar da ake yimin ce ta janyo.
Ya Umar da Ummi ne ke rarrashi na amma sai suka ga abin yayi yawa, sai kuma suka fara shiga damuwa kada wani abu ya sameni.
Daga k'arshe Ummi ta samu Baba wata juma'a da yazo dubani
ta sanar dashi abinda ke faruwa, ya shiga damuwa mai yawa, yace wa Ummi
zai d'aukeni mu koma bauchi, Ummi ta ce amma a gaskiya dole ya nemi mata
ko don saboda ni, yace insha Allahu zai naima.
Haka ya d'aukeni muka koma Bauchi, bayan y'an watanni abokinshi ya had'ashi da Aunty.
Aunty y'ar kafin madaki ne da ke garin Bauchi, a bazawara
Baba ya aureta domin ta na da yara uku da suka haifa da tsohon mijinta
wanda suka rabu.
Ita ce ta cigaba da rik'ona tamkar ita ta haifeni.
*******
Bayan Ya Umar ya kammala bautar kasarsa nan ya samu aiki a SPECIALIST HOSPITAL da ke Bauchi kafin kuma ta koma ATBUTH.
A gidan mu ya fara zama, ba k'aramin dadi naji lokacin da
Ya Umar ya dawo gidanmu ba, domin yana d'ebemin kewa sosai, sannan ya
tsaya min a harkar karatuna sosai, domin daga farko naki karatun sam na
daina mayar da hankalina, bani da lokaci sai na kuka ko tunani, gani
nake bani da wani sauran anfani a rayuwata.
Ya Umar shi ya tsaya, tsayin daka wani lokaci har wayan
wuta yake tsoratani da shi, har dai naga Ya Umar fa ba gajiya zaiyi ba,
anan nasawa raina gara na yi mai biyayya, amma bawai don ina so ba.
Anan fa na dage sosai, ban zuba mai k'asa a ido ba, na dage
da karatun domin nasan ba wani abun da ya saura na rayuwarta a duniya
badda na dage da bautawa Allah sai kuma neman ilimi.
Duk wani abun bukata ba sai na nema ba, Baba da Ya Umar suna iyakacin k'ok'arinsu.
Ina SS2 Ya Umar yaje da kanshi yayi min register na WAEC da
NECO, karatu sosai mu keyi da Ya Umar, bani da wani lokacin hutawa,
cikin ikon Allah kuwa muka zana exams d'in, ba laifi result d'in NECO
yayi kyau fiye da na WAEC.
Lokacin da Ya Umar ya nema min form d'in JAM ya kuma ce wai
medicine zan karanta anan fa rigima ta, tashi domin ni na ce ba zanyi
medicine ba, shikuma yace ba gudu ba ja da baya.
0 comments:
Post a Comment