Har k'aran shi nakai gun Ummi lokacin da tazo Bauchi
dubani, Ummi ta kirashi ta yi mi shi magana amma sam ya kafe ya kuma
rantse a gabana, sannan ya kuma ce.
"kar ki yi tunanin idan baki samu wannan shekarar ba, zan
hakura, a'a wallahi ko da zai zamo duk shekara sai kin zana jarabawar
nan ne ba zan gaji da kashe kud'ina ba"
Yana kuma gama fad'an haka yayi ficewar shi.
Ummi ce ta ce min "Farida kinfi kowa sanin halin yayanki,
kin kuma sanshi da kafiya idan zan baki shawara to fa kiyiwa yayanki
biyayya, bana so kema ki zamto mai kafiya kamar shi"
Sai a sannan Aunty ta ce "nifa banga dalilinki na k'in
amincewa ba, Umar fa gata ya ke miki, nan gaba za kiyi alfahari da
hakan, sannan kuma bakyaso ki zamto mai taimako ga addininki?"
"Farida"
ta kira sunana, d'ago kaina na yi na kalleta ba ta re da na ansa ba, cikin kwantar da murya ta ce.
"Inaso ki zamto mai kishin mata y'an uwanki, da'ace yau namiji ke duba mata ai gara muma asa mu mata, ace matan ma na musulmai"
"Shin ba za ki yi koyi da matan k'warai masu kishin
addininsu ba, Farida wannan karatu da za kiyi jahadi fa za kiyi, domin
Allah kad'ai yasan mutane nawa za su anfanu da karatunki"
Haka suka yita nuna min anfanin karatun, har naji zan iya, kuma na sawa raina zan jure duk wata wahalar da ke cikinshi.
Cikin ikon Allah na samu abinda ake buk'ata, na kuma samu
gurbin karatu a Abubakar Tafawa Balewa university (ATBU), wanda nake
karantar gynecology.
Tabbas karatu akwai wahala ba kuma k'aramar wahala nasha
ba, a haka ma Dr (Ya Umar) sosai yake taimakamin, domin wani lokacin
idan bani da lectures nakan bishi asibiti ina ganin yadda su ke gudanar
da aikinsu, kuma ina fahimta sosai.
Sannan duk abinda ban gana ba, dangane da karatuna wurinshi na ke zuwa ya k'aramim haske.
Ban sha wahala ta fannin zirga-zirgar makaranta ba, domin
Dr shi ya ke kaini ko'ina ya kuma dawo dani idan har ba shi da aiki,
domin zuwa wannan lokacin ya siya motarshi ta farko k'aramar Golf, idan
kuwa aiki yayi mai yawa, sai ya tura a d'auko ni.
Kasancewar a rayuwata ni ba mutun bace mai tara k'awaye
hasalima bani da k'awaye domin haka har na gama zaman Jos sai dai wanda
mukayi wasan k'asa da su.
Ko da na dawo Bauchi ma hakance, abinda ya ke gaba shi na
keyi, sai dai lokacin da na shiga university, na had'u da Mansura,
Mansura itace k'awata ta farko, daga kanta na fara kawance saboda na ya
bawa hankalinta da tarbiyarta.
Cikin k'ankanin lokaci muka shak'u da Mansura, sai dai sam Dr ba ya son kawance na da ita.
Mansura har gidanmu ta na zuwa amma ni sam Dr yak'i naje gidansu, tabbas bana son 6acin ranshi, shi yasa nake bin umarninshi.
Mansura ita ce mace ta farko da na fara ba tarihin rayuwata saboda yardar da na yi da ita.
A wannan lokacin samari da dama sun fito dan neman
soyayyata amma duk wanda ya fito haka kawai sai ya d'auke kafarshi ba ta
re da nasan dalili ba, anyi hakan yafi kashi hud'u, a hankali abin
yafara damuna har ya fara ta6a karatuna.
Daga k'arshe na yakice abin a raina na fuskanci karatun da ke gabana.
*******
Ina 300lv Alhajin su Dr ya umarce shi da yaje ya nemi
d'iyar abokinshi Alhaji sama'ila mai suna Mariya, suma y'an asalin garin
Bauchi ne.
Jininmu bai had'u da Aunty Mariya ba, sam ba ta k'aunata, sannan na rasa dalilin da yasa ta ke nuna min hakan.
So da yawa idan Dr zai je hira wurinta ta re muke zuwa da
shi, sai dai da k'yar ta ke ansa gaisuwata tun Dr bai fahimci hakan ba,
har yazo ya fahimta.
Ya nuna ma ta 6acin ranshi sosai, toh tun daga lokacin sai
ta daina nuna wannan halin a gabanshi, ni kam daga baya idan na fahimci
zai je wurinta sai na k'irk'iro da bacci koda kuwa ba naji.
Shima sai yayi zamanshi yak'i zuwa, haka ranar za ta yita
kiranshi awaya ta na tambayarshi dalilin k'in zuwan nashi, shi kuwa haka
zai sanar da ita dalilin fasa zuwan nashi, domin shi mutun ne mai
fad'an gaskiya, ko da kuwa kai ba zai maka dad'i ba.
Da farko idan ya fad'a ma ta sai ta d'au fushi dashi, shi
kuwa ko a jikinshi don so dayawa ma baya nuna ma ta yasan ta na yi, haka
zata ba kanta hakuri.
Domin na lura son da ta ke yimai yafi wanda ya ke ma ta,
lokuta da dama idan na rakashi hira wurinta duk hiran ita ta keyi, sai
dai ya bita da eh ko a'a, idan ya gaji ya ce mu tashi mu tafi, na lura
da hakan ba k'aramin 6ata ma ta rai ya ke ba.
Sannan duk abinda zai siya mata ta re yake siya mana sai dai kala ya ban-banta.
****
Wata rana bana mantawa ya ce na shirya muje jos domin kaiwa
Ummi kayan auranshi, bayan na shafe shekaru masu yawa ban sake waiwayen
garin ba, sam nak'i yarda, bana tunanin akwai kuma ranar da zan so
kafata ta k'ara takawa izuwa garin, garin da abubuwa da dama suka faru.
Dak'yar Dr yasa na bishi, amma koda muka isa halin da yaga na shiga yayi mugun d'aga mai hankali har sai da yace.
"Faridana da nasan bakya son zuwa Jos har haka, da ban takura miki ba, ki yafe min"
Ya fad'a yana had'a hannuwanshi alamar neman gafara.
Sosai na yi k'okarin danne duk abinda ya ke damuna, domin idan akwai abinda na tsana shi ne ganin tashin hankalin Dr.
Koda muka shiga gidansu ma, haka Ummi ta yita janyoni ajiki
ta na k'ok'arin mantar dani duk wata damuwa, sam bata barni na zauna
shuru ba.
Lokacin da na idar da sallah la'asar aka fara shugo da akwatuna, ina daga d'akin Ummi naji shugowan Dr.
Muryar Ummi naji ta na ce wa "Yayan Farida kamar akwati set
biyu na gani kuma kayan ciki kala ne kawai ya ban-bantasu, duka na
Mariya ne?"
Murmushi Dr yayi kafin kuma ya ce "a'a, set d'aya na Farida ne" cikin d'oki naji Ummi ta tareshi da cewa.
"Kace min mata biyu zaka h'ada yayan Farida"
Kafin ya kai ga magana wayar Alhajinshi ta shigo, alama yayiwa Ummi da ya na dawowa.
Ga mamakina sai naji Ummi ta d'au waya ta na kiran wata kawarta da ke Sudan akan ta na so tazo ta gyara ma ta d'iyarta.
Nidai ba naji abinda waccan ta ke fad'a na daiji Ummi ta na fad'a ma ta da zaran ta tabbatar da lokacin bikin zata sanar da ita.
Ranar farincikin da naga Ummi ta na yi abun sai da ya bani
mamaki, na kuma tabbatar Ummi mutum ce, tabbas bamu da abinda zamu
sakawa Ummi dashi sai addu'a
0 comments:
Post a Comment