Sai bayan Isha'i Dr ya shigo gidan, nikam ina d'aki wani kunyarsu yanzu nake ji, Ummi ce ta k'wallamin kira.
Ba dan inaso ba na fita dan kawai bani da yadda zanyi ne, hijab d'in da na yi sallah shi na mayar na je kiran Ummi.
"Ummi gani"
Na fad'a cikin wani sabon ladabi da na samawa kaina.
Cikin sakewar fuska Ummi ta ce Yayanki za ki kawowa abinci"
"toh " nace had'e da bin hanyar da zata sadani da madafin.
Bayan na ajiye abincin ne, na bud'e fridge domin d'auko ruwa, na tsinkayi muryar Ummi ta na ce wa
" ka sanar da Baban Farida ko?" ta ke tambayar Dr.
Sai naji Dr ya ce " me kenan Ummi"
"ji mun sha-shanci dai, toh ina kata6a ganin anbada aure ba
ta re da sanin Uba ba, toh wa kake tunanin zai aurama Faridan" cewar
Ummi.
"Ikon Allah, Ummi ko dai tsufan ne tun yanzu, waye ya fad'a
miki zan auri Farida" Dr ya fad'a yana ajiye wayar hannunshi a k'asa.
Ummi ta ce "kaci gidanku, d'azun nan kace min setin akwati d'aya na Farida ne ina"
Girgiza kai Dr yayi kafin kuma ya ce "Ummi bazan iya yiwa
Farida wani abu ba sai da dalili? Nifa na siya ma ta ne kawai a
matsayinta na k'anwata"
Cikin muryar damuwa naji Ummi na cewa "ai na yi zaton duk
da ita za'a had'a har naji dad'i, toh itama Allah ya fito ma ta da miji
nagari"
"Ameen" Dr ya ce, gami da fara cin abincinshi, ba wanda ya k'ara magana a cikinsu.
Tabbas hankalina ya tashi da jin ansar Dr, amma ni banga laifinshi ba.
Ba yadda zanyi domin na riga na cuci kaina ba kuma namijin da zai so auran mace fanko.
Shiyasa na gadawa kaina dauriya, na kuma yi k'okarin kwantarwa da kaina hankali, tunda nasan bani da wata mafita.
****
Anyi biki an watse, da shike Dr ba mai son hayaniya ba ne, wannan ne yasa walima kawai yayi bayan an gama d'aurin aure.
Fannin amarya itama walimar ta yi, ba yadda Dr baiyi dani
naje walimarta ba, nak'i zuwa domin bana so naje wurin da za'a
wulak'antani.
Ko da aka gama bikin ko lek'a gidan amarya banyi ba, ba
yadda Dr baiyi dani akan nazo na rakashi siyan baki ba ranar da aka kai
amarya ba nak'i, na mai k'aryan kaina na ciwo amma yadda naga
hankalinshi ya tashi sai da na yi da nasanin fad'a mai hakan.
Da k'yar ranar ya tafi, ga amaryar ta dameshi da kira wai an barta ita d'aya.
****
Tun Dr ya na min uzirin rashin zuwa gidanshi har ya daina
ranar ya ce saina fad'a mai dalilina nak'in zuwa gidanshi, na rasa mai
zance mai k'arshe dai nace mai
"ai idan muka saba da ita zan dinga zuwa sosai"
Murmushi yayi ya ce "Faridana a rashin zuwa gidan ne zaku
saba, inaso kisawa ranki gidana gidanki ne, karki yarda ko da zancen
wasa wani dalilin ya hanaki iko da abinki, kuma ba na jin dadi, raina
yana 6aci da rashin zuwanki"
"Yayana ranka ya daina 6aci, na maka alkwawarin zuwa gidan har sai kai da kanka ka koreni"
Na fad'a ina dariya, shima murmushin yake had'e da cewa wa ya isa ya kori Farida Umar daga gidansu"
Tun daga wannan lokacin na cigaba da zuwa gidan Dr, duk da
matarshi ba wai ta daina nuna min tsanar da ta ke yimin ba ne, nidai ina
zuwa ne domin Dr.
****
Akwai wata rana da bazan manta ba na je gidan Dr da yamma lokacin Dr bai jima da siyamin mota ba.
Lokacin da na shiga gidan na samu Aunty Farida da d'ansu na
fari wato Khalil ta na bashi Indomie, yaron da gudu yazo gareni
kasancewar ya saba dani, wurgashi sama na yi na cafe, shi kuwa sai
wangale baki yake yana dariya.
Aunty Mariya ce ta zo ta fisgeshi a hannu na gami da cewa
"zonan kar ashafa maka rashin zuciya da naci, kamar yadda mutun ya dawo, sai bin mazan wasu"
Ta karashe da fad'in "ke don Allah kibarmin mijina ba aurenki zaiyi ba, haba Allah dai ya rufa mana asiri da bin mazan wasu"
Wannan maganar da ta fad'a a kunnen Dr, 6acin ran da na
gani a idanunshi ba zai misaltu ba, a lokacin zuciyata ta karye wani
irin kuka na fashe da shi kafin kuma na yi hanyar fita.
Kamo hannuna Dr yayi gami da rungumeni, abinda bai ta6a yimun ba tunda na mallaki hankalina.
Kallonta yayi cikin 6acin rai ya ce " sa'arki d'aya ke mace
ce amma da kinyi kad'an ki zagi Farida, na miki uziri a yanzu amma
karki manta akanta zan iya rabuwa da ke"
Ya cigaba da magana cikin zafin rai.
Sannan abu na k'arshe ke da Farida taso aure na ke kinyi kad'an da ki shigo gidana, wawiya ke d'in ba tallarki aka kawomin ba"
Ya na gama fad'a yaja hannuna muka fita, haka yayita rarrashina ita kuwa a ranar tayi yaji.
Koda su Ummi sukaji labarin abinda ta yi ba wanda ya goyi bayanta, Ummi kam ma ta d'auki abin da zafi sosai.
Sai daga baya aka sasanta ta dawo d'akinta, ni kuwa na
d'auke kafata, lokacin da ta sake haihuwa ne ma naje wannan ma tare da
Ummi mukaje.
Haka rayuwata ta cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i.
*ABINDA YA FARA SHIGA TSAKANINA DA DR*
****
****
Bayan na kammala karatuna ina shirin zuwa bautar k'asa na
had'u da wani saurayi mai suna Adamu, tun bana saurarenshi har na fara
sauraranshi ba kuma wai don ina sonshi ba sai dai zuwa wannan lokacin
mahaifina yana yawan damuna da batun aure, nasan tabbas zamana a gida ya
na tuno mai da abubuwa da dama.
Wanda wani lokacin har ya ke zargin kanshi, wannan ne yasa har yanzu ya kasa samun cikakkiyar lafiya.
Dalilin hakan yasa na fara sauraran Adamu, har na ba shi daman zuwa gidanmu.
Sai dai akwai wasu abubuwa da Adamu ya kemin wanda ya ke sa
naji bazan iya aurenshi ba, shi mutun ne da ya ke ganin ta6a jikin mace
ba komai ba ne, ga maganganun batsa a bakinsa, sannan na lura yana da
son kallon mata wanda shi a ganinshi wata wayewa ce.
Sosai na ke nuna mai rashin dacewar hakan, sam bana yarda
ya ta6a ni, tabbas a wannan lokacin da inada wani saurayin na yi imani
zan iya rabuwa dashi.
0 comments:
Post a Comment