Ranar farko da Dr ya fara ganinshi ya zo hira, naga 6acin
rai, domin korata yayi gida sannan ya cewa Adamu kar ya sake ganin
kafarshi a kofar gidanmu.
Wannan bai isheshi ba har sai da ya biyoni gida ya dinga
sirfamin kwandon fad'a tamkar wacce ta aikata sa6o, nikam saboda haushi
ma ko kulashi banyi ba.
Kuma na k'udiri aniyan duk maitar shi bazan rabu da Adamu
ba domin banga dalilin da zai dinga shiga rayuwata haka ba, ina shi ga
matarshi harda yara biyu (khalil da Ammar) ga cikin na uku, wato ni ce
zan zauna haka.
Haka ya gama fad'an shi ya tafi, yana fita kuwa na kira Adamu mukasha hiran mu, na kuma ce mai ya cigaba da zuwa.
Koda Mansura tazo na fad'a ma ta halin da ake ciki k'ara zugani ta yi akan karna yarda, na kuma na d'auka.
Sam ban sanar da su Baba ba, domin nasan duk bayanshi zasu bi.
****
Wata rana da yamma Adam ya yi min waya gashinan akan hanya, murna fal cikin zuciyata.
Ba tare da 6ata lokaci ba na shiga toilet na yi wanka gami
da tsantsara kwalliya mai d'aukar hankali, har mamakin kaina na keji
domin ban ta6a yin irin wannan kwalliyar da sunan zuwa zance ba.
Ina kan gyara d'aurin d'an kwalina wayarshi ta shigo d'auka na yi, ya sanar dani gashi a waje.
Turare na fesa gami da yafa gyalena, na fita, yana jikin
motarshi, ya na jifa na da wani mayaudarin kallonshi, bazan iya jure
irin wannan kallon ba, kallo ne wanda ya ke tuno min da mutumin da nafi
tsana a rayuwata.
k'arasawa na yi, ya min umarni da na shiga motar na ce a'a a tsayen yafi, bai min musu ba.
Muna cikin hiran ne na ke mai zancen turo magabata, na lura
duk lokacin da na mai zancen ya turo sai ya bada uziri, aikuwa hakance
ta sa ke faruwa cikin rashin jin dad'i na ce mai
"Gaskiya Adamu ban gane maka ba, karmu yaudari kan mu idan abinnan ba zai yuwu ba karmu 6atawa kan mu lokaci"
Nan fa ya fara rarrashina ya na min dad'in baki "Farida ina
tsananin sonki, ki daina saka damuwa a ranki ni d'in nan naki ne, akwai
abubuwan da nake jira ne amma da zaran sun kammala zan turo magabata
na"
Na ce "maganar gaskiya Adamu na fara sarewa da lamarin nan nifa gani nake kamar abin nan bazai yuwu ba"
"Ba ki yarda dani bane Farida, zo kiji yadda zuciyata ta ke bugawa, wannan shi zai tabbatar miki da irin son da nake miki"
kamani yayi yana k'ok'arin rungumeni, banyi aune ba naji ya
na k'ok'arin had'a bakinshi da nawa, ina k'ok'arin k'wacewa amma karfi
namiji da mace ba d'aya ba.
Wani irin fizga naji anyi min har sai da hannu na ya ansa, ban ankara ba naji anyi jifa dani a k'asa.
Shak'ar wuyanshi yayi, wanda da k'yar Adamu yake fitar da
nunfashi, ihu nake ina wayyo zai kasheshi, Baba ne ya fito a sukwane ya
rik'e hannun Dr yana
"Don Allah Umar ka sake shi kar kayi kisa, rok'onka na ke" tun kud'eshi yayi har sai da ya bigi motarshi.
A sukwane Adam yaja motarshi ya bar gidan mu, Baba ne ya
kama hannun Dr idanunshi sun kad'a sunyi jazir, Aunty ta ruk'o hannuna
muka shiga falo.
Baba ne ke tambayar abinda ya faru, Dr bai iya cewa komai ba, ni ce na fashe da kuka.
Dr ya ce "gwara ma ki yi shuru domin na sake ganin kafar yaron nan a gidan nan sai na karyashi kafin na mik'ashi ga hukuma"
Ga mamakinsu tashi tsaye na yi gami da ce wa "idan ka isa
shegiya nake, wai kai wani irin mugu ne da kanka kawai kasani, toh wlh
baka isa ba"
Maganar gaskiya naji zafin abinda Adamu yamin kuma nasa
araina dole na hukuntashi, amma kuma lokaci yayi da zan nunawa Dr na
gaji da mulkin mallaka.
Baba ne ya daka min tsawa, cikin 6acin rai Dr ya ce "Baba
kyaleta ai idan ba ta yi hakan ba baza ta nunamin ita ishashshiya ce ba,
toh ki gama duk abinda za kiyi amma wannan yaron kun rabu kenan"
Cike da rashin kunya na ce " ka ma isa, ka na wani abu tamkar ubana, toh wallahi ka ta6a shi sai kayi dana sani"
Tasowa yayi ciki karaji da niyan dukana, nima na tashi da hanzari gami da d'aukan kujera na ce "kana ta6ani ina sauke maka aka"
K'arar fad'uwar Baba ne da salatin Aunty ya ankarar damu,
lokaci guda mukayi kanshi, Dr shi ya kama Baba ya sashi a mota bayan ya
mai temakon gaggawa ya farfad'o.
A motarshi yasa Baba ni kuwa motata da Dr ya siyamin na shiga, na bisu a baya,domin ba zanyi gangancin shiga motarshi ba.
Washegari Baba yayiwa Ummi waya domin dukanmu mun kafe akan ra'ayin mu.
0 comments:
Post a Comment