A washegari Ummi tazo Bauch, ta ce ita bata ga dalilin k'in amincewar Dr ba, zanyi ta zama ne ba aure ai bai isa ba.
Shi kuwa ya ce "Ummi ni bazan hana Farida yin aure ba, amma badai wannan yaron ba"
Ni kuma nace shi nake so, Dr ya ce tofa sai dai na mutu banyi aure ba amma nasa a raina ba zan ta6a auran wannan yaron ba.
Cike da 6acin rai na ce " me yasa kake son kanka da yawa, wannan zalunci ne da mugunta" cike da 6acin rai Dr ya kalle ni ya ce
"Yau ni kike jifa da mugayen kalamai Farida"
Tsawan da Ummi ta yi mana yasa mukayi shuru, kafin kuma tace
"ashe mu bamu kai matsayin da zaku saurare mu ba"
Kai Yayan Farida kaga bana son fad'an rashin gaskiya, banga
dalilin hanata auren wanda ta keso ba, baka isa ba, kaji na fad'a maka"
Ba ta re da ya sa ke cewa komai ba yayi ficewarshi, Ummi ta cewa Baba ya nemi yaron ya sanar mai ya fito.
Baba kuwa yace shi a ganinshi tunda Umar baya so na hakura,
Ummi ta ce Umar yayi kad'an, aure ne ba fashi, idan shi bazaiyi ba zata
samu Alhaji.
Baba ya ce ba komai Ummi za'ayi ba sai anyi haka ba.
Baba da kanshi ya nemi Adamu, sai dai kuma ranar da muke sa
ran zuwan magabatanshi, da safe ina zaune a d'akina laptop ce a gabana,
naji alamar shugowar sako, abinda sak'on ya k'unsa yayi mugun tayar min
da hankali.
Wayar na d'auka na fita falo, Aunty ce da Baba suke ba Dr hakuri akan ya amince tunda na kafe sai Adamu.
Cikin ladabi ya ce "Baba ba wai bana son Farida ta yi aure ba ne, akwai abinda na ke jiye ma ta..."
Katse shi na yi gami da cewa "Ku daina bashi hakuri ai
burinshi ya cika ya je ya sanar da Adamu tarihin rayuwata, Adamu yace
ba zai auri macen da ta zubar da mahaifarta a titi ba"
Na k'arashe da kuka, dukan su jikinsu yayi sanyi, Dr ne yayi karfin halin cewa.
"kina tunanin zanje na fad'a mai wannan maganar, to meye ribata idan na fad'a"
"Kai kasan ribar ka, Umar bansan bakar zuciyarka ta zarce
tunanina ba, mugu azzalumi sai muntsaya agaban Allah, kuma na rok'eka da
Allah idan kai musulmi ne ba kafiri ba ka fita a rayuwata hakanan"
Ina gama fad'an hakan na yi ficewata ba ta re da na saurari Baba da ya ke ta min magana ba.
Tun daga ranar bama ga maciji da Dr kuma naji labarin har
kwanciya sai da yayi a asibiti Baba yayi-yayi naje na ba shi hakuri
nak'i.
Wannan ne silar 6atawa ta da Dr har zuwa wannan lokacin, amma bai fasa duk wata hidima da ya saba yimin ba.
****
Na san zakuso kuji meye dalilin da yasa duk wani saurayin da ya fito da niyar aurena k'arshe sai ya fasa .
Kawata wacce na yarda da ita, na amince da ita, na d'auketa aminiyata, itace ta ha'inceni "Mansura".
Ban san mai na mata taza6i ta k'untata rayuwata ba, ban ta6a yin k'awance ba sai akanta amma ta koyamin darusa da dama.
Dr shi da kanshi ya je ya binciko hakan, domin Ummi da
Alhajinshi sun d'auki fushi da shi sosai, Ummi ko gaisuwarshi ba ta
ansawa, wannan ne ya sa ya shiga tashin hankali mara misaltuwa.
Bayan da na samu labarin na yi k'okarin neman yafiyanshi
amma sam yak'i saurarata, tabbas nasan Dr mutun ne mai zuciya amma ban
san, abin zaiyi tsanani har haka ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ban sa ke sauraran wani
saurayi ba sai acikin wannan shekarar da muka had'u da Ahmad d'ina abin
sona abin k'aunata, wanda ya amince na zama abokiyar rayuwarshi.
Wata rana naje F.W.A Store (Store mallakin masu Fikrah)
anan muka had'u da Ahmad, hakuri tausayi da nacinshi yasa na amince mai,
har kuma na kamu da soyayyarshi.
Sai dai wannan karan tun farkon had'uwarmu Baba ya sanar
dashi komai dangane dani, Ahmad ya tausaya min k'warai ya kuma ce idan
dai ta shi ne zai aureni ya kuma zauna da ni bisa amana.
Amma Baba ya ce ba'ayi haka ba dole ya sanar da magabatanshi, mahaifiyarshi ita kad'ai ta rage mahaifinshi ya jima da rasuwa.
Ansha wahala kafin ta yarda ya aureni, amma da sharad'in
sai ya had'a mata biyu tunda ni ba haihuwa zanyi ba, dukan mu mun amince
akan hakan tunda ni k'addara ta haka tazo dole na kar6eta hannu biyu.
Wannan shi ne tarihin rayuwata.
****
Jidda ta ce "kawata tabbas kin fuskanci jarabawa kala-kala Allah yasa kin cinyesu, na tausaya miki k'warai da gaske"
Maryam ta ce "Dakta Allah yajikansu Mama ya gafarta musu,
wannan labari naki Izna ce ga mu y'an baya ina rok'on Allah ya miki
kyakykyawan sakamako"
Duka suka ansa da "Ameen" kafin Jidda ta ce "amma fa kawata
sai yanzu na fahimci tsakaninki da Dr Umar, tabbas Dr masoyinki ne na
gaskiya"
Maryam kuma ta ce "wallahi Dakta ina miki sha'awar Dr, dama kuyi aure"
"Mu dage da addu'a Maryam ni kaina ina sha'awar hakan wallahi" Jidda ta fad'a.
"Hmm" kawai Farida ta ce, gami da cewa "Ku tashi muje muyi sallah.
~Ummu Hanan~
0 comments:
Post a Comment