*It hurt to think that you're not here anymore, ...it's has
been 10years since you left us UMMINA, but the memory of your humble
personality will remain a scar in our heart , Allah sarki uwa tagari
Allah yamiki rahma ke da sauran musulmai....Death change everything!
Time change nothing*
kuyi ma mahaifiyata addu'a da bakin Ku mai albarka.
kuyi ma mahaifiyata addu'a da bakin Ku mai albarka.
*****
Ranar lahadi Ahmad ya dawo murna sosai masoyan nan suke, ranar da ya zo wurinta tamkar kar su rabu.
Ahmad matashi ne wanda ba zai wuce d'an shekara talatin da
takwas (38) ba a duniya, dogo ne fari, mai cikakkiyar kamala, siriri ne
mara jiki.
Su biyar mahaifansu suka haifa, kuma shi kad'ai ne namiji duk sauran mata ne.
Mahaifinshi Alhaji Ibrahim mai naira, ya mutu yabar musu
arziki, domin shi d'in d'an kasuwa ne, sannan ita kanta mahaifiyarshi
Hajiya Indo ba ta zauna ba, itama y'ar kasuwa ce sosai.
Ahmad ma kasuwancin ya keyi ba ma a gida Nigeria ba, yana saro kaya har daga k'asashen k'etare.
Wannan kenan.
Bayan dawowan Ahmad ansa ranar bikinsu shi da Farida sati uku masu zuwa, murna a wurin masoyan nan ba'a magana.
Shirye-shirye ake ba kama hannun yaro, Ummi da kanta ta gayyato kawarta daga Sudan domin a gyara ma ta amarya.
*****
Kwance ta ke akan gadonta, hankalinta na ga labaran da ta ke kallo a tashar BBC,
Iya ce ta shigo da sallama, Farida ta ansa, Iya ta ce "uwar d'akina Dr yazo yana falo ya ce na kiraki"
Gabanta ne ya bada rasss yau kuma da me yazo, karfi hali ta yi gami da cewa " Iya kice ina zuwa"
Sanin halinshi yasa hijab kawai ta zura ta fita, ya na zaune ya kame akan kujera, waya ce a kunnen shi.
Sai da ya gama wayarshi, sannan ya kalleta na d'an wasu dak'iku, kafin kuma ya ce.
"Banso ace na sa ke shiga wani abun da ya shafi rayuwarki ba, amma kiyi hakuri zan yi miki tambaya"
"Kina ganin za6in da kikayi hankalinki ya kwanta da shi,
kin tabbatar zai rik'eki amana, sannan baza ki fuskanci wata matsala
daga gareshi kokuma wani nashi ba, zuwa gaba"
Tabbas wannan tambayoyin nashi sun yi ma ta tsauri, ita
kanta ta na yawan yiwa kanta irin wannan tambayoyin, amma toh zata
cigaba da zama ne haka, sanin kanta ne rayuwarta ta jima da 6aci ba ta
da sauran wani jin dad'i.
"Yi hakuri da shishshigin da na yi miki, ga wannan" key ya ajiye ma ta a gabanta, ficewa yayi ba tare da ya jira cewarta ba.
Ba ta iya cewa komai ba, komai ya tsaya ma ta, lalle ta na bukatar mafita.
Ta jima ta na zaune a wurin kafin kuma ta janyo key motar da mamakinta ta ga wani key na daban wanda ba nata ba.
Ita a zaton ta key matar ta ce ko angyara tunda dama ya
aiko an kar6in key motar tun washegarin, "Allah sarki Ya Umar" ta fad'a a
fili.
Fita harabar gidan ta yi, mota ta hango an fakata sai d'aukan ido ta ke, kai tsaye can ta nufa da murna.
Motace mai kyau ta zamani, bud'ewa ta yi gami da shiga,
k'amshin shi na koyaushe wanda ya ke sawa ta shiga wani irin yanayi aduk
lokacin da ta shak'a.
Rufe idanunta ta yi a hankali, cikin wani irin yanayi, ita
sam ba ta gane wa kanta Ahmad shi ne wanda ta keso amma mai yasa aduk
lokacin da taga Dr koda kuwa k'amshin shi ta shak'a ta ke shiga wani
irin yanayi.
Ajiyar zuciya ta yi kafin kuma ta bud'e idanunta, a
hankali ta sauke su akan wasu takardu, da alama na motar ne, bud'ewa ta
yi.
FARIDA UMAR shi ya fito 6aro-6aro a rubuce, "ashe Dr zai
iya cigaba da anbata na da wannan sunan" wani lokaci Dr ya na bata
mamaki, idan yayi wani abun tamkar ba shi ba.
Ta na so ta mishi godiya amma ta na tsoron fad'anshi, haka
ta hakura sai dai text da ta tura mai ta waya, bai turo ma ta da ansa
(reply) ba, da ma batayi tsammanin reply d'in shi ba.
Su Baba da suka ga motar sosai sukayi farinciki a ta ke ya kirashi yayita samai albarka.
****
Ana sauran sati d'aya bikin, Hajiyar Sudan ta iso ta fara gyara amarya, dama tuni Farida ta d'auki hutu a wurin aikinta.
Amarya kam sai godiyar Allah ta sha gyara ciki da waje har ta gaji, tsayawa fad'an irin kyawun da ta yi 6ata lokaci ne.
Ranar laraba gida ya cika makil da y'an uwa, mutanan Wase
da na gombe harma da na jos sun fara hallara, sai hidima akeyi gwanin
sha'awa.
****
Wai mai yasa zuciyarshi ta keyi mai zafi ne, shin wai meke faruwa kar dai maganar Faridanshi ta zamto gaskiya.
Toh idan hakan ne meye ribar zuciyarshi idan tayiwa Farida bakin ciki.
"Kai ba haka bane, tayaya zanyiwa wacce nafi k'auna bakin ciki don ta cigaba, No tausayin halin da zata shiga na keyi"
Ya kasa zaune ya kasa tsaye, damuwa ta mai yawa, sam ya
rasa tudun dafawa, "Dr kiranka fa ake a waya" Mariya ta katse mai
tunani.
Cikin kasala ya d'auki wayar, ita kam kwana biyu ta rasa
gane mishi, sam bashi da walwala a y'an kwanakin nan, girgiza kai kawai
ta yi gami da fita.
****
Tun ranar da ya kawo ma ta key mota Farida bata sa ke sa Dr
a idanunta ba, ta na so ta gan shi ko dan ta nemi gafararshi amma abun
ya gagara sai dai kayan d'aki da ya aiko dashi na kayan su kujeru kayan
kallo da sauransu, a ranar Farida sai da ta yi kuka had'e da dana sanin
anbatar shi da munanan kalamai da ta yi.
"Tabbas Dr ya rik'e amanar Mama nikam na kasa rik'ewa" abinda Farida ta ke fad'a kenan ta na kuka.
Ranar alhamis da yamma labari ya riskesu cewan Dr ya yanke jiki ya fad'i a asibiti, hankalinsu ya tashi matuk'a.
Ta re da ita aka tafi asibitin amma suna shiga kallo d'aya
ya ma ta ya kau da kai bai sa ke kallonta ba, ita kam tasan Dr ya
tsaneta kuma ko ganinta baya son yi.
Zuwa ta yi ta durk'usa da gwuwowinta a gaban gadonashi ta na kuka ta ce
"Yayana ka yafemin na yi kuskure ka yafemin, bazan k'ara
ba, wallahi ni kad'ai nasan rad'ad'in da na keji idan na tuna yayana
yana fushi dani, kayi hakuri na tuba"
Ummi ce ta d'aga ta kafin kuma ta ce "Farida Umar karki damu Yayanki zai yi hakuri kwantar da hakalinki"
Shi kuwa Dr kau da kansa yayi bai sake kallon inda ta ke ba har suka tafi.
Likitoci sunce damuwa ce ta yi mai yawa, Ummi da Alhaji har
ma da Baba suka saka shi a gaba suna so ya sanar dasu damuwarshi amma
ya ce shifa babu abinda yake damunsa.
Da fad'a Alhaji ya ce " zaka raina mana wayo kenan, ka yanke jiki ka fad'i sannan ka ce ba komai"
"Alhaji ba komai fa gajiya ce ta sani na fad'i ba wani abu ba" sun jishi ne kawai amma ba don sun yarda ba.
*26.3.2016*
Jama'a da dama suka shaida d'aurin auran Farida da angonta.
kakaninta ne suka sata a tsakiya sai tsokanarta suke, ita
kam sam hankalinta baya wurinsu tunanin rashin samun wayar angonta ta
ke.
Tun jiya da safe rabonsu da yin waya ga shi ta gwada duk wayoyin shi a kashe.
Aunty ce ta zo ta ce taje su Baba suna kiranta a falo,
gyale Aunty ta yafa ma ta had'e da ruk'o hannunta jama'a sai yaba
kwalliyarta suke.
Zama ta yi a kasa gami da gaishe su, Alhajin su Dr ne, da
Ummi sai Innayo da kaka ta gombe sai kuma Baba da Aunty, dukansu da ka
kallesu kasan suna cikin farin ciki, Alhaji ne yayi gyaran murya, kafin
kuma ya fara magana kamar haka.
"Yau rana ce ta farinciki a garemu, mun godewa Allah da ya nuna mana wannan rana"
Ya d'anyi shuru sannan ya cigaba
"Farida duk wani d'a nagari yana biyayya ga iyayenshi a duk abinda suka umarce shi idan bai sa6a koyarwa addini ba.
~Ummu Hanan~
0 comments:
Post a Comment