Zaune ta ke amma sam hankalinta baya ta re da ita da alama
ta luluk'a duniyar tunani wanda ya zame mata kamar ibada saboda kullum a
cikinshi ta ke.
K'aran da wayarta ta ke ne ya dawo da ita da ga duniyan
tunanin da ta jima aciki, har sai da kiran ya kusan katse wa kafin ta
tashi cikin kasala ta isa inda ta ajiye wayar.
Ganin sunan da ya baiyyana akan screen d'in wayar shi yayi
sanadin k'aruwan bugun zuciyarta, sanin halin mai kiran da rashin raina
laifi komin k'ank'antashi yasa ta d'aga wayan gami da karawa a kunnenta
kafin kuma ta yi sallama.
Sallamarta kawai ya ansa gami da cewa " kije asibitina
akwai wata mai haihuwa da dole sai anyi ma ta CS, ni ba zan samu zuwa
ba, domin ni ne on call yau a T.H"
"toh" kawai ta ce da shi, ita dai kam ta na mamakin izza
irin ta Dr Umar jibi yadda ya ke ba ta umarni! ba ruwanshi da ko ta na
da wani uziri, tabbas baza ta iya mai musu ba dan bai can-canci hakan
daga gareta ba.
Muryashi ta tsinkaya ya na cewa "karki kuma tsaya 6ata
lokaci, domin ta na bukatar taimakon gaggawa" ba ta re da ya jira
cewarta ba ya kashe wayarshi, ita d'in ma dama ba ta da ta cewa.
Kaya kawai ta sauya domin ba ta jima da yin wanka ba, gyara
fuskarta ta yi, kafin kuma ta feshe jikinta da turarukanta masu
k'amshi.
Sannan ta d'auki dukkan abinda za ta buk'ata, jin muryar
Auntynta a kitchen ya sa ta nufi kitchen d'in kai tsaye, a kitchen ta
same ta, ta na ta faman shirya abinci, ido waje ta ce "Aunty yaushe ki
ka dawo da ga kafin madakin"?
Cikin sakewar fuskar Aunty ta ce " tun d'azu na dawo na
lek'a d'akinki naji kamar kinsawa kofar key sai na yi zaton bacci kike,
sai kawai na kyaleki"
" Ya kuka bar su Hajiya Baban?" Farida ta fad'a, Aunty ta
ce "suna nan kalau, ta ban sak'o ma na kawo miki" Farida ta ce "Allah
sarki Hajiya baba"
Aunty ta k'ara da cewa "na ga kamar fita ma zakiyi ina aka
nufa ne" Farida ta Sosa kunnenta da key d'in motar da ke hannunta had'e
da cewa.
"Dr ne ya ce naje na duba wata mai haihuwa da za'a mata operation ga shi kuma shi ne on call a T.H"
Aunty ta ce "to ma za yi sauri ki tafi don bamu san halin
da ta ke ciki ba inkin dawo mayi magana" "sai na dawo Aunty" kawai ta ce
da Auntyn, ita kuma Aunty ta bita da addu'an dawowa lafiya.
**************
Gumi ta had'a sosai wani bak'in ciki ne ya ziyarce ta, ace
mota ba'a rufa sati biyu sai ta kawo ma ta matsala, gaskiya dole ne ta
canja motar nan, ga dare yayi karfe kusan goma (10am) kuma tak'i tashi,
ba kuma samun abun hawa za ta yi har zuwa unguwar da ta ke ba, tsaki
taja had'e da dukan sitiyarin motar.
Hango motarshi a gefe anyi parking d'inta yasata yin hamdala domin ta na da tabbacin ya dawo.
Zuciyarta ce ta gargad'eta da ce wa "Idan dai gunshi za ki
neman alfarma, tabbas za ki had'u da 6acin rai gara dai kiyi tunanin
wata mafitar" d'aya 6ari na zuciyarta kuma ya ce " zakiyi ta zama ne
anan yanzu haka hankalin su Baba ya fara ta shi, toh wai ita ya zata yi
ne"
Wani 6ari na zuciyarta ya ce "ba ki da mafita illah dai
kawai kije ki same shi" gama wannan tunanin kawai ta rufe motar kaitsaye
office d'inshi ta nufa.
Bubbugawa ta yi gami da yin sallama aciki taji ya ansa,
bud'e kofar ta yi had'e da shiga kafin kuma ta ce "ina wuni" bai ansa ba
hasalima ko kallonta baiyi ba idonshi nakan na'uwar laptop.
Ita d'in ma dama ba ta sa aranta zai ansa ba, ba ta kuma yi
gigin zama ba tunda tafi kowa sanin k'a'idarshi da sai ya bada izini
kafin azauna.
Kusan minti goma (10mns) ta na tsaye ba ta re da yako d'aga
ido ya kalleta ba, har ta fara ji kafarta na mata zugi don dama ta gaji
bayan Tiyatan sai da ta duba marasa lafiya.
Muryarshi ta tsinkaya ya na ce wa "ya dai" yadda yayi
maganar cikin sanyin murya abun har ya ba ta mamaki, kallonshi ta yi don
ta tabbatarwa da kanta shi d'in ne kuwa yayi maganar, kafin ta bashi
ansa ta sa ke tsinkayar muryashi ya na ce wa " tambayarki na ke kin wani
kafeni da ido tamkar mayya" wannan karan yayi ne cikin fad'a.
Cikin sanyi murya ta ce "dama motata ce tak'i tashi kusan awa d'aya ina fama amma tak'i tashi gashi dare yayi"
Ta kuma kasa kunnenta don jin masifar da zata kuma biyo
baya, mutum kamar mai aljanu dubi fa d'azu ita dai tasan tunda ta shiga
office d'in bai ko d'aga ido ya kalleta ba, to ya'akayi yasan ta na
kallonshi, a zuciyarta ta ce "Allah ya kyauta"
Sai da ya sa ke d'iban lokaci kafin ya sa ke ce wa " yanzu me kikeso na miki "
Toh mai za ta ce mai sai kawai taja bakinta ta yi shuru
had'e da sunkuyar da kai, wannan karan ma ya sa ke d'aukan wasu mintoci
kafin ya sake ce wa.
0 comments:
Post a Comment