*S*allama take tayi tun daga k'ofar gidan,amma ko tari ba ayiba,ga rana dake dukan kanta...
Banda maik'o babu abunda take,jin ank'i ansawa,yasa ta d'aga allonta dake hannunta ta d'ora akanta,don kare ranar da ta addabeta...
Zuwa can ta sake maimaita yin sallamar,nanma dai shiru aka mata babu amsa....
Hakan ne yasata tsugunawa,ta cire silifanta ta zauna akai kamar mai d'aukan darasi.....
Tun daga nesa dattijon dake tahowa,yake kallonta,sauri ya K'arawa k'afarsa dan tabbatar da zatonsa....
Daf da ita ya k'araso,tare da fad'in *"NANA KHADIJATU*, Uwata me kikeyi a cikin wannan ranar da kowa yake gudunta???"
'Dagowa tayi da saurinta jin muryan mahaifinta dake tsaye,da murnarta ta kalli mahaifin nata tana fad'in "Abba na dawo ina sallama,ba a amsaba shi yasa na zauna anan ban saniba ko ba kowa a gida"....
Banda abunki kuma uwata sai kizo cikin wannan ranar ki zauna kamar an miki dole...
"Tashi maza mu shiga ciki,kar kuma ki sake zuwa ki zauna kinji ko,wannan ai sai wani ciwon ya kamaki"...
Fad'in abban *KHADIJATUL KHUBRA*.....
Hannunta ya kama suka kama hanyar shiga gidan....
Tun daga bakin k'ofar gidan yayi sallama,jin shiru ba a amsaba,yasa abban yaci gaba da kutsa kai cikin gidan had'e da sake yin wata sallamar....
Abunda ya matuk'ar bawa abba mamaki bai wuce ganin da mutum a tsakar gidanba.....
K'arasawa yayi yana k'are mata kallo,kafin ya iya furta ‘’ladiyo dama kina zaune muke sallama,amma amsawa ta gagareki‘’.....
Fuska ta yatsina (tamkar kayan miyan da yaso lalacewa).....
kafin ta bashi amsa da cewa ‘’ina ji sai me??
ko kuwa cewa akayi an ajiyeni ne dan na amsa muku sallama?''......
Ganin zata kunyata shi gaban y'arsa yasa yabar maganar ta hanyar fad'in ''Allah ya kyauta''......
Bud'ar bakin ladiyo sai cewa tayi ''ya kyauta abinda yafi haka''.....
Bai kuma tanka mataba,ya juya yana girgiza kai,ya shige d'akinsa.....
Duk wannan budurin da ake a gaban KUBRA ake,kanta na k'asa sai hawaye dake tsiyayowa daga ciki......
Ganin abbanta ya bar gurin itama ta juya da niyyar barin gurin....
Sai dai muryar ladiyo ta rigata k'arasawa bakin k'ofar d'akin,ta hanyar mako mata mula²n zagi......
Da sauri ta k'arasa shigewa,gabanta na dukan 9²....
Can ku'ryar D'akin ta nemi guri ta zauna,tana jiran gawon shanu....
Cikin d'akin da baida wadataccen haske,take zaune,tayi shiru sai kalle² take tamkar wata bak'uwa,ko wacce ta fara rayuwa inda bata saniba,haka taketa fama ita kad'ai,a haka bacci yayi awon gaba da ita.......
Wani k'ayataccen guri ta hango mai kyan gaske....
Sauri take ta k'arasa gurin,amma duk da haka ta kasa k'arasawa gurin,saima gajiya da tayi......
Haka ne yasata neman guri ta zauna,tana k'arewa gurin kallo ko zata hango inda ruwa yake.....
Rashin ganin alamar ruwa yasata,juyawa ta kalli hanyar da ta biyo.....
hanyace mik'ak'kiya wacce ko farkonta bata ganiba,bare k'arshenta,hakan yasata kifa kanta ta fara rera kukan rashin Madafa....
Tun daga nesa ta fara jiyo hayaniyar mutane had'e da wani daddad'an k'amshi da yasata saurin d'ago kai,tana bin hanyar da hancinta.....
Ayarine na mutane da suke da mayuk'ar yawa suke shirin giftawa ta kusa da ita......
Da sauri ta mik'e tabisu duk da suna kan abun hawa,hakan bai hanata shiga gabansuba,tana fad'in
"Dan Allah ku taimakamin"....
Babu wanda ya saurareta,sai zagayeta da sukayi suka ci gaba da tafiya......
Da gudu² ta sake shiga gabansu,tana rok'onsu.....
Wannan karon kam saboda haushi da ta bawa wasu daga cikinsu yasa su yi mata tsawa....
A firgice,jikinta har rawa yake saboda tsoro take kallonsu,wani k'ato da yayiwo kanta d'auke da bulala yasata fara kuka....
tana bashi hak'uri,d'aga bulalar ya d'aga da niyyar sauke mata a jikinta......
Kafin ya k'arasa ida nufinsa,wata siririyar murya daga bayansa take fad'in kada ka kuskura ka aikata abunda kake k'ok'arin yi .....
Da hanzarinsa ya juya don ganin mai magana,sai dai ganin fuskar wanda yayi maganar yasa shi kaucewa daga kusa da ita,jikinsa na kad'awa tamkar Mazari.......
Kyakykyawan matashi ne ya bayyana daga inda ya kauce,yana sanye cikin fararen tufafi,tafiyarsa cike da k'asaita,har ya k'araso Inda suke.....
Kallon k'aton yayi kafin ya bud'e baki,har ya rigashi cikin ladabi da girmamawa yake fad'in ''tuba nake ranka ya dad'e''......
Hannu ya d'aga masa,ba tare da ya sake yunk'urin yin maganaba,ya juya da nufin barin gurin............
.
*C*ikin sauri tabi bayansa,tana k`ok`arin tsayar da shi,sai dai hak`anta bai cimma ruwaba…....
Duk da bawai sauri yakeba,haka take binsa tana fad`in *"BAWAN ALLAH* ka tsaya"......
Ganin ta kasa cimmasa,kuma baiyi kokarin tsayawaba,yasa taci gaba da binsa....
Sai dai kamar wanda yake tafiya a cikin iska,haka ta kasa riskarsa,tsayawa tayi,lokacin ne ta hangoshi har ya dad`a mata nisa sosai..…
Zama tayi cike da takaici,gashi ko sunansa bata saniba,a matsayinsa na wanda ya ceci rayuwarta..…
Murmushi ta saki lokacin data tuna cewar zasu sake had'uwa koba wannan lokacinba....…
***************
*LADIYO* dake zaune tsakar gida,wadda tun wucewar *KHUBRA*,take rafka mata kira...…
Jin shiru babu amsa yasata mikewa tayi hanyar d'akin,da niyyar dubawa taga uban me take da har zata kirata tak'i amsawa...…
Shigarta d'akin ta tarar da ida kwance kan dagargazajjiyar tabarmarta,da take kwana kai..……
Ganinta tana bacci ba k'aramin b'acin rai tajiba,Kai ta girgiza,kafin ta koma da baya,tana fad'in da ni kike zancen yarinya...…
K'aton randan k'asa ta d'auka,ta nufi d'akin dashi,bata jira komaiba,ta juyeshi akan *KHUBRA* dake tsaka da dreaming....…
****************
A razane ta mik'e tana duba jikinta da yayi sharkaf da ruwa ga shi duk d'akin ya jik'e ruwan har ya kwanta,a tsakar d'akin...…
'Dagowa tayi ta kalli *LADIYO* dake tsaye tana watsa mata wani mugun kallo...…
Sake juyawa tayi ta kalli d'akin duk wani kaya dake ciki a jik'e yake,saboda ruwan ba kad'an bane...…
Kayanta ta fara tattarawa da niyyar gyarawa...…
*LADIYO* dake tsaye,tana raba ido akanta,ta fizgota tare da wanke mata fuska da mari...…
Gigicewa *KHUBRA* tayi,ta rasa me zatayi,shin kuka za tayi ko kuwa me????
Rashin madafa yasata neman hanyar ficewa daga d'akin...…
Ashar en da *LADIYO* tayi ne ya dakatar da ita,juyowa tayi,cikin ladabi tana fadin
"Kiyi hakuri baba ladiyo,zan gyara gurin ne"…………
''Dan ubanki ni kike fad'awa zaki gyara guri,to billahillaziy baki isaba'' fad'in LADIYO kenan kafin ta d'ora da cewa......
''Maza tun kafin na sab'a miki,ki wuce ki d'ebo ruwa,kin san aiki na nan yana jiranki,kika shigo d'aki kika kwanta ke ga sarauniya koh?''......
Rab'awa tayi ta kusa da ita ta fice,ba tare da ta sake cewa komaiba,sanin irin aikin dake gabanta.....
Tulunta ta d'auka ta kama hanyan rafi,jikinta duk babu dad'i ga kayanta dake jik'e.......
Tafiya take duk kunya ya isheta,saboda surar jikinta dake bayyane ta jikin kayan,duk da bawai banyan ne yake da mutaneba,sai dan kasancewarta mace mai tsanin kunya......
Tana tafe tana tunanin abunda ya faru yanzun,kafin fitowarta daga gida.....
A wani b'arin kuma na zuciyarta tana tunanin mafarkinta,Wanda shi ne kusan zata iya sashi a matsayin silar faruwar komai.......
A haka ta kammala d'iban ruwa,ta sake duk'ufa kan aikin cikin gida,duk da kasancewarta ba mai yawan shekaruba,amma yau da gobe yasata gogewa a fannin aikin gida......
Wuni guda tana aiki,tamkar jaka har kusan almuru ta kai,kafin ta kammala aikin.......
Sai a lokacin ne ta samu kwanciyar hankali,bayan ta je ta watsa ruwa,alwala ta d'auro ta shige d'akinta,da tun fitarta bata sake samun damar komawa cikinsaba sai ynzn.......
***************
Ta jima a tsaye tana kallon yadda k'asar gurin ta tsotse ruwan.....
Haka ta lallab'a ta rab'a gefe ta kabbara sallah...
Kafin wucewar wasu sa'o'i har ta idar....
Kwanciya tayi a gurin duk ta takure guri d'aya......
Sai a lokacin tunanin mafarkinta ya sake dawowa,murmushi tayi,tare da fatan sake ganin fuskarsa ko da a mafarkin ne,duk da dama bata tsammanin ganinsa a zahiri......
*************
Haka rayuwar *KHUBRA* taci gaba da kasancewa,kullum safiyar Allah za taje makarantar allo,daga zarar ta dawo kuma zata fad'a harkar aikace² har goshin maghreb.....
Bata da wajen zuwa,kullum tana gida (kamar daddawa).......
Rayuwarta ita kad'ai,babu k'awaye,bare ta samu abokin shawara......
Babban damuwarta baya wuce rashin zuwa dangin mahaifiyarta,Wanda tun kafin ta girma,shima bawai zata iya tunawa bane.....
Siraran hawayen da suka sakko mata ta goge,tare da tausayawa rayuwarta,irin k'angin da take ciki............
*_~
*D*a sanyin safiyar wata laraba,tana tafe a hanya,tunanin mutumin da ta gani a mafarkinta ya sake dawo mata,ji tayi duk duniya babu abunda take da muradin gani sama da shi......
Wanda rabonta da shi tsawon sati guda kenan......
Sauri ta shiga yi na ganin ta k'arasa gida,burinta bai wuce tayi aikin da ta saba ta k'are ta kwanta ko zatayi dace a yau tayi katarin ganinsaba....
Da haka ta k'arasa,sai dai me zata tarar,zuwanta gidan ta tarar da LADIYO da wata k'anwarta da tazo daga garin KANO suna zaune cikin rumfa banda shewa babu abunda suke,duk sun cika gidan da hayaniya.... .
Tayi sallama yafi a k'irga,amma cikinsu babu Wanda yayi yunk'urin amsawa..
Haka ta wuce ta ajiye allonta.....
Dawowa tayi har k'asa ta durk'usa ta gaida ASMA'U wacce akema lak'ani da MA'U........
Yatsina fuska tayi,kafin ta kalleta had'e da zabga mata wata uwar harara........
Tsakine ya biyo baya,cikin tsawa take fad'in
''ke ni dallah b'acemin anan gurin,kinibabbiya kawai''.....
Cikin sanyin jiki KHUBRA ta mik'e ta bar gurin,ranta duk a b'ace,haka ta Shiva aiki babu ji babu gani......
*°°°°°°°°°°°°°°°*
LADIYO ce ta buga wani uban tsaki,da yasa k'anwarta MA'U kallonta,tana fad'in ''YAYA ince dai lafiya''.......
''Inafa lafiya,wannan shegiyar yarinya tana gidan nan ina naga kwanciyar hankali'',cewar LADIYO..........
Nan MA'U ta samu dama,ta fara magana da cewa
''YAYA aradu nu kaina na tsani tarinyar nan,da nazoma banyi tsammanin tana nanba,amma yanzun ga wata shawara.......
Me zai hana ki bani ita mu tafi birni,a samamata aikatau,duk wata abunda aka biya sai ina aiko miki da shi,kinga kin huta zaman banzan nan,ke ba sana'aba,ko kuwa ya kikace?''
Ta k'are maganar tata da son jin amsar da za a bata.......
Tunanin maganar MA'U ta shiga yi,zuwa can kuma ta ce
''To amma banda abinki MA'U ta ina zaki tafi da ita ba tare da ubanta ya saniba,ni da bani na haifetaba,dama anamin gorin ko kwai na kasa ajiyewa,kuma na tabbatar ba yarda zaiyiba''......
''Haba YAYA ke kam kamar ba mace ba ko da yaushe aka kawo magana bakya saurin amincewa sai kin kawo suka,shi kenan kinga ai sai kiyi ta zama babu sana'a'' ta fad'a tana had'e fuska,da alama bata hi dad'in maganar da y'ar uwar tata ba........
A'a MA'U baki fahimci me nake nufiba,dolefa sai malam BUBA yasan inda zata,kodama ace an tafi da ita babu saninsa saiya tambaya,kuma yana ganin bani na haifetaba ta ina zai amince da abunda zan fad'a.......
''Shi kenan na gane,amma dai kisan yadda za kiyi ki had'a mata kayanta,a kaita aikatau kema kya samu kifi k'arfin wani abun''.......
Yanzun an daina saka y'ay'a a gaba ana kallonsu,barema ke da babu d'a bare jika........
Ki lallab'ashi akan ni zaki bawa aronta,mijina ne baya nan zata tayani zama,zuwa nan da wani d'an lokaci zata dawo.........
Kinga daga nan sai dai yaji kid'a a magwan.......
Nan suka sa shewa,har da tafawa.......
Wunin ranar haka MA'U ta zauna tanata yiwa LADIYO hud'uba,wanda k'arshe sai da ta amince,akan ko Malam en baya so sai ta aikata........
*°°°°°°°°°°°°°°°*
Kwanakin MA'U uku a k'auyen na KASHIN DILA,tayi niyyar komawa inda ta fito.......
Kayan da KHUBRA ta fito da shi ne ya tabbatarmin da sunyi nasara akan k'udurinsu......
Fuskanta cike da damuwa,haka sukayi sallama,har bakin k'ofar gida LADIYO ta rakosu,tana yiwa y'ar uwarta fatan sauka lafiya......
Nan suka kama hanyan barin garin,mashin d'in achab'a suka hau,daga nan bai saukesu ko inaba sai tashar garin na HAD'EJIA........
Misalin k'arfe d'aya na rana motarsu ta harba kan titi.......
*~#SAFE TRIP KHUBRA...~*
Tafiya ta mik'a,inda KHUBRA dake cikin booth,tsakiyan kaya,tunanin abun duniya duk ya isheta,tana ta sak'a da war-wara bata san lokacin da bacci yayi gaba da itaba.......
*°°°°°°°°°°°°°°°*
Juyowa yayi ya hangota durk'ushe ta kifa kanta,banda kuka babu abunda take......
Cikin takunsa na k'asaita ya k'araso har gabanta......
Bata san zuwansaba,sai k'amshinsa da ta jiyo daf da ita.....
Cikin hanzari ta d'ago,baki ta bud'e da niyyar magana.......
Hannu ya mik'a ya rufe mata bakin,nan KHUBRA ta zaro ido,ganin abunda yake faruwa.....
Da sauri ta cire hannun nasa daga bakinta,cikin damuwa take fad'in
''Me yasa zaka tab'ani bayan ni ba muharramarka bace?''.......
Kallonta yayi tun daga sama har k'asa kafin ya iya bata amsa
''Kin tab'a jin inda akace idan miji ya tab'a matarsa yayi laifi?''......
"Bud'e baki tayi tana k'are masa kallo,ta ina na zama matarsa?"
Abunda KHUBRA bata saniba a fili tayi maganar.......
Cikin b'acin rai da fushi ya fara magana
''Nayi miki k'arya kenan? tunda kin d'aukeni a mak'aryaci,daga yau bazaki sake ganina ba,zanyi nisa da ke,har zuwa lokacin da zaki fuskanci gaskiya''
Daga haka bai sake yi mata magana ba ya juya yaci gaba da tafiya.........
Hak'uri take bashi akan ya dawo,amma ina haka duk kukan da take bai koda sake waiwayeba.......
Kuka mai tsanani ta keyi,tana fad'in dan Allah karka tafi ka barni,ka dawo dan Allah na yarda............
*°°°°°°°°°°°°°°°*
Dai² lokacin da take tsaka da dreaming,suka k'araso birnin KANON DABO gari mai tarin albarka.......
Baccinta take shak'a a Booth sai bakinta dake motsi tana juya kai,hawaye sai layi yake akan face enta......
Har aka bud'e booth en bata saniba,sai da MA'U ta k'araso gurin tana masifar rashin fitowar KHUBRA nan ta tarar da ita tana bacci,mari ta zabga mata,a firgice ta tashi,tana dafe da kuncinta,ta sakko ta shiga jidar kayan,suka kama banyan fita daga tashar.......
Sai lokacin ta tabbatar da cewa abunda ya faru duk mafarki ne.....
fuskanta ta shafa,ruwan da taji ta gogo yasata mamakin inda ta sameshi.......
Dallah ni kina b'atamin lokaci,kin wuce mun tafi ko saina zane miki jiki.........
Cikin sanyin jiki ta ja k'afafuwanta suka ci gaba da tafiya...........
*_~
*T*afiya kawai suke ba tare da *KHUBRA* ta san inda suke nufaba,sai kalle² take a haka har suka fito bakin hanya...
Kafi babur suka tare,MA'U ta tak'ark'are ta hau yi masa bayanin rijiyar lemo zai kaisu......
Kud'in da ya yanko mata zata bayar,ta tsaya wangale da baki,nanfa suka tsaya ciniki,yi take kamar ba za a dainaba,d'an adaidata da yaga bazai iyaba,yaja kekensa yayi gaba.....
Duk Wanda za ta tsayar idan taji bai mata yanda take soba sai dai yaja Babur ensa ya k'ara gaba.......
Son kud'i irin nata ya hana su tafiya.......
Sun jima tsaye ba tare da sun samu abun hawaba.....
Ita MA'U son kud'inta da ganin tsada ya hanata ta biya akaisu inda zasu.....
Haka sukaci gaba da jira,yamma na dad'a kunno kai......
'Bangaren KHUBRA kuwa wata azababbiyar yunwace tafi addabarta ga bakinta da ya bushe saboda tsabar k'ishi da ya dameta.....
Rashin sanin abunyi da kuma hali irin na MA'U yasa ta ja bakinta tayi shiru,sai raba ido da take akan hanya......
Ganin tsaiwa bazai kai musuba,da kyashin biyan kud'in motar yasa MA'U juyawa ta kalli KHUBRA,tana yatsina mummunar fuskarta......
Tunda nake a rayuwata ban ta'ba zuwa na b'ata lokaci a tsaye ba tare da samun abun hawaba sai yau da na d'auko MAI BAK'IN JINI......
Jin furucinta na k'arshe yasa jikin KHUBRA dad'a yin sanyi....
Ba tare da ta kalletaba,haka bata ce uffanba.......
''Yanda kikaimin bak'in ciki na rasa abun hawa haka wallahi saina fanshe kud'ina tare da ke MATSIYACIYA Y'AR MATSIYACI''.......
Maganan da ya fito daga bakin MA'U kenan wanda ba k'aramin sosawa KHUBRA rai yayi ba,take hawayen da bata son fitowansa ya b'alle,ita kam da ita ta zaga babu da zai sa ta damu,abunda yafi komai bak'anta mata rai zagin ABBANTA da MA'U tayi....
Ko ganin girmansa batayiba,bare d'aga masa k'afa a matsayinsa na miji ga yayarta.......
Wannan shi ne abunda ya jawo mata ZUBAR HAWAYE.....
Dad'a sunkui da kanta tayi k'asa,ta shiga goge face nata,dan ta tattabata idan MA'U ta san halin da take ciki tana mai iya jibgarta a gurin tamkar kayan wanki......
Sake tsaida wani tayi,babu ko ciniki ta afka tare da cewa ''idan kinga dama kya taho mu tafi.....
Jan k'afafunta tayi ta shiga,duk da haka bata tsiraba,k'arshema sai cikin booth d'in mashin en ta zauna,tun daga kasuwar ta y'an kaba har zuwa unguwan na rijiyar lemo......
**************
Sun is a unguwan ana sallan Maghreb,yana saukesu ta laluba cikin d'an topinta ta zaro masa kud'insa....
Kud'i sosai KHUBRA ta gani ta fito da shi,nan ta tabbatar matar tana da bak'in hali....
Tunani ta shiga yi,na irin rayuwar da zata fuskanta nan gaba,ko yaya zata kaya tsakaninta da MA'U?........
*_Ni ko nace ai KHUBRA bakiga komaiba......._*
*_~Kumin uzuri fan's in sha Allah next page zaizo ba kamar wannan ba..... ~_*
*_Masoya novel ena na RAYUWAR WANI kuyi hak'uri na jina shiru kwana biyu in sha Allah zanci gaba daga inda na tsaya,na gode sosai_*
*_~IYA WUYA MUNA TARE......~_*
*_~
*B*inta kawai KHUBRA take a baya² har suka k'arasa k'ofar gidan.....
Mukulli ta zaro irin wanda ake kira da (KUBA) en nan ta shiga murd'awa a jikin k'ofan,da kyar ta samu ta bud'e saboda taurin da k'ofan yayi.....
Gidan bak'i k'irin da shi,ga uban daud'a da yayi,kai saika rantse bai tab'a ganin wani abu mai kama da tsintsiyaba.....
Kunna kai tayi ciki ba tare da ta damu da addu'ar shiga gida ba,duk dama dai bana tunanin ta iyata....
KHUBRA dake baya,ta tsaya k'ofar gidan kafin ta shigo....
Sai da tayi addu'ah ta sanya k'afanta cikin gidan,kasancewar mahaifinta yana koyar da ita ilimin FIQHU,AZKAR da sauran abunda ba a rasa ba na zamantakewar duniya......
Bata tarar da MA'U a tsakar gidanba,guri ta samu ta zauna gudun kada tayi laifi,coz ta san yanzun sai ta bi a hankali,tunda tasan halinsu ba k'aunarta sukeba......
Tayi nisa cikin tunani,kan mafarkinta...
Abunda take son fuskanta kan mafarkin ya gazawa tunaninta....
Tashi tayi tana k'ok'arin shiga band'aki danta samu ta rama sallolin da ke kanta,nan ta bar kayan ta shige.....
Ko uzurin da ya kaita bata k'arasaba ta tsinkayo muryan MA'U daga tsakar gida tana surfawa iyayenta zagi....
K'irjinta ta dafe had'e da zaro ido,dan ko ba a fad'a mataba tasan laifinta.....
Addu'ah ta hau yi a zuciyanta,tana me neman tsarin ubangiji tsakaninta da MA'U da kuma zaman da zasuyi nan gaba......
Fitowanta ta tarar da ita tsaye ta rik'e k'ugu kamar wata k'aramar yarinya sai girgiza take.....
Kallo d'aya ta mata ta d'auke idonta a kanta,ta sunkuya ta fara alwala......
''Don ubanki ni zaki mayar mahaukaciya ina magana ki juyamin baya,ko ubanki wannan matsiyacin bai isaba wllh''...
Maganar da ta biyo bayan hucin da take kenan kamar wata KUMURCIN MACIJI.......
K'in magana,duk da kalmomin da tayi amfani dasu sun shigeta,shiru tayi har sai da ta idar da alwalan,sannan ta juya tana bata hak'uri......
Wata uwar harara ta rakata da shi kafin ta figi kayanta tayi cikin d'aki.......
Gajiya da tayi da tsaiwa,ganin ank'i kulata bare ta samu a kirata,kan dole ta nufi hanyan d'akin bakinta na d'auke da addu'ah....
A kwance ta tarar da MA'U,nan ta tsaya tunanin koh wane hali mahaifinta yake ciki a yanzun......
Tsayawan mutum MA'U ta gani kanta cikin sauri ta bud'e idonta,tana zabga mata harara....
Kame² KHUBRA ta fara kafin da kyar ta iya furta
''Dama abun sallah nake so''...
Bata tanka mataba,haka bata tashi ba,saima dad'a rufe idonta da tayi,tana daga kwance kan gadon k'arfe irin na da ennan.....
Ganin tsaiwa bazai kai mataba,ta kabbara sallah daga inda take tsaye.....
Tana sallah tana dafe cikinta da yake ihun yunwa,a haka har ta samu ta idar ba tare da ta kai GA fad'uwaba.....
MA'U kam bacci ne ya kwasheta nan,ba tare da tunanin tashi ta gaida mahaliccinta ba.....
Har bacci ya fara d'aukanta ta tuna da k'ullin kayanta dake waje,cikin hanzari ta fita ta d'auko bata dawo d'akin ba saida ta tabbata ta kulle k'ofar gidan.....
'Dakin ta dawo ta hau bud'ewa,can k'asan kayan ta binciko wani k'ullin leda da ABBANTA ya bata tun jiya....
Bud'ewa ta hau yi,k'uli² ne mai d'an yawa irin wanda ake yinsa da sugar ennan.....
Ci ta fara,kamar wacce ta samu nama,haka ta far masa,sai da taci mai yawa,sannan ta hak'ura ta d'aure ta mayar cikin ledan......
Waje ta sake komawa cikin randa ta d'ebi ruwan da tasan zata iya shanyewa....
Godiya tayiwa Allah,sannan ta koma d'akin ta kwanta a k'asa dai² inda ta idar da sallah.....
Take kuwa bacci yayi gaba da ita......
************
Daf da kiran sallan assalatu ta farka,kasancewar ABBANTA kullum shi yake tashinta idan zashi masallaci sallah da asuba....
Fita tayi ta d'auro alwala,tsakar gidan da duhu sosai,haka ta daurewa zuciyarta tayi sauri ta dawo d'akin.......
Har ta idar da sallan MA'U ko juyin farko batayiba,haka itama KHUBRA batayi gangancin tashintaba.....
Gefe ta koma,ta had'a kai da gwiwa,tana tunanin duniya da makomar zuwanta wannan gari,tasan dai babu komai cikinsa face zallar wahala......
Ganin tunani ba kaimata zai ba,ta shiga karanta AZKAR na safiya,tana zaune har gari ya k'arasa wayewa......
Hijab dake jikinta ta cire ta fita tsakar gida......
Tsintsiya ta d'auka ta hau shara,kafin wani dogon lokaci har ta kammala,sai ga gidan yayi haske daga bak'ar daud'ar da yayi.....
Har tayi wanka MA'U bata san me yake faruwaba...
'Dakin ta dawo,da tunanin ta tasheta ko kuwa......
Tsayawa tayi tana nazarin ta inda zata fara,amma fargaba ya hanata tab'uka komai.....
Kan dole ta hak'ura,ta zubawa sarautar Allah ido......
*************
Sai misalin k'arfe 8:00am ta farka tana ta faman zabga hamma,had'e da mik'a....
Da kyar ta iya tashi tayi waje,ganin tsakar gidan a share tas,ta tab'e baki,ta rarumi buta tayi band'aki,ta jima aciki,tamkar wacce ta sami d'aki,zuwa can kuma ta fito,ta sake d'iban ruwa a bokiti ta koma....
K'arar ruwa kawai kake ji kamar wacce taje suuuu kogi,haka ta shek'ashi a jikinta ta fito,cikin abunda bai wuce minti 5 ba.......
Alwalan ma buji² akayi aka fad'a d'akin.....
Shigarta ta tarar da KHUBRA har ta gyara d'akin tsaf duk ta gyare tarkacen dake cikin d'akin.....
Babu ko sannu bare an gode,saima ladan gaben harara da yatsina da ta shiga yi......
Shiryawa tayi cikin gaggawa,tasa wata atamfa riga da zani,taja gazal a idonta......
Takalminta ta sharfad'a tayi waje ba tare da yin ko da sallan da akayi alwala domin taba......
Babu magana bare KHUBRA ta sa ran ganin abinci tayi waje,tana gaisheta ma ko ta kanta bata biba.....
Ta k'arawa k'afafuwanta mai.......
*_~ALLAH YA SHIRYA.......~_*
*_~
*I*ta d'aya zaune tayi shiru,abun duniya duk ya taru ya mata yawa......
Tunanin gida da mahaifinta duk shi yafi damun zuciyanta,ko a wane yanayi yake? Allah shi ne masani......
Ganin babu sarki sai Allah,shi yasa ta bawa zuciyanta hak'uri......
'Daki ta sake komawa,bayan ta tura k'ofan gida,da yake ta san ita kad'ai ke gidan,gudun kuma kada wani abu ya faru......
***********
Tafiya take duk inda ta samu watsa k'afafuwanta take,tamkar wacce zata tashi sama.....
Son kud'i irin nata ya hanata neman abun hawa......
Sai da tsakiyan rana,ganin babu haza yasa ta hak'ura ta nemi keke napep,daga UNGUWAN KURNA zuwa RIJIYAR ZAKI,a ganinta nan ne unguwar masu kud'i,za tafi samun gidan aiki,idan bata samuba kuma,zuwa gobe sai ta nausa cikin gari......
Zafin rana da k'ishi su suka haddasa mata tsaiwa,ta nemi abun hawa,idan yaso sai ta k'arasa,in da ta nufa......
Ta tsayar da masu napep sama da guda goma,amma da sun tsaya suke k'arawa babur en nasu wuta suyi gaba.......
Da kyar ta samu abun hawa,kan neman ragi irin na MA'U......
Yinin ranar yawo ta dungayi gida² take bi a unguwan na rijiyar zaki,kan neman gidan da suke neman Y'AR AIKI.....
Sai da ta sha wahala,kafin ta samu gidan da suka nuna mata suna buk'ata......
Sun gama ciniki kan dubu biyar per month......
Duk iya yinta na su k'ara mata wani abu,hakan ya faskara....
Gudun kada tayi asara gashi wannan d'inma da kyar ta samu,bayan yini da tayi tana GARARIN DUNIYA yasa ta amince,akan zata kawota daga zaran sun gama shiryawa......
Abinci matar ta kawo mata da ruwa mai sanyi.......
Ta gama d'amke cikinta,sannan tayi mata sallama........
Godiya tayi ta tafi da alk'awarin nan da Sati d'aya zata dawo......
***********
Kwance take tana ta faman bacci wanda bata san lokacin da ya d'auketaba,tayi nisa cikin baccinta.......
**************
Tun daga nesa ta hango ingarman dokin wanda akewa lak'ani da KILI ( wato mai fari biyar),kansa mutum ne zaune,cikin farare tas en tufafi......
Matsowa yaci gaba da yi,wanda har sai da yazo daf da ita sannan ne ta iya gane mahayin murmushi d'auke kan fuskansa......
Sai da ya zo gabanta,sannan yaja linzamin dokin ya tsaya.....
Har lokacin tana tsaye fuskanta cike da mamakin ganinsa......
Mutumin daya ce bazai sake dawowaba yau shi ne a gabanta yau.......
Saukowa yayi cikin isa,ya tako har zuwa gabanta....
Cikin wani irin voice da bata tab'a jin irinsa ba tunda take a gaba d'aya tsawon rayuwanta,ta tsinkayo shi yana fad'in
_''Amincin Allah yaci gaba da tabbata agareki''........_
Kasa amsawa tayi saboda tsananin mamaki da yak'i barinta har yanzun......
Hannunta ya kama cikin wani irin salo,ya jata jikinsa.....
_''Haba wifey,ni en ne baki ganeba ko kuwa na zame miki wata sabuwar halitta?''......_
Kuka ne ya kufce mata,jikinta banda rawa babu abunda yake,tsabar tsoro ta kasa magana,sai hawaye dake ta ambaliya a fuskanta.....
Duk k'ok'arinsa da son ganin ta bud'e baki tayi magana abun ya gagara......
Janta yayi ya had'a jikinsu guri d'aya,ganin yanda jikinta yake ta faman b'ari......
Maimakon a samu sauk'i saima k'aruwa da aka samu.........
Kukantane ya sake tsananta,kan dole ya raba jikinta da nasa....
Fuskanta ya kama ya d'ago,tsura mata ido yayi
_''Shin bakiyi farin ciki da ganinaba ne wifey?''...._
Kai ta girgiza masa,alaman
A'a
_''Baby maganafa zakiyi,bana son wannan nodding en''......_
Cikin hanzari ta bud'e baki da niyyan magana
_''A'a,ina mamakin yanda ka dawo gareni ne,alokacin da bantab'a tsammaniba''........_
Fuskanta ya shiga goge mata,yana murmushin jin dad'i......
**********
k'afafuwanta tamkar wacce taje sharan gona,sunyi futu² kamar basu tab'a ganin mai ba.......
Sai murna take na samun gidan aikin da tayi,haka ta sauka a napep en da ya sauketa bakin titi.....
Ta sake ninkawa ta shiga cikin unguwan,a k'ofar gida taja burki,ganin k'ofan a rufe,ta shiga huci.....
Bugun k'ofa ta shiga yi,jin shiru ba a bud'eba,ta shiga dukanta da k'arfi tamkar zata karya.......
************
Cikin baccinta mai dad'i mai cike da mafarkin da a kullum shi ne birinta....
Ta tsinkayo bugun k'ofan da tamkar a tsakiyan kanta ake......
Bud'e idonta tayi,cikin sauri ta mik'e ta nufi k'ofa,har tana had'awa da d'an gudu,wanda saura kad'an ta fad'i,amma haka ta daure ta tunkari k'ofan..........
*K*okawa ta shiga yi da k'ofan,wanda da kyar ta samu ta bud'e......
K'ofan na gama bud'ewa idanuwanta sukayi arba da MA'U tsaye,idanunta sunyi jajur dasu kamar garwashi.....
Kamar ance ta kalli k'afarta,ai kuwa nan ta hangi k'afar tayi busu²,dan k'ura da daud'a......
Duk k'ok'arinta na ganin ta kaucewa yin dariya abun ya faskara....
Nan ta fara tuntsirar dariya,kamar kwancen mahaukata.......
MA'U dake tsaye tana jiran a bud'e mata k'ofa,taga ta tsaya tana mata dariya.....
Tsaiwa tayi ta dafe saman gini,tana kallonta,sai dariya take,kamar sabuwar kamu.......
Tsabar mugunta irinta KHUBRA har dafe gefen cikinta take,ita bata matsa daga kan hanya,ta bawa MA'U guri ta wuceba,ita kuma bata tsaida dariyan taba......
Kallonta MA'U taci gaba dayi,ganin abun nata ba na k'are bane,kuma ta rasa me KHUBRAN kewa wannan dariyan a tare da ita,abun ya soma bata haushi....
Ga haushin ta rufe mata k'ofa,sannan ta zo tana mata dariyar rainin wayo.......
Hankad'ata tayi cikin soron,ta shigo tare da maida k'ofa ta rufe.....
Wani gigitaccen mari MA'U ta aikawa KHUBRA da shi,wanda ta jishi,babu shiri kuwa ta had'iye dariyarta.......
Gashin kanta ta dank'a ta jata zuwa cikin gidan,sai zage² take kamar y'ar maguzawa......
Babu zato bare tsammani MA'U ta shiga jibgar KHUBRA kamar ta samu jaka ko ince kayan wanki.....
Tun tana dukanta KHUBRA na iya yin ihun neman ceto har ta koma muryanta ma bata iya fita saboda laushi da jikinta yayi.....
Sai da tayi mata dukan sa'a,sannan ta yasar da ita a gurin ta shige d'aki,ba tare da ta furta ko 'A' ba,zuciyarta kamar zata fito waje saboda haushi.....
KHUBRA dake yashe a k'asa babu,abunda ake iya ji na daga sautin muryanta,banda numfashinta dake fita da sauri²......
Ta jima kwance a gurin,wanda ta gagara koda motsin kirki......
***********
Tun tahowar MA'U da KHUBRA birni,hankalin ABBAN KHUBRA yak'i kwanciya.....
Kullum cikin tambayar LADIYO yake yaushe MA'U zata dawo da ita.....
Amsar dai guda d'aya ce kullum,dazaran lokacin da suka d'auka alk'awari yayi zata dawo da ita.....
Shi kam kullum yana jinta ne,don kuwa ya fuskanci idon MA'U bud'e yake da son nera,tsoron sa d'aya kada su cutar masa da ita.....
Abu sai dad'a gaba yake,LADIYO ta shiga tashin hankali ganin yadda malam en yake neman d'aga mata hankali,har bata so ya shigo ya tarar da ita zaune,yanzun zai dasa mata maganar y'ar tasa mai kama da aljanu.....
Yau ma zaune take cikin y'ar rumfar karan dake bakin d'akin nata,wanda daga nan kana iya hango k'ofar shigowa gidan.....
Zafi duk ya addabeta,daga ita sai d'aurin zani iya k'irjinta.....
Malam buba ya kawo kai zai shigo cikin gidan,da sallama a bakinsa....
Ko amsawa bata yiba ta mik'e cikin hanzari zata bar gurin.....
''Dakata LADIYO,na fuskanci kwanan nan nema kike ki mayar dani wani sha ka tafi''.....
''Ko dai yau ki fad'amin inda y'ata take ko kuma aradu ina mai kai k'ararki gurin MAI GARI''.......
Ido waje LADIYO ta juyo,nan ta shiga bashi hak'uri.....
Saboda LADIYO irin matan nan ne masu d'an karen tsoro,ammafa akwai tsokana....
Idan akwai abunda LADIYO take tsoro a duniyarta kuwa baya wuce MAI GARI ko a ambaci mai bak'in kaya wato ('DAN SANDA).....
Har k'asa ta zube tana masa magiya,akan zata kira MA'U ta dawo da KHUBRA idan ma bata sametaba zata je da kanta ta dawo da ita har gida ba sai maganar ta jega HUKUMA ba.....
Girgiza kai MALAM BUBA yayi,ya juya ya nufi d'akinsa
''Da dai yafi miki kwanciyar hankali''......
Yana fad'a ya k'arasa shigewa ciki.....
LADIYO dake durk'ushe a inda MALAM BUBA ya barta ta d'ago tana dafe k'irji....
Ganin babu MALAM en a gurin tayi wuf ta fad'a d'aki....
Nan ta shiga raba ido kamar shege a rabon gado (yo dama me zai kawo shi tunda yasan bashi da ko allura)?.....
Ita kad'ai ta shiga magana da kanta
_''Ya zama dole nayi aron waya na kira MA'U ta dawo da wannan shegiyar yarinyar mai kamar aljana,tun kafin kashina ya bushe''....._
Ko gama tunanin batayi ba ta zara mayafinta ko riga babu ajikinta,tayi waje......
Bata zame ko inaba sai gidan k'awarta mai suna TABAWA.....
******
TABAWA irin matan nan ne y'an duniya,wad'anda suke da bud'ad'd'en ido.....
Da shigarta ta tarar da TABAWA ta cokalo d'an kwalinta sai zabgawa mijinta rashin mutunci take....
Shi kuwa bawan Allah kansa a k'asa kamar wanda ke gaban uwarsa haka jikinsa sai b'ari yake.....
Bata k'arasa shigowa ba ta tsaya daga bakin k'ofa,tana kallon wannan abun aljabi.....
''Dillah can banza kawai,zaka bani ko kuwa sai na cajeka?
Katabbata idan har na laluba na tarar da kud'i a jikinka,wallahi yau kam babu kai babu cin abinci a gidan nan''.....
Ta fad'a tana hak'ik'an cewa....
Rantsuwa ya shiga yi mata,sai kace d'a da uwa,amma hakan bai sa TABAWA ta yarda ba.....
Rigarsa ta kama ta cukuikuyo shi,ta shiga lalube aljihunansa kaf,sai da ta tabbatar da abunda ya fad'a sannan ta kyaleshi tana fad'in
''Allah ya cece ka''.....
''Amma ba kyaleka nayi ba wallahi,zan ranta maka kud'in cefanen yau,kana samu kayi hanzarin biyana idan kuma ba hakaba,zaka had'u da tijarar da tafi wannan''......
Ita kam LADIYO na nan tsaye tamkar an dasa bishiya,ta lula cikin tunani,har bata san lokacin da mijin k'awar tata ya fita ba......
Dogon ajiyan zuciya tayi,kafin jiki a salub'e ta afko gidan ko sallama babu......
Binta kawai TABAWA tayi da ido
A ranta kuma tana fad'in ko lafiya?
*_~.
*T*ana nan kwance in da MA'U ta yasar da ita,kamar matacciya,idan ba wai mutum ya kula da yanda chest nata dake shibring ba,za a iya cewa ta jima da mutuwa....
**********
Cikin kwanciyar hankali MA'U tayi kwance kan gadonta,ko kad'an batayi nadamar abunda ta aikataba,bare ta duba taga halin da y'ar mutane ke ciki ba....
Idonta tar kan selling tana nazari kan wannan gidan aiki da ta samu....
Ita kam a nata ganin,da zaran ta samu wani aikin da yafi wannan maik'o zatayi watsi da wannan....
Ko dama ace ba a garin kuwa zatayi aiki ba,ita meye damuwarta,tunda ba ita ta haifeta ba.....
Burinta bai wuce a kawo mata masu gidan rana......
************
Wani uban tsaki TABAWA tayi lokacin da ta kalli LADIYO,da alama tunani take....
Da k'afa ta kai mata hauri...
A firgice LADIYON ta d'ago tana k'ok'arin mai da kallabinta da yake shirin fad'owa....
Jajayen hak'oranta ta bud'e wanda babu abunda ke fitowa daga bakin nata banda wani irin azababben wari,ga su duk sun dafe saboda tsabagen daud'a.....
Kallonta TABAWA tayi tana fad'in
''LADIYO ince dai ko lapia kike irin wannan dogon nazari haka?''.....
''Ke dai bari TABAWA ina cikin tashin hankali wollahi''....
Fuskanta da tsananin mamaki take kallon LADIYON da take koro mata jawabin abunda ya had'o ta da MALAM BUBA akan yarsa......
Dariyar mugunta TABAWA ta hau yi,tana tafe hannunta....
Sai da tayi mai isarta kafin ta saurara,tana k'arema LADIYO kallo,tana tab'e baki....
''Uhmmmm!LADIYO kenan,ni ai a ganina ke kika so,da har kika tsaya MALAM BUBA yake zuba miki irin wannan rashin mutunci,da d'iban albarka haka
Ni baki ganniba,washar da ni,tunda mu ba haihuwa za muyiba,ai gara muyi abunda muke so,kafin dare d'aya suzo mana da maganar k'arin aure''.....
Baki bud'e LADIYO ke kallon TABAWA,da ta tak'ark'are tana koro mata datar......
''Kinga yanzu ba zama ne ya kamacemu ba,abunda kawai za ayi,ki biyo sahuna,mu d'ora daga inda aka tsaya....
Har zamu tsaya ne muna kallonsu,mu tashi a tutar babu,shi kenan munyi ba wan ba k'anin?''.....
Karatun na d'an kama......
"Ina kuma zamu nufa yanzun?"
LADIYO tayi tambayar.....
"Kinga yanzu ba lokacin tsaiwa dogon jawabi bane,idan kina da buk'atar mafita kawai ki taso,bana son dogon sharhi".....
Jiki na b'ari ta mik'e tabi TABAWA a baya,kamar
RAK'UMI DA AKALA......
************
Rashin madafa shi yasa KHUBRA dake kwance,lallab'awa da jan ciki,ta d'ebi ruwa a buta......
Da yake lokacin zafine,ruwan da zafinsa,rana ta gama gasashi....
Haka ta lallab'a ta shige,wanka tayi ta d'aura alwala ko za taji dama²....
Da kyar ta iya mik'ewa tana bin bangon toilet en,ta fito daga ciki,jikinta duk ya mata nauyi....
Haka ta ci gaba da takowa tana d'aga k'afa da kyar,har ta samu ta fito......
'Daki ta shiga da niyyan ta samu ta lallab'a tayi sallah,dan kuwa lokacin har an idar da sallar maghreb......
Ko da ta shiga d'aki da sunan za tayi sallaah......
'Dagowa MA'U tayi,tana K'are mata kallo.....
Cikin tsawa ta hau fad'an da tun d'azun batayiba.....
************
Can cikin wani surk'uk'in hanya suka shiga bi jikin LADIYO sai kyarma yake saboda tsoron hanyan da ko a mafarki bata tab'a tsintar kanta a cikiba....
Bin bayan TABAWA kad'ai take,wacce ita kam ko d'ar bata jin tsoron komai,haka take watsa k'afafuwanta cikin jejin.....
Haka har suka tsinci kansu gaban wata y'ar bukka dake saman wani sand dune hill....
TABAWA da yake tasan kan hanyar yanda ake hawa,haka ta shiga raba k'afafuwanta,har ta ida hawa.....
LADIYO kam ta kasa hawa,sai ta hau sai ta dawo k'asa,jikinta duk ta kurjeshi garin k'ok'arin hawa....
Daga saman dutsen TABAWA ta hango LADIYO yanda take ta faman kaiwa da komawa dariya ta tuntsire da shi,nan ta shiga kokawar komawa k'asa.....
Kokawa suka shiga yi na hawa,in da TABAWA ta rik'e hannun LADIYO kamar wasu k'ananan yara,tana koya mata yanda zata hau,har dai sukayi nasarar hawa saman dutsen.....
Guri suka samu suka zauna kan wasu fatu dake shimfid'e uwa tabarma,suna jiran zuwan mai gurin.....
.
*B*ayyanarsa kawai LADIYO ta gani wanda ba k'aramin tsorone ya cika mata zuciya ba....
Jikinta sai kyarma yake,duk ta firgita,sai neman b'oyewa da take a bayan TABAWA.....
Dariyar da ya kece da ita,wadda ta haddasawa d'an k'aramin forest en amsawa,mai kama da kukan jaki....
Ita ta sake rud'a LADIYO wadda a sanadin hakan har fitsari ta soma,ta mak'alk'ale TABAWA.....
Wata razananniyar tsawa ya mata yana fad'in
''Shiga hankalinki la'ananniya,b'atacciya,duk wanda yazo nan ya tabbata wakilin shaid'an,bama wa muminai aiki....
Idan kin san da sofanen imani a tare da ke maza ki b'ace anan tun kafin yaran shaid'anu su sauke fushinsu akanku''.....
Ya k'arashe maganar yana zare jaajayen idanunsa,masu kama da garwashi......
''A tafiyarmu babu tsoro,bamu san mene shiba bare muyi shi,idan har kin kiyaye wad'annan sharud'a,muna maraba dake yar jakar uba''.....
Ya sake kecewa da wata dariyar da ta fi ta farko....
Ita kam LADIYO yanda yake magana da dariyarsa shi yafi komai tayar mata da hankali.....
Harara TABAWA ta aika mata wadda tasa ta shiga hankalinta,ta zauna sosai,amma da zaka ce mata kyattttttt to kuwa zaka nemeta ka rasa....
Kafin su kaiga yin magana ya tare su yana fad'in
''Bana buk'atar kuce wani abu,nasan abunda ke tafe daku''.....
KEEE ya nuna LADIYO,kafin ya d'ora daga in da ya tsaya....
''Akan mijinki ne da kuma y'ar kishiyarki wacce mahaifiyarta ta rasu''.....
''Me kike so a yi wa mijin naki?
Kina so a kasheshi ne,ko kuwa a rabashi da y'arsa kamar yanda ya rabu da iyayensa, kar ya sake tambayarki in da take,ko kuwa kina so ya koma jin tsoronki tamkar ke kika haife shi?''...
Gyad'a kai tayi cikin farin cikin samun mafita,sannan ta shiga yi masa bayanin abunda take so ayi musu akan MALAM BUBA.....
Haka bokan nasu ya juya yana mai kecewa da dariya ya shige bukkar tasa......
Wasu uban layu ya fiddo ya mik'a mata...
Kinga wannan ya nuna mata wata k'arama daga ciki,zaki sata a cikin matashin kanki da kike bacci (pillow)....
Wad'annan kuma ki samu dai² bakin k'ofar d'akinsa ki hak'a rami ki binne su,idan kikayi haka kuma aikinki ya kammala,sai ki jira kiga mai zai faru''......
Ku tashi ku bani guri.......
LADIYO da shishshigi sai cewa tayi
''MALAM mene ne kud'in aikin nawa?''.....
Tsawa ya watsa mata yana fad'in
''Kaji y'ar jakar uba,mu nan ba a tab'a biyanmu idan mukayi aiki sai bayan aikinmu ya kammala.....
Maza ku bar nan,kada ku sake ku waiwayo''.....
Cikin sauri ko wacce ta suri takalminta suka kamo hanyar barin jejin,ko da wasa babu wacce ta juya,har suka fito daga ciki.....
**********
A fusace MA'U ta mik'e tana shirin dank'o KHUBRA da tayi tsaye....
Ba shiri tayi waje har tana neman fad'uwa du da dama jikintan ba wani k'wari ne da shiba.....
''Da kin tsaya ai y'ar jakar uba,yau da na nuna miki k'aryarki,dan yau na lahira sai ya fiki jin dad'i''.....
Ta fad'a tana huci,sai jijjiga jiki take,uwa wacce take shirin fad'a da sa'anta....
Komawa tsakar gidan tayi,nan ta shimfid'a d'an kwalinta,tayi sallah,ta ci gaba da jiran gawon shanu.....
Sai da ta raba dare a zaune a gurin ba tare da ta motsa ba....
Lokacin da ta tabbatar da LADIYO tayi nisa a cikin baccinta,ta mik'e ta lallab'a....
Gurin kayanta ta dosa d'an ragowar k'uli²n da ABBANTA ya bata shi ta d'auko ta ci,ta sake d'aurewa ta mayar...
Ta d'ebi ruwa ta sha,tayi godiya ga mahaliccinta....
Har ta gama abunda za tayi a d'akin MA'U bata san ta shiga ba.....
Sake komawa ta sake yi ta d'auko zani a cikin kayanta ta fito tare da jaa mata k'ofan....
A inda tayi sallah ta shimfid'a,hijab en jikinta kuma ta cire shi ta lullub'e jikinta....
Takurewa tayi guri d'aya saboda rashin girman hijab en ba zai kai mata ta rufe jikinta gaba d'ayaba.....
A wannan daren sai dai da yake an ce bacci b'arawo ne,amma da KHUBRA zata iya cewa ba zata iya bacciba...
Duk da baccin nata ya kasance rabi² ne....
Sai bayan da tayi sallan Asubah sannan wani nannauyan bacci yayi gaba da ita.......
************
Shigowar MALAM BUBA gida yana ta kwad'a sallama,yaji shiru ba'a amsa ba....
Nan ya shiga kiran LADIYO,jin shirun yayi yawa,ya shiga nemanta lungu da sak'o na gidan,amma ko mai kama da ita bai ganiba bare kuma itan....
Girgiza kai yayi ransa a b'ace yake fad'in
''Duk inda kikaje zaki dawo ki tarar da ni,kuma xa kiyi bayani,wannan iskancin na gaji da shi''.....
Yana gama bambamin fad'an nasa yayi waje......
***********
Kamar yadda ya musu bayani,direct gidan LADIYO suka nufa....
Gidan babu kowa,kasancewarsa haka kuwa da shigowarsu,suka hau dube²,bayan sun tabbatar babu mutum ciki,suka hau aiwatar da nufinsu......
Sai da TABAWA ta tabbatar sun gama aikata komai kamar yadda aka fad'a musu tukun,ta sake d'orata akan hanyar b'ata,wacce su a ganinsu ita ce dai²......
Sannan tayiwa LADIYO sallama,ta nufi hanyar nata gidan,babu fargabar tayi dare bata dawoba,za ta tarar da fad'a......
*********
Sai da gari ya gama wayewa sannan MA'U ta fito daga d'aki....
Kamar kullum cikin al'adunta,tana hamma had'e da mik'a.....
Mutum ta gani kwance,sai alokacin ta tuna abunda ya faru......
Batayi magana ba ta wuce bakin randa,sai da ta cika bokiti da ruwa,ta d'auko shi da k'yaar....
A dai² kan KHUBRA ta d'aga shi ta juye mata shi a kanta....
A firgice KHUBRA ta mik'e tana dube².........
.
*T*saye akanta taga MA'U da k'aton bocket,tana ta faman aiko mata da uwar harara....
Mik'ewa tayi tana kama kayan tana matsewa...
Sunkuyawa tayi ta kamo zanin da ta shimfid'a...
Ko kafin ta kai ga d'aukowa MA'U dake tsaye bayanta ta d'irka mata hannunta mai kamar na maza a bayanta....
Lank'washewa tayi a gurin saboda azabar dukan da ya shigeta,ko bata fad'a ba....
Kuka ne ya kufce mata,ta shiga rerawa babu saurarawa...
.
Kamar mutuniyar arziki haka MA'U ta juya,a bakin randan ta ajiye bocket en ta sake dawowa ta wuce KHUBRA dake faman kuka uwa ranta zai fita...
Sai da ta kalleta kafin ta wuce cikin d'akin,ta d'an jima aciki sannan ta fito...
Hannunta d'aya a goye a bayanta,ta nufo inda KHUBRA take sunkuye ta saka fuskanta a tsakanin laps nata...
KHUBRA da bata san meke faruwa ba bare tasan abunda zai faru nan gaba,sai jin duka tayi ta ko ina yana ratsa jikinta....
K'ok'arin karewa ta shiga yi,amma hakan ya gagara...
Gaba d'aya MA'U ta hanata motsi,ta kama ta nad'eta acikin hijab enta....
K'ok'arin guduwa ta shiga yi,ga MA'U bata daina dukanta ba,ganin azaban yayi mata yawa yasa ta dage ta ingije MA'U ai kuwa nan sai ga MA'U a k'asa timmm....
Da gudu ta nufi hanyan fita daga gidan....
''Kada ki kuskura ki fita daga gidan nan,dan wallahi na lahira sai yafi ki jin dad'i yau,yarinya zaki gane ni kika tura na fad'i''...
Tana daga kwance a inda KHUBRA ta tura ta take koro bayani...
Da k'yar ta mik'e daga gurin tana d'ingishi,haka ta koma d'aki tana duba jikinta...
Hannayenta ta k'urje su,ga d'an yatsanta na k'afa da yake mata rad'ad'i....
MENTHOLATOM ta hau gogawa gurin...
Azabar da yake mata ce ta sata bari babu shiri...
Haka ta kafawa d'an yatsan nata ido,ganin ya soma kumbura ta tabbatar ta samu targad'e...
Dafe kai tayi tana jin rad'ad'in da yatsan ke mata har tsakiyar kanta...
Lallai wannan yarinya koi ja'ira,amma babu komai ta ciji lips enta,
''Zanyi maganinki''
Ta furta ciki².....
*************
Haka ta shige d'aki ko tunanin sallah batayi ba,tana shiga kuwa ta turo k'ofar d'akin nata...
Kwanciyarta tayi take kuwa bacci yayi awon gaba da ita....
.
K'arfe 9:15pm MALAM BUBA ya nufo gidan nasa,da tunanin ko LADIYO ta ga dama ta dawo?
Tun da ya tunkaro gidan gabansa ke faman fad'uwa...
Bai kawo komai a ransa ba,haka ya shigo gidan,k'ofar dake jingine ya d'aga ya karata a saitin k'ofan...
Juyawa yayi ya shiga da sallamarsa...
Da yake yasan ma koda tana nan ba amsawa za tayi ba,hakan ya sashi wucewa d'akinsa.....
Jiri ne ya fara neman kada shi,da sauri ya dafa wall en d'akin,ya daddafa ya shiga ciki,tun da ya shiga d'akin bai sake sanin inda kansa yake ba......
***********
Lek'owa tayi tana daga soron,jin shiru da tayi,shi ya bata tabbacin bata gurin...
Da sand'a ta shigo ta lallab'a ta kwashe kayanta daga gurin....
Kan wall en toilet en gidan ta kai ta shanya,ta dawo ta nemi guri ta zauna tana jiran gawon shanu,nan ta sake lulawa duniyar tunani...
'Daga labule taga anyi,ai kuwa karaf akan idonta...
zaraf tayi ta mik'e tsaye,tana rab'ewa gefe....
Harara MA'U ta aika mata,ta wuce ta shiga toilet,kamar ko wane lokaci,kafin cikar mintuna biyar har ta fito....
Kallon KHUBRA tayi kafin cikin wata irin murya ta hau fad'in
''Uban meye kike jira a nan?
Ki zo ki wuce ki samo ruwa sannan ki tabbata kin sharemin gidan nan''...
.
Sum² ta zo ta wuce,haka ta d'auki k'aton bocket en da MA'U ta ajiye,ta jaa silifanta tayi waje...
Lokacin da ta fita rasa ina zata nufa tayi,coz tun da tazo yau ne rana ta farko da ta fara fitowa...
Ta jima tsaye tana tunanin in da ya kamata ta nufa....
Tambaya ta yanke shawaran tayi,amma wa zata tambaya? unguwan shiru,babu kuma masu wucewa....
Haka tayi ta tsaiwa a gurin....
Gajiya tayi da tsaiwan,zuwa wani lokaci har ra fara gumi,haka kan dole tabi ra'ayin zuciyanta..
Gidan dake gefensu ta nufa,sallama tayi ta shiga...
Babu kowa a tsakar gidan,sai wata mata da ta gani tana fitowa daga d'aki...
Da d'an murmushi akan fuskanta ta amsa mata,tana fad'in
''Maraba,k'araso daga ciki''..
Murmushin itama KHUBRAN tayi tana fad'in
''Laa da kin barni ma daga nan''...
Gaidata KHUBRA tayi,kafin ta shiga tambayanta inda zata sami ruwa....
''Laaa kinga ai ba nisa ma,kina fita akwai gida da yake kallon nan,suna da rijiya''-....
Godiya tayiwa matar ta kama hanya ta fice,matar na binta da kallo....
Haka ta shiga gidan,suka gaisa da matar mai kirki,sai jan KHUBRA take da fira,ita kam ta kasa sakin jiki da ita,haka taita kaiwa da kawowa,har ta kammala d'iban ruwan.....
Bayan ta kammala haka ta duk'ufa kan shara,zuwa wanke²...
.
Lokacin da ta gama tana murna za ta huta,har ta nemi guri ta zauna,MA'U ta lek'o tana fad'in
''To hakima ba zama za kiyi ba,maza duba wancan d'akin akwai kwanuka maza ki tattarosu ki wanke su,idan kin gama kimin magana....
Haka ta shiga tattaro kayan wasuma har sun fara fungi,wani kuwa cikinsa yayi bak'i kamar an shafa kwalta...
da k'yar ta gama wankewa,ko da ta gama haka ta kwashi k'afafunta ta je k'ofar d'akin
''Na gama'' abunda ta iya fad'a kenan...
''To jirani'' MA'U dake d'aki ta fad'a....
Fitowa tayi da uban kaya a hannunta,haka ta watso mata su,ta sake komawa ta d'ebo wasu...
''Ga shinan maza ki tabbatar kin wanke su sun fita tas,dan idanma basu fitaba,zaki sake ne''...
Juyawa tayi tana k'arewa kayan kallo,gasu da uban yawa,ga kuma daud'a,wanda ko kayan d'an goye ba zai nuna musu daud'aba....
Har ta kai bakin k'ofa KHUBRA ta furta ''Sabulun wankin''....
Shigewarta tayi,sai da ta gama b'ata lokaci,sannan ta cillo mata...
Haka tayita gurzarsu,babu iyaka,har dai ta samu ta kammala,lokacin ana kiran sallan ISHAA.....
Ranar gaba d'aya KHUBRA haka ta yini aiki daga wannan sai wancan...
Haka ta tashi jikinta sai kyarma yake,ga ciwo da yake mata,ga tsananin yunwa,ga uban ciwo da kanta yake tamkar zai rabe...
Tashi tayi da k'yar ta tattara kayan da tayi amfani dasu,ta shiga d'akin shirgin nan ta gyara shi,duk da tana cikin wannan halin haka ta share shi...
Ruwa ta d'iba ta shiga ta wanke jikinta,sannan ta d'auro alwala,ta fara jera sallolin da ake binta bashi,dan kuwa MA'U hanata tayi ta motsa ko nan da can...
Tana yi tana ZUBAR HAWAYE,tana rok'on Allah gafara da kuma neman d'auki daga gare shi.....
Ta jima acikin sujudah tana rok'on Allah,kafin ta d'ago tayi tahiya,ta sallame....
Da k'yar ta iya motsawa daga gurin,ta lallab'a ta fito daga d'akin...
'Dakin MA'U ta shiga sai tare kanta take da hannu wanda ke mata barazanar fashewa...
''Dan Allah BABA ki taimakamin da abunda zan ci,wallahi ina tsananin jin yunwa,kuma kaina ciwo yakemun''
Ta fad'a kamar zata fad'i....
''Ke dallah dakata,karki fad'o kaina,dan kina jin yunwa shi ne me?
Malalaciyar kawai,d'an wannan aikin da kikayi kinzo kina min raki''.....
Haka MA'U ta koroto ba tare da ta tausaya mataba...
Kuka ta fashe da ta nemi guri abakin d'akin ta shiga rerawa...
Ashar en da MA'U ta k'unduma ne ya sata tsagaitawa...
Kamar daga sama ta ga MA'U da jakar kayanta a hannu,cillo mata tayi tana fad'in
''Idan zaki iya tafiya bismillah,abincine banga dama ba,kina iya ki nema da k'arfinki sai ki ci......
0 comments:
Post a Comment