MAFARKIN ABDUL Part 1
.
Zaune take gaban fannin kimiyya (Faculté des Sciences) ta jami'ar Abdoul moumouni (Université Abdoul Moumouni Dioffo) da ke Niamey a jamhoriyar Nijar. Sun fito lectures kenan kasancewarsa ɗaliba yar aji uku a fannin tsirrai (plant biology), Yarinya ce 'yar kimanin shekaru ashirin a duniya, tana da matsakaici tsawo, Albarkan mazaunen da ke gareta da kumatunta yasa akan mata kallon mai jiki kasancewar ta ma' aboki yar sa hijab. Kalarta mai tsada ne, baka ce ba wuluk ba ma'abociyar fararen idanu kalar madara. Wasu na mata kallon mai girman kai yayin da dayawa kan so ta saboda hakurin ta da yalwataccen fara'an da ake samu a fuskanta. A zahirance kallon wayarta takeyi fuskarta ba yabo ba fallasa, amma tunaninta ya tafi chan wani duniyar. Ko a aji yau ba zata ce ga abinda akayi musu ba. Kiran da ya shigo wayarta yasa ta sakin ajiyar zuciyar da ya sa kawarta da ke zaune gefenta kallonta. "Sweetyna kana lafiya, duk hankalina ya gaza kwanciya, ina ka shige" Ta faɗi a marairaice kamar zatayi kuka. "barci na tashi ya kike ya makaranta?" "Alhamdulillah, ka ci abinci" Ta sake tambaya cikin yanayin kula "Bana jin cin abincin ne, ga de ni nan Haj na min favorite ɗina" Ya faɗi yana dariya. Itama dariyan tayi. Haka suka cigaba da hira cike shaukin juna. Har wajen mintuna ashirin sannan suka rabu cike da kewan juna.
.
"Halima fisabillillahi bazakiyi ma kanki faɗa ba, wallahi Hammad ba aurenki zeyi ba. Ki natsu ki roki Allah ya baki nagari, kada so ya rufe miki ido" faɗin kawarta da ke zaune a gefenta. "Faɗima wallahi muna son juna da Hammad, kun kasa fahimtarmu ne, kuyi mana fatan alkhairi kawai" "ina guje miki halin mazan zamanin nan ne, basu da alkawari musamman in son da mace ke musu ya zarce misali, duk abin sa kar ki yarda ayi gwajin takalmi da ke" Faɗima ta ce cikin halin ko in kula. "in ma gwajin riga zai yi ba komai bane mu dai muna son junanmu kuma za muyi aure" Ta faɗi a kufule duk ranta ya ɓaci. Fuuuu ta tashi kamar mai shirin tashi sama.
.
Safiyyah Ummu Abdoul Da kyar ta iya isa gidan baffanta da take zama wanda ke bayan Homeland Hotel, da ke Off Ave du General de Gaulle, a wahalance ta yi sallama, ta iske matar baffanta haj Mas'uda a zaune tana kallon tashar Sunna TV. "Momma barka da gida" Ta faɗi tana mai samun wajen zama a kusa da kafanta. Kallo ɗaya tayi ma ta ta fahimci bata cikin natsuwa. "Halimatus sa'adiya taje makah da madina ta sha miya mai daɗi har da kadangare soyayye" Ta shiga rera mata tana tafi. Dariya Halima ta farayi yayinda ranta ya fara sanyi. "faɗa min waya taɓa ki" Ta tambayeta tana mai tsareta da idanu.
.
"Faɗima ce na rasa mai na tsare mata, tsakani da Allah nake zaune da ita amma sai ta yi ta min bakin ciki da hassada" Ta faɗa ido cike da kwalla, zuciyar ta na mai jin an ci amanar kauna. "tohhhh fa, me ta yi miki, kwata kwata ba tayi kalan mai wannan halin ba" Ta amsa mata fuska cike da alhini. "Momma a 'yan kwanakin nan sai tayi ta ce min in rabu da Hammad ba aure na zaiyi ba, ki duba fa ko haushin yafi mijinta kyau da kuɗi take yi ko mai yasa ni ban sani ba" Ta karasa tana kukan da yafi jini ciwo don a duniya bata da kawar da take kauna sama da Faɗima duk da kasancewarta kanwa a wajen kishiyar uwarta. "Na rasa me ke damun mutanen zamanin nan. Sam bama son gyara, da ga an nuna mana kuskurenmu maimakon mu gyara sai mu ce ana mana bakin ciki ko hassada. Mai sonka ke gyara maka, nasan son da Faɗima ke miki ba za ta bari ki cutu ba. Hammad dai iyayen ki ba sonsa suke ba, asali ma cewa su ka yi ki rabu da shi, ina mai shawartanki da ki roki zaɓi Allah in Hammad ne alkhairi Allah ya tabbatar in ko ba shi bane Allah ya kawo wanda ya fi shi a komai" "Momma ko ba Alkhairi bane Allah ya sa mu mallaki juna, ina sonsa da yawa Momma" Ta katse ta gudun yan aameen su amsa ma addu'ar ta,. "Halima ko dai Hammad ya sanki a ɗiya mace ne, in ba haka ba wannan irin nacin son da kike masa ya zarce hankali, dama mamanki ta faɗi na karyata gashi kina neman gaskata maganarsu". Ba ta jira amsarta ta ba barta zaune tana gunjin kuka. Kiran sallar la'asar da akayi ne ya tashe ta daga barcin wahalan da ya kwashe ta a wajen. Tashi tayi ta sallace la'asar da azahar ɗin da ake bin ta bashi. Tare da Momma da babbar yar momma Amina da suke kira Amna suka kammala girkin dare. Suka shirya, karfe shida duk suka haɗu gaba ɗaya suka ci abincin, don ka'ida ne a gidan cin abincin dare karfe shida don ya zazzage kafin ayi barci, sannan abincin safe baya wuce karfe takwas ɗin safe duk don samun ingantacciyar lafiya. Bayan kammala sallah isha'i ta koma ɗaki da nufin barci.
.
Shafin Facebook ta shiga don duba abubuwan da ke kai, har zata sauka sai sakon gayyata ya shigo ta buɗe sai taga "ABDOULLAH ABOUBAKAR (ABDOUL ABOU)" Sai da ta duba shafinsa ganin bai bada wasu bayanansa masu mahimmanci ba iyaka dai taga shima ɗan Zindar ne. Har zata goge sai ta tuna da tobashinta Abdoul Abou sai tayi tunanin Shine. Tsaki ta ja kafin ta amince. Haka ta cigaba da shige shigenta tana hira da kawarta da suka haɗu a Facebook ɗin Tiddar Azzoubir. Da ta gama ta kalli agogo ganin goma saura na dare ta sa ma ranta tabbas Hammad ya gama kallon kwallo. Waya ta ɗauka ta kira shi sai da ya kusan tsinkewa sannan ya ɗaga. Yanayin yanda ya amsa mata yasa ta tambayeshi ko ya fara barci ne "ke dai bari hajiyata, wallahi na ɗanyi aron hannu ne kinsan gajiya yake sawa" Ya faɗi cikin halin ko in kula Bakin ciki ya cikata amma haka nan ta ɗaure ba tare da nuna ta damu ba tace "sweetyna yaushe zaka daina zuwa rage ruwan nan ne, lokaci yayi da ya kamata mu san mai muke ciki" "anya in munyi auren nan baza'a samu matsala ba, kishin ki na neman kaiki ga zargi na, gaskiya da sake toh" Ya katse ta a fusace. Nan take ta fara bashi hakuri da kalaman soyayya da tasan yafi so. Haka suka shirya suka cigaba da soyayya har sha ɗaya da rabi sannan sukayi sallama suna masu begen junansu .
.
Juyi ta ke yi hannunta rungume da filo Mafarki take amma na ido biyu (day dreaming) ga ta da Hammad ɗin ta sunyi aure. Auno su take irin soyayyar da zasu kwasa, kamar an mintsile ta tashi tayi ta lalubo kananan kayan da ta siya don kaiwa gidan aurenta. Murmushi ta saki gani take an ɗaura aurensu da Hammad an gama. "Toh in ya cigaba da Aron hannu fa?" wannan sashi na zuciyar mutum da ba'a taɓa yaudara ya tunatar da ita, bata ɓata lokaci ba tayi fatali dashi kana ta faɗin "ai na san zai daina da munyi aure". Kwanciya tayi don tayi barci amma ko gezau barcin ya gagare ta, sai ma tunani da ke neman kar da ita, bata bari ya hargitsa ta ba ta dauki wayarta ta hau Facebook "Assalamu Alaikum yan mata" Ta iske na Abdoullah Aboubakar, ita sam ta manta wani Abdoul. Amsa sallamar tayi , ashe yana kusa nan yayi ta janta da hira, tun tana sharewa har ta fara bashi amsa. *** TUSHEN SU Alhaji mousa uomarou ɗan asalin garin Zindar ne, duk da tarihi ya nuna fatauci ya kawo kakanninsa Kasar Nijar daga Kano, har auratayya da chakuɗeɗeniya ya sa sun zama yan kasa.
.
Yara biyu Allah ya mallaka masa wato Idrisa da Abbas. Gidansa sannan nan gida ne da a unguwar yadakwandage kasancewar yafi sauran rufin asiri. Yayi kokari wajen ganin yaransa sun samu yalwataccen ilimin zamani, haka ma na addini. A rana ɗaya sukayi aure inda Idrissa ya auri Mas'ouda balarabiyar Kasar Aljeriya amma mazauna Kasar Nijar shi kuma Abbass ya auri yar gwoggonsu khadija. Wata goma sha ɗaya bayan aurensu khadija ta haifi yar ta mace wacce aka sa ma suna Halima. Mas'ouda kuma sai bayan shekaru haɗu Allah ya buɗe mata kofar haihuwa. Lokacin Idrissa ya sami aiki a fannin kuɗi da tattalin arzikin yammaci Afirka wato Union Économique et Monétaire Ouest Africaine (UEMOA). Don har sun koma garin Niamey da zama. Halima ta taso cikin gata da kula, sannan ta sami ingantaccen ilimi tun daga na addini har zuwa na zamani. Rashin haihuwar mahaifiyarta tun bayan haihuwanta yasa Abbass kara aure, inda ya auro Sauda.
.
Tun da ya auri Sauda kuma haihuwa ta sake buɗe wa a gidan. Sai ya zama kamar ana gasar haihuwa ne a gidan tsakanin khadija da Sauda. Bayan Halima ta kammala sakandarenta a LYCÉE AMADU KURAN DAGA (LAKD) ta samu gurbi karatu a université Abdoul Moumouni Dioffo, dalilin haka ta koma gidan baffanta Iddrissa. A shekaran Halima ta haɗu da Hammad wata rana ta dawo daga registration dai dai kwanar da ya raba su da homeland hotel shi kuma ya fito daga otel ɗin. Hammad Touareg(Buzu) ne ɗan asalin Agadez ne. Fari ne kyakkyawa kamar shi ya kera kansa.
.
Ba shi da hayaniya don magana wahala take bashi Yana da son kyale kyalen duniya amma mace da kuɗi sune kan gaba. Bai sha wuya wajen zulmiyar da Halima zuwa ga sonshi ba amma bai taɓa yunkurin taɓa ta ba yanda bai yi yunkurin zuwa neman aurenta wajen iyayenta ba. A dalilin haka iyayenta suka raba ta da shi amma fir ta ki don a tunaninta bata fara sonsa don ta daina ba haka kuma a shirye take da ta jira shi duk lokacin da ya shirya suyi auren.

0 comments:
Post a Comment