MAFARKIN ABDUL Part 2
.
Babu abinda ya fi faranta ran Halima kamar ta zauna tana MAFARKIN ido biyu. Zaune take da Hammad suna ciyar da junansu abinci a baki, suna yi suna jifan juna da kallo mai cike da kauna. Yaransu suka shigo suna kwala mata kira cike da murnan dawowasu.... Ire-iren mafarkan nan Halima keyi sai ta ji duk duniya babu macen da ta kai ta dacewa da samun masoyi. A haka har ta kai aji uku ana saura mata shekara ɗaya ta kammala karatunta hakan ya tada hankalin iyayenta don sun so ta kasance a ɗakinta a wannan shekaran kasancewar ta cika shekaru ashirin a duniya. Nan dai Halima ta kekashe ta ce ita bata da masoyi sai Hammad....
.
WANNAN KENAN
*** Washegari kamar kullum ta Shirya ta isa makaranta, faɗi ma bata ga wani fara'anta ba, ba yabo ba fallasa suka kasance tare har aka tashi. A hanyar ta na komawa gida ta shiga Faba-faba (wata yar bus da ake motar haya dashi a Nijar) nan ta iske wasu yan mata biyu a ciki. "Kin san Allah Faɗima, ko da tonton oumar ya ce an tsaida ranar auren mu da Hammad ban yarda ba, tsoro na kar in ya ce ya fasa" faɗin ɗaya daga cikinsu. Wacce da gani ta fi rawan kai.
.
"ke ma kinsan yana sonki kawai don ya fiye ka'idoji ne amma kawai ki kiyaye shike nan. Allahu ya nuna mana" faɗin wacce aka kira da faɗima. Hankalin Halima ya kasu kashi kashi sai take ji kamar Hammad ɗin ta ne, wani zuciyar na faɗi mata ai Hammad ba ɗaya bane a duniya. Bata san sanda bakinta ya fara furta "kar dai a ce ke ce amaryan grand frère (yaya namiji)". Nan duk suka juyo suna kallonta. Murmushi ta sakar musu sai ta ɗauko littafin da ahlin ɗinsu Hammad sukayi wai barka da sallah ta ce "ko ba wannan bane angon naki grande soeur (yaya mace)" Nan ma fuskarta cike yake da murmushi yayin da ranta ke rokon Allah kar ya kasance Hammad ɗin ta. "kinga irinta ko Sadiya, da rashin mutunci mukayi da kin kwan ciki, yi hakuri kanwarmu .
.
Ya gida ya su mama" "Lafiya lau, gashi har na zo in da zan sauka, zan faɗa masa mun haɗu da pretty damsel ɗinsa" Ta faɗi tana dariyan da yafi kuka ciwo. Tana sauka ta hau kabu-kabu wanda shi ya karasa da ita gida. Jinta take kamar mahaukaciya, haukan ma sabon shiga. Ko da ta isa ɗaki ta shiga Direct, sai da ta tuɓe ya rage daga ita sai breziya da siket sannan ta kira shi a waya. "Akan me zaki je kina min bincike Halima, ko an ce miki sadiya bata san duk yan gidanmu bane" Ya tare ta da shi kafin ya amsa gaisuwanta.
.
"Ai ban san cewa gidanku ɗaya ba sai yanzu. Yanzu Hammad sakayar da zaka min ke nan" Ta faɗi a raunane, idanunta na fitar da kwalla. Zuciyarta kamar ta fitar dashi saboda azaba kunan da yake mata. "ki fahimce ni Halima, ban taɓa miki Alkawarin zan aure ki ba, ina sonki mais (but) kin san hali na, hakan yasa kike zargi na kuma kike bincike na, bafa muyi aure ba kenan. Kuma kinga sadiya shekarunta goma sha shida ne kawai, zan iya zama in tsara ta yanda nake so" Ya karasa yana dariya.
.
Halima da jikinta ke karkarwa burinta ta tashi daga muguwar MAFARKIN da take tayi kokarin faɗin "Amma Hammad.... " bata kai aya ba ya katse ta da ban hakuri. " Don Allah Halima kiyi min rai s'il vous plaît (please) kada wannan ya taɓa soyayyar mu kinji Don Allah " bata karasa jinsa ba tayi hurgi da wayar ta kara rushewa da kuka wanda ya fi jini ciwo.

0 comments:
Post a Comment