MAFARKIN ABDUL Part 3
.
Tsabagen kukan da tayi ya haifar mata da matsanancin ciwon kai. Tun da ta shige ɗaki ba ta fito ba sai faɗi ma mommansu zazzaɓi take yi. Washe gari ma haka ta yini sukuku, mamaki ya cika ta rashin ganin kiran Hammad, zuciyar ta guda na ingiza ta kan cewa ta kira taji ko lafiya yayin da ɓangaren zuciyarta mafi gaskiya na faɗi mata ta kyale shi. Waya ta ɗauka ta kira Abdoul saboda amincin da ke tsakanin su yasa basa kyashin faɗi ma junansu sirrin rayuwarsu. Saurarenta yayi cikin natsuwa da fahimta. Sannan ya ce "ki ɗaure ki fitar da shi a ranki tun a yau, kar ki saurare shi, zafin da zaki ji kaɗan ne akan sai gaba ki sami ɓacin ran da yafi wannan. Ina office yanzu za muyi magana in na koma gida" Ta gode masa kana ta ɗan yunkura don cire damuwa a ranta. Haj. Mas'ouda na ankare da duk wani take takenta amma ta basar. Cikin lokaci kankani ta zabge ta rame, fara'anta ya zama ragagge ga yawan tunani. A lallaɓe ta kammala jarabawan zangonnan ta tafi Zindar. Abdoul kaɗai yasan matsalarta hakan ya sa shakuwa fiye da farkon haɗuwansu. Bakin cikinsa ɗaya sanda suka haɗu tana tare da Hammad da babu abinda zai hana masa aurenta. Ga shi saura wata bakwai a ɗaura aurensu da Agaysha. Kaifin basiranta da hankalinta yasa yake saka ta kan gaba a dukkan lamuransa don duk shawarar da zata bashi matukar zai yi amfani da ita toh akwai nasara.
***
Tana Zindar aka ɗaura auren Abdoul da Agaysha. Duk wani shiri na biki akan shawaran Halima akayi. Halartan bikin ne kawai batayi ba amma ko a ranar sunyi waya yafi sau goma, yana lallaɓata da ban hakuri akan matsalarta da Hammad. Amarya Agaysha ta tare a gidanta da ke Jeune cadre wanda ya sha gyara kasancewarta yar gidan masu kuɗi..
.
Agaysha Iggalher fara ce mai jiki, tana da tsawo bata da wani diri amma baza'a kira ta a chushe ba, yar asalin agadez ce buzuwa ce, amma ta taso a Dosso, iyayenta masu kuɗi ne kuma yan boko. Sun haɗu da Abdoul ta hannun yayanta sidi inda da farko ta ki amincewa da shi kasancewarsa talaka, amma tunda ya samu aiki ta makale masa. Aurensa bai sa shakuwarsu ta ragu ba sai ma a ce ta karu don duk wanda yake tare da ita ya san alakarta da Abdoul, wanda bai san danginsu ba takan ce masa yayanta ne, walau uwa ɗaya ko tubashinta. Tayi samari kala kala amma ba wanda ta yi soyayyar wata uku da shi ba gani take duk mayaudara ne. "Na rasa me ke damun matan adarawa (hausawa) da buzaye sam basu san wani abu kula da miji ba, duk soyayyar da za'a maka kafin ayi aure ne sama they are not caring" Abdoul Ya turo ma Halima ta bbm ɗin da suka maida hanyar hiran su, hakan yasa suka rage 2go.
.
Ɗan Aljani dariya haɗe da ɗaga hannun ba ruwa na ta tura masa "Allah ba wasa ba, kin san aboki na bayarben nan da wannan inyamurin wallahi har ban son zuwa gidansu, kinga dai ba Kasar su suke ba amma matan basu yi kyashin kula da su ba" Ya sake tura mata, bata so ta shiga harkan iyalinsa, don bata so ayi mata. Amma ta dake ta amsa da "Allah GF (grand frere) matanmu na kokari wajen kula sai dai abinda ba'a rasa ba, aure ɗan hakuri ne" Ta tura haɗe da aljani mai murmushi "Ni wallahi har danasanin aure yanzu nake, kai aure dama haka yake, mace bazata natsu ta kula da kai ba wai kar ka raina ta, na yaushe kuma.
.
Shi yasa mazan Hausawa da buzaye suka gwanance a Aron hannu " Sai da tayi dariya ma'ishi kasancewa ta san ya tsani kalmar nan ta aron hannu da gayu ke amfani dashi mai makon zina. "dariya ta kike wai, kin san dai a nahiyar mu anan ba Kasashen fa suke da Al'ada iri ɗaya kamar Nijar da arewacin Nijeriya. Toh kina isa arewacin Nijeriya zaki ga korafin iri ɗaya ne, matan banda rashin kula har da da rashin biyayya suna tunanin gyaran gado ne kawai aure, mstwww " Nan ma dai dariyar ta sake bin shi da shi, tana mamakin sa. Toh ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Don kuwa yanda ta tsara rayuwar Aurenta bata tsammanin za'a samu matsala da ita a wannan fannin. Burinta kullum rayuwar aurenta ya zama sanadin shigar ta Aljanna mai babban daraja. Ganin ba ta niyyar bashi haɗin kai balle har ya c faɗa mata matsalarta yasa ya juye hiran zuwa tambayar ta ya zancen karatunta da take shirin kammalawa. Karfe goma na dare yai mata sallama ta sa masa tsiya faɗi take "wajen buzuwa fa zaka kake sallama, ashe suna da rana haka" dariya sukai gaba ɗaya sannan sukai sallama.
.
Zaune take tana kintsa kayanta saboda zata kai ma Haj Mas'ouda ziyara kasancewar ta kammala karatunta na licence na shekaru 3, (kwatankwacin kwalin degree inji yan 9ja) sakamako fito yayi kyau. Wannan zuwan ma baffanta ya sa ta nemi gurbin karatun masters a cewarsa tunda taki aure. Wayarta ce ta fara kuka, kallon number ta yi don ko mutuwa take bazata manta numb nan ba. Kamar bazata ɗaga ba chan dai yana gab da tsinkewa ta ɗaga haɗe da sallama. "meye duniyar ne Halima, ace zaki iya share ni haka. Shekara biyu kenan fa, haba Halima alkawari bai ce haka ba" Ya faɗi yana mai kwantar da murya. " qui est sur la ligne (wanene akan layi) ta faɗi a ɗan fusace duk da ta fahimci muryan.
.
Dariya yayi mai isarsa sannan yace " mon nom est Hammad de agadez (sunana Hammad daga agadez)" Ya faɗi yana dariya. "Au wai kai ne, ni ban gane muryan ba." Nan suka gaisa. "ina takwarata" Ta tambaya "hmmmn hajiyata kinsan mun rabu kuwa" Ya faɗi cikin halin ko in kula. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Me yayi zafi haka Master" Ta faɗi tana mai dafe kirji kamar yana ganinta "Wallahi bazan iya ba, idanunta sun buɗe da yawa, duk wani hanyar rage ruwa ta san shi, wai yarinyar nan ce ke faɗa min don bana laguda ta toh tana shakkar son da nake ikrarin ina mata" "haba Hammad, yarinya ce fa karama, hakuri zakayi, amma dai da aka tsaida rana sannan zaka ce ka fasa, ka yi hakuri" "yarinya ce karama amma ko ke da kika gama jami'a ba za ki yi abubuwan da take ba, har ɗaga wuya fa ance tana yi." " Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ni ko ta ɓata wayonta kuma ta kunyata ku, Allah raba mu da zaɓen tumun dare." Ta faɗi tana mai kashe wayar. Cigaba da shirya kayanta tayi sannan ta ɗauki hanyar Niamey Sai chan cikin dare sannan ta labarta ma Abdoul duk inda hankalinsa ya kai a yawa duk sun tashi.
.
Ya rasa meyasa lamuran Halima ke tsayar masa a rai, ko dan tana mutunta shi ne ko menene shi kan shi ya rasa ganewa. Tun daga ranar Halima da Hammad suka fi tif da taya mannewa kafin a ankara shakuwarsu tafi na da. *** Ziyara suka kai birnin Paris na Kasar Faransa. Sun sauka a ɗaya daga cikin otel da suka fi tsada watau RITZ Paris da ke lamba ta 15 Place Vendôme, 75001 Paris. Sunyi wanka, sun rama sallolinsu sannan suka zauna cin abinci. Daga nan kuma suka Lula duniyar da su kaɗai suka san da shi don kawar da gajiya.
.
Basu kai ga isarwa ba yaji saukan ruwa a fuskarsa. A firgice ya farka yana lalube ko idanunsa zai kai ga Halima amma ina sai ta kai ga Agaysha tana huce kamar mai shirin dambe. "Zina kake min a kan gadonmu na sunna" Ta faɗi hawaye na kwarara daga idanunta. "Zina kuma Agaysha" Ya faɗi a ruɗe, ko dai abinda ya ke tunanin a mafarki ne a gaske abin ya faru, amsar da ta bada ya dawo da shi daga tunani. "Ya zaka kwanta kana numfarfashi a cikin barci, Allah ya isa tsakanina da Aljannar da ke shiga gona ta. Don taga bana ganin ta, kai kuma sai jin daɗi kake" Ta karasa tana gunjin kuka. Rungumo ta yayi yana tura mata sakonni masu wuyan fassarawa, "mafarki nayi kina shayar dani zumanki nefa ma femme (matata)" da haka ya rufe bakinta. Bata sake ɗaga zancen ba yayin da shi kuma ya gagara cire shi a ransa

0 comments:
Post a Comment