MAFARKIN ABDUL Part 6
.
Sannu a hankali ta fara farfaɗowa daga cutar da ke addabarta, tun tana tuna Hammad sau ba adadi har ya zama takan kidaya su, tafiya tafiya har bai wuce ya faɗo mata sau biyu ko uku a rana ba. Kwatsam wata ɗaya da faruwa wannan Al'amarin suna kallon tashar Dounia TV (Radio Télévision Dounia) su duka har da baffa, bayan Ummitr Bingel sa Gimbiya Zuby sun gama shirin da sukanyi na mu shakata sai aka sako tallan auren Hammad da wata Amina. Shiru ya ratsa su a falon har aka sa wani shirin. Se chan ne baffa ya nisa ya musu nasiha mai ratsa zuciya, ya nuna musu illar yaudara da kuma mata su zubar da mutuncinsu. Tun daga ranar ta tattara lamuran Hammad ta sa a bola sannan ta kona. Ta samu aiki a makarantar da ta gama wato Université Abdou Moumouni bayan ta kammala masters ɗin ta. Ba laifi tayi kiba tayi kyau abinta yayinda maza suka sa ta gaba, ita kuma bata basu uzuri daga sun nemi raina hankalinta zata kora su, tsoranta zuciyarta ta kamu da son wani ta kara wahala. *** 2014 ... Gari na wayewa dare na yi kwanaki na tafiya har su isko watanni. An wayi gari Halima kan manta Hammad in ba taji an kira sunan shi ba ko taganshi kasancewar yakan kawo matarsa makarantar da take aiki. Bata da wani abokin ɗebe kewa da ya wuce Abdoul sun shaku sosai, komi ta samu in na yara ne takan siya ma yaransa ne safiyyah da ta ci sunan mahaifiyarsa hakan yasa suke ce mata Ummu abiha ,sai biyun Halima kuma a hakan suke kiranta. Agaysha ta san da zaman Halima kuma tana kishi da ita amma bata ɗauka da gaske bane don a cewarsa Halima kawarshi ce kawai da ya ɗauka kanwarsa uwa ɗaya. Hakan ya kwantar mata da hankali don duniya in dai kawance kawai Abdoul ɗin ta zeyi da koma wacece ba soyayya ba toh babu abinda ya shafe ta. Kalmar budurwa ne dai ta tsana don ko da wasa kace mata "ga budurwan Abdoul" toh zaka shiga cikin jerin makiyanta da bata da kamar su.
***
Wata rana cikin ranaku, Halima na zaune a ofishinta da ke cikin Faculté des Sciences, kira ya shigo wayarta wanda daga amon kiɗan ta san yayanta ne. Da sallama ta amsa wani farin ciki na ratsa ta, lumshe ido duk sukayi a yayin da suka ji muryoyin junansu, shiru sukayi na yan dakikai, su kaɗai suka san mai zukatansu ke raya musu. "yan mata jiya nayi mafarki da ke wanda naga ya chanchanci in isar miki shi ta hanyar labarta miki". Ya katse masu shirun. "wow! Allah sa alkhairi ne MAFARKIN ABDOUL ɗin" Ta faɗi tana dariya. Shima cikin dariyar ya caɓe "Au wai har kin sa mai suna ne, tun kafin kiji" tun kan ya dire tace "kasan da ace ina da fikrar rubutu babu abinda zai hana in mai da shi littafi har in sa mai sunan MAFARKIN ABDOUL" Ta faɗi cike da alamun iyakan gaskiyarta kenan. "wai tsaya, in kuma mafarki nayi ana nakaɗa miki duka, shima alfahari zakiyi dashi" Ya faɗi yana mai cigaba da dariya, wanda ta kasa bambantashi da na keta. .
.
Cikin Alamun gundura da dariyarta tace "Ni ba abinda ke cikin mafarkin ya sani murna ba balle ka samu abin tsokanata da shi, wanda yayi mafarkin ne ke da mahimmanci Alaranma" dariyan ya cigaba da yi ba tare da ya damu da fushin da ta fara ba. " Toh hajiya halimatu ai ba yau ne farau ba, ina ga ba'a cike sati. Banyi sau biyu ba, wannan dai kawai ya tafi da hankali na sannan ya magance min matsalar da nayi shekaru biyu ina fama. Shiyasa zan faɗa miki in ba haka ba ai se kin biya. Ya sake kara sawa yana dariya. "yanzu kana da matsala shi ne baka taɓa faɗa min ba, kuɗi ne ko ciwo ko har yanzu mamansu Ummu abiha ba ta dena tozarta ka bane." Ta faɗi kamar zatai kuka. Wannan na ɗaya daga cikin dalilin da yasa take da mahimmanci a gareshi. Takan nuna damuwa ko farin ciki yayinda ɗaya ya same shi. "ba ko ɗaya, wato ke hajiya ko. Kina kwasan. Albashi, toh cepa miliyan ɗari nake so, karkaɗa kunni ki sha labari" Ya faɗi. Yana dariya, itama ta tayashi
.... "Na ganni ne a wani lambu mai ban sha'awa, bayan kayan marmari da ya yalwatu a cikin lambun har da wasu furanni masu fitar da daddaɗar kamshi wanda ya sa na kara kishingiɗa a resting chair ɗin da nake zaune a kai. Lumshe idanu nake farin ciki na yalwatuwa a zuciyata. Sallaman da kikayi ne yasa na buɗe idanu ina mai sakin murmushi. Farantin hannunki kika aje a gefe sannan kika fara shayar dani salad ɗin kayan marmarin da kika zo da shi.
.
Wanda daɗin sa bai sa na ankara da ya kusan karewa ba har se da kika daga Yankar karshe na abarba sai na na riko hannunki haɗe da spoon ɗin da ke baki na. Hakan yasa kikai saurin ɗago idanu kika kalle ni, idanunmu na haduwa kika kasa ɗauke idanu na wasu dakiku. Muna cikin haka sai ga yara biyu sun zo a guje suna kiran "Abbu! Ummu!" kallo ɗaya nayi musu na san yan biyu ne kuma daga tsatsonki suka fito saboda tsabagen kaman da sukayi da ke. Sun faɗo jiki na kenan suna haki kiran sallah ya tada ni daga barci, faɗa min me kika karanto a ido na da kika tsare ni da kallo" Ya karasa yana mai tsokanarta, "ka bari sai mun sake haduwa a dreamland sai ka min tambayar, kasan me?" Ta dakata ko zai amsa "A'a se kin faɗi" Ya bata amsa Se da tayi dariya son ranta sannan tace "za ka yi kyau da rubuta labarin soyayya fa. Wannan iya tsara lbr haka" ba ta dena dariyar ba shi kuma kansa duk ya ɗaure, "yanzu ba za ta ba MAFARKIN mahimmanci ba bare ta kai ga fahimtar abinda ya ke damuna game da ita b" Ya faɗi a ranshi yayin da a bayyane shiru yayi mata kawai. Jin ya kyale ta yasa T faɗin "hello!" dariya kawai ya bi ta dashi kana sukai sallama.
.
Shiru tayi tana tariyo labarin da ta sanya ma MAFARKIN ABDOUL, bata san me ke shiganta ba ta dai tsinci kanta cikin wani yanayi daga tafin kafarta har Kirjinta wanda salon bugun zuciyarta ya chanza nan take. Amon muryar Abdoul take ji a kunninta sa'ilin da yake bata labarin. Nan take wani farin ciki ya mamaye ranta yayinda tsoro kuma ya shige ta sanda ɓari guda na zuciyarta yace da ita "in baya sonki fa". Nan take sai ta shiga damuwa. Sai sa su ka yi sati biyu babu wani kwakkwaran magana da ta shiga tsakanin su, iyaka sukan gaisa da ɗan hira sama sama. "Amarya a gidan Abdoul barka da yini" Ya shigo WhatsApp ɗinta daga lambar aminin Abdoul Yahai. Aljani mai dariya kawai ta tura masa sannan suka gaisa a mutunce. "kina gara ɗan uwa na fa Halima shi tsoransa ki yankuna shi wanda hakan zai taba zumuntarku amma wallahi nasan duk kuna sonjunanku, meye amfanin cutar da kai, in shi ya kasa buɗe hanya ke baza kiyi ba?
.
Ya tura mata haɗe da aljani mai jan kai. Bata ce komi ba sai aljani mai dariya da hawaye ta tura masa, ganin bata da niyyar bashi haɗin kai yasa ya kyale ta. Daren ranar ta tsawaita hirarsu da Abdoul har yake faɗi mata mafarkan da ya keyi kusan kullum inda yake kara hura mata wutan sonshi a ranta. Chan dai ta ɗaure ta tura "inaama! Inaama!" Yana gani ya tashi zaune, sannan ya kira ta. Ringing biyu ta ɗaya da sallama. "me kike cewa ne Halima ɗazu" addu'a yake ta faɗi abinda ranshi ke son ji. " cewa nayi inaama! Inaama MAFARKIN ABDOUL zai tabbata. Da an samu maaurata gwanaye da zasu sadaukar da rayuwar su wajen faranta ma juna" Ta faɗa bil hakki abinda ke ranta kenan.
.
Ya daɗe da sanin Halima irin mutanen da masana psychology kan kirasu da extrovert ne, sam bata ɓoye ra'ayinta akan abu, ya daɗe yana jinjina mata ɓoye soyayyar sa dake zuciyarta, ko da yake matantakanta ya taimaka mata ainun wajen ɓoyewa. "Halima kina da matukar mahimmanci a rayuwata, in na koma zindar karshen sati, zanyi magana da mama da Maman Ummu akan auren mu, fata na kar su kawo matsala, shekara mai kamawa zamu tabbatar da MAFARKIN ABDOUL, sai in kama miki gida a nan Niamey ko ya kika ce" mamaki ya cikata, wannan sai kace jira yake ta furta. "Amma wannan assurance ɗin da kayi min anya beyi wuri ba, bana son abinda zai taɓa alakarmu fa, kasan ban iya son abu ba, ina sonka da yawa Abdoul" Ta furta a sanyaye wanda hakan yasa yaji tausayin ta ya mamaye shi. " kar ki damu ina tare da ke insha Allah ba gudu ba ja da baya" da haka suka dulmiya duniyar soyayya ba ji ba gani. Wasu kalaman in ya furta mata har mamaki takeyi da ma chan yana sonta ne.
.
Da kyar sukayi sallama bayan sun tsara yanda zai nemi aurenta da kuma yanda aurensu zai kasance. Cikin watanni biyu sun shaku sosai fiye da wanda sukayi a baya. Kulan da suke ba junansu abin ba'a magana, ko da yaushe suna nane da juna walau a Chat ko a waya. Cikin tsarinsu ne bazata faɗa ma kowa ba har se yaje yayi magana da iyayensa in sun tashi zuwa neman aurenta. Duk yanda yaso zuwa aiki ya hana shi motsi kasancewar ya fara aiki da Ministère des Affaires Étrangères et de la Coopération ( Nigerien Ministry of Foreign Affairs and Cooperation) hakan yasa ya kan bi tawagar da ke zuwa duba République Niger ambassade na sauran kasashe. Yanayin rashin zama yasa bai tafi da Agaysha ba amma wani sa'in musamman in yara na hutu sukan je a tare.

0 comments:
Post a Comment