MAFARKIN ABDUL Part 7
.
Soyayya suke mai cike da tsafta, har yanda aurensu zai kasance sunyi, wani zuwansu Abuja a tarayyan Nigeria ya siya yadin material ya bada a Hanifa boutique ya ba da a ɗinka bridal gown a Hanifa creations & couture da ke lamba ta 10, Gimbiya Street area 11, garki Abuja. Tun da ya kai yake manta santin ɗinkin. Don sai da ya ba mai wajen haj. Hadiza shawara in da hali ta buɗe musu a Nijar ko suma zasu ci romon ɗinki hadaddu. Dariya tayi tace " me zai hana, Nijar da Nijeriya ai duk ɗaya suke, zamu duba se a buɗe a Niamey in de zaku kawo ɗinki". Yini yayi yana faɗa ma Halima karamcin su tun daga siyan material har ɗinki fatansa su cika masa alkawari. Halima bata tabbatar da haɗuwan dinkin su ba sai da ta leka shafinsu na Instagram, rudewa tayi tana nuna ma momma haj mas'uda, faɗi take "momma anya bazamu aika sauran ɗinku nan ba, ɗinki sunyi kyau" itama dai haj mas'uda ta yaba da kyawun dinkin har tayi shaawar aika ma kawarta haj. Maijidda dake birnin Kano in za'a samu wanda ze kai tunda suna home delivery a Nijeriya. Hakan kuwa sukayi sanda Abdoul ya tabbatar masu da cika alkawarin su. Sai akayi da Abdoul ya karbo tunda za'a kammala kafin su dawo Nijar. Bata tsaya ba sai da tayi booking kwalliyar da za'a mata wajen ramat makeover, sannan ta bada aikin waka wajen mai zazzakar murya da amon muryarta yafi zuma daɗi wato sa'a Vocal. "wai ke iyayensa basu zo ba duk kun gama shiri ko dai ku zaku aurar da kanku ne," faɗin haj mas'uda da ta fada mata ta yi booking wakar sa'a Vocal, da irin karamcin da sa'a tayi mata da ta kira ta a waya. "momma kinsan yace January yake so ayi, da sunzo za'a yi komi gaba ɗaya" Ta faɗi tana rufe ido. "Au! Wai dama kina da kunya, bayan ina ganin kosawa a tare da ke." itama ta faɗi tana dariya. "momma shekaru na fa ashirin da biyar, kinga kenan ai na tsufa, ko" dukan da aka kai ma cinyarta yasa ta yin shiru. "Toh shi ɗin kin tabbatar da ya isa da iyalinsa? Kuma baza'a samu matsala ba, kin san maza in har basu isa da matansu ba aurensu matsala ne. Ki cigaba da addu'a de, in Alkhairi ne Allah ya tabbatar, in babu ya zaɓa miki abinda yafi alkhairi" Jikinta yayi sanyi, yaushe rabon da tayi addu'a, a ganinta ai shi ne alkhairi tunda ya zo bayan rabuwanta da Hammad. Haka dai ta fara istigfari tun daga zaune. Ranar itace har da tsayuwar dare. Dawowannan Abdoul ya sa ta farin ciki da annashuwa, gani kawai aurensu ya zo. Bayan ya aje musu sakon ɗinki ya dauki hutu ya wuce zindar. Nan ma ya samu tarbo mai kyau daga Agaysha. Sai da ya kwana biyu sannan ya fara mata Maganar wata rana suna hira "Madam aure nake son yi, ba don bana sonki ba sai don gazawarki wajen kula dani, ina sonki, banda niyyar kara aure amma yanda kike tafiyar dani yasa har shakuwar mu tayi karfi da Halima tace tana so na, kuma nayi niyyar aurenta" Ya faɗi kai tsaye. Kuka sosai ta fara, ganin yayi shiru yasa ta cakume masa wuyar rigarsa tana ihu tana kuka "kaci amanata, Halima ta munafunce ni, tayi ta ban shawara ashe sonka takeyi toh wallahi baka isa ba, zan kai karanka wajen baba don wallahi bazan yarda ba, ka gama zubar min da mutunci a idonta sannan kace zaka aure ta" rungumar ta yayi yana bata hakuri. Rigima taki ci taki cinyewa, kuka Agaysha takeyi ta ki cin wani abinci, tayi baki ta rame, yaranta ko wanka bata musu, ya bada hakurin taki, har sai da ta tsare shi ya kira Halima. Ringing yake Halima na kallo taki dagawa don takaicin tunda ya koma ko WhatsApp yaki hawa, bai dauki wayarta ba haka bai kira ta ba..
.
Sai da yayi kira uku sannan ta ɗauka da fara'arta ta gaisheshi, a dakile ya amsa sannan yace "Na kira ki ne in baki hakuri, sannan in faɗa miki bazan iya aurenki ba, tunda na faɗa ma Maman Ummu abiha zancen auren gida na ya koma sansanin rigima, matsalar gida na yasa nayi tunanin kara aure kuma ta min alqawarin canzawa, kiyi hakuri ki jingine zancen soyayya tsakaninmu". Saurin tare shi tayi tana mai kuka "kar ka min haka, ina sonka zan jira ka har zuwa sanda zaka shirya amma don Allah kada ka rabu da ni" kuka take Bil hakki. "kinga Halima matata ta ishe ni bazan iya ba nace, ko ana dole, mtswww" Ya karashe da jan tsaki kana ya kashe wayar.
.
Tun daga ranar bai sake ɗaga wayar Halima ba, Agaysha kuwa hadiye shi ne batayi ba saboda kula. Tarairayan da yasa ya manta wata Halima a doran duniya. A ɓangaren Halima tun tana ganin abin wasa, taga har anyi sati ba kiranshi ba alamun shi yasa ta kira amininsa Yahai Bayan sun gaisa ta faɗa masa duk abinda ya faru ta kara da faɗin "ka bashi hakuri in laifi na masa, duk Dokan da zai sa min na yarda in dai zai aure ni, don Allah ka taimaka min." "shike nan Halima, yanzu haka yana hanya munyi alkawari zamu haɗu, zan kira ki yayinda nake masa maganar don ki ji komi daga gareshi" godiya tayi ta zuba masa kamar yai mata bishara da Aljanna.
.
Ba'a yi awa ɗaya ba kuwa sai ga kiran Yahai, da saurinta ta ɗaga tayi shiru tana ji Yahai yace "wai ni Abdoul ina Halima ne ya zancenku ya kwana" "mtsw! Tana chan, ni bazan kara aure ba ina son zaman lafiyan gida na, tunda na faɗa mata ban sake neman ta ba" " ko dai ka gano wani mugun halinta ne, yanzu kake neman rabuwa da ita? " Yahai ya sake tambaya "kasan in da banyi aure ba babu abinda zai hana aje Halima a matsayin mata, rigima ce dai banso. In kana so kuma Allah sanya Alkhairi". Mamaki da takaici ya cika Halima, ta yi saurin katse wayar kafin taji abinda zai ɓata mata rai. Tsam ta tashi ta je ta faɗa ma momma abinda ke faruwa, mamaki ya cika ta kwarai amma ta bata hakuri haɗe da nasiha akan addu'ar su ya karɓu Abdoul ba Alkhairi bane a gare ta.
***
A kwana a tashi Halima ta zama wata mara fara'a, kallon ko wani namiji a matsayin mayaudari take in akai mata magana tace tunda Abdoul yayi kowa ma zeyi. Wata rana kawarta faɗima ta zo gidan momma kamar yanda ta saba kawo mata ziyara. Suna cikin hira tace "wai dama Agaysha Iggalher ce matar Abdoul?" "Eh! Ina kika Santa?" itama ta tambaya. "kin san kanwar miji na ke auren babanta, da kyar uwar ta yarda akayi, jiya muka haɗu a gidan da yake ita ayshatou din ta haihu, Shine fa take nuna hotonki wai kin nace ma mijinta kina son shi har tana muyi kafa kafa da mazajenmu kwacen miji ki keyi " kukan da Halima ta fara yasa yin shiru. Ta fara bata baki tana cewa " bafa na faɗa miki don ki bata ranki bane, ina so dai ki yi aurenki ki huta sa surutunta, don ta ɗauki alwashin sai ta hukunta ki" "Ta ya zata hukunta ni, asiri ko tsafi bazai taɓa kama ni ba don na rike addu'ar da manzo SAW yace mu rike ma kariya. Manta da ita kinji yar uwa, jiya na dawo daga zindar fa" haliman ta karasa tana mai chanza hiran.
.
Bayan magriba ta dauki waya ta kira Abdoul, sun gaisa kamar da ya tambaye ta mutan gida, itama haka. Chan ta ce "Na kira ka ne in ce ka ja ma matar ka kunni, babu abinda zanyi da mijinta, tun tana kira na tana zagi na ban tanka mata ba, har ya kai zata dinga yawo da hoto na da guntuwar wasikar da ban san da zamansa ba wai na rubuto maka, ai laifin ba nawa bane naka ne mijinta. Don Allah ku fita harkata nima daga yau na fita naku" "kinga bazaki zo ki ma mata na sharri ba, kuma Allah ya saka mata, aure ne dai nace banyi ko dole ne" Ya katse ta a fusace, "in da ina bin ta da sharri kasan da tuni na barka ka saketa ko, ko ka manta sirrin gidan ka yayi zama hannuna, Allah bamu Alkhairi" Ta kashe wayar gaba daya ta sallaci isha'i wani farin ciki take ji ta rasa na menene, hatta yan gidan sun kula don sai da baffa ya ce mata "Halima Albishir ɗin Aljanna akai miki?" Tayi dariya tace "kusan haka ne fa, kasan an ce budurwa in bata taɓa zina ba ta rasu tayi shahada da ladan jihadul Nafs. Ko dai zancen mutane ne baffa? " Ta tambayeshi tana dariya. " se kinga auren jikokinki Halima, Allah sa jinkirinki alkhairi ne " momma ta katse musu.
.
" Allah dai yasa in tafi a sa'a, momma bata so in tafi, se hakuri in lokaci yayi" Ta faɗi tana dariya Haka sukai hira har goma da rabi sannan tai musu sallama ta je kwanciya Kwanciyar ta ke da wuya ta fara ciwon ciki, da kyar ta daga waya ta kira momma, a ruɗe ta shigo ta iske ta cikin amai cikin na murɗa mata. Cirko Cirko sukai akanta, bayan cikin ya lafa, faɗi take "ku yafe min, kuce su mama su yafe min, na yafe ma kowa" "ciwo ba mutuwa ba ai kinji sauki, sannu halima" kawai suke cewa. Huɗu da minti arba'in cikin ya sake motsawa, wannan karan tana wani irin mika in ya rike ta. Ɗaukan ta sukai zuwa mota don kaita asibiti basu san sun kai ta ga ajalinta bane. Daidai kwanar fita anguwansu tayi wani mika haɗe da salati, shike nan ta amsa kiran ubangiji. "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai baffa ke faɗi. Hajiya mas'uda kuwa mutuwar zaune tayi. Hawaye na gasar tsere a fuskarta.
.
.. Tunda ya sauke wayar jikinsa yai masa sanyi. Anya ya kyauta mata kuwa, yarinyar da ke ɗaukan shi mai babban daraja ya yankuna haka. Shiru yayi kalamanta na dawo masa ɗaya bayan ɗaya. "wai me yasa ake ɗaukan maza masu mata mayaudara ne, duk wanda nace ma kai zan aura sai sun ce Allah sa kar kayi min halin, in dai aje wani spare, tunda soyayya ba mota bace meye amfanin tara samari" Ta faɗa masa wata rana suna waya. "Ni dai ba yaudaranki zanyi ba. In kinga ba mu yi auren nan ba mutuwa ce, kece fa mafarki na kece tunani na a farke" sai da yaji kunyar kansa da ya tuna alwashinsa gare ta. "momma cewa tayi ba komi ya sa maza masu aure iya yaudara ba sai ganin suna da matan su a gida, ba su da halin karin aure amma su je suna kwadayin soyayya da wasu, basa ko la'akari da suna da yaya mata ana iya musu suma. Wasu kuma ba laifinsu bane matan su ke hana su aure, su ma basa tunanin mazajensu na iya mutuwa ko su rabu wani mara matan ne zai aure su, ai aure kanta wa'adi gareta ban ga abin tashin hankali akai ba" "lafiya ka zauna kana tunanu" Agaysha ta katse masa tunaninsa nan de ya zauna sukuku har lokacin barci yayi ya kwanta.
***
Sanye take cikin shiga mai kyau, kyallin da tufan jikinta ke fitarwa kaɗai abin kashe ido ne, babu wani al'auranta da ke waje, fuskarta cike yake da murmushi. "Abdoul kaga ɗaukakan da Allah yai min ko, ka gafarce ni in na saɓa maka amma na tafi bazan sake damunka ba" Ta na faɗin haka ta fara tafiya, taurari sun kewaye ta, haske ya bayyana, kamshi ta ko ina. "Halima! Halimaaaa! Halimaaaa!" yake faɗi iya karfinsa wanda ya tada Halima daga barci. Kallon agogo yayi karfe biyar na asuba ya tashi ya ɗauro alwala nan ya fara jero nafilfili kasancewa biyar da rabi ake kiran sallah. Tunani yake dole ya je Niamey su sasanta kansu bazai ma Halima haka ba, bata chanchanci abinda yai mata ba, ai Halima matar alfahari ce, wacce Burinta tayi aure tayi Ibadan da zai zama sanadin shigar ta Aljanna.
.
Yana fita Agaysha ta kira kawarta da ke mata rakiya zuwa gidan malamin da ke mata aiki akan zasu je, Abdoul ya tashi cikin dare yana kiran sunan Halima. Ko da ya dawo sallah yayi mamaki da bata tsare shi da masifa ba, illa hillatarsa da tayi ta yi har ya shagala. In bayan sun samu nutsuwa take faɗa ma sa zai kai ta gidan kawarta zasu je ta'aziyya, ba gardama ya amince. Karfe goma sha biyu suka bar gida ya sauke ta sannan ya karasa Mirriah don ya samu sallar Jumma'a a Grande Mosque de Zinder. Bayan an iddar da sallah ne aka bada sanarwan za'ayi sallan jana'iza, na wata baiwar Allah da ta rasu.
.
Haka kawai yaji tsoro ya shige shi. Bai gama jawo natsuwa ba idonsa ya kai ga baffa, da mahaifin Halima suna share kwalla. Kallon zanin da aka rufe ta yayi in bai manta ba yana daya daga cikin ɗinkunan da ya amso masu har yana mata tsiyar tayi zani plane. Se da ya sa ma zuciyar sa mahaifiyarta ce ta rasu sannan ya samu natsuwar tashi ayi sallan da shi. An idar haka yabi tawagar farko, ya kula da yanda mahaifinta ya rushe da kuka sanda suka yi ido hudu dashi. A harabar masallacin aka shigo da hillux aka shimfiɗe gawar. Yana ta kallon mutane ɗai ɗai, ga yan uwanta mata daga sashin mata na masallacin. Da kyar ya shiga motarsa, inda wasu yan anguwan su haliman suka cika motar. A hankali akai ta tuka motar har makabarta inda an riga an gine mata lahda ɗinta. Ko a nan sai da mahaifin Halima ya jawo shi, yayin da ake maida kasan da zai rufe ta. Suna nan tsaye bayan an rufe ba ma kusan minti arba'in suna mata addu'a kamar yanda manzo SAW ya umurce mu kar muyi saurin barin makabarta yayinda muka rufe wani namu. Har suka fito babu wanda yace uffan, ya kula da Muguwar kallon da baffa ke jifan shi da shi, yayin da mahaifin Halima ke masa kallon tausayi. Sun fito gate din makabarta kenan mahaifin Halima yace "Abdoul ya hakurin mu, Halima kuma wa'adi ya cika. Sai mu" be kai aya ba sai ganinsa sukai a zube sumamme. Shafa masa ruwa akai sannan aka sa shi a mota, baffa ne ya ja motar suka dunguma zuwa gida.
.
Banda ajiyar zuciya babu abinda Abdoul ke yi, ina ma zai farka daga barcin nan. Nasiha sosai suka haɗu sukai masa har baffa da ke cike da jin haushin sa. Ya shiga cikin gida yai musu ta'aziyya sannan ya koma wajen maza. Shi dai zai kira kan shi da mutum mutumi don motsin kirki gagaransa yayi. Ya kasa yarda Halima ta rasu.
***
Can su Agaysha sun gurfana gaban malaminta, bayan duk surutanshi da shafe shafensa yace "Halima anyi ta ne kawai don ta kawata MAFARKIN ABDOUL, sai de akwai wasu yara a gaba da nake hange, kuma bana tsammanin naki ne amma tabbas na Abdoul ne, yanzu de za'a yanka bakin bunsuru ayi rubutu dashi ki sha, kishiya sai ta abin hawa ba dai mutum ba, " yana gama faɗi ta aje masa cepa dubu talatin sannan suka juya. Ko da ta isa gida bata iske shi ba, nan tsoro ya cika ta kardai ya je wajen Halima ne. Karfe tara da rabi ya shigo gidan da sallama, a cikin ta amsa amma ganin idanunsa jawur gashi yana jan kafafu wanda shi ne abin da yafi tsana a rayuwa.
.
"lafiya abban ummu" Ta faɗi a firgice tana taro shi, a zuciyarta fata take Ace an ɗaura ma Halima aure amma se taji yace "Allah yayi ma Halima rasuwa jiya da dare" "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah ya jikanta yasa ta huta. Wai hankali na yanzu zai kwanta babu mai takurawa miji na" dukan da ya fara mata ta ko ina ya sa tayi shiru haɗe da shekawa ɗaki ta rufo kofa don gani take mutuwar ta taɓa kwakwalwar sa. Nan shima ya zube yana mai sakin kuka, abubuwa da dama yai ta dawo masa dangane da soyayyar su da Halima.

0 comments:
Post a Comment