MAFARKIN ABDUL Part 8
.
Dashi akayi zaman makoki aka gama, Agaysha ko a kwalar riganta don tunanin ta Abdoul nata ne ita kaɗai. Duk da walwalarsa ya zama tarihi ba don son da yake ma Halima ko kuma don ya gagara ɗaukan kaddara, A'a, ya kasa yafe ma kansa rabuwa da Halima da yayi. Shin dama bai shirya aure bane yaje ya fara neman ta. Shi ma yana cikin jerin maza masu yaudara kenan. Me yasa ya gaskata ma Halima zancen da ake cewa maza masu aure sun fi yaudara. Mafi yawan lokutta ba laifinsu bane tsoron fitina yake sawa su hakura, amma ai Allah ya basu ikon yi me yasa ya biye ma Agaysha har ya saɓa ma Halima, ya ci amanar yardan da ta mishi, ya sa kafa ya ci mata mutunci duk da girmama shi da take yi. Me yasa tun farko ya amince zai aure ta bayan yasan bai shirya kari ba. Anya Halima ta yafe masa kuwa. Da irin wannan tunanin ya shirya ya je gidan baffa. Cikin sa'a ya same shi a gida. Bayan sun gaisa sunyi ma juna ta'aziyya sai kawai ya sa musu kuka, tun suna takaici har ya dan soma basu tausayi. Basu hana shi ba har sai da yayi mai isarwa sannan ya ce "Halima ba ta yafe min ba ta tafi ta barni. Na ɓata mata da yawa ban san da hakan ba sai da lokaci ya kure min, fitinar Agaysha ya sa na ki zuwa, ni kadai na san abinda na fuskanta." Ya karasa yana sakin wani kukan mai tsuma zuciyar mai saurare. "Da ma chan ba sonta kake ba Abdoul mu barshi a hakan kawai" faɗin momma don ita da tana da hali zata murkushe shi take ji. "mu dai barshi a yana sonta ɗin, babu sauran abinda za'a iyayi se dai hakuri. Halima kafin ta rasu sai da ta furta yafiya ga kowa. Muyi fatan inda take tafi nan da ta bari, in da rabo ai ss ku kasance a Aljanna," kuka dai Abdoul ya cigaba, nan Baffa ya zauna yayi ta bashi baki, nasiha yake masa mai shiga jiki sannan ya rufe da addu'a. *** 2016... A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, shekaran Halima ɗaya da rasuwa. Kullum kwanan duniya sai Abdoul ya bi ta da addu'a wani zubin har da sadaka da azumin nafila da niyyar Allah ya kai ladan zuwa gareta. Agaysha tun da ta buɗe idanu ta tabbatar da gaske Halima ta rasu ta chanza salon rayuwar aurenta duk wani nau'i na kula da take ma Abdoul ta janye. Bata kyashin zaginsa ko ci masa mutunci ko a gaban wanene. Ta kanyi amfani da kuɗin da dangin mahaifiyarta ke dashi tayi ma danginsa gorin arziki. Irin haka ne ya faru yau, ya shigo ya iske tana hira da kanninshi. Duk suka gaisa da shi ita kuma ta yi kamar bata ganshi ba. Har ya shiga ɗaki ganin minti goma bata biyo shi ba yasa ya dawo falon ya same su. "Madam me kika girka, zanyi baki wasu Diplomate yan Nijeriya zasu zo" Ya faɗi zuciyarsa na bugawa ɓat! ɓat! Kar ta kwaye masa baya. Ilai kuwa buɗan bakinta sai cewa tayi " Au nom de Dieu il partir au restaurant le plus près pour nous acheter à manger (kasan Allah ka je Restaurant mafi kusa ka sayo muku abinci) , don ko naka na ba kanninka, ni na gaji ba abinda zanyi tun safe nake aikin girki Haba!" ta karasa tana murguɗa bakin ta. Kallonta yake yanda ta jinɓire waje ɗaya. Rigar sa mai tambarin wajen aikin su ne ta sanya da zaninta. Shike nan don tana da ciki ba zata yi ma kanta faɗa ta dinga kwaliya ba, ko yaya ne ta yi shiga mai kyau. "kin san Allah babu abinda zai hanaki girkin nan in ba so kike rayuka su ɓaci ba" Ya faɗi yana haɗa fuska ko Allah zai sa yayi mata kwarjini amma ina don tsaki tayi tace "banga uban da ya isa ya sa nayi girki ba, dilla kalle ka wai kai har namiji ne anan. Mtsww! An dai rako maza wallahi, banda ba makwanci wahala ba abinda mutum zai buga kirji ya ce ya iya. Ka gayyato Halima daga inda take tayi maka" Ta faɗi tana barin shi zaune a inda yake. Kaninsa dama tun da ta fara masa masifa suka fice daga wajen. Dafe kansa yayi da hannu biyu yana tunanin wani irin hukunci zai mata. Ashe dai haka take. Wasu siraran hawaye ne suka fara zubo masa, yana tausayin kansa. A haka ya fara tunanin rayuwar sa, wanda ya sani da wanda aka bashi labari. ABDOULLAHI ABOUBAKAR Asalin kakanninsa yan jihar Borno ne a gabashin Nijeriya, sana'ar siyar da citta da tafarnuwa ya kawo su Nijar inda suka sauka a zindar. Mahaifinsa Aboubakar ya taso ɗan dangi kasancewarsa auta cikin yaran kakansu talatin da shida. Yayi karatu zuwa sakandire kafin ya faɗa harkan kasuwanci, tun yana karkashin ubangidansa mommadou har ya samu kantin kansa.
.
Amanarsa da gaskiyarsa yasa ubangidansa masa tallar yarsa mafi soyuwa a gareshi Safiyyah . Nan take kuwa don shi ma ya daɗe yana sha'awar mallakarta a matsayin mata sai dai tsoro ya hana masa tunkararta. Anyi biki amarya ta tare a nan cikin gidansu tare da sauran yan uwansa maza. Shekarar su ta farko ta haifi yarsu Aisha, daga nan sai Abdoul wanda tsakanin sa da Aisha shekara uku ne, daga nan kuma Safiyyah tayi haihuwa bakwai wanda ya cika su tara gaba ɗaya. Duk abinda Alh Aboubakar ya tara akan karatun Yaransu yake karewa, makaranta mai kyau yake tura su, duk da kasancewar daga shi har safiyyah ba suyi wani karatun zamani ba hakan bai hana Yaransu samun sakamako mai kyau ba don kullum suna musu addu'ar samun nasara.
.
Abdoul na da rauni ɗaya 'yan uwansa, baya son abinda zai ɓata musu, burinsa farin cikinsu sannan yana hakuri da duk wani mai son su. Wannan raunin da kuma kalaman Halima ya hana shi ɗaukan muguwar mataki akan Agaysha don duk abinta bata wulakanta su sai da in shi ta zage su a gabanshi ko tayi amfani da kissa ta hana masa yi musu wani abin arziki. Karar da wayarsa tayi yasa ya dawo daga duniyar tunanin da yake. Share hawayen da ya gangaro masa yayi sannan ya ɗaga wayar. "kun iso? Toh gani nan" Ya faɗi yana ɗaukan mukullin mota. Fita yayi dasu zuwa Assemblée, Auberge Mourna ya tsaya inda ya kasance gidan abinci mai lamba ɗaya. " wannan rowan abinci har ina, salon kada mu gaisa da Madam ne ko" faɗin Ɗahiru ɗan jihar Kano. Dariya Abdoul yayi yace "kun san tayi nauyi. Muna gama waya ɗazu sai ga kiranta. Wallahi oder nayi ɗazu na kai masu" Ya karasa yana istigfari a zuciyar sa. Ya kashe musu kuɗi sun ci sun yi kat sannan suka koma gidansa gaban sa na faɗi. Ba laifi ta karɓe su da kyau kuma ta chanza kaya zuwa shiga na kamala. Har cikin ransa ya ji daɗi don har lemun abarba da kankana ta basu mai sanyi.
.
Hira sosai sukayi da abokansa, sai da akayi magariba sannan sukayi sallama. Ranar duk sai ta wanke laifukanta saboda lafiyayyar abinci tuwo da fakku (malohia murzazza) ta kawo musu karfe shida na maraice. "Ga fa fakku ku ci ku ba Yan Nijeriya labarin daɗinsa" Ta faɗi tana dariya. Kasancewar ta gwana a fannin girki yasa basu so ya kare ba, tas suka tashi da shi suna ci suna santi. Kudi suka aje mata dubu hamsin na kuɗin Nijeriya, zo Kuga murna wajen Agaysha saboda sanin da tayi in ta juya su zuwa cepa zata samu kusan dubu ɗari don ma darajar cepa ya faɗi. Da naira dubu daya za'a baka cepa dubu uku, Yanzu kuwa dubu da dari shida zaka samu. Ko da ya dawo daga rakiyansu ya iske har ta gyara wajen ta baɗe gidan da kamshi. Har cikin ransa ya ji daɗi. Nan suka baje hira bayan ya ja musu limancin isha'i. *** "Yanzu Agaysha haka zamu dinga kallon su Ummu Abieha da sadiya, shekarun Sadiya and kusan talatin fa balle ayi maganar Ummu. Wai bakya jin wani iri ganin su a gida ba aure" faɗin Abdoul ransa ya kai kololuwa a ɓaci.
.
Ace Yaransu mata babu wanda ya fito da niyyar aure. "wallahi kuwa babansu, duk masu zuwa kuma da matan su, da anyi maganar aure matayensu su tada rigima, nima fa abin na damu na." Ta faɗi tana gyara zama. "kin san har Halima ta mutu bata yafe min ba, kar ya zo alhakin ta ne ya ke kama mu. Allah ka yafe mana yaranmu su samu mazajen aure" Ya faɗi yana kwalla. "Aameen ni ko na hudu ne in dai za'a so su ba komi, " faɗin Agaysha "Amma ke bakya son kishiya, kike fatan ayi ma wasu don a auri yaranki. Lallai son kai ya miki yawa" Ya faɗi yana mikewa, don ya fara jin kiran sallah. Kiran sallan ya ki karewa, tun yana Jinsa daga nesa har yaji na bayan gidansu an kira. Leman da ya ji yasa ya taɓa gadon da yake kwance. Jike yake da zufa, da ma ana mafarki mai tsawo ne haka, shi dai har ga Allah bai taɓa ko jin labarin mafarki a bayyane kuma mai tsawo hakaba, tun da ya samu natsuwa da Agaysha, kalaci kawai yayi barci ya kwashe shi kafin ya kai ga wanka. Kallon agogo yayi karfe huɗu da minti biyar, tabbas la'asar aka kira, shi kuwa wani irin barci ne wannan tun karfe tara na safe.
.
Abinda bai sani ba haka kawai Agaysha taji bata aminta da shi ba, ta sa masa maganin barcin da take ɗura ma yaranta in suka ishe shi. Don kar ma ya nemo Halima kafin ta dawo daga wajen bakanta. Abin tambaya anan shin dama ana mafarki a barcin da ba na Allah ba ko kuwa MAFARKIN ABDOUL daban ne. Amsar na wajenku masu karatu Tashi yayi jiki babu kwari, yunwa yake ji amma bayi ya fara isa yayi wanka, gami da alwala. A zaune yayi sallah sannan ya shiga kitchen ya iske tayi tuwo kafin ta fita. A nan ya zauna ci hannu baka hannu akushi. Sannan ya samu karfin gwiwan fita.
.
Gidan Yahai yaje don ya samu rakiyansa, nan ma ba wani zama yayi ba suka ɗauki jiki zuwa gidan iyayen Halima. Bayan an musu iso, sun gaisa da mahaifinta wanda murna ya hana shi ɓoyewa. Baffa ya faɗa masa komi dangane da alakar Halima da Abdoul banda rabuwansu. Nasiha sosai yayi musu musamman akan aje mace fiye da ɗaya a gida, mahimmancin hakuri da adalci. Sunyi murna kwarai da karamcin dattijan arziki. Tsoron Abdoul ɗaya yanda Halima zata amshi Zancensa, hakan ya sa Yahai ya bashi shawara da ya bi ta hannun iyaye kawai.
.
Yasan dai yana da fada a wajen iyayenta maza shi yasa ya fara da mahaifinta. Bayan tafiyar su Abdoul ya ɗaga waya ya kira Baffa. Nan ya ke faɗa musu zuwan Abdoul da kuma yanda suka kwashe. "shi Abdoul ɗin ne yazo wajenka?" Ya tambaya cike da mamaki. Dariya yayi sannan ya bashi amsa da cewa "shi fa, ko minti uku basu yi da fita ba. Ga ma tsarabar da ya kawo ma yara nan. Yace zuwa Asabar kaga jibi kenan zai shigo wajenku". "Allah ya kaimu, yanzu muka dawo asibiti Halima har oxygen aka sa mata da muka isa, mun aza ma rai yayi halinsa sai mommansu ta nace akan Halima bata rasu ba. Amma Alhamdulillah har drip ɗin da akasa an cire kafin in dawo. Ban kira ku ba don bana son hankalin ku ya tashi ne" hawayen da suka zubo masa ya goge don ya san da Ace Halima ta rasu ko iyayenta baza su kai shi rashin ta ba, in bai yi karya ba ai cewa zaiyi ya fisu sanin wacece Halima da darajan da Allah ya bata. Samun irinta sai an tona.
.
"Allah ya bata lafiya, gobe bayan Jummu@ zamu zo mu duba ta, in kuma an sallame ku shike nan" Ya faɗi bayan ya gama tunanin anya a duniya akwai sauran masu riko da zumunci irin yayansa. "Toh shike nan, Allah ya baku iko, ya sanya Alkhairi tsakanin ta Abdoul in babu ya musanya mana" "kai baffa ba bu ko yar kunyar nan. Yar farin ku ce fa kar ka bari a ji kana kwararo addu'a fa" mahaifin Halima ya tare shi da tsokana, nan sukayi dariya. *** Ko da su Abdoul suka isa gida Agaysha ta dawo tayi yan birne birnenta wanda aka tabbatar mata da in har Abdoul ya shigo gidan toh sai yanda tayi dashi. Suna gab da shiga gidan Yahai ya ja shi gefe yace "karanta addu'ar shiga gida haɗe da suratul ahad, ba wani jinsi na shaiɗan da zai kasance tare da kai.
.
Kayi sallama kuma tun daga bakin kofa kar ma Ace sun rako ka zuwa bakin falo. Ire iren sakacin nan ke sa tsafi yai tasiri a gidan mutum. Rashin yin addu'ar fita gida da shigowa " Ba musu ya karanta, suka shiga da sallama. A ciki ta amsa tana yatsine fuskanta kamar taga kashi. Cikin tsawa ta ce " Daga ina kake na dawo baka nan" Ta tambaya kamar wani ɗan ta da take shirin mazga. "Gida na ya zo fa gashi na kawo miki shi har gida, dafatan banyi laifi ba" Yahai yai saurin amsa mata don ya san kaidinta, Allah kaɗai yasan tsafin da tayi.
.
"Auho! Kasan akwai wata karuwa da take neman rusa mana zaman lafiya a gidanmu, wallahi na aza wurinta ya je don yau da asuba sunanta ya tashi da shi a baki, tsoron zuwansa wajenta na bashi maganin barci a tea, kasan abinda ya ban mamaki" Ta karasa tana jefa ma Yahai tambaya, dama ita haka take da son nuna isa, in tayi abu gani take wayonta ne ya kaita ga hakan. "Sai kin faɗa madam" "ko da na fita kuka yake yana kiran Halima ta rasu, tsakanin ka da Allah ko a littafi ka taɓa karanta mutum na barci yana mafarki Alhali barcin magani ne, nayi Alkawari sai na hukunta yarinyar nan, duk tsafinta sai na hukunta ta" Ta karasa tana kara yamutsa fuska kamar Halima ne a wajen. "gaskiya shi yasa na gagara yarda da ita, a sani na ke kaɗai ce aboki na ke so, kwatsam ya zo min da zancen wata Halima.
.
Allah raba nagari da mugu, mtsw! Mata basa kyautawa wai takan namiji su siya wuta da hannunsu, sai ki ji suna malam malam yoh ko da ayar Kur'ani akai lakani dashi ai bazai tashi da ga shirka ba. Annabi ya faɗi su zasu fi yawa a wuta. Kuma ba komi bane zai kai matan zamanin nan wuta sai son mallake ɗa namiji. Allah ya shirye ta da sauran masu yi " Fuuuuu! Ta shige ɗaki ba tare da ta amsa aameen din ba. Nan ya ja Abdoul kofar gida suka tsara yanda komi zai kasance. Ya kara nanata masa kar ya yarda tasan aikinta bai ci ba, tunda hutun sa ma ya kare, ya lallaɓa ta kafin ya wuce.

0 comments:
Post a Comment