MAFARKIN ABDUL Part 9
.
Ranar Asabar tun da safe Abdoul ya shirya ma tafiya. Karfe tara Yahai ya iso suka ɗauki hanyar Niamey. Duk kayan marmarin da suka gitta mawa sai sun tsaya sun siya. Sannu a hankali suka isa, hiran da ya ɗau hankalinsu yasa basu ga wani nisan tafiyar ba. Sun isa sun taradda an sallame Halima har ta dan warware. A falon Baffa aka sauke su inda shi ya fara tarbonsu kafin kowa. Bayan sun gaisa ne ya kalle su yace "ko zan san me ke tafe da ku?" Duk da sunyi mamakin tarbon arziki da suka samu, amma basu yi tunanin zai jefe su da wannan tambayar ba. Sunkuyar da ka Abdoul yayi sai Yahai ne ma da yayi karfin halin tattaro natsuwarsa ya ce "Baffa mun zo neman izinin ka ne, don neman auren Halima" Shiru ya sake ratsa wajen. Zukatansu nai musu ki ɗan lugude don basu san ko zai amince ba. "Ba zan ce komi ba sai Halima ta faɗi ra'ayin ta, in ka samu ta amince ka gaggauta turo min waliyanka, in kuwa bata amince ba ina rokon ka arziki kar ka sake zuwa min gida, na barku lafiya" yana kai aya ya tashi ya shige gida. Sun zauna ma kamar minti goma sai ga Halima ta shigo da kawarta Shamsiyya Ummu A, fuskarta a sake, amma ko kallon ɓarayin Abdoul bata yi ba. Hankalinta gaba ɗaya ta ba Yahai. Sun gaishe shi, sai shamsiyya ta kalli Abdoul ta ce "ɗa na! Fatan dai kana lafiya" da murmushi mai nuna tsantsan farin cikin an san da zamansa ya ce "Mommy ina fa lafiya, nayi zunubi mai girma, don Allah ki sa baki a yafe min kinji" Ya faɗi yana marairaice fuska. Jin duk sunyi shiru ya sa ya fara basu labarin duk abinda ya faru da ya koma gida har zuwa mafarkansa da yayi masu ban al'ajabi. Shamsiyya dai da ka kalle ta kasan ta na cike da tausayin sa yayin da Halima tayi ko oho, ganin sun tsare ta da kallo ne alamun suna son ji daga gareta ne ta muskuta ta ce "Abdoul mafarki ba gaskiya bane, Allah ne yake aikowa bawa wasu lamarika daga cikin buwayarsa, domin ya haskaka masa wata baiwa tashi wadda zai gane rayuwa da abinda yake cikinta.... Idan bawa yayi mafarki mai dadi kona ra'ayinsa sai yayi Sadaka kamar yadda yazo a hadisi Majma'ul Bahraini cewar "Annabi yace kunemi yayewar bakin ciki, da bacin rai wajan yin Sadaka " hardai zuwa karshen hadisin, shiyasa akeso bawa ya kasance mai yawan addu'a aduk lokacin dazai kwanta barci, sbd yanayin mafarkin dazai iyayi, idan mai dadine sai yafadama mafi kusanci dashi kuma abokin sirri agareshi amin domin yatayashi rokon Allah nake alheri akan mafarkin.
.
Idan kuma mafarkin abin tsorone kokuma tashin hankali wanda zai haifar da bacin rai, ana so kana farkawa ka nemi tsari ka tofa ɓarayin hagu sannan ka chanza kwanciya, shima dai mutum sai yayi Sadaka yanemi tsari akan abinda yagani acikinsa, yanemi kuma zabin Allah na alheri akan mafarkin, yazama mai sirri akansa wajan barwa cikinsa sirrin mafarkin, tosai Allah yaji tausayinsa kuma yayi imani tare da tawassali da Annabi wajan zabin alherinsa. Wannan bayani kadan kenan daga cikin abubuwan da Mafarki yakunsa, Allah yasa mudace da rabo mai amfani adukkan rayuwarmu Amin. " tana kaiwa nan ta tashi tsam sai zuwa cikin gida. Dukkansu ba wanda kansa bai ɗaure ba don a zahiri sun ga tsantsan rashin bawa lamarin mahimmanci.
.
Sunyi zugum na wasu yan mintoci chan shamsiyya tayi karfin halin magana inda ta ce "Kun san ba lafiya ta cika ba, jiya aka sallamo ta daga asibiti, mu ɗan ɗaga mata kafa. Ɗa na kasan dai kai me laifi ne sai ka san yanda zakayi ka wanke kanka" Duk sukai dariya sannan suka tambaye ta jikin Halima inda ta amsa musu da taji sauki sosai. Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani sukai sallama suka tafi. Wasa wasa se da akayi wata biyu Abdoul na zaryan neman sulhu amma Halima ta kafe akan ba'a haifi namijin da zai wulakanta ta ba, nan ta maida hankali a aikinta ba ta saurari zancen ba. Yanzu ma zaune take ya zo, momma ta kora ta dole taje gare shi, tsayuwa tayi a kan shi, bata ce masa komi ba. Kiran da taga ya shigo wayarta ne ya hana mata cewa komi don niyyar ta kwance masa rashin mutunci . Ɗaga wayar tayi da sallama. Maimakon a amsa sallama sai saukar ashar taji, neman tsari take da ga sheɗan. Faɗin da tayi "Abdoul yafi karfin ki jaka" nan ta fahimci wacece kuma.
.
Shiru tayi ma wasu dakiku sannan ta ce "kin kira a sa'a ma, tun ɗazu ya ke jira na fitowar kenan se ga kiranki, gashi ku gaisa" Ta karasa tana mai mika masa wayar fuskarta cike da murmushi.
.
"macuci, azzalumi, annamimi, wallahi in baka tuba ba wutan Allah sai ya ci ka" Ta faɗi tana haki bayan muryarsa ya sauka a dodon kunninta. Murmushi kawai ya saki ya katse kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya. "bani wayata, meye nufin ka na kashe min wayar gaba ɗaya" Ta faɗi a tsiwace, kallonta yake yana so idanuwar su su haɗu amma fir ta ki. "Ki zauna, magana nake so mu yi" Ya ce yana nuna mata kujera. Zama tayi babu gardama. "Halima, L'erreur est humaine, (ko wani mutum na tare da kuskure) ki yi hakuri s'il vous plaît Il faut me pardonner. (don Allah ki yafe min)" Ya faɗi yana rusunawa. Ganin tayi shiru ya sa ya cigaba "Nasan ba a son rai mafi yawa daga cikin mata ke auren mijin aure ba, burin kowacce mace ta kasance uwar gida, amma ina zamu kai kaddarar rayukanmu. Allah ya faɗi a cikin littafi mai tsarki LIKULLI AJALIN KITAAB, wato ko wani kaddara a rubuce ta ke. Ba wai zan aure ki don in cikata giɓin da nake da shi a gida na ba, kin san dai ina son matata, toh ba wai zan aure ki don son nata ya ragu bane, sonki da kaunarki yasa nai sha'awar aurenki, don in yi bautan Allah in nemi yardansa.
.
Bayan wannan banda wani dalili. Bana so in miki karya shiyasa kika ga nayi shiru akan zancen laifin da nayi Il faut me pardonner." tsare ta yayi da idanu, burinsa su haɗa ido amma fir ta ki yarda. Shiru sukayi na kusan minti biyar, zuciyar ta na rawa kamar pendulum, chan dai ta tuna isa da mulki da Agaysha ke Gwadawa akan Abdoul na ta ne ita kaɗai yasa ta tsaida zuciyarta ta ce kamar bazata magantu ba "ka turo ayi magana" Ta na faɗi ta shige cikin gida. Murna a tare da shi ba'a magana, sai da ya kira baffanunsa suka tsaida masa da ranar da zasu je sannan ya bar falon da aka sauke sa. Itama da ta shiga ciki ta faɗa ma momma abinda ta yanke ta ji daɗi sosai. Nan suka yi addu'ar Alkhairi amma kowannensu zuciyar sa kal da murna. *** Kamar yanda suka yi alkawari haka suka zo da zancen neman aurenta.
.
Iyayensa sun yaba da karamci da halin girma iri na iyayen Halima. An tsaida auren bayan wata uku kamar yanda Halima ta roka sanda momma ta tambaye ta. Tun da lokacin wani sabon shaukin kaunar juna ya shiga tsakaninsu. In baya gari ko Kasar suna manne da juna a waya. Agaysha tayi asirin, tayi tsafin amma kullum lokacin bikin matsuwa yake duk da bokanta ya tabbatar mata baza'a taɓa auren ba. Yau ma ta shirya zuwa maraɗi don ganin wani boka, sarkarta da ammbasadan Nijar a Saudiyya ya ba Abdoul ne ta siyar, tayi karyan zuwa ta'aziyya ta ɗau hanyar maraɗi. Sanda layi ya kai kanta ta shiga don ganin sa. Kallo ɗaya yayi mata ya kwaɗaitu da ita. Nan ya ce mata "Halima ba ko mi bace face abin da zai kawata MAFARKIN ABDOUL, yanzu dai ɗan tsatsuba ya na son ya ji kalan ruwanki, da shi zai halaka Halima" " Ruwa kuma ya mai biyan bukatu" Ta tambaya cikin rashin fahimta. "eh! Kwaye min wannan zanin in ɗiba" ba musu ta Kwaye, ta tsorata da ya cire zanin da ya ɗaura a kugu amma zuciyar ta da ta tuna mata shike nan kafin ta koma an hallaka Halima da auren saura mako ɗaya ya sa ta sakin jiki.
.
A wahale ta fito runbun boka ta sa mu abin hawa, Gidan kawarta Taghayshuwane ta je, nan ta huta washe gari ta koma zindar. Shiru! Shiru tana jiran a ce mata an fasa aure amma sai shirye shirye ake, ta kira boka yace shi dai yasan baza'a yi auren nan ba, ta kwantar da hankalinta ko an taru za'a fasa. Hakan yasa ta ji sakayau fatanta a fasa ranar ɗaurin aure don zai fi musu zafi. BIKI BIDIRI .... Karfe goma na safen 13 ga watan febweru 2016 a Nijar, Nijeriya, Kamaru da Chadi aka ɗaura Auren Abdoullah da Halima bisa ga sadaki mafi karanci. Anyi shagulgula sosai inda mawakiya Sa'a Vocal ta wake ango da amarya. Hanifa creations and couture suka fito da amarya da ango da zafafan ɗinkuna inda mutane sukai ta santi. Ranar Lahadi da safe aka yi walima a gidan ta da ya kama mata a nan Niamey.
.
Agaysha bata yarda da an ɗaura auren ba sai da aka kai amarya gidan iyayen mijinsu da maraice sannan taga sun dau hanyar Niamey. Nan ta ɗau waya ta aika ma Abdoul sako kamar haka "Ango mijin Amarya, ina maka murna, na ba ka wata uku kyauta kasha amarci lafiya" ko da ya karanta sai da yai dariya a ransa cewa yake "wannan bata san abinda ke damunta ba" nuna ma Yahai wayar yayi ya karanta. "mtswww ! Wasu matan fa na kwafsawa, akan wani dalili zaki bar ma wata mijinki wata kawai don ya auro ta da yaudaran kai zata ginshe shi. In kaga an ginshi juna amaryar bata iya takunta bane. Ai ta baku daman fahimtar juna a ne amarya kuma ta kafa gwamnatin ta da kyau. Aminina kasha amarci lafiya" Ya karasa suna masu tafawa.

0 comments:
Post a Comment