Kwanci tashi ba wuya har Meenalle ta gama Secondary school ...
Alokacin ne Mus'ab ya fara nuna mata abunda ke ranshi ...amma fur taki yarda ...har ta manta da wani aure a rayuwarta ...duk wata zaa kaita garinsu gurin su kaka da mamanta har lokacin mamanta bata koma gidansu Musa ba ....haka Musa ya kasa Hakura da Meenalle kullun cikin bala'i yakewa ubanshi ya nemo mashi matarshi ...su duka hankalinsu ba kwance ba ...
Wani zuwa da tayi har bangazar musa tayi amma sam bai ganeta ba ...don kwata kwata ta canza hutu da jin dadi sun canzata. ..bara ka taba cewa diyar hausawa bace
Duk zuwan da zatayi sae ta shiga gidansu Ma'aruf haka zaa ce mata baya nan sannan babu mai numbershi tunda ya tafi bai nemi kowa ba ...haka zata ci uban kukanta har ta taho ...
Shima mus'ab kokarin cusa kanshi yake amma hakan bai samu ba ......
Lokacin da waec and neco. ta fito a lokacin Alhaji Abubakar ya ce zaya fitar da ita kasar india karatun lawyer ....Alhaji Sadee ya yarda don har lokacin bata san waye ubanta ba ....
Cikin saa ta samu Visa cikin sauri ...Su biyun suka kaita indiya tare da mika amanarta gurin wani lecturer amininsu dake can ....
°°••°°
Batayi wata uku ba ta goge wata wayewa tazo mata ta kara kyau da diri duk wanda ya kallu meenalle alokacin sae ya kuma kallonta
Kyakykyawa first class ...duk fadin makarantar ba wanda bai san MMA _Meenat Ma'aruf Abubakar_ ...
Sun fito daga lecture su kusan Uku a jere ...Shamy ta dauki ihu tare da fadin ....Wow *Mr M*...da sauri suka kalli wani ginin dake kallon makarantar .....
Yana rike da glass cup hannushi guda dauke da magzine sannan idonshi sanye da farin siririn glass ....
Feena ta daka uban tsalle tana fadin Yaushe ya dawo ...
Shamy tace jiya sajan Sadam ke fada man ...Kai *Mr M* ji yanda ya kara uban kyau ....Wallahi Ina mutuwar kaunar ...nayi missing dinshi wallahi.....kissing hannunta tayi tare da Nunashi
Sae lokacin Meenalle ta da ido ta kalli wanda suke maganar akae ....
Tafi minti ashirin tana kallonshi har sae da soofy ta buga mata littafi a kai sannan ta sauke ajiyar azuciya
Soofy please meye real name dinshi ....ta fada a hankali ...
Tsayawa sukayi suna kallonta cike da mamaki. .....karo na farko kenan da suga Meenalle a wannan yanayin ....kamar tayi kuka tace....Please i need to know ....
Shamy tace ...lallae MMA har kin kamu da sauri haka ...ina cika bakin ?...injin yau kin yarda akwae mutumin da yafi Maikamshin kyau ....
Please ku fada man dan Allah ...ta kwantar sa murya ...
Soofy tace ...kyaji da gulmarki yadda kike da class wancen babanki ne a wannan fannin ...sunanshi *Mr Ma'aruf* .....
Ihu ta kurma ta ruga da gudu dakinsu ........
.
Wae Meena me ya sameki kike ta murna ko dae Dady zaya zo .....Shamy ta tambayeta. ..
Ido ta waro tare da lumshe ido. . Sirrin Zuci ne ..ba bukatar ku sani .....tana gama fada ta shige toilet ...wanka tayi sannan ta fito ...ta dade tana shafe shafe ...sannan ta dauko wani sabon turare cikin jikkanta ta fesa ta dauko kayan fulani ta saka tare da takalmi mai tsinin ...babu abunda bata saka ba cikin kayan fulani har abunda suke daurawa a kai sae da ta daura ....ta fito ....su shamy suka bita da kallon mamaki har ta fice daga makarantar ...
Ba tare da shakkar komae ba ta shige gidan Mr Ma'aruf ....
.
Da Sallama ta shige falonshi ....ba kowa ciki sae kamshi dake tashi .....bisa kujera ta samu ta zauna ....ga wani tafkeken hotonshi manna jikin bango a gefen dama. ...tana kara juyawa ta hango abunda ya saka dole fararan hakoranta suka fito ...photon Meenalle ne kafe a gefen haggu anyi rubutu da gold a jiki ...Meenatou ...amma duk ya farfashe..
Bata fuska yayi lokacin daya shigo falon ....
Me kike bukata ...ya fada lokacin da ya dauki remote ...
Shiru tayi tare da kura mashi ido ...jin shirun yayi yawa ya saka ya dago da kanshi .
Suna hada ido yayi saurin janyewa ....
Hanya ya nuna mata tare da fadin ...idan kallo ya kawoki ga kofar da kika shigo a bude .....
zuwa nayi mu gaisa dakai ...kullun Sae na ganka amma baka taba ko da kulani ba irin dan kallon ma da akeyi a kauda fuska idan an kamaku baka yi man ...ko baka kula mata ?..
Ido ya dago yana kallonta sannan ya maida kallonshi ga tv ....
Allah sarki ashe magana kadan kake kayi shiru ....ta sake fada a hankali .....wae ma dan rowa ko ruwa bara ka bani ba nazo gidanka...ko ka bani baran karba ba....Mai rowa dae dan wuta
Da sauri ya kalli photon Meenalle ..ya tuna lokacin da tazo gidansu ta zauna tana zuba mashi surutunta .. yana rike da ice cream take ce mashi...Gidanku fa nazo Mai kamshi dan rowa bara ka bani ko ruwa ba ..ni bana ma shan abunda kake sha..ko ka bani so daya kawae zan sha ..shima sae kace man please sannan. ...Maikamshi me rowa fa dan wuta ...
itama photon ta kalla tare da kallon fuskarshi ...ga mamakinta sae taga hawaye na zuba ....
Da sauri ta dawo kujeran dake kusa dashi tana kallonshi cikin rawar murya tace. ..nayi wani abu daya bata maka raine Mr Ma'aruf?..please ka yafe man ...
wannan karan ma da sauri ya kalleta ...kije please ..ki tafi ...ya fada a hankali ...
A hankali ta mike ta juya tana tafiya kallo ya bita dashi ...yana ganin zata juyo yayi saurin dauke kanshi ....
••°°••
Har kusan sati daya bata kuma ganin Mr Ma'aruf ba inda yake zama .suna fitowa daga lecture ta ...ta bar su Shamy ta shige gidanshi ...
Falo ta zauna tana jiranshi ...amma har kusan minti 39 bai fito ba ...sae dae tana jin nishi sama sama yana fitowa daga dakin dake facing dinta .....tun yana fitowa a hankali har ya fara fitowa da karfi ....zaune tayi tana son taje ta duba kuma tana tsoron ...
Jiki ba karfi ta mike tana Sanda ta tura dakin ...Ganinshi tayi kwance kasan tiles ...hannunshi rike da kirjinshi ....da sauri ta ida bude dakin ta dago kanshi tare da daurawa saman kafarta tana girgiza shi ...
.
Mr Ma'aruf me damunka ...ta fada a rude ...
Lunshe ido kawae yake ...ya kasa budesu gaba daya....sannan bakinshi ya kasa furta wata kalma
Kuka take iya ranta ..tare da girgiza shi tana kiran sunanshi ....
Jin kukan yake cikin ranshi ..sannan so yake ya bude idon yaga wacece amma sam ya kasa ......
Ma'aruf ka tashi dan Allah ....
Please Ma'aruf ka bude idonka don Allah ka kalleni ...nice Meenallen Maikamshi ..ka tashi bana so na rasa ka wannan karan ....
Yana jin Lokacin data fadi Meenalle kokari yake ya bude idonshi ...amma ya kasa ..bakinshi kawae yake motsawa. ..ita kadae ke iya jiyo sautin ..Meenatou ...da yake fada ....
Rungumeshi tayi tana kuka ...sannan ta fice daga dakin ganin baya numfashi ta kira security dinshi suka sakashi mota aka wuce dashi asibiti .....
Emergency aka shiga dashi ...abu na farko da aka fara bukata shine jini .....Har lokacin Meenalle kuka take .....
Amma tana jin ance zaa kara mashi jini ta mike tace a debi nata ...
Doctor yace ..Madam baa Fiye dibar jinin mace ba ...amma akwae jinin fresh anan sae a sanya mashi ...
Aa Ku debi nawa ku saka mashi na yadda ...ta fada tana kuka. ..
Kiyi hakuri ..wanda muke dashi normal yake ...
Bana so a gauraya mana jini da na wani ...koda jinina idan kuka diba zaya kare na yarda ki dauka indae Ma'aruf zaya tashi ....
Ganin ba yarda zaayi da ita ya saka aka auna nata cikin saa tana da isasshen jinin da zata bashi ...nan da nan aka kwantar da ita gadon da yake kusa da nashi aka diba .....
Kafin a saka mashine suka dibi nashi jinin jikinshi aka auna sannan aka kara mashi da na Meenalle ...
Har 10 dare bai farka ba ...secutity din yace ta tafi zaya kula dashi ...amma hararan data zabga mashi itace amsarshi ....
Anan ta kwana ...ganin har da asuba shiru ya saka taje ta samu nurse din tana kuka ta fada masu ...ce mata sukayi karta damu zaya iya tashi ko da yaushe tayi hakuri ....
°°••°°
Duk wani test da zaa mashi an gama ...doctor ya kira Meenalle kamar yarda tace mashi ita matarshi ce ...
Bayani ya mata mijinta nada Kidney problem ( _Nephropathy_) kuma yayi attacking dinshi sossae dole a saka shi adjoining room zuwa wani lokacin kuma baa bukatar kowa yaje inda yake akwae nurse. din da zasu dinga kula dashi ...idan kuma har lokacin da suka yankar mashi baiyi ba to gaskia sae dae ayi mashi transplant na kidney ...
Yarda ta dinga kuka ...shi kanshi likitan sae da yayi nadamar fada mata ...
Wata nurse ta tambayi doctor din ko mai ke saurin kawo ciwon ...
Rashin bacci na saurin haifawa da mutun ciwon koda ...ke har ciwon sugar da ciwon zuciya duk rashi isasshen bacci na kawosu .....amma indae mutun zaya samu isasshen bacci to lalurar zata iya gushewa ...idan kuma har tayi illar da sae an mata aiki to bayan anyi insha Allah zata gushe ...
Harta ta ruwa gurbatattu zaka iya daukar ciwon koda ...don haka ya kamata mu dinga kula da rayuwarmun ....
Sannan rashin shan isasshen ruwa ..mussaman lokacin zafi. ...sannan rike fitsari. ..shima yana nakasa koda ...sannan yawan cin gishiri...sannan yawan cin nama shima yana kawo matsalar koda ....haka kuma yawan amfani da magungunan saukaka zafi ko antibiotics ..sanna yawaita shan lemuka masu gas ...kamar coca cola ...lacasera da ire irensu ..
••°°••
Kwananshi 5 A gurin amma ko fardadowa baiyi ba ...duk da an hana kowa zuwa gurinshi amma Meenalle na makale ta glass kullun ...abinci ma sae da likitan yayi mata da gaske take ci ...
Maganar makaranta kuwa ta manta da labarinta .....sae a kwana na 6 ne Ma'aruf ya fara bude idonshi ....lokacin tana tsaye inda take zama ta hango yana motsa bakinshi .....
Da sauri ta matsa gurin .tare da dafa glass din gurin tana hawaye mai dauke da murmushi ....
..Meenatou ..yake fada a hankali .... Why Meenatou ? Me ya maidoki rayuwa. .ko kinzo kiyi proving abunda kike aikatawa ...Karki kuma zuwa inda nake ...i hate you Meenatou ...Bana son ganinki ...kin cutar da zuciyata da yawa...idan ina ganinki baran iya rayuwa ko kinzo ki kasheni ne Meenatou ..na rokeki karki bari idona yayi tozali dake in dae har soyayyar yarintarki gaskiyane ....hawaye ke bi ta gefen idonshi kamar an bude fanfo ...yayinda da kirjinshi ke sama da karfi
Baya tayi da sauri ta jingina da bango ...kanta ya fara juya mata .....
.
Da Gudu ta fice daga asibitin ...dakinsu ta koma ta fada saman carpet tana kuka ....su shamy dake nemanta sukayo kanta suna tambayar inda taje ..ganin ba magana zata masu ba ya saka suka kyaleta sae ta koma ....
Bata koma Asibitin ba sae da ta tabbatar ya koma bacci ..sanna taje tana lekenshi tana hawaye ...ji tayi an dafa kafadarta ta juyo da sauri.
Ganin Nurse din dake taimaka mashine ya saka ta goge hawayen ...
Kiyi hakuri Mrs Ma'aruf ..mijinki zai samu sauki Soon ....
daga mata kai tayi tare da share hawayen ...taji dadi sossae ko ba komae yau an kirata da Mrs Ma'aruf .....
Murmushi tayi mata sannan tace ..doctor yana bukatar magana dake ....
Binta tayi suka shiga office dinshi ...ya zaune da uwayen takaddu gabanshi ....yace ta zauna ....
Mrs Ma'aruf nasan dae ke musulmace ..kuma zaki yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau. ....
Kallonshi kawae take tana hawaye ...so take ya fada mata kai tsaye abunda yake son fada ...amma sae da ya mata waazi da yake balarabene sannan ya fada mata gaskia sae sun wa Ma'aruf dashen koda ..don duk yarda suke tunanin abun ya wuce nan .....
Tun da yake maganar take kuka har ya gama sannan yace dole ta kira yan uwanshi domin ciki wani zaya bashi kidney daya ...
Meye amfani doctor?
.komae zaa bukata na yarje a cire nawa indae Ma'aruf zaya tashi ...ko da zuciyata a cire a saka mashi ..Doctor nafi sonshi da kaina a duniya ...ku shirya duk abunda zaa kashe zanje na kawo ...ina so ayi mashi aiki ya samu sauki da wuri ....tana gama fadar haka ta mike tana kuka ...
Dady ta kira tace tana bukatar kudi masu yawa ...babu musu ya turo mata 10 million. ..da ta ga kamar bara su isheta ba ta fitar da sarkar gold dinta da Alhaji Abubakar ya sawo mata da wata sallah ...ta sayar naira million 5.5
Wanshekare da safe ta hada kudin ta kai masu ...naira million 9 kadae suka amsa suka bata sauran. ..ko a ranar sae da doctor yayi encouraging nata aka ta kira wani ko mahaifiyarshi ta bashi wanda baya da wata damuwa a tare dashi ...amma ta saka mashi kuka ...dole suka fara preparing cire tata daya a saka mashi ...duk wani aune aune da yakama suyi sae da sukayi ...suka tabbatar idan an cire tata daya wadda aka barta zata iya fuctioning sossae a jikinta ...sannan aka shiga dasu dakin tiyata .....
*4 Hours*
Aka fito gangaro su sannan aka kaisu adjoining room su biyu aka jerasu ......
Ta fishi jin jiki sossae don har sae da ta kwana biyu bata farfado ba ...shi kuwa kwana daya ya farka. ..tana kwance kusa da gadonshi ...ya kura mata ido. ...har doctor ya shigo. ....
Ya mashi alluran da ya kamata sannan ya fice don baa cika son a takura masu da magana ba ....
Ranar da ta farka tana bude ido suka hada ido ...murmushi ya sake mata tare da lumshe ido ...ita murmushin ta maida mashi ..sannan ta kawar da kanta gefe guda ta goge hawayen dake neman zubo mata .....
Lokacin da likitan ya shigo ..ya sameta ta farka shi kuma yana bacci ....
Murmushi yayi mata yace ...Congrat Mrs Ma'aruf ...yanzu hankali ya kwanta ya samu sauki ko ...
Murmushi tayi ta lumshe ido....a haka ya mata allura ya fice ...
••°°••
Satinsu biyu acikin asibitin suka samu sauki ...sae dae har lokacin suna daure da belt don sae yayi wata shidda zaa cire ....
Haka har lokacin Ma'aruf bai san taka maimai wanda ya bashi kidney ba. ..don tun kafin ayi aikin ta roki Doctor din da kar ya fada mashi ita ta bashi ....
Meenalle na kwance bisa gado Ma'aruf ya fito daga toilet dinshi sanye da jallabiya ...kallonta yayi dauke da murmushi yace ...
Fateema ya jikin ... _kamar yarda ta fada mashi sunanta_
Murmushi tayi tace Alhamdulillah....
Good ...ga abinci nan an kawo ki tashi kinji ko ...
Tashi tazo yi amma ta kasa ...ya matso tare da dagota ta ya jingina ta da kirjinshi kafin ya dauko filo ya saka mata abayanta ya janye jikinshi ...yana fadin Sorry Sister kinji
Zama yayi yana bata abincin har sae da ta dauke kai sannan ya tashi yayi sallah ....
Da yake ya fita lafiya kuma doctor yace mashi tare akayi masu aiki. ..shi yasa yake tausayinta da yaga shi har ya samu sauki amma ita ba wani sauki sossae ....
A wani bangaren na zuciyarshi ...yana jinta sossae matsalar ya riga ya saka mata tsanar soyayya ....
Idan tana bacci bashi iya dauke idonshi a kanta ...haka idan yana bacci bata iya dauke idonta daga kallonshi ...
Ana Gobe zaa sallamesu ...doctor ya shigo ....Ma'aruf yayi ta rokanshi akan kar ya bar asibitin sae ya fada mashi wanda ya bashi koda ...
Doctor ya saci kallon Meenalle yaga idonta na kanshi ...sannan ya mai da kallonshi ga Ma'aruf ....yace ...gobe zan fada maka ...ya fice ...
Yana fita ta bi yanshi ta sameshi da kuka kar ya fada mashi ....
Yace Mrs Ma'aruf mai yasaka baki san yasan ke kika ceceshi?
Bakomae doctor dan Allah karka fada mashi ..
wannan ba hujja bace Aminatu ...dole a nuna mashi wanda ya bashi ...
Zaa nuna mashi amma bani ce zaa nuna mashi ba doctor
.
Me yasa bake ba Aminatu Abubakar? ...sannan wacce kike so a nuna mashi ...
Doctor ni zan kawota ..kawata shamsiyya ita nake so ka nuna mashi ..ka taimakeni ...ta fada cikin kuka. .
Me yasa to Mrs Ma'aruf?..
Wannan Sirrin zuci ne ....
Wayarta ta fito ta kira Shamy tace ta zo ta yanzu ta mata kwatancen asibitin da suke .....
bata fi 10 mints ba sae gata ...tana zuwa doctor ya mata bayanin abunda suke so tayi ...
Dadi kamar ya kasheta don dama tana mutuwar son Mr Ma'aruf ..kuma ta tabbata idan aka ce ita ta bashi to babu abunda bara ya iya yi mata ba ....don doki kasa barin asibitin tayi sae da wata nurse tace mata baa kwana ba wani dalili sannan ta tafi ...
°°••°°
Murmushi ya sake yana kallon Meenalle sannan yace ....yau zan huta da tashin dare da kukanki ..
Hararansh tayi lokacin da take neman maida hawayen da suka zobo mata tace ...ni kuma zanyi kewarka ..
Nima ai zanyi kewarki Fateema wasa nake maki kinji ko ...karki bari hawaye ya kara fitowa daga kyawawan idanuwannan ..
Lumshe ido tayi tace ...Da Zan iya da tuni na tsaidasu Ma'aruf ......
Yauwa ga doctor nan ...ya fada lokacin da ya mika mashi hannu ...lokaci guda kuma ya bata rai yana cewa ...ya na ganka kai daya ..tana ina ?
Doctor yayi murmushi tare da daga murya yace ...Mrs Ma'aruf ...
Da sauri Meenalle ta kalleshi lokacin da gabanta ya yanke ya fadi ...ganin ya kira wata da sunan da ta dade tana mafarki...Sunan da tun tana karama ta so ta amsa sunan ...hawaye suka zo mata. ..tayi saurin Mikewa daga kujeran da take ta juya da niyar ta bar dakin...
Hannunta taji an rike da sauri. ..ta juyo tana kallon Wanda ya rike mata hannu ....
Kanta ta sadda ta kasa cigaba da tafiyar ganin Ma'aruf rike da hannunta. ...
Ina zaki Fateema bara ki tsaya kiga wadda ta taimakeni ba ...lokacin da lumfashina ya nemi ya bar jikina dalilin wata?....ya fada yana kallonta
Shamy ta shigo taci uwar kwalliya ...
Meenalle ta girgiza kai tana toshe bakinta ...
Ma'aruf yace ..Doctor baka ga wata yarinya ba Wadda ta kawoni Sunanta Meenatou ..ko ba ita ta kawoni ba ...
Doctor ya nuna Shamy yace ..Shamsiyya ce ta kawoka kuma ita ta baka kidney dinta daya ...bansan wata mai suna Meenatou ba anan ...
Da sauri Meenalle ta kwace hannunta ta fice daga dakin tana kuka. ...Ma'aruf duk dokin ganin wadda ta taimaka mashi da yake ..sae da ya yunkura zaya bita amma doctor ya tareshi ....lumshe ido yayi duk da ba karan kukan yake ji ba amma yana jin zafin kukanta a ranshi ....
Gurin Shamy ya juyo yana mata godiya sae washe baki take
Yace ...kin taimaki Rayuwata Shamsiyya ..banda bakin da zan gode maki ...amma ina neman Alfarmar ki aureni a lokacin ne zan nuna maki tsantsar godiyar da nake maki ....
Mr Ma'aruf. ..ta fada lokacin da take washe baki ...da gaske zaka aureni ...
daga mata kai yayi yana kallon gadon Meenalle ...
Shi daya kamata ya nuna zakewa amma itace ta nuna zakewa a gurin ...
Tare suka koma gidanshi...sae rawar kai take mashi ...kokari yake ya sakata zuciyarshi amma ina ..babu wani babi face na Meenalle ....
Sae dare ta tafi shima sae da ya lallabata sannan ...
Da safe ya yanki ticket ....sannan ya kira Shamy sukayi bankwana ta bashi address din iyayenta ya tafi akan bara ya dawo ba sae angama maganar komae akansu ...
*
Ina labarin Musa?
Da musa ya matsawa Malan sani lamba sae an nemo mashi matarshi ...
Malan sani ya rasa yarda zayayi ...gashi abokanshi na bashi shawarar ya shigar da kara don Uwar Meenalle da kakarta su suka boyeta ....
Alokacin baida ko sisi ga musa ya addabeshi ...dole ya sayar da gidan da suke ciki _Gidan Rabi_...ya shigar da karar ...
Su kaka na zaune tsakar gida aka kawo masu sammaci daga kotu ....
Wae ana tunanin sun sace matar Musa ....ana nemansu ranar litinin akotu ...
Haka suka shirya suka tafi kotu da safe ...aka karanto masu da karar da akayi akansu ..tare da tambayarsu sun san da zance ...
Kakata ta murje ido tace bata san da zancen ba kuma sae an fito mata da diya ....
Da Alkali yaga kamar zaa rainawa kuto hankaline sae ya kori karar .
Da yake akwae kudin gidan sae Malan sani ya daukaka kara tare da daukar lauya ....
Lokacin da suka shiga kotun ...anan ne aka rufe kaka don ana tunanin ita ta sace kaka ...aka rufeta sati biyu a sail ....
Ran Rabi in yayi dubu ya tashi ...taje har kano tasami Alhaji Sadee ta fada mashi
••°°••
Meenalle tun da ta koma hostel ba abunda take sae kuka ....Friends dinsu sunyi lallashin duniya amma taki kulasu
Kwata kwata rayuwar garin ta fita ranta. ...haka shamy bata da Labari sae na Ma'aruf ...wata sa'in idan suna waya sae dae Meenalle ta bar gurin tana kuka .....Sannan taki fadawa Shamy din dalilin da ya saka take hakan ...
Sae a hankali sannan ta fara komawa dae dae har ma ta fita lecture ...
Da marece ta fito daga lecture ta daga idonta ta kalli benen Ma'aruf kamar yadda take kullun ...suka hada ido ....alama ya mata da ta jirashi yana saukowa .....gurin tayi tsaye kanta na kasa har ya karaso ...
Dariya ya sake bayan ya leka fuskarta tare da lakutar Hawayen yakae baki ....Bara naji ko hawayen nada zakine shi yasa basu wahalar fitar ....
Murmushi tayi ta saka hannu zata share ...yayi saurin saka hanky dinshi ya share mata yana girgiza kai ......
Guri ya samu ya zauna ...yana tambayarta ...Meke faruwa Fateema ...ko har yanzu baki warke ba ....
Girgiza mashi kai tayi tare da juyawa bangare guda ....
To me yasaka kike kuka ? ...Wani ne ya sakaki kukan? ..ya sake fada a hankali yana leken fuskarta ..
Kamar tace Kaine Ma'aruf ...amma ba dama ...sae dae girgiza mashi kai tayi ...
To kiyi hakuri kinji Fateema ...bana son ganin hawayenshi ko kadan ...kin koma gida bayan kin warke? ...
Nan ma girgiza mashi kai tayi tare da share hawayen dake binta .....
Kinci abinci ? ....ya tambayeta lokacin da yake kallon bakinta ...
Uhm ...tace mashi ..
Lumshe ido yayi yace ban yarda ba. ..tashi muje kinji ko ...kamar kin taba zuwa gidana can baya ...kece ?
Daga kai tayi tana murmushi ....
Hararan wasa ya sake mata yana fadin. ..lokacin kinje kallona ne ko kinje ki saka man ciwon da zamu hadu asibiti .....
bata ce komae ba sae murmushin da tayi..wanda har hakoranta suka bayyana
*
Ina labarin Musa?
.
Da musa ya matsawa Malan sani lamba sae an nemo mashi matarshi ...
Malan sani ya rasa yarda zayayi ...gashi abokanshi na bashi shawarar ya shigar da kara don Uwar Meenalle da kakarta su suka boyeta ....
Alokacin baida ko sisi ga musa ya addabeshi ...dole ya sayar da gidan da suke ciki _Gidan Rabi_...ya shigar da karar ...
Su kaka na zaune tsakar gida aka kawo masu sammaci daga kotu ....
Wae ana tunanin sun sace matar Musa ....ana nemansu ranar litinin akotu ...
Haka suka shirya suka tafi kotu da safe ...aka karanto masu da karar da akayi akansu ..tare da tambayarsu sun san da zance ...
Kakata ta murje ido tace bata san da zancen ba kuma sae an fito mata da diya ....
Da Alkali yaga kamar zaa rainawa kuto hankaline sae ya kori karar .
Da yake akwae kudin gidan sae Malan sani ya daukaka kara tare da daukar lauya ....
Lokacin da suka shiga kotun ...anan ne aka rufe kaka don ana tunanin ita ta sace kaka ...aka rufeta sati biyu a sail ....
Ran Rabi in yayi dubu ya tashi ...taje har kano tasami Alhaji Sadee ta fada mashi
••°°••
Meenalle tun da ta koma hostel ba abunda take sae kuka ....Friends dinsu sunyi lallashin duniya amma taki kulasu
Kwata kwata rayuwar garin ta fita ranta. ...haka shamy bata da Labari sae na Ma'aruf ...wata sa'in idan suna waya sae dae Meenalle ta bar gurin tana kuka .....Sannan taki fadawa Shamy din dalilin da ya saka take hakan ...
Sae a hankali sannan ta fara komawa dae dae har ma ta fita lecture ...
Da marece ta fito daga lecture ta daga idonta ta kalli benen Ma'aruf kamar yadda take kullun ...suka hada ido ....alama ya mata da ta jirashi yana saukowa .....gurin tayi tsaye kanta na kasa har ya karaso ...
Dariya ya sake bayan ya leka fuskarta tare da lakutar Hawayen yakae baki ....Bara naji ko hawayen nada zakine shi yasa basu wahalar fitar ....
Murmushi tayi ta saka hannu zata share ...yayi saurin saka hanky dinshi ya share mata yana girgiza kai ......
Guri ya samu ya zauna ...yana tambayarta ...Meke faruwa Fateema ...ko har yanzu baki warke ba ....
Girgiza mashi kai tayi tare da juyawa bangare guda ....
To me yasaka kike kuka ? ...Wani ne ya sakaki kukan? ..ya sake fada a hankali yana leken fuskarta ..
Kamar tace Kaine Ma'aruf ...amma ba dama ...sae dae girgiza mashi kai tayi ...
To kiyi hakuri kinji Fateema ...bana son ganin hawayenshi ko kadan ...kin koma gida bayan kin warke? ...
Nan ma girgiza mashi kai tayi tare da share hawayen dake binta .....
Kinci abinci ? ....ya tambayeta lokacin da yake kallon bakinta ...
Uhm ...tace mashi ..
Lumshe ido yayi yace ban yarda ba. ..tashi muje kinji ko ...kamar kin taba zuwa gidana can baya ...kece ?
Daga kai tayi tana murmushi ....
Hararan wasa ya sake mata yana fadin. ..lokacin kinje kallona ne ko kinje ki saka man ciwon da zamu hadu asibiti .....
bata ce komae ba sae murmushin da tayi..wanda har hakoranta suka bayyana
*
Haka kawae yake jin farinciki idan yana tare da ita ...tare suka jera har cikin gidanshi ...ya dauko mata abinci ..tare da lemon ..sannan ya zauna yana tsokanarta har ta koshi ....
Komae nata na burgeshi ...bata tafi ba sae da ta gyara mashi gidan sae kamshi yake sannan ta tafi ...
Bayan ta tafi ya kira Shamy ya mata bayanin komae ...yace mata duk wata magana an riga an gamata ...iyayenshi sunje gidansu an kuma bashi ita .....
Haka ta koma hostel Meenalle na kwance ta fada kanta sae hauka take ..ta kusa zama matar Mr Ma'aruf ....
Kamar saukar aradu Meenalle ke jinta ...har ta gama ta haukanta bata motsa ba ...sae da ta leko fuskarta tace mata ...You're not happy MMA
Am very happy Shamy ...Allah ya sanya albarka ...tana gama fadar haka ta fice .....
Ma'aruf dinne yazo ya kira Shamy ...tana zaune bisa wani dutsi tana hango su....sae wannan iyayi yi Shamy take .....
Dukar da kanta tayi daga barin kallonsu ...motsi taji a bayanta ...ta dago a tsorace ....Ma'aruf ta gani ya harde hannuwa ya zuba mata ido ....
Saurin juyar da fuskarta tayi tana kakaro murmushi ...
Fateema. ..ya kira sunan a hankali ...akwae abunda ke damunki kawae baki so na sani ....
Allah ba komae Mr Ma'aruf kawae kaina ke ciwo na fito na sha iska. ..ta fada tana murmushin yake ..
A nan zaki huta ...? ..ta so muje na kaiki inda ciwon kan zaya tafi kinji ko ..? ..
Shamy ta iso gurin tare da dafa Meenalle tana fadin ...Hubby wallahi mu kanmu bamu san Meke damun MMA ba ...
Ido ya waro ..dama kin santa ne ..
Yeah friend dinta ce... Shamy ta fada tana murmushi .
Tashi muje to kinji ko ...ki bar nan gurin akwae sanyi da yawa kinji ko ...rigar sanyin dake jikinshi ya ciro tare da rufa mata ...sannan Shamy ta dagata suka jero tare ..
Ma'aruf ..yace su shiga mota bara su tafi a haka ba ...Shamy mai miji aka shige gaba ....ta glass din yake kallon meenalle ...duk wani motsi da zatayi a idonshi take ...yaso ace itace ta bashi kidney don ya masifar tausayin yarinyar ...sannan kallonta yake Meenalle komae tayi burgeshi take ....
Wani guri ya kaisu ...ya masu shopping sossae ...aka saka a bayan mota ...sanna ya dauko wasu kananan ledoji guda biyu ...ya mikawa Shamy daya ..ta karba tana godiya ....
Sannan ya mikawa Meenalle guda ...ta saka hannun dama zata karba ...ya kurawa zoben dake hannunta ido sannan yaki sakin ledar ....
Da Sauri ta janye hannun ta maidasho baya ...
Yaso ya ce ta fito da zoben ya gani amma sae wata zuciya tace mashi ba abunda yake tunani bane ...don yanzu tuni zoben yamata Meenalle kadan ...haka ya kauda tunanin zoben a ranshi ..
Lokacin Alhaji Sadee na tunanin case din karamine ...ko Alhaji Abubakar bai fada mawa ba ...ya shirya ya tafi ...
Ranar da sukaje kotun ..Alkali ya tambayi Rabi shin da saninta aka aurar da Meenalle .....
Rabi tace eh da saninta aka aurar da Meenalle ..
Alkali ya tambaya ..shin ko ubanta ya san da auren ? ..
Tace. ..aa ubanta baisan da auran ba domin ba gurinshi ta tashi ba. ...
Alkali yace a kira mashi Wadanda aka daura auren gabansu ....babu shamaki malan sani ya kirawo har wanda ya daura auran ...Alkali yace aure ya dauro kuma ba wanda zaya warware auren ba tare da wata kwakwkwaran hujja ba ..
Alkali ya nemi a kira Meenalle ...Alhaji Sadee yace sam bata kasar ...
Alkali yace to nan da sati biyu a kawo Meenallen ...sannan aka sake kaka suka tafi da ita ..
.
Hajiyar Abubakar ta tasa Abubakar dole sae ya karbo diyarshi don tana bukatar ganin jikarta ...
Murmushi yayi yace shi yanzu baisan inda zai ga su Rabi ba ....sae dae tayi hakuri ...
Kuka ta saka mashi amma ya tashi ya fice daga gidan ...
Lokacin tayi nadama sossae ...kuma Meenalle ta bar mata son diya mace ...don ta gane Rahamace ...itama so take ta ga jikkarta ko da ace musakace bama mai lafiya ba ...
0 comments:
Post a Comment