Lokacin da musa ya dawo ya iskesu tsaye bakin gate ....ya taresu yana tambayar lafiya...sae suka ce masu police ne suka zo suka tafi da Meenalle basu nan ...
Kamar mahaukaci ya juya ya tafi police station din rike da bindiga ...da yake shashasha ne yama manta da nemanshi ake soyayya ta rufe mashi ido ...
Yana zuwa ya fara harbe harbe yana zage zage ...nan da nan suka kamashi suka daure ...
••°°••
Ina Raliya ..
Da Raliya ta tabbatar Mr Ma'aruf ya rigaya ya mata nisa ...don ko tana tsafi da bakar jaba bara ta sameshi ba ...har office dinshi taje messenger shi ke fada mata yayi aure ...sae ta tattara kayanta ta koma nigeria ...ta sayi gida ta bude wani bariki na yan lesbian ...da yake dama maza ba damunta sukayi ...ba ...dama Mr Ma'aruf ne take bala'in so kuma bata samu ba ...
Haka ta lallashi partner ta Ruky da ta rude tana son Meenalle tun tana yarinya don tun lokacin da Meenalle ta shigo gidansu har ta dauketa bata kuma kara kula Raliya ba ...suka shirya suka koma kamar da ..
°°••°°.
Bayan an rufe musa ne aka sake Malan Sani ....Lokacin Ya koma yana so rabi ta koma gidanshi ...amma fur kaka tace bara ta koma ba ....
Sannanne kaka ta murje ido tace Malan Sani sae ya tashi daga gidan ...
Malan sani ya tsorata ganin Kaka zata maidashi kotu ...gashi ya sayar da gida kuma ba kudi. ...yayi nadama sossae Rabi tace a kyaleshi amma ya saketa dan bara ta koma gidanshi ba ...
Jiki na kyarma ya bata takardar saki ... .
••°°••
Meenalle kuwa tana dawowa kaka ta mayar da ita gidan ubanta ...ko sati bata kara ba ta koma makaranta ...
Ranar da ta isa kasar bata san wanda ya fadawa Ma'aruf ba sae ganin kiranshi tayi ..bata dauki kiran ba sae da suka hadu School da Shamy take mata tsegumi ..... .
Duk yarda Shamy taso Meenalle taje gidanta amma taki yarda taje ...haka ta hakura ta kyaleta ...Shima Ma'aruf yayi kokarin su hadu ya ganta amma duk ta toshe hanyar da zasu hadun ....
••°°••
da Hajiya ta ishi Abubakar maganar diyarshi ...sae ya dauko mata Sadee ..ya gaya mata gaskia ....
Su hajiya har da kuka tana neman gafararsu. ..sannan tace akaita gurin Rabi ta roki gafara ...haka suka shirya suka tafi ....
Lokacin da Abubakar yaji auren Rabi ya mutu ..ba karamin farinciki yayi ba. ...ya fadawa Hajiya yana so ya maido rabi ...da yake hajiyar tasha wahala gurin matar da ta sakq ya aura ..sae ta amince dan da nan ...
••°°••.
Cikin wata hudu akayi komae aka gama ..rabi ta koma gidan tsohon Mijinta ...wancan matan kuwa tana jin zayayi aure tace bara ta zauna da kishiya ba ..ta tattara komatsunta ta yi tafiyarta ....
Da Hajiya kuwa ta gyara halinta suka zauna lafiya da Rabi. ...da labari ya sami Meenalle har kukan murna sae da tayi ...
*Feedohm💞*
💧💧SIRRIN ZUCI ....
💞
💦Talented Writers Forum💦
ðŸ”
Na Feedohm💞
81 to 82
*Nine Month*
Tun da Safe Ma'aruf ya kira Meenalle ...yace tazo Shamy na kiranta bata lafiya ....
Taxi ta hau ...kasan cewar tsakanin makarantar da gidansu Shamy din akwae nisa ...minti biyar tayi ta isa gidan ...
Lokacin har an fito da Shamy din daga cikin gida zaa kaita asibiti ...
Da Sauri ta isa gurin Ma'aruf tana tambayarshi lafiya ....
Lumshe ido yayi yace tana labour ne wallahi ...tun jiya ...
Bayan sun je asibitin ne akace. ..sae an mata CS saboda haihuwar tazo amma kuma Mahaifar ta rufe. ...
Canza mata asibiti yayi ya maidata asibitin da aka masu aiki ...yana tunanin ko zasu iya mata wani abu ...don baya kaunar CS ...Cikin Saa ya tarad da doctor din da ya mashi aikin Kidney ...
Thesame nan ma cewa akayi sae anyi aikin don barata taba iyawa ba ...
Haka aka shigar da ita dakin tiyata ...Meenalle duk ra rude. ..bayan minti 45 ..wata nurse ta fito da baby boy ...
Ta nufi wani room dashi da sauri ...Meenalle ta bita tana tambayarta lafiya. ...
bayan ta fito daga dakin ta zo tana masu bayanin ...boy dinne yasha ruwan mahaifa kuma akwae matsala. ...
Abunka da ruwa ruwa nan da nan idon Meenalle ya ciko da kwalla ...don tasha jin inda yaro ya samu irin wannan matsalar da wuya ya tashi .....
Minti Talatin da shigar nurse din ta fito ta fada masu cewa baby boy din ya koma ga Allah ....
Meenalle ke ta hawaye ...amma Ma'aruf lumshe ido yayi kawae yana kallon dakin da Shamy ke ciki ....
Zuwa can aka gangarota ....aka shigar da ita wani dakin ....lokacin idonta biyu tana kallonsu ...ta yafito Meenalle da Hannu ....
Doctor din ya girgiza mata kai ...yace tana bukatar hutu ....
Bayan an shiga da itane ..ta dinga rokan doctor din akan ya barta tayi magana da Meenalle minti 30 kawae ....daga farko cewa yayi tayi hakuri ...amma daya fahimce ta sossae sae yaga bai dace ya hanata ba ....
Shi da kanshi ya kira Meenalle yace ta shiga patient din nason magana da ita ....
ta shiga da gudunta ...Ma'aruf ya bita da kallo ....
Shamy ta rike mata hannu suna kuka ...Ma'aruf dake kallonsu ta cikin glass ya kura masu ido ...ya rasa wace irin shakuwace tsakaninsu ..wadda har daga fitowarta da operation take son magana da ita bayan gashi ...
Meena ...Shamy ta kira sunanta ahankali ...
Meena ya maimata a ranshi tare da matsawa saitinsu yana kallonta ..
Ki fadawa Ma'aruf gaskia...Dan Allah Meena ko bayan na mutu ki fada mashi ki gaya mashi bani na bashi kidney ba Meena. . ki fada mashi ke ki bashi ..kece masoyiyarshi ta gaskia bani Meena ..ki fada mashi kece Meenallen shi ....
Girgiza mata kai tayi tana kuka ...aa Shamy zaki warke dan Allah ki bar wannan maganar ...zaki warke insha Allah ..
Hannuta ta kawo ...bazan tashi ba Meenalle ..baby din na haifa ki rikeshi Meenalle ke na bawa amanarshi ..ki auri Ma'aruf dan Allah ...idanuwanta suka fara rufewa
Kuka ta saki da karfi tare da ficewa da gudu ...a kofa ta bangaji mutun tsaye amma ta wuceshi ...ta fita tana kiran doctor ...
Ma'aruf na tsaye idonshi a lumshe doctor yazo ya jashi yana fada mashi matarshi ta rasu ....
Meenalle kuwa gurin ta suma ....ko bude ido Ma'aruf baiyi ba bare yaga yarda akayi da ita ...
Bayan sun shiga office da doctor din ..Ma'aruf ya tambayeshi ...wacece cikin su ta bashi Kidney ...
Ganin babu bukatar boyewa yanzu doctor din yace ...Meena Abubakar ....
Idonshi ya lumshe hawayen dake makale suka gangaro ...
Waya ya fito ya kira wani friend dinshi dake aiki airport yace yana son helicopter yanzu ....
bai kuma cewa komae ba ya nemi a bashi gawar Shamy ..
Cikin wani box aka sakata sannan aka nufi airport da ita ...suka koma nigeria ......
*
A gidan Iyayenta aka mata sutura ...bayan sati biyu ...ya taka har gidan Kaka ...ya fada mata komae sannan ya nemi yaje gurin iyayen Meenalle ...
Kaka baki yaki rufuwa ...ita da kanta ta kaishi har gidan Alhaji Abubakar ..lokacin su Rabi an murje ..ni kaina kasa ganeta nayi ...
Maganar da Ma'aruf ya gayawa kaka ita ya maimatawa Rabi da Alhaji Abubakar ....sannan ya nuna yana bukatar aurenta kafin ya koma ..
Alhaji Abubakar yace sae an nemi Meenalle anji ta bakinta ....
Haka aka kira Meenalle a waya aka tambayeta ...
Kasa cewa komae tayi ..sae kaka ta ce ...ta yarda ...
••°°••
Biki ake amma bada sanin amarya ba ...komae an mata cikin gata da aminci ....
Kaka kuwa baki yaki rufuwa .....haka hajiyar Abubakar sae nan da nan ake da dangin rabi ...
Kudi kawae Abubakar ya tura aka sayar mata komae acan.....aka hada mata komae na jin dadi ....
°°••°°
Ma'aruf kuwa sae da aka gama komae sannan yama iyayen Shamy bayanin duk abunda ya faru sannan ya taho ...
Meenalle kuwa tunda Kaka ta kirata ta fada mata an daura mata aure gabanta keta faduwa ...haka Ma"aruf bai kirata ba ko sau daya ...
Karfe 8 din dare Ma'aruf ya dawo ...direct makarantar su ya nufa ...Soofy ya kira yace ta kira mashi Meenalle din ...
Yana cikin mota ta iso sanye da maroon din hijab mai hannu ...cikin sanyin murya ta mashi sallama ..
Ya amsa kasa kasa tare da dagowa ya kalleta ..wani abu ya tokare mashi kirji ....ya lumshe idonshi ....
Shiga tayi ta zauna ...tana zama ya rufe kofar yaja motar .....
.
bata ce mashi komae ba ..har suka isa wani katon gida ..ba wanda aka aje Shamy a ciki ba ....
Ya fito ya yi gaba abinshi ...haka itama ta biyoshi cikin sanyi jiki har ta iskeshi falon tsaye ....
Bayanshi ta tsaya kanta na kasa tana wasa da yatsunta da suka sha jan lalle ....
Juyowa yayi idonshi a lumshe ya kira sunanta ...a hankali ...
Bata dago ba ...amma ta amsa a hankali ...
Na dawo dake rayuwata Meenatou ba wae don ina son haka ba.....
Idonta ya ciko da kwallah ...bata yi tunanin gogesu ba ...
Ya cigaba ....Meenatou duk da irin son da nake maki kina yarinya lokaci guda kin gogeshi ...zan maki adalcine saboda abunda kika man ...amma maganar so ..babu sam ...bazan so yarinyar da ta yada darajarta ba. .....
Da sauri ta kalleshi ....tana nuna kanta da hannu .....daraja Ma'aruf ....
Yes Meenatou ...ya fada idonshi na kanta ...
Girgiza kai tayi ...tana fadin ...Nagode sossae ..Meenalle Maikamshi ...na fita fitina Allah ..ko ka manta
Murmushi yayi kasa kasa yace ...Ta ya zan manta ....wucewa yayi ya shige wani daki ya barta tsaye ....bayanshi ta bi itama ta shiga ....
Bai kalleta ba....ya cire suit din dake jikinshi ya fada toilet ...hijab dinta ta cire ...ta haye saman gado ta kwanta .....
Tana kwance ya fito daure da towel ya tsaya gaban mirrow daga ya shafa wannan sae ya shafa wannan ...kamar mace ...nan da nan dakin ya dauki kamshi .....
Da gefen ido ya kallota tana kwance ta rufe ido ....takowa yayi a hankali ya sauko pillow a kasa tare da shimfida bargo ...ya dawo ya sabeta ya dire ta saman shimfidar ya koma ya kwanta saman gado ....
Wallahi Ma'aruf baran kwana a kasa ba duk abunka ..ta fada tana kallonshi ...
Hararanta yayi yace ...idan bara ki kwanta anan ba ki koma dakinki ..
Itama hararan ta sake mashi tana fadin ..haka kuma baran kwana ni kadae ba ...Na rantse maka da Allah baran kwana ko ina ba...
Juya baya yayi ya kyaleta ...yana jin lokacin da tazo ta kwanta gabanshi ...don neman magana ma daura kanta tayi a hannunshi tayi pillow ...
Baice mata komae har tayi bacci a haka ..gangarowa tayi ta shige kirjinshi ...ajiyar zuciya ya sake tare da gyara mata kwanciya ...sannan shima baccin ya daukeshi .....
Ya rigata tashi da asuba ...yayi wanka tare da alwala ...ya dawo ya tadata yaga har ta tashi ...jallabiya ya saka ya tada sallah ...sae da yayi nafila sannan ya jirata ta fito ya ja masu jam'i ......
Yana kwance wajen 9 ta fito cikin shirin makaranta ...tun daga sama har kasa ya bita da kallo ...sannan ya kau da kai. ...
Ki sako Hijab ..sannan ...ya fada ahankali ...
Bata ce komae ba ta sako hijab din ta fito tana tura baki ...mikewa yayi ya dauki keys yayi gaba ..Kamar kurame suke tafiya...
Restaurant ya biya da ita sae tayi breakfast sannan ya wuce da ita makaranta ...
*
kasuwa ya wuce ya sawo masu duk abunda zasu bukata sannan ya dawo gida ya aje kayan ya wuce office ...
lokacin da Meenalle ta dawo ...sannan ta samu damar zagaye gidan ...ba karamar dukiya aka kashe mata ba ...dakin da take tunanin nata ne ta shiga .....buda baki tayi tana kallon ikon Allah ....drawer ta bude akwatuna ta gani set Hudu masu shegen kyau ...da kyar ta saukosu duka ta zazzagesu kaf kasa tana dagawa ....
Dae dae lokacin Ma'aruf ya shigo dakin ...jingina yayi da kofar ya kallonta ...sae da ta gama daga komae ...sannan ta dauko wata sarka da yan kunne ta aje gefe guda ....tana fadin ....Duk da bana magana da maikamshi bara ya dawo ya fada man yarda ya sawota ...
Lumshe ido yayi tare da barin dakin ba tare da ta sani ba ....
da kyar ta mayar da kayan cikin akwatunan ..amma ta kasa maida akwatunan inda suke .....
Cikin lefen ta fito da Riga da siket na material milk colour ta aje bisa gado .....wanka tayi sannan ta saka kayan tare da sarkan da ta fito ....
Yana kwance falo daga shi sae farar singlet da boxer ja idonshi a rufe ......
Ta dade tsaye tana kallonshi ....sannan ta matso kusa dashi ta dafa kujeran ...Uncle Ma'aruf ta fada a hankali...
Banza yayi da ita kamar bacci yake. ...sajenshi ta shafa...shiru ya mata ...amma wani zafi yake ji a ranshi
..
Ma'aruf dan Allah ka tashi kayi hakuri ...wallahi bansan me na maka ba ka yafe man ....ta fada kamar zatayi kuka ...
shiru ya mata .....tasake cewa ...kaji to Dan Allah idan bara ka bude idon ba ka fada man nawa ka sayi wannan sarkan mai stone a ja ta cikin wadannan akwatinan ...
Dariya sossae ta bashi ...amma ya danne ya bude idoshi ...ya murde hannun da ta shafi sajenshi dashi ...ta sake kara tana kokarin janyewa ....
Tashi yayi zaune ...sannan ya sake mata hannun yana hararanta ....duk lokacin da kika kuma tabani sae na karya hannu ....yana gama fada ya shige daki ...
Zama tayi gurin ta sake kuka tana rike da hannun....
Jin kukan yake har cikin ranshi ...keys ya dauka ya fice daga gidan kwata kwata
Lokacin da ya dawo da daddare har tayi bacci a inda ya barta ...wuceta yayi ya shige daki yayi wanka sannan yayi kwanciyarshi .....juyi kawae yake amma babu alamun bacci a idonshi ....ganin kwanciyar ba zata fishsheshi ba ya saka ya fito falon .....
Kanta na bisa hannun kujera ...ya dauketa ya daura saman doguwar kujera ....
Cikinta ya shafa yaji kamar bata ci komae ba ...ledan da ya shigo dashi ya dauko ...kazane da fresh milk sae dugheese ya zazzage cikin plate tare da knife ...
Kumatunta ya dinga shafawa tare da hura mata iska ...tayi saurin mikewa tare da sakin sabon kuka ...
Shiiiiiitttt ya daura hannunshi saman lebenta ...sannan ya tura mata plate din ....
Mikewa yayi ya koma saman kujera ya kunna TV ...hararanshi kawae take ...suka hada ido ...jira take yace.. taci ..amma ya shareta ...
Hawayen takaici suka gangaro mata ...ya dan saci kallonta ...ta bashi tausayi ...
Kici mana Meenatou ....ya fada a hankali don ya gane abunda take so taji kenan ..
Hawayen ta saka bayan hannu ta share tana fadin ...dama ko baka ce na ci ba yanzu nayi niyyar ci ....
Murmushi yayi kasa kasa ....baice mata komae ba ...
Har ta koshi sannan ta dawo kusa dashi ta zauna kasan carpet .
..
Plate din ta mika mashi ...tana kallonshi ..
Harara ya banka mata ....tayi saurin dauke kai tana fadin ..
dan Allah kaci kaima ...
Murmushi ya sake kasa kasa yace ..ba bukata ...
Please ....ta fada ..
Girgiza kai yayi yace ...A da Meenatouta tayi forcing dina naci irin haka .. yanzu ke ba tawa bace ...kuma baran ci ba ....ya mike ya shige daki ....
Ni din taka ce ...ta fada a hankali sannan ta mike ta shiga dakin
Kayanta ta cire daga ita sae inners...sannan ta daura towel ta shige toilet ....akan idonshi tayi komae har ta fito ....duk abunda yake shafawa sae da ta shafa ....sannan ta leka fuskarshi taga idon a rufe ...murmushi ta sake tana murza hannu..
..
*
Pillow ta sauke kasa tare da shinfida bargo ....sannan ta hawo gadon ta koma gabanshi ta dinga murginoshi kasa ....
Yana jinta yayi banza da ita yasan dai barata iya daukarshi ta maidashi kasa ba. ..sae uban nishi take ...sae da ta gaji dan kanta taga bara ta iya maidashi kasa ba ....sannan ta janyo hannunshi ta daura kanta ....bata fi minti 10 ba ya gane bacci ya dauketa ta gangaro jikinshi ...ya saka hannun ya gyara mata kwanciyar sannan shima baccin ya daukeshi ....
••°°••
Ganin bata fito ba har karfe 9 ya saka ya leka dakinta ....tana kwance saman gado ido a rufe ....
Meenatou ...ya kirata a hankali ....
Shiru ta masa ....Ki fito ina jiranki falo ....ya wuce abunsa ...
Yayi minti 20 yana jiranta amma shiru bata fito ba ......
Dan karamin tsaki ya sake lokacin da ya duba agogon dake makale a hannunshi ....
Ya koma dakin a fusace ya tsaya bakin gadon tare da dago kanta ....
Da sauri ya taro kan ...ganin ya koma da kanshi ....jijjiga yayi ...yana kiranta ....sae lokacin ya lura da ba lumfashi a jikinta .....
Daukarta yayi ya sakata mota ya ja motar da gudu ...tun yana tafiya ya kira doctor
Yana zuwa suka amsheta emergency ....kusan 1hours sannan aka samu numfashinta ya dawo normal shima da taimakon oxygen ...
Ma'aruf na wajen dakin sae..kae da kawowa yake ...doctor na fitowa ya tareshi yana tambayar lafiya ...
ce mashi yayi ..zafin masassara ne ke damunta ... da marece aka sallamesu suka koma gida ....
A gate din gidan ta saka mashi kuka wae barata iya takawa ba ....jikinta ya taba yaji da zafi ...sannan ya dauketa suka shiga ...
Dakinshi ya direta ...ya shiga kitchen ya dafa mata ruwan zafi ..sannan ya dafa mata kwae guda biyu ya kawo mata ....Ya aje saman stool din dake gefen gadon ya fita ...
Sae da yayi kusan Awa daya sannan ya dawo ...yarda ya aje haka ya tarad da abunshi ...ya kalleta ta gefen ido ...ta maida hankalinta kan wani dan karamin littafi dake aje gefen gadonshi ...
Bakya jin yunwa ne Meenatou ...ya fada tare da zama gefen gadon ...
Bakya jin yunwa ne Meenatou ...ta maimaita abunda ya fada tare da sake mashi harara ..sannan tace ....ko wannan abun zaya shekara anan baran ci ba duk da ina jin yunwan ..tunda nima lokacin da baka lafiya idan naje gidanku ai a baki nake ba ...nima din sae ka rama man ..har dukana ake a makaranta idan na makara ..to wallahi sae ka rama man ..
Murmushi yayi kаsa kasa tare da fadin ...Dama Halinki ne Meenatou ...gori ba ...
Sannan ya janyo flask din ya hada mata tea din tare da dauko sandwitch ya mika mata ....
Ka Wanko hannunka ta fada tana hararanshi ...
Ni ai ban taba hamatar ko wane kato ba ...ya bata amsa ba tare da ya kalleta ...
Nima da nake tabawa ai yanzu na daina ....
Sae ta mata? ...ya tambayeta tare da kura mata ido ...
Bata ce komae ba ta koma ta kwanta tare da rufe idonta .....
Ki tashi kici ....ina da aikin yi da yawa ...ya fada tare da kallonta ...
Bata motsa ba tace ...Alhamdulillah ...
Kafada ya dage tare da ficewa daga dakin .....
Bai kuma dawowa ba sae bayan isha'i ....
lokacin ta dan tashi tayi wanka tare da sallah sannan ta koma ta kwanta amma jikinta kamar wuta ga Uwar yunwar dake damunta. ..kuka take a hankali ...
Ya shigo da sauri ya shige toilet yayo alwala tare da kabbara sallah .. ..
Sannan ya janyo ledar daya shigo da ita ya fito da abunda ke ciki ...
Ya zauna yaci ya koshi sannan ya yo wanka...sae lokacin ya leka fuskarta ...tare da duba duba abunda ya bar mata ...
Da Sauri ya kira sunanta ....Meenatou ...
Tana ji tayi banza dashi ...hannu ya sanya ya cire hannunta dake saman goshinta ...
Zafi sossae yaji jikinta ...nan da nan ya rude ..ya janyo kayan da ya. shigo dasu ..ya fito da Fresh milk ya bata ...da yake yunwa take ji ..batayi gardama ba ta amsa. ...
*
Towel ya jiko da ruwa sannan ya dawo zaya jika mata jiki ....
Bargon data nannade jikinta dashi ya cire tare da tadata zaune zaya cire man shirt din dake jikinta ....
.
Hannunshi ta rike ...duk da zafin masassaran dake damunta bai hana ta sake mashi harara ba tare da fadin. ...Meye zaka cire man riga ...
Karamin tsoki yaja ..yace ...cire hannunki daga jikina Meenatou ...
Allah Ma'aruf bara ka ga jikina ba ....ta fada kamar zatayi kuka ..
Hararanta yayi tare da fadin..Meye a jikin naki da zan kalla Meenatou ...jikin da kowace kazama ta gama kallo ..mtsee ..
Hannunta duka biyu ya hade ya rike da hannu guda tare da cire mata rigar ...ya barta daga ita dae bra .....haka ya zare Siket din ya bar mata Pant ...sae uban ihu take mashi amma ko kulata bai yi ba ....
Har sae da zafin jikinta ya ragu sannan ya sake hannun sae lokacin ya lura da tayi bacci ....
Har ya dauko rigar zaya maida mata ya tsaya tare da kurawa surarta ido ...tabbas Meenalle ta hadu ta ko ina ....
Sauke ajiyar zuciya yayi tare da jefar da rigar gefe guda ...ya mike yayo wanka ya kashe haske sannan ya dawo ya kwanta ....janyota yayi ya rungume yana maida numfashi a hankali ....
Da asuba ta rigashi tashi ....ta kwace kanta daga rikon da ya mata ...tare da sake ihu ganin yarda take ...lokacin jikinya ya koma lafiya lau ...
Jikinshi ta haye tare da dukanshi da pillow tana fadin Allah ya isa ka gani Maikamshi ...ganin hakan bai mata ba ya saka ta daga jallabiyarshi ta zare hannuwan ta cireta ...ta barshi daga shi sae boxer dake jikinshi tare da sake mashi cizo a kumatu tana fadin ...Nima na rama ...kuma baran kara kwana da kai da mugu ....ta dauki rigarta ta fice daga dakin ....
Tana fita ya mike tare da girgiza kai ..don duk abunda take yana jinta shareta kawae yayi ...
••°°••
Lokacin sun gama Exam ba makaranta ..da safe ta hada masu Break su zauna su ci tare sae dae babu magana sae harare harare ...
Ranar da daddare taki zuwa dakinshi ...duk da take ...haka shima ya kwanta sae juyi yake ...kusan Karfe biyu yaji ta bude kofa a hankali tare da kwanciya kusa dashi .....bai yi motsi ba sae da ya tabbatar bacci ya dauketa sannan ya janyota jikinshi ...a haka bacci ya daukeshi ......
tunda Asuba ta sulale ta koma dakinta a tunaninta bai sani ba ...
Da Safe da ya fito ..kamar abun arziki ta tareshi tace ..
Good Morning ...
Ya dan kalleta kafin yace ....Morning ...sannan ya ja kujera ya zauna ...
Ta hada mashi komae sannan ta tura mashi gabanshi tana fadin ...kasan me yasaka na gaidaka ?,..
Girgiza mata kai yayi yana kallonta ...
Ta washe baki tana fadin ...so nake bakin ciki ya dameka na kwana ni kadae ban mutu ba ...ta watsa mashi harara ...
Dariya ya sake har da rike ciki .....
Me kakewa dariya ..? ta tambayeshi tana hararanshi. ..
Hararan ya maida mata ba tare da yace mata komae ...har ya gama breakfast dinshi ya mike ya tafi office ..
Haka da daddare ranar yana jin lokacin da ta dawo jikinshi yayi murmushi ya janyota ya rungume ...da asuba yana jin tana kokarin kwace kanta amma yaki sakinta ....
Tayi kwance sae Mazurai take ...ya bude ido tare da zuba mata harara ...
Ta hadiyi yawu tare da zuba mashi harara itama sannan tace ....
Daga zuwa tayar dakai Sallah sae ka rikeni ....
Harara ya zuba mata yace ...ta ina kika shigo ...
Ta kalli kofar tare da fadin ...ta kofa mana ...
Keys din kofar ya fito daga kasan filon daya daura kanshi ...
0 comments:
Post a Comment