Turo baki tayi tare da fadin ...To Maikamshi na dawo din dakinka sae akayi me ..dadin abun ma ba cire maka kaya nayi ba nace zan gasa maka jiki don na kalleka ..kuma anan din ma zan dinga kwana kullun duk tsiyarka....tana gama fadar haka ta mike tare da fadawa toilet ..
dariya ya dinga yi sossae yana jinjina baki irin na Meenalle ..gashi dae ya nuna mata ya san nan take kwana maimakon ta nuna taji kunya sae ma ta nuna ta fishi baki ....
°°••°°
Zamansu haka ya fara damunta ..har lokacin bai fada mata asalin laifinta ba ..sae dae ya dinga jifarta da maganganu ......
Soofy ta kira a waya ta fada mata matsalarta ....
Shawarwari ta bata sossae tace ta dameshi ya fada mata laifin da tamashi ..sannan kar tayi zuciya baa banza yake mata haka ba ....
yana zaune falo ...rike da wani novel .. tayi sallama ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata ...
Hannushi ta bude tashige jikinshi tare da maidawa ta rufe ....
Ya dan Saci kallonta ...tana sanye da karamar riga pink sae three quater baki ....manyan kalaba ne akanta ....ya saki ajiyar zuciya tare da maida kallonshi ga littafin ....
Ta rasa yarda zata mashi magana ...shimq ma ya gaji da zaman da take a jikinshi Allah kadae yasan me yake ji ....
Ya rufe littafin tare da zareta ya maidata saman kujera yana fadin .
Menene Meenatou ..
Bakomae ...Dama magana nake son muyi ...ta fada a hankali ...
Ina saurarenki ....ya fada tare da lumshe ido..
Dan Allah ina so ka fada man abunda na maka ....
Banda lokacin wannan maganar Meenatou ...tashi ki fitar man daga falo indae wannan ya kawoki .
Kayi hakuri dan Allah .....Da Kana sona Ma'aruf ...amma yanzu me yasa kake man haka ...ta fada a hankali ..
Saboda bana sonki yanzu ...ya fada kai tsaye ...
Kana sona mana ...ta fada tare da sakin kuka ..
Idanuwanshi sukayi jawur ..cikin tsawa yace ..karya kike bana sonki Meenatou ...ya karashe maganar tare da fadawa saman kujera ya dafe kanshi
Kai ta girgiza tare da fadawa dakinshi da gudu ...
Drawer dinshi ta dinga janyowa tana kuka har ta fito da glass din da ribbon din da ta bashi yake ...sannan ta fito dakin ...
Yana ganin ta fito ya mike da sauri tare da nunata yana fadin ...ki mayar dashi Meenatou .
Cikin kuka tace.. idan baka sona me kake da wannan ...
Ki maidashi nace Meenatou ..ya fada tare da nufota ...
Kasa ta jefar dashi da karfi glass din ya fashe ...
Daga hannu yayi da niyar marinta yayi saurin rufe ido ....ta cikin fasasshen glass din ta bi zata wuce ....
Da sauri ya duka tare da saka hannunshi inda zata taka saman kwalaban ...
Rufe ido tayi zata daura kafar a hannunshi Ta taka ta wuce ....amma ta kasa ...kuka ta sake da karfi tare da juyawa ta canza hanya da gudu .....
Binta yayi da kallo ...hawayen dake makale a idonshi suka sauko ...ya dauke ribbon din ..sannan ya kwashe kwalbar ya koma daki ....
°°••°°
Kusan satinsi biyu a haka ...gurin bacci kawae ke hadasu
Duk rintsi basu raba makwanci duk da ba wani abu ke shiga tsakaninsu ba ...sae dae ta daura kanta a hannunshi ...idan tayi bacci ya maidota jikinshi ...
Soofy ta sake kira tagaya mata yarda sukayi ...
Cewa tayi Meenalle kiyi hakuri ki sake jaraba tambayarsa karkiyi zuciya ...indae kinyi imani da soyayyar da yake maki tun ta yarinta to har yanzu akwaeta ....
To kawae tace ...zata je amma wannan shine na karshe ...idan ya fada mata to ..idan kuma bai fada mata ba. ..sae dae su cigaba da zama haka ...
*
Shigowa Meenalle tayi yana zaune yana kallo ....ta samu guri ta zauna ..tana kallonshi ...
Mr Ma'aruf ....ta fada a hankali ....
Ido ya dago a lumshe ...yace . Meenatou Wani abu kike bukata ....
Girgiza kai tayi a hankali tana wasa da zoben dake hannunta. ...
Ok. .ya fada tare da cigaba da kallonshi ...
Ganin baida niyar kulata ya saka ta mike ta koma kusa da kujeran da yake zaune. ..
Ta kwantar da murya tace ...Kayi hakuri Ma'aruf ...wallahi bansan laifin da na maka ba ...Dan Allah ka yafe man ...
Ya danyi murmushi ciki ciki yace ...Meenatou kenan na rasa kalmar zan bi wajen fada maki ki daina zuwa inda nake amma kin kasa ....please ki fice daga falon nan ....
Daga kai tayi tana kallonshi idonta cike da hawaye tace ..Dan Allah Ma'aruf ka fada man laifin da na maka ...wallahi bansan nayi maka shi ...tun ina karama muka rabu ..yaushe har mukayi haduwar da ka tsaneni kuma wane kalar laifi na maka ...
Kayi hakuri dan Allah nice fa Meenalle Ma'aruf ka tausaya man mana. ...
sossae yaji tausayinta ...sae dae yana tunano pictures din da Raliya ta nuna mashi ...tsawon shekaru masu yawa da suka wuce ....lumshe ido yayi ...yace ...Idan har Meenatou zaki iya bawa wata wace jikinki shekaru da suka wuce tun kina yarinya to yanzu fa ....
Kuka ta fashe dashi tace ...ban fahimceka ba Ma'aruf ...wallahi ban gane me kake nufi ba .....
Mikewa yayi ya daga hannunta sama tare da janta har zuwa kofar falonshi...ya bude tare da turata waje. ...karki kuma zuwa falona ...
Kuka ya kwace mata ta toshe bakinta ta juya da gudu ...sae ji tayi ya kamo hannuta tare da sakata a jikinshi ya rungumeta ....
Daga kai tayi sossae tana kallonshi ...sannan ta maida kanta a kirjinshi ...tana jin lokacin da ya sake ajiyar zuciya ...a haka ya zauna saman kujera tana kirjinshi ...sun dade a haka sannan ya dago kanta yana kallonta ...
Meenatou ...yaja sunan...
Bata amsa ba sae da ta kalleshi ...kin san Raliya ...ya tambayeta ..
Girgiza kai tayi a hankali tana share hawaye ......
Mikar da ita yayi ya zaunar da ita sannan ya shiga dakinshi .
ya fito dauke da wata waya ya kunna tare da mika mata a hannu ...
Da sauri ta yardar da wayar tare da sakin kuka ....take ta tuno da abunda ya faru lokacin da ta shiga gidan wadannan yan iskan ...
Wallahi dole suka man Ma'aruf ...ta fada tare da buga kanta jikin hannun kujera ...
Fuskarta ya kamo ya saka hannunsa cikin gashinta ...yana kallonta ...
Kwantar da kanta yayi bisa kirjinsa ...Sorry Meenatou ...i trust you yanzu kinji ko ...kiyi hakuri ..na yarda baki aikata ba ...
Kuka take sossae bata ga laifinshi ba abunda ya mata ...don ta tabbata kara karuwa mai bin maza da yar lesbian ....
Cikin kuka take fadin wallahi banyi ba Ma'aruf ...me yasa ka yarda ...
Lallashinta ya dinga yi har ya samu tayi shiru. ..shima yayi nadamar abunda ya dinga mata ...ashe bada hakkinta ba .....
a haka bacci ya dauketa sae ajiyar zuciya take ....Allah kadae yasan iya kissing din da ya mata ...kafin ya dauketa ya kaita dakinshi ya kwantar da ita saman gado ya fita ....
Cikin wayar ya duba ...number raliya ya gani ...yayi hamdala Allah yasa bai gogeta ba ...tunda dama tunda abun ya faru da ya dauki wayar bai kuma kunnata ba ....
Ringing daya ta dauka ...ya tambayeta inda take ...da yake bata ganeshi ba tunda ba da numbershi ya kirata ba. . ta mashi kwatancen gidan da suke ...da yake ta dawo da taga nigerian ba harka
Direct can ya nufa ....yana zuwa yacewa mai gadin ya kira mashi ita ....
Ta fito rike da sandar guragu tana tafiya .....lumshe ido yayi lokacin da ta iso ...
Mr Ma'aruf ...ta fada tana washe baki ...
Alhamdulillah Raliya ...yaushe kika zama haka ....
Tabe baki tayi tace ...accident muka samu wallahi ..amma dad yace zaa gyara man kafar ta koma kamar yarda take da ...idan aurena kazo karka damu da wannan ...
Dariya ya sake ...yace ai ta riga ta zama haka Raliya ..wannan shine makomar munafiki...kin rabani da Meenatou kike tunani ...well da zuwa nayi ki fada man wace shegiyace tayi forcing din Meenatou ...amma yanzu yarda na ganshi ma naji dadi ..dan nasan soon itama waccen zata hadu da tata kalar masifar ....
Yana gama fadar haka ya shige mota ya barta tsaye .....
*
Kwafa tayi ta shige cikin gidan tana dogara sandarta ....
Yan matane birjit sunata shashansu ....kusa da wata taje ta zauna ...tana rada mata magana a kunne ...murmushi sukayi tare da tabawa ...
••°°••
Zaune ya isketa tana cin Apple ...kusa da ita ya zauna yana murmushi ...
Har kin tashi ....ya fada tare da kanne mata ido ...
Da kai ta bashi amsa sannan ta mika mashi wanda ke hannunta ...
Bai amsa ba sae dae ya bita da ido tare da janyota jikinshi ....
Am sorry Meenatou ....ya fada a hankali ...
Batace komae ba ta saka mashi apple din a baki tare da mikewa ta dauko mashi dinner ....
A plate ta zuba mashi ta tura mashi gabanshi kamar yarda ta saba ...sannan taja nata ...
Kujeran da take zaune ya dawo ya dagata sama ya zauna sannan ya daurata saman cinyarshi ....ya karbi plate din ya debi tare da bata a baki ....
aa Maikamshi ....ta fada tare da kau da kai gefe guda ....
Why Meenatou ....? .
Ka manta abunda kace ...ta fada tare da kura mashi ido ...
Lumshe ido yayi tare da girgiza kai ...Me na fada Meenatou ...
Hararanshi tayi tare da fadin ...ka manta kace bara ka taba bani abinci da hannunka ba ...
Dafe kanshi yayi ...dama yasan zaa rina. yanzu komae ya mata baya yasan sae ta dinga tunawa tana fada mashi ...
Cikin lallashi ya shafi wuyanta ....tare da langwabar da kai yace ...To ai lokacin Meenatou kin bata man raine ...
Harara ta banka mashi tace ...yanzu fa. ...
to yi hakuri na tuba kinji ko ...ya fada tare da mika mata abinci ..
Karba tayi tare da kwafa ....
Shi ya rigata fitowa daga wanka ...ya shinfida tarduma yana jiranta ....
Sanye da kayan bacci ta fito daga toilet din....
Sabon salo ...ya fada a ranshi ...bai san taji shi ba ...sae da ta banka mashi harara tare da hayewa gado abinta ..
Meenatou ...ki sauko muyi sallah ko ...? .
Nayi a toilet ...ta fada tare da gyara kwanciya ...
Girgiza kai yayi ya tada sallah shi ya gama sannan ya hawo gadon tare da janyota ...
Kin tuna?,...ya fada cikin kunnenta ..
Girgiza kai tayi tana kallonshi...
Lumshe ido yayi ..yace ...lokacin da kika ceman malamarku bata sallah ..yanzu ai kin gane dalilin rashin yinta ...
Duka ta kai mashi a kirji tare da lafewa tana dariya ...
Shima dariyar yayi yana fadin ...I love you Meenatou you're my everything ...
••°°••
Tana zaune taji Sallama ...ta mike tare da daukar hijab ..
Tana bude kofar ta sake uban Tsalle tare da rungume kaka ...
Imagine kakata ...ta fada tana dariya ...
Hajiya tayi zuru tana kallonta ...sae da kaka ta buge mata hannu tana fadin ...baki ga hajiya bane ..
Turo. baki tayi tace. ..na ganta ..ai bata sona ...
naki kaniyarki Meenalle ..bata sonki ta hawo jirgi kamar zamu fado tazo inda kike ....
Ma'aruf dake tsaye jingine da kofa tunda suka shigo ..sam bata lura dashi ba ...
Ya ja hannu hajiya yana murmushi yace ...Taho hajiya rabu da ita zata neme mu ne da kanta ...
Sae lokacin tasan tare suke ...ba kunya ta nufeshi tare da rungumeshi ta mashi kiss a kumatu ...
Oyoyo ......
Hancinta yaja a hankali har ta saki kara ...yace ...baran amsa ba ..
Ta dan ja baya kadan tare da waro idanu tana kallonshi ...acikin shagwaba tace ...Why ..
Hannu ya mika mata ta matso kusa dashi sannan ya kalli hajiya ya kalleta ...
Murmushi tayi taje ta rungumi hajiyar tana mata sannu da zuwa ...
*
Bayan sun hutane Kaka ta kurawa Meenalle ido tace ..
Meenalle banga alamar samun da ba da wuri ....
Kaka a Ina ...ta tambayeta cikin rashin fahimta ..
to ba hausa ina nufin banga ciki ya fito ba ...
Ta sake dariya tare da kwalawa Ma'aruf kira ....yana tsaye yana shan ruwa gaban fridge ya iso yana tambayarta lafiya da ido ..
Hannunshi ta janyo tare da zaunar dashi kusa da kaka tace ....Fadawa kaka me kace ..
Me nace kuwa Meenatou ....ya tambayeta a hankali ..
Harara ta sake mashi ...ya saurin dafe kai ...yasan Meenalle da naci ta yiyu wata magana ya mata shine bata hakura ba zata tada ta yanzu ...
Lokacin da kace bana da ko. ...
bata karasa ba ya tashi tare da jan hannuta da karfi ya shige da ita kitchen ...
Am sorry Meenatou ...baran sake fadar komae ba ...
Harara ta sake mashi tana fadar ...naji to ka sake man hannu ko ....
Zan sake amma karki sake fadar komar kinji ko ...ki manta ...
In manta me ..har cewa da kayi karuwa ta ...
bakin ya murde ta sake kara ...ya daure fuska sossae ...yace ...
Kar na kuma jin wannan kalmar a bakinki ....me kika hadawa su kaka .
Yanzu dae zaka tayani mu hada masu ..ta fada tare da kwantowa jikinshi ....
Murmushi yayi suka fara aikin tare sae da suka gama girkin suka gyara kitchen din tare
Kwanansu goma cif ...tun Meenalle bata sakin jiki da Hajiya har ta koma tana sakin jikinta kamar yarda take da kaka ...
Ranar da suka tafi kuwa kuka ta yini mashi ...sae da kyar ya samu ya lallasheta tayi shiru ....
Da yake rigima take ji ...ko abinci bata masu ba ...fita yayi ya sawo masu abinci ...inda yake sawo wa ya samu sun rufe ...sae ya sawo mata kaza da ice cream ya dawo ....
Tana kwance bisa kujera ya dawo ko dan oyoyon da ta saba mashi batayi ba ...ya wuceta ya shiga kitchen ya dauko plate ya juye da knife sannan ya dawo falon ...
Ya leka fuskarta tare da kiran sunanta a hankali ...Meenatou ...
Zaune ta tashi tana sharar kwalla ...da sauri ya rungumota ..
Ya Salam Meenatou ...kukan ne har yanzu ...Sorry yi shiru kinji ko ...Muna next month zamu je ....
Da sauri ta washe baki ...tana fadin da Gaske ...
Daga mata kai yayi alamar eh ...tare da janyo plate din
sauko kici ...
Saukowa tayi tana cin abunta ba tare da ta sake cewa komae ba ...sae da ta koshi sannan ta kalleshi tana murmushi tace ...
Kasan dama ina son kazar amare ..amma wadda na taba ci bata kai dadin ta nan ba ...
Hararanta yayi yana fadin ..waya baki wata kazar amare ...
Musa ya sawo man ita ...amma karamace bata isheni ba ...
Baki ya tabe yace. ..Bata amaren bace shi yasa kika cinye...
Allah itace....kuma ban rage ko kadan ba ....
Dawowa yayi kusa da ita tare da janyo hannunta yana murzawa ....
Idan na sawo maki ta amaren zaki cinye ...ya fada dae dae kunnenta
Harara ta sake mashi tana fadi ...dukanta kuwa .. .
Girgiza kai yayi tare da jan hancinta .....
Idan na sawo maki ta amaren ma Meenatou bara ki ci ba ....
Giranta ta hade tana fadin Kana wasa da ni ...
Ko ? .. ya tambayeta .....
Eh .....
Zakiyi bayani da kyau ...ya fada tare da mikewa tsaye ...
Kaima din zakayi bayani .....ta fada tana hararanshi ...
Hannunta ya janyo ta mike tsaye yana kokarin zura hannunshi cikin rigarta
0 comments:
Post a Comment