_Gidan Alhaji ISMA’IL YUSOUF Unguwar Dutsen Tanshi, Bauchi, Bauchi State._
Matsakaicin gida ne ba yabo ba fallasa, na d’an kasuwa meh arziki dai-dai ba irin na hauka d’innan ba, arzikin sa beyi yawa ba be kuma kasa ba. Kalan arzikin Alhj Isma’il Yusouf ake kira da middle class earners. Gidan nasa wanda ya k’unshi sashi biyu, k’arami na bayan ya kasance BQ. Daga babban sashin wata ‘yar yarinya chocolate skinned meh k’imanin shekaru goma sha d’aya (11) ce tafito a gurguje ta nufa kitchen inda ta d’au wani k’warya da magani ciki tafito a hanzarce, tsabagen saurin da take har tafashashshen maganin na zube mata a hannu amman hakan be hana mahaifinta k’olla mata kira a fusace daga ciki ba “MARIAM! MARIAM! Wai d’auko maganin ne har yanzu?! Mschww!” kamar wacce zatayi kuka takaici kwance fal a fuskarta tace, “gani nan zuwa fa Baba” chan k’asa k’asa tace, “haihuwa sekace hauka Ya Allah karkasa Mama ta haifi na mac-” bata k’are maganan ba tayi kacib’us da Baban nata a bakin k’ofa, wani kallo ya galla mata tare da wabje k’waryan maganin ya nufa ciki da hanzari a yayinda Mariam ta juya tayi d’akinsu da k’anwarta YASMIN.
“Gashi HAFSAH sha kinji? sannu, sannu ko?” Baba wanda ya kasance dark skinned amman kyakkyawa ajin farko yanada ball eyes da long eyelashes with thick brows, sajen fuskarsa ya had’e da moderate gemun dayake ajiyewa, ya kasance cikakken na miji me tsayi dakuma kauri kad’an, sede ba wani babban mutum bane dududu shekarunsa talatin da takwas (38) ne. Maganar yayi ma fara kyakkyawar matar dake kwance kan turkey bed dake d’akin. Mace ce me shekaru talatin da d’aya, (31.) A very young and beautiful woman. Miqe akan gado take tana juyi da tsohon ciki tattare da ita se nishin nak’uda take duk tabi tayi zufa sede sam yanayinta be hana kyawunta wanda yasamo asali daga tushen Fulani fitowa ba. Gefenta wata ungozoma ce zaune tana mata sannu. A sannu a sannu ungozomar tasamu ta d’ura wa Hafsah maganin har a yanzu Baba na a tsaye kan matarsa hankali tashe yana me addu’a a ransa Allah sa Hafsah ta sauqa lafiya ta haifo masa santaleliyar ‘ya mace. Yake ga ba me kaisa murna in matarsa ta haifi ‘ya mace, ‘ya macen da ze samu yayi wa margayiya beloved sis nasa ZAINAB takwara. Zainab takasance best sibling na Alhaji ISMA’IL cikin yayyun sa mace da miji d’aid’ai dakuma k’annensa mata biyu ciki harda Zainab d’in wacce take binsa dab daga shi se ita. Duk cikinsu ba wacce yafiso suka kuma fi shiri da shaquwa kamar marigayiya Zainab ba, shekaranta d’aya (1) da aure mutuwa yayi halinsa, shekaru biyar (5) da suka wuce kenan yanzu amman Alhaji se gani yake kamar jiya ne rasuwan nata, tun rasuwan ta Alhaji Isma’il yad’au alk’awarin da zaran Hafsah ta sake samun ciki ta haihu muddin mace ce takwaran Zainab sistersa zeyi kodan zena tunawa da alkhairun data masa wanda kad’an daga cikinsu ya kasance na basa jarin fara kasuwancin da yakeyi har a yanzu wanda Allah ya mugun sa masa albarka ciki se bunk’asa yake.
Sede kash! tundaga kan Yasmin meh shekaru shida (6) yanzu wacce takasance ‘yar auta cikin yaransa hud’u wanda biyu daga ciki maza ne biyu kuma mata, tun daga nan haihuwa yayi rana wa matarsa mafi so fiye da komai a rayuwansa, yau shekaru hud’u (4) kenan rabuwanta da haihuwa se a shekara na biyar (5) Allah ya azurta ta da wani cikin wanda Alhaji Isma’il yad’au buri da gatan duniya ya aza wa cikin, burinsa a kullum bayyafin Allah yabasa santaleliyar macen da zema margayiya Zainab takwara. 2 months back yaje aikin hajj inda ya riga d’awafi yana rok’an Allah cika mai burinsa.
Babban d’ansa IBRAHEEM wanda ya kasance fari ne tas wane mahaifiyarsa Hafsah, kyawunsa kuwa sak na mahaifinsa yanada 13years ayanzu yana matakin JSS 3 a karatu a Havardth School wanda ke kusa da unguwansu da k’afa ma suke tahowa se kaisu ne mahaifin keyi a motansa k’iran Corolla S baqa, dan gudun kada suyi latti. Daga Ibraheem se k’anwarsa MARIAM shekaru biyu (2) ne a tsakaninsu. Mariam wacce takasance 11years kyakkyawa ce itama kamanninta irin na Baba kaman Ibraheem sede ita ba fara kamar mahaifiyarsu bace bakuma baqa kaman mahaifin nasu ba chocolate skinned take tana JSS1 a matakin karatu itama a Havardth. Daga Mariam se OMAR shekara d’aya da rabi (1½) ne a tsakaninsu, Omar is 9½ years yana Primary 5 a karatu shima a Havardth, skin colour nasu d’aya da Mariam sede kaman yad’an fita haske. Daga Omar se Yasmeen auta. Shekara uku (3) ne tsakaninsa da Yasmeen she is 6 years tana matakin Primary 2 a karatu itama a Havardth, tanada haske sosai sede bara a kirata da fara ba.
Cike da tashin hankali da tsatsan tausayin Hafsah data kasa haihuwa tin tin d’azu, a kaita asibiti kuma taqi, bana wai haihuwan gida takeson yi. Alhaji ya d’ago kai yana kallon Omar daya sasa yima Mamansu fifita kafin Ibraheem ya siyo petir da za’a sa a engine a tayar.
“Wai a bangon duniya Ibraheem yaje siyo petir d’inne?!” Yayi maganar cikin kakkausar muryan dayasa Omar b’ari ko amsa mahaifin nasu yakasa se fifita Maman su yake da sauri da sauri. “Omar dakai fa nake magana! Ina Ibraheem?”
“Bbb... Bbaba ban sani ba kaifa ka aikesa siyo petir yana han-” be k’arisa maganan ba Ibraheem yashigo da galon na petir a hannunsa tare da yin Sallama “Baba gash-” tunkud’esa Baba yayi tare da wabje galon d’in “se yanzu kaga daman dawowa kabar mahaifiyarka tana jiqewa anan dan zufa ko?!”
“A’a fa Baba yau gidan man da layi ne-”
“Rufa min baki ka wuce kaje kasa ka tayar yanzun nan” ya danqala masa galon d’in a sanyaye yaje ya aiwatar da abinda mahaifinsa ya buqacesa.
_30 minutes later..._
A’ee (Ungozoma) ce tafito da jariri nannad’e cikin shawul pink a hannunta batai ko inaba se d’akin Baba inda tayi Sallama, rashin amsawansa yasa kawai tasa kai ta shige, zaune kan Sallaya hannayensa biyu d’age a sama yana addu’a ta tarar dashi. Bayan Sallaman da tayi tanemi gu ta zauna har anan Baba be juyo ya kalleta ba sakamakon kukan jariri dayaji yasa yabar dukkanin abinda yake ya juyo da hanzari “A’ee bade Hafsah ta sauqa ba?”
“Ga santaleliyar ‘yarku nan anan.”
“ ‘Ya mace?!” Yayi maganar cike da k’in yarda tsantsan murna da farin ciki “kina nufin mace ta haifa?!” yayi maganan a lokacinda yake amshe jaririyar daga hannunta, yarinyace kyakkyawa ajin farko hanci tun tana k’arama a miqe ba abinda ya rabata da mahaifiyarta Hafsah illa fari da Hafsah tafita, jaririyar ta kasance tana da haske sosai erin masu golden skin d’innan amman da alama harda hasken jarinta tattare da ita nan gaba barata kai hakan haske ba, kyau de kam masha Allah ga gashi kota ina a fuskarta.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah mai iko kai Allah abin godiya azumin bakancen dana yi alk’awarinyi a gobe zan fara in shaa Allah ya Hafsah da jiki?”
“Alhamdulillah ta sauqa lafiya tana wanka ne.”
“Masha Allah! Wannan kyauta haka daga Allah, Hafsah taci kyauta!” nan yayi hud’uba wa jaririyar a b’oye sannan a fili yace, “Allah ya raya ZAINAB, Allah raya Mana ZEEZEE a tafarkin addinin muslinci ya albarkaci rayuwarta AMEEN” shida A’ee suka fad’i a lokaci d’aya. “Toh masha Allah Alhaji Allah ya cika maka burin ka sekaje kaga Hafsah kai mata godiya nikuma barin je in sanar da yaran kyautan da Allah yayi mana gabad’aya” ganin tanada niyyan amshen Zeezee Baba yayi saurin dakatar da ita, “barta kije ki fad’a musu a baki ban gaji da riqe Zeezee ba.”
“Oh! Oh! Oh! Alhaji anya zakazo kayi adalci tsakanin yaran nan kuwa?”
“Ke ina ruwanki?! Matsa min anan” yana kaiwa nan ya miqe yabar mata d’akin zuwa d’akin Hafsah har alokacin Hafsah bata fito daga bayin ba dan haka yayi zaman jirarta a bisa gado se k’are wa Zeezee kallo yake yana taking nata pictures a yayinda take ta mummutsika jiki da hannu which is damn adorable.
***
“Assalamu Alaikum gwamnoni da matan shugabannin k’asa” A’ee tayi maganan alokacin da take sa kanta cikin d’akinsu Mariam inda dukansu dasu Ibraheem suka taru sukayi jugum tare da had’a tagumi kowannen su na addu’a a ransa Allah kar yasa mahaifiyarsu ta haifi ‘ya mace, Allah yabata na miji inda hali ma maza biyu su basu damu ba amman de kam banda na mace dan kuwa tun baby’n na ciki basu samu sakat ba ina ace an haifosa yau?
“Samari da ‘yan matan nawa barasu amsa bane?” Tayi maganan tana k’ok’arin zama gefen Yasmeen dake kusa da Ibraheem, se ayanzu hankalinsu ya buga duk suka dawo da kallonsu kan A’ee dake binsu da kallo fuskan kowannensu d’auke da tambaya da tsantsan tashin hankali. Kusan atare sukace “Baaba A’ee meh Mama ta samu?” Dariya ta saki kad’an sannan tace, “meye haka? Sekace dugjal aka haifo maku?” Nanma almost a tare sukace, “dan Allah mana Baaba A’ee meh Mama tasamu?” Kowannensu na me kasa kunne dan jin amsarta. Ibraheem yayi k’wafa yace, “Allah sa ba mace ba” qannensa suka amsa da “ameen” a takaice ciki harda ‘yar Yasmeen, ita yanzu shikenan baby’n da aka haifa zata k’wace mata autanci.
“Toh ku kwantar da hankalinku d’a na miji Mama ta samu” ta musu k’arya don ganin reaction nasu, zan so kuga yadda ake sakin hamdala a d’akinga daga meh “yes!!” Se meh “alhamdulillah” semeh “thank god” se me sujjada seda ta barsu suka gama haukansu sannan tace, “lallai kuwa yaran nan! Toh ‘ya mace mesuna Zainab Mamanku tasamu”
Ibraheem ya had’e gira kai “Baaba A’ee banda wasa please.”
Mariam tace, “ai ma wasa take bawani macen da Mama ta haifa na miji ne born boy!” tad’an murmusa.
Omar ya bud’e baki zeyi magana kenan Baba ya k’olla ma Ibraheem kira.
“Ibraheem! kazo nan kai da k’annenka” anan duk suka tabbatar da maganan A’ee gaskiya ne, “shikenan mace ce, wallahi mace Mama ta haifo mana” Mariam tayi maganan tare da dafe kanta. Omar yaja ‘yar tsuka “mace ko jaraba Adda Mariam?” Yasmeen wacce takaici yabi ya ratsa ta tace, “Adda Mariam yanzu banice auta ba??” Ita abinda ke damunta kenan sau dayawa friends nata a school sukan ce mata da zaran an mata k’anwa ko k’ani shikenan nata ya k’are, Mama da Baba zasu bar sonta se new baby. Ganin Mariam batada niyyan amsata yasa Yasmeen karkato da kallonta gareda A’ee cikin sauti cike shakwab’a tace, “Baaba wai Baba da Mama zasu bar sona yanzu se baby?” Dogon sumanta A’ee ta shafa a hankali tana mata murmushi “inji wa? Yasmeen d’in Baba? Har a kullum Baba ze cigaba da sonki keda sabuwar k’anwarki Zeezee kinji?” Badan ta yarda ba ta gyad’a mata kai.
Omar ya miqe tare da fad’in “yanzu duk sallolin daren da muka tayi a iska kenan?” A’ee ta dafe baki in suprise _wato yaran nan har Sallan dare suke kar Mamansu ta haifi ‘ ‘ya mace? Lallai ga dukkan alamu Alhj bareyi adalci tsakanin yaran nan ba._ Tayi tunanin haka a ranta.
“Wai ina kuke neh?” Baba yayi maganar wannan karan a fusace. Firgit duk suka miqe Ibraheem ne a sahun gaba k’annensa na a bayansa suka fice zuwa d’akin Mama inda suka hango Baba ciki suka shige ciki A’ee na mara musu baya. Akan kujerar 3 seater dake d’akin sukayi lining suka zauna according to girmansu suna me kallon Baba dayayi banza da shigowansu se wasa wa ‘yar jaririyan da bata ma san yana yi ba yake.
Ganin sunci fiye da minti biyu Baba baida niyyan kulasu Ibraheem yace, “gamu Baba” daidai nan Hafsah (maman su) tafito daga bayi da zani d’aure a k’irjinta, murmushi ta sakar wa ‘ya‘yan nata one by one suka gaisheta da jiki suna faking murnan k’aruwan da suka samu banda Yasmeen data turo baki taqi koda magana da Mama ta gano hakan seta murmusa, dankuwa Yasmeen akwai kishi. “Yasmeen d’ita” cewar Mama. “Zo mamana kinji? Zo auta taa” a sanyaye Yasmeen ta nufa wajen Mama suka k’arisa kan gado inda Baba ke zaune da Zeezee se kallonta yake yana mata wasa suka zauna. Daga d’an nesa Mama ta zauna da Yasmeen a gefenta Baba yayi saurin d’ago kai “haba Hafsah na matso nan mana ko bakisan yau k’ima da darajar ki ya k’aru bane? Matso please.” D’an murmushi ta saki tana wasa da gashin Yasmeen “kai Baban Yasmeen barade kabar halinkan nan bako?”
Gira ya had’e “waye Baban Yasmeen? Na kashe sunan nan daga yau Baban Zeezee nakeso” cike da mamaki kowa ke kallonsa a d’akin harta Mama, a hankali ‘yar Yasmeen tafara kuka Mama ta rungumota tana jijjiqa ta.
“Yi shiru kinji Auta ta? Baban Yasmeen wace erin magana kuma kake haka? Yanzu dan an samu Zeezee se a k’i Yasmeen kuma?”
“Toh meh? Yayinta ya wuce ke Yasmeen banason shakwab’a meh haka? Tashi ki zauna! Ke bakisan ke yaya babba ce yanzu ba? Kukuma Ibraheem da Mariam haka ake yi a garinku ko? Harda kai Omar, ba wanda yayi yunk’urin amshe Zeezee yaganta cikinku, an samu k’aruwa amman ko ajikinku kuzo kuga lafiyar abinda aka samu dana Mamanku koh? Ku kiyaye nifah!”
Ibraheem ne yasoma yunk’urin magana Baba yadaka mai tsawa “rufa mani baki! tarbiyyan dana baku kenan koh?”
“A’a Baba kayi hakuri” suka fad’i a tare. Ibraheem ya miqe tare da nufowa gun Baba haka Mariam ma hannu ya miqa ze amshi Zeezee Baba ya bige hannun “seda na tambaya toh banaso barin bada taba matsa min anan!” A sanyaye suka koma kan kujeran suka zauna.
“Hafsah ya jiki? Ba inda ke maki ciwo koh?” Baki ta tab’e sannan ta amsa “a’a babu alhamdulillah.”
“Masha Allah, sannu Hafsah ta sannu kin chanchanci a baki tukuici Hafsah.” Cike da mamaki su Ibraheem ke kallon Baba a hihuwar Yasmeen Baba be bada tukuici wa Mama ba se ana wannan Zeezeen?
“Tukuici kuma Baban Yas... Aww Baban Zeezee” ta gyara kanta ganin yadda Baba ke hararta. “Tukuicin meh kuma?”
“Sekin tambaya ne? Na wannan kyautan mana, kap yaran nan bame kyan Zeezee gashi ita kad’ai ke kama dake, kin chanchanchi kyautan dubu hamsin.”
“Baban Zeezee dubu hamsin?” ta zaro manyan idanunta, “In ban manta bafa kace kwana biyun nan bakada kud’i yanzu ga harkan suna ga na dubu hamsin kuma?”
“Kinga erin halinki da banaso kenan inde akan Zeezee ne toh ba abinda barinyi ba in barakiyi godiya bane fine.”
“A’a Alhaji na meyayi zafi? Godiya nake Allah dad’a bud’i.”
“Ameen” yace daidai nan Zeezee tasoma ‘yar kuka. A’ee tanufo gaban Baba dan amshe crying Zainab Baba ya hanata, baki ta tab’e “Alhj anya kuwa zakayi adalaci tsakanin yaran nan?”
“Ke A’ee ina ruwanki? Yaran nan de kowa yasha gata yanzu kuma lokacin Zeezee ne itama a barta taci gatan ta saboda wannan *_YAR GATA CE!_”* Su Mariam de har yanzu sun kasa cewa komai se kallon abinda Babansu ke suke harda wai tukuici wa Mama saboda ta haifi ‘ya mace suna cikin wannan nazari a zuqatansu Baba ya daka masu tsawa “ku kuma yayyun banza kuna jin kukan k’anwarku ko a kolan rigunan ku koh? Banason mugunta fah!” Da wuri Mariam ta doso gun ta miqa hannu zata amshe Zeezee Baba ya bige hannun nata itama “matsa min sekace dagaske Hafsah yi sauri ki karb’eta ki shayar da ita.”
Mama dake shafa mai tace, “toh Baban Zeeze yanzu zan gama shafa man ina zuwa.”
“Har sekin gama? Itakuma abarta tana kuka? A dalilin meh?”
“Yo! Alhj barin shafa man zanyi?” tayi maganan baki asake.
“Eh Hafsah bari zakiyi ki amsheta” zata sake magana Baba yayi tsawa “kibari nace!” kowa ya tsaya kallonshi haka Mama ta yanke shafa man ta amshe Zeezee tasoma shayar da ita se anan hankalin Baba yasoma kwanciya ganin yadda Zainab ke tsotsan abincinta a hankali Baba besan lokacinda yasoma sama Hafsah albarka ba.
Kusan minti biyar Mama tad’au ta na shayar da Zeezee, a hankali ta zare Mamanta daga bakin Zeezee take Baba yayi magana “ya haka Hafsah? Har ta k’oshi ne?”
Mama batai magana ba Zeezee tasa kuka “miyar mata, miyar mata nace!”
“Baban Zeezee nima fa inada abinyi zan miqa ta wa A’ee tad’an jijjiqata nan danan zatayi bacci.”
“Akan yinwan? Akan yinwan zatayi bacci nace?”
“Wani erin yunwa kuma Alhj bayan na shayar da ita” har anan Zeezee bata bar kuka ba.
“Hafsah ki miyar mata nace karna sake nanata kai na.”
“Oh Allah!” Daga fad’in haka ta miyar wa Zainab mama karap ta chafke tacigaba da tsotsa da zaran Mama tace zata cire se Baba ya hanata haka seda Zeezee tayi bacci Baba ya yarda aka kwantar da Zeezee kan gado anan su Ibraheem suka miqe zasu fice suma.
“Ina kuma zakuje?” Baba ya dakatar dasu.
“D’akinmu Baba” Omar yabada amsa.
“Ita kuma Zeezeen fah? Ita kad’ai zaku bari anan?”
“Baba ga Mama da Baaba A’ee.” Cewar Ibraheem.
“Uwarka nan! Uwarka nace! Dawo kaida Omar ku tsaya akanta kuyi mani gadinta.” Baki wangalau Ibraheem ya bud’e, bashi kad’ai ba harta su Mama.
“Baban Zeezee gadi kuma bayan gani da A’ee a d’akin?”
“Bansani ba yimin shiru kicigaba da abinda ke gabanki.” Ganin Ibraheem be motsa ba har yanzu Baba ya buga musu tsawa “daku fa nake magana!” k’iris yarage Zeezee bata farka ba, a sanyaye suka juyo sukayi kan gadon Ibraheem na k’are wa d’an abar da za’a sasu yima gadi kallo.
*ACIGABA...???*
*©MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
Page 02
And this page goes to *ANEELURV* thanks for everything dear #OneLove
“Yauwa Hafsah ta barinje in siyo miki gashin koh?”
“Alhaji ni banga amfanin gashin nan ba kawai madara da milo nake buqatan k’ari sabida insamu k’arin ruwan nono ma Zeezee.”
“Toh angama Hafsah ta ina dawowa.”
“Toh Allah ya kare Baban Zeezee.” Dad’i sosai yaji ya miqe kan gadon tare da kissing Zeezee a hanci sannan ya d’ago kai ya galla ma Ibraheem da bakinsa kan ya tab’a bango dan turi harara “sauran kuma in na fita kai da qaninka kufita kujira kuga abinda zan muku” yana kaiwa nan ya fice zuwa garrage achan yasamu Yasmeen tana wasa “Baba ina zakaje?”
“Zanje siyowa Mamanku da sabon baby kayan tea ne.” Tanajin sabon baby ta had’e rai har Baba ya gano kishi take “zo nan” ya kirata bayan ta iso yace, “baraki bar wannan banzan kishin naki da bansan daga ina yasamo asali bako? Yanzu da k’anwar nakin kike gaba? Iyyeh? Kicigaba.”
“Baba kacewa Mama wai karta sake cemaka Baban Yasmeen se Baban Zeezee ni banason Zeezee.” ta turo baki.
“Karki sotan maras kunya kawai, zamuga me siya miki chocolate a gidan nan ai.” Da gudu ta ruga ciki tana kuka taje ta samu Mama.
*~ * ~ *~
Daidai nan Baba yadawo daga d’an siyayyan dayayi ma Hafsah bayan yayi parking mota yaciro tsire da kazan daya siya mata a hannu sannan ya danna wa Mariam kira. “Na’am Baba” ta amsa.
“Zo nan kicire kayakin daga mota kikai d’akin Mamanku.” Daga kitchen tafito tayi mai sannu dazuwa kafin ya amsa yaji wani erin kukan jaririya wane ana cire mata rai cike da tashin hankali ya kalli Mariam “meke faruwa? Kukan waye wancan bade na Zeezee ba?”
“Nata ne” ta fad’a wane tana enjoying kukan Zeezeen.
“Me akeyi mata?”
“Wankan gargajiya Baaba A’ee ke mata tana miqar mata da joints.”
“Meneh?” Daga nan yayi d’akin Hafsah a 360, Mariam tace, “daidai kenan” sannan taje ta soma ciro manyan gongonin madara da ovaltine number 1 da Baba ya siyo wanda barata iya tuna when last ya siya musu kalan suba.
Yana shiga ciki yaci karo da A’ee zaune kan kujera da bahon wanka gabanta ta juya hannun Zeezee a baya tana matsawa ayayinda Zeezee keta ihu kan ba gobe “Subhanallahi! Ya haka me kike mata A’ee?” yayi maganan yana k’ok’arin ajiye ledan tsiran kan kujera a yayinda Mama ke zaune kan kujerar, kafin Baaba ta amsa Mama tace, “sannu dazuwa Alhj, wankan gargajiya A’ee ke mata.”
“Wanka ko azabar da yarinya?” Be jira me zasuce both ba ya k’wace Zeezee daga hannun A’ee.
“Alhj ya da haka?” Mama tayi maganan baki bud’e haka ma A’ee.
“Banason wankan in baza kuyi mata asalin wanka ba se abar wankan gabad’ai haba me haka?” Ya kwantar da Zeezee a jikinsa yana bubbugata ko zatayi shiru amman ina se kuka take. “Daga yau kada a sake yimata wannan wankan, ke Hafsah kinada matsala wallahi d’iyarki na kuka amman ko a jikinki wad’ancan sakararru biyun kuma” ya dawo da kallonsa kan su Ibraheem da suke da shirin dariya. “Kaman ma kukan nata dad’i yake masu.”
“Amman Alhj fa kasani wankan nan dole ne shi ze miqar mata da kasusuwa ya hana kasala ko Yasmeen ma anyi mata kuma da chan bakayi magana ba.” A’ee ta gwada masa bayani.
“Naga ai wannan Zeezee ce ba Yasmeen ba, bana so nide na fad’a muku aka sakeyi ko a bayan ido na ban yafe ba.”
“Toh munji kawota a gama mata wankan.” Mama ta miqa hannu tana jiran ya dire mata Zeezee.
“Eh kafin nan kibata mama tasha tayi shiru.”
“Toh ai naga seda ruwan nonon zan iya shayar da ita kokuwa? Kuma babu.”
“Wannan ba matsala bane ina Mariam kawo madaran nan” dai-dai nan Mariam ke shigowa da gongonayen madara da ovaltine, baki Mama ta bud’e in suprise “Alhj wannan fah?”
“Madaran ki saboda Zeezee tasamu ruwan nono itama.” Hannu ta tafe, “lallai Baban Zeezee dagaske kake!”
“Niba wannan ba yanzu had’a kisha kibata mama tasha.”
“Kawota bara’a rasa na bata ba.” Nan da nan Mama ta amsheta ta shayar da ita sannan aka gama yima Zeezee wanka aka shafa mata mai anzo sa kaya tasoma kuka.
“Kekuwa A’ee kiyi mata a hankali mana bafa Yasmeen bace kina wani sa mata kaya da k’arfi da kuma hanzari haka seki b’alla mata hannu ai. K’asusuwanta ba k’wari garesu ba.” cewar Baba.
Mama kanma kasa cewa komi tayi dan mamakin sabon halin Baba da take. A’ee ne ta tab’e baki tace, “yanzu Alhj sa kayan ma koya min za kayi? Ko ka manta ungozoma ceni?”
“Chan miki nide kimata a hankali in kuwa bara kiyi ba zan mata da kaina.”
“Yi hak’uri zan mata.” Nan tabi Zeezee a hankali ta gama shiryata tsaf cikin baby pink rigan sanyi da shawul, amsheta yayi daga hannun ta ya nufi bakin k’ofa da niyyan fita, yana kaiwa bakin k’ofar Mama ta dakatar dashi ta hanyan kiran sunansa.
“Baban Zeezee ya haka? Ina zaka kaita?”
“Ina kuwa? D’aki na mu zauna.”
“Toh Alhj in ‘yan barka suka zo ganin baby fah, se in ce masu meh?”
“Se kice masu babyn na gun Babanta meson ganinta yazo d’akina, kuma ki tabbata kinsha tea da kyau kar Zeezee tasoma jin yunwa kice ba ruwan nono.” Yana kaiwa nan ya fice cike da mamaki Mama ta kalli A’ee dake kallonta itama sannan ta tab’e baki tajawo cup ta had’a tea tana kurb’a a hankali. Koda ‘yan barka suka fara zuwa Mama taje d’aki ta samu Baba kan yabata Zeezee haka yaqi ya sake nanata abinda ya gaya mata akan duk meson ganin *_‘YAR GATA_* yazo d’akinsa.
*~ *~ *~
Bayan Sallan Isha Baba na a zaune a d’akinsa da Zeezee kwance kan cinyarsa se buga budget na bikin suna yake, Zeezee ta soma ‘yar kuka take yayi gefe da abinda yake ya nufa d’akin Hafsah inda ya tarar da ita tana bayi tana wanka. K’ofan ya k’wank’wasa daga ciki tace, “waye?”
“Baban Zeezee ne me kike kifito.”
“Alhj wanka nake.”
“Nasani ai shine nace kifito.”
“Inbar wankan kenan?”
“Eh kibari.”
“Toh Alhj kumfan dake jikina kuma fah?” Nan Zeezee ta dad’a kuka. “Kifito nace Hafsah karki bari na sake nanata kaina tam!” Haka nan dan dole ta watsa ruwa ta goge jikinta da sauri tafito tana tura mai baki. Hannunta yaja izuwa gado ya ajiye mata Zeezee kan cinya “gashi yi ki shayar da ita yunwa takeji.”
“Wai Alhj kana magana se kace kasan meke damunta halan kukan bacci ko k’ishin ruwa fa take ba na abinci ba, kuma na cigaba da shayar da ita minti minti haka ai seta ramar dani.”
“Karki damu za kina cin abinci bata mana da sauri ba kijin kukanta ne?” Seda ta k’are masa kallo sannan ta shayar da Zeezee har seda tayi bacci, duk anan albarka Baba keta sa mata.
“Yanzu da tayi bacci ka yarda in zare abuna?”
“Abinta de ba naki ba Hafsah zare ai tayi bacci.” A hankali Hafsah ta zare mamanta daga bakin Zeezee ta kwantar da ita. “Yanzu kuma se a barni inyi wanka aiko?”
“Sosai ma Hafsah kiyi kifito akwai tsaraban dana tanadar miki.”
“Again akan dubu hamsin d’in?”
“Sosai ma kuwa jeki, kika gama kizo ki sameni a d’akina.” Cike da jin dad’i ta miqe tare da fad’in “toh” ta fad’a bayi.
D’akinsu Ibraheem Baba yayi inda ya sami duka yaran zaune suna assignments nasu, yana shiga suka yi masa ‘sannu’ banda Yasmeen datak’i koda kallonsa, ‘yar murmushi ya saki yasa hannu a aljihu yaciro chocolate na bounty guda biyu ya miqa mata “zo ki karb’a Mamana na kaina” ba yabo ba fallasa taje ta amsa tare da yin godiya “Yauwa Ibraheem wuce kaida Omar kuje ku tsaya kan Zeezee tana bacci.” Cike da mamaki Ibraheem ya d’ago kai yana kallon Baba totally speechless, wai shin Baba bega yana assignment bane da zesa sa yima Zeezee gadi? Tambayan dayayi ma kansa kenan.
“Da kaifa nake magana d’an fari ka kuma jini koh?” Baba ya sake magana. “Kai Omar miqe! Kabar abinda kakeyi ka dawo seka cigaba.”
“Ayyii Baba assignment fa nakeyi” cewar Ibraheem.
“Ai nagani ba makaho ne ba ni, kuje kuyi gadinta in nagama abinda nake zan karb’e ku.” Ibraheem ze sake magana Baba ya daka mai tsawa “wuce nace!” A sanyaye shida Omar suka bi gefensa suka fice se gunguni suke.
*~ *~ Bayan Mama tagama kimtsa kanta ta kalli su Ibraheem da suke tsaye kan Zeezee se harararta suke ayayinda take bacci peacefully. D’an murmushi ta saki tace, “dade kunbar wanan kumbure kumburen koni mahaifiyar ku ban tsira ba inde akan Zeezee ne kuma ku hak’ura kawai wataran se labari.”
“Toh shikenan Mama wai in wannan abar zatayi bacci se an tsaya a na gadinta mschw!”
“Katayi kaji? Bari yazo ya jika ni ba ruwana, Omar d’ina karka kulasa kaji ko? Yanzu zanje in dawo seku tafi.” Daga nan ta wuce d’akin Baba dake chan babban parlour, Sallama tayi sannan ta shiga, zaune ta tarar dashi kan gado da paper akan cinyansa se budget list yake bugawa. Bayan ta zauna gefensa tace, “Alhj gani” tayi maganan tana leqa abinda yakeyi nan taga budget yake had’awa kona meh oho?
“Yauwa ina zuwa, Hafsah” yana kai wani point ya ajiye biron ya miqe ya nufa wardrobe nasa tare da ciro wasu manya-manyan shopping bags guda biyu ya dire mata a gaba “wannan nakine, wannan kuma na Zeezee.” ya nuna mata da yatsa. Baki ta sake in shock.
_Bade kayaki bane cike ciki?_ tambayar data iya tama kanta kenan aiko tana bud’ewa ta tabbatar da zaton datake, d’ayan cike yake da zannuwa manya dakuma laces sekuma d’ayan kayan babies had’ad’d’u qualitative ones.
“Alhaji duka wad’annan?!” Abinda bakinta ya iya furtawa kenan.
“Ai ba yawa Hafsah, farin cikinki yafiye mani komai a duniya, kalamu barasu iya kwatanta irin farin cikin da kika sanya ni ciki ba yau kinga ko dole insan taya zanyi in kwatanta miki, komi anan naki ne dana Zeezee.”
“Wayyo! Baban Zeezee you are too much duka wad’annan?!” Ta zazzago kayakin k’asa tana bi da kallo kap ciki ba k’arami zani. “Nagode sosai Baban Zeezee Allah ya qara bud’i yabarmin kai.”
“Ameen Hafsah ta ai ni naki ne ke kad’an ki.”
“Ba kishiya koh?” Ta gwada jin bakinsa.
“Haba! Ai alk’awarin nan dana d’au miki tun kafin muyi aure yana nan har yau kuma har gobe.”
_“Kafin ke ba kowa Hafsah, haka zalika bayan ke ma ba kowa, kece first and last I’m all yours”_ Hafsah ta nanata alk’warain da Baba yayi mata tun kafin suyi aure.
“Exactly! Kinga ko ba zancen kishiya duk abinda nake so nake buk’ata kina dashi kina yimin dan meh zan miki kishiya?”
“Gaskia ne Alhj Allah yabar soyayya I love you.”
“I love you too” ya yi maganan tare da zama a gefenta.
“Alhj na kayakin nan sunyi yawa! Karka biye min da Zeezee ka tsiyaye kana mana siyayya wallahi koba kayakin nan ma ni am satisfied and happy...”Ta nisanta “amman fa kace bakada kud’i kwana biyun nan ina kasamu kud’in wannan siyayya?”
“Ai na gaya miki inde akanki da Zeezee ne toh inada millions.” Baki ta tab’e ba tare da tace komai ba se bin kayakin take da kallo chan ya miqo mata dubu hamsin “as promised, wannan kuma sekiyi d’inki dashi koh?”
“Alhj!! Karkasa in kasa bacci mana yau.”
“Aikuwa dana ji dad'i kinga sekita gadin Zeezee.”
“Toh nikam ba abinda zance banda Allah ya qara bud’i barin je in samu Zeezee su Ibraheem su samu su gama homework nasu.”
“Toh toh ba abinda kike buqata again koh? In akwai speak up.”
“Ba komai Baban Zeezee... Yauwa nace me kakeyi shigowa na? Naga kaman budget kake had’awa kona meh?” ‘yar murmushi ya saki “karki damu you’ll find out soon My Dear.” Bayan d’an nazarin datayi ta juyo tana kallon sa kamar yadda shima ke kallonta “Alhj bade taron suna kake planning yiba koh?”
“Me kike fad’i wai? Jeki samu Zeezee kibar suaratan banza” daidai ze miqe ta riqe hannunsa “Alhj gayamun gaskia taron suna kake shirin yi?”
“Toh haramun neh? Kuma naga yaran nan duk kowa anyi taro a sunansa se ana *_YAR GATA_* ne zakice bara ayi ba?”
“Alhj ni bafa abinda nake nufi ba kenan, kaifa kace min kwana biyun nan baka samu sosai kuma ni banga amfanin kashe kud’i ba dalili ba, taron sunan nan de ba dole bane ‘yar ragon suna aka yanka walillahil hamdh.”
“Maki kenan amman nikam senayi taron sunan nan aci asha a tayani murnan samun Zainab.”
“Yanzu Alhj murnan da mukayi nan du be isheka ba?”
“Be isheni ba Hafsah se kap ‘yan unguwa, ‘yan uwa da mutan arziki sun min congratulations zanji dad’i so tun wuri ki fara tura gayyan suna.” Baki ta tab’e tace, “toh duk abinda kace amman wallahi kasani in kazo daga baya kana min complaining cewa bakada kud’i barin saurareka ba.”
“Karki sauraran” nan ta miqe tare da ledojin a hannunta “seda safe toh.”
“A huta gajiya Hafsah ta, Allah yabamu alkhairi.”
“Ameen” har ta kai bakin k’ofa Baba ya dakatar da ita, “Hafsah please kar kiyi ignoring kukan Zeezee koda da daddare ta tashi buk’atan nono kibata.”
“Toh Baban Zeezee naji” daga nan ta fice su Ibraheem suka samu daman k’arisa assignment nasu suka yi kwanciya kasancewar da akwai school gobe.
*~ *~ ~RANAR SUNA* ~* ~*
Gidan Alhj Isma’il Yusouf cike yake da ‘yan uwa da abokan arziki se hidima ake ana ci ana sha ana d’aukan hoto, wato yadda Alhj ya tsara bikin sunan Zainab ya wuce tunanin kowa daga kan iyalansa har ‘yan unguwa. Bikin suna amman sekace na aure, komai is in abundant supply, Mama data d’au ko zob’o za’ayi serving guest dashi ta mugun shan mamaki ganin ana sauk’e canned and bottled drinks ga snacks, ba abinda babu, uwa uba ga kaji nan barkace. Babu kaman su Ibraheem da suka ringa satan drinks suna kaiwa fridge na d’akinsu, tunda yake be tab’a ganin anyi suna akayi bushasha haka kamar na Zeezee ba, ba shakka Zeezee *_‘YAR GATA CE!_*
Bikin suna de ba abinda za’a ce banda Allah shi raya Zainab dan kuwa abin se wanda yagani!
_6:50PM_
Yawancin mutane sun watse kad’an daga ciki ne suka rage wanda yawancin su ma dangi ne, Hafsah da Zeezee sunci kyauta sosai na sosai zannuwa da kayan baby har neman wajen sasu ake, kan gado cike yake dam da kayaki. Kwance Zeezee take bisa kan gado agefe guda tana ta zuba bacci ita kad’ai a d’akin. Daga bisani tasoma kuka alokacin Mama na bayi tana watsa ruwa se sauri sauri take tafito ta d’auketa, ai kaman alarm Baba keda yajiyo kukan Zeezee ya shigo da hanzari ya tarar da ita se kuka take. Da hanzari ya d’agata yashiga danna wa Hafsah kira.
“Na’am Alhj gani fitowa ” nan da nan tafito.
“Kinajin Zeezee na kuka bara ki bar duk abinda kike ba ki d’auketa? Ina yaran suke?”
“Sun shiga nan mak’ota, Alhj da Allah riqe min ita in samu in sa kaya.”
“Har kisa kaya tana jirar ki kenan? Amsheta ki shayar da ita.”
“Wai-” katseta yayi, “bana son jin wani zance amsheta nace” haka ba yadda Mama ta iya ta karb’eta ta shayar da ita har seda ta koma bacci Baba ya yarda ta zare maman.
Da misalin k’arfe 9:34PM Mariam dake taya Mama kwana tun haihuwan Zeezee tashigo cikin shirin baccinta ta dire bargonta gefen Zeezee tare da k’are mata kallo. Lallai kuwa gaskian jama’ah kap cikinmu ba me kyan wannan ‘yar jaraban tayi maganan a zuci tare da sakar da tsaki a fili ba tare da tasan tayi hakan ba, tas taji an buga mata k’eya har ribbon nata na neman fad’i a hanzarce cike da rikicewa ta juya tana kallon direction dataji sauk’an marin, Baba taga tsaye akanta.
“Baba nikuma menayi?” Ta tambayesa tana shafa k’eyar tata.
“Zeezeen kike kalla haka harda jan tsaki?” Daidai nan Mama tafito daga bayi itama da shirin kwanciya.
“Baban Zeezee ya haka? Baka kwanta ba?”
“Ina kuwa zan kwanta bayan jikina na bani keda wannan muguwan” ya nuna Mariam da yatsa “kuna ignoring Zeezee da daddare saboda haka anan zan kwana yau. ”
“Anan kuma?” ta tambayesa fuskarta d’auke da neman k’arin bayani.
“Eh anan Hafsah ai na gaya miki jiki na na bani da daddare kuna barin yarinyan nan tai ta kuka da wannan muguwan yartan” ya galla wa Mariam harara yanzu kuma.
“Yo Alhj ba sena gama arba’in ba tukunah?”
“Ke kika sani, nide anan zan kwana Mariam fice kije ki d’ago Yasmeen daga d’akina ki kaita d’akinku achan zata kwana yau.”
“Toh” ta fad’i tana jin dad’i dama harga Allah ta gaji da tashi kullum da daddare tana yawo da Zeezee a hannu har seta koma bacci, “seda safe Mama, seda safe Baba” tace dasu tare da ficewa.
Bayan Mama taja comforter ta kwanta ta kalli Baba dake zaune gefen gadon yana ma Zeezee addu’a tana turo baki tace, “ni wallahi Alhj nasan yau hanani bacci zakayi in kasa wannan Zeezee agaba.”
“Ai dama nasani ignoring nata kike da daddare kuma daga yau hakan bare sake faruwa ba” nan ya miqe ya kashe masu wuta suka kwanta da Zeezee rigingine a jikinsa.
_2:47AM_
Cikin bacci Baba ya soma jin kukan Zeezee, take ya tashi tare da kunna wutan d’akin ya d’agata yana jijjiqata ganin tak’i yin shiru ya maido da kallonsa kan Mama da tayi kamar bataji kukan Zeezee ba tana ta bacci.
“Hafsah!” yayi whispering sunanta, shiru bata amsa ba.
“Hafsah tashi nasan kina jina tashi nace ko ba kijin kukan Zeezee ne?”
“Alhj dan girman Allah ka barni in huta, ka fa san irin hidiman da na sha jiya.”
“Meaning baraki bata mama ba kenan komeh? Tashi nace!” yasa hannu yana jijjiqata da k’yar ta miqe ta zauna tana galla mai harara har a nan Zeezee bata bar kuka ba. Chan ta miqa hannu ta d’ago feeder’n Zainab ta mik’a mai, “gashi bata ruwan tasha k’ishi takeji” kallonta kawai Baba ya tsaya yi totally speechless mah.
*© MIEMIEBEE*
PAGE 03
*December, 2016*
“Amshi mana Alhj bacci fa nake ji.” Ganin baida niyyan karb’a ta ajiye mai akan gadon ta juya zata kwanta, sede wani hanzari ba gudu ba kafin kanta ya dire kan pillown Baba yasa d’ayan hannunsa yaja “hab-” take ya katse ta;
“Bana son dogon surutu karb’eta nace ki karb’eta mana!” haka tana gunguni ta amshe Zeezee ta shiga bata mama da zaran tace zata cire Baba ya hanata, yau kam koda Zeezee tayi bacci Mama ta gwada zare maman daga bakin Zeezee seta sa kuka haka Baba ya sata gaba ta kwanta mamanta maqale bakin Zeezee, da zaran tace zata cire Zeezee tasa kuka Baba yahau mata surutu a takaice de a tak’ure Mama tayi bacci ranan.
*~ *~
Mu kwana mu tashi be ragar komi ba, a yanzu haka Zeezee nada 4 months a duniya, yarinya tana girma tana dad’a kyau ko kad’an hasken ta be gushe ba, ga gashi masha Allah. Gatan da Baba ke bata yasa har ita Mama kanta abin na bata haushi atimes, banda yayyun ta da suka d’au karan tsana suka aza mata dan duk wani abinda Baba yasamu Zeezee kad’ai ya sani komai Zeezee, Mama tayi tayi dashi a fara baiwa Zeezee madara amman yaqi haka har ta rame dan irin shan nono na Zeezee bata qi a yini ana shayar da ita ba. ‘Yan unguwa kuwa kowa yasan Baba da Zeezeen sa duk da 'Baban Zeezee' suke kiransa akoda yaushe da yamma ze zauna a harabar bakin gate na gidanshi da Zeezee ajikinsa suna shan iska, kap cikin yaransa ba wanda yake jinta a jikinsa kaman Zeezee kodan tanada sunan margayiya ne oho?
****
Zeezee ce kwance bisa kan gado da abin wasanta a hannu se wasan miyau take ayayinda Mariam ke k’ok’arin canza mata diaper (pampers) se wani tuttura baki take daidai ta cire ma Zeezee used diaper d’in tana k’ok’arin sa mata sabo kenan Zeezee ta tsula mata fitsari siiirrrr! a fuska. Ihu ta saki wanda yasa su Ibraheem shigowa da sauri ganin meke faruwa. Dariya sosai suka saki ganin fuskan Mariam na yoyon fitsari, Zeezee kuwa ganin yayyun ta na dariya itama ta kama dariyar, ba kaman Ibraheem da har yana dafe ciki, kusan a tare Mama da Baba suka shigo suna tambayan meke faruwa a zatonsu ba lafiya ba.
Kamar wacce zatayi kuka Mariam tace, “Baba wai dariya sukemin saboda Zeezee tamin fitsari a fuska.”
“Amman Mariam kema seda na fad’a miki kibar b’ata lokaci a duk lokacin da zaki canza ma Zeezee diaper saboda incasities haka ai ga irinshi nan.” Mama ta yi scolding nata. Baba daya k’arisa kan gadon ya d’aga Zeezee yana mata wasa yace, “shine zakiyi kuka dan Zeezee ta miki fitsari? Mschw! Banason sakarci fah Mariam.”
“Ayyi Baba kalli dariyan da Ibraheem kemin fah.” Idanun Baba da na Ibraheem na had’ewa Ibraheem yayi tsit tare da calming kansa. “Dariya ko? Nasan maganinka, Hafsah amsheta kisa mata pant tasha iska” nan da nan yaran sukayi waje se neman tsokanan Mariam suke.
Chan bayan Azahar su Ibraheem suna zaune a tsakar gida suna chin abinci Baba ya k’wala mai kira, ba tare da b’ata lokaci ba ya miqe ya je kiran “na’am Baba gani.”
“Yauwa zo ka amshi Zeezee kayi mata tsarki ka kuma wanke pant d’in tayi kashi aciki.”
“What?!” Yayi exclaiming batare da yasan yayi hakan ba.
“Meh kace?”
“Bb.. Babu banji me kace ba Baba”
“Cewa nayi kazo ka ma Zeezee tsarki ka kuma wanke pant d’in tayi kashi ciki.” Fuska Ibraheem ya maraice “Baba kayi min rai dan Allah, taya zan wanke wa Zeezee kashi? Ni wallahi ban iya ba.”
“Baka iya wanke kashi ba?”
“Eh wallahi ban iya ba Baba.”
“Tohhhh... In kayi naka wake wanke ma? Ni ko Mamanku? Will you come and carry her my friend!” Ya daka mai tsawa.
“Baba dan Allah kayi hak’uri.”
“Ba ka iya ma Mariam dariya ba? Nan gaba zakayi hankali.”
“Baba kayi hak’uri wallahi na tuba.”
“Ibraheem kaji na rantse kasake barina na nanata abinda na fad’i maka ranka ze b’aci” haka kan wanda zeyi kuka ya k’ariso ciki ya amshi Zeezee daidai nan Mama ke fitowa daga wanka idanunta basu sauqa ko ina ba se kan pant na Zeezee dake a cike dam “laaa bade pupu tayi ba Alhj? Shi yasa ban son barinta ba pampers kawota Ibraheem in wanke mata in mata wanka gabad’ai.” Dad’i sosai Ibraheem yaji wanda ya kasa b’oyewa bekaiga miqa wa Mama Zeezee ba Baba yace, “ka wuce nace!”
“Ayya Baba mana, Mama tace zata wanke mata.”
“Meke faruwa neh?” Mama ta tambaya, nan Baba ya labarta mata komai ta tab’e baki tace, “Alhj dade ka barsa zan wanke mata kai kuma nan gaba se kayi hankali.” Har b’ari bakinsa ke yace, “wwa...walla..wallahi nayi, nayi hankali Mama.”
“Hafsah ki basa waje ya wanke ma yarinyan nan jiki bakyau fa barin kashi jikin yaro akwai harmful acids ciki.”
“Jeka wanke mata Babana yi hak’uri.” Mama tace dashi a hankali.
“D’an banza kawai!” Baba ya fad’i yana hararansa, haka yasa kai cikin bayin yana galla wa Zeezeen dake ta faman masa dariya harara har yasamu ya wanke mata jikinta tsaf sannan ya riqo pant d’in a d’ayan hannunsa ya fito daga bayin akan gado ya direta ya fice nan qannensa da suke ta faman leqansu tin d’azu suka hau masa dariya banda kaman Mariam da har take sauqa k’asa tana hawaye, bece dasu komi ba ya nufa bakin famfo tare da neman kara haka yana yamutsa fuska ya samu ya wanke pant d’in ya shanya. Akan yayi wajen abincinsa seya hau yin d’akinsu.
“Ya Ibraheem abincin naka fah? Ka k’oshi ne ko Yasmeen ta kai ma d’aki?” Mariam ta tambayesa full of sarcasm.
“Wallahil azimu Mariam kika sake min magana me hanani dukan ki agidan nan se Allah hegiya kawai.”
“Oho dai! Allah ya rama min, daidan ka kenan nan gaba zaka sake min dariya.”
Har ya kama tafiya yaga bare iya hak’ura ba da gudu ya nufo inda take ganin haka ta miqe itama tasa gudu tanayi yana binta har suka isa d’akin su Baba. Bayan Mama Mariam ta k’arisa tana b’uya “ya haka? Meke damunku ne wai? Shin baku iya sallama bane?” Baba yayi scolding d’insu a yayinda Mama ke k’ok’arin k’wace kanta daga rik’on da Mariam ta mata.
A fusace Ibraheem ya soma magana, “Baba wallahi ka ja mata kunne ta dena shiga harkana in ba haka ba b’ab’b’allata zanyi into pieces.”
“Ehhh sannu fah, sanu ubanta” cewar Baba cike da mamaki yana mamakin k’arfin hali irin na Ibraheem. “Kai d’in ba dariyar ka mata d’azu ba? ” Shiru Ibraheem yayi bece komai as se harara n Mariam yake. “Da kai fa nake?!”
“Alhaji ya isa please, Ibraheem Baba na kayi hak’uri” Mama tace cikin sanyin murya sannan ta dawo da kallonta kan Marian “ke kuma ki shiga taitayinki kidena yima wan ki rashin kunya kina ji ko?” Baki Mariam ta turo “toh Mama ni d’azun bemin dariya bane?”
“Oya find your way out!” Baba yayi masu nuni da hannu. Ganin Ibraheem yak’i motsawa Mariam ma tak’i fita.
“Daku fa nake” this time a tsawace.
“K’el” cewar Ibraheem yana nodding kai yana kallon Mariam nufin ‘inya kamata d’innan’ daga nan ya fice ya b’oye bakin k’ofa Mariam na fitowa ya cafko hannunta tare da danna mata nank’washi me uban zafi akai, k’ara ta saki sosai idanunta auka ciko dm da hawaye, “Allah ya isa mugu kawai” ta murgud’a mai baki beyi ta kanta be ya wuce BQ ko a babu ya kusa sata kuka.
Bayan Sallan La’asr Baba ya shirya tsaf ze fita kasuwa, ganin haka Mariam tabi sahunsa Mama dake a kitchen tana had’a dinner tayi tsaye tana kallonsu ta window.
“Baba!” Cewar Mariam, chak Baba ya tsaya tare da kewayowa.
“Wani abu ne Miryaamu?” Ya tambayeta.
“A’a Baba” tace tana wasa da yatsun ta, “uhm Baba nace ko akwai kud’i zaka siya min jakar makaranta nawa ya tsufa.”
“Yaushe ne na siya miki jakan Mariam?”
“Baba tun last last year fa, tun primary 5.”
“Toh naji Mariam, Allah ya kawo kud’i.” Shiru tayi bata ce komai ba as tana nazarin wani irin kud’i Baba yake magana baida shi. “Ba kiji me nace bane? Allah ya kawo kud’i.”
“Amman fa Bab-” da sauri ya katse ta “in baki iya fad’in amin ba seki jira in Maman ku ta kwashe adashe ta sai miki.”
“Ameen” ta fad’a a hankali sannan ta juya ta basa waje. Seda Mama taga ficewar Baba daga gidan takira Mariam take mata magana.
~* ~* Da goshin Maghrib Baba ya dawo daga fitan da yayi, wasu manya manyan shopping bags ne k’waya biyu hannunsa wanda ya shige dasu d’akinsa nan da nan ya d’auro alwala ya fice masallaci. Ashe kam tun shigowansa su Mariam suke leqensa yana fita suka shiga d’akinsa ita da Omar suka soma neman inda ya dire ledojin daya shigo dasun, cikin wardrobe nasa suka samu suka zaro tare da bud’ewa kayaki ne bil adadi masu kyan gaske wanda ko ba’a gaya ba ansan masu tsada ne duk na Zeezee ba ko na Yasmin d’ai ciki, dam ledojin duka kayakin Zeezee ne ciki bayan ko wanda aka mata suna dasu ma bata gama sawa ba amman ya sake yimata siyayya, Mariam da tace a sai mata jaka ance mata ba a da kud’i.
Omar ya nisanta yace, “ai dama na sani when it comes to Baba and Zeezee expect more.”
“Amman Omar yanzu Baba ya kyauta? Wallahi su Bilqees, Khadija, Sadiya dasu Halima a class namu har dariya suke min akan jaka ta.”
“Hak’uri zakiyi Adda Mariam tunda aka haifo jarababbiyar Zeezeen nan kam ai namu ya qare” ahaka ya taimaka mata suka miyar da kayakin ledan. Bayan Mariam ta idda Sallan Maghrib taje tasamu Mama ta mata bayani, cike da mamaki Mama tace, “lallai Babanku! ina Zeezee zata zo ta kai kayakin? Karki damu Mama na zan mai magana za’a siya miki sabon jakar kinji?” Kai Mariam ta gyad’a “nagode Mama” nan ta nufa d’akinsu suka hau kallo.
Bayan dawowan Baba ya kinkimi ledoji yayi d’akin Mama dasu, zaune ya tarar da Zeezee cikin gadonta se wasa take, tana ganinsa ta soma tsalle nufin ya d’auke ta, bayan ya gama yimata wasa ya cire mata kayan jikinta ya hau gwada mata sabin daya siyo wanda duk suka mugun amsheta. Ana cikin haka Mama ta shigo da sallamarta ta zauna a gefensa tana kallonshi daga bisani tace, “sannu da k’ok’ari kaya sunyi kyau.”
“Sekin fad’a ma? Ai nan da kike gani duk kayan dubu hud’u da d’ari biyar (N4,500) yayi sama ne, a shagon Yusha’u na siyo su.” Baki Mama ta dafe da hannunta d’aya tace, “yanzu Alhj kayi adalci kenan?” Cike da k’in nuna damuwa yace, “name fah?” Yana me sake gwada wa Zeezee wani kayan.
Mama bata b’oye komi ba ta basa labarin dukkanin abinda tasani, shiru Baba yayi chan yace, “ni wallahi banason suratai yanzu me kikeson implying? Bana adalci tsakanin yaran nan ko meh? Jaka de baze kawo fad’a ba.” Hannu ya cusa a aljihu ya fito da dubu d’ai-d’ai ya irga biyar ya watsa wa Mama “seku siya mata jakan, da an sai wa yarinya kaya shikenan kowa idonsa na kai toh Allah kyauta.”
“Ameen koma me de ka bada kud’in jakan.” Cewar Mama tana k’ok’arin barin d’akin. Ko uffan Baba bece da ita ba ya cigaba da abinda yakeyi.
★★★
Gata mara misaltuwa Zeezee ke samu gun Baba a yayin da hakan ke tusa tsanar ta gun ‘yan uwanta. Sosai take girma wane kazan agric sam Baba bai barin Mama tabar ta da yunwa, aduk lokacin da Zeezee ta soma jinyan hak’ori kuwa Baba ji yake kamar shi ke rashin lafiyar duk yabi ya tada wa kowa hankali a gidan barin ma Mama da take yini tana shayar da Zeezee 24/7.
Zazzab’in sati biyu Zeezee tayi ta mulmule ta sake komawa old self nata. Da yamma bayan yaran sun tafi islamiyya Baba kuwa tun fitarsa safe be dawo ba Mama tafito rik’e da Zeezee a hannu, d’ayan hannunta kuwa ribbons ne da comb da kifiya da alama so take ta kamawa Zeezee gashin ta bayan ta nemi kujera ta zauna ta shafa mai akan sannan ta soma tajewa a hankali, comb d’in na tab’a gashin, Zeezee tasa ihu a rayuwa in akwai abinda ta tsana shine a tab’a mata kai dai-dai nan neighbours nata su Maman Sudeis, Ummu HH, Maman Sultan da Maman Samha suka shigo dan duba jikin Zeezee dan ko basu da labarin ta warke. Sannu da zuwa Mama tayi musu a yayinda suka k’ariso kan daddumar dake a kusa da Mama suka zauna bayan gaisuwa suka tambayi ya jikin Zeezee Mama take cemasu jiki da sauk’i, anan suka soma hira. Da zaran Mama ta tab’a kan Zeezee seta sa ihu.
Maman Sudeis ce ta bada shawara kan asa ma Zeezee mama a baki zatayi shiru, hakan kuwa Mama tayi, kum Zeezee tayi tsit wane bata gidan sede Mama na sake tab’a gashin ta saki maman tasa ihu, dariya Maman Samha da Sultan sukayi suna mamakin wayo irin na Zeezee “wato ita de kar a tab’a mata kai.” cewar Ummu HH. Maman Samha ta tab’e baki tace, “ai kuwa de ga gashi har gashi amman bayason kulawa, ina ma ace Samha ta keda wannan gashin? Yanzu ya zakiyi toh Maman Zeezee?”
Mama ta kalli Zeezee da tayi lamo a jikinta sannan tace, “danne ta zanyi wallahi ai Baban nasu bai gida, ‘ya‘yan kowa ana masu kitso ni bance zan mata kitso bama, d’an kamawa da ribbon da zan mata tace baza ayi ba!” Nan tasa comb tana taje sumar, Zeezee na dad’a ihu kaman ana cire mata rai tasha mama ma tak’i se ihu take amman haka be hana Mama fara sa mata ribbon d’in aka ba. Daga sama kawai ta jiyo sallaman Baba, ko kad’an bataji k’aran honk na motansa ba kodan kukan Zeezee ne oho? Cike da tashin hankali ya nufo inda matan suke zaune. Ko ta kan gaisuwan da su Maman Sudeis suke mai beyi ba ya soma masifa.
“Ya haka? Meke faruwa Hafsah?!”
“Sannu da zuwa Alhj.” cewar Mama.
“Ba abinda na tambaya ba kenan” yayi maganar tare da d’ago crying Zeezee daga cinyan Mama yana lalashinta har ta samu tayi shiru, se anan ya amsa gaisuwan su Maman Samha.
“Ina jinki Hafsah me kike ma Zeezee kukanta ya cika unguwa haka?”
“Alhj me zan mata? Gashin nata na keson kama mata naga yayi tsawo dayawa ana barin sa haka.”
“Da kuma bata so fah?”
“Al-” yayi saurin katse ta;
“Nace da kuma bataso fa? Me ya kamata kiyi?”
“In bari” ta fad’a sounding humiliated a gaban k’awayenta yana scolding nata haka. Ido ta d’an mai ko zeyi shiru ya bari se bak’in nata sun tafi yaso se yayi scolding natan amman ina se kaman cewa ma tayi ya cigaba.
“Toh meyasa baki barin ba? Kama kan banza da wofi!” ya miqa hannu kan cinyarta yayi watsi da ribbons d’in, “kinsa yarinya kuka ba gaira ba dalili dududu yaushe yarinyan ta samu sauk’i neh? Wallahi Hafsah ki kiyaye ni.” Ran ta ne ya b’aci bata san a lokacin da tace, “shikenan kai Alhj ba’a isa a tab’a yarinyan nan ba ka hau ma mutum surutu? Kalli kan Samha nan ba kitso neba akai? Amman kai kace wai bara’a tab’a ba se a aske gashin ai kowa ya huta.”
“Bara a aske ba bara kuma ayi mata kitson ba haka za’a bar gashin ku kuma Maman Sudeis da saura ina ganin ku da hankali amman kuna ganin Hafsah na rashin hankali baraku mata magana ba?”
“Kayi hak’uri Baban Zeezee hakan bare sake faruwa ba” cewar Ummu HH.
“Allah kyauta” ya fad’i tare da nufan ciki, binsa Mama tayi da harara tana meh mamakin hali irin na Baba, kap cikin yaranta ba wanda Baba ya tab’ayi mai abu haka banda Zeezee. A time na Yasmeen ma kam sata yake a mota ya kaisu gidan kitso yace ayi ma Yasmeen amman na Zeezee yace bara’a tab’a kanta ba? Toh Allah kyauta!
Hira kad’an suka tab’a da friends nata tayi masu rakiya sannan ta dawo ciki.
Ita a zaton ta ma Baba d’akinsa yake ashe a nata yake ya zauna kan gado yana wasa wa Zeezee, tana shiga ta gansa kafin ta juya ya kira sunanta chak ta tsaya tare da kewayo wa. “Gani” ta fad’i rai a b’ace sam ba annuri a fuskarta, daya gano hakan seya saki murmushi ya gyara zamansa kan gadon.
“Haba! Hajiya Hafsah ta ya da haka kuma?” Banza dashi tayi. “Maman Zeezee dake fa nake.”
“Alhj kaga zan d’aura girki in wani abun kake buk’ata ka fad’amin inada abinyi.” tayi maganan in an I don’t care manner.
“Zo ki zauna anan” yayi mata nuni da space dake gefensa nan ma tayi banza dashi “yi hak’uri mana Maman Zeezee nayi kuskure toh amman kiyi hak’uri.” Sexy long eyes nata wanda Zeezee tayi gadonsu ta d’ago tana kallonsa a yayinda ya kashe mata ido d’aya “yi hak’uri my wonderful Wife.” Batasan a lokacinda ta saki murmushi ba taje ta zauna gefensan kamar yadda ya buk’ata. Dad’i sosai yaji “yauwa ko kefa tawan?”
“Uhm” tayi murmuring.
“Nace kafin ki shiga kitchen kid’an bawa Zeezee mama inason mud’an fita strolling da ita.”
“Wai Alhj ni shikenan kullum cikin bawa Zeezee mama, banida aikin da yafi wannan! Ni gaskiya wallahi na gaji a had’a mata da madara, barin iya ba”
“Kin gaji? Ke bakisan farillah neba shayar da yaro?”
“Eh nasani amman ai ba’ace koda yaushe ba, abanza ta zubar min da nono ta mai min dasu slippers, ni gaskiya banaso ina maintaining jiki na.”
“Ahh lallai fa Hafsah sannu! Sekace bana biyanki albashi k’arshen wata kamar yadda muslinci ya tanadar as kyautatawa? Ko badan haka bama baraki shayar da ‘yarki ba?” Zata sake magana ya dakatar da ita “yimin shiru ki bata muyi mu fita kema kiyi abinda ke gabanki.” Harararsa tayi ta gefen ido sannan ta amshe Zeezee ta shiga bata mama seda ya tabbata Zeezee tayi nak ya yarda Mama ta zare abinta sannan suka fice da Zeezee.
Haka nan rayuwa ta cigaba da kasancewa, family’n Alhj Isma’il Yosouf komi Zeezee, ba’a tashi kama wa Zeezee kai se in an tabbata Baba ya fita dan kuwa in yana gida bayi bari. Ahaka yarinya take girma da kuma tashi cikin gata da tsantsan so gun mahaifinta tun tana yarinya ya saba mata da samun duk wani abinda takeso.
There was a time a gidan biki Mama taje da Zeezee, Zeezee taga kayan wasa gun wani yaro ta ringa kuka tana shure k’afafu itama tanaso, Baba najin haka ya ari sample na kayan wasan yaje ya siyo mata exactly irinsa har guda biyu, itade Mama tayi magana har ta gaji, ya zamanto ta zuba mai ido kawai yanzu. Shi da kansa wataran zeyi nadaman abinda yake ma Zeezee.
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 04
★★★
A kwana a tashi babu wuya game rai, Zeezee nada shekara d’aya (1 year) tal a duniya yanzu! Yarinya son kowa k’in wanda ya rasa, sede Mama bata fita da ita unguwa ko gidan biki ba idon kowa na akanta, ga kaya masha Allah tun tana Baby se to-match ake sa mata kasancewar Mama ‘yar gayu ce ajin farko amma wani abu Zeezee se tashi take da uban k’uiya, banda ‘yan gidansu bata san kowa ba again, a cikin ‘yan gidan nasu ma wani sa’in zab’a take, atimes in tana hannun Baba ko hannun Mama batason zuwa.
Tunda Baba yake be tab’a celebrating birthday’n yaransa ba se akan na Zeezee. Grand birthday party had’ad’d’e ya tsara wa Zeezee lokacinda ta cika 1 year. D’imemen cake ya sai mata akayi celebrating, families ne da ‘yan unguwan da basu fi a k’irga ba se friends nasu Mariam suka ziyarci party’n. Su Mariam se palli ake anje an gayyato friends gabad’ai ana ta rawan kai. Se a ranan suke marmarin Zeezee kan ba gobe saboda ganin yadda tayi kyau. Har dan haka suka so yin fad’a ita da Omar. Sosai Zeezee tayi kyau ranan, an gyara mata gashinta cikin colourful ribbons, bugu da k’ari kuma ga yadda glassy green princess ball gown nata ya mata kyau da silver crown nata. Pictures suka sha sosai, suka ci suka sha suka kuma chashe!
_Wannan ke nan!_
Tun da Zeezee ta cika shekara d’aya da watanni biyar a duniya Mama ta soma zancen yayeta amman inaaa Baba ya hana wai sam se Zeezee ta k’ara watanni uku ko hud’u kamar yadda muslinci ya tanadar sannan ze yarda a yayeta.
“Haba Alhj dan Allah! Yarinyan nan de tayi wayo ko a yanzu aka yayeta ba’ayi depriving nata komi ba, aiko a muslincen ma cewa akayi 18-20 months ba’a ce lallai se yaro ya cika 20 months d’inba tukuna kuma yarinyan nan is 17 months now me marabar 17 da 18?” Baba da yayi shiru yana sauraronta tun da ta fara wannan zuba yace;
“Ki fad’i koma meh Hafsah, kin ga dama kita bayani daga nan har gobe but believe me wallahi se yarinyan nan ta cika watanni ashirin (20) d’innan ki yayeta.” Yayi maganan tare da miqewa da Zeezee a hannunsa.
“Ai sede in kai zaka cigaba da shayar da ita, yarinya gata doguwa ina ma ace wacce bata girma ne! Ni wallahi har kunyan cireta nake cikin jama’a zan shayar da ita, mutane se gani suke kamar ma tayi girma a shayar da ita saboda tsawonta.”
“Awww! Yanzu Hafsah sabida bakin jama’a kikeson tauye wa Zeezee hak’k’inta? Da kyau ban yarda ki sake fita gidan suna ko biki ba har se in kin yaye Zeezee kuma ki shirya nan da anjima zan kawo ta ki bata mama seta k’oshi sannan kiyi wani harkan gabanki.” Be jira me Mama zata sake cewa ba yayi tafiyarsa.
Anyi haka da kwana uku tafiya ya tasowa Baba zasa Lagos saro laces da zannuwa da sauran abubuwa, ranar Asabar tafiyar ta kama. Duk iyalan nasa suna a garriage suna jiran ya shiga mota su mai ‘Allah kare’ amman ina seya kama hanyan zuwa mota ya dawo ya karb’e Zeezee, itama data gane tafiya zeyi se kuka take tana ‘Baba’ duk jikin sa yabi ya mutu seji yake kan ya fasa tafiya if only an yaye ta da yayi tafiyan da ita. Da k’yar ya iya ya shiga mota yayi wining glass k’asa yana kallon yadda Zeezee keta kuka hannun Mama.
“Toh ki lalasheta mana Hafsah!”
“Alhj wani irin lalashi ne ban ma yarinyan nan ba? Ai inba wai tafiya kayi ba barata bar kukan ba.”
“Zeezee na yi hak’uri kinji barin dad’e ba zan dawo.” Cikin kuka take ta fad’in “Baba... Baba... Baba.”
“Toh wallahi Hafsah sauran bayan tafiya na ki yaye Zeezee ki jira kiga abinda zan miki.” Shiru tayi batace koami ba, “dake fa nake magana!”
“Yanzu Alhj nace wani abu ne? Allah dawo da kai lafiya.”
“Ameen, kuma kar ki barta da yunwa, Ibraheem, Mariam nabar Zeezee a kulawanku in wani abu ya sameta ban yafe ba.”
“Toh Baba Allah ya kare hanya ya dawo da kai lafiya” yaran suka fad’i a tare. D’ari biyar-biyar ya bisu dashi sannan ya tada mota nan fa Zeezee ta fara sabon kuka ahaka Mama tayi ciki da ita. Yau Baba ya tafi washegari Mama ta yaye Zeezee, yarinya data saba kowani minti shan nono kam seji take duniyar ma gabad’ai ba dad’i tata kukan ‘mama... mama’ ina sede Mama ta d’au abinci ta bata haka zata k’i chi da yamma Mama ta aika Ibraheem kasuwa ya siyo cerealac aka fara bawa Zeezee sam tak’i sha ita wai se mama seda yunwa yaci k’aniyanta ta amince tasha cerealac d’in. Na yini biyu Zeezee ta saba dashi sede still atimes zata ta kukan mama ko tata sa hannunta cikin kayan Mama amman hakan bai sa Mama ta cire ta bata.
Baba kuwa tun tafiyarsa kullum se yayi video call yasa a had’a sa da Zeezee ya tai mata wasa tana dariya. Sati d’aya cus Baba yayi kamar yadda Mama tayi addu’a dan kuwa inhar ace before a week ya dawo tsab zece beji abinsa haka ba se an mayar wa Zeezee nono amman yanzu da ya kai sati Zeezeen kanta ta manta da nonon. Pounded yam and eghusi soup me rai da lafiya Mama ta shirya wa Baba sannan duk sukayi wanka suka shirya tsaf bayan kintsa gidan da sukayi sannan suka fara zaman jiran shigowan Baba.
Da misalin k’arfe 5:14PM Baba ya shigo Bauchi seda ya tsaya a Bauchi club ya siyo masu gashi sannan ya k’arasa gida duk sun yi murnan dawowan sa tare da mai sannu da zuwa sannan suka soma shiga da kayakin ciki, shide Baba Zeezee ya amshe yana ta mata wasa sosai itama taji dad’in dawowan Babanta.
*~ *~ Zaune suke duka a parlour se cin tsire suke suna sipping cool Maltinan su hankalin kowa na ayi a gama ci abud’e kaya. Baba dake tauna naman yana bawa Zeezee yaga alaman kamar yunwa takeji dan yadda take taci har in be sa mata a baki da wuri ba ta soma kuka. “Hafsah anya kuwa yarinyan nan ba yunwa takeji ba?”
“Yaushe ne ta sha cerealac natan?” Tayi maganan ba tare da tasan how and when ba.
“Dawo baya meh kikace?” Baba yayi maganan cike da k’in gaskata abinda kunnensa suka jiye mai. Nan fa Mama ta shiga kame-kame tayi tsit ta kasa cewa komai. “Dake fa nake Hafsah, meh kikace?”
“Alhj...” Ta kasa k’arisa maganan.
“Yayeta kikayi koh?” Shiru... “Nace yayeta kikayi ko?!” Yayi maganar cikin sautin tsawan da yasa Zeezee cusa kanta jikinsa. “Wai mesa bara’a tab’a gaya miki magana kiji bane iyyeh? Mena gaya miki kafin nayi tafiyar? Kinsan ko gun Allah kinada laifi koh?”
“Alhj kayi hak’uri” be sake cewa komai ba ya miqe ya bar musu wajen nan su Mariam duka suka dawo da kallonsu kan Mama. Ibraheem yace, “Mama wallahi da baki yaye wannan Zeezee ba a banza yanzu ran Baba ya b’aci d’an tsaraban da ya kawo manan ma seya fasa badawa.”
“D’an banza abinda ke daminka kenan koh? Mschw!” Nan itama Mama ta miqe tabi sahun Baba, d’akinta ta fara dubawa bata gansa ba hakan yasa ta nufa d’akinsa direct, k’ofar tasamu a rufe tayi knocking shiru Baban dake zaune bakin gado yana bawa Zeezee bobo yayi be amsa knock natan ba.
“Baban Zeezee na shigo?” Bata jira amsar sa ba ta bud’e k’ofar ta shige, ko d’ago kai ya kalleta beyi ba se feeding Zeezee yake. A hankali tazo ta zauna gefensa a bakin gadon tana kallon yadda Zeezee keta shan bobon sekuma ta bata tausayi taji dama bata yaye tan ban. “Baban Zeezee kayi hak’uri nayi laifi.” Kamar wanda bareyi magana ba yace;
“Ita ya kamata ki baiwa hak’uri bani ba” yayi maganar ba tare da ya d’aga kai ya kalle ta ba. Daga nan Mama bata sake fad’in komi ba seda Zeezee ta shanyen bobon sannan ta miqa hannu ta d’agota daga cinyan Baba ta aza ta kan nata. Hannu tasa ta ciro mamanta ta gwada kaiwa Zeezee duk Baba na kallonta bece ko uffan ba sede abin mamaki ko kallon nonon Zeezee bata son yi hasali kuka ma ta soma kai Baba ya kad’a yace, “tsami kika ringa shafawa bakin nonon seda kika kori hankalin ta daga kai ko ba haka ba?” Shiru Mama tayi duk kunya yabi ya kamata, “ko ba haka ba?” Ya sake tambayar ta. A hankali ta gyad’a kai.
“Kin kyauta sosai bani ‘yata” ya miqa hannu ya amshe Zeezee.
“Alhj nafa baka hak’uri we are humans we all make mistakes wallahi da zata kama maman yanzu na yarda zan cigaba da shayar da ita se lokacin da ka yarda a yayeta, kayi hak’uri kaji?”
“Yaushe kika yayetan?” Chan k’asa k’asa tace, “washe garin tafiyar ka.”
“Hmm! kin kyauta Hafsah.” Hak’uri Mama tata bashi da k’yar ta samu ta shawo kansa ya hak’ura. Bayan Sallan Maghrib duk ya tara yaran a parlour ya ciro wa kowa tsarabansa Ibraheem da Omar English wears qualitative jeans da T-shirts set biyar-biyar, Mariam laces uku masu tsadan gaske da atamfofi super biyu, se Yasmeen laces biyu da ‘yar kanti masu kyau guda uku. Mama kuma laces biyar da atamfofi super biyu, se Yasmeen laces biyu da ‘yar kanti masu kyau guda uku. Mama kuma laces biyar da atamfofi super biyu sena uwa uba Zeezee wanda suke nan fiye a k’irga.
★★★
Life couldn’t be better for Zeezee! Wato duk wani abinda take so shi ake mata a gidan sede in Baba bai gida, yarinya tana girma tana dad’a kyau da kuma dad’a kama da mahaifiyarta. Cikin rumfa da rayen Allah Zeezee ta kai har shekaru biyu da watanni goma a duniya (2 years 10 months) baki ya nuna ras se aukin surutu da kuma rashin ji da b’arna. Sede duk laifin da tayi komin girman sa Baba bai bari ko tsawa ayi mata bale wai amata duka koda wasa ba wanda ya tab’a d’aga hannu ya daki Zeezee harta Mama da kanta.
*~ *~
Yau ranar ta kasance Sunday as usual tin k’arfe 7:00AM Zeezee ta tashi ta d’ago babban teddy bear nata sannan ta sauk’o daga kan gadonta fuskan Mama da Baba ta leqa taga du bacci suke sannan a hankali ta fice daga d’akin ta sake ja musu k’ofar. D’akin su Mariam ta nufa ta bud’e ta tarar da su suma suna ta bacci kan gadon nasu ta d’ale ta fara tsalle-tsalle a kai, badan komi ba dan kawai ta tadasu. Cikin bacci Mariam ta soma magana tun bata bud’e ido ba tasan waye da d’anyen aiki haka.
“Zeezee dan Allah kiyi wa Allah kiyi hak’uri ki koma d’akin ku Baba na kiranki.”
“K’ayyan kine Baba na basshi.”
“Toh muma ki bar mu mana muyi baccin.”
“O’o ce kun tashi dan sha tea.”
“Fisabilillahi Zeezee sau nawa kike shan tea a rana? Kibari se anjima.”
“O’o ni yanzu nake sho” ta cigaba da tsalle kan gadon. A fusace Mariam ta miqe ta galla mata wani mugun harara aiko Zeezee dan munafirci tasa kuka sekace dukanta akayi. Yasmeen da k’aran kukan Zeezee ya tada ta tace, “Adda Mariam kin shiga uku me kika mata?”
“Kibar munafuka ko tab’ata banyi ba.”
“Zeezee dawo” cewar Yasmeen. Kafad’a Zeezeen dake bakin k’ofa tana k’okarin bud’ewa ta buga da nufin o’o. “Wayyayi chena fad’a ki da Baba.”
“A’a Zeezee ta yi hak’uri kar kije zo abinki kinji?” Cewar Yasmeen trying to sooth her.
“Ki barta tajen in ta fasa ai in taga ana tsoron takai k’aran mutum ne take jin dad’i yake kuma sake bata garab’asan cigaba da yin hakan, kije ba wanda ya rik’e miki k’afa.” Mariam na kaiwa nan ta juya masu baya tare da rufe fuskarta da bargo ta cigaba da kwanciya. Zeezee na barin d’akin tasa sabon kuka ahaka har ta isa d’akinsu Mama ta hau jijjiqa Baba. Jin kukanta take ya tashi ya zauna, “ya haka Zeezee keda waye?” Ya azata kan cinyansa. Cike da shakwab’a kan yadda ta saba tace, “Adda Mayyam.”
“Ai kaman na sani muje mu sameta.”
**
Banging k’ofar d’akin su Mariam yayi firgit suka miqe zaune dukansu. “Me kika mata?” yayi tambayar wa Mariam yana me hararta.
“Nifa ba abinda na mata tazo muna bacci tana mana tsalle-tsalle kan gado shine nace ta bari take wannan kukan.”
“Laaa! Baba wayyayi kayyan tane, mari na tayi a zuciya na.”
“A zuciyanki Zeezee? Ni?!” Mariam ta nuna kanta. “Yaushe ma naga zuciyan naki bale in mara?”
“Eh a zuciya na.” Zeezee ta kuma jaddada mata.
“Sannu ko k’anwata” Baba ya shafa kan Zeezee “yi hak’uri” sannan ya dawo da kallonsa kan Mariam “Allah Mariam ki kiyaye ni in sake jin kin tab’a yarinyan nan kiga! Ke shikenan kullum kina cikin bin gindin yarinya kina sata kuka sekace ba babba ba, this should be the last time I’ll warn you again.”
“Allah sark-”
“Rufa min baki!” yayi saurin katse ta.
“Shikenan Zeezee?” Kai ta gyad’a a shagwab’ance sannan tace, “zan sha tea.”
“Tea? Ko a dafa miki Indomie kina jin yunwa ne?” Ya matse cikinta yana mata cakul-kuli, nan ta hau dariya.
“Eh” ta basa amsa.
“Oya Mariam miqe ki je ki dafa mata Indomie da k’wanta guda biyu akai kafin nan Yasmeen kije ki had’a mata tea sauran ki d’ibar mata madara kisha kuma.”
Kamar wacce zatayi kuka Mariam tace, “wallahi Baba ko an dafa mata Indomie’n ba ci take ba haka jiya ma k’arshenta zubar wa akayi kawai dan tasa nutum aiki ne.”
“Toh ina ruwanki ai bake kike siya ba, shegen rashin son aiki maza tashi yaso kuka gama seku koma baccin, ku tashi mana!” A sanyaye suka miqe suka nufa bayi dan washing up se gunguni suke.
~* ~* Tea’n ta me kauri Yasmeen ta kawo mata tana zaune kan dining table nata da chair ta shanye tas, a rayuwa Zeezee akwai son tea bayan 25 minutes Mariam dake ta kumbure kumbure har yanzu ta kawo wa Zeezee abincin. As expected Zeezee ta jagualgwala taci kad’an ta k’ara mai abinta.
_09:34AM_
Su Mama na a kitchen suna had’a breakfast, bayan Yasmeen tayi wa Zeezee wanka ta saci jiki tayi d’akinsu Mariam daidai gaban dressing mirror ta tsaya ta fara bi ta kan cosmetics d’in tana applying ita a dole tana kwalya, kaca-kaca tayi da kayakin kwalyan, data kama sharpening eye pencil seda taga k’arshen shi, data waina jan baki seda ya karye, liquid eyeliner ta bud’e ta zana a saman girarta saura ta zagar a k’asa. Komi seda ta b’ata sannan ta masu wanka da turare, daidai tazo fitowa kenan tayi kacib’us da Mariam dake shigowa. Hannu bibbiyu Mariam ta aza kan bakinta da taga fuskan Zeezee.
“Ki masha min in wuce” cewar Zeezee tana k’ok’arin kare fuskanta.
“Da kayan kwalyan wa kika-” bata k’are maganan ba idanunta suka sauqa kan ta’addancin da Zeezee ta masu da kayan kwalya. Fincikota tayi da hannu takai ta gaban mirron.
“Meh amfanin haka? Ban hanaki tab’a min kayan kwalya ba?” Ganin haka Zeezee tasa ihu wane ana cire mata rai, Baba da Mama ne suka shigo a tare a cewansu ma ko Zeezee ta fad’i ne. Zeezee na ganin Baba ta ruga aguje wajensa ya d’agata sama “Baba kaga Adda Mariam koh?”
“Me haka a fuskan ki Zeezee?” Mama ta tambaya.
“Mama dubi fa, kalli abinda ta min da kayan kwalya komai seda ta b’ata kuma da gangan take.”
“Taya zaki ce da gangan?” Cewar Baba, “bakiga yarinya ce ba? A jinki in tasan whats right and wrong zata yi abinda tayin neh?”
“Amman fa Baba this is not her first time kwanaki da tayi seda na mata magana” tayi maganan idanunta na cikowa da hawaye.
“Toh Mariam kema seda na fad’a miki ki riga sa kayan kwalyan naki cikin wardrobe kina rufewa achan Zeezee barata iya tab’awa ba.”
“Shikenan Zeezee?” Kai ta gyad’a a shagwab’ance sannan tace, “zan sha tea.”
“Tea? Ko a dafa miki Indomie kina jin yunwa ne?” Ya matse cikinta yana mata cakul-kuli, nan ta hau dariya.
“Eh” ta basa amsa.
“Oya Mariam miqe ki je ki dafa mata Indomie da k’wanta guda biyu akai kafin nan Yasmeen kije ki had’a mata tea sauran ki d’ibar mata madara kisha kuma.”
Kamar wacce zatayi kuka Mariam tace, “wallahi Baba ko an dafa mata Indomie’n ba ci take ba haka jiya ma k’arshenta zubar wa akayi kawai dan tasa nutum aiki ne.”
“Toh ina ruwanki ai bake kike siya ba, shegen rashin son aiki maza tashi yaso kuka gama seku koma baccin, ku tashi mana!” A sanyaye suka miqe suka nufa bayi dan washing up se gunguni suke.
~* ~* Tea’n ta me kauri Yasmeen ta kawo mata tana zaune kan dining table nata da chair ta shanye tas, a rayuwa Zeezee akwai son tea bayan 25 minutes Mariam dake ta kumbure kumbure har yanzu ta kawo wa Zeezee abincin. As expected Zeezee ta jagualgwala taci kad’an ta k’ara mai abinta.
_09:34AM_
Su Mama na a kitchen suna had’a breakfast, bayan Yasmeen tayi wa Zeezee wanka ta saci jiki tayi d’akinsu Mariam daidai gaban dressing mirror ta tsaya ta fara bi ta kan cosmetics d’in tana applying ita a dole tana kwalya, kaca-kaca tayi da kayakin kwalyan, data kama sharpening eye pencil seda taga k’arshen shi, data waina jan baki seda ya karye, liquid eyeliner ta bud’e ta zana a saman girarta saura ta zagar a k’asa. Komi seda ta b’ata sannan ta masu wanka da turare, daidai tazo fitowa kenan tayi kacib’us da Mariam dake shigowa. Hannu bibbiyu Mariam ta aza kan bakinta da taga fuskan Zeezee.
“Ki masha min in wuce” cewar Zeezee tana k’ok’arin kare fuskanta.
“Da kayan kwalyan wa kika-” bata k’are maganan ba idanunta suka sauqa kan ta’addancin da Zeezee ta masu da kayan kwalya. Fincikota tayi da hannu takai ta gaban mirron.
“Meh amfanin haka? Ban hanaki tab’a min kayan kwalya ba?” Ganin haka Zeezee tasa ihu wane ana cire mata rai, Baba da Mama ne suka shigo a tare a cewansu ma ko Zeezee ta fad’i ne. Zeezee na ganin Baba ta ruga aguje wajensa ya d’agata sama “Baba kaga Adda Mariam koh?”
“Me haka a fuskan ki Zeezee?” Mama ta tambaya.
“Mama dubi fa, kalli abinda ta min da kayan kwalya komai seda ta b’ata kuma da gangan take.”
“Taya zaki ce da gangan?” Cewar Baba, “bakiga yarinya ce ba? A jinki in tasan whats right and wrong zata yi abinda tayin neh?”
“Amman fa Baba this is not her first time kwanaki da tayi seda na mata magana” tayi maganan idanunta na cikowa da hawaye.
“Toh Mariam kema seda na fad’a miki ki riga sa kayan kwalyan naki cikin wardrobe kina rufewa achan Zeezee barata iya tab’awa ba.”
“Ahtoh! In har dagaske kike, kuma me kika ma Zeezee take ihu?”
“Duka na tayi a zuciya na.”
“A zuciyanki koh? Yi hak’uri, wallahi Mariam ki kiyaye ni sau biyu nake miki magana kenan yau na uku duka ne.”
“Alhj amman Zeezee’n ma kai mata magana ta rage b’arna ko jiya a islamiyya seda ta yage wa Mrs. Bee littafi.”
“Lokacin ta ne ba maganan da zan mata ke Allah kad’ai yasan kalan b’arnan da kikayi kema” yana kaiwa nan ya fice k’arisawa Mama tayi kusa da Mariam da har ta fara kuka tana bata hak’uri haka seda Mama ta bata dubu biyu tayi shiru.
Su Baba suna zaune a tsakar gida da Zeezee’nsa se hayewa jikinsa take tana wasa wane d’an biri, Ibraheem ne ya dawo daga yawonsa, da wayansa riqe hannunsa ya bashi full attention nasa a haka har ya k’arasa d’aki Zeezee na ganin shigewan sa ta taso daga jikin Baba tabi bayansa. Zaune ta tarar dashi kan couch dake d’akinsu a hankali taje ta zauna gefensa ko uffan bece mata ba se chatting nasa yake yana murmusawa time-to-time, da Zeezee ta d’anyi observing nasa seta gane chatting yake a whatsapp. “Ya Ibyaheem da whashapp.” tace da shi.
“Ya akayi Zeezee?”
“Ya Ibyaheem zanyi game.”
“A’a Zeezee ni gaskiya bara ki kashe min battery ba duk games d’in ma gogewa zanyi” ba tare da tace mai komai ba ta miqe ta kama tafiya “k’ara na zaki kai gun Baba koh? Zo in sa miki toh.” Ko ta kansa batayi ba taje ta samu Baba ta fara kuka “wa ya tab’a min k’anwa?”
“Ya Ibyaheem ne.”
“Meh ya miki shi kuma?”
“Yak’i bani wayanshi nayi game.”
“Ibraheem! Ibraheem!”
“Na’am Baba!” ya amsa tare da goge dukka games na wayan nasa sannan ya fito. “Gani Baba” ya durqusa gefe guda.
“Ina wayan naka? Bata tayi game d’in.”
“Baba nifa ba game a waya na.”
“Ka goge kenan?” Kafin Ibraheem ya amsa Zeezee tace, “eh Baba yace min zeyi deleting.”
“Ni? Yaushe nace miki haka Zeezee?”
“A’a barshi Zeezee jeki amso wayan nasa.”
“Baba me zaka min da waya?”
“Downloading mata zanyi ba ka iya gogewa ba? In na sake installing seka sake gogewa kaine da asaran data dan ba shi ze hanani next in ka goge na kuma downloading ba, amso min wayan Zeezee.”
“Baba in na fita anjima zan tura a wayan friend d’ina wallahi ba nida data nima managing nakeyi.”
“Wannan kuma damuwan ka amso min Zeezee” haka Ibraheem naji yana gani Baba ya shiga playstore “wani game kikeso K’anwa ta?”
“Shubway churfers da plincess salon.”
“Zeezee har biyu Baba wallahi data na ze k’are.” Banza dashi Baba yayi yama Zeezee downloading duka sannan ta fara playing. “Kaje in ta gama zata kawo maka wayar.” Kamar wanda zeyi kuka Ibraheem ya kalli Baba sannan Zeezeen dake ta game nata ya miqe ya bar gidan ma gabad’aya.
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
beeenovels.blogspot.co.ke
PAGE 05
*December, 2016*
_This page is in honour of *Fathooma Ali* a great fan I never knew I had. I have recieved your message, thank you so much for the love stay blessed Habibti #OneLove💕_
Game Zeezee tai tayi kamar ba gobe, dan kanta ta gaji da bugawa ta shiga photos tata kallon pictures saura kuma ta rik’a gogesu a takaice seda tayi mai battery low wayar ta mutu gabad’ai sannan ta kai mai wayan alokacin yana zaune a parlour a side nasu yana assignment nasa na Technical Drawing “Ya Ibyaheem ga wayan ka” ta fad’i tare da ajiye mai a gefensa ko kallonta beyi ba ya cigaba da abinda yake chan tace, “Ya Ibyaheem zane kake yi?” Nanma ko uffan be ce mata ba feeding bottle nata da ke rataye a wuyanta wanda tea ne had’e ciki ta d’aga zata bud’e dan sha. A garin haka tean da yake ciki ya zube kan zanen Ibraheem, “shikenan ai kin huta yanzu! Tashi ki ficemin daga kallo!” ya daka mata tsawa.
Lamo tayi tana kallonsa a yayinda hawaye ke ciko mata a ido, “baraki fita bane?! Ace mutum kullum se bad luck fice min! Yaso in Baban naki ya dawo ki fad’a mai, get out!” kuka ta soma ba makawa amman ko a jikinsa, kamar kyaftawan ido ya fisgota da hannu ya direta bakin k’ofar tare da rufewa harda kwad’o. Kuka Zeezee ta ringa yi wajen haka dan kanta tayi shiru sabida Baba yafita bai gida Mama kuwa nacan d’akinta tana kwance. Mariam dake tsakar gida ko a kwalan rigarta ta lalasheta daman acike take da ita for what she did to her makeup items earlier.
Chan da ta gama kukan ta k’arisa wajen garriage inda takejin hayaniyan su Omar. Zaune ta tarar dasu yana ma Yasmeen homework nata na ‘paper mache.’ Waje ta nema ta zauna kusa dasu itama sannan tace, “Ya Omal meh kukeyi?” Kamar wanda bare amsa taba yace, “homework.”
“Ya Omal paper ne kuka dafa?”
“Eh da Allah shegen tambayoyi sekace ‘yar jarida kinga baraki iya yin shiru ba find your exit” daga nan Zeezee bata sake cewa komai ba sede duk abinda suke tana observing nasu.
K’arfe uku suka gama shiri suka wuce islamiyya nan Zeezee ta samu kanta, da full confidence nata taje tana k’ok’arin bud’e k’ofa only to find it locked kamar Mama tasan b’arna data saba zatayi any moment yayyun nata suka barta ita kad’ai a gida, dalilin rufe k’ofan d’akin datayi kenan don restraining nata.
“Mama ki bud’emin k’ofa.” Banza da ita Mama dake shirin bacci tayi.
“Mama ki bud’e.” tayi maganan tana jijjik’a k’ofan.
“Saboda kije kiyi b’arna ba taho mu kwanta in bara ki kwanta ba ga kayakin wasan ki can se kiyi wasa.”
“O’o ni ki bud’e min.”
“Barin bud’en ba mab’arnaciya kawai.” Kuka Zeezee ta soma rusawa wajen tun Mama tana ignoring nata har ya soma daminta haka seda ta bud’e mata k’ofar bayan jan kunnen data mata na karta tab’a kayan yayyun ta. Like a good girl tace ita wasan ta zatayi. Mama na maida k’ofanta Zeezee ta zarce d’akinsu Mariam luckily yau sun mance basu rufe k’ofan su ba nan ta samu ta shiga. Bata nufi ko ina ba cikin d’akin se inda suke jera school bags nasu, na Yasmeen taja ta bud’e ta ciro notebook d’aya sannan ta fice izuwa kitchen inda ta nemo tukunya ta loda ruwa ciki sannan ta bud’e littafin Yasmeen wanda ya kasance Mathematics ta soma yagewa tana kacancanawa tana sawa cikin kwanon in aka tambayeta wai haka taga su Omar sunyi d’azu. Hakan ta cigaba da yi seda taci rabin littafin sannan ta ajiye ta d’au tukunyar ta aza akan charcoal stove, ashana ta shiga nema wanda bata samu ba saboda chan saman cupboard Mama ke ajiyewa. Dan kanta ta hak’ura bayan ‘yan mintuna ta sauk’e tukunyan sannan ta d’ibo cups da plates da saucers duk bibbiyu ta zauna tsakar gidan itama a dole zatayi paper mache.
Moulding jikin cups d’in ta shiga yi tana manna papers d’in jiki amman ina se sumb’ilewa suke, haka ba fashi ta tayi sannan data gama taje ta jerasu layi d’aya da inda Omar ya ajiye wa Yasmeen nata.
_5:30PM_
Anan yaran suka dawo daga islamiyya se Allah Allah Yasmeen ke ta ajiye jakarta ta duba home work nata ko yayi dan gobe Monday zasuyi submitting. Dad’i sosai taji ganin Zeezee bata tab’a mata abinta ba sede ganin wasu cups datayi a gefe bayan data gama duba nata seta d’au na Zeezee tana dariya “wai! Ji shirme itama wai a dole tayi pap-” maganan da Yasmeen bata k’arisa ba kenan ganin handwriting nata jikin paper’n data lura da kyau kuwa taga Mathematics note nata ne. Salati ta saki sannan tasa gudu zuwa d’akinsu ta shiga neman Maths note nata sede its nowhere to be found. Dam idanta ya cike da hawaye ta kama hanyan d’akin Mama dan kai k’ara, tana fitowa taga rabin Maths note nata a k’asa gabad’ai ya canza kamanni tunanin irin dukan da Mr. Chika (Maths teacher’nsu) ze mata kawai take. D’akin Mama ta nufa tana kuka, Zeezee da tasan this was comig tuni taje ta lab’e jikin Mama.
“Ya haka Yasmeen waya tab’aki?” Cikin sautin kuka tace, “Mama kalli fah, kalli abinda Zeezee tamin da Maths notebook d’ina” se kuma ta fashe da kuka. Amsan littafin Mama tayi ta k’are mai kallo sannan ta mai da kallonta kan Zeezee datayi tsit, daga bisani tace;
“Mama bani bane.”
“In ba keba ai nice, mesa bakiya ji ne iyye? Meh amfanin hakan? Wallahi ga ta Yasmeen kimata duk abinda zaki mata nan gaba ko cewa akai ta tab’a jakarki barata tab’a ba” da hannu Yasmeen ta finciko Zeezee ta nad’a mata na jaki, Mama na kallonsu batace komai ba se anan Yasmeen taji tad’an huce. Kuka Zeezee take wane dan shi aka kawota duniya. Chan ta wuce wajen garriage ta cigaba da kukan har tazo tayi shiru, tana jin k’aran motan Baba ta soma sabon kukan aiko parking na arziki Baba beyi ba yafito yana tambayarta ita da waye. Nishinta har wani sama sama yake tace, “Mam.. Mama ne tasa Yasmeen tamin duka.”
“Duka?! A dalilin meh? Muje ina Maman naku?” tun daga gun ya shiga k’wala wa Mama kira.
“Alhj lafiya haka?” Tayi maganan tana k’ok’arin fitowa daga kitchen.
“Me kika sa Yasmeen ta mata? Yasmeen! Yasmeen! Kema fito nan.” Nan da nan ta fito rik’e da Maths note nata.
“Ehen ina jinki kibani k’wararren dalilin da zaisa kice Yasmeen ta daka min k’anwa.”
“Yasmeen mik’a mishi littafin naki” cewar Mama, nan Yasmeen ta miqa wa Baba bayan daya k’are wa littafin kallo yace, “wa yayi maki haka da littafin?”
“Zeezee ce.”
“Taya kika san itan ce? A idonki tayi ne?”
“Alhj wani irin magana kake haka? Mu biyu da ita aka bari a gidan nan ko ni kakeson kace nayi wannan b’arna?”
“Ba abinda nake nufi ba kenan abinda nake nufi shine ku dena zato tunda ba kamata kukayi in the process ba, ko ke kikayi Zeezee?” Kai ta girgiza alaman a’a. “Toh baga erin saba kun kama kun d’au alhak’in yarinya a banza.”
“Baba wallahi Zeezee ce, ita tamin kuma Maths teacher’n mu duka na zeyi wallahi.”
“Naji gobe zamu je makarantar naku na masa bayani amman koda wasa karki kuskura ki sake d’aga hannu ki tab’a Zeezee ever!”
“Meh kake nufi da hakan Alhj? Baka yarda Zeezee ce tayi wannan tabargaza ba kenan ko meh?”
“Taya zan yarda bayan ban kamata red-handed ba?”
“Lallai kam!” Mama ta had’e hannunta biyu ta dafe a ciki “baka yarda bama bale ace ka ja mata kunne koh?”
“A dalilin me zan ja mata kunne, ba abinda zan mata.”
“Toh wallahi Alhj ka cigaba kai da kanka wataran zakayi nadaman abinda kakeyi, yarinya ace bata jin maganan kowa se naka Allah kyauta!”
~* ~*
Da daddare bayan Sallan Isha’i Baba da Mama suna d’akinsu yaran suma haka a d’akinsu. Zeezee ne zaune a parlour ta baje kayakin wasanta se wasa take chan da taji ta gaji ta miqe ta nufa d’akinsu Mariam inda duk yayyun nata suke mik’e suna kallo a laptop na Ibraheem ba tare da tace dasu komai ba ta jawo k’ofan tayi d’akin Mama taje ta samu Baba.
“Baba zan kayyi fyozen (Frozen.)”
“Toh je kice wa Ibraheem ya sa miki.”
“Toh” tace sannan taje ta samu Ibraheem. “Ya Ibyaheem Baba yace kasha min fyozen.”
“Bara asa ba ke baki tashi kallo se kinga mutane sunayi toh bara’a sa ba, se mun gama za’a sa maki.” Ibraheem yayi maganar ba tare da ya kalli direction nata ba.
“Dai-dai kenan” cewar Mariam “wai ita a rayuwa dan iskanci seta ga mutane suna kallo take fad’in zatayi toh bara a saba tunda ba laptop naki bane.”
“Muguwa ba, naji ba nata bane amman naga ai ni na saya koh? Ni ke da iko dashi” atare suka d’aga kai suka ga Baba tsaye gabansu da alama tun d’azu yake tsaye gun.
“Baba!” Cewar Mariam.
“Eh ni, ai kaman nasan this was coming, ke bara ki tab’a barin halinki na muguntan nan bako Mariam? Oya sa mata frozen d’in.”
“Allah sarki Baba sauran episodes biyu mu k’are season d’in fah.” Ibraheem said trying to explain calmly.
“Se ku jira in Zeezee tagama ku k’arisa, sa mata ka kuma kai mata laptop d’in chan d’akina tayi kallonta ba tak’ura.”
Se kumburi da gunguni suke Ibraheem ya sa mata frozen d’in yakai d’akin Baba ya ajiye. Bayan dawowansa d’akin ya d’au wayansa kamar ance ya shiga gallery yana shiga yaci karo da tabargazan da Zeezee ta mai almost half of his pictures are gone kuka ne kawai beyi ba.
Washegari Monday duk yaran sun shirya school kafin nan seda suka kukkule d’akunansu suka bawa Mama key gudun kar uwar b’arna ta musu tabargaza. Aikuwa bayan Mama ta mata wanka ta karya ta nufa d’akinsu Ibraheem taji a rufe tayita jijjigawa ganin yak’i bud’uwa kawai ta je ta samu Mama tayita mata k’ananun b’arna a kitchen tana sata surutu. Da Azahar Baba ya dawo gida as always Zeezee taje ta mai oyoyo a parlour ya direta ya d’ago d’aya daga cikin ledojin daya shigo dasun ya bud’e sabuwar ipad ce pil ciki. Cike da murna Zeezee tace, “Baba ipad na waye?”
“Naki ne k’anwata” daidai nan Mama ta shigo d’akin. Tsaye tayi in akinbo style tace, “Alhj menaji kace?”
“Me ruwanki? Ipad na siyo mata.”
“Ipad fa kace Alhj?” Kasa gaskata kunnenta tayi ta k’ariso ciki taga ipad d’inne dagaske hannun Baba.
“Lallai Baban Zeezee ina jinka da Yasmeen last week take ce maka ka sai mata waya duk kusan kowa a ajinsu nada waya k’ememe kace wa yarinyan nan ba kada kud’i but here you are ka saya wa ‘yar Zeezee ipad bama tab ba ipad gabad’aya ko me zatayi dashi ban sani ba.”
“Kinsan meh Hafsah in bakinki bare fad’i alkhairi ba seki fice min daga d’aki daman bani na gayyato kiba.”
“Ai gaskia ne wallahi baka kyautawa, Yasmeen ya kamata ka sai ma waya ba Zeezee ba kaima kasani.”
“Mschw! Ke dama kika kama surutu baki gajiya” hannu yasa a aljihunsa ya zaro dimbun kud’ad’e sannan ya irga dubu goma ya danka mata “sekiyi mata ciko ki siya mata.”
“Ta rage hanya dai” tace tare da ficewa.
“K’anwata karki kula Mama kinji? Kishi suke saboda basu da ipad” yace da Zeezee dake zaune kan cinyarsa. “Mu had’a miki a charging koh?”
“Eh Baba akwai games a ciki?”
“Sosai ma K’anwa ta kuma zan sake miki downloading sabi.”
“Yauwa Baba nima barin bawa Ya Ibyaheem da Ya Omal ba tunda suna min rowan wayansu.”
“Ai kuwa naki ne ke kad’an ki daga yau ba ruwanki da wayoyinsu tunda ga naki nan babba”
“Yeyy Baba” nan ya had’a mata a charging, an hour later ya zaro yayi mata downloading games turum yarinya kam dama ta riga tasan kan amfani da torch screen. A waje ta zauna kan sallayanta tayi cross-legging legs nata ta hau buga game.
2:30PM yaran suka dawo daga school. Da an gansu anga wanda suka kwaso gajiya from school Yasmeen ce ta soma shigowa harta wuce Zeezee seta kuma dawowa dan gaskata abinda idanunta suke gane mata. “Ipad!” Tayi maganan tare da k’wararo idanunta waje disbelievingly. “Ya Omar kuzo kuga abin al’ajabi.”
Daga nesa Ibraheem yace, “wai me neh kike wani tafe hannu?”
“Kude kuzo mana!” A sanyaye suka k’ariso wajen duk baki suka wangale ganin ipad hannun Zeezee, itako yi tayi kaman batasan suna tsaye a kanta ba se game nata take tayi.
“Zeezee” Ibraheem ya kira sunanta seda ta b’ata lokaci sannan ta amsa “meh?” cike da rashin kunya.
“Kalleni” ya buk’ace ta. Nan ma seda ta b’ata lokaci sannan tasa pause ta d’ago sexy long eyes nata tana kallon sa, “meh?”
“Ipad na waye a hannunki? Uncle Abdallah yazo ne?”
“Nawa ne” ta basa amsa confidently. Dariyan rainin hankali suka hau yi dukansu especially ma Mariam da tanan tafi kauri dama. “Ipad naki?” Omar yayi maganan in between laughter.
“Is good to dream big my sister” cewar Mariam harda hawaye dan dariya.
“Uban wa ya siya miki?” cewar Ibraheem.
“Ubanku ya siya mata” cewar Mama dake tsaye akansu tana kallonsu tun d’azu. Nan duk suka dawo da kallon su a gareta.
“Mama jokes apart please ipad na waye?”
“Gashi kuwa ta fad’a muku, nata ne Babanku neya siya mata.”
“Buro uba!!” Cewar Ibraheem “yanzu ipad Baba ya siya ma yarinyan nan?”
“Eh cewa yayi kuna mata rowan waya and he can’t stand it kuna ma k’anwarsa rowa ya siya mata uwa uba gabad’aya.”
“Amman shine last week nace Baba ya siya min waya yace min baida kud’i?” Yasmeen ta tab’e baki.
“Karki damu nasa sa gaba seda ya bada dubu goma zan cika miki mu sai miki wayar.”
“Yeyy!!” Ta hau tsalle. Dogon tsuka Omar yaja, “Banza mena murna? An siya wa k’anwarki ipad ke za’a had’aki da wayan da befi na 20k ba kuma kina murna.”
“Yo naga kai ma Zeezeen k’anwarka ce kuma bakada ipad d’in.” tayi retaliating.
“Wallahi barata saku ba wai bindiga a ruwa, nima se an canza min waya.” Mariam tayi k’wafa ta fice daga wajen. Ibraheem sarkin wayo ya k’arisa wajen Zeezee yana shafa dogon sumanta “My Zeezee taho muje d’akinmu yau na siya miki big bomb.”
“Dagaske Ya Ibyaheem?”
“Sosai ma taho muje” ba gardama ta bisa d’akinsu bayan ya canza kaya ya d’au mata sweet d’in as promised ya bata seda ya bari hankalinta yagama bin kan sweet d’in yace, “Zeezee zaki ara min ipad naki?”
“O’o ba nima kana min rowan wayan kaba.”
“Ai na dena yanzu, bakiga na baki sweet ba, so zaki ara min na ‘yan minutes ne kawai friends d’ina zasu so inason in nuna musu inada ipad da laptop ne kinji?”
“Ni banasho su b’atamin ipad d’ina” tayi maganan tana lasan sweet nata.
“Ai barin ma basu ba bale su b’ata miki so zaki bani?” Ta gyad’a mai kai. “Yauwa My Princess and one more thing please koda sunzo kada ki shigo nan side d’in kinji?” Like a good girl ta gyad’a mai kai.
Bayan sallan La’asr friends na Ibraheem suka iso ina irin shi big boy d’innan gabansa mac book ne da ipad se palli yake musu yana wani feeling achan d’akin Mama Zeezee ce zaune se shan sweet da Ibraheem ya had’ata dashi take chan fa taga barata iya hak’ura da ipad nata ba ta miqe ta nufa BQ kaman yasan da haka yasa lock. Knocking ta shiga yi seda ya taso ya bud’e, ganinta da yayi ba k’aramin razana sa yayi ba murya chan k’asa k’asa yace, “Zeezee ya mukai dake?” Yana maganan yana leqan friends nasa da suke danne-danne cikin ipad d’in. “Kije ki jirani d’akin Mama kinji?”
“Ina ipad d’ina?” da sauri yasa hannu ya toshe mata baki ai ta shiga shuresa, a garin haka taga ipad nata rik’e da friends nasa fisge kanta tayi da k’yar ta sa ihu “ku bani ipad d’ina!” ta fad’i da k’arfi. Ibraheem da ji yake kaman ya tone k’asa ya shige dan kunya ya gama yima friends nasa k’arya ipad nasa ne Zeezee tazo ta fasa mai tyre.
Atare friends nasan suka juyo suna kallon Zeezee fuskokinsu d’auke da tambaya. “Wayyayi sena gaya wa Baba ka basu ipad d’ina.” Fuska yaci “wani erin ipad naki? Ke shikenan duk abinda aka saiwa mutum seki ringa fad’in naki? Mschw! In game kikeso ai seki fad’a a sa maki Auwal miqo min ipad d’in da Allah” yayi maganan a fusace erin baya son bullshit d’innan “gashi!” ya miqa mata “sauran kije ki b’ata min abu na” daga nan ya turata waje kafin ta sake sakar masa da wani bomb.
“Phew!” Yayi sighing sannan yaje ya zauna ganin friends nasan basu bar binsa da kallo ba ya tuno da wata dabara “dudes kun kalli empire season 3 kuwa?”
“A’a please kana dashi?”
“Sosai ma!” yaja laptop nasa ya sa musu da haka ya samu ya gusar masu da tunanin incident daya farun daga brain nasu.
_9:12PM_
Mariam ce tsaye bakin k’ofan d’akin Baba tun d’azu ta kasa gathering courage da zata shiga seta bud’e baki zatayi sallama se ta kasa ana ckin haka Zeezee tazo shigewa ko ganin Mariam ma batai ba dan yadda hankalinta yabi kan game da take. Dabara ce ta fad’o wa Mariam ta kira sunanta cikin wani irin salo, “Zeezee kyakkyawar gidan mu” se anan Zeezee ta d’ago kai tana kallonta “meh?” Tayi snarling at her
“Haba *_YAR GATAN BABA_* meh nayi kuma kike b’atamin rai haka?” Tayi maganan tare da tsugunawa tana gyara mata ribbons na kanta. “Ipad naki yayi kyau sosai.”
“Na sani ai.” ta fad’a mata gatsau da alama ‘yan rashin kunya suna kusa yau.
“Allah baki hak’uri beauty meh kama da Mama, Zeezee nace zaki tayani yima Baba magana nima a canza min waya?”
“O’o zaki ce a shiya miki irin nawa bana sho.”
“Wane ni? Ai wannan naki ne ke kad’ai ni d’an k’arami za’a siya min kinji My Darling Sister?” Shiru Zeezee tayi tana nazari da k’yar Mariam tasamu tayi convincing Zeezee ta yarda zata yima Baba maganan.
Bayan shiganta Mariam ta kasa kunne jin abinda Zeezee za tace. Gado ta haye ta samu Baba.
“K’anwata zaki kwanta ne?”
“A’a Baba a canza wa Adda Mayyam waya.”
“Ita ta turoki ko?” Nan zuciyan Mariam ya buga Allah sa kar Zeezee ta tone ta.
“A’a ba ita bace naga wayan ta ya shufa ne Baba.”
“Are you sure K’anwata? Ba turoki muguwan chan tayi ba?”
“Eh Baba zaka canza mata?”
“Anything for you My Sister zan canza mata.”
“Toh Baba zanje in kwanta gu’ night.”
“Yauwa Zeezeen Baba sena shigo nima” ya bata peck a forehead ahaka suka rabu tana fitowa Mariam ta d’aga ta sama tana showering kisses all over her face. “Thank you, thank you, thank you, very very much.” Hannu Zeezee tasa tana goge kisses d’in “ni banasho Baba ne kawai yake kishing d’ina.”
“Toh ‘yar autan mu yi hak’uri nagode kinji? Zaki sha tea ko in dafa miki Indomie?”
“Eh Indomie.”
“Taho muje toh Beauty.”
Sab’anin kullum yau Mariam ce da kanta tayi feeding Zeezee tayi mata wanka sannan ta karance mata good night story ta nufa d’akinsu Ibraheem alokacin har sun fara shirin bacci. Bayan ta zauna kan couch tace, “chab Ya Ibrahem ashe de Zeezee nada advantage” nan ta labarta masa komai bayan dogon nazarin da yayi yace, “excellent! nima kod’ata zan gobe wallahi se an sai min machine.”
“Ai kuwa de tanan za muna getting on Baba tunda yace komai shi Zeezee.” Hannu suka tafe da Ibraheem suna masu jin dad’in wannan cigaba da suka samu!
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 06
Yau Tuesday ya kasance ‘public holiday’ ba school don haka yaran duk ba wanda ya tafi school ko wannen su na a d’akinsu yana bacci. 7:00AM Zeezee ta tashi kamar meh alarm as usual ta fita tabar d’akinsu tayi d’akin su Ibraheem yau kuma, a kulle ta samu k’ofar don haka tayita knocking dan dolen Ibraheem yasa Omar ya bud’e mata.
“Me kuma ya kawo ki nan?” Ya tambayeta in between hamma. “In kinsan fitina kika zo yi maza ki juya ki koma.”
“Ya Omal zan kwanta ne.”
“D’akin ku ba wajen kwanciya aiko?” Ibraheem yayi maganar fuskarsa rufe da pillow. Ganin zata soma masu kuka suka shigo da ita, a tsakiyar su ta kwanta tare da shigewa bargon Ibraheem. Tun tana shiru taga barata iya ba ta soma kiran sunan su, shiru suka mata wane basu jinta chan ta miqe ta nufa toilet tayi pupu.
“Naaa gamaaa!!” Ta fad’a da k’arfi. Banza su kayi da ita se a karo na biyu Ibraheem yaja dogon tsaki. “Nifa shiyasa banason ta shigo nan, shegen k’azanta sekace farillah kullum se mutum yayi pupu da safe mschw! Omar jeka wanketa ka kuma tura ta waje ga teddyn ta.”
“Ni wallahi-”
“Kai wallahi meh?” Ibraheem yayi saurin katse sa “da ni kakeso in wanke mata? Lallai yaro will you stand up my friend!” A sanyaye Omar ya miqe se kumbure kumbure yake ya shiga bayin yana wani mata mugun kallo. Se da ta bari ya k’ariso ciki ta kallesa tace, “ni banashon ka, ba kai zaka wanke min ba.”
“Mumu daman ni d’in nace maki ina sonki ne? Tsaya nikam na wanke miki bacci nakeji.”
“O’o banashon ka tab’ani banasho!” Tasa kuka. Fitowa Omar yayi yaje ya samu Ibraheem yace, “Ya kaji wai bata son na wanke mata har kuka take.”
“Toh da waze wanke mata? Ke Zeezee ki miyar da hankalinki kinajina koh?”
“Ni kai zaka wanke min.”
“Lallai yarinya zaki mutu da kashi a jikinki inde ni zan wanke miki”
“Ya Ibyaheem na gama” tasa kukan shakwab’a.
“Barta gun hau gado ka kwanta” yace da Omar haka suka barta zaune kan toilet sit da abin ya isheta tasa wani irin d’an iskan ihun da har su Baba seda suka jiyo ta. Ba tare da b’ata lokaci ba Baba ya tashi miqe, a zaton shi ma wai ko ita da Mariam ne ganin ba haka bane ya nufa b’angaren su Ibraheem, tsaye a d’akin ya iskesu suna raba ido. Kai kawai yayi nodding ya kira sunan “Zeezee.”
“Baba! Baba!” Toilet d’in ya nufa ya sameta. “Ya haka K’anwata pupun yak’i fita ne?’
“Ya Ibyaheem ne nace yamin tsarki yak’i.”
“Yak’i tun yaushe?”
“Tun d’azu.”
“La ila! Ibraheem!” Ya kira sunansa a fusace, “Zo nan d’an banzan yaro kawai.” A sanyaye Ibraheem ya k’ariso cikin bayin. “Na’am.”
“Nanata abinda ka gaya mata.”
“Nifa bance mata komai ba.” Masifa sosai Baba ya masa harda make sa a k’eya sannan yasa sa ya wanke Zeezee tas harda yi mata wanka ya shirya ta tsaf sannan ya d’au K’anwarsa suka bar musu d’akin. Omar da dariya keson fin k’arfinsa se kare fuskarsa yake amman inaa seda dariyan yayi finding way nasa out.
“Ma wa kake yiwa dariya?” Ibraheem yayi maganan in a serious tone.
“Bb... Babu.” Yayi stammering.
“Da yafi ma kam.”
****
_Later during the day, 1:30PM_
Zaune yaran da Maman su suke duk a tsakar gida kowa na harkan gaban sa. Gefe guda Zeezee ce rik’e da ipad nata se game takeyi a yayinda Yasmeen ke zaune gefenta itama duk ta zuba mata ido tana me kwad’ayin son buga game d’in itama.
“Zeezee na baraki sammin ipad naki inyi game ba koh?”
“Eh ba kin ce min Mumu ba d’azu.”
“Toh ai kuma na baki hak’uri kuma kinga nima in Mama ta sai min nawa zan baki.”
“Bana shon naki kowa ya riqe nasa.”
“Zeezee yi hak’uri mana fad’uwa d’aya zanyi in baki.”
“Sekin ce min Aunty Zeezee.”
“Aunty kuma? Ni dake waye babba?”
“Toh cikenan balin baki ba.”
“Toh Aunty Zeezee bani toh.”
“Toh ki tsaya mana in yi nima tukunah.” Duk maganan nan da suke Mama na kallonsu daga bisani tace, “amma ke Yasmeen Sokuwa ce wallahi, yanzu k’anwarki kike kira da Aunty akan banzan game?”
“Ai kuwa sede Sokuwan kam” Omar ya mara wa Mama baya. Ibraheem da keson sa baki amman baison ruining plan nasa yaja baki yayi tsit.
“Ai duk laifin Babanku ne, bari kema zuwa next week na kwashe adashe na in siya miki naki, ke kuma Zeezee kar kibar wannan banzan rowan kinji ba? Ki cigaba muga ina ze kaiki.” Harara mai rai da lafiya Zeezee ta galla wa Mama da dala-dalan idanunta kan zasu zubo a k’asa.
“La’ila! Ni kike harara?” Mama tayi maganan tana k’ok’arin miqewa kenan Baba dake lab’e jikin k’ofa tin dawowan sa daga Masjid ya k’ariso ciki a hanzarce tare da dakatar da Mama. “Koma ki zauna” ya nuna mata gun zamanta da yatsa “da dukanta zakiyi sabida ban gida komeh?”
“Baban Zeezee harara na fa tayi.”
“Eh toh ai ke kika jawo da kikace mata marowaciya, yayyun nata ba duk haka suke ba suma?”
“Lallai Alhj ka goyi bayan harara na da tayi kenan.”
“Why not? Nide karki tab’a min K’anwa.” Kai Mama ta gyad’a continiously cike da mamaki “toh wallahi Alhj ka cigaba da b’ata yarinyan nan.”
“Kanki akeji, kuma bayan nan meh naki dan Yasmeen ta cewa Zeezee Aunty? Ba sisters bane su? Ni na lura bakison Zeezee a gidan nan komi Yasmeen komi Yasmeen to kema ki cigaba.”
“Me kake implying wai Alhj?”
“I mean baki adalci mana, kinfi son Yasmeen kan Zeezee ko ke bakisan Zeezee ce auta ba?” Hannu Mama ta tafe sannan ta d’aura a waist nata “lallai har kura kece wa kare maye? Baban Zeezee kai baka ganin abinda kake ma Zeezee a gidan nan ne? Ai in akwai wanda ke partiality tsakanin yaran nan toh kai ne” ta nuna sa da yatsa “mena siyawa Zeezee ipad kabar Yasmeen ba waya? Waye babba cikin su?”
“Hafsah kinji na rantse duk abinda ya samu ipad na Zeezeen nan kece, dan bakin ki kad’ai ya isa yayi destroying ipad d’in kuma believe me idan hakan ya faru cikin kud’in adashen ki za’a sai mata sabo.”
“Hmm Allah kyauta Yasmeen Mama na karki damu Tablet me kyau zan sai miki in shaa Allahu.” Da gudu Zeezee tayi wajen Baba ya d’agata “Baba kaji Mama koh?” tayi maganan a shagwabance.
“Share ta K’anwata nasu tablet ne naki kuma ipad duk girman tab na Yasmeen bare kai naki ba ko kema kinaso a sai miki tab d’in?”
“Eh” tayi nodding kanta.
“Toh angama.”
“Gaskia nima in ta haka a sai min tab d’in na had’a da waya na” cewar Omar.
“Kai asuwa? Wai daddawa acikin kunu in kaga na siya maka tab agidan nan to kabar mugun halin kan nan ne.”
“Shikenan Baba komi Zeezee komi Zeezee sekace ita kad’ai aka haifa a gidan.”
“Kai! Ni kake gayawa magana?”
“Bar shi ai gaskia ya fad’a” Mama tasa baki. “Kai nan da Zeezee ta harare ni ba cewa kayi batayi laifi ba don haka bar sa shima.”
“Haka kikace koh? Yayi kyau muje d’aki Zeezee akwai dambun naman dana saya miki.” Mariam glutton jin an ambaci dambun nama ta lasa lips nata.
“Yauwa Baba zaka siya wa Ya Ibyaheem machine?”
“Machine kuma Zeezee? Me zeyi da machine?”
“D’azu fyends nashi sukazo dukan su suna machine illa shi.”
“Shi ya turoki koh?”
“A’a Baba” ta kad’a mai kai. Juyowa Baba yayi yana kallon Ibraheem.
“Kai ka turota ko?”
“A’a fa Baba ka tambayeta kaji.”
“So kake a siya maka machine kafara yawo a gari anyhow ko?”
“Wallahi a’a Baba.”
“Se a sai mishi ai tunda nasan da akwai kud’i a k’asa” cewar Mama.
“Eh dake kina biya na salary ai dole kice da akwai kud’i a k’asa” ya watsa mata harara.
“Baba dan Allah ka siya min wallahi barin na yawo a gari ba.”
“Zeezee a siya mishi?”
“Eh Baba” ta basa amsa.
“Toh K’anwata anything for you” ya dawo da kallonsa kan Ibraheem “seka bari in na samu kud’i tukunah.”
“Toh Baba nagode Allah ya dad’a bud’i.”
“Ameen” ya amsa sannan ya fice.
_Few minutes later..._
Mariam ce tsaye bakin k’ofan d’akin Baba tun ji da tayi an ambaci dambun nama ta kasa samun sukuni, gabad’ai kwad’ayinta ya shiga cikin dambun naman. Dabara ce ta fad’o mata tad’an yi baya da k’ofan kad’an ta shiga k’wala wa Zeezee kira ina irin tana nemanta ta bata abu d’innan.
“Zeezee! Zeezee na!”
Daga cikin d’aki Zeezee dake cin dambunta akan cinyan Baba hankali kwance tace, “Baba wancan ba mulyan Adda Mayyam bane?”
“Nata ne shareta kici abinki nasan yanzu haka wayo take son miki.”
“Zeezee!” Mariam ta cigaba da kiran ta.
“Baba zanje” ta gwada yunk’urin sauk’owa daga cinyansa.
“Tsaya tukuna. Ke Mariam!” Ya k’wala mata kira. Dum! Zuciyarta ya buga sannan ta amsa “na’am Baba.”
“Me zaki bata kike wani kiranta haka?”
“Baba na siya mata Awara ne.” Zeezee najin an ambaci awara miyan ta ya tsinke arayuwa tana son Awara.
“Baba zanje, Adda Mayyam kar ki cinye ina zuwa.”
“Toh kiyi sauri Zeezee ta.”
“Toh Zeezee da dambun naki zaki tafi? Baraki ajiye anan ba sekin dawo?” Baba yayi maganar yana kakkab’e mata kayanta.
“O’o zan je dashi.”
“Toh karki ba wa kwad’ayayyun nan fa kinji ba?”
“Toh Baba” ahaka ta fice ta tarar da Mariam tsaye bakin k’ofa, d’agota tayi kaman dagaske, “muje d’akinmu in baki ko?” with a nod takai Zeezee d’akinsu ta direta kan gado sannan ta shiga neman Awaran da bashi a d’akin, tafi minti uku tana nema har Zezee ta gaji da jiranta, “Adda Mayyam ina Awaran? Ni nagaji”
“Na nan Zeezee ina nema ne” ganin Zeezee ta kusa cinye dambun nata dabara ta fad’o wa Mariam tace, “laaa Zeezee ashe Yasmeen da kwad’ayintan nan ta cinye d’azu amman kinsan meh? Muka fita Islamiyya I promise zan siya miki kinji beautiful Sis?” Kai Zeezee ta gyad’a mata tare da miqewa dan ficewa daga d’akin, ganin haka Mariam tayi saurin tare ta “toh Zeezee bara’a sanmin Dambun bane?” Kafad’a ta make “o’o.”
“Aww ni in baki Awara ke ki hana ni Dambun ki? Nima inta haka na fasa.”
“Toh ai baki bani ba.”
“Zan baki ai Zeezee I promise.” Da k’yar ta sha kan marowaciyan ta bata.
~* ~* *~
Bayan tafiyan yaran Islamiyya Mama ta fiddo da duka kayakin ta daga wardrobe da nufin gyarawa, Zeezee na a zaune kan gado tana kallon kowani move nata kasancewar Ipad nata yayi running outta charge. Sallaman Aunty Sis da Mama taji yasa ta bar duk abinda take ta fice da sauri dan taro wannan babbar bak’uwa. Nan fa uwar b’arna ta samu kanta, a nitse ta sauk’o daga kan gadon, ninkakkun kayakin Mama Zeezee ta shiga wargazawa tana warwarewa tana sa saura kusan minti ishirin Mama sukayi da Aunty Sis, koda ta tambayi ina Zeezee Mama tace tana ciki bari ta kirata. Haka Zeezee naji Mama na kirarta tak’i fitowa da k’yar ta fito daga baya. Aunty Sis wane ta cinye Zeezee haka kawai yarinyan ta shiga mata rai kamar yadda ta saba shiga wa mutane rai. Aunty Sis da son kyauta koda tazo tafiya seda ta d’au dubu biyu ta bawa Zeezee. Bayan tafiyan ta Mama ta dawo d’akin only to see the biggest suprise of her life.
“Zeezee! Meh haka? Bakida hankali neh? Kayakin nawa kika ma wannan tabargaza?! Iyyeh!”
“Mama bani bane.”
“Ni ce ai tunda ba keba wallahi me hana ni dukan ki a gidan nan yau se Allah” kafin Zeezee tasa gudu Mama ta yi kanta ta shiga mammaketa, kuka sosai Zeezee tasa ganin ba mahalicci se Allah tayi shiru don kanta sannan ta kama hanyan bakin k’ofa seda taci ready sannan ta kira sunan Mama. Mama na juyowa Zeezee ta d’aga hannu ta seta ta tayi mata alaman ‘Uwaki’
“Ke! Ni kika zaga? Zaki raina wa kanki wayo yau” Da gudu tabi Zeezee nan itama tasa gudu har sunkai bakin k’ofa kenan sega Baba shigowa, chak ya d’aga Zeezeen da tuni tasa kukan munafirci.
“Ya haka Hafsah? Me kika ma Zeezee? Karki gaya min bin yarinyan nan kike.” Nan Mama ta labarta masa dukkanin abinda ya faru to her suprise Baba yace shi sam be yarda Zeezee ta zageta ba wai sharri take mata har maqora yakai Mama tace, “wallahi Baban Zeezee ka cigaba da goye ma yarinyan nan gindi wataran kaima barata barka ba, mu zuba da kai.”
“Ba ruwanki nide karki kuskura kitab’a min k’anwa. Inba sharri ba wai har Zeezee zakice ta d’aga hannu ta zageki” A fusace Mama ta juya zata koma ciki Zeezee tace da Baba, “kuma Aunty Sis tazo tabani kud’i Mama ta k’wace wai zata siya wa Yasmeen tab dashi.”
“Haba ita da Sultan suka zo?”
“A’a tace ya tafi islamiyya.”
“Hafsah!” Baba ya kira Mama data kusan shiga d’aki. “Ina kud’in da aka bawa yarinyan nan? Maza ki bata abinta ba naki bane.”
Da tafin ta tajuyo tana kallonsu sannan tace, “LOL ni kuma me zan da dubu biyun K’anwar ka? Zoki amshi abinki.”
★★★
Haka Zeezee ta cigaba da girma cikin *_GATA_* maras misaltuwa. Ko kad’an Baba bayi ganin flaws nata duk abinda tayi da dai-dai da ba dai-dai ba shi dai-dai ne a idonshi. Kuma duk abinda tace ayi shi akeyi machine da sabon wayan da tace asai wa Mariam da Ibraheem seda aka sai musu. Da yaran suka gano haka kuwa duk wani abinda suke buk’ata Zeezee suke samu suyi ta mata zak’in baki daga baya har Mama itama in tanason abata kud’in anko kokuwa na d’inki muddin bata son tab’a kud’in adashen ta Zeezee take turawa wajen Baba. Sede kafin Zeezee taje musu se sun sha wulak’anci harta Mama tace se Mama tace mata Aunty Zeezee tukun taje.
Ahaka har yarinya takai 3 years sosai ta k’ara wayo ga kyau har na k’in k’ari in aka barni ma se ince tafi Mama kyau. Sede uban rashin kunya kan ba gobe, bata ganin kowa da gashin ido se Baba shi kad’ai ne in yace mata bari zata bari in bahaka ba sauran duk bata jin maganansu ciki harda na Mama.
Mama kam dad’i kashe ta za’a sa Zeezee a school this year, ko a babu bakinta ze huta da surutu.
CIKIN GARI.
Kasancewar yaran sunyi hutun 3rd term a School, in aka koma yanzu new section zasu shiga ga kuma siyar da admission da ake yanzu a school nasun yasa Mama tsayawa dan sai wa Zeezee form a cika mata itama. Bayan isarta gida ta tarar da family’n ta zaune a babban parlour’n Baba kowa na harkan gabansa bayan duk sun bita da sannu da zuwa Yasmeen taje ta d’au mata ruwan sanyi. Tana shanye ruwan tasa hannu a jakarta ta ziro form data siyon “gashi Alhj form na siyo wa Zeezee se a cika mata gashi Yasmeen miqa wa Babanku.”
“Form na wani school?” Baba yayi tambayan lokacin da Yasmeen ke miqa masa form d’in.
“Ji Alhj da wata magana da na wani school zan sai mata? Na Havardth mana ba duk can yaran suke ba.”
“Se kuma akace miki can za’a sa Zeezee? Nifa banason shishshigi wallahi, waya rok’eki? Waya saki siyo matan?” Attention na kowa ne ya dawo kan Baba fuskokin su duk d’auke da neman k’arin bayani.
“Ban fahimce kaba Alhj.”
“Ai baraki tab’a fahimta taba daman, toh I mean kinyi asaran kud’in siyan form d’in dan ba’a Havardth zan sa Zeezee ba.”
“Ikon Allah wani school zaka sata?”
“Wai ina ruwan ki? Tambayoyi sekace ‘yar jarida? When the right time comes you’ll know.”
“Hmm! ba gaskia kam ai dole kak’i fad’a anyways tayi tsami ma ji.”
“Wai ma tsoronki akeji ne? A LYS zan sata.”
”L meneh?” Mama ta kwararo manyan idanunta waje disbelievingly, ba ita kad’ai ba haka siblings na Zeezee mah.
“LYS!” Yaran sukayi exclaiming in shock a tare.
“Eh shi ‘yan bak’in ciki kawai, shi za’a sata.”
“Alhj kasan me kake shirin yi kuwa? Kasan ko nawa ne fees na school d’in kuwa kake wannan magana?”
“About N70k (dubu saba’in) fah” cewar Ibraheem still in shock.
“Ina sane, shi yamin shi zan sa ta ba ruwan ku tunda bada kud’in ku bane.”
“Lallai Alhj! Makarantan dubu saba’in sekace bamusan me zamuyi da kud’i ba? Ni wallahi ban goyi bayan shawaran nan ba. Yaran nan naga duk a Havardth suka fara karatu kuma shi zasu gama in shaa Allah, d’an dubu ishirin zuwa talatin gashi yanzu SS 3 Ibraheem ze shiga kuma naga ana karatu bawai ba’ayi ba amman kace Zeezee se makarantar dubu saba’in?!” ta k’are maganan still not believing whats happening.
“Toh ni yanzu na ce miki dama ba’a karatu ne ciki? Kawai achan d’in nafi son insa Zeezee. Makarantan ‘yan gayu, makarantan masu kud’i ba kalan nasu Ibraheem da kowani d’an unguwa ke ciki ba. Harta ‘ya‘yan Sarkin Bauchi a LYS Academy suke.” Kafin Mama tayi magana Yasmeen tayi saurin fad’in “Baba nima asani.”
“Ja chan tsohuwa dake kawai! Kamar yadda sauran ‘yan uwanki suke Havardth kema chan zaki cigaba.”
“Oh ni Hafsatuu! Partiality a filin Allah haka! Nide kar a zo ana cemin ba’ada kud’i aga ko I will care dan makarantan 70K kam ba abin wasa bane.”
“Kanki dana yaranki akeji K’anwata de LYS zata shiga ko kuna so ko baku so ‘yan bak’in ciki kawai instead kuyi rejoicing za’a k’anwarku a School mekyau se uban kishi da hassada koda shike ba laifin ku bane halin Mamanku ne.”
****
Washegari bayan sun gama breakfast Baba yasa Mariam tayi ma Zeezee wanka tsaf ita de Mama nata ido ne. Bayan an gama shirya ta cikin leggings and armless top nata suka fita chan akayi mata passport sannan ya wuce dasu New GRA, LYS Academy inda ya siya mata form. Washegari suka koma inda akayi mata interview, yarinya da uban baki duk abinda aka tambayeta ta sani Baba se dad’i yakeji ana yaba K’anwarsa ana ce mata zatayi ilimi.
_One Week Later..._
CIKIN KASUWAN CENTRAL, BAUCHI.
Zaune family’n Alhj Isma’il Yosouf suke cikin wani babban shagon da ya kasance mafi girma cikin kasuwan. A gobe zasu koma makaranta shine sukazo yin shopping. Kowa an sai mai jaka d’aya takalmi d’aya seda dozen na socks banda Zeezee da aka sai mata school bags uku had’ad’d’u, takalma ma uku da dozen na socks masu uban kyau guda uku suma. Itade Mama ba abinda take banda kallon Baba dan kuwa yafi k’arfinta yanzu. Bayan nan suka wuce shagon provisons juice carton-carton kala uku ya d’au wa Zeezee ba a maganan chocolates da sauran snacks, shopping de kaman ba gobe yayi wa Zeezee bayan isansu gida duk suka fiddo da kayakin kowa ya shiga gwada nasa yana jin dad’i sede any moment suka tuna komi na Zeezee yayi tripling nasu se sujiyo tokari a zuciya amman ya suka iya? Zeezee *_‘YAR GATA CE!_*
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 07
*December, 2016*
Lunch Mama da Mariam suka shiga had’awa nan da nan suka gama aka d’iba ma kowa nasa da nama d’ai-d’ai akai. Ihu Zeezee ta k’urma “ya haka Zeezee wani abu ne?” Mama tayi saurin tambayarta.
“Ni banashon nama d’aya, banasho!”
“Jimin ‘ya da guda nawa kikeso? Bakiga plates na yayyun naki bane?”
“Baba! Baba!” Tashiga k’wala mai kira a gigice ya fito “K’anwata meya faru haka?”
“Mama ne!” Tasa kukan da anayin sane amman ba hawaye.
“Wai Hafsah shin yaushe ne zaki koyi son yarinyan nan? Kullum ace bakida aikin da yafi sata kuka?”
“Seka gayamin mena mata ai, daga sa mata abinci seta hau min kukan banza Mariam mik’on plate d’ina in d’iba in bar musu kitchen d’in.”
“Meya faru K’anwata?”
“Nama d’aya Mama ta shamin.”
“D’aya kacal? Adalilin meh?” Wabje serving spoon d’in yayi ya kwashi ragowar naman tas ya zuba wa Zeezee a plate nata ido kawai Mama ke binsa da “ni kuma me zan samu inci?”
“Inba keda abinki bama me zakiyi da cholesterol a jiki? Jekici abincin ki K’anwata.” Kafin su Ibraheem su soma cin namansu Zeezee har ta cinye 15 meats dake kan plate natan ko tab’a tuwon batai ba, ahakan tana neman k’ari wajen Ibraheem ta nufa ta zauna “Ya Ibyaheem nama.”
“Naman uwaki, ki gama cinye na miyan duka ki wani ce in baki nawa, bazan bada ba.” Su Mariam najin haka suka b’oye nasu cikin tuwonsu ihu ta k’urma daga ciki Baba yace, “wa kuma ya tab’ata yanzu?”
“Ya Ibyaheem ne yaban nama wai o’o.”
“Kai Ibraheem kaci girma ka bata mana.”
“Baba ni shikenan kullum sede ban d’ibi abinci ba seta riga cinye min nama.”
“Ka bata nace karka bari in fito.” Dogon tsuka yaja sannan ya d’au naman ya cusa mata a baki cike da mugunta “seki cinyen ai Mumu kawai.”
“Kaima Mumu” ta murgud’a mai baki.
Fitan su Baba sallan Azahar Zeezee ta fito da had’ad’d’un throw and doghnurt shaped pillows na Mama wanda take jerasu kan gadon d’akinta waje ta baza kan varenda tana wasa dasu. Mama na idar da Sallah tafito ta hau ta da masifa, “maza tashi ki mayar min su d’aki, iskancin naki har ya kaiga fito min da pillows waje mayar dasu nace!”
“O’o balin mayal inba.”
“Bazaki mayar ba?”
“Eh ni ki banni” mari Mama ta sakar mata a baya nan tasa ihu “Allah ya ishana!” ana cikin haka su Baba suka dawo “ya haka tun daga waje nake jin hayaniya.”
“Sekazo kayi mata magana, kace ta miyar min da pillows na d’aki tunda bata jin maganan kowa se naka.”
“Yanzu Hafsah meye aciki dan yarinya tafito da pillows tana wasa dasu.”
“Alhj kalli a k’asa fa take gurzasu.”
“Yi wasan ki k’anwata kinji?” Yayi maganan yana shiga ciki binsa Mama tayi tana k’orafi “wallahi ka cigaba da goye wa k’arya gindi ace yarinya duk abinda tayi dai-dai ne a idonka wataran da kanka zakayi kuka wallahi mu zuba mu gani.”
“Kanki akeji” yace da ita lokacinda ya mik’e kan gado “muddin ina gidan nan kam keda yaranki bazaku tak’ura wa K’anwata ba.”
Futu-futu Zeezee tayi da pillows na Mama sannan ta barsu gun ta zarce tsakar gida ta hau wasan banza da ganganci, koda Mama tafito ta ganta tanayi bata ce mata komi ba saboda there is no point doing so, koda tace mata ta bari ba barin zatayi ba. Kan turmi ta d’alle tana wasa daga bisani kawai ya juye da ita ta fad’i nak! A k’asa se ihu malam!
“Ai ga erinta nan kita wasan banza sekace na miji kad’an kika gani ai.”
“Eh kad’an tagani muguwa kawai ‘yarki ta fad’i amman ko kiyi yunk’urin d’agata” Baba wanda sanadiyan ihun Zeezee yafito dashi yayi maganar yana d’ago crying Zeezee daga k’asa. “Sannu koh? Sannu K’anwata” d’an hannu da gwiwa ta gurje amman se kuka take wane kanta ne ya fashem
“Sosai ne taji ciwon?”
“Ban sani ba kina zaune achan kaman kayan wanki shiga ciki kid’au min first aid sannu ko K’anwata yi shiru.”
A sannu a sannu ya samu ya shafa mata dettol wajen sede har yanzu bata bar kukan ba ita zafi “toh K’anwata me kikeso ayi miki?”
“A kila Ya Ibyaheem ya hula min.”
“Shi kikeso?”
“Eh da Ya Omal.”
“Ibraheem! Ibraheem!”
“Na’am Baba.”
“Kazo kai da Omar” bayan isowan su sukayi tsaye gun not minding halin da Zeezee ke ciki, “bakuga k’anwarku taji ciwo bane? Can’t you tell her sorry? Banason sakarci fah.”
“Sannu” sukayi murmuring in unison.
“Oya Ibraheem zo ka mata blowing air a wajen yana mata zafi.”
“Ni kuma Baba?” Yayi maganan yana pointing kansa.
“A’a ni dan k’aniyanka zo ka mata blowing air nace” haka yana kumbure-kumbure ya iso ya tsuguna gaban Zeezee k’afan nata ta mik’ar ta aza kan cinyansa take ya tunkud’e k’afar “meh haka zaki wani samin k’afanki me dottin nan kan kaya, bakiga farin kayane a jikina ba.”
“Bata gani ba sa k’afan naki Zeezee” nan ta miyar “ayyi Baba kayan fa zeyi dotti.”
“Ungo naka nan kai da farin kayan naka maza! hura mata iskan kaima Omar turn naka na zuwa in wan naka ya gaji.”
By 3:00PM as always yaran suka hau shirin islamiyya Mama dake neman hutu in any way possible ta kalli Zeezee dake mak’ale jikin Baba tana game nata hankali kwance tace, “Zeezee shin ke se yaushe ne zaki fara zuwa islamiyya wai kam? Mates naki duk sun soma zuwa” Kai Zeezee ta d’ago ta galla wa Mama harara sannan tace, “ban shani ba.”
“Ya miki kyau, ina Alhj kana ganin irin abinda nake yi maka magana akai ba? Yanzu ina zan iya shiga cikin jama’a da maras kunyan yarinya haka.”
“Ke shikenan bakida aikin yi a gidan nan se yiwa Zeezee baki?” Baba yayi maganar a fusace. “Gaskiya banaso, baki tashi zagi a gidan nan se akan Zeezee, islamiyya ne barata shiga ba seta k’ara girma haka kawai barin kai ‘yata islamiyya a jibgeta a banza ba.” Hannu Mama ta tafe tare da sakin salati.
“Su Yasmeen da suke zuwa ai ba haifan su akayi ba.”
“Yasmeen daban Zeezee daban.”
“Kuma bokon da zaka satan shi ai ba’a duka koh?”
“A LYS? Kin tab’ajin inda akace miki an daki d’alibi a LYS? Ai rashin dukansu is the number one reason da yasa zan sa Zeezee school d’in.”
“Lallai kanada aiki toh ko su basu dake taba ni nan zan dake ta sede bata sake zagina ko min rashin kunya ba.” Ba tare da ta jira me Baba ze sake fad’i ba ta fice masu daga parlourn.
“Shareta kinji K’anwata? Karki kula Mama and anytime ta tab’a ki tell me kinji? Zan rama maki da kaina.”
“Yeyy! Baba ni duk nan gidan nafi shonka.”
“Ai nima na fi sonki Zeezee ba a gidan nan kad’ai ba a duniya gabad’aya.” Ya shafa dogon sumanta.
***
Da fitan yaran bada jimawa ba Baba ya yi alwala ya fice Masjid shima. Bayan Mama ta idar da Sallah tajiyo sallama daga waje, ba tare da b’ata lokaci ba ta fita, Sultan yaron Aunty Sis ta tarar da ‘yar basket a hannunsa bayan ya gaishe da Mama ya mik’a mata basket d’in tare da fad’in “Mama nane tace in kawo miki.”
“Allah sarki Aunty Zainab, toh Sultan d’an albarka kace mata na gode sosai kaji?” tayi maganan tana bud’e flask d’in. Miyan ganye had’ad’d’e taga ciki (her favorite.) “Maman Zeezee zan tafi ina Zeezee?” Kaman ance Zeezee leqo tafito daga d’akin tana kallonsa wane yau ta soma sasa a ido. “Baraka jira kuyi wasa da Zeezee ba zaka tafi Sultan?”
“Zeezee!” yace da ita yana mata murmushi.
“Kazo gidan mu dan ka d’auke min ipad k-” bata idda maganar ba Mama ta bige bakinta “ce maki akayi yana d’auke-d’auke? Toh in baki sani ba shima Sultan nada ipad nasa d’an gatan Baban sane shima.”
“Allah ya isha” tace tana kuka.
“Ni kike jawa Allah ya isa?” Mama ta sake bige mata baki, volume na kukan nata ta k’ara “kuma wallahi shena fad’awa Baba” data ga Mama bata kallonta ta d’aga hannu ta zageta se anan taji ta huce.
“Zeezee bar kuka kinji?” Cewar Sultan warmly ko ta kansa batai ba ta nemi gu ta zauna tana ciccire ribbons da suke kanta tasan sarai Mama ta washi ta ganta tana yin hakan.
Kai kawai Mama ta kad’a da taga abinda Zeezee ke tasan sarai on purpose takeyi.
“Maman Zeezee zan tafi tunda yau Zeezee tak’i kula ni.”
“Share ta Baba na tsaya in d’an d’auko maka koda juice ne.” Nan tayi ciki, Zeezee na jin an ambaci juice hankalin ta ya tashi, sahun Mama tabi taga Mama na k’ok’arin bud’e mata sabon carton na juice nata. Wani irin shegen ihu tasa sannan tayi gudu ta cafko hannun Mama. “Ni wayyayi ki aje min jush d’ina ai nawa ne ba naki ba ki ajiye!” Ta rushe da kuka.
“Sake min hannu marowaciya kawai, da Uwarsa tazo ta baki dubu biyu kin iya karb’a ke kice baza a bashi juice ba? Wallahi kinyi k’arya sake min hannu!” Sake dandameta Zeezee tayi tana ihu kaman ana cire ranta, ko ta kanta Mama batai ba ta d’iba juice uku wa Sultan da sauran chocolates and snacks komi uku-uku sannan ta sa mai a leda. Uwar rowa tayi kuka har nishinta na wani sama-sama dan kanta tayi shiru ta fice varenda taje ta kwanta flat wajen tana birgima only if ace gun da k’ura da tayi putu-putu da kayan jikinta ko k’ala Mama bata ce mata ba ta juyo abincinta a plate ta samu waje ta zauna tana ci. Sarkin rowa ga kwad’ayi tuni kwad’ayinta ya shiga abincin, ba kunya bale tsoron Allah taje ta samu Mama “nima zanci.”
“Ba abinda zaki ci.”
“Wayyayi sena ci” ta miqa hannunta zata sa cikin plate d’in.
Bige hannun Mama tayi, “da hannu du dottin zaki sama min a plate? Bud’e bakin marowaciya kawai” haka suka yita drama har suka k'are abincin.
Bayan da suka gama cin abinci Zeezee ta nemi wayan Mama qirar Samsung galaxy S4 ta nufa chan ta side nasu Ibraheem inda ake ajiye manya manyan roba cike da ruwa ta jefa wayar ciki, se da ya kusan minti biyu sannan ta cire ta basa few seconds ta sake miyarwa tana murmushin jin dad’in abinda takeyi tace, “nan gaba jaki shake d’auka min jush kibawa Sul-” sunan da bata gama k’arisawa ba kenan due to lafiyayyen marin da Mama ta sakar mata a baya. Ihu ta saki Mama ta fisgota zuwa main tsakar gidan “bakida hankali ne iyye? Da wayonki da komai zaki d’au min waya ki jefa a ruwa?” Hannunta taja zuwa kitchen sannan ta zari tsintsiyan kwa-kwa guda biyu ta tattara kayan Zeezee sama ta shiga shwad’eta. Zeezeen da tunda tasan kanta ba’a tab’a mata duka ba se yau ta ringa kuka kaman ba gobe ana cikin haka Baba ya dawo gida. Tun daga bakin k’ofa yake jin kukan K’anwarsa a hanzarce ya k’ariso only to see the biggest suprise of his life.
“HAFSAHHH!!!” Ya kira sunanta da wani irin kakkausar murya amman hakan be hana Mama cigaba da aiwatar da abinda take ba, seda ta sake shwad’e Zeezee sau biyu again sannan ta barta alokacin har Baba ya iso inda suke yasa hannu ya d’aga Zeezeen da ko kukan arziki ma ta kasa yi don azaba. “Meh haka? Kashe ta kikeson yi komeh? Wani erin sakarci ne haka? Amman Hafsah da hankalin ki kuwa?” duk wannan tambayoyi jerosu yayi da numfashi d’ai. Hannu yasa ya fisge tsintsiyan dake hannun nata, har ayanzu Mama bata ce komai ba hannu yasa ya kwantar da crying Zeezee a jikinsa yana bubbuga bayanta.
“Kinsan baki fi k’arfin in d’au belt in zaneki ba kema koh?”
“Ka fad’i koma meh, kekuma kad’an kika gani ki sake d’aukar min waya kisa a ruwa kigani,” tayi maganan tana huci.
“La’ila!! Yanzu Hafsah akan waya kika daki yarinyan nan haka se kace zaki kaita lahira? Ina wayar?”
“Gashi nan” ta miqa mai. Abinda ya aikata ne ya mugun bata mamaki, to her suprise taga ya nufi wani daron dake cike da ruwa wajen wanke-wanke ya sake tsunduma wayar ciki baki Mama ta sake in disbelieve.
“Ansa a ruwan an kuma sawa, akan banzan wayan da be kai ya kawo ba zaki kashe min K’anwa? Nace ansa a ruwan maganan banza kawai!” ya watsa mata harara sannan ya wuce da Zeezee d’aki. Binsa tayi da kallo tace, “wallahi se ka sai sabo.”
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 08
*December, 2016*
_9:46PM_
Kowa na a zaune a babban parlour yana harkan gabansa Mama ta shigo bata nufi ko ina ba se kan Baba dake riqe da Zeezee yana kallon NEWS. Gabansa ta sha “ya haka?” Yayi saurin tambaya.
“Kud’in wayata zaka bani.”
“In nak’i fa?”
“Nikuma inja Allah ya isa.”
“Toh Hafsah kija kinji? Kija please.”
“Ni gaskiya ka bani kud’in waya na ai ‘yarka ce ta b’ata.” Maido da kallon sa yayi kan Zeezee yace;
“Zeezee abawa Mama kudin waya ta sai sabo?”
“O’o” tace tare da make kafad’a “ba ta bawa Sultan jush d’ina ba ta kuma min duka.”
“Toh kinji?” ya d’ago kai yana kallon Mama “tace kar a baki kud’in, maganan K’anwata kuma ya zauna baza’a baida kud’in ba.”
“Allah ko? Wallahi Alhj kar ka bani kud’in wayana kaga aiki da cikawa gobe, ai nasan shagunan ka da suke Wunti zuwa zan in d’ibi duk abinda yamin.”
“Allah baki sa’a toh ni matsa min kallon NEWS nake” yace da ita. Rai a dak’ule ta koma gefe ta zauna ta hau taya Yasmeen tsefe kitson ta kasancewar jibi Monday zasu bud’e school.
Ana cikin haka k’ishin ruwa ya addabi Mama ganin Zeezee ce k’arama cikinsu kuma ita ke zaune ba abinda take tace, “keh Zeezee wuce ki d’auko min ruwa.”
“O’o” tace gatsau cike da rashin kunya.
“In aike ki kice min o’o? Tashi nace!”
“O’o bayin jeba.” Kallon Baba Mama tayi taga ko a jikinsa ma Zeezee na mata rashin kunya, “dole kayi pretending kaman baka ji ai dake bakada gaskiya” tace dashi. Se anan ya juyo ya kalleta sannan yace, “ai da gaskiyar ta ko wani aike kice se Zeezee, kika tashi kuma ba wanda kike duka kaman ta ba inda zataje, Yasmeen dake gabanki ba mutum ce ba? Ki aiketa ko ki tashi ki d’auko da kanki cigaba da game naki Zeezee na.” Kai kawai Mama ta girgiza “ka cigaba wallahi, Yasmeen Mama na jeki d’auko min ruwa.”
****
Washegari su Mariam sukayi wanka tsaf harda Zeezee suka shirya wai zasu gidan kitso for the first time Zeezee za’a gidan kitso. Baba da kansa yayi dropping nasu by tunda harda Zeezeen sa yau. Kitso me kyau sukayi kasancewar za’a koma school. Banda ma kiston Zeezee dayasha beads da ribbons kamar a sace kan a gudu. Da Azahar aka gama musu Baba yaje ya d’aukosu nan ma. Dawowan su gida suka tarar da kayaki sabi zube kan tabarma ta bakin k’ofa wajen duk suka nufa suka shiga duddubawa. Kayaki suka gani duk sizes nasu masu kyan gaske, suna cikin duddubawa Mama ta fito daga ciki tare da masu sannu da zuwa. “Iyye kitson autan nawa yayi kyau” ta shafa kan Zeezee.
“Batai kuka ba Mariam?”
“Batayi ba kasancewar game tayi ta bugawa a ipad nata.” ta amsata a takaice.
“Toh ko kefa? Kin ganki kuwa?” best smiles nata ta sakar wa Mama sannan tace,
“Mama kayan waye wannan?” Zeezee a rayuwa akwai son sabon kaya.
“Naku ne” nan ta rarraba masu se godiya suke shide Baba bece ko k’ala ba. Bayan da yaran suka wuce d’akinsu Mama ta matso kusa da shi tace, “kayi shiru tun d’azu baka ga kayakin bane ko basu ma kyau bane?”
“Tsakanin ki da yaranki meya kaini sa baki.”
“Hmm haka ne? Seka kawo kud’i dan duk a bashi na d’auka.”
“Bashi?!” Yayi exclaiming yana nodding head.
“Eh bashi Alhj da aiki nake da zan iya biyan wannan uban kayaki.”
“Shin wa kika tambaya ma kafin kikayi wannan karambani?”
“Karambani? Yanzu Alhj saiwa wa yaran nan kaya shine karambani?”
“Eh mana tunda bakida kud’in biya, nima banda kud’i seki jira in kika kwashe adashenki ki biya.” Dai-dai ze miqe kenan Mama tasa hannu ta zaunar dashi. “Wallahi Alhj baka isa ba sekace ni kad’ai na haifi yaran da zaka wani ce ni zan biya duka?”
“Da ni nace ki siya musu? Kaya de yara sunada tunda ba tsirara suke yawo ba sabida haka sake min hannu.” Sake dandame hannun nasa tayi, “ba kai kace ba amman ai ya kamata ne shiyasa kai bakasan rufin asirin ka bane ana ganin yaran ka da kayaki masu kyau ba?”
“Aww! duk wanda suke dashi be ishesu ba kenan? Sake ni nikam nikam ko ki biya koki miyar wa Maman Fadeel kayakin ta.”
“Ka d’au wai barin iya miyarwan bane? Wallahi miyarwa zan.”
“Yauwa sakeni toh.” Fuska ta maraice sarai Baba yasan barata iya miyarwan ba da biyu ya fad’a hakan shima “Baban Zeezee dan Allah karka min haka, baka ma ji kud’in bafa kake wannan magana.”
“Nawa ne?”
“Dukan su ukun fa 35k ne kacal.”
“35k?” Ya zaro ido waje. “Shine kacal? Gaskia banida wannan kud’in yanzu sede in zamu biya rabi da rabi in biya 20k kibiya 15k.”
“In nayi hakan kuma da me zanyi ciko na sai sabon waya tunda kak’i bani kud’in duka.”
“In kinsan zance zakiyi ta tadawa toh kije kiyi duk abinda ya miki 20k d’inma na fasa baiwa.”
“Alhj mana dan Allah karka min haka.”
“Tsaya ma tukun d’an set uku-ukun ne har 35k nifa na lura kayan matan nan tsada ne garesu.”
“Alhj ai kasan kayan yara da tsada, Zeezee nan kad’ai taci 17K.” Hannu yasa a aljihu ya zaro kud’ad’d’e masu dimbin yawa sannan ya irga dubu sha bakwai (17) ya miqa wa Mama. “Ga na Zeezee nan, na sauran ki biya ko kuma ki jira in k’arshen wata yayi an bibbiya ni bashuka na se in gama biya.” Cike da mamaki Mama ta d’ago kai tana kallon Baba sannan tace;
“Lallai ma Alhj! wato in na Zeezee ne ka iya biya amman na sauran dake ba ‘ya‘yan ka bane baraka biya ba.”
“Wai ce miki akai barin biya ba? Nace maki banida kud’i” da hanzari ya miqe tare da adjusting hulan shi without giving ber a chance to speak yace, “zan wuce kasuwa.” Zeezee ya hau kira.
“Eh Baba!” Ta amsa daga ciki tana k’ok’arin fitowa. Daga k’asa-k’asa Mama tace, “wai ace yarinya in an kirata sede tace eh bata iya fad’in na’am ba, Allah ya kyauta deh.”
“Ina ruwan ki? Mschw! Zeezee na zan fita kasuwa kina son in saya miki wani abu?”
“Eh Baba ice cream da dambun nama.”
“Toh K’anwata sena dawo koh?”
Ba-bye ta mishi tare da komawa ciki.
“Ni matar gidan ba’a tambayeni ko me nakeso ba saboda banice a gabanka ba aiko?”
“Oh! Hafsah! Yanzu kishin Zeezee kike?”
“Ban sani ba nide a sai min gashi na kwana biyu ban motsa baki ba.”
“Seki kawo kud’i don ni banida.”
“Kaje tunda se na kawo kud’i na fasa cin” ba tare da yace k’ala ba ya fice.
_2:27PM_
Dai-dai nan Baba ya dawo gida bayan yayi parking ya kira Ibraheem yazo ya ciro wani babban kwalin da Allah kad’ai yasan meh a ciki faga motar. A varenda ya sauk’e se anan sunan dake jikin kwalin ya fito. “Washing machine?!” Ibraheem yayi excaliming da d’an k’arfi, jin haka Mama da yaranta suka leqo suma. Zeezee na fitowa ta d’ale jikin Baba.
“Baba ina aish clim d’ina?”
“Gashi anan K’anwata, Yasmeen ungo kai fridge na d’akina ki sa mata.” Baba yayi maganan tare da cire ma Zeezee ice cream d’aya daga cikin ledar. A sanyaye Yasmeen ta amsa sannan tace, “Baba nima zan sha”
“Wai ke wace irin kwad’ayayya ce?”
“Nima zan sha Baba” cewar Mariam.
“Kwad’ayayyun banza kawai! ku d’au d’ai-d’ai Yasmeen ki kai sauran d’aki.”
“Wannan kuma fah?” Cewar Mama tana me bin washing machine d’in da kallo.
“Bakida ido ne? Washing machine ne.”
“Ina da shi kuma nagani tambayata itace, washing machine na waye neighbours suka kawo a ajiye masu ko kuwah?”
“What do you mean? Ban kai in sai washing machine ba kenan ko meh?”
“Ni ba abinda nake nufi ba kenan naga d’azu ka gama cewa bakada kud’i.”
“Toh ba ruwanki bane, Zeezee K’anwata kinga wannan?” yayi pointing machine d’in da yatsa. Kai ta gyad’a as an answer. “Good, naki ne kinji? Ke kad’ai za ana yi maki wanki ciki.” Zeezee kanta seda tasha mamaki talkless of her siblings.
“Nawa Baba? Duka wannan?”
“Sosai ma K’anwata naki ne.”
“Yeyy!” Ta rungume shi tare da sauk’a daga hannunsa tana shafa jikin kwalin. Har a yanzu cikin Mama da yaranta ba wanda ya iya fad’in ko qala. Mama ta nisanta tace, “amman wallahi abin naka ya soma yin yawa Alhj, washing machine fa? Kuma kace na Zeezee kad’ai sauran ba yara bane? That aside d’azu anan nace ka bada kud’in kayan yaran nan kak’i kace ba kada kud’i, ka sai min gashi nan ma duk bakada kud’i amman ka iya d’auko washing machine da ke...” tayi pausing tana neman price tag na machine d’in. Kafin Baba yasa hannu ya tare ta karance “75k ka siya kuma wai ma Zeezee kad’ai.” Sosai Baba yaji a jikinsa ba dad’i amman ya dake yace, “toh se meh? Da tsofi dasu ne zan siya masu washing machine? Sabi’u na masu wanki me kyau shi kuma ze cigaba da musu amman de kam wannan na wanke kayan Zeezee ne kawai.”
“Ka kyauta toh Ibraheem zo muje ka siyo mana gashi.”
“Tsaya Ibraheem” Baba ya dakatar dashi da wuri, hannu ya sa a aljihu ya irga 3k ya miqa mai “gashi saya muku shikenan?”
“Nifa bana buk’atan kud’in ka” cewar Mama “miyar masa da kud’insa Ibraheem.”
“In ke bakiso yaran suna so wuce kaje ka siya muku sauran kuma kayita yawo a gari.” A sanyaye Ibraheem ya wuce.
*** _9:23PM_
Mik’e Mama ke kan gado da shirin baccinta a yayinda Baba ke other bedside d’in shida Zeezeen sa suna game, daga bisani Baba yace “K’anwata mu kwanta koh? Kinga akwai school gobe.”
“Baba gobe ne zanje school d’in?”
“Eh K’anwata.” Shiru tayi na ‘yan seconds sannan tace, “toh Baba banida uniform.”
”Karki damu zuwa next week zasu baki yanzu mu kwanta tashi in saki cikin gadon ki.”
“O’o ni yau anan zan kwana.” Kafin Baba ya amsa Mama tace, “kamar ya anan? Gadon kin kuma fah? Tashi da Allah.”
“Ke wai Hafsah meh matsalaraki ne? Anan d’in zata kwana.”
“Haba Alhj yarinyan nan ai tayi girman kwana tsakiyan mu.”
“Kanki akeji” ya miyar mata, d’aga Zeezee yayi tare da kwantar da ita tsakiyansu. Mama de bata ce komai ba, wuta Baba ya kashe yabar dim light zalla sede sam Zeezee takasa bacci ta juya nan ta juya chan da abin ya isheta ta miqe zaune “Baba!” ta kirasa yadda ta saba always.
“Na’am” ya amsa cikin bacci.
“Baba ni acile min beads d’in suna hanani basshi.” Nan Mama da batayi bacci ba tace, “kamar ya acire Zeezee? Ko kin manta yau aka miki kitson kuma kinada school gobe?”
“Ni acile min.” tayi maganan almost crying.
“Baza a ciren ba mschw!” Duk nan Baba besan me suke ba sautin kukan Zeezee yayi shooking nasa awake.
“Ya haka? Meke faruwa Hafsah?”
“Seka tambayi K’anwar taka ai.” Tayi maganan tare da juya masu baya.
“Meya faru Zeezee?”
“Baba ni acile min beads d’in suna hana ni basshi.”
“Acire kuma K’anwata? Kinsan gobe fa zakije school yara dayawa za’ayi musu kitso da beads.”
“Ni bana sho.”
“Toh an gama K’anwata, Hafsah!” Yasa hannu ya jijjiqata. Shiru Mama tai bata amsa ba. “Hafsah!!” Zeezee ta kira Mama da unanta da k’arfi.
“Lallai kam!” Mama tace tare da juyowa. “Rashin kunyar kin har ya kaiga kirana da suna na?”
“Toh ba kiran ki nake tun d’azu kika manna min hauka ba, karki tak’ura wa K’anwata please.” Baba ya kare Zeezee. Ba tare da Mama ta sake cewa abu ba ta koma ta kwanta.
“Hafsah! Magana fa nake miki.”
“Dan Allah kubarni inyi bacci ko na fice guest room.”
“Tashi ki cire mata beads d’in in kin gama yaso seki koma baccin.” Zama Mama tayi ba tare da tasan tayi hakan ba duk dan yadda kalamun Baba suka bata mamaki wato shima ya goyi bayan wannan rashin hankali. Ganin bata soma cirewa Zeezee beads d’inba se kallonsa take yace, “kefa muke jira ko a kunna maku wuta neh?”
Mik’ewa yayi ya kunna wutan d’akin sannan ya dawo ya zauna, ganin har yanzu Mama bata soma cirewa Zeezee beads d’in ba ita kuma bata bar fitinan acire ba, Baba ya d’aga ta ya azata kan cinyan Mama “oya ciccire mata su duka.” Kai kawai Mama ta girgiza ta hau cire beads d’in, na gaban tace Zeezee tayi hak’uri abar mata su amman ina sam Zeezee tace se an cire duka hakan ko akayi.
*** Washegari.
_Monday, 6:00AM_
On the dot Mariam tayi knocking bisa k’ofan d’akinsu Baba, yin haka sau biyu Baba yace, “come in.” A hankali ta bud’e tare da shiga, sanye take da wandon uniform nasu seda vest a jikinta bayan ta gaishe shi ya amsa tace, “nazo d’aukan Zeezee inyi mata wanka.”
“K’arfe nawa ne yanzun? 6 yayi neh?”
Eh Baba.”
“Toh ina zuwa” dawo da kallonsa yayi kan Zeezee tare d tapping nata. “K’anwata! K’anwata tashi kinji? Today is your first day at school.” Zeezeen da tayi nisa a bacci ko jinsa ba tayi ba, sake jijjigata yayi “tashi kinji yau zaki fara zuwa school tashi amiki wanka.” Cikin baccin tace, “yau ne Monday?”
“Eh K’anwata yau ne Monday tashi toh.”
“O’o ni abanni inyi basshi se anjima inje.” Haka da k’yar Baba ya iya ya tada Zeezee, Mariam na ganin kanta ba beads ta dafe k’irji, “Zeezee ina beads naki?” Kafin Baba ya amsa Mama ta juyo tana fuskantan su tare da fad’in “ba ga tanan ba fitinanniyar yarinya, haka ta sani gaba jiya seda na ciccire mata su.”
“Kuma se kika biye mata Mama?”
“Ke ina ruwanki? Mschw! d’auke ta kiyi mata wanka da Allah” Baba yasa baki.
“O’o ni ba Adda Mayyam bane zatayi min wanka.”
“Se waye kuma Zeezee?”
“Nishe Ya Ibyaheem.”
“Shi kikeso?”
“Eh” ta gyad’a kai.
“Toh angama, Mariam fice kije ki kiramin Ibraheem kice yazo yayi wa K’anwata wanka.”
“Toh” tace tare da ficewa.***
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 09
*December, 2016*
D’akinsu Ibraheem ta nufa direct, kwance ta tarar da shi bisa gado da laptop nasa zaune kan cikinsa ya had’a da earpieace da alama kallo yake. “Ya Ibraheem wai kaje kayi wa Zeezee wanka” tayi informing nasa. Earpieace d’in yacire tare da miqewa zaune “what?!” Yayi exclaiming. “Inyi ma waye meh?”
“Kayi wa Zeezee wanka.”
“Buro-uba zan mata ba wanka ba, in ba iskanci ba I have three siblings kizo kina wani cemin ni zan ma wancan Zeezeen wanka toh barin yi ba kije kice barin yi ba, aikin banza kawai! Mschw!”
“Oho bani zaka gaya wa hakan ba se kaje kasamu Baban daya saka yimatan ka fad’a mai anan ne zan san eh ka cika saurayin Eesha White.” yi yayi kan beji last statement nata ba;
“Baba ne yace in mata wanka?” Yayi maganan a bit shocked.
“Eh naje Zeezee tace se kai.”
“Wallahi se naci uwar yarinyan nan kap gidan nan ba wanda ta raina se ni” Mariam de bata sake cewa komi ba ta fice kitchen dan had’a musu breakfast.
_10 Minutes Later..._
“Wai kam ina Ibraheem ne? Yazo yayi ma yarinyan nan wanka ne yake b’atan lokaci haka?” Baba dake riqe da Zeezee a hannu yayi maganar a fusace. “Wai Hafsah ni kad’ai ne a d’akin?”
“A’a kaida K’anwarka ne a d’akin” ta miyar masa da amsa tare da juya mai baya. “Oya kema tashi yau ‘yarki zata fara zuwa school kin kama kin wani baje kan gado ga ke baki damu ba koh? Tashi da Allah kije ki had’a mata lunch pack nata, ki sa mata komi bibbiyu sannan ki soya mata k’wai biyu ki dafa mata biyu up you go.”
“Alhj!” Mama ta zaro ido waje, “k’wai hud’u ita kad’ai?”
“Ina ruwanki da kud’in ki ake siya?”
“Allah kawo ranan da zaka ce min bakada kud’i.”
“Kan ki akeji, ke wai bakisan ana hakan bane don asa mata son makarantar a ranta? Kinada matsala wallahi.”
“Allah kyauta” tace tare da miqewa, dai-dai nan Ibraheem shima dake sanye da singlet da ¾ trouser yayi sallama ya shigo d’akin.
“Se yanzu kaga daman zuwa?” Shiru... “Magana nake ma da wani d’an banzan farin fuskan ka kamar k’osai a wajen.”
“A’a” ya sadda kansa k’ansa.
“Zoka d’auketa da Allah.” Kai ya d’ago in disbelief yana kallon Baba shin Zeezee batada k’afa ne da za’a ce masa yazo ya d’auketa? Halan k’afafun nata na kwalya ne.
“Me kake jira wai?” Da wuri yayi kan Baba yasa hannu ze amshe Zeezee dake bacci abinta, hannunsa na tab’a jikinta ta hau shure sa “ni banasho.”
“Zeezee Ibraheem nefah tashi ya miki wankan” a hankali ta bud’e idanunta tana kallon Ibraheem sannan ta yarda ya d’auketa. Maimakon yayi hanyan bathroom dake d’akin, se ya hau hanyan barin d’akin, ya kai dab ga fita Baba yace, “d’an fari ina kuma zaka kaita? Ko ka manta hanyan bayin neh?”
“Zanje na mata a bathroom namu ne.”
“Brush nata da sponge nata kuma fah?”
“Bari in d’auk-”
“Wuce da Allah kayi mata anan kaima kayi wayo wai ko? So kake kaje can ka mata mugunta mugu kawai wuce ina ganin ka.” Haka Ibraheem kaman yayi kuka ya shiga bayin da Zeezee ya cire mata kaya ya mata brushing sannan ya hau mata wanka yana tab’a mata fuska tasa wani d’ankaren ihu, take Baba ya shigo “ya haka? Me kake mata?”
“Meh kuwa Baba? Wanka nake mata.”
“Kayyanshi ne Baba ya matse min fuska.”
“Ai nasani mugu kawai” Baba yakai masa bugi a baya “yimata a hankali nace!” kuka ne kawai Ibraheem beyi ba da zaran yad’an tab’a mata fuska seta sa ihu Baba ya mauje sa shikuma, a haka har suka samu suka gama wankan yafito da ita nannad’e cikin towel. Man shafawanta ya d’auko da niyan shafa mata ta shiga turesa.
“Meh haka? Da Allah nikam ki tsaya in shafa miki.”
“O’o nishe jikina ya bushe.”
“Yaushe ne jikin naki ze bushe? Ki tsaya in goge jikin naki da towel.”
“O’o ni banasho.”
“Baba kace mata ta tsaya.”
“Zeezee tsaya ya shafa miki kinji?”
“O’o ni banashon Ibyaheem (yau ba Yayan ma) ni Yashmeen nake sho.”
“Tafi nono fari” cewar Ibraheem tare da galla mata harara. “Oya Ibraheem jeka kira Yasmen kace tazo ta shafa wa Zeezee mai.”
*** A kitchen...
Dawowan Mama kitchen Mariam dake riqe da stirring spoon a hannunta tana kula da indomie’n su tace, “wai Mama kam ina zaki kai wannan eggs haka?”
“Sekin tambaya ne? Na Zeezee mana.”
“4 eggs ita kad’ai?”
“Iyi kuwa.”
“Wallahi baramu yarda ba muma, ai muma haifan mu akayi mu ace mu d’au k’wai dai-dai ita hud’u? Hud’u? Nima bibbiyu zan d’aukan mana yau.”
“Na yaushe kuma bayan an riga an aza k’wan kan wuta.”
“Soya mana zan” nan ta nufi fridge ta ciro musu k’wai ta hau soyawa.
“Kins-” shigowan Baba kitchen d’in ya sa Mama katse maganarta.
“Wai ina breakfast na yarinyan nan ne? Ko sekun sata latti tukuna?”
“Gashi nan fa Alhj mu fita nikam.”
“K’wan can fa nawaye?”
“Na Zeezee.” cewar Mama.
“Kamar ya na Zeezee? Ba biyu nace ki soya mata ba?”
“Kai ni Alhj ka cika bin diddigin abu wallahi ga breakfast na K’anwarka nan ba seka fice ba, ina ruwanka da abinda ke gudana cikin kitchen d’in kuma?”
“Ke Mariam k’wai nawa kika d’aukar muku yau?” Shiru... “Dake fa nake!”
“Bibbiyu.” tayi maganan a tsorace.
“Bibbiyu? Ban hana ba?”
“Ka hana amma naga Zeezee fa har guda hud’u ita kad’ai.”
“Uwaki nan da kike had’a kanki da Zeezee toh wallahi daga yau in sake ganin me d’aukan k’wai biyu a gidan nan ya soya yaga abinda zan mai” yana kaiwa nan ya wabje plate daga hannun Mama yayi ficewarsa.
~* ~* ~*
7:07AM aka gama shirya Zeezee, kowa a gidan seda yayi contributing to shirinta as Baba yayi ta tada musu hankali. Pink leggings da vest meh crossed arms fari me kwalyan pink aka sanya mata sannan aka d’aura mata k’aramar blazer pink akai. Shoes nata kuwa pink ne seda farin socks sosai tayi kyau wane ‘yar turawa wai ahaka ma tasa an cire mata beads nata jiya. Bayan Baba ya gama yi mata wanka da designer turarukansa ya saqala mata pink disney bag princesses nata a baya sannan ya riqe mata had’ad’d’en lunch pack nata me heart shape suka hau tafiya, ganin sun iso har bakin k’ofar barin d’akin Mama batace komi ba, bata kuma da niyan cewa komin Baba yace, “ke wai haka akeyi neh? Yau ranar farkon zuwan ‘yarki school bako Allah yabada sa’a? A wani wajen ma ke da kanki zaki kaita.”
“Toh Alhj naji nayi laifi, Zeezee Allah ya bada sa’a kinji Mamana?”
“Niba Mamanki bane niba shohuwa bane.” Ta k’are maganan tana bubbuga k’afa, dariya ne yaso kub’uce wa Mama amman batason yi kada Baba yad’au wai ta huce seta maze.
“Toh Auta na Allah yabada sa’a ayi karatu sosai fah.”
“Toh ba-bye” se anan suka fice da Baba har sun iso tsakar gidan amman cikin sauran yaran kap ba wanda ya fito duk suna ciki suna kan shiri Yasmeen kamma ko uniform bata sa ba.
“Ibraheem! Ina kuke? Zaku fito ne ko sekun sa min K’anwa latti tukuna?”
“Baba gamu nan” Ibraheem yayi ihu daga ciki yana k’ok’arin sa oil a hannunsa dan shafawa a kai.
_2 more minutes..._
“Baku san ni bane wallahi tafiya zan in barku, taho mu tafi Zeezee” dai-dai nan Ibraheem da Omar suka fito. “Su Mariam fah?”
“Bansani ba nima” cewar Omar yana adjusting collar rigarsa.
“Da kyau mutafi, Mariam! Ke da Yasmeen seku biya ta keke napep kokuma ku taka da k’afa mu mun tafi.”
“Allah sarki Baba gamu nan zuwa fah” cewar Mariam da ihu tana sa kajol a idonta, Yasmeen dake gefen gado tana pulling socks tace, “ba duk shi yasamu lattin ba aka fara shirya Zeezee kaman tashin duniya.”
“Kede bari ina lip gloss yake?”
“Na cikin chess of drawer’n farkon nan ki duba.” Har seda Baba ya kunna mota ready to leave them behind sannan su Mariam suka samu suka fito nan ma Mariam bata sa socks ba wai se a cikin mota.
As always Ibraheem ya nufa k’ofan gaba ze shiga da wuri Zeezee ta sha gabansa ta rik’e handle d’in restarining him. “Ke ya haka?”
“Ni jan jauna a gaba.” Tayi stating confidently cike da rashin kunya.
“Ke asuwa? K’aramar kwaro dake matsa min da Allah!” ya tunkud’e ta. D’ankaren ihu ta saki wanda ya dawo da attention na Baba kansu.
“Ya haka meke faruwa?”
“Ya... Nama fasa ce maka Ya d’in” ta harare sa sannan ta cigaba, “Ibyaheem ne ya mareni a kaina.”
“Mari?!” Exclaimed Baba, “ba kada hankali ne? Yarinya zata school ka sata kuka? Ka kiyaye nifa.” Baba yayi scolding nasa.
“Baba ni yaushe na mareta? Ta matsamin na shiga gaba wai a’a.”
“Eh ni jan jauna kaje baya.”
“Oya koma baya toh Ibraheem.”
“In koma baya?”
“Kaji ni deh” ze saki magana Baba ya katse sa “ka shiga ko kuwa ka tafi da kanka.”
“Ai wallahi gwara na tafi da kainan” ya juya kenan Baba ya kirasa “maras kunyan yaro kawai dawo! Dawo nan dan Ubanka seka zauna a bayan wuce ina ganinka!” Ya tsawata masa haka yana kumbure kumbure yayi joining k’annensa a baya, suka matsu su had’u a yayinda Zeezee ke gaba ita kad’ai tana shanawa abinta. Su aka soma dropping sannan Zeezee, a inda aka tanadar dan parking motoci wato parking space Baba yayi parking motarsa sannan ya zagayo ya ciro Zeezee a hannu ya riqeta suka k’arisa class nasu Nursery 1.
Form teacher’n su Zeezee Mrs. Anderson na hango Baba tayi sauri taje ta taresa wato tun ranan da akayi interview Zeezee ta shige wa Aunty’n su rai, ba yadda Aunty’n batai ba amman Zeezee tak’i zuwa wajenta. Bayan sun gaisa da Baba ta nuna masa seat na Zeezee wanda yake nan close to her table, ajiye Zeezee Baba yayi yamata adjusting kayanta sannan yace, “se kiyi karatu ko K’anwata in kun tashi by 12:30PM zanzo in d’auke ki okay?” Cike da rashin fahimta tace, “Baba tafiya zakayi ka banni?”
“Eh Zeezee bakiga sauran ‘yan class naku suma iyayensu sun ajiye su sun koma gida ba?” Mai da kallonta tayi kan ‘yan class d’in tana binsu da kallo taga duk ba parent bayan nan gashi duk yara matan an musu kitso da beads gwanin sha’awa, ita yanzu bama wannan ba wai tafiya Baba zeyi ya barta ta d’au yadda suka zo tare haka zasu koma kamar a kyaftawan ido ta sauk’o daga kan seat d’in ta shige jikin Baba “ni o’o tare zamu tafi mu koma gida na fasa makalantan.”
“Zeezee kin tab’a ganin inda aka fasa karatu? Yi hak’uri ki zauna kinji? Anjima kad’an zan zo in d’auke ki.”
“Ni o’o” ta b’arke da kuka tabar Mrs. Anderson ta tab’a tama tak’i duk ‘yan ajin se kallonta suke.
Ana cikin haka wani mutum wanda a shekaru ze girmi Baba koda irin 5 years haka ya shigo, babban mutum ne da an gansa, hannunsa riqe yake da wata little angel wanda ga dukkan alamu ‘yarsa ce saboda tsantsan kaman da suke. Mrs. Anderson na ganinsu tayi excusing kanga gun Baba ta nufa wajen mutumin.
“Lubabatu right?” Tayi maganan tana kallon ‘yar mutumin data sha ado sosai wane Zeezee ga beads kota ina akanta, “follow me please Mr. Maitafseer” tace da mutumin. Seat na Zeezee ta ajiyewa Lubabatu jakarta tace da Zeezee, “look here, I’ve made you a friend her name is Lubabatu Maitafseer so stop crying okay?” Zeezeen da tunda Aunty ta fara magana ba gane abinda take fad’i tayi ba banda Lubabatu dataji ta ambata ta sake sa kuka bayan data k’are wa Lubabatu kallo, sosai Baba ya shiga lalashinta “shikenan toh ya isa Lubabatu koh? Ta tab’a min ke? Sorry toh” Kukan take har yanzu ba makawa, Lubabatu da dad nata suka tsaya kallon ta chan Zeezee tace, “an yima Lubabatu kitson beads ni ba’a min ba” ta kuma fashewa da kuka. Dariya sosai dukansu wajen suka hau yi Alhj. Matafseer ya nisanta yace, “da alama wannan itace auta koh?”
“Itace” Baba ya amsa mai yana murmushi, miqewa yayi da Zeezee a hannunsa suka gaisa da Alhj. Maitafseer tare da yin formal introduction. “Zeezee sauk’a kije ki zauna kinji K’anwata?”
“O’o se ammin ilin kishon Lubabatu.” Baba ya kalli Dad na Lubiee dake murmushi yace, “karka manta fa an mata kitso da beads me kyau tasa mahaifiyarta a gaba sam se an cire mata take wanan fitina yanzu.”
“Ahab! Ko Lubiee nan jiya seda tace a cire mata na hana uwar, ba duk abinda yara suke so zamuna musu ba.”
“Hakane...” cewar Baba kamar dagaske.
“Zeezee mama na sauk’o kinji? Ga k’awa nan na miki kinji sunan ta Lubiee.”
“O’o ni ba maman ka bane niba shohuwa bane.” tasa kuka. Dariya duk suka tsaya yi at her comment, “ya isa, sauk’a toh K’anwata” da k’yar ya samu ya sauk’e ta, ta tsaya tana kallon kitson Lubiee “ni se ammin ilin wannan.”
“Karki damu, muka koma gida za’a miki” Baba yayi assuring nata. “Sunan ki Lubiee?” Zeezee ta tambayi Lubiee.
Kai Lubiee ta d’aga in response “ke kuma Zeezee?” Itama ta gyad’a mata kan.
“Yauwa jeku zauna toh se kuyi karatu fah” hannunta Lubiee taja suka zauna ko ba’a tambaya ba za’a san Lubiee ta girmi Zeezee danko ta fita wayo, shiru Zeezee tayi bata sake cewa komi ba seda taga Baba ya d’au hanyan barin ajin ta sake sa ihu shima se yaji bare iya barinta ba, da k’yar Dad na Lubiee yajasa sukayi waje. Kuka kenan! Kuka Zeezee ke wane ana cire mata rai Lubiee ce ke lalashinta har ta samu tayi shiru ko da aka fita break Aunty da Nanny suka bubbud’ewa kowa lunch pack nasa seda suka sha mamaki ganin yadda aka cika wa Zeezee nata.
Sede wani abin mamaki sekace ba Zeezee me rowan da muka sani ba, ganin nata chocolates d’in sunfi na Lubiee yawa ta d’ibi guda biyu ta bata cikin d’an k’ank’anin lokaci wasa da shak’uwa ya shiga tsakanin Zeezee da Lubiee.
~* ~* ~*
Ko minti d’aya Baba be k’ara kan 12:30PM (lokacin tashin su Zeezee) ba, ana ringing bell ya shiga school yayi class nasu Zeezee alokacin suna ta wasa ita da Lubiee da sauran ‘yan class nasu, tana ganin sa taje tayi hugging nasa, sosai Aunty ta sake yabawa k’ok’ari irin na Zeezee dai-dai Baba yazo fitowa suka had’u da Baban Lubiee gaisuwa kad’an sukayi kowa yabi path nasa.
~* ~* ~*
Dawowan su Baba gida Zeezee tayi ciki da gudu, Mama ta tarar tsaye a tsakar gida da gudu taje tayi mata oyoyo Mama ta d’agata sama “yaya school d’in?”
“Mama nayi k’awa sunanta Lubiee ko Baba?”
“Sannu da zuwa Alhj.”
“Yauwa sannu”
“Zeezee tayi kuka da ka ajiye ta?”
“Sosai ma se a hankali zata saba ai.”
“Toh Auta na me aka koya muku?”
“Littin (written) form of A and sound ‘ahh’, and litten form of B and sound bhh.”
“Ahh gaskiya autan nawa na ja.”
****
Da yamma bayan tafiyan yaran islamiyya Baba kuma masallaci Zeezee ta samu kanta, k’usa ta samu ta nufa garriage inda Baba ke parking motarsa da yake mugun ji dashi fiye da duk wani abinda ya mallaka. Dai-dai driver’s door ta zana babban letter A sannan da small one a gefensa haka tabi other side d’in ma tayi thesame thing with letter B, jiki ta sata wane batai komai ba taje tasamu Mama dake zaune tsakar gida tana tsifa, “Mama zan tayaki.”
“Inba kaud’i ba ina ke ina tsifa?”
“Ni shena miki.”
“Nace baza kiyi ba kuma ki yasar da k’usan” ihu tasa ta soma kuka, badan Mama na so ba tace ta taso ta tayata. Tsifan da ba’ayi ba ranan kenan, ita ta hana Mama yi ita kuma bawai iyawa tayi ba.
Atare Baba da yaransa suka iso gida kaman ance Baba duba motanka yana kai dubansa yaga letter A na mai sallama “subhanallai me wannan? Waya min wannan d’anyen aikin? ‘yan unguwa ko meh?”
“Laaa Baba gashi ma har a nan!” cewar Yasmeen da hanzari ya zagaya ya duba.
“Aiko ba’a tambaya ba ansan Zeezee ce” cewar Mariam, a rayuwa ba abinda tafiso kan taga Baba da Zeezee suna fad’a. A fusace Baba ya nufa ciki su Mariam ne a sahun baya suna binsa.
“Zeezee! Zeezee! Zo nan!” tana jin muryan Baba ta lab’e bayan Mama dake zaune kan sofa a parlour. “Ba babanki bane yake kiranki? Kije mana!”
“O’o, Mama karki bari ya tab’ani jan baki shweet d’ina.”
“Me kika masa tukuna?”
“Bab-” bata k’are maganan ba sega Baba da gayyansa suna shigowa cikin parlourn, cusa kanta tayi jikin Mama.
“Ya haka Alhj wani abu ne?”
“Zeezee!” Ya kira sunanta a tsawace, kakkarwa ta soma, “mesa kika zana min jikin mota? Dan bana dukanki koh? Wayace ki zana min mota?” Shiru... “Dake fa nake magana!” Ya sake fad’a a tsawace. Kuka Zeezee tasa “toh kayi hak’uri amman kad’an ka gani wallahi ai nasha gaya maka kadena biyewa ‘yar nan bakaji ga irin ta ai.” Ignoring what Mama said yace, “kika sake zana min mota sena zane k’afafuwanki da tsintsiya ce miki akayi mota gun rubutu ne?” Hannu ta d’aga ta zagi Baba, baki kap dukansu including Baban suka sake in shock.
“Zagi! Ni kika zaga Zeezee?” D’ayan hannunta ta d’aga ta sake zaginsa sannan daga bisani ta sauk’e duka ta b’uya bayan Mama “ai kad’an ka gani nasha gaya maka adinga taka mata birki bakaji yau kanka abin ya koma ai.”
“Waya koya miki zagi? Iyyeh! Zan zane kifa! Ni kika zaga? Toh ki sake ki gani da wayan charger zan shod’e kafafunki!” ya tsawata mata sosai, kuka ta shiga yi sosai ko ta kanta beyi ba yabar parlour’n.
Dariya kenan! Ibraheem and others dariya suke tsakanin su da Allah wane dan shi aka turo su duniya, suna dariya suna yimata rawa da wak’ar shoki ita ko se k’ara volume na kukan nata take Mama ce kad’ai ke lalashinta “yi hak’uri amman kema kar ki sake, ba kyau zagin Baba ku kuma haka akeyi ne? K’anwar ku ce fah.”
“Ai Mama ajiye wanga zance a gefe” cewar Mariam in between laughter.
“Ahtoh! Bature beyi k’arya ba, 9 days for the thieve one day for the owner.” Omar ya mara mata baya suka cigaba da yiwa Zeezee dariya ita ko se kuka take.
Da dariyan yayyun nata ya isheta ta fice musu daga parlour’n gabad’ai taje chan bayan BQ ta baje a k’asa se kukanta take sha kan ba gobe.
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 10
_Words can’t ever explain how much I love you *AUNTY SIS*, thank you for everything, thank you for being that one great special person to me. ILY eternally😘😘😘😘 I devote this page in special honour to you! Don’t thank me you deserve more and more!_
_5 minutes later..._
Baba ya dawo parlour da alama ya huce yanzu, Mama kad’ai ya tarar a parlour’n tana tsifa, “Ina Zeezee?” Ya tambaya.
“Oho yayun ta sun sata gaba suna mata dariya ta fice ban san ina ta shiga ba” ba tare da ya amsa taba ya fice tsakar gida ya shiga k’olla wa Zeezee kira tana jinsa tak’i amsawa har a yanzu kukan take. Nemanta ya shiga yi chan bayan BQ ya tsince ta nishinta har wani sama-sama yake sekuma tabasa tausayi yaji dama be mata masifan ba, a nitse ya k’arisa gabanta yace, “Zeezee” kanta ta kawar daga kallon sa.
“K’anwata yi hak’uri kinji? Tashi mu koma ciki” nan ma shiru. “Yi hak’uri kinji K’anwata Baba is sorry amman kema karki sake zana min mota kinji? In rubutu kikeson yi let me know sena baki paper ko book kiyi. Mota ba wajen rubutu bane kinji?” da k’yar ya samu ya shawo kanta dan banzan zuciya irin na Zeezee, bayan ta yarda ya d’auketa yace, “su Ibraheem sun yita miki dariya ko?” Ta gyad’a kai a shagwabance.
“Yi hak’uri toh muje su baki hak’uri” a k’aramar parlour Baba ya tadda yaran, “waya miki dariya cikinsu?” Ya tambayi Zeezee.
“Dukan su” tayi pointing nasu da finger.
“Oya ku bata hak’uri.”
“Hak’uri?” Exclaimed Ibraheem, “meh muka yi mata da zamu bata hak’uri?”
“Uwarka kayi mata, d’an banzan yaro bata hak’uri nace!” Chan k’asa-k’asa alsmost like mumbling Ibraheem yace, “yi hak’uri.”
“Ban jika bafa, ka bata hak’uri kace Zeezee kiyi hak’uri, oya ina jinka.”
“Wallahi Baba raina ni zatayi.” yayi protesting.
“Da kai da rainin duk uwaku, bata hak’uri nace!” Haka Baba ya sasu individually sukayi ma Zeezee apologising.
“Shikenan koh K’anwata yi hak’uri” sauk’eta yayi tare da ficewa. Habaici ‘yan uwan nata suka hau yi suna zaginta kota kansu batayi ba taje ta d’ibo baby dolls nata da teddy bears ta jerasu kan table a waje sannan ta d’au ruwa cikin wani d’an karamin bucket ta ajiye se sponge case nata ta shiga ta d’auko. Wanka ta shiga yima dolls natan tafara da teddy’n kenan Allah ya fito da Mama “kai! Kai! Karki sa ma teddy’n ruwa!” dakatawa Zeezee tayi tana kallon Mama, “‘yar k’auye kawai wayace miki ana wanke teddy bear?”
“Ni shena wanke, tunda Baba ya shiyo min su bashuyi wanka ba.”
“Ce maki akayi mutane nesu? Karki sa musu ruwa nace!”
“Ni shena sa, Baba! Baba!”
“Na’am K’anwata, Hafsah dan Allah kifita daga harkan yarinyan nan, dan Allah nace” Baba yayi maganan daga cikin d’aki.
“Teddy bears fa zata ma wanka.”
“Eh kibarta please.”
“Dama ai ta nan kafi kauri, d’aure wa k’arya gindi, gidan wa aka tab’ayi wa teddy bears wanka?” Dawo da kallonta tayi kan Zeezee “kinji wallahi karki kuskura ki shigo min da su ciki in kin jik’an kinaji ko?”
“Shena shigo dasun” tana kaiwa nan ta kwarawa teddies d’in ruwa tahau musu wanka jak’ab ta jik’asu da ruwa tazo shigowa dasu Mama ta bud’e mata ido sosai koda Baba yayi magana ta nuna mai she’s damn serious baza’a shigo dasu ba.
“Shikenan K’anwata karki kula Mama kinji? In sun bushe seki shigo dasu, jeki cigaba da wasan ki” ciki tayi ta d’auko mai sannan ta bud’e kit na Mama ta zaro scissors ta fice da wuri bayan ta bi baby dolls da teddies d’in ta goggoga musu mai ta d’au d’ayan baby doll me uban gashin tasata gaba ta yayyanke gashin tas, haka tayi da sauran gabad’aya tayi musu aski Yasmeen ce tafito ta kamata in the act.
“Laaaha’ila! Bade aski kika yiwa dolls nakin ba?” Dariya tasa ta kira Mariam, “Adda Mariam! Zokiga wani abu” atare Mariam da sauran suka fito, dariya suka hau yi ganin yadda Zeezee ta tand’e gashin kan baby dolls natan wane aikin wanzami. Dariya suka tsaya yi har seda Mama dake kitchen ta fito “wai haka kuka ta dariya lafiya dai ko?”
“Dubi fa Mama” Yasmeen tayi maganan tana k’ok’orin d’ago d’aya daga cikin dolls d’in cizo Zeezee takai mata “kal ki tab’a min Baby na.”
“Zeezee yanzu aski kika ma baby dolls nakin? Meye amfanin hakan?”
“Gashin je fito ai, ba Mulan (cartoon) ma ta ashke gashinta ba kuma ya shake fitowa, nashu shuma je fito.”
Habbaa!! Dariya dukansu suka sa gun, saura harda hawaye da k’yar Mama ta iya tayi shiru tace, “sekuma aka cemaki wannan cartoon ne? Ai tunda kika aske musu bai sake fitowa.”
“Sheya fito”****
Kasancewar yaran basu je islamiyya ba yasa bayan Sallan La’asr kowannensu ya kwanta yin bacci, Mama ma can ad’akinta ta mik’e tana bacci Baba da Zeezee ne kad’ai idonsu biyu shima don yana buga lisafi ne yana gamawa ya mik’e kan gadon d’akinsa “K’anwata zo mu kwanta kinji? Ajiye Ipad d’in kinga kinje school yau kamata yayi ki huta kema, bakiga sauran yayyun naki duk sunyi bacci ba?”
“Ni o’o banajin basshi.”
“Toh Allah baki hak’uri ni zan kwanta” nan da nan Zeezee tabar d’akinsa tayi nasu Mariam kulle ta tarar da k’ofan nasu, ba kalan knocking da batayi na suna ji suka k’i bud’ewa dan kanta ta nufi nasu Ibraheem suma haka suna jinta tana knocking suka k’i bud’e mata. D’an shirme tayi a tsakar gida, data gaji don kanta taje ta samu Baba a d’aki ta mik’e gefensa itama tana wasa da d’an gemun dayake ajiewa. Ahaka har bacci yayi gaba da ita ba ita ta tashi ba se 7:35PM alokacin gari yayi duhu shaarrr. Bayan ta fito daga parlour ta nufi parlour inda ta tarar da ‘yan uwan nata suna kallo “ni ahad’a min tea shafe yayi.”
“Ke waya gaya miki safe yayi? 7pm nefa yanzu.” Cewar Yasmeen.
“Meh 7pm? Ni a had’a min tea shafe yayi.”
“Shareta Yasmeen fitina ne da ita ai Baba ya hanata shan tea da daddare ba abinda za’a had’a miki.” Mariam tayi stating. Kuka Zeezee tasa awajen tana kiran sunan Baba seda yafito tayi shiru, “K’anwata kin tashi neh?”
“Baba kace Adda Mayyam ta had’a min tea.”
“Babu shan tea da daddare yana saki fitsarin kwance, in kina jin yunwa a dafa miki indomie da egg naki koh?”
“Yanzu ai shafe ne ba dale ba ni a had’a min tea.”
“Dan fa bata saba baccin yamma bane shiyasa take gani kaman safe ne yanzun” Ibraheem yayi explaining.
“Ba shakka kam, K’anwata ba safe bane fa yanzu dare ne.” Mik’ewa tayi k’asa agun tana birgima tana ihu ita a had’a mata tea, ba yadda Baba beyi da ita ba ta gane fa ba safiya bane dare ne yanzun amman inaaa sam takasa ganewa ita tunda tayi bacci ta tashi toh safe yayi don haka kuma a had’a mata tea. Haka Mariam ta had’a mata tean itade Mama tausayin katifanta take gudun kar Zeezee ta tsula mata fitsarin kwance.
**** 8:23PM
Baba da kansa ya taya Zeezee suka yi mata homework, bayan sun gama yasa mata book nata cikin jaka “sauran bacci ko K’anwata? Akwai school gobe.”
“Nishe an sha min beads ilin na Lubiee” nan Mama dake karatun Qur’ani ta juyo ta watsa mata harara “waye boyi-boyin ki agidan nan? Jiya kice se an cire yau kice a miyar? Kinyi k’arya.”
“Ni nace ke jaki shamin ne” tayi maganan tare da murgud’a wa Mama baki.
“Ai ko kince nima ba sa miki zan ba.”
“Toh ya isa haka da Allah, kisa ‘yar yarinya a gaba kina exchanging words da ita, Zeezee asa miki beads?”
“Eh” ta gyad’a kai.
“Oya Hafsah ibo beads d’in maza ki sa mata.”
“Wallahi-”
“Ni banashon Mama Ya Omal nakeso” Zeezee tayi sauri katse Mama.
“Omar kuma?” asked Baba.
“Eh shi.”
“Toh Hafsah mik’a mata beads d’in taje ta same shi ya samata.” Bayan Mama ta mik’a mata ta fice a k’aramin parlour ta tsinci yayyun nata suna kallon King Of Hearts gaban Omar tasha yayi saurin fad’in “ya haka? Matsa min nikam” beads natan ta nuna mishi “gashi ka samin.” Wani kallon rainin hankali ya sakar mata sannan yasa dariya ba shi kad’ai ba har sauran ‘yan uwan nasa.
“D’an daudu ne ni da zakice in sa miki beads?”
“Ni kasha min.”
“Bazan san ba maras kunya kawai, matsa min ko na gaggaura miki mari inba iskanci ba ki dubi Adda Mariam da Yasmeen ki wani ce wai ni zan sa miki beads bakida kai.” Kuka tasa wajen har seda Baba ya fito tayi shiru, “ya haka? Meke faruwa?”
“Omal ne yashamin beads wai o’o.”
“Laha ila! Ni? Yaushe nace barin sa miki ba?” Cewar Omar.
“Munafiki na sanka sarai maza zaunar da ita ka fara sa mata” ba tare da ya sake musu ba ya soma aiwatar da abinda aka sashi.
“Ni banashon wannan film asa min dijney junior.” Banza da ita sukayi kaman basu jita ba.
“Ashamin dijney” ta k’are maganar a shagwabance.
“Shin baku jita bane?” Asked Baba.
“Ayyah Baba yanzu fa ze k’are” cewar Mariam calmly.
“Wayyayi kayya ne ni asamin disney.”
Dogor tsuka Ibraheem yaja ya sa mata disney’n “kalli fa Baba shirme ake.”
“Eh bar mata shi takeso” yana kaiwa nan ya fice, habaici yaran sukayi tayi tsakaninsu suna zagin Zeezee a yayinda Omar keta samata beads na mugunta yana d’ad’d’angale gashin bayan ya gama mata ta wuce d’aki ta kwanta tsakiyan su Baba ma yau.
***Washegari...
_6:05AM_
Bayan Mariam ta shigo ta gaishe da Baba kaman jiya ta gaya mai dalilin zuwanta da ‘toh’ ya juya ya shiga tada Zeezee dake ta sharb’an bacci.
“Zeezee tashi kinji? Akwai school yau ko bakison kije kiga Lubiee?” Shiru... “Tashi kinji K’anwata.”
“Ni o’o bayin jeba.”
“School d’in?”
“Eh bayin jeba.”
“Yi hak’uri.”
“Ni o’o” ba yadda Baba beyi da ita ta tashi ba tak’i. Bayan sunci fiye da minti goma Zeezee tak’i tashi Baba yace da Mama “to ke bazaki sa baki bane?”
“Ni asuwa? Wai daddawa acikin kunu, bayan kai Zeezee tana jin maganan wani a gidan nan ne? Tsakaninku” tana kaiwa nan ta juya mai baya tare da jan comforter.
“Zeezee tashi kinji?”
“Baba ni bayin jeba” tasa kuka, kuka take tsakaninta da Allah ita bazata jeba, at long last Baba ya amince mata “jeki Mariam, Zeezee bazata je school ba yau se gobe.” Kai kawai ta gyad’a cike da mamaki sannan ta fice bayan ficewarta Mama tace, “lallai ka cigaba da yima yarinyan nan duk abinda takeso muga ina ze kai ka da ita duka” banza da ita Baba yayi yaja Zeezee sukayi kwanciyar su.
*** A takaice ranan ba abinda Zeezee ta tsinana banda yima Mama rashin kunya da rashin ji, washegari ma da k’yar Baba ya iya tadata aka shirya ta school. Koda taje yau ma tayita kukan shagwaba seda taga Lubiee hankalinta ya d’an kwanta. Cikin sati Zeezee ta saba da school sede kullum kafin a tasheta se anyi drama ga zab’an wanda zeyi mata wanka, sa mata uniform, yi mata polish na takalami sa mata, do komi.
_Saturday afternoon 2:32PM_
Bajewa Zeezee tayi a tsakar gida tana kukan banza ita se an kaita gidan su Lubiee tunda yau ba school. Kota kanta Mama batai ba, hasali ma ignoring nata tayi ta shige d’akinta ta kwanta 2:40PM Baba ya dawo gida as always ya tambayeta whats the problem bayan ta irga masa ya share mata hawaye tare da fad’a mata ta kwantar da hankalin ta ze kaita gidan su Lubiee tunda yanada lambar Alhj. Maitafseer. Ba tare da b’ata lokaci ba ya kirasa bayan sun gaisa ya sanar dashi halin da ake ciki, cike da jin dad’i Alhj. Maitafseer yama Baba bayanin gidan sa dake Old GRA. D’aki direct Baba ya wuce ya tarar da Mama kwance “Hafsah! Hafsah tashi ko bacci kike?”
“Ya akayi Alhj? So nake in huta kafin La’asr please.”
“Hutu? Ai hutu be kama kiba.”
“Me kake nufi?” tayi maganan tare da miqewa zaune.
“Zaki shirya kanki da Zeezee yanzu in kaiku unguwa.”
“Unguwa? Unguwa a ina?”
“Zaki raka Zeezee gidan k’awarta Lubiee” yayi stating in an I-don’t-care manner.
“Lallai kuwa!” Mama tasa hannunta a kunkumi “ba inda zani, akan ganin k’awarta za’a tauye min hak’k’i, ina nan ba inda zani.”
“Semuga in zaman kanki kike a gidan nan na baki minti talatin ki shirya kanki da Zeezee wallahi in bakiyi haka ba ranki yana iya b’aci” nan ya sauk’e Zeezee k’asa, “karki damu kinji K’anwata zan kaiki gidan su Lubiee.”
“Toh Baba” anan ya fice. Mama tafi minti biyar a zaune tana hararar Zeezee sannan daga bisani ta mik’e ta hau shiri exactly after 30 minutes Baba yadawo d’akin ya tarar da ita sun gama shiri tsaf, dad’i sosai yaji “kaiii masha Allah, Hafsah ta bade kyau ba tsaya keda K’anwata in d’auke ku hoto.”
Dad’i sosai Mama taji dan yadda Baba ya yaba kyanta da kuma kwalyanta amman sede me? Batason nuna masa ta huce kan abinda yayi minutes ago, burning face tayi kan bataji me yace ba.
“Haba Hafsah ta? Menayi kuma yanzu? Hoton ne bakiso?”
“Ban sani ba” tayi speaking up finally.
“Yi hak’uri toh ki tsaya” remembering that tana son ta tambayesa kud’in ankon bikin ‘yar k’awarta yasa ta saki fuska taja Zeezee ya d’auke su hoton. “Yauwa masha Allah, gaskiya in godewa Allah da yasa a beautacious woman like you ta kasance mata ta” yayi maganar yana editing picture nasun.
“Uhm! Alhj ba de zak’in baki ba.”
“Ai kema kin sani Hafsah, a kullum dad’a kyau kike.”
“Uhm Alhj nace bikin ‘yar Aunty SDY fa ya matso.”
“Toh Allah sa ayi a sa’a ya kuma bada zaman lafiya mu tafi ko? Inason in wuce kasuwa bayan nayi dropping naku.”
“Ameen kud’in ashobe nakeso.” Ai take mood na Baba ya canza, a rayuwa ba abinda ya tsana kaman a tambayesa kud’i.
“Ke shikenan kullum cikin tambayan kud’i kina ruining happy moments? Mu tafi da Allah.”
“Bangane ruining happy momnts ba daga tambayan kud’i seka haura min sama.”
“Toh ni banida tashi mu tafi kina b’ata min lokaci.” Komawa tayi ta zauna tace;
“Ai wallahi ba inda zani ina nan seka bada kud’in nan had it been matter’n ya shafi Zeezee da without a second thought ka cire kud’i ka biya mata buk’ata wallahi nima ko ka bani kud’in ashobe dana gudumawa ko kuwa kaida K’anwarka kuyi ficewar ku” tayi stating in a serious tone. Ganin eh fa dagaske take ba inda zata inbe bata kud’in ba ya nisanta yace, “haka zaku k’are ai mutane sun d’au rayuwan k’arya sun aza wa kansu wai ba’a zuwa gidan biki seda ashobe toh Allah ya shirya ku wallahi”Zeezee kam se raba ido take ta kalli Mama ta kalli Baba.
“Ameen ka fad’i koma meh nide ka bani kud’in kawai shikenan.” Dogon tsuka yaja “mschww! Nawa ne kud’in?”
“Dubu ishirin ne duka, dubu goma na ashobe goma na gudumawa.”
“Har dubu goma zaki kai as gudumawa saboda auren Aneesa ne?” (blood sister ta)
“Muna zumunci sosai da Aunty SDY da kunya in kai mata abinda ya gaza dubu goma tunda akwai kawai ka kawo.”
“Mschw! Allah shiryaki wallahi” hannu ya sa a aljihu yaciro wallet nasa tare da irga fifteen thousand (15K) “amshi.” Hannu ta mik’a ta karb’a tare da irgawa bayan da tagama taga be cika ba, “ya haka Alhj? Sauran biyar d’in fa?”
“Abinda nake dashi kenan in na kwashe duka kud’in na baki me zamuyi cafani dashi gobe? Ki cikata da kud’inki maza tashi mu tafi.” Chan k’asa-k’asa tace, “ko a babu na rage hanya” wardrobe nata ta nufa ta adana kud’in sannan suka fice.
~* ~* ~*
Dai-dai 3:07PM suka isa gidan su Lubiee bayan sun fito daga motan Baba dake daga ciki yace, “se bayan La’asr in shaa Allah zanzo in d’auke ku.”
“Kai balaka shiga bane Baba?” Asked Zeezee.
“A’a K’anwata keda Mama na kawo ku ba-bye.”
“Toh se anjima” cewar Mama tare da jan hannun Zeezee suka shige.
*** Cikin d’an k’ank’anin lokaci Mama da Ummin Lubiee suka saba se hira suketa zubawa wane sun san juna dama da jimawa, a yayinda Zeezee da Lubiee ke chan suna ta wasa, sosai Lubiee taji dad’in ganin Zeezee, su ci abinci ma sunk’i se wasa suke a tsakar gida kasancewar gidan nasu nada sarari sosai. Chan suka shigo ciki suka sami su Mama a parlour inda ake ajiyewa Lubiee motar wasanta wanda yake nan Babba sosai, ciki ta shiga ta tuk’a sannan tasa Zeezee ma ganin Zeezee bata iya ba tad’au remote control d’in tana driving nata dashi. A hankali Zeezee ta koyi driving d’in itama seyi takeyi ana cikin haka Baba yayi wa Mama waya kan gashi shigowa zasu gaisa da Abban Lubiee se su tafi.
Bayan sun gaggaisa Mama ta d’ibo takalaman Zeezee dan sa mata ai atafir Zeezee tace bazata koma gida ba anan zata kwana in ma zata koma chan gida sede in da motan Lubiee zata tafi.
“Shin motan naki neda zakice zaki tafi dashi?” Lectures Mama. Cikin kuka Zeezee tace, “ni wayyayi shena tafi dashi” tana shure k’afa.
Se hak’uri parents na Lubiee da Lubiee ke bata amman ina se kaman ma sake tinzirata suke, if only zasu iya cewa ta d’au motan, atlast Baba yayi speaking up “taso toh K’anwata irin wannan kikeso?” Nan ta gyad’a mai kai.
_Bade sai mata zakace zakayi ba?_ Mama tayi maganan unbelievably a zuci.
“Toh shikenan za’a saya miki” Baba ya fad’a tabbatar wa Mama da zarginta.
“Alhj a ina ne ka sayo wa Lubiee?”
“Anan Central...” nan yama Baba kwatancen shagon.
“Toh thank you.”
“You’re welcome incase ya ganka Alhj ya bugeka price d’in is 42K.”
“Haha toh nagode mu tafi Hafsah” ya k’are maganan yana sharewa Zeezee hawaye. Baki Mama ta tab’e batare da tace komai ba, har gun motansu parents na Lubiee sukayi masu rakiya akayi ba-bye sannan Baba ya kunna mota suka tafi. A maimakon yayi hanyan gida seya kama hanyan kasuwa da Mama ta gano hakan se kawai ta girgiza kai “bade central d’in zaka wuce siyo wa K’anwarka motan ba.”
“Toh ina ruwanki? Ke bakiga kukan datake tayi bane?”
“Toh wallahi in haka ne nima se ka cika min dubu biyar d’in.”
“Se mugani ai” haka Mama naji tana gani Baba yaje ya siyawa Zeezee motar itama sede nata har yafi na Lubiee ma girma, her’s costs 50K. Ba rigimar da batai wa Baba ba amman yak’i cika mata wai se k’arshen wata itan da za’ayi biki tsakiyan watan yau.
0 comments:
Post a Comment