Hausawa suka ce wai rana bata k'arya, sai dai uwar d'iya taji kunya. Yau ne ranan da aka daura auren Jaleelah da mijinta Wanda a yanzu ma bata damu data San ko wane ne ba, aikin gama ya riga ya gama. 11AM aka daura auren amma tun bayan da aka daura ta shige dakinta ta kwanta tana ta kuka. Da k'yar Mommy ta samu tayi wanka ta saka light purple cotton lace din da aka dinko mata daga cikin kayan lefenta wanda ma bata san an kawo ba. Har mai kwalliya Mommy ta kira amma kiri kiri Jaleelah taki yarda ko powder ta shafa. Allah ma ya taimaka tun ranan Thursday taje salon tayi lalli.
12PM Mrs Maryam ta isa gidan bikin, mutane sun cika sosai, da Hadiyya ta fara haduwa, nan tayi leading dinta zuwa dakin Mommy tayi mata murna sannan ta wuce d'akin Jaleelah. Duk a tunaninta zata ga kawayenta sun cika dakin amma sai taga wayam, ba kowa sai Jaleelar ita d'aya. Da sauri ta kariso ta rungume ta tareda fashewa da matsanancin kuka, patting dinta ta dinga yi a baya daga bisani su ka koma kan gado suka zauna, kukanta ta cigaba da yi har na tsawon husan 10mins sannan Mrs Maryam ta fara bata ha'kuri, "ya isa haka mana" ta fada mata tareda share mata hawayen fuskanta.
"Tunda kika ga an d'aura auren nan alkhairi ne, you've been praying and I also help you did, haqiqa Allah yana amsa kiran duk wanda ya kira shi kuma nasan yaji kiran mu kuma ya amsa, kisa a ranki wannan auren ba komai bane face alkhairi, okay?"
Nodding kanta tayi ta share hawayen da ya kwaranyo daga idanuwanta.
"Ina kawayen naki?" Ta jefo mata tambayar, tace "ban gayyaci kowa ba sai ke"
Murmushi tayi tace "thanks for it. I feel honoured. Ina kwalliyar taki?",
"Banyi ba"
"Haba.. Yau fa ranar aurenki ne, daga yau sai labari, abeg dauko min make up kit dinki ni inyi miki", haka nan ta tashi taje ta dauko mata ta zauna ta fara mata kwalliyar. Tayi matukar yin kyau bayan an gama kwalliyar ta daura ash bridal satin. Mrs Maryam tayi ta daukanta hotuna suna dariya, har videos suka yi.
Mommy data leko taga fuskarta da kwalliya sai da tayi mamaki kuma tayiwa Mrs Maryam godiya da ta taimaka ta fito da ita.
Tare sukayi sallar azahar da la'asar. Maryam bata tafi ba har sai da 'yan biko suka zo daukan amarya lokacin sun idar da sallar la'asar bada wani jimawa ba. Sai da ta sauya kayanta zuwa atamfa mai kyau ta daura alkyabba a sama sannan aka kaita wurin Daddy yayi mata fada, sai a lokacin ta k'ara gasgata eh tabbas fa tayi aure, fada yayi mata sosai amma kuka da tunane tunane bai sa sun barta taji abinda ya fad'a da kyau ba. Daga nan aka kaita d'akin Mommy inda 'yan bikon suke jiranta. Tsugunnawa tayi a gaban Mommy ta rike kafafuwanta tana rusa kuka kamar wacce aka kashewa iyaye, a cikin kukanta babu abinda take fadi sai Mommy Mommy Mommy. Nan da nan ita ma idanuwanta suka kad'a suka kawo ruwa, mik'ewa tayi ta mik'ar da Jaleelahn itama sannan ta share mata hawayen fuskanta. Tsagaitar da kukan tayi for like two seconds sannan ta rungume ta tareda fashewa da sabon kuka. Mommy ma ta rungume ta tana patting d'inta a baya. Elder sis d'in Mommy ce ta shiga taga abinda ke faruwa, k'arisawa tayi wurinsu ta jawo hannun Jaleelah amma taqi jawuwa mata ta rik'e Mommy da k'arfi, da kyar aka samu suka rabu ita kuka Mommy ma kuka. Matan da suka zo guda ukun suka wuce da ita fuskarta rufe da hular Alkyabban. Gaba d'aya duhu ta koma gani, jinta kawai tayi a cikin motar. Mace daya na right side dinta daya kuma left side dinta, dayar kuma na front seat. Ita bata ma san ina za a kaita ba amma taga motar tabi Northward.
Jira take taga an shiga wata unguwa amma taga motar bata da niyyar sauka daga highway, a haka har ta gaji ta rufe idanunta kamar tana bacci, gaba daya abubuwan da ke faruwa ya kama ta ace nightmare ne ba reality ba. Sai da journey din yayi lasting 2½hrs sannan suka isa. Motarsu na parking mata suka furfito suna rangad'a gud'a ayyiriri. They're all strangers. Ko kad'an bata san akwai wa'inda suka biyo su ba sai da ta fito taji familiar voices, which she was sure Aunty Umma (elder sis din Mommy), dasu Aunty Murja (younger sis din Daddy) da kuma wasu. Wata mata ce ta rik'e mata hannu ta jagorance ta har cikin gidan mata suka mara musu baya, cikin wanni babban parlour suka shiga daga nan kuma suka shiga wani parlourn, a nan suka yi masauki a d'akin mahaifiyar mijinta. Kasa magana tayi ta nemi duk wani word dake bakinta taji ya gudu, "matso nan 'yata", taji matar ta fad'a, side din da taji muryar ta d'an matsa. Gaisawa suka yi cikin girma da arziki da 'yan uwan Jaleelah. Sai da sukayi sallar magrib suka ci abinci sannan suka yi sallama da matar a cewarsu sun kawo mata yarta ba sirika ba. Sosai tayi farinciki har bakin gate tayi musu rakiya sannan ta koma ciki wurin Jaleelah, ji take kamar ta dauke ta ta goya, ta jima tana rokon Allah ya nuna mata wannan ranan don har ta cire rai da ganinshi sai gashi Allah ya nufeta data ganshi.
A bathroom din dakin tayi alwala sirikarta da suke kira Umma ta bata hijab tayi sallah, a cikin sujadarta tayi ta addu'o'i da rokon Allah yasa auren nan ya zame mata alkhairi ya bata hakuri da juriya kuma ya bata zuriyya dayibba. A kan pray mat din ta cigaba da zama tana ta hawaye har Umma ta shigo tace mata ga abinci amma sam tak'i ci har akayi sallar isha.
9PM
Umma ta fito da ita zuwa parlour bayan ta feshe ta da turare, suna fitowa taji voices din maza na gaishe da Umma, alkyabbanta ta kara ja ya rufe mata fuska sosai ta fara sabon hawaye, "to D'an Alhaji, ga matarka nan amanar Allah ce a gareka, idan ka cutar da ita Allah zai saka mata, gata nan, ku je Allah yayi muku albarka", bata ji yace komai ba sai kama mata hannun ta yayi suka fita suna tafia a hankali, suna fitowa compound din mata suka sa musu guda har suka fita, front seat ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga driver's seat suka wuce. Har suka isa bata bar kuka ba shi kuma bai ce mata komai ba.
Tafiyar da suka yi bai fi na 5mins a mota ba suka isa. Da kanshi ya fita ya bude gate din sannan bayan sun shiga ya dawo ya rufe. Shi ya bude mata kofar ta fito, ba tareda yace mata komai ba ya fara tafiya ta bishi a baya har suka shiga cikin parlour, duk inda yabi nan take bi har ya shige bedroom, suna shiga ta wuce shi ta zauna akan gadon, karisawa yayi gabantanta ya dafa kanta "Allahumma inni as'aluka min khairi ha wa khari ma jabaltuha alaihi, wa a uzu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltuha alaihi", sama sama taji voice dinshi ta jira shi ya gama ya fita. Yana fita ta cire alkyabbar tayi saurin shigewa toilet don a matse take. Tana shiga taga arhan ruwa ta tsaya tayi wanka ba tareda ta sa ko sabulu ba bare shower gel. Ta mayar da kayanta ta fito ta fara bin d'akin da kallo, duk a tunaninta ma zata fito ta ganshi, ba laifi d'akin yayi mata kyau. Wardrobe ta bude ga mamakinta taga wasu kayanta a ciki, ko yaushe ma aka kwaso su oho. Nan ta nemi doguwar riga mara nauyi ta sauya, tana cikin sawa ya shigo d'akin, bata kai ga daga kai ta kalleshi ba tayi saurin juya mishi baya, dariya yayi yace mata "idan kin gama kiyi alwala, ina jiranki a dayan d'akin", yana fita tayi alwalar ta saka hijab ta je, tana shiga taganshi a zaune yana jiranta, ga mamankinta shima d'akin da akwai set din gado. Yana jin shigowarta ya mike ita ma ta tsaya daga baya suka gabatarda nafila raka'a biyu, sun jima suna addu'a bayan nan ne yayi mata pointing wata farar leda dake gefenshi yace "d'auki wannan", dauka tayi tayi wucewarta. Tana shiga dakin ta bude taga kaza ce sai babban kwalin hollandia. Kadan taci ta sha taje ta kuskure baki tayi addu'ar bacci ta haye gado.
A hankali yake shafa fuskarta yana kiran sunanta, squinting idanuwanta tayi tana miqa tareda amsawa, yace "ki tashi kiyi sallah", kamin ta sake wani kwakkwaran motsi ya fice zuwa masallaci, itama ta tashi taje ta yo alwala ta gabatar da nata sallar.
Har 7am tana zaune akan pray mat din tana azkar. Daga bisani ta tashi ta duba sabulu ta je tayi wanka ta fito ta shirya a cikin kayanta na cikin wardrobe riga da skirt na atamfa. Lekowa yayi yace mata ta fito su yi breakfast ya juya yadda ko fuskarsa ma bata gani ba. Kazar jiya ta bude taga ba abinda tayi ta zauna taci sosai ta sha hollandia din sannan ta goge bakinta don kar ma yasa rai zata iya cin abinci da shi. Mayafi ta dauka ta rufe jikinta sannan ta fita zuwa parlour, da sallama ta shiga kanta a duk'e kamar mara gaskia, ya amsa mata sannan ta karisa ta zauna daga nesa.
"Baki iya gaisuwa ba ko Jaleelah", bata fuska tayi ta dago da zummar yarfa mishi harara. Zaro idanunta tayi waje "uncle Abdu.......", ta kusa four seconds tana fadin sunansa surprisingly.
"Mene ne?" Ya tambaye ta. Mamaki ne rubuce a fuskarta tana so tayi magana amma ta kasa, murmushi yayi yace d'auki plate dinki gashi nan nayi serving dinki, idanuwa ta kashe shi da shi, yace "ya ishe ki haka. Zo ki dauki abinci", girgiza kanta tayi ta fara hawaye, "why you?"
Yace "idan kika ci abinci zan fada miki amma idan baki ci ba shikenan",
"A ina ka samo abincin?"
"Umman mu ta aiko izuddeen da shi"
Matsawa tayi ta dauki plate din ta fara ci a hankali kamar ba zata ci ba, plantain chips ne da irish, kadan tashi ta barshi yace dole sai ta cinye, kasa ci tayi tace mishi ta ci kazar jiya da daddare.
"Pls tell me.. I'm so flabbergasted, how comes? Kaine Daddy yace zai aura min?"
Nodding kanshi yayi alamar a'a, "to mesa ka yarda ka auri Mara mutunci?"
Ji yayi kamar ya mare ta, "are you insane? Idan kika sake fadin haka sai na bige miki baki", turo mishi baki tayi yace "mijinki kike turawa baki? Haka nace miki a text dina?" Rufe fuskarta tayi da hannayenta saboda kunya.
"But let's talk serious, ya akayi ka zama mijina?"
Nan ya bata labarin yadda suka yi da babanta bai boye mata komai ba har ya zo ya daina d'aukarta a hanya bayan tayi rashin lafia, shi kuma yana jin tausayinta sosai shine ya TAIMAKE ta ya aure ta. Numfasawa tayi tace "thanks a lot, haqiqa ka taimake ni, if not ban san wanda Daddy zai aura min, duk da nasan barazana ce dai kawai somehow"
Tana ida zancenta wayarsa ta fara ringing, dauka yayi ya duba yaga Raheemah ce ta kirashi har sai da gabanshi ya fadi, jiran call din yayi yayi disconnecting sannan ya kira ta, "my love" ta fara furtawa, ya amsa mata da na'am, tace "my love ka manta dani, three days baka kira ni ba haba, ko nayi laifi ne?" Dariya yayi yace "a'a wlhy commitments ne",
"Ba wani commitments, da ko me kake yi sai ka kira ni morethan once a day, ko dai dagaske ne mafarkin da nayi wai kace ka fasa aure na?"
Slight hiss ya saki yace "wannan ba gaskiya bane, you are mine, auren mu na nan"
Sam yama manta da Jaleelah a wurin, ita kuwa zuba mishi idanu tayi tana kallon ikon Allah, wani abu taji ya tsaya mata a wuya, ko ba a fada mata ba tasan kishi take yi, wani side din zuciyarta yace mata "cool down babe, taimakon ki yayi", tsaki tayi a fili sannan tace "I'm stupid" cire wayar yayi daga kunninshi yace "lafia?" Da sauri ta girgiza kai tana murmushi tace "lafia lau"
Mayar da wayar kunninshi yayi ya cigaba da hirarshi ba tareda ya sake ko kallon inda take, sai da ta bukaci kiran Mommy sannan ta tuna wayarta na Kaduna, tsaki ta sake yi Wanda yayi dai dai da gama wayarshi ya sake tambayarta "wai lafia?"
Tace "ina so zan kira Mommy ne kuma na bar wayata a gida", mika mata nashi yayi yace ta kirata da yake ta haddacen number din, hira suka yi da Mommy inda tayi mata nasiha akan tabi mijinta ta kuma girmama mishi yan uwa sannan tayi magana da Hadiyya da Afdal da Yaseen. Tana gamawa ta miqa mishi wayar sannan tace "wai ba kowa ne a gidan?" Yace "ba gani ba, mene ne?"
"Gaishe su zanje nayi", dariya yayi yace "mu kadai ne mana"
"Oh oh. Ba a Yarwa close kake da gida ba?"
Yace "eh wancan ni na gina wannan kuma Abbanmu yake ginawa kowa, kowa na da gidanshi"
Tashi tayi tace mishi bari taga irin gidan. Ga mamakinta parlour biyu ne, jiya bata tsaya ta duba da kyau ba. Kana shigowa main parlour zaka ga Dinning hall wanda zai shigar da kai kitchen, sannan akwai hall way da zai bi da kai cikin dayar parlour din mai dauke da three bedrooms guda biyu na kallon juna sai data daga gefe, sai kitchen ta store, ta kitchen din zaka dinning hall again ka isa parlour.
Dawowa tayi ta zauna tace "gidan yayi kyau"
Yace "sosai?"
Tace "eh"
Yace "sample daya ne da gidana, sai dai shi wancan akwai BQ"
Shiru tayi kamar me nazari sannan tace "to meyasa ba zan zauna a kd ba?"
Yace "Umma ce tace in kawo mata yarinyarta kusa da ita"
Murmushi tayi tace "da ta bari idan na gama schl muka yi waec & neco sai na dawo nan kusa da ita, idan ma kana Kd sai na koma gidan ta, koma kana nan sai na koma can"
Yace "to ki bari idan muka je can sai ki fada mata"
Bata amsa mishi ba tayi shiru tana kallonshi sai shafa wayarshi yake yi yana murmushi, a ranta ta ayyana da Raheemah yake chatting, haushi taji amma nan da nan ta tuna taimakonta yayi, kuma tun kamin ya aureta ta san suna soyayya, Allah yasa gidanshi ma biyu ne, ita zata koma Kaduna garinsu ita kuma Raheemar ta zauna a nan Rijiyar Zakin kusa da iyayenta, but koma mene ne ai yanzu AbdulHakam mijinta ne, MIJIN JALEELAH ne ba mijin Raheemah ba.
*Need your prayers I'll be sitting for exams on Saturday.. So I won't be able to post again till on Monday Insha Allah. Yours ever loyal, Shatouh*
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
22
By Linah Shams✍🏼
Washe gari da safe bayan sun kammala breakfast din da Umma ta aiko musu da shi suka zauna zamanan hira. Shi surutu ita surutu, da an had'u da an dace. Wuraren 10AM ya tashi yace mata zaije yayi wanka, to kawai tace mishi, wayarshi ya bata ya fad'a mata password din *AirFOrce* yace ta cire ta buga games amma banda leqen asiri. Jiki na rawa ta amsa dama an kwana biyu ba a had'u ba. Har kusan 1hr bai fito ba ita kuma ta fara gajiya da buga games din. Lek'en asirin daya hanata shi taje yi, messages ta shiga taga irin texts din da yake turawa Raheemah da wa'inda take turowa. Tiryan tiryan take karantawa har sai da ranta ya fara b'aci, hakan kuma bai hanata cigaba da karantawa ba har sai da ta kammala, tsaki tayi sannan ta sake assuring kanta cewa taimakonta yayi ya aure ta ba a son ranshi ba, kuma tasan Raheemah bata san yayi aure ba. Tana cikin wannan tunanin ne call din Raheemar ya shigo, da sauri ta tashi ta nufi bedroom don kai mishi, ai kuwa tana shiga tayi kicib'is dashi yana sa kaya, da gudu ta juya ta fita duk da ba abinda ta gani ta koma parlour ta zauna. Ko cikakken minti d'aya bata had'a ba taji ana knocking, mamaki ne ya kamata, ko waye? Ta tambayi kanta, may be Inteesar ce, autarsu AbdulHakam.
Tana bud'e kofar taga akasin abinda take tunani. Aunty Umma ce, da Aunty Rabi, da Aunty Sadiya da Hadiyya hannun ko wanne dauke da kaya. Farinciki ne ya kamata ta rungume Hadiyya sannan tayi ushering dinsu zuwa inner sitting room, lokacin yayi daidai da fitowar AbdulHakam cikin English wears, cikin fara'a da girmamawa ya gaishe su sannan ya fita. Ruwa taje ta d'ebo musu daga fridge ta zubo a tray ta aje musu, saboda farinciki ji take kamar ta goya su a baya. Bayan sun d'an huta ne suka fita suka shigo da sauran kayan da suka zo mata da shi da ke mota (hilux) da suka zo a ciki. Lefenta da sauran suturunta da kuma wasu kitchen utensils.
"Aunty Umma me zan dafa muku?" ta tambayeta baki a washe, Hadiyya tace "dambun shinkafa", hararta tayi sannan tace "me kuke so Aunty?", tace "ke bar girkin nan kinji, nan da 30mins zamu wuce ba zama zamu yi ba"
"Yauwa Jaleelah, gara da Allah yasa na tuna, ga wayarki inji Mommy", ta saka hannu a jaka ta fiddo mata da wayar, amsa tayi tareda yi mata godia, dama tana ta so ta kira Mrs Kiyawa tayi mata ban gajiya. Kamin thirty minutes din kuwa ya k'are Raheemah tayiwa Abdul 5missed calls Wanda duk a idanuwan Jaleelah suke shigowa. Sai da taje yi musu rakiya sannan ta je kai mishi wayan bayan shima yayiwa su Auntyn sai anjima. Yana zaune karkashin bukkan dake gaban gidan, mik'a masa tayi tace "gashi ana ta kiranka", amsa yayi yana saka password din yace "wa?" Kamin ta bashi amsa har yayi unlocking. Kiran Raheemah ne reras, a tsanake ya kalle ta yace "meya sa baki kawo min ba kina gani a na kirana?"
"Ai kaga ina tareda su Aunty shi yasa"
"How long will it take you to come out?" ya fada cikin fad'a fad'a
Marairaicewa tayi tace "uncle Abdu ai ban san kana nan ba", tsaki yayi mata ya mi'ke ya nufi parking lot wurin motarsa ya bud'e ya shiga, ba k'aramin b'aci ranta yayi ba har sai da idanuwanta suka kawo ruwa, da gudu ta wuce ciki bata zame ko ina ba sai cikin toilet, jinginawa tayi da bango tana kuka shi kuwa bai ma san tana yi ba, tuni yasa kai ya bar gidan ya wuce gidan Umma.
Bayan sun gaisa Umma ta tambayeshi "ina d'iyata?" Yace "tana gida lafiyanta k'alau", tace "shine baku zo tare ba ka barta ita daya a cikin gidan?", shafa kanshi yayi yace "Ai bata san nan na zo ba", tace "d'an Alhaji? Matar taka haka kawai sai ka tsallake ta kasa kai ka fita baka fada mata inda zaka ba?"
Dariya yayi yace "haba Umma bafa nice matar ba"
Tace "amma dai baka kyauta mata ba"
Yace "idan na fad'a mata zata ce ne sai ta biyo ni kuma dududu kwana nawa ne da auren?"
Tace "yo ina ruwan wani daku?", yace "ki bari idan zan tafi nan gidan zata dawo ai"
Murmushi tayi tace "to shikenan ai", hira suka yi sosai daga bisani ya fita zuwa gidan Gwaggonshi. Sai da yayi sallar isha ya dawo gidan. A inner sitting room d'insu ya tadda dinner Umma ta aiko dashi, da alama ko ci bata yi ba. Bedroom ya nufa ya bude da sallamarsa ya shiga, a takure a jango ta a karshen gado tana kwance ta rufe ilahirin jikinta da duvet. Da sauri ya karisa ya zauna daga gefe yace "baki da lafiya ne?", girgiza masa kai tayi alamar a'a, yace "then what happened to your eyes?", nan ma ta girgiza masa kai alamar a'a, yace "bana son gesture, you either talk or remain still" with a serious note in his tone, sannan ya sake cewa "baki da lafiya ne?" Kasa magana tayi bata san sanda ta sake yin nodding ba, cikin fada yace mata "what the hell is wrong with you?". Fashewa tayi da kuka ranta na k'ara b'aci, ashe tsugunni bata k'are ba, "keep shut or I slap you". Had'iye kukan tayi sai dai hawaye basu daina fitowa daga idanunta ba, "see.. Let me warn you, kin ga..." Bai kammala magana wayarsa ta ta fara ringing wanda ya tabbatar mishi da kiran Raheemah ne, gyara zama yayi ya amsa call din suka fara magana, sai lallamarta yake akan rashin kiranta da yake yi ya kuma yi mata alkawarin canzawa, Jaleelah nata kallon yadda yakewa Raheemar magana da sanyin murya amma ita yazo yana tada mata da jijiyar wuya. Tunowa tayi da cewa taimakonta yayi don haka idan yayi making call da woman of his dreams ai baiyi laifi ba. Had'a kanta tayi da gwiwa ta fara kuka soulfully, shi kuwa ko lura da ita ma baiyi ba har ya gama sannan ya tuna da ita, kallonta yayi tareda tab'e baki yace "have you eaten?"
Sam ta manta da warning din daya bata ta sake nodding, tsawa da daka mata wanda yasa tayi saurin dagogowa a firgice, sannan yace "na lura you are starting to disrespect me, may be it is because we slept in the same room last night, daga yau ai ba za a sake ba, dama TAIMAKON ki nayi", sake fashewa da kuka tayi ranta na dad'a k'una, a ranta tace "so this is who AbdulHakam is...", kukanta ta cigaba da yi tana shesshek'a, sai lokacin ya fara jin rashin dad'in tsawan da yayi mata, yace "move out and eat", tace "na koshi", yace "me kika ci?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "tashi ki je ki ci abinci nace", sake cewa tayi na koshi, bai tsaya bata amsa ba ya mik'e ya kama hanyar fita yace "ina jiranki, and don't let me come and meet you here", yana fita ta d'auki hijabinta ta Ciro sabon flat shoe ta saka ta fita, kallon ya tsaya yi da mamaki kamin yace "zo nan ki zauna", ba musu taje ta zauna a kasa kusa da shi, yace "ina zaki", fuskarta a murtuke tace "gidan Umma", dariya taso ta bashi, yace "da wannan daren? Kin san hanya ne? To me ma zaki je yi in the first place?", sunkuyar da kanta tayi sannan tace "a can zan kwana",
"What happened to your room?"
"I'm scared I can't sleep alone"
"Eat and I'll sleep with you"
Kawar da kai gefe tayi tace "a'a ni nafi son gidan Ummu, sai na kwana da Inteesar, d'azu ma da ta kawo min abinci kamar zan bita"
D'aga mata gira yayi yace "oh really? Da na karya miki kafafu kuwa, ba inda zaki, dauko place ki dibi abinci", tashi tayi ta nufi hanyar bedroom ya dakatar da ita "yanzu kuma idan nayi miki fada kiji haushi na ko? Abinci nace ki zo ki ci but look at what you are doing, a bedroom ne ake dauko plate?". Dole yasa ta dawo ta zauna taci abincin amma kad'an ta tashi ta koma bedroom.
Sai after eleven ya shiga d'akin kuma har lokacin bata yi bacci ba amma tana da shirin yi. Canjawa yayi zuwa nightie sannan ya hau gadon rike da wayarshi a hannu yana chatting, ya sami wuri ya kwanta bai ko kalle ta ita kuwa sai binsa take dana mujiya duk da cewa d'akin was dim lit. Murmushi kawai yake yi hakan kuma baya buqatar dogon jawabi a wurinta, a duk lokacinda taga yana haka sai taji wani haushi ya kamata, dole ta juya masa baya ta ja bargo tayi addua.
Har sukayi kwana shida da aure kullum sai tayi mishi mitar ya kaita gidan Umma amma yace bazai kaita ba. Duk da yanzu basu hira kuma ya daina bata wayarshi, da tana so ya sa mata kati tayi making phone calls amma yanzu tasan ba wannan maganar, duk da bai san an kawo mata wayar ba. Sai a rana na bakwai ya kaita gidan Umma harda kayan kwananta, saboda washe gari zai koma Kaduna don haka zata koma gidan Umma ko Inteesar ta dawo gidanta, ita kuma tace tafi son zama da Umma.
Bayan sallar magrib suna zaune suna hira su uku, Umma da Inteesar da Jaleelah Inteesar tace "Jaleelah ya labarin WAEC dinki? A Kaduna zakiyi ko zaki so schl din mu muyi tare ne?"
Sai lokacin taji kewar Ni'ima, tace "a'a a Kaduna zanyi"
Umma tace "can kika fi so?"
Bata bata lokaci ba tace "eh, Umma dama ya tafi dani muje idan anyi Hutu sai na dawo, nafi so na yi exams a makarantan mu"
Ita dai Umma tana matuqar sonta, har cikin ranta take jinta tamkar yar data haifa, tace "to"
Tace "amma Umma dan Allah ki roke shi idan ya shigo", ta sake amsa mata da "to", hiransu suka cigaba itada Inteesar suna dariya.
Bayan sallan insha kuwa sai ga Abdul ya zo. Murna wurin Jaleelah baya boyuwa, zata koma Kd taga Ni'imah da Mrs Kiyawa. Dakin Inteesar suka koma tana jiyo muryar Umma na maganar komawarta.
"Umma nifa da sassafe zan wuce shiyasa ma na dawo da ita nan, kuma sai yau ne zata ce Kaduna take so?"
Umma tace "idan suka yi hutu ai zata dawo ko"
Yace "ta zauna a nan kawai taje makarantar su Inteesar ta rubuta exams din idan lokaci yayi", Umma tace "to karatun nata fa? Ko so kake ta k'unshe a gida?"
Yace "zan sata a wani ko ta je makarantar su Inteesar"
Tace "to ban ce ba, ka tattara ka wuce da ita can tace min tafi so", girgiza kai yyi yace "wato shiyasa ta nace sai ta zo gidanki", tace "eh ko gidan uwarka ta zo?", dariya yayi yace "to ai sai ta zo mu wuce ta kwashi abinda zata buqata"
Duk a kunninta suke magana ita da Inteesar, wani tsalle ta daka tareda rungume Inteesar. Muryar Umma taji tana kwala mata kira tayi hanzarin fita. Basu kara 10mins a gidan ba suka yiwa Umma sallama suka tafi, har bakin gate suka yi musu rakiya ita da Inteesar.
Har suka kai gida bai ce mata ko uffan ba haka itama. Suna isa ta fita daga motar tayi wucewarta, amma sai da ta sha tsayuwa a balcony tana jiran shi ya zo ya bud'e kofar.
Trolley din da aka kawo mata kayanta ta dauko ta zuba kayan a ciki, harda English wears din da take bacci da su yan k'anana. Majority din kayan na lefe ne wa'inda aka kawo a dinke.
Washe gari da sassafe suka fito, ko 7AM bata had'u ba lokacin. Banda ina kwana ba abinda ta sake ce mishi haka shima bayan lafiya k'alau bai sake magana ba. Gani tayi sun d'auki hanyar fita daga unguwar tace "ba za mu gidan Umma ba?"
Bai kalleta ba yace "sauka ki tafi", sam bata jin dadin abubuwan da yake mata, ko be aureta ba at least they were friends before, cikin low tone of her voice tace "uncle Abdu..", yace "what is it?", sighing tayi tace "I'm sorry"
"For?" Ya tambayeta
Tace "for getting married to you", abinda ka da mai saurin kuka tuni ta fara hawaye, kasa magana yayi sai daga baya yace "meaning?",cikin muryar tausayi tace "naga kamar na takurawa rayuwarka ne, nasan kuma bada son ranka ka aure ni ba. Kawai ka mayar dani gidan mu"
Twitching brows dinsa yayi yace "ni na fad'a miki kina takura min?", tace "amma ai ba sai ka fad'a ba"
"Meya sa kika ce haka?"
"Kullum sai kamin fad'a on a slightest mistake"
He felt remorse saboda yasan duk abubuwan da yake mata, yace "yanzu don nayi scolding d'inki laifi ne? Remember ni mijinki ne yanzu"
Shiru tayi mishi bata ce komai ba. Yace "to I'm sorry, shikenan?"
Murmushi tayi har tayi nodding tayi sauri tace "eh", jingina kanta tayi da jikin kujera tana ta kallon hanya, bata taba zuwa Kano ba ko sau daya kuma bata da kowa a can.
Sunanta taji ana kira sama sama sai cewa take uhum, uhum, yace "ki tashi we're home", a hankali ta bude idanuwanta ta kalla taga eh dagaske ne, bude kofar tayi ta fita shima ya fito, ya zagaya ya bud'e boot din motar ya fiddo mata da trolley dinta. Tare suka jera yana janye da trolley din har suka isa ya bude musu suka shiga, it looks exactly like the other house, hatta paint din, sai dai wannan ba komai a main parlour din sai rug da couch, karisawa suka yi ciki, nan ma ba komai sai rug da couch amma da kwai kayan kallo. Bedroom din ne kawai akwai set din gado kamar akwai mace.
Sai da suka huta sannan yaje kitchen da kanshi ya dafa musu indomie. A plate d'aya suka ci sannan yake ta janta da hira don wanke kanshi. Da daddare ma indomie din suka k'ara ci sab'a'nin ra'ayinta. Da cewa tayi sai dai ya koma the next day ya kwaso musu gaaran da aka kai mata da sauran snacks, wanda ta debo ba yawa sosai yace ba zai koma Kano ba sai weekend, kuma ko ya je snacks din zai dauko mata bazai dauko mata ko maggi ba.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
23
By Linah Shams✍🏼
Ranan Monday da wuri ta tashi tayi shirin zuwa schl saboda d'oki, ko breakfast ta kasa yi sai da ya mata dole. Kayan tea da indomie ne kad'ai a gidan ita kuma tace ba zata iya cin indomie again ba, tea kawai ta sha. Da mufti zata schl saboda uniform dinta da schl bag da stockings duk suna gidan su. Bayan sun gama breakfast ta tashi ta dauki mayafinta d'an figigi ta yafa tace "uncle abdu na shirya", daga sama har k'asa ya kalleta yace "ina zaki a haka?", kallon kanta ta tsaya yi sannan tace "mene ne?", yace "je ki dauko hijab ko ki zauna a gida", da sauri taje ta dauko ta fito dauke da side bag. Sai da suka tsaya a wani shagon dake layinsu ya siya mata notebooks guda biyar yace tayi amfani dasu idan an tashi tabi Hadiyya su je gida, idan ya tashi daga aiki zai biya ya d'auko ta. Saboda tsabar farinciki yau zata je gidansu bata san sanda ta rungume shi ba tace "thank you", janye ta yayi daga jikinshi yace "let's get moving", mota suka shiga suka wuce zuwa schl din. A tare suka fito suka shiga schl din, direct office din principal suka wuce dake upstairs. Cikin girmamawa suka gaisa da principal din sannan yace "I'm sorry sir she came in mufti"
Principal din yace "yes I see"
Abdul yace "yes we came back from a travel, and also, that's why she hasn't been coming last week, unfortunately we forgot her uniform and school bag so she will be coming in mufti before we get the uniform may be today or tomorrow insha Allah", principal din bai ko tambayi garin yaya za a yi tafiya da uniform ba yace "no problem sir", Abdul yace "thank you", ya amsa masa da "welcome", hannu suka yi sannan suka fita tareda Jaleelah, kamin su k'arisa wurin class dinsu ya ja ya tsaya, yace "saura ki dinga wasa kar kiyi karatu", dariya tayi tace "to uncle", dari biyar ya ciro ya mika mata break money, godiya tayi mishi tareda yi mishi bye bye hug wanda ya faru akan idanuwan IRS teacher dinsu. Da fara'arta ta shiga class kowa ya bita da idanu kamar basu taba ganinta ba, kusa da Ni'imah ta zauna suka yi musabaha cikin fara'a, tace "meyasa baki zo schl ba last week, kinyi missing classes", tace "eh munyi tafiya ne, munje Kano wurin Umma"
Tace "wacece Umma?"
Tace "sistern mommy ce"
Kadan kadan suke magana saboda an hana su Hausa su kuma sun nace sai da hausa zasu yi magana a haka har akayi ringing assembly suka wuce downstairs.
English ne first period dinsu, Jaleelah duk ta kosa Aunty Maryam ta zo, tun daga cikin class ta jiyo muryarta tana koron students zuwa classes dinsu, da sauri ta fito ta zo ta rungume ta dukansu with toothy grin. Aunty Maryam ta rike hannunta tace "Mrs"
Dariya tayi tace "good morning", ta amsa mata tace "how comes kika dawo kuma?", tace "eh na rok'a ne, idan aka yi hutu sai in koma can", ita bata ma san inda aka kaita ba, tace "ina zaki koma?", tace "Kano mana"
"Oh, can aka kaiki ko?"
Ta girgiza mata kai alamar eh sannan tace kinga kuwa ban san yau zaki zo ba dana kawo miki sak'on, tilaren wuta ne dama da humra da pure honey sai wasu abubuwa. Nan maths teacher d'insu ya zo wucewa sai da ya tsaya ya tofa albarkacin bakinshi, Aunty Maryam tace "let's get into the class kamin baki ya cinye mu, we'll talk after the class is over"
Bayan sun gama karatu suka sake fitowa waje tare, shawarwarin zamantakewar aure Aunty Maryam tayi ta bata amma duk ta bayan kunni suke wucewa saboda ita ba abinda yake had'a ta da shi. They just live like a brother and sister. Zasu yi hira, su ci abinci tare su kwana a d'aki d'aya amma ba mu'amular auratayya, don ko hannunta bai tab'a rik'ewa ba purposely saboda wani nufi. Bayan tayi ta gama Jaleelah tayi mata godia sannan ta tambaye ta ko wa ta aura, saboda taga kamar duk damuwarta ta kau, nan ta fad'a mata ko wanene and fortunately ma ta had'u dashi a downstairs zai fita, sosai tayi mata murna sannan ta wuce ita kuma ta koma class.
Bayan an tashi schl ta tsaya a bakin gate tana ta jiran Hadiyya, sai da ta dad'e sannan ta fito tana tafiya a gajiye, tana hango Jaleelah ta k'arisa da sassarfa had'e da yak'e, "Hajiya Matan aure" ta tsokaneta, tsuke fuska tayi tace "zan ci miki mutunci wlhy, ni tukunna ma, hope baki fada ma kowa I'm married ba", tace "eh", sannan ta k'ara da cewa "garin yaya kika dawo kuma?", tace "Umma na roka tayi mishi magana shine ya yarda na dawo nan amma idan aka yi hutu zan koma"
"Yanzu zaki koma gidanki kenan"
Tace "a'a, cewa yayi inje gida idan ya dawo zai zo ya dauke ni, zan dauko uniforms dina ne da schl bag", suna cikin magana driver ya iso ya dauke su.
Mommy har rungumeta tayi saboda farincikin ganinta. Tayi missing gida sosai.
Sai after six sannan Abdul yaje dauko ta, ta so ace taga Daddy amma bai dawo ba, hakanan tabi mijinta suka tafi bayan ya shigo ya gaida Mommy. A hanya suka tsaya ya siya mata sweets da chocolates masu tarin yawa kamar wata k'aramar yarinya. A bedside drawer ya zuba yace amma kar ta ci komai a ciki har sai ta tambayeshi idan ba haka ba cikin ta yayi mata ciwo to babu ruwanshi. Kallonshi tayi sannan tayi kwafa, wai ma sai ta jira shi sannan zata ci sweets din.
The next day ma shi ya kaita makarantar, da aka tashi ya koma ya dauke ta daga can suka wuce kasuwa suka siyo food stuffs.Washe gari da safe da wuri ta tashi don tana so ta tafi da abinci schl, abubuwan dake schl shop basu k'osar da ita ga tsada ga kuma rashin dadi. Coated yam with egg ta hada musu for breakfast da coffee. Sannan tayi plaintain chips da scrambled egg Wanda zata tafi dashi schl, ba karamin bata lokaci tayi ba wurin soya doyan hakan yasa tayi latti, har past 7AM tana cikin kitchen ko wanka bata yi ba. Tsayawa yayi a bakin kofar kitchen din yana kallonta tana juye plaintain chips din a food flask in a fluffy short nightie dinta wanda iyakarsa gwiwa sai woolen cap data saka, yace "wai ke me kike yi har yanzu?", hankalinta kacokan na kan abinda take yi tace "na kusa gamawa"
"Oh baki ma gama ba? Wallahi zan tafi in barki"
Da sauri ta dago ta kalleshi tace "to ga breakfast din ka nan akan dinning table ka rufe min flask din bari naje nayi wanka", bata saurari me zai ce ba ta wuce shi da gudu zuwa yin wankan. Da hanzari ya sake mata breakfast din gudun bata lokaci sannan ya koma dinning table din ya dauko breakfast din ya dawo inner sitting room ya zauna ya fara ci, a hankali yake sipping tea din data had'a mishi, "kamar na sata?" Ya fada a zuciyarshi while yana enjoying, da sauri ta fito tana buttoning sleeve din rigarta, ajiye mug din hannunsa yayi a kasa yace "Jaleelah me kika yi?", dariya tayi mishi harda kashe ido, shima dariyar yayi tace "wanka!", yace "kin dai yi b'arna da ruwa, kina dawo daga schl kiyi sauri ki sake wanka", dariya tayi sannan ta zauna a gefenshi tana saka socks, yace "kinyi breakfast ne?", kanta a durqushe tace "a'a munyi latti, five minutes to 7:30AM kaga idan na tsaya breakfast zamu dade, kuma idan na kai 8AM ba za a barni na shiga schl ba"
Shiru yayi yana ta kallonta tana shiri, ta mik'e ta kwaso sandals dinta ta saka sannan tace mishi "ina flask dina?"
Yace "yana kitchen"
Tace "baka dauko min ba?", hararta yayi sannan ya mike ya nufi kitchen din ya fito da flask din, yace "kiyi sauri ki ci abinci zan jira ki a waje", da sauri tace "to ga schl bag dina ka wuce min dashi", da saurinta ta ufafa bedroom ta fito dashi ta bashi yabi ta dinning hall ya fita.
Akan dinning ta ci abincin, cuccusawa kawai take yi sbd bata so tayi latti, hakan kuma bai hanata zuwa ta debo sweets ba ta dunqule su a left hand dinta, ko five minutes ba ayi ba ta fita ta rufe d'akin.
Tsaye yake a jikin motarshi yayi folding arms dinsa, kallonta ya dinga yi har ta gama rufe kofar ta fara tafiya cikin sauri, uniform din sosai yake kara mata kyau, milk shirt and hijab wanda ko waist dinta bai kawo ba sai coffee skirt. Socks dinta da sandals dinta duka baqaqe da headscarf dinta. Mika masa keys din tayi tace "gashi"
Ya sake cewa "Jaleelah me kika yi?"
Tace "breakfast"
Girgiza kai yayi yace "kinyi kokari, mu tafi"
Kamin ya zagaya ya shiga tayi sauri ta shiga ta zuba sweets din cikin schl bag, yana Shiga motar tana gamawa gaba daya daka ganta kasan akwai wani magana, murmushin yak'e tayi mishi yace "mene ne?"
Kamar tana jira tace "kasan mene ne?"
Ya amsa mata da a'a, tace "yau idan ka zo dauka na zan nuna maka Aunty Maryam, ita kadai tasan ina da aure a schl din mu, ko besty na ma bata sani ba"
Yace "yau bazan zo daukan ki ba da kanki zaki koma"
Tace "saboda me?"
Kallonta yayi with mouth agape, yace "na miki alkawari ne?"
Fuskan tausayi tayi bata amsa shi ba, dariya yayi yace "my Jaleelah! Seriously bazan zo ba yau sai da ki nuna min ita yanzu, zan jiraki a bakin schl gate ki shiga ki kira ta"
Shiru tayi mishi alaman tayi fushi, itama kanta bata san meyasa tayi fushi ba, yace "to fridays zan dunga zuwa daukanki, kinga five nake tashi to yaushe na zo nan tun daga airforce? Kema kin san da nisa", sai sannan ta saki ranta tace "to. idan na koma gida sweets nawa zan ci?"
"Ban ce kici ko daya ba, firstly, when is your period?" Kunya taji kamar ta nutse, ya sake maimaita mata tambayar, cupping palms dinta tayi ta yi burying fuskarta sannan tace "on 16th ko 17th", yace "in eight or nine days time kenan, ki bari sai kin gama kici, if not ciwon ciki yayi miki yawa babu ruwa na", dariya tayi a ranta tace "dama wa yace maka da ruwanka?".
7:45AM suka isa schl din lokacin an fara tare late comers, Abdul ya dube ta yace "acici dauki abincinki ki tafi, kiyi sauri ki kira ta idan ba haka ba zan wuce"
Tace "baka gani ana tsare latti"
Yace "eh bana gani, kin san ni makaho ne"
Turo mishi baki tayi ta kawar da kanta gefe. Nan ya bude motarsa ya fita hankalin kowa ya karkato izuwa gareshi. Khakinsa duk ya dauki hankalinsu saboda tsabar kyawun da yayi mishi, musabaha ya isa sukayi da teacher on duty wanda ke tsaye a bakin gate din, waigawa yayi bayanshi ya ga wayam bata biyo shi, kadan ranshi ya baci ya juwa zuwa mota da niyyar balbaleta da fada sai ta tuntsire da dariya, tsaki yayi yace "ki fito ko inyi knocking dinki", tana dariya ta fito suka isa wurin malamin ya bashi hakuri akan zuwanta latti aka daga mata kafa, sannan yace tayi sauri ta kira Maryam din ko ya wuce. Staffroom taje ta kirata suka dawo tare, cikin girma da mutunci suka gaisa, Aunty Maryam tace "to Allah ya bada zaman lafia" ya amsa mata da amin sannaan ya kara da cewa "cewa tayi wai na tsaya na ganki yau", cikin fara'a tace "ayya", ya mayar da dubansa ga Jaleelah yace "ki shiga schl mana", lips dinta tayi twitching tace "to baka bani kudin break ba", yace "banda abincin da kika dafa? Ga dai fifty naira nan ki siya ruwa" ya fada tareda ciro wallet dinsa, tace "to kudin dawowa fa?", #250 ya dunqula ya bata yace "daga nan zuwa gida #200 ne drop, kar ki fara ki hau bike na fada miki, kuma keke napep drop zaki dauka, ga keys din nan" ta amsa mishi da "to, yau ba zaka min bye bye ba?" Yace "Jaleelah!...." Bai kai ga ida maganarshi ba tayi hugging dinsa sosai sannan ta sake shi tana dariya and bade him bye, tsintar kansa yayi yana murmushi tareda yi mata bye bye sannan ya mayar da dubanshi ga Aunty Maryam da itama take murmushin, yace "Mrs right?" Tace "yes", yace "dan Allah ki dinga duba min yarinyar nan, ki dan dinga mata fada let her not get involved in a case da zai sa ayi punishing dinta, kinga matar aurece ita tace min kuma ba wanda ya sani sai ke", tace "insha Allah zanyi iyakar iyawa ta" godiya yayi mata suka yi sallama ta shige schl shi kuma ya wuce wurin aikinshi.
Tana Shiga class dinsu idanuwa suka yi mata maraba da zuwa, mamaki ne bayyane karara a fuskanta ta wuce seat dinsu, hatta malamar kallonta take yi kamar anyi maganarta, cikin k'asa k'asa da murya Ni'imah tace "what have you turned to?", tab'e fuska tayi ta dube ta idanuwanta cike da raini tace "me ke nan?", Ni'imah tace "'yar iska ji wani kallo", tace "to me na zama? Look at how you guys are looking me, am I a zombie?" Ta rufe maganarta da tsaki, Ni'imah tace "kefa banza ce kar kimin hayagaga, don na san mutuncinki ragagge ne", malamar ta katse su ta hanayar kiran sunan Jaleelah, "get up", ba musu ta mike ajin yayi tsit kowa na kallonta, IRS teacher din tasu tace "what's wrong with you?", furrowing brows dinta tayi tareda girgiza kanta tace "excuse me ma, as in.... I didn't get you"
"I never know you are such a shameless girl, why should you be hugging your non-mahrem? Don't you know it is sinful and it can lead to fornication? And you shamelessly do it even on streets, what's even the relationship between you and that airforce?.. Ehm ehm that military man", ranta ne ya baci hatta idanuwanta sai da suka yi ja, cikin fushi tace mata "and how does it affect you? Are you told that I'm a ignorant or I'm a whore? I hugged him and I will do it again? What's your own business with that? Your business is to teach AMMS students not to put an eye on anybody's personal affairs. And if you also want to sermonize to me, is this how you were taught to do it? In public? You are supposed to be a private adviser not a public tribunal" taja dogon tsaki sannan ta zauna, kallo sai ya koma sama wai shaho ya d'aga giwa. Ran Miss Aneesah yafi na Jaleelah baci duba da yadda ta dinga lallasa mata magana, kasa ce mata komai tayi tace mata ta fito tayi kneel down, ita kuma tace Allah ya kashe ba zata yi ba, direct Miss Aneesah ta wuce office din principal kai report saboda tana ganin Jaleelah na ganin girmansu d'aya kuma bata girmeta da abun arziki bane yasa tayi mata rashin kunya. Tana fita aji ya kaure da surutu wasu na ta burge su wasu na bata da kunya, jin kowa kawai take yi amma tafi so mutum ya tare ta yace bata da kunyar. Dama sanadiyyar auren da aka ce za a mata ne yasa tayi sanyi, Ni'imah tace mata "Anjayjay wai what's wrong with you? Haka a SS1 kika yiwa Mrs Kiyawa, a SS2 kika yiwa Mr Charles yanzu kuma Miss Aneesah", tace "haba Ni'imah! Meyasa zaki ga laifi na? Ita meyasa ba zata kirani waje tayi min magana ba?", tace "ai Atika Mukhtar ce da Sadiya Bello suka shigo suna maganar shine aka fara hiran sai ga ki kin shigo", saboda b'acin rai hawaye ya fara fita daga idanuwanta sai ga Mrs Kiyawa ta zo kiranta, sai da suka fita waje sannan ta tambayeta abinda ya hada su. Bata boye mata komai ba ta fada mata, "you shouldn't have shouted at her, yanzu muje PC na kiranki, zaki bada number ko Mom dinki ne wai na babanki baya shiga", tace "na MIJI NA zan bada"
"Okay let's go"
Bayan PC ya saurari both parties tareda kwararan shaidu ya dokawa numban Abdul kira Wanda Jaleelah ta bashi a matsayin numban uncle dinta, ya shaida masa makaranta nason ganinsa. Ko 20mins bai dauka ba ya isa schl. Ran Mrs Kiyawa ko kadan baiyi dadi ba, ba yadda bata yi dasu ba akan suyi hakuri a sulhunta amma Aneesah tak'i yarda.
[4/9, 11:03 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
24
By Linah Shams✍🏼
"I'm so sorry for what she has done sir, hakan ba zai sake faruwa ba in Allah ya yarda", bai amsa mishi ba ya umurci Mrs Kiyawa da Miss Aneesah da su koma bakin aikinsu sannan ya mayar da hankalinshi ga Abdul, "kaga wannan yarinyar! Wannan yarinyar! May be it's because she's among our best students shiyasa", ya fada yana pointing dinta, Abdul yace "kayi mata hakuri insha Allah zanyi maganinta", yace "ai the annoying part is that; ba yau ta fara wannan iya shegen ba, da suke ss1 haka tayiwa Mrs Kiyawa", Abdul ya tari numfashinsa yace "Kiyawa?", he was surprised upon hearing that saboda yadda yaga suna good time da matar. PC yace "ofcourse, akayi warning dinta, a ss2 Mr Chales shima tayi mar, yanzu kuma gashi ta sake. I'm sorry, but we have to design her suspension letter", dafe kai Abdul yayi sannan ya kalleta, yace "yanzu kin ji dadi, zaki je gida ki dinga zama", tsuke fuska tayi ba tace mishi komai ba. Principal din ya tashi ya fita zuwa duba schl din. Yana fita ta k'arisa kan visitors' couch din da Abdul yake zaune ta zauna a gefenshi tace "I'm sorry, it's never my fault", takaici ma ya hana shi yayi mata fada, yace "then it's mine", shiru tayi mishi can kuma ta langabar da kanta akan shoulder dinshi ta lumshe idanuwanta. Sai after almost 20mins PC din ya dawo rike da suspension letter d'in, for seven days, ba zata dawo schl ba sai next week thursday. Abdul ya amsa suka yi sallama da PC din suka fita. A gefen class d'insu ya tsaya jiranta ta shiga ta d'auko schl bag dinta ta fita ba tareda tayiwa kowa magana ba, har sun kama hanyar stairs zasu sauka Ni'imah ta kwalla mata kira "Anjayjay", waigawa tayi hakan yasa shima ya waiga, "your food flask", tace "ki tafi dashi ki ci abincin next week thursday ki kawo min flask dina ko dai ma, ki bawa Aunty Maryam" tace mata to tareda juyawa ta wuce class.
A tare suka isa kusa da motar, ya wuce driver's seat ita kuma ta wuce front seat, ya riga ta shiga. Tana bude kofar yace mata "bana baki transport fare ba? You made me waste an hour or so yanzu kuma you're expecting me to give you a drive back home?", binshi tayi da idanu, how embarrassing? Kallonshi ta gama yi yadda ba zai iya fassara kallon ba sannan ta ja gefe ta rufe masa motarsa ta kama hanyar fita zuwa bakin hanya don samun abun hawa. Har ta kusa kaiwa sai gashi ya iso, a gefenta yayi parking ya bude mata kofar motar daga ciki, she has no choice, haka nan ta shiga. Shiru ne ya biyo baya har sai da wayarsa ta fara ringing, har itama tasan ko kiran waye idan taji irin ringing tone din, murmushi ne ya bayyana a samar fuskarshi ya jira call din yayi disconnecting sannan ya kira, "sweetheart" ya fara fad'a, ita dai shiru tayi ta zuba ma hanya ido sannan taji yace "ina driving ne idan na samu time I'll call", "take care... Bye", daga haka call din yayi ending. A bakin layinsu yayi dropping dinta yace shi ba zai iya karisawa da ita ba, bata ji haushi ba ta sauka ko godi bare nagode. K'in tafiya yayi ya tsaya yana kallonta sai ya ga kulewarta. Ko nisa bata yi ba iska ya k'ada, hakan yasa uniform d'in ta ya d'ame ta ilahirin surar jikinta ya bayyana, he never know haka take da shape, ko dai don hankalinsa bai taba karkata zuwa can bane. Haushi ya kama shi sosai saboda yadda iska yayi mata, yanzu ba abin mamaki bane ace wani ya kalleta, takaici yasa ya bar layin ba tareda yaga k'ulewarta ba. Ita kuwa bata ma san yana yi ba. Kai tsaye shago ta nufa ta siya recharge card na kudin komawar da ya bata sannan ta shige gida.
Tun daga main parlour ta fara unbuttoning shirt dinta har ta isa bedroom. Zafi duk ya isheta kamar ana dafa ta. Gudun fanka ta kure jikinta daga skin tight sai bra, wata yar singlet ta dauko ta saka sannan ta haye gado tayi ta rolling. Ta so tayi bacci amma gaba d'aya baccin ya k'i zuwa. Hakanan ta tashi ta fara aiki, gyara bedroom din tayi ta wanke toilet sannan tayi shara da mopping da sauran goge goge. Sai da huta sannan tayi wanke wanke ta cigaba da kwanciyarta amma ta kasa bacci. Wayarta ta d'auko a wardrobe tayi loading recharge card d'in ta koma gefen gado ta zauna. Rasa wanda zata kira tayi, Mommy ta so kira amma tayi tunanin idan ta kira ta zata tambayeta dalilin da ya sa bata je schl ba sai ta fasa, nan ta canja shawara ta kira Aunty Maryam, ita kuma lokacin tana staffroom suna mayar da magana da sauran staff. Mikewa tayi ta fita waje don amsa kiran saboda surutunsu ba zai iya barinta taji da kyau ba. Da sallamarta ta amsa Jaleelah ta amsa mata, "kina gida kenan"
Tace "eh na koma"
Maryam tace "hutu ya same ki", 'yar dariya tayi tace "ki bar matsiyaciyar yarinyan nan, ta sa an bani suspension akan gaskiya na", tace "wlhy nata bata hakuri taqi yarda", Jaleelah tace "manta da ita, Ni'imah Sulaiman zata baki food flask dina gobe, ki ajiye min may be gobe na roki uncle abdu idan ya barni zan zo gidanki"
Tace "da nima gobe nake so na zo ai", tace "dagaske Aunty Maryam?", tace "eh wlh tun ranan tuesday na so zuwa", tace "to ki bari mana sai ranan saturday, ranan zai je Kano daga can zai dauko min snacks d'ina sai ki zo dasu Maijidda", tace "to shikenan Allah ya kaimu", ta amsa mata da Amin suka yi sallama. Contacts list dinta ta cigaba da bi tana neman wanda zata kira har ta kai kan numbern Khaleefah, ta jima tana kallon numbern kamar ta kira sai kuma ta tsallake shi. Kan numbern Abdul ta isa wanda har yanzu bata canja mishi suna daga Uncle Abdu ba ta kira, as usual sai da ya yanke sannan ya kirata, shiru yayi bayan tayi picking yana jira ta fara magana, tace "uncle Abdu"
Ya amsa mata da "mene ne?", tace "ba komai" shiru yayi ita ma tayi shiru, sun kusa five seconds a haka sannan yace "ya kike?" Tambayar ta bata mamaki da dariya, tace "ga dai ni nan, gidan ba dad'i wlhy", yace "ai dama abinda kike so kenan, wani ya aike ki yace kiyiwa malama rashin kunya?" Tace "ai na fada maka ba laifi na bane", yace "eh ai shine nace miki laifi na ne"
Tace "ni strolling ma zani, gidan ba dad'i, tsoro nake ji", yace "idan kika kuskura kika tsallake gate din wlhy sai na baki mamaki, ki bari in dawo inga baki nan", hade giran sama dana k'asa tayi tace "to ni tsoro nake ji", yace "haka nan zaki jira har sai na dawo", tace "to, sweets nawa zanci? Ko chocolates zan dauka?"
"Ni dai bance ki ci ko daya ba"
Ta kyalkyace da dariya, sama sama shima yayi dariyar, yace "oh dariya ma na baki ko? Idan kika ci sai na cire miki baki", ta sake yin dariya tace "alright bye. Sai ka dawo", ya amsa mata da "okay bye".
Sai around 2PM bayan ta tashi daga bacci tayi sallah ta idar ta fito zuwa kitchen. Rasa me zata dafa tayi, tayi deciding kawai tayi d'an wake da sauce.
To 4 ta kammala komai ta fito parlour rik'e da plate d'aya da glass cup d'in ruwa. Sai da taci ta k'oshi sannan ta je tayi sallah ta fito sitting room ta kunna TV bayan ta debo chocolates da sweets daidai ta son ranta, channel tayi ta canjawa tama rasa katamaiman inda zata tsaya, hakanan ta tsaya a MBC3 tana kallon cartoons. Sosai ta nutsu tana kallon yadda kasan an sata ko tana kallon abin arziki, "sannu da k'okari", da sauri ta d'ago kanta suka yi ido hud'u da Abdul, da fara'arta ta tashi ta zagaya bayan couch tayi hugging d'insa kamar zata shige jikinshi, ta kusa 2mins a jikinshi bata da niyyar sakinshi, yace "baki so in huta ne Jaleelah?", murmushi tayi kamin ta sake shi sannan suka wuce bedroom tare, zama yayi a gefen gado yace "I'm dog tired dear", ya fada yana kai hannunsa kan takalminshi na dama. Da sauri ta karisa ta tsugunna a gabanshi tace "let me help you", tsayawa kallonta yayi tana cire masa takalman. He was so carried away by her body's plump physique. A hankali ta sab'ule black socks d'in dake kafafunshi ta d'ago tana murmushi still bai bar mata irin kallon da yake yi ba. Tace "na gama", kasa motsi yayi yace "help me with this please", ya mik'a mata hannunshi ta cire mishi wrist watch. Ta juya zata fita da nufin barinshi yayi wanka ya kirata ta dawo, mood dinsa gaba d'aya ya canja, yace "je ki hada min ruwan wanka to", chuckling tayi tace "yau kuma?", girgiza mata kai kawai yayi ta shiga ta had'a mishi, ta fito ta ganshi a zaune kamar yana tunani, tace "na had'a, ka tashi to", deep sigh yayi yace "help me get undress please", mamaki ya bata tayi sauri ta fita ba tareda ta amsa shi ba.
Ta kusa 1hr tana zaune amma bata ga fitowarshi ba, tasan yanzu ya gama shiryawa may be yana hutawa ne tunda yace mata ya gaji sosai. Ko kadan bata damu da abinda ke jikinta ba, ta tashi ta nufi bedroom, tana shiga suka ci karo zai fito cikin brown three quater da white T-shirt, riko hannayenta yayi yace "ina zaki?", tace "na zo duba ka ne naga baka fito ba", yace "okay, kinyi min abinci?", d'ago kanta tayi ta kalli kwayoyin idanuwanshi tayi nodding, cikin sanyin murya yace "bana son nodding", tace "eh nayi maka", shiru yayi sannan daga bisani ya rungume ta sosai. Kwantar da kanta a kirjinshi tayi tana shaqar qarmshin tilarenshi, sunfi four mins a haka sannan ya dago da kanta yana kallon fuskarta, ya rasa me yake ji game da ita, sunkuyar da kanta tayi sannan ya sake d'ago mata da kan, a hankali ya kai lips d'inshi kan nata ya fara kissing dinta, bata yi detesting ba saboda tasan mijinta ne, yana daga cikin fadan da Mommy tayi mata kuma ko Mrs Maryam ta k'ara jan hankalinta akan k'in bijirewa miji. Sun kusa 10mins a tsaye sai da ta fara gajiya sannan ta fara kokarin dakatar dashi, yana bari tayi yunk'urin guduwa ta bar d'akin ya janyo ta ya rungumeta. Sai a yanzu shima yaji wani iri, yana considering d'inta too young. A tare suka fita zuwa parlour sai sissinar da kai take yi gaba daya ta kasa sakewa, shi kuwa ko a jikinshi. D'an waken ma da cewa yayi sai dai tayi feeding dinsa tace ba zata iya ba, amma kuma da bai yi kissing d'inta ba sarai zata bashi. Tashi tayi ta juya zuwa bedroom ya bita da na mujiya, bata jima ba ta fito mishi da wayarshi ta mik'a mishi, "gashi an kira ka kamin na iso yayi disconnecting", yasa hannu ya amsa ya duba missed call, abokin aikinshi Muneer ne ya kira shi last sai other ten missed calls kuma duka na Raheemah ne, "fitina" ya fada a fili, kara wayar yayi a kunni yana jira tayi picking
"Baby ka daina so na" ta fad'a kamar zata yi kuka
"I'm so sorry baby, it's not like that at all, na fadi miki commitments ne suka yi min yawa"
Kad'an ya rage ta fashe da kuka, tace "AbdulHakam sai yaushe zaka samu time d'ina? Kullum commitments! Commitments! Commitments my ass!!"
Shi dai yasan shi mai laifi ne, hakuri ya dunga bata kamar me rokon gafarar uwarsa da kyar ta hakura, Jaleelah kuwa bata jira sun karisa hiran ba ta koma bedroom tayi slamming kofar ta jingina dashi, kanta ta d'aga sama tana kallo a hankali take fad'in "why? Why? why?", heart dinta ne ke beating faster than usual, ta sa right hand d'inta ta dafe left side din kirjinta where her heart is, hawaye ya fara zirarawo daga idanunta, haushin kanta take ji sosai saboda yadda take jin haushi idan Abdul yana waya da Raheemah. Meya sa zata ji haushi afterall bawan Allahn nan taimakonta yayi? Meya sa ba zata iya hakuri ba? Kuka sosai ta fara yi daga baya ta shige bathroom gudun kar ya shigo yaga tana kuka, idan har ta cigaba da jin haushin relationship dinsa da Raheemah tamkar tayi butulci ne.
Sai da tayi wanka sannan ta fito d'aure da towel. Fitowarta yayi daidai da shigowarshi bedroom d'in. Wucewa tayi ta zauna a gaban dressing mirror ta ciro wani handkerchief ta share ruwan fuskanta. A hankali take rubbing Vaseline kamar ba zata yi ba, tunaninta kawai take yi akan yadda Abdul yake waya da Raheemah. Jin hannun mutum a kafadarta yasa ta d'ago suka yi ido hud'u, saurin kawar da kanta tayi amma duk da haka sai da yayi observing idanuwanta sun yi ja, "tunanin me kike yi haka?", ya tambayeta, murmushi ta k'irk'iro tace "ahm ba komai", ya sake tambayarta "to meya sami idanunki?", shafa idanuwan tayi tace "sabulu ne ya shiga min ido", yace "ayya.. Sorry", bata amsa shi ba ta tashi taje ta bud'e wardrobe ta d'auko light cotton gown zata sa, juyawa tayi taga idanuwanshi a kanta, tace "uncle zan sa kaya", yace "and so? Ki sa mana", tace "to kaje waje mana", gira ya daga mata yace "uhum? Ni idan zan sa ai ba korarki nake yi ba ke kike koran kanki, ko na taba cewa kiyi excusing dina?", shrugging tayi ta kwashi inners dinta da gown din ta tafi dayar empty bedroom ta sa. Gudun kar ma ta sake ganinshi a can d'akin ta bar towel d'in ta dawo parlour ta zauna, haushinshi da haushin kanta take ji at once.
Sai da yaji shiru bata dawo ba ya fito sitting room ya ganta, a gefenta ya zauna yace "Anjayjay", murmushi tayi jin ya kirata da sunan da bestfriend d'inta kad'ai ke kiranta, yace "yau ba labari ne? Ko har yanzu haushin malamarku kike ji?"
Tace "a'a ni da kai nake fushi"
"Amazing! Me nayi ni kuma?"
Tace "you refuse to understand me"
Tana so ta fada mishi yadda take ji idan yana waya da Raheemah amma tayi tunani sam hakan bai dace ba, yace mata "nobody understands you the way I do, I know your moves, I can interprete your silence and words", twitching lips d'inta tayi tace "but not this time, sai blaming d'ina kake yi" ta canja maganar daga abinda take so ta fada mishi
Yace "to ba dole ba, sau uku kina abu daya"
Tace "how can you judge without hearing from both parties?"
Yace "okay I'm listening"
Tunda yace mata yana fahimtar yanayinta ta sha jinin jikinta, bata so ya gane amma ko ya gane she has to prove him wrong ta hanyar sakin ranta, tace "kaga Mrs Kiyawa cewa tayi wai bana jin turanci, Mr Chales kuma zakin mamana yayi, ita kuma Aneesah a bainin nasi take farfad'a min maganganu wai ina hugging namiji banida kunya"
"Oh I never know, shine PC din bai fito directly ya fada min ba?"
Tace "munafukin k'ila sonta yake yi, a gaban class fa"
Yace "to wa kike hugging?"
Dariya tayi tace "kaima kasan wanda nake hugging"
Jan hancinta yayi yace "cutie"
Rike hancin tayi tana murmushi amma bata bar damuwa ba. Hira suke tayi suna yi suna dariya har magrib tayi yayi alwala ya tafi masallaci sai after isha ya dawo. Saboda dadin labari tea kawai suka sha suka kwanta ranan
Washe gari.........
⚜Mijin Jaleelah⚜
25
By Linah Shams✍🏼
Washe gari tare suka fito zuwa compound tayi masa rakiya, har wurin motarsa ta raka shi, kamin ya shiga motar tace "uncle yau ba bye bye?", murmushi yayi yace "akwai mana", spreading arms dinsa yayi ta fada kirjinsa ya rungume ta. A hankali ya d'ago da kanta yace "kinga yanzu kin yi min bye bye, now it's my turn", a hankali ya fara kissing lips d'inta, yi yake yi kamar ba zai barta ba. Ganin suna ta jan lokaci yasa ta dakatar dashi, tace "zaka yi latti", ajiyar zuciya yayi yace "ban fa gama ba", d'an murmushi tayi tace "idan ka dawo zanyi maka", yace "to, take care matar AbdulHakam", farinciki sunan ya sata, tace "yauwa uncle, dan Allah ina so yau na fita", yace "zuwa ina?", tace "gidan neighbours d'in mu", yace "ya akayi kika san su?"
"A'a ban san su ba, kawai so nake yi na san su, kaga muna ta zama a wuri ni ban san kowa ba", yace "alright, gida biyu kawai na yarda ki shiga", tace "to thanks, sai ka dawo" tayi waving dinsa bye ta shige gida.
Har ya isa wurin aiki yana tunaninta haka itama, tun data shiga gida ta kwanta take tunanishi. Sai da ta d'auki fiye da one hour tana abu daya sannan ta tashi ta fara aikin gida. Cikin sauri tayi ta gama sannan ta zauna zaman warware kitson kanta. Bayan ta gama tayi combing ta kama shi da ribbon wanda bai wuce kamu uku ba sannan ta shiga wanka.
Atamfa mai kyau d'inkin riga da skirt ta d'auko ta saka ta yi light make up sannan ta d'auko white hijab ta saka. Lokacin it was almost 10:30AM. Sabon flat shoe ta d'auko ta saka ta feshe jikinta da tilare sannan ta d'auki wayarta da keys d'in gidan ta fita.
Tababan wani gida zata fara shiga take tayi, dama su biyu ne da she would be a bit comfortable amma yanzu idan ta shiga gidan bata ma san wani katamaiman hanya zata bi ba ya sada ta da d'akunan gidan ba.
Gidan dake hannun dama da gidansu ta nufa, sai da tayi ta knocking sannan mai gadi ya zo ya bude mata, sai da ta tambaye shi ko masu gidan na nan yace mata eh suna nan. Tace to ya mata jagora zuwa ciki ita bakuwa ce, a hanya suka had'u da wata matashiyar budurwa wacce bata wuce kimanin shekaru ashirin da hud'u ba. Maigadi yace "Aunty Fadeelah ga bak'uwa nan, dama shigo da ita zan yi", cikin fara'a Fadeelah tace mata "sannu da zuwa", cikin fara'a Jaleelah ta gaishe ta sannan tace "Umma na nan dan Allah?", tace "eh mu shiga, da rabon ma zaki ganta ne don yanzu zata fita unguwa", tare suka shiga cikin tank'amemen parlourn wanda yasha k'yalek'yale, Fadeelah tace mata ta zauna ita bari ta shiga ta duba mata Umman. Zama tayi akan sofa tayi zugum hankalinta soon ya fita daga jikinta kuma ita ba tunanin wani abun kirki take yi ba. Muryar dattijuwan mace ta tsinkayo tana ce mata "sannu da zuwa", da sauri ta d'ago tareda planting murmushi a fuskarta ta. Umman ta k'ariso ta zauna ita kuma ta zame jikinta zuwa k'asa, Umman tace "a'a da kinyi zamanki 'yar nan", fara'a tayi sannan tace "a'a Umma nan ma ya isa" bayan nan ne suka gaisa cikin girma da arziki sannan Jaleelah tace "dama mune muke mak'wabtaka da gidan ku", daidai lokacin Fadeelah ta iso parlorn da ruwa da lemon kwali a cikin tray sai glass cup ta ajiye mata a gabanta sannan ta zauna a gefen Jaleelah, Umma tace "wane gida kenan?", tace "wannan wanda yake hade da nan gidan", Fadeelah tace "ko gidan airforce din nan ne?" Harda girgiza kai tace "eh nan", Umma tace "Allah Sarki, hala ke kanuwarsa ce", d'an murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tace "a'a", Fadeelah tace "matarsa dai Umma", Umma tayi murmushi tace "masha Allahu, Allah ya bada zaman lafia, gashi kin zo zan fita", tace "eh". Umma ta dubi Fadeelah tace "je ki d'auko min hijab d'ina da purse da takalmi", tashi tayi ta wuce ta dawo d'auke da saqon, Umma ta amsa ta sa tare da mik'ewa, tace "to sai na dawo, ki gaida gida ko", dukansu su kayi mata a dawo lafia Fadeelah ta raka ta har bakin kofa sannan ta koma wurin Jaleelah, tace "kin ga ma baki fada min sunan ki ba", tace "Jaleelah"
"that's nice, pleased to meet you"
"It's my due pleasure"
Hira suka d'an fara kad'an kad'an shima game da karatu ne. Ita Fadeelah ta kammala degree a masscom daga Udusok har tayi service. Tun Jaleelah bata sakin jiki tana bata gamsassun amsoshi har ta fara, a nan ta tambaye ta inda ake kitso tana so tayi, Fadeelah tace mata gidan da d'an tafia amma for now zata mata. Shuku ta rangad'a mata mai kyau, da hair cream d'inta tayi mata kitson kuma gata da sauri.
Tana d'aga kai ta kalli makadeden agogon dake jikin bango taga 12:30 na rana. Da sauri ta mik'e ta d'auki hijab d'inta, Fadeelah tace "ba dai tafiya ba", tace "tafiya zan yi kam", tace "haba ke kuwa, ki bari nayi mana abinci, kuma kinga ni kad'ai ce a gidan kema haka zaki je ki zauna ke d'aya"
Tace "bana k'i miki bane Aunty Fadeelah, kinga yau Friday kuma uncle ya kusa dawowa gashi banyi girki ba", tace "wane ne uncle?"
Tace "miji na mana". Dariya tayi tace "amma baby baki da kirki, mijin naki kike ce ma uncle", murmushi tayi tace "sunan shi kenan", tace "to ina laifin ki d'an kira shi da koda sweetheart ko honey?"
Dariya tayi tace "kin ga sai ja na kike yi da hira, bari na wuce". Har compound tayi mata rakiya tareda yi mata alk'awarin shigowa yi mata ban gajiya.
Tana shiga gidan ko 5mins bata yi ba AbdulHakam ya Shigo. Daidai da kitchen d'in ma bata lek'a ba bare tunanin me zata dafa. Da sallama ya shigo parlour d'in ta amsa mishi. Sakarwa junansu murmushi su kayi sannan ta tashi zuwa gareshi tayi hugging d'insa as usual, almost abinda ya faru jiya shi ya faru a ranan. Tare suka yi girki suka dafa jallof rice, shima ranan basu dafa abincin dare ba.
The next day, weekend yayi shirin tafiya Kano da safe. Ya so tafiya da wuri amma hakan bai samu ba, a jiddin yana liqe da ita. Tare suka yi aikin gida suka yi komai. Sai to eleven AM sannan ya wuce bayan sun yi sallamarsu irin ta musamman.
Zaune take akan couch ta hard'e kafafunta, zulluminta d'aya yau ita d'aya zata kwana a gidan nan duk girmanshi. Da farko bata damu ba sai da dare yayi sannan hankalinta idan yayi dubu ya tashi gashi babu wutar lantarki. Fita compound tayi taga da hasken farin wata taje tayi locking gate, ta shiga d'aki ta kulle sannan ta kashe kayan wuta. Shima bedroom din data shiga sai da tayi locking sannan ta kwanta, ko motsi mai k'arfi ta kasa yi. Saboda gani take wani abun tsoron zai iya bayyana from no where. Wayarta dake kan dressing mirror ta hango tana haske, bayan kusan twenty minutes kuma sai ga call, tsoron tashi ta d'auko take yi, sai da aka kira for the fourth time sannan taje ta dauko da tiptoe. AbdulHakam ne ko ba a fada mata ba, sai da ta zauna a tsakiyar gado sannan tayi picking, shi ya fara magana yace "anjayjay", tayi k'asa k'asa da murya tace "uncle abdu", ya amsa mata da "na'am, ya kike?", kamar zata fashe da kuka tace "uncle ni bazan iya kwana a gidan nan ni d'aya ba tsoro nake ji, dan Allah ka dawo"
Yace "it's past nine yanzu fa", kuka ta fara tace "eh", yace "Jaleelah kiyi addu'a mana, bazan iya dawowa ba yau", kuka ta fashe mishi dashi tace "ni tsoro nake ji", yace "to ki daina ji, ai ina tare da ke, kuma nima kinga ni kadai zan kwana, kiyi addua kinji?", nodding tayi ba tare da ta amsa ba, yace "good night", bye kawai tace masa tayi hanging up tana jin haushin rashin shi.
Tana hanging yayi dialing numbern annurin zuciyarshi Raheemah. Hiran masoya suka sha Wacce rabon da su sha irinta sun kwana biyu, nan take sanar dashi saura two months ta dawo Nigeria, burinta bai fi taga na ta auri AbdulHakam ba, ya zama mallakinta halak malak, ita ma haka. Sosai take son sa fiye da yadda yake sonta, duk gidansu da kawayenta ba wanda bai san sunanshi ba a bakinta. Bayan ya kammala waya da ita yaje yiwa Umma sai da safe, ita ko kadan bata ga dalilin da zai sa ya kwana ba tunda yanzu yana da iyali, amma ya turje shi sai ya kwana. Sai da safe yayi mata ya koma gidansu ya kwana saboda yana so ya koma da wuri yaga lafiyarta.
Da safe sai da ya kirata suka gaisa, tace idan ya koma gidan Umma ya bata su gaisa. Sai da ya d'auko mata snacks da wasu kayan sannan ya wuce gidan Umma don yin breakfast sannan sai ya wuce.
Bayan ya kira mata Umman sun gaisa ne ta buk'aci a ba Inteesar su gaisa Umma tace ta wuce Islamiyya amma idan ta dawo zata fada mata sai ta kirata.
Ita sam bata ma ga abin gyarawa a gidan ba amma haka nan tayi few things sannan ta turare gidan da tilaren wuta. Short nightie ce kawai a jikinta sai kai komonta take yi. Ringing d'in wayarta dake bedroom ta jiyo ta mike da gudu zuwa daukowa don tasan ba call din kowa bane sai AbdulHakam amma sai taga akasin haka. *Khaleefah* ne ya kirata gabanta har sai da ya fad'i, da kamar ba zata d'auka ba amma ta d'auka, shi ya fara magana sannan ita, yace "madam ya kike? Kinyi scarce"
Murmushi tayi tana ji tamkar a mafarki, tace "kadai yi scarce, ya amarya?"
Yace "lafia k'alau wlhy, kwana dubu"
Tace "ai KHALEEFAH baka da kirki, na aza ko HML text message zaka turo min bare kuma kira", dariya yayi yace "anyi min overtaking shine har kike expecting zan turo sakon taya murna? Haba", tsuke fuska tayi tace "ai kai ka ja, gashi yanzu an aura min wani daban baya so na ba na son shi, kullum iqirarin taimako na yake yi", shiru yayi for a while sannan yace "haka Allah ya so Jaleelah, amma fa in ke mata tace sai kiga Allah ya kashe mijinki na aure ki", waro idanuwanta waje tayi tace "ba amin ba", yace "yanzu ma nasan kin daina so na Jaleelee", tace "ina son ka mana amma a...". He couldn't help it anymore, ji tayi an jayo mata shukun data yi da k'arfi, wani razanannen k'ara ta saki ya juyo da ita ta kalleshi. Wayar ya fincike yasa a kunnenshi cikin fada yace "how dare you call someone's wife! Baka da hankali ne ko baka je islamiya ba? Are you crazy?", shiru Khaleefah yayi ya kasa cewa komai. Abdul ya tunkudata fuskanta ya bigi bango sannan ya ciro simcard dinta ya b'alla shi sannan yayi jifa da wayar ta daki bango tayi tatsatatsa. Cikin fada yace "and saboda munafirci that's why you've been crying last night na dawo na kwana dake while this is what you are doing. If you like tell the world TAIMAKON KI nayi kuma bana son ki, tell anybody you want, kuma I regret helping you tunda ke butuluce!" Gidan ya bari gaba d'aya don har tsanarta yaji ya fara yi. Sai da yayi driving me nisa sannan yayi parking a gefen hanya ya kifa kanshi a kan stir wheel. Ranshi ne ke k'una any moment idan ya tuna shine MIJIN JALEELAH, da yana da damar mayar da hannun agogo baya da zai koma ranan da ya fara haduwa da ita ne da kuma ranan sai ya ki fitowa ko bakin layinsu.
Durkushewa tayi a kasa ta fashe da matsanancin kuka ga kuma hancinta dake fitar da jini da goshinta gaba daya ta rasa hanyar da zata bi ta taimaki kanta. Ana haka Mrs Maryam ta iso gidan, ita ta taimaka mata ta wanke mata fuska sannan ta canja kayan jikinta ta kaita near by chemist aka wanke mata ciwon goshinta sannan aka yi treating dinta. Kamin su dawo Abdul ya fara dawowa, ranshi ya k'ara b'aci ganin bata gidan kuma ta tafi da keys d'in, motarshi ya koma dake fake a gaban gate din. Zuwa wani lokaci ya hango su sun tahowa da yaran Mrs Maryam d'in guda biyu, kawar da kanshi gefe yayi saboda baya son ma ganin fuskarta. Suna isowa Mrs Maryam ta tsaya ta gaishe shi da fara'a tare da yi mishi sannu da zuwa, tace "ashe haka ya faru", biye mata yayi yace "eh wlhy", tace "da sauqi ma ai tunda basu yi harming dinta sosai bama"
Yace "eh", sannan Jaleelar ta bude musu gidan suka shiga. Kasa shiga cikin gidan yayi iyakarsa parking lot. Bai taba tunanin ranshi zai iya b'aci kamar haka akanta ba.
Ganin yaki shigowa ne yasa Mrs Maryam tayi tunanin ko nauyinta yake ji kuma yana son ganin matarshi, shiyasa ma bata k'ara ko 20mins ba a gidan tayi mata sallama ta tafi.
Kanta ke ta sara mata kamar ana faskare gashi ya rike mata idanu. Da kyar ta samu tayi wanka ta sauya kaya zuwa k'ananu irin Wanda ta saba sawa wai a cewarta saboda zafi. Allah ma ya taimaketa tana da set d'in wankakken uniform don har zazzabi zazzabi take ji. Parlour ta dawo tayi kwanciyarta bayan ta kashe fanka saboda sanyin da take ji sama sama. Ko sallama bai yi ba ya shiga d'akin, tsayawa yayi daga bakin kofa yana kallonta, he wished babu abunda ya faru, da yanzu tayi hugging d'insa yayi kissing dinta. Kayan jikinta ya gama kallewa sannan ya karisa cikin dakin. Da sauri ta tashi daga kwance ta zauna feeling so guilty. Bata ma san da wani bakin zata bashi hakuri ba. Shiru tayi ta fara fidgeting fingers d'inta, ya gaji da kallonta tunaninsa na sauyawa, tsaki ya ja yace "bloody fool", sannan ya kara da cewa "dama daga yau kar na sake ganinki da tsinannun kayan nan, kinji ko baki ji ba?", a hankali tace "naji", yace "good for you, now tashi kije ki cire su" tsam ta tashi ta wuce ta cire su ta saka doguwar riga Mara nauyi ta haye gado. Tuni hawaye ya wanke mata fuska kanta na k'ara mata ciwo. Bargo ta ja ta rufe kanta a haka har bacci yayi awon gaba da ita.
Ko da ta farka bayan la'asar ciwon kan yayi mata sauqi. Saboda halin da take ciki ko yunwa ma bata ji. Alwala tayi sannan ta gabatar da sallar azahar da la'asar ta cigaba da zamanta ko fita parlour ta kasa, a haka har magrib tayi, nan ma tayi sallah har aka yi isha bata fito ba kuma Abdul bai shiga inda take ba. Koda ta fara jin yunwa chocolates kawai taci taje ta yi brush, ga k'ishi tana ji amma hakanan ta hakura ta kwanta.
Da tsakar dare k'ishi ya farkar da ita, ta aza zata ga Abdul by her side amma taga bashi, hakanan ta je kitchen ta sami ruwa ta sha ta koma bedroom. Duk a tunaninta zata ganshi a parlour amma babu shi, "where must he be?", tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan har bacci ya dauke ta.
[4/4, 8:11 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
26
By Linah Shams✍🏼
Haka suka cigaba da rayuwa a cikin gidan ba mai yima wani magana. Washe gari da tayi abinci ma bai ci ba, ta rasa yadda zata yi da shi. Shiyasa ta daina dafa abincin gaba d'aya. Bata iya cin komai sai snacks, cornflakes ko ta hada tea saboda damuwa ga rashin fita bare ta ga mutane taji sanyi. A cikin yan kwanakin har rama tayi sosai kuma ya lura da hakan, jiranta yake yi ta bashi hakuri ya nuna mata mistake dinta.
Da safiyar ranar alhamis gaba daya kasa sakewa tayi. A k'asa ta zauna kan rug tana sipping Lipton, ko sugar d'in arziki bata sa ba saboda tsabar fargaba. Guilty consciousness. A kan couch ya zauna tareda ajiye takalmansa da ya dauko gefe. "Ina kwana" ta gaishe shi, bai amsa mata ba yace "ina keys d'in gidan nan?", gabanta ne ya fadi, tace "yana cikin drawer", yace "to gama ki d'auko min", ajiye cup d'in hannunta tayi tana yunk'urin mikewa, yace "cewa nayi ki gama", cikin in'ina tace "ai na gama", yana hangowa saura kusan rabin cup. Sai da ta kammala shirinta ta fito mishi da keys d'in ta koma inda ta tashi ta zauna. Call din Raheemah ne ya shigo cike da fara'a yayi picking, "hello baby", ya fad'a.
Tace "honey ka tashi lafia?"
Yace "alhamdulillah ke fa?
Tace "gani nan badly missing you", yace "bayan jiya kin hanani bacci da wuri sai after 3AM kuma har yanzu ma wai missing d'ina kike yi"
Shagwaba ta fara yi mishi tace "honey ai auren mu ya kusa ko?"
Murmushi yayi, yace "of course my love, insha Allah, first dai Allah dai ya dawo dake lafia"
Bak'in ciki ne ya taru ya tattare mata, ga fushinshi dake kanta ga kuma haushin waya da Raheemah, hawaye ya kawo a idanuwanta ta mike da sauri zata bar wurin ya dakatar da ita "dawo ki zauna", haka nan ta koma ta zauna, bata san me Raheemar tace ba amma taji yace "haba baby, ba wata bace fa, wata yarinya ce dana taimaka", taji ya sake cewa "no no dear, don't think stupid, ai ni MIJIN RAHEEMAH ne. Juyama side din da yake baya tayi ta fara hawaye ko zata samu relief. Bata san lokacinda ma ya gama wayar ba ta dai ji yana cewa ta tashi ta zo ta tafi schl. Sai da ta share hawayen sannan ta mik'e ta fara tafiya zata fita ya tsayar da ita, yace "a tsaye ne zaki tsaya min?", hakanan ta tsugunna har kasa don tsoron shi ma take yi, yan #500 ya zaro daga cikin wallet dinsa ya irga guda biyar, ya mika mata sannan yace "nawa ne", tace "#2500", yace "good, #2000 kudin fare d'inki for five days, five hundred din kuma kudin break, tashi ki wuce", amsa tayi ba godi bare nagode. Sannan ya umurceta da taje ta sa zumbulelen hijab, hakanan ta saka ta fita ta barshi a gidan tana ta sake sake a zuciyarta game da amsan keys din da yayi. A bakin hanya tafi 10mins bata samu abun hawa ba. A haka har Abdul ya fito daga gida, tun daga nesa yake kallonta har ya karisa inda take zai hau kan hanya, winding glass yayi ya tsaya yana kallonta. Jikinta ne ya bata wani na kallonta ta waiga taganshi, kallonshi tayi ido cikin ido with affection, sun kusa 30scs suna kallon juna hawaye ya fara taruwa a idanuwanta, ta kawar da kanta gefe Allah ya taimake ta sai ga mai keke napep ta tsare ta shige ko tambayarsa ma nawa zai kaita bata yi ba.
Haushin kanshi yaji da ya tuna cewa no matter what matarsa sa ce. Ita kam keke napep sai sharan hawaye take yi har suka isa makaranta bayan ta sanar dashi inda zata da kuma adadin kudin da zata bada.
Tana fita ta yaye hijab d'in daga jinkinta sannan ta ninke ta shiga schl din dashi a hannu. Tana shiga schl d'in da Aneesah ta fara cin karo, nunawa tayi kamar bata ganta ba ta sa kai zata wuce sai ta ambaci sunanta, waigawa tayi ba tareda ta amsa ba tana jiran ji daga gareta, tace "how are you", ta amsa mata da "fine". Aneesah ta sake tambayarta "how is your uncle?" Ji tayi kamar ta shak'e ta, tace "are you related? Don't ever ask me about him. Mind your business" ta sa kai ta wuce ta.
Kamin ta karisa cikin class Ni'imah ta fito da gudu ta rungumeta, farinciki ne ya kama su both suka wuce class. Ranan throughout surutu suka sha duk inda d'aya zata tare suke zuwa, har gaishe da Mrs Maryam ma tare suka je.
Gaba d'aya notes d'in Ni'imah ta ara zata tafi dasu gida tayi updating nata.
Koda akayi closing abun hawa ta tara ta hau bayan sun yi hira da Hadiyya ta wuce gida. Sai a sannan ta tuna keys basu wurinta. Har kofar gidansu yayi dropping dinta mai adaidaitan sannan ta koma gefe daga jikin bango inda inuwa ya sauka tana jiran isowar Abdul. A haka har tayi 30mins bata ganshi ba su da suke closing 2pm saga schl. Tsayuwa ta cigaba dayi amma bashi ba labarinsa har aka fara kiran sallahr la'asar. Har bacci take ji saboda tsabar gajiya kawai sai gashi ya bud'o gate ya fito. Da sauri ta gyara tsayuwarta ya kalleta a kaikaice, yace "me kike yi a nan? Sai yanzu ne kika ga daman dawowa?", shi duk a tunaninshi ma ta gudu gidansu. Tace "jiranka fa na tsayi yi", gudun kar ya dizgata a layi yasa ya matsa mata ta shige ciki ya bata keys d'in ya wuce masallaci.
Tab'e fuska tayi da ta shiga inner sitting room ganin sababbin kujerun da aka sa masu kalar navy blue da sky blue. Haka ma curtains d'in da rug. Ko zama akansu bata yi ba tayi shigewarta ciki ta sauya kayanta sannan tayi alwala tayi sallar la'asar.
Snacks taci da ruwan Lipton sannan ta kwaso notes d'inta ta koma main parlour ta hau kan dinning ta fara rubuta notes tana yi tana yan wake wake. Yana bud'o kofa ya shiga yaji muryarta bata ma san ya shigo ba, kallonta yayi ya jinjina kai a ranshi yace "lallai yarinya duniya ta miki dad'i". Ci gaba tayi da rera wak'ar "tears in the ocean" na Jay Sean. Lokacin da ya isa dinning hall d'in ita kuma tana rera "how many sorry(s) will it take? How much of me talking will set it straight? Don't even remember the guy's name (instead of girl's name), you're my forever and that won't change", yaji d'adin baitin, he wished ace apologising take yi, yace "sannu", da sauri tayi gum da bakinta ko 10secs bata k'ara ba ta kwashe littafanta tayi gaba, inner sitting room ta koma ta cigaba da rubutunta cox tama san idan bata bar wurin ba shi zai bari saboda tunda incidence d'in nan ya faru basu sake zama wuri d'aya ba sai ya zama dole.
Duk a tunaninsa bedroom ta koma gabatar da wani uzuri amma sai yaci karo da ita a nan, bai kawo komai a ransa ba ya sami wuri ya zauna. Yana zama ta kwashe takaddunta ta wuce d'aya daga cikin empty bedrooms. Kallon kanshi yayi yaga ko ya sauya kama ne yaga he was still thesame. Tashi yayi yabi bayanta nan ma yana shiga ta fice. Ba k'aramin baci ranshi yayi ba, sai sannan ya dangata yadda yaji da yadda itama take ji idan ta zauna a wuri yake tashi. Kai tsaye bedroom dinsu ya nufa nan ya cidda ita akan gado tana rubutu, yana zama ta nad'e takaddunta zata fita yace "ke zo nan"
Dawowa tayi ta tsugunna a gefensa yace "baki da hankali ne ko baki san cewa ni mijinki bane?", tace "na sani", yace "then why are you running away from me?", onething about her is that she is bold, tace "you are running away from me", kallonta yayi yace "really? Je kiyi rubutunki"
Ba musu ta mike ta fita ta cigaba da abinda take yi.
Washe gari ya so ya kai ta schl amma haushin tashi a wuri idan ya zauna har ta kai ga taki kwana a bedroom yasa yak'i kaita. Yama lura yanzu she don't give a damn about him.
After Last period duk ranan friday club&societies suke yi. Ita da Ni'imah saboda rashin ji basu san ma katamaiman club d'insu ba amma asali da zasu shiga SS class Jet club suka yi choosing. Daga baya kuma sune entrepreneur, sune computer, sune debating ko drama club. Yau kuma basu ma san inda zasu je bane shiyasa suka yi zamansu a class su kadai. Jaleelah na kwafan notes Ni'imah na bata labari har akayi closing. Su dad'i surutu har kusan 15mins da closing basu fito ba sai ga wani classmate d'insu ya shigo class d'in yace "Jaleelah your uncle is waiting for you", muguwar faduwar gaba taji tayi saurin dafe kirjinta. Nan da nan ta hada notes d'inta ta zumbula hijab tace "babe let's go kamin ya min masifa".
Da sallam ta shiga motar ya amsa mata. Bata sake cewa komai ba yace "baki iya gaisuwa ba ko? Da yake ba islamia ma kika dawo ba, I don't blame you" tabe baki tayi ta kuma k'i gaishe shin, yace "me kika tsaya yi kin san na fada maki I will be coming on fridays", tace "kwafan note"
What sort of answer is this? Short short. Shiru ya mata bai sake tanka ta ba tace "ina so zani gidan mu"
Yace "ina kenan?"
Shafa hancinta tayi tace "gidan baba na"
"Me zaki je yi?"
"Kud'in registration d'in jamb zan karba"
Har waigawa yayi ya kalleta, yace "yaushe aka fara?", tace "tun last week"
Yace "shine baki fada min ba Jaleelah?" Shiru tayi yace "I think it will be good idan muka je akayi miki registration d'in yanzu ko? Nayi sallar juma'a a Sultan Bello", tace "to thank you".
❇❇❇❇❇
A kwanakin da suka gabata sosai Raheemah ta samu kulawar Abdul saboda sabanin da suka samu da Jaleelah. Hakan yasa duk ta kosa kwanakin da suka rage mata su kare ta dawo Nigeria ta kasance kusa da masoyinta.
❇❇❇
Tsaye take a gaban dressing mirror tana gyara buttons din riganta. From nowhere taga mutum a bayanta sai ta kasa tafiya tayi jim a wurin. Duk lokacinda ta dago fuskanta ta kalli cikin mudubin sai taga yana kallon ta. Dafa kafadunta yayi yana kare mata kallo ta cikin mudubin ta saka loose shirt da wandonsa. A hankali yace "dagaske ne baki so na?"
Kunya taji ta kasa cewa komai har suka kusa 4mins a haka, yace "it's okay, it's fine" ya juya zai fita. Da hanzari ta rungumeshi ta baya ya tsaya cak, hakan ya bata damar kwantar da kanta a bayan nashi.
"I'm sorry, dan Allah kayi haquri kaji?"
Waigowa yayi ya shafa fuskarta kaana yace "though we don't love each other, I always protect your dignity as my wife, haqqi na ne a matsayina na mijinki, ya kama ta ki dunga tunawa ke matar aurece, and although we had not any affair, ko yanzu kika kashe aurenki kika fita ba Wanda zai kiraki da budurwa. Bazawara zaki zama. Destiny dina ne na zama mijinki that's why na fara baku lift, if not, mata nawa ne suke fita kullum da safe zuwa schl? Ko yaran neighbours din mu ban taba d'auka a mota ta ba sai ke da sis d'inki, da I won't. Ya kamata ki kiyaye dokokin Allah. Yarinta ba hauka bane tunda nasan kinje islamiyar nan ilimin kina dashi daidai gworgodo, okay?". Cike da jin nauyinsa tace "yes" ya juya ya fita daga dakin.
Kusan wasan mage da bera suka fara sai dare yayi suka fi haduwa saboda tare suke bacci.
Ranan Monday ta tashi da ciwon mara sama sama. Tana fata har taje schl ta dawo ba zaiyi worst ba saboda kunya take ji ta fadawa Abdul bare ya siya mata magani. Ko da suka zo fita yaga tana ta yamutse yamutse ya tambayeta cewa tayi lafiya qalau take. Bayan ta isa schl ta zauna tayi shiru kamar wata marainiya ta tsaya jira ayi ringing assembly. Ciwon kamar karuwa yake yi with every second. Hakanan tayi ta cijewa har akayi assembly suka shiga class. As usual english ne first period dinsu kuma double period. Har aka cinye first period tana ta gurmusu tana yi tana cijewa har Mrs Maryam ta fuskanci haka, ita ma ko da ta tambayeta ce mata tayi lafiyarta qalau duk da bata yarda ba. Kamin second period yayi nisa abun yayi worst gashi ko pad bata saka ba don bata yi tunanin bakon nata zai iso ba. Kuka ta fara mara sauti ta daura kanta akan desk, Ni'imah ta fadawa Mrs Maryam ta matsa zuwa inda suke ta duba ta. Principal tayi ma reporting yace a maida ta gida ko a kira a zo a d'auke ta. Nan tayi deciding ta kira mijinta ta sanar dashi. Lokacinda ta kira shi yana tsaka da aiki don bama a son ranshi yayi picking ba, yana d'agawa suka gaisa sannan tace "you are speaking with Mrs Maryam Kiyawa from Aunty Maya memorial school", sai da gabanshi ya nemi ya fadi don yasan this time around expelling din ta za ayi, ya tambayi dalilin kiran ta sanar dashi cewa Jaleelah ce bata da lafiya gata nan sai kuka take yi. Hankalinsa ya tashi tuni yayi signing ya dauki excuse ya tafi zuwa daukanta.
Lokacinda ya isa ta galabaita sosai saboda aman data yi kusan sau uku. Kamar ya shiga cikin jikinta yake ji. Ni'imah ce ta taimake ta ta d'auko mata schl bag dinta fuskarta tayi kaca kaca da hawaye. Tana fitowa daga class din da kanshi yayi hugging dinta. Shi ya amsa schl bag din Mrs Kiyawa ta raka su har bakin mota suka wuce direct zuwa asibiti.
Bayan likita ya duba ta yayi prescribing mata drugs aka basu file da zasu je pharmacy suyi submitting a basu magani suyi making payment, kamin su fita likitan ya tambaye su "but are you couples?"
Taran numfashinshi tayi tace "no, he's my uncle", yace "okay".
Pharmacy suka nufa aka basu drugs sannan aka mata allurai guda biyu bayan ta sha malt.
A restaurant ya tsaya ya siya mata abincin da zata ci ta sha magani. Sai da ya jira taci abincin ya bata magungunan sannan ya koma wurin aiki da keys d'in saboda gate d'in da jamlock kuma zata yi bacci yayi locking gate din.
Saboda wuyar da taci sai almost 4pm ta tashi bacci tun 10:30am. Ji tayi kamar an yaye mata duk damuwarta da laruranta saboda yadda jikinta yayi mata sakayau sai dai swollen eyes.
Cornflakes ta sha sannan ta sha maganin rana ta koma ta sake bin lafiyar katifa. Ta kusa 1hr sannan ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta tsabtace jikinta ta sake kwanciya.
Da dare suna kwance akan gado kamin suyi bacci suna hira tace "uncle kasan me?"
Yace "ina dai jinki"
Tace "dazu naga Aneesah, ta tambaye ni wai ya kake?"
Yace "to ke kuma sai kika ce mata me?"
Tace "cewa nayi kar ta sake tambayana tunda ba d'an uwanta bane kai".
Shiru yayi for some seconds yace "kin san mene ne ma?"
Tace "a'a"
Yace "the next time you introduce me to anybody as your uncle zan bata miki rai"
Da mamaki ta kalleshi. Tace "but why?"
Yace "haka dai na fada miki"
Kwafa tayi don bata ga abin jin haushi ba a ciki ta juya masa baya ta ja bargo tareda fadin "good night".
[4/4, 8:11 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
27
By Linah Shams✍🏼
After two weeks
Yanzu kam rayuwa ta koma musu normal kamar yadda suke yi a baya sai da ta daina shigan k'ananun kayan da take yi koma saboda canjin weather. A schl kuma revision week suke next week zasu fara end of term examinations, suna samin hutu zata koma Kano amma sai ta fara zuwa gidansu tayi three days. Ba wani karatun arziki tayi ba tunda bata saba ba.
Kullum shi yake kaita schl ta dawo da kanta. Fridays kuma shi yake dawo da ita har suka yi exams d'in. Ranar da suka gama ta matsa mishi ita sai ya kaita gidansu da daddare kamar anyi mata wani mugun abun har sai da ya kaita.
Mommy har mamakin ganinta tayi at around 9PM kamar an koro ta, tace mata kwana uku zata yi on the fourth day zata koma Kano shiyasa ta damu sai ta zo.
Tare suke yin aiki da Mommy, girki da gyaran gida. Suna yi suna hira da dariya abinsu. Wani lokaci ne kawai Hadiyya take d'an taya su. Daddy ma ya sake da ita kamar ba abinda ya faru tun bayan da Mommy tayi mishi explaining komai.
Ranar da zata koma gida ta kama monday. Don haka yace da yamma zai zo d'aukanta idan ya ta so daga wurin aiki. Tun bayan da tayi sallar la'asar Mommy ta sata ta shirya don kar ta b'ata mishi lokaci. Bayan ta shirya ta d'auko jakarta ta dawo parlour, ta ajiye hijab d'inta a gefe tana ta kallon TV ba tare da tasan ma wani movie bane sai ga Mommy. Ta zauna akan seater tace "shi Khaleefahn har yanzu bai zo bane?", d'an b'ata fuska tayi tace "Mommy waye Khaleefah kuma?"
Tace "zaki mayar dani kakarki kenan"
Tace "to ai ban San wa kike nufi bane"
Mommy tace "ungo nan" ta mika mata d'akuwa. Dariya tayi tace "Mommy dagaske ban gane bane", tace "to mijinki"
Zaro halshenta waje tayi tace "waya ce miki Khaleefah sunanshi, AbdulHakam sunan shi"
Tsaki Mommy tayi tace "sai kiyi, hala shi Khaleefan sunan gaskiya ne"
Tace "wallahi Mommy dagaske ba Khaleefah bane, shi Khaleefah sunanshi Thabit, wannan kuma AbdulHakam"
Mamaki ne ya kama Mommy, tace "to how manage?"
Ajiyar zuciya tayi tace "hum! Shifa lift yake bamu a hanyar schl shine fa Daddy shima yayi tunanin wai Khaleefah ne, sai yayi mishi magana wai ya turo, yaji haushi sosai dama na fada mishi za a min aure a aura min mara mutunci shine sai ya TAIMAKE NI ya turo iyayenshi aka yi auren"
Shiru Mommy tayi and ran short of words don bata ma san me zata ce ba sai suka jiyo muryar Abdul yana ta zabga sallama. Jaleelah ce ta fita ta shigo dashi ciki suka gaisa da Mommy, har wani nauyinsa take ji. Sai da yaci abinci suka jima a gidan suna hira har sallar magrib a unguwar yayi sannan suka wuce gida.
A gida yayi dropping d'inta ko shiga ciki baiyi ba ya fita zuwa masallaci don ana kiran sallar isha. Itama sallahr tayi data shiga ciki sannan ta dawo main parlour ta zauna saboda tsoro. Yana shigowa yaci karo da ita har dariya ta bashi, yace "mene ne haka Jaleelah?", mik'ewa tsaye tayi tace "wlhy tsoro nake ji", yace "to ai gani na dawo, je ki hada min black tea ki kawo min waje ina cikin hut sai muyi hira a can". Gudu gudu ta had'a tea d'in ta sa a mug ta fito zuwa kawo mishi.
Iska ne ya nemi ya d'auke d'an d'ankwalin dake kanta tayi k'ok'arin jawo shi kar ya fad'i amma sai ya zamo kafad'arta. K'ok'arin mayar dashi kanta yayi sai mug d'in dake hannunta ya kufce ya fad'i k'asa yayi tatsatsa. Allah ma ya taimake ta bai kware mata a jiki ba kuma bai fad'i mata a k'afa ba.
Karar fad'uwar mug d'in ne yasa shi mik'ewa sai ya hangota a tsaye a wurin, da sauri ya k'arisa yaga abinda ya faru. Explaining kanta tayi sannan suka koma daga ciki ta sake hada mishi wani, amma this time around a dinning suka yi hira.
Washe gari da taje yi masa rakiya ya umurceta da ta kwashe broken mug d'in kar wani ya taka ya ji masa rauni. Koda ta koma daga ciki sam ta manta. Uzurorin rayuwarta ta dinga gabatarwa kuma koda ta gama bata tuna yace ta kwashe kwalban ba.
Rashin aikin yi yasa ta *hau uwa ba kwabo uba ba harara* wato gado kenan. Kallo bai cika damun ta shiyasa kullum bata da aiki sai na lotsa katifa. Bacci mai dad'i yayi awon gaba da ita. Tun daga mafarki ta ke jin sanyayyar iska na kadawa, curtains d'in d'akin nata swaying. Iskar ta tsananta tana ta k'ara dole ta farka daga bacci ta lek'a window taga hadari ya had'u a sararin samaniya yayi bak'i. "Subhanallahi wa bi hamdih, subhanallahil azim", ta fad'a tana k'arewa yanayin garin kallo. Ruwan sama a early December lokacinda aka fara sanyi, wani iko sai Allahu. Hankalinta bai dawo jikinta ba sai da akayi tsawa mai tsoratarwa. Dama yaya lafiyan giwa bare kuma tayi Hauka. Tsoro ya dabaibaye ta ta duba agogo taga it was already 2pm. Cike da jin tsoro tayi alwala tayi sallah don ta kasance mai jin tsoron ruwan Sama.
Da tsoron da take ji gara ma ta fita waje. Bumshot ta sa da yar vest ta nufi empty bedroom ta d'auko wani ragowan igiyar shanyan data gani few days back ta fita zuwa compound tana tsalle tana dariya. Skipping rope tayi da igiyar taje centern tsakar gidan tana tayi tana dariya kafafuwanta ko takalma babu. It was fun. Tasan there's no way AbdulHakam zai dawo gida yanzu bare ya ganta a cikin irin kayan da ya kira da tsinannu.
Dad'i ke d'ibanta tana kara buga tsalle. Skipping d'in ma ta koma mai crossing. Idan ta gaji sai ta tsaya tayi bowing tayi ta mayar da numfashi. Tana hutawa ko na minti biyu ne sai ta dasa daga inda ta tsaya. Saboda tsabar jin dad'i har ya bud'o gate ya shigo bata ganshi ba har yayi parking.
Daga mota ya tsaya yana kallonta sai tsalle take yi. Idan ta gaji sai ta d'aga kanta sama ruwa ya zuba sannan sai ta sa hannayenta guda biyu ta share tana wage baki. He was completely taken by her physique and was all of sudden horny, "you must be stupid AbdulHakam", ya fada a ranshi, "she's just a girl of 17years". Mood d'insa gaba d'aya ya sauya a haka ya bude motar ya fita. Yana fita daga inda ya ke ya ware murya yace "what do you think you are doing", tsoro ne ya kamata ta saki rope d'in ta sauri zata gudu. But unfortunately ko taku uku bata yi ta taka kwalban mug d'in data manta bata kwashe ba. Tsala ihu tayi ta durk'usa a wurin ta rik'e k'afar tana wooing. K'arisawa yayi cikin sassarfa shima ya d'urkusa, jini ya gani yana fitowa daga tafin k'afarta na dama. "Baki kwashe kwalban da nace ki kwashe ba kenan, ai gashi nan tunda baki jin magana. Look at what's on your body", bata ko d'aga kai ta kalleshi ba saboda azabar zafi ga kuma sanyin data fara ji. D'aukan ta yayi cak kamar jinjira ya wuce da ita har bedroom. A bakin gado ya ajiye ta sannan yayi lighting lantern saboda babu wuta. Kafar ya tsaya kallo tana d'igan jini ita kuma sai rawar sanyi take yi.
K'ok'arin cire kwalban da ta taka ya fara, ta sa hannu ta rik'e shi tana kuka a hankali mara sauti mai k'arfi, "uncle da zafi" haka take ta fad'a yana bata hak'uri har yayi nasaran cire mata sannan yasa tissue ya danne wurin. Rawar sanyi ta cigaba dayi tana hawaye, nan take zazzabi ya rufe ta.
Sosai ta bashi tausayi yace "kin gani ba? Gashi yanzu zazzabi ya kama ki and sai da nace ki kwashe kwalban nan baki kwashe ba, wannan shigar ma na hana ki yanzu duba duk jikinki a waje kanki ba scarf kika fita duk jiki a waje"
Runtse idanuwanta tace "uncle sanyi nake ki". Ta k'ara k'ank'ame jikinta ruwa na d'iga. Kayan jinkinshi yayi sauri ya sauya ya shiga bathroom Allah ya taimake shi ya samu da ruwa amma ba zafi sosai ya sirka mata. Koda ya fito ya kalleta yaga baya tunanin zata iya yin wankan ya dauke ta zuwa bathroom, duk a zaton ta ajiyeta zai yi ya fita amma taga ya rufo kofar ya fara kokarin undressing dinta. Ai nan ta ware idanuwanta ta kalleshi. Tace "uncle..." Bai kula ba tace "ka barshi zan iya", she felt like pushing him out amma ko saurarenta yak'i yi.
••°••Oh God! He was out of reach. Yau kam kasa hak'uri yayi and that fateful evening marked their first night duk da bata da lafiya (I don't need to explain)••°••
Da safe sai da yayi mata breakfast har gado ya kai mata saboda da k'yar ta sauka tayi sallah. Kunyarsa take ji yanzu kamar ta tsaga k'asa ta nutse. Shi kam tun yana blaming kanshi for been hard and most of all sleeping with her har ya gaji, "she's my wife, my right", ya dinga assuring kansa har sai da ya fara ji he need her more than ever, amma saboda tausayinta ma ba abinda zai iya mata, zai dai iya kissing soft lips d'inta. Bayan tayi breakfast ta sha pain killer saboda yadda jikinta yayi mata ba dad'i.Ranan ji yayi kamar kar ya fita saboda ya kula da ita sai dai ko waya ma bata dashi bare idan ya isa office ya kira yaji lafiyarta. Kamin ya tafi sai da yayi kissing d'inta for morethan ten minutes har sai da ta gaji ta kore shi. Ranan yana closing bai zame ko ina ba sai plaza ya siya mata sabuwar waya ya kawo mata. Lokacin har ta tashi ta dafa farar shinkafa taci da mai da yaji ta kwanta a nan. Duk ya k'osa ya shigo gidan ya ganta. Yana sallama ya ganta a kwance bai ma jira ta amsa ba ya k'arisa ya durkusa a gabanta yayi hugging dinta, har yanzu kunyarsa take ji, ya shafa kuncinta yace "ya jikinki?", hakanan ta daure tace "da sauqi", yace "baki ci abinci ba ko?", daurewa kawai take yi saboda kunya tace "naci"
"Me kika ci? Ba dai cornflakes ba?"
"Shinkafa da mai da yaji"
Mamaki yayi yace "kinji sauqi kenan"
Tayi nodding kanta alamar eh amma bai ce mata ko uffan ba sai murmushi kamar gonan auduga.
Washe gari ne ya kamata ta koma Kano amma Abdul yace ba zata je ba sai taji sauqi tafiyarta ta saitu. Wayar daya siya mata ya bata ya saka mata wani simcard dinsa da baya amfani dashi. Umma tun safe take kiransu taji labarin zuwa Abdul yace Jaleelar bata da lafiya, da kekasa kasa tayi tace ya dawo mata da yarinyarta tayi jinyarta da kanta ta San a nan ba wani kula da ita zaiyi ba, duk a zaton jikanta ne ke kan hanya, amma dai an kamo hanyar.
Kamar kwai haka yake lallabata ita kam da taga haka har sake narkewa tayi. Har mantawa da wata Raheemah yayi yana kula da halas d'insa. Sai da ta kwana uku sannan ta nuna mishi alamun jin sauk'i.
Ranan friday sai ya dawo daga aiki zasu tafi yayi spending weekend d'insa a can. Sai da taje tayiwa Ummansu Fadeelah sallama suka yi exchanging number da Fadeelar sannan ta koma gida ta shirya kayanta da abubuwan da zata yi amfani da su.
6pm suka isa Kano gab da kiran sallar magrib. Umma saboda farinciki hugging d'inta tayi tana ta mata lale marhabun da zuwa. Shi kam ko gaisuwar kirki basu yi ba ya je ya gaisa da Abbanshi daga can suka wuce masallaci sai after isha suka dawo.
Bayan sun dawo Jaleelah taje har part d'insa ita da Inteesar ta gaishe shi. Bayan sun ci abinci sun huta zuwa 9 Abdul ya buk'aci da ta tashi su koma gida, ita a zaton ta a nan zata zauna ta karisa hutun ta. Alamu ta dinga nuna masa na ita fa ba zata bishi ba don ko ba komai tana tsoron sake afkuwar abinda da ya faru cox he was hard kuma ita kadai tasan azaban data sha while shi kuma abinda ke ranshi kenan.
Sai da Umma tasa baki tace mata ranan Sunday zata dawo sannan ta yarda ta bishi tana ta fargaba. A cikin kwanaki ukun da suka yi ba k'aramin hanata sakewa yayi ba. Sallah kadai yake fitar dashi daga gidan tun tana jin kunyarshi har ta daina ji saboda yadda ya addabe ta.
Ranan Sunday da rana ya kaita gidan Umma bayan ya bata 5k ta samu na kashewa da keys d'in gidan ko da zata buk'aci wani abu sannan yayiwa gida sallama ya tafi tareda kewar 'yar matarshi, haka ita ma duk damunta da yake yi ji tayi kamar ta bishi su koma tare.
Yana isa Kaduna ya kira ta ya shaida mata. Gidan sai yayi masa fadi da rashin dad'i. Duk inda ya Shiga na gidan ita yake tunawa. She missed her troubles. Itama tayi missing d'insa for just one night sai tunaninsa take yi da abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin. Sai da ya kirata da daddare yaji lafiyarta ya tura mata good night text message.
Bayan ya tura mata yana zaune a inner sitting room ya lumshe idanu yana ta tunaninta yaji wayarsa ta d'au ruri wanda ya shaida masa shigowar kiran Raheemah, yasan yau da rigima don it's almost a week bai neme ta ba. Yana d'agawa ta cika mishi dodon kunni da "guess what honey!!!"
Jin bata yi mishi abinda yake tunani bane yasa he felt at ease, yace "baby kema kin san I'm not good at guessing"
Tace "okay okay! To I'm home honey.....!"
Mamaki yayi yace "amma ai lokacin dawowarki bai yi ba"
Tace "eh we just squeezed it out, dama surprise nake so na maka"
Nodding kansa yayi yace "you indeed surprised me"
"Nasan yau kana Kano and you'll probably show up"
"I just came back, you should have informed me earlier"
Bubbuga kafa tayi kamar yana ganinta, tace "to ai Kaine baka kirana, I doubt if you still love me"
Murmushi yayi tunda yasan ba son Jaleelah yake yi ba yace "ke inada patient ne shiyasa"
Tab'e fuska tayi tace "Allah sawwaka. Dama I thought you're in town ne shine na kira ka naji ko zaka yi attending welcoming party d'ina da Mom and Dad suka shirya min"
Bai kai ga cewa komai ba tayi hanging call d'in, shi kam tsaki yayi yana kallon image d'in matarsa duk sanda ya kifta idanuwanshi.
[4/4, 8:11 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
28
By Linah Shams✍🏼
Week d'in gaba daya spending dinsa suka yi cikin begen juna. Kullum sai ya tura mata text explaining how much he missed her tareda yi mata alkawarin zuwa duk weekend to check on her. Raheemah kuma jefi jefi suke waya duk da a haka kullum claiming sonta yake yi ya kuma yi mata alkawarin zuwa ranan friday ya dubata.
Da ita da Jaleelah duk suka k'osa Friday d'in tayi don isowarshi. Ita tana kewar masoyinta ita kuma dayar tana kewan mijinta.
••°••
Bayan sallar la'asar
Lace mai kyau ta d'auko maroon mai kwalliyar pink, milk da silver ta sanya. Light make over tayi sannan ta koma d'akinsu ita da Inteesar ta zauna tana jiran zuwan Abdul.
Ita kuwa Raheemah heavy make over tayi ta sanya english wears short dress da pencil trouser sai d'an k'aramin veil data d'aura a saman kanta daya sha gyara. Sannan tayi mishi girki na musanman.
Sai after Isha sannan Abdul ya isa Kano. Farincikin Jaleelah kasa b'oyuwa yayi har Inteesar ta fara tsokanarta. Amma a gaban Umma muk'us take yi bata nuna alaman ta damu bare tayi farinciki. Satan kallonta yayi tayi duk ya k'osa su bar gidan su koma nasu gidan ya nuna mata how much he missed her don a nan jin kansa yake a takure.
A haka har sai da yafi one hour a gidan sannan suka yi haramar tafiya. Bai ki ace ya bude ido ya Ganshi a gida ba.
A mota kasa jurewa yayi ya riko hannunta da right hand d'insa yana driving da left hand. A hankali yake caressing hannun. Ko cikakken three minutes ba ayi ba Raheemah ta kira shi, nan take ya sake mata hannunta yayi picking call yana mai tuna alkawarin da yayi mata. Cikin salo tace "honey ka fasa zuwa ne?"
Yace "a'a mene ne?"
Tace "ai na aza ka fasa ne saboda nasan yanzu baka d'auke ni da muhimmanci ba"
Yace "ni kam na d'auke ki da muhimmanci"
"Okay then prove it"
"I will baby"
Nan take ya yanke hanya zuwa gidansu. Da zai kalli idanuwan Jaleelah da yaga flames of jealousy dake ruruwa a cikinsu da b'acin rai, amma gaba d'aya ma mantawa yayi da existence dinta acikin motar bare yayi observing wani abu. He has been yearning to see this Angel's face, kusan wata takwas rabonsa daya sata a cikin kwayoyin idanuwansa.
Zuba ma sarautan Allah ido tayi yayinda da Raheemar ta sake kira ta sanar dashi cewa she will be at the gate waiting for his precious arrival.
Tun daga nesa ya hasaketa da fitulun gabar motarsa nan ta tsaya k'are mata kallo tun daga nesa har suka iso kusa. Babu abinda zata gwada ma Raheemah tun daga kyawun fuska da surar jiki. Gabanta ne ya fadi, if not tasan idan ba taimako ba ba yadda za ayi Abdul ya kyalla ido ya kalleta yayinda yake tare da tsaleliyar mace kamar Raheemah. Duk da haka she won't give up, she could do one to two things.
Sai da yayi parking a gefen hanya sannan Raheemah ta karisa da sauri zuwa kusa da motar shi kuma ya bud'e ya fita suna fara'a wa junansu, ji yake kamar yayi hugging d'inta. Itama Jaleelah bud'e motar tayi ya fita ta shiga tsakiyarsu ta tsaya, sai sannan Abdul ya tuno da ita. Marairaice fuska tayi hawayen da suka cika mata ido suka fara zuba, nan take ya susuce yasa hannayensa biyu ya tallafo fuskarta, "what's it?"
Cikin muryar shagwaba tace "bana jin dadi kuma bacci nake ji"
Damuwa ce ta bayyana k'arara a fuskarshi yace "baki jin dadi?"
Nodding tayi alamar eh, yace "yanzu to.... Mu tafi gida ne?", ta sake yi mar nodding alamar eh.
Daga kai yayi ya kalli Raheemah wacce tuni kanta ya d'au caji tana mamakin ko wace yarinya ce though ya fada mata yana da teen sister may be ita ce. Yace "baby bari mu wuce gida, we talk on phone okay?", bak'in ciki ne ya kamata taji kamar ta shak'e shi. Bai jira amsarta ba yaja hannun Jaleelah ya bud'e mata k'ofar seat d'in baya yace ta shiga zata fi samun balance. Ya shiga driver's seat sannan yayi winding glass ya kalleta, "ki gaida Mom da mutanen gidan", nan ma banza tayi masa duk da ba a son ransa yayi mata haka ba matarsa ce bata jin dad'i. Juyawa tayi ta shige gida cikin fushi tayi banging k'ofar gate shi kam tada motarsa yayi ya wuce.
Jaleelah ji take yi kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha saboda tsabar murna don tana kallon yadda Raheemah tayi fushi. Babu ciwon da take yi illa gaskiyar da ta fad'a masa cewa ita bata jin dadi, dama wace ce zata ji dadi idan hakan ya same ta.
Da kanshi ya fita ya bud'e mata k'ofar ta fito bayan sun isa gida, ya tambaye ta "zaki iya tafiya?", dariyarta ta gimtse ta fito tace "eh uncle", b'ata rai yayi yace "how many times should I tell you ki daina kirana uncle uncle...? How am I your uncle?", itama b'ata ran tayi tace "to me kake so na kira ka dashi?", yace "ko wace mace mahaifinta is her king, mijinta kuma is her prince saboda haka prince zaki dinga kirana", dariya tayi tace "prince d'in ina?", shi kuwa tsakaninshi da Allah yake magana, yace "prince d'in rayuwarki"
"Tab! To sai dai idan nima zaka dinga kirana princess"
"No wahala in dai zaki daina kirana wannan uncle d'in saboda kina diacouraging d'ina da sunan"
"To zan dinga kiranka my Ameer ni kuma your Ameerah"
"To naji, muje ki sha ko paracetamol ne kamin ki kwanta, ni nasan ma ba ciwon gaske kike yi ba"
Dariya tayi yayinda suka kama hanyar shiga gidan, tace "to ciwon me nake yi?"
Dariya shima yayi yace "tsoro kike ji ai na sani", sam ta manta sai yanzu, tace "a'a ba wani tsoro nida ma nake so na kwana kiyamul layl"
Murmushi yayi da ya bayyana muryarsa yace "ai sai kiyi"
Tace "idan na idar da sallar ma da azumi zan tashi gobe"
Sosai ta bashi dariya yace "duk zanji zan gani indai ina gidan"
D'aure fuska tayi tace "I'm serious", yace "to who isn't serious? ai yau kam I'll show you how serious I am"
Zare idanuwanta tayi tace "haba haba mana I'm sorry, kaji my Ameer", d'aga mata gira yayi yace "to kar ki damu, I will be less serious ba irin na farko bane".
••°••
Raheemah na shiga gida mai tsaye d'akinta dake upstairs ta nufa ko kallon gabanta bata yi. Mom bin ta tayi da idanu don ta saba da ganin haka kuma sau tari idan tana irin wannan fushin mahaifinta ne kadai ke iya bata baki ta hakura. Lambar wayar Aminyarta Sufayya ta nemo ta dokawa kira, bata jira tace komai ba cikin murya mai dauke da tashin hankali tace "girlfriend honey ya daina so na"
Sufayya tayi kwafa tace "as in? Ban gane ba, wani honey d'in?"
Tsaki tayi tace "ke wani honey kika sani bayan AbdulHakam?"
Tace "ayyoooo... Kice min Mr Airforce"
"Ji rashin mutunci kamar baki San shi ba"
Tace "a'a baby girl baza ki gane bane, abubuwa ne sunyi min yawa, yanzu me ya faru?", tace "girlfriend kar ki so kiga yadda ya dizgani a gaban wata yar fiqiqiyar yarinya"
Murmushi tayi tace "wace ce ita yarinyar?"
Shrug tayi kamar Sufayyar na wurin tace "dunno"
Ta sake tambayarta "to me yayi miki da zaki ce ya daina sonki?"
Tace "girlfriend kar ki so kiga kwalliyar da nayiwa bawan Allahn nan, har girki na masa da kaina wadda ko uwata bata sani amma wlhy yana fitowa yarinyar itama ta fito wai bata da lafiya su wuce gida, shi kuma kamar wani sakarai ya bita"
Dariya tayi tace "ai dama sakaran ne"
Raheemah ta had'e giran sama dana k'asa tace "wani irin wulakanci ne haka?"
Sufayya tace "ke fa kika fara zaginshi" tace "yo to baki bari na zagi abuna ni d'aya?"
Kwafa tayi tace "wai ke d'aya, haka kuka yi dashi cewa ke d'aya ce? Kaji wani wauta"
Ran Raheemah ya k'ara b'aci saboda bak'in kishin dake damunta, tace "pls wai meya sa kika tsani Abdul ne? Ko nice kika tsana?", tace "babe ban tsaneki ba shi d'in dai na tsana, ni jini na ne bai had'u da nasa ba", takaici yasa Raheemah ta kashe wayar gaba d'aya tana jin mugun haushin Sufayya. Ita kuwa Sufayya tun kamin Abdul yace yana son Raheemah take son shi har suka zo suka fara dating, taje ta nemi phone number d'insa ta fara kiranshi, zage ta yayi fesss sannan yayi mata concrete warning shiyasa ta tsane shi duk da Raheemah bata san me ya faru ba.
••°••
Washe gari da safe ta zauna ta nutsu ta kitsa duk abinda take so ya faru don bata k'aunar ganin Abdul ya rab'i Raheemah duk da kuwa tasan cewa eh dagasken taimakonta yayi amma sarai ta fara ture stupid idea d'in daga zuciyarta, mijinta ne ba saurayinta ba ko friend d'inta, ko yau d'ayansu ya kwanta ya mutu sai d'ayan ya gaji d'an uwansa.
Lik'e masa tayi throughout sai dai idan zashi sallah amma ta hana shi saqat kamar yadda yake hanata. Girki ma tare suke yi. Ita kuwa Raheemah already ta hau dokin fushi jira take yi ya kirata ya bata hak'uri amma shiru kamar Malam yaci shirwa. Gajiya tayi da jira around 5pm ta kira shi lokacin phone d'in na hannun Jaleelah, dariyar mugunta tayi mata sannan ta mik'a masa, tace "ga budurwanka nan tana kira"
Amsa yayi ya kara a kunnesa tare da fadin "hello" muryarshi a sanyaye cike da kwanciyar hankali, tace "ka kyauta ai"
Yace "da nayi me?"
Tace "oh tambayata kake yi"
Lumshe idanu yayi yace "kiyi hakuri to ko nayi laifi ko ban yi ba... I'm sorry"
Cikin fad'a tace "bazan yi ba! Hak'uri ba? To bazan yi ba"
Hankali a kwance yace "ke excuse me, don't sound like a boss here kina ji na? Ni ba k'aninki bane kuma ba d'an cikin ki bane, likewise I'm not working under you so don haka kar ki fara ki b'ata min ear drum"
**Supermamakious!!**, tace "Abdul, ni kake fad'awa haka?"
Gajeruwar dariya yayi sannan ya cire phone d'in daga kunnensa ya kalli screen d'in yaga dai it's obvious Raheemah ce, yace "ko baabata ce?"
Tsaki tayi tace "Mr man I'm sick of these your abrupt behaviours!! I can't help it anymore, let it be over"
Gira ya daga yace "oh really? Abin har ya kai ga haka?"
Cikin tsiwa tace "yama wuce! Bye".. Disconnecting call d'in tayi zuciyarta na k'una. Kuka ta fara yi ko zata samu relief.
Jaleelah xuciyar ta tayi mata fari tarrr. Yana ajiye wayar ta matsa kusa dashi ta kwanta a jikinshi tayi lamo kamar mage. Shirunta ne yayi yawa ya shafo wuyarta yace "Ameerah", a hankali tace "na'am", yace "is everything okay?"
Tace "ni Umma nake so na gani"
K'asa k'asa yayi da muryarsa yace "amma baki min adalci, kullum fa kina gidan Umma amma just three nights and two day time with me kina complaining gidan Umma, ko kin gaji da gani na ne?"
Gyara kwanciyarta tayi tace "my Ameer kasan mene ne?", yace "a'a", tace "from Monday to Friday kamin ka zo idan na rufe idanuwana kai nake gani. Friday evening kuma zuwa sunday idan na bud'e idanu na sai naga na ganka... You're all that I see", murmushi yayi yana jinta har cikin ranshi, yana jinta so special amma Sam bai taba kawowa a ranshi yana k'aunarta ba, itama a side d'inta hakane, amma banda kishi akanshi ba abinda take yi. Wasa da yatsun hannayenta ya shiga yi, yace "to meyasa kike so kije gidan Umma?"
Tace "ziyara zanje yi", yace "to kar ki damu ba next week zaki koma KD ba? To ranan Sunday sai muje ziyarar tare on Monday morning sai mu tafi da sassafe, okay?"
Tace "to Allah ya kaimu da rai da lafiya, amma da ina da ina zamu je?"
Yace "wuri da yawa, ke dai ki shirya.. Zamu gidan Aunty Safiyya (second born d'insu da yake bi ma), sai gidan Khaleel (first born d'insu), da gidan Mustapha, idan ma mun samu time zamu je gidajen su Basheer da Munawwar, sai gidan Aunty Yabi.. Infact wasu ma hanya zai bi damu"
Tace "innarududu d'in fa kenan, Allah ya kaimu to", ya amsa mata da "ameen my Ameerah".
••°••
Ranan Tuesday at around 5:30pm yana zaune yana making wani research yana amfani da system yaji shigowar message. Bris yayi da text d'in har sai da ya gama abinda yake yi sai kuma aka fara kiran sallar magrib. Tsallake wayar yayi yaje yayi alwala ya tafi masallaci. Sai da ya dawo sannan ya samu damar d'aukar wayar don bai zaci text mai muhimmanci bane, zungureriyar apology text ne Raheemah ta turo mishi, sai da yayi dariyarsa ma'ishi sannan ya cigaba da karantawa inda take ta bashi hakuri akan kalaminta, cewa ita she does not really mean it that it was a slip of tongue. Bayan ya gama karantawa ya tura mata da reply kamar haka "to be frank baby I was so upset with you, ya kamata ki dinga tunawa ni ba k'aramin yaro bane and.. There is no innocent one in this game for two. Duk irin abubuwan da kike min ban tab'a ce miki ta tafasa ba amma ke kawai da rana tsaka kice zaki min rashin kunya. However, I still love you Raheemah"
Kunyar kiransa tayi saboda ta d'an yi maintaining class d'inta as a lady, lokacin da reply d'in ya shigo mata tana kwance a cinyar Mom a bedroom d'inta, tun kamin ta karanta tayi ihu tace "oh Mom!", Mom tace "lafiya", ce mata kawai tayi "honey ne". Bayan ta bud'e text d'in ta karanta ta tura mishi da reply :"I'm so sorry dear, wannan yarinyar ce tayi upsetting d'ina and I felt offended"
Koda ya karanta shima ya bata reply :"don't ever be upset or feel offended. Wannan yarinyar da kike gani means a lot to me kuma amanar Allah ce a gare ni, gara ki sawwak'e ma rayuwarki"
Bata kawo komai a ranta ba duk a zaton ta Inteesar ce ta k'ara tura masa da text sai bashi hakuri take yi yace mata everything is alright, har wani yanga yake mata duba da yadda take ta bashi hak'uri.
[4/4, 8:11 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
29
By Linah Shams✍🏼
A cikin week d'in sosai sukayi waya da Raheemah suka sami fuskantar juna. K'orafi tayi mishi akan rashin son zuwanshi ya ganta yace mata next weekend idan ya zo in Allah ya yarda zai zo. Wannan rana ne na musanman a wurinta don ji take kamar ta jawo ranan.
Jaleelah ma bai manta da ita ba, kusan kullum sai sunyi waya sau hudu sau biyar. Kullum cikin kewar juna suke, amma dai ai k'arshen tika tik ne, wannan zuwan tare zasu koma.
Ranan friday ta nemi izinin fitanshi suka fita zuwa kasuwa da Inteesar ko don taga gari don bata tab'a fita ba on her own sai dai tare da Umma. Rasa abin siya tayi ta k'are a siyo cover d'in waya, ribbons, da head bands, sai gurasa falle shidda data siyawa Ummansu Fadeelah tsaraba. A hanyar dawowarsu ne suke hira da Inteesar tace "Inteesar ban baki labari ba", itama da ba k'afar baya bace wurin surutu tace "shafa min sis"
Tace "uhuhum.... Ke dai bari kawai, kin san uncle Abdu nada budurwa, wai last week friday da zamu koma gida saboda ya raina min wayau wai ina cikin motar ne zai yi tad'i"
Inteesar tace "baki fita kin wawwanke ta da mari ba?"
Sakin baki tayi tace "ke! Bafa k'aramar yarinya bace, wannan ta kusa 24 idan ma bata fi ba"
"And so? Ita bata da hankali ne dududu yaushe kuka yi auren?
Jaleelah tace "gata zuk'ek'iya ina fad'a miki, kyakkyawa ce ajin farko", tsaki Inteesar ta ja tace "ni kin ma fara bani haushi, sai wani kod'a ta kike yi, hala ke ba mace bace"
Jaleelah tayi murmushi tace "ke raba ni, idan za ayi aurensu ai zaki fidda mana da anko"
Inteesar ji tayi kamar ta kwashe ta da mari haushi ma ya hanata magana, Jaleelah tace "but please let's be serious, dan Allah kar ki fadawa Umma"
Tace "ba don kin ce don Allah ba da wallahi sai na fad'a mata, haba! Ai ya jira a kwana biyu, ni Ya Izuddeen ma nake ta so ya fitar da mata ya daina cinye mana tuwon gida"
Dariya Jaleelah tayi tace "ke dai kika sani, Allah yasa ya jiki"
A waje suka had'u da izuddeen d'in, suna hangoshi Jaleelah ta fara dariya. Yana isa gab da su yace "daga ina haka?", Jaleelah tace "kasuwa. Sai ina haka?", yace "gidan Mardiyya za ni", Inteesar tace "na zo mu je", harararta yayi yace "to muje mana", d'aure fuskanta tayi tace "Jaleelah mu wuce", Jaleelah tace mishi "to a dawo lafiya, pls ka gaishe ta" ya amsa mata da insha Allah.
Khaleel shine first born d'in gidan, sai Safiyya, sai AbdulHakam, sai Mardiyya, sai Izuddeen then autarsu Inteesar.
Da daddare bakinta yayi ta mata k'aik'ayi tana so ta bama Umma labari amma sai ta tuna Jaleelah ta rok'e ta kar ta fad'a amma k'iris ya rage ta fad'a saboda yadda abin ya dinga cin mata rai.
Ranan Friday Abdul ya dawo spending weekend d'insa as usual. Tun ranar saturday suka fara aikin ziyararsu har ranar sunday. Sun je gidaje da yawa wasu na yan uwa wasu kuma abokananshi. Wani gidan idan suka shiga suyita janta da surutu idan taji zata iya tayi responding ko tayi murmushi kawai. Ranan sunday da suka fita tun after 10am sai after magrib suka koma gidan Umma saboda gobe da sassafe zasu tafi.
Abincin da Umma ta dafa suka ci suka yi mata hira har past nine sannan suka yi mata sallama suka je suka yiwa Abba, sai kuma next vacation zata dawo shima zuwarsa duk weekend ba tabbas. Inteesar ji tayi kamar ta bita su koma tare saboda sabo da juna da suka yi.
A hanyarsu ta komawa gida Jaleelah ta kalleshi ta gefen ido, tace "Prince Mr Airforce d'an ara min wayarka"
Yi yayi kamar bai ji ta ba yace "mene kika ce?"
Tace "cewa nayi my Ameer d'an ara min wayarka"
Hankalinsa na kan tuk'i yace "banida caji, kuma ina so zan kira Raheemah"
Tab'e fuska tayi bata sake ce mishi komai ba taga ya d'auki hanyar zuwa gidansu Raheemar, a d'an fusace tace "ina zamu je?"
A kaikaice ya kalleta yace "gidansu budurwata"
Tace "but ai kana ganin dare yayi kuma zan je na had'a kayana kana sane ban had'a ba"
Cije leb'e yayi yace "ammm ina fata ba dai fad'a kike min ba"
Turo mishi baki tayi tana kunakunai har suka isa layin gidan ya samu wuri yayi parking. Kallonta yayi yace "bari na shiga bazan dade ba kinji my Ameerah?"
Kawar da kanta gefe tayi tace "kuma dama kayi sauri"
Bai saurareta ba ya fita ya shige gidan.
Abin duniya ne yabi ya dame ta, ta rasa me zata yi ta ji dad'i. Hakanan ta saduda ta cigaba da zaman jiranshi har k'arfe goma, ta kira wayarshi taji switched off. Tana gama kira call din Umma ya shigo, da farincikinta ta d'auka tace "hello Umma.."
Umma tace "na'am.. Kinga na mance ban baki turaren wuta da humran da Hajiya Kareemah ta aiko miki dashi ba gashi kuma kunce tafiyar sassafe zaku yi"
Tace "eh Umma"
Tace "to bari, bari na aiko Izuddeen ya kawo miki amma Ku bar gate a bud'e kar ya zo yayi ta knocking"
Murmushi tayi cikin makogoro tace "Umma ai bama gida yanzu"
Tace "tohhh! Ina kuka je haka? D'an Alhajin ma inata kiranshi wayar bata shiga"
Tace "eh bashi da caji ne"
"To yanzu kuna ina ne haka?"
Tace "yaje gidansu budurwanshi ne, ni ina waje ina jiranshi ya fito ne"
Har wanni amsa kuwwa kunnenta ke jiyo mata, tace "budurwa kika ce ko me?"
Tace "eh Umma"
Inteesar na daga gefe tana jinta, tace "to kiyi maza maza ki shiga gidan nan ki ce mishi nace ya fito ya zo ya wuce idan ba haka ba sai ranshi ya b'aci, ke kai mishi wayar ma" ta fad'a cikin fad'a
Ai da sauri ta bud'o murfin motar ta fita knocking d'aya biyu gateman ya zo ya bud'e mata cikin ladabi tace "dan Allah zan d'an ga AbdulHakam ne", ba musu ya matsa mata ta shiga sannan ta roke shi ya nuna mata inda yake.
Ita kuwa Umma tana cire phone d'in daga kunninta ta fara fada kamar me, Inteesar ce ta katse ta tace "ai Umma ba yau ya fara zuwa tad'in ba tunda rannan ma da zasu koma gida sun je, Jaleelar take ba ni labari"
Izuddeen dake gefe yayi kamar be san me ake yi ba ya jefeta muguwar harara, yace "munafuka kawai", tab'e baki tayi alamar ko oho ita dai ta fad'a. Umma tace "ba zancen munafirci, zai ci uwarshi da ni kuwa, idan ba rashin hankali ba kwana nawa da yin auren na shi? Sakarci banza kawai!"
Tuni suka yi nitso da nink'aya a cikin kogin masoya sai tsinke fure suke yi. Shi gaba d'aya ma ya manta da wata Jaleelah sai da yaji sallamarta ba kuma ta jira sun amsa ba ta shiga cikin parlourn. D'aga kai yayi yaga it was 10:30pm kamin ya tambayeta me ya shigo da ita tace "gashi Umma tace za kuyi magana", tana mik'a mishi yayi dialling numbern ba tare da b'ata lokaci ba Umman tayi answering, har wani sadda kai yayi kamar yana gabanta yace "hello Umma"
Bud'an bakinta tace "zaka ci ubanka da ni d'an Alhaji, ashe baka da hankali ban sani ba? Haukan naka har ya wuce iya misali? To kayi maza maza ka tashi ka wuce gida na fad'a maka ko inci mutuncinka billahil azeem", b'oye b'acin ranshi da damuwarshi yayi yace "to Umma" saboda baya son Raheemah ta gane abinda ke faruwa. Kallon Jaleelah yayi da slight b'acin rai yace "je ki gani nan zuwa", tace "to bani wayata", tunanin kar ta k'ara haddasa mishi fad'an Umma yasa yace ba zai bada ba ta wuce ta tafi. Ta gefen ido ta kalli Raheemah tayi mata murmushi tareda kashe mata ido sannan ta fita tana jin wani irin matsanancin dad'i duk da bata san me Umma tace mishi ba. Tana fita Raheemah ta mayar da dubanta gare shi tana huci, tace "AbdulHakam just be real! Wannan wace irin tsinanniyar yarinya ce? A ina ka samo ta or is she your security agent? I don't understand. Ya za ayi ka dinga yawo da ita duk inda za ka? Ko housemaid d'inka ce ai a gida ya kamata ka barta kuma sannan har tana da guts d'in da zata kashe min ido? Ba zai yihu ba, ka fad'a min wace ce ita or else wlhy yanzu zan fita sai naci k'aniyarta"
Rasa mai zai ce mata yayi, yace "I'm sorry, Ameeran guda nawa take da zaki ci kaniyarta, yanzu kinga ai munyi hirar ki bari zan sake zuwa but for now gida zan tafi kinga Umma ta kira", kallonshi ta tsaya yi yayinda ya tashi ya zira takalmansa ya fice daga gidan.
Ajiyar zuciya yayi yayinda ya shiga motar, yace "me kika fada ma Umma?"
Tab'e baki tayi had'e sa shrug tace "ta kira bata same ka bane shine nace kana ciki wurin budurwarka"
Yace mata "why?"
Tace "dana tambayeka ina zamu ai cewa kayi gidansu budurwarka zamu, or what do you expect me to say?"
Ji yayi kamar ya mareta saboda yadda tayi mishi magana. A tare suka isa gidan da Izuddeen da yaje akan mashin roba roba, yana mik'a mata sak'on yayi musu sai da safe ya wuce. Suna shiga gidan ta fara harhada kayanta saboda tasan idan bata yi yanzu ba dole zasu yi makaran komawa kuma hakan zai sa tasha masifarsa saboda abinda ya faru shi kuwa sai shan kunu yake yi. Ko kallonshi ma bata yi saboda ita dad'i take ji.
Washe gari haka suka wayi gari ba mai ce ma kowa komai. Ko wannensu sai sha'anin gabansa yake yi ita kuwa Jaleelah da ka ganta kaga wacce ta kwana farinciki, haushi AbdulHakam ya fara ji saboda ya lura bata ma san yana fushi da ita ba, duk yadda ya so yaga ranta ya b'aci abin faskara yayi hakan shima yayi banza da ita. Bata tashi gaishe shi ba sai da suka hau kan highway from Kano to Kaduna. Zaman cross leg tayi tace "Mr Airforce ina kwana"
Wata muguwar kwafa yayi ya girgiza kai, yace "idan kin ganshi ki kamo min shi"
Wani irin dariya mai mugun cin rai tayi "ihihihihi", ai kuwa ranshi ya b'aci, shi haushin shi d'aya ita ma ya kasa b'ata mata rai, amma yasan maganinta.
Banza tayi mishi a motar ko kallon inda yake bata sake yi ba, shi bai san reply d'in daya bata ya masifar b'ata mata rai ba shine ta binne shi tayi dariyar rainin wayau. Games tayi ta bugawa da wayarta har caji ya k'are sannan ta d'auko nashi zata yi amfani dashi. Da sauri ya cafko mata hannu yace "ajiye min wayata", b'ata fuska tayi tace "pls ka sake min hannu mana ji yadda ka rik'e ni", matse mata hannu yayi ya sake cewa "ajiye min wayata", cikin muryar kuka tace "shi mutum da wayar mijinshi amma ka wani matse min hannu", dariya ta bashi hakanan ya sake ta. Bata yi zuciya ba hakanan ita ma ta cigaba da accessing wayar har suka isa gida around 7:30am. Bai k'ara ko 15mins ba a gidan ya fita zuwa Base.
Ita kuwa kwanciya tayi ta samu baccin safe, kamin ta kwanta tayi plugging wayarta a caji. 9:30am ta farka daga baccin ta shiga toilet ta gabatar da uzururrukanta and freshen up sannan ta fito. Wayarta ta kunna ta kira Mrs Maryam suka yi hira kad'an sannan ta shaida mata resumption d'inta ranan wednesday. Numbern Abdul ta kira wanda ya samu muk'ami daga Uncle Abdu zuwa My Ameer. *tsakanin mata da miji sai Allah*, hira suka dinga yi suna dariya kamar ba abinda ya tab'a had'asu sannan ta fad'a mishi bayan sallar Azahar zata shiga gidan Ummansu Fadeelah ta kai mata tsarabar gurasar data siya mata ya yarje mata.
Kamin ta tafi sai da ta kira Fadeelar ta tambayeta ko tana nan tace mata tana nan amma Umma tayi tafiya, taje Gombi Baffanta ya rasu. Da taje sai da suka ci hira ma'ishi sannan ta bata tsarbar, tace "ba yawa, kin san ban san adadin 'yan gidanku ba shiyasa", murmushi tayi tace "ai bamu da yawa, daga ni sai Umma da Abba da Ya Hassan"
Tace "baku da yawa kenan ma, shi yayan baya nan ne?"
Tace "a'a yana nan, ya tafi asibiti ne da yake doctor ne"
Jinjina kai Jaleelah tayi tace "uhum! Yayi kyau"
Fadeelah tace "dama kar kiji a gari kice ban fada miki ba, aure na saura wata d'aya"
Dariya tayi tace "iyye! Ammarrya! Allah sa dai a nan kusa zaki zauna"
Tace "eh a'a. A unguwan Rimi zamu fara zama after two months zamu wuce Canada"
Jaleelah tace "Allah ya kaimu da rai da lafiya"
Ta amsa mata da "amin". Har bakin gate tayi mata rakiya.
Kamin ta shiga gida ta hangi wata yarinya mai tallar cabbage tana zuwa. Tsayuwar jiranta tayi ta jirata suka shiga gidan tare. Cabbage da cocumber da su carrots ta siya zata yi coleslaw saboda rice and stew take da ra'ayin dafawa. Ita kuwa mai talla dad'i kallo Jaleelah ta kunna mata Indian film, dama tallar ta kusa k'arewa ta karya kwankwaso ta zauna tace ta kawo cabbage d'in ta yanka mata. K'yama ta bata, saboda ba yadda za ayi ta bari wannan yarinyar ta yanka mata cabbage Ameer d'inta yaci, ta dai iya bata carrots ta kankare mata suna yi suna d'an hira har sai da Jaleelah tace mata ta tashi ta tafi gida tayi shirin islamiya tunda la'asar tayi.
Hadaddiyar Rice and stew tayi da coleslaw, sai coconut and dates drink da condensed milk data saka a fridge yayi sanyi sannan tayi setting dinning table d'in ta kawo cutleries ta ajiye abun gwanin ban sha'awa. Sai around five minutes to five Abdul ya kira ta bayan tayi wanka taci kwalliyarta cikin d'aya daga cikin kayan akwatinta. Sai ta fito a amaryarta. Sai wani yauqi take yi da tayi picking call d'in, yace "My Ameerah", itama tace "My Ameer", yace "do me a favour", tace "me ya faru?", yace "kar ki tsaya jirana na dawo muyi girki tare, dan Allah ki d'aura zan yi bak'i ne"
Tace "daga ina?"
Yace "ba daga nesa bane, colleagues d'ina ne"
Tace "har su nawa ne?"
Dogon numfashi ya saki yace "su biyu ne"
Ta sake cewa "but banda matayensu ko?"
Yace "eh ban da su"
Tace "to shikenan sai ka dawo, ka dawo da wuri kaji? Pls don't be late"
Yace "okay Ameerah, do take care pls, stay safe"
Tsintar kanshi yayi da kissing screen d'in wayar bayan call d'in yayi disconnecting.
Abincin taje ta duba taga for sure zai ishi mutum biyar in dai cin musulunci zasu yi sannan ta d'auko wanda zata ci data sa a plate da cup d'in drink ta koma inner sitting room.
⚜Mijin Jaleelah⚜
30
By Linah Shams✍🏼
Ita kam yau burinta shine ta burge AbdulHakam duk da dai irin tips d'in da Mrs Maryam take bata da yadda Fadeelah ke zuzutata. Bayan ta kammala abincin ta shige bedroom ta tsaya a gaban dressing mirror. Kallon kanta tayi tayi a mudubi har sai da ta tabbatar kwalliyarta tayi kyau komai ya ji. Bathroom ta shiga ta hada mishi ruwan wanka don tasan any moment from now zai iya shigowa sannan ta dawo ta fiddo mishi da kaya. Tsadajjen navy blue din yadi da ya sha aiki ta fito mishi da shi, shima dole sai yayi mata kwalliya kamar yadda tayi mishi, shima miji ai ya kamata atleast ya dinga yiwa matarsa kwalliya. Har da hula ta had'a da komai da zai canja idan ya fito wanka ta ajiye daga gefen gado. Murmushi tayi had'e da k'ankame jikinta tace "yesss!", saboda yadda ta yaba da kokarin kanta. Kai tsaye ta fito zuwa sitting room don zaman jiran shigowarshi amma sai fitowarta yayi daidai da shigowarshi. Murmushin nata na yau ma with class ne don had'e yake da yana yi na jan girma. Murmushi yayi mata ya ajiye brief case d'insa a kan seater yayi spreading arms d'insa, tana mai murmushi ta isa gare shi yayi hugging dinta. Yana sakinta ta dauki brief case din tace "sannu da dawowa", ya amsa mata da "yauwa, sannu da gida". A tare suka dunguma suka nufi bedroom din, sai jira take yi taji yace tayi kyau amma yayi muk'us. Bata nuna mishi damuwarta ba ta ajiye briefcase din kan bedside drawer shi kuma ya zauna akan sofa. Tips din Mrs Maryam suka dinga mata yawo a ka ta furzar da iska a ranta tace "I'm also a woman. I know my husband..", karisawa tayi kusa dashi ta zauna, tace "Ameer ka gaji ko?", ya jinginar da kansa jikin backrest yace "sosai Ameerah, gashi ma nayi latti nayi committing laifi, kince na dawo da wuri", matse baki tayi tace "eh to, yanzu dai sai ka rubuto apology letter not less than 500 words", murmushi yyi ya jawo hannunta, yace "okay madam, yanzu kiyi unbuttoning min wannan uniform din zafi nake ji"
Karkatawa side dinsa tayi tana unbuttoning din, tace "wanka zaka yi amma", yace "da ruwan ne?"
Tace "eh na had'a maka", lumshe idanuwanshi yayi yana jin dadi a ranshi. Amfanin aure kenan, ka dawo gida ko kai ba kowa bane mace tayi treating dinka kamar Sarki, amma fa abin dace ne.
"To kaje kayi", ya bude idanuwansa ya sauke su akan soft lips dinta da suka sha crimson lipstick. A hankali ya kai thumb dinsa kan lower lip dinta ya shafo lipstick din, ita dai bata ce mishi komai ba sannan ya murje shi da ring finger dinsa. Sake kai hannu ya dangwalo yayi ta matsar da kanta, tace "uncle..", yace "ai bakinki ne uncle din", ta turo mishi baki tace "to kaje kayi wankan mana", sake gyara zama yayi yace "muje tare", dariya tayi ta mike da sauri ta fita ta bashi wuri. Kintatan lokacin da ya fito tayi ta koma duba shi, taga ya tsaya a gaban wardrobe yana kallon kayan, muryarta kawai yaji tace "ga kayanka nan akan gado", ya waiga ya kalli kayan ta gefen ido sannan ya rufe wardrobe din, yace "ya za ayi nasa wa'innan kayan?", tace "to ni dai su nake so ka sa", rike kugunsa na hagu yayi yace "hala ni na zaba miki naki", ta daure fuska tace "me yayi zafi harda bakin magana, ka zaba wanda kake so to", banza ya mata yace "anyway.. Zo ki samin", hade gira tayi tace "tsayi na ba zai kai ba", yace "to je ki samo stool ki dawo", tace "to, amma ka fara sawa kamin na dawo"
Sai da ta d'auki almost ten minutes sannan ta koma lokacin ya gama shiryawa yana kokarin saka riga, tace "stool d'in yayi min tsayi da yawa Ameer", tace "it's okay, zo ki taka gado ki sa min buttons din, I always understand you"
Dariya tayi taje ta haye gadon ta sa mishi buttons din, hakan ya bashi damar kallonta son ranshi, sannan ta dauko hular ta sa mishi ta sauko kasa. Murmushi tayi mishi tare da yi mar fari da idanu, tace "kayi kyau", shima murmushin yayi mata amma tana expecting yace wani abu than just a thank you. She couldn't help it ta matsa gab dashi tareda b'ata fuska, tallafo fuskarta yayi yace "mene ne?", tace "ni baka ga nayi maka kwalliya bane baka ce komai ba"
Murmushi yayi daya bayyana sautin muryarsa, yace "na gani mana kuma kinyi kyau sosai my Ameerah"
Sake b'ata fuska tayi tace "banyi ba, nasan da nayi da da kanka zaka ce"
Yace "kema kin san kiyi kyau, kuma nima na sani, har kyauta ma zan baki saboda na yaba da kwalliyar bare ma it's purposely done for my sake, kuma nima gashi nayi miki kwalliyar har kin yaba"
Tace "kyautar mene ne?"
Matso da fuskarsa yayi gab da nata yana mai niyyar kissing dinta ta ja baya tana dariya, binta da idanu yayi yana admiring dinta. Wayarsa dake kan table din dake gaban sofa din da ya zauna ya fara ringing, da kanta ta dauka ta kai mishi yaga call din Sha'aban, amsawa yayi, call din ko lasting five seconds bai yi ba. Ya kalle ta yace "bari naje na shigo da su, amma ya labarin abincin fa?"
Tace "muje ka gani"
Tare suka fita zuwa dinning hall ya duba abincin sannan ta dauko masa drink din data hada ta ajiye. Sosai ya yaba da kokarinta ya riko hannunta, yace "yau kam zan baki babbar kyauta Ameerah"
Tace "in dai irin kyautarka ce to na yafe"
Murtuke fuska yayi yace "waya fad'a miki mace na rejecting kyautar mijinta?" Sannan ya matsa daf ta ita yayi mata rad'a a kunne, cike da jin kunya ta rufe idanuwanta tayi saurin wuce shi zuwa bedroom shi kuma ya fita shigo da abokanansa.
Tun daga hanya suke yi masa tsiya wai har wani fresh yayi shi kam sai dariya yake yi har suka isa. A main parlour ya ajiye su suna ta barkwanci, tun daga bedroom take jiyo muryoyinsu. Sai da suka gaisa sannan yaje da kanshi ya dauko musu abincin dake kan dinning ya kawo musu har inda suke sannan ya koma ya dauko musu drink din data hada. Bedroom din ya koma ya tarar da ita a zaune tayi zugum ya zauna a gefenta, yace "meya same ki kuma?", tace "ba komai, ara min wayarka na buga candy crush", bai musa mata ba ya bata sannan ya koma wurinsu.
Kamar jiran fitansa call din yayi, yana fita call din na shigowa, ko da taga Raheemah ce bata wani damu ba, saboda wani lokaci tana tunawa ita ce wacce ya so ya aura ba ita ba, ba tareda ta ji ko d'arr a ranta ba tayi picking call din tareda sallama. Raheemah was slightly confused, for the first time da taji muryar mace yayinda ta kira AbdulHakam, kuma tasan baya Kano bare ace ko teen sister dinsa ce, kasa amsa sallamar tayi tace "ina mai wayar?"
Tace "yayi bak'i ne"
Tace "okay, but ke wace ce?"
Jaleelah tace "ba huruminki bane, amma idan kina da sak'on da kike so a fada masa ne ki fada alabarshi idan bakin sun tafi sai na fada masa".
*Gaga!!*
Tace "excuse me baby girl, who the hell do you think you are da har zan kira AbdulHakam kice na fada miki sak'on da zan fada?"
Ko kadan Jaleelah bata ji haushi ba, tace "this simply means baki da abinda zaki fada mishi"
Raheemah tace "kin san ko wace ce ni kuwa? Firstly ma uban mene ne tsakaninki da saurayi na?"
Yar gajeruwar dariya tayi tace "ina ga to wrong number kika samu"
Cikin tsawa tace "how dare you!!!"
Cikin sanyin murya tace "to ai gaskiya na fada miki, domin wannan lambar da kika kira lambar wayan MIJIN JALEELAH ne and I'm adamant sure mijina ba shi da budurwa"
Kwakwalwarta gaba daya ta rikice, tace "mijinki for where? Kaga min yar iskan yarinya yan matan banza, kadangarun bariki ko? Wato yaje Kaduna har mace yake ajiyewa, ko ki kai mishi wayar ko inci miki mutunci ta inda baki taba tunani ba"
Sai yanzu taji haushin abusive words dinda tayi amfani da su a kanta, tace "ya isa haka malama, naga kamar ba wani wadataccen tarbiyyar arziki kike da shi ba"
Raheemah ta katse ta tace "sai dai uwarki ce me wadataccen tarbiyya ko"
Jaleelah tace "tabbas kuwa baby girl, ke kuma uwar taki fa? Da kuma kika kirani da kadangaruwar bariki, kije ki tambayi ita uwar taki, aminiyata ce a harkar barikin, jaka kawai" ta karishe maganar da hiss sannan tayi gaggawar disconnecting. Sake kira tayi amma Jaleelah taki picking don kar ta fada mata maganar da yafi wanda ta fada mata zafi, sai gashi ta tura mata text kamar haka
"Banza karuwa kawai. Ai da kin sani baki yanke kiran ba dana gwada miki yadda ake cin uban yan Tasha a kwana lafiya. Karamar yar iska kawai, ni bana harka da kananun yara irinki but idan suka shiga sabgata I make sure I beat the tar out of them.. Stupid daughter of a bitch"
Hawayen bakin ciki ne ya taru mata a idanu sai ga AbdulHakam ya shigo amsar wayarshi. Ko da yace ta bashi wayar bata amsa mishi ba ta mika masa ba tareda ta fita daga inbox din ba ga mood dinta da ya canja. Daga ganinta akwai matsala. Karanta text din yayi for an umpteenth time yana kallonta. Hawayen ne suka gangaro ta sa hannu ta share cike da kunar rai. Bata ko kalleshi ba ta tashi zata bar d'akin ya riko ta ta fada kirjinsa ta fashe da kuka, ranshi b'aci yake yi hade da fitan sautin kukanta. Sai da tayi me isanta sannan ya zaunar da ita a kan sofa ya share mata hawayen, yace "ya isa haka, me ya hada ki da ita?"
Kasa magana tayi hawaye ya sake fitowa daga idanuwanta ita ta manta zagin da tayi mata, tace "kira kawai tayi nace kayi baki tace na kai maka, shine nace idan tana da sako ta fada na fada maka shi kenan ta fara zagina"
Sake share mata hawayen yayi yace "to ya isa haka, ki daina kuka I will talk to her, okay?" girgiza masa kai kawai tayi shi kuma ya tashi zuwa yi ma abokansa rakiya, dama ya zo kiranta ne su gaisa, yace "kije kiyi sallah, okay?"
Har riga shi tashi tayi ta wuce abinta.
A waje suka yi alwala duka suka tafi masallaci Sha'ban da Mufeed suna ta masa tsokanarsa suke akan yaki bari Madam din ma ta fito su gaisa saboda kar su gane mishi ita. Shi kuwa hankalinshi gaba d'aya ya karkata zuwa wurin Raheemah saboda yau sai yaji dalilin da zai sa ta kira matarsa ta zage ta.
Daga masallaci suka yi sallama da su Mufeed don sun ki yarda su bishi su koma saboda ko wannensu mai iyali ne yana so yaje ya gana da Madam.
Akan wata rubber chair dake balcony ya zauna. Numbern Raheemah ya kira yaga ansa mishi call waiting, hakan kuma bai hana ta yanke wayar da take yi ba don amsa nashi, ita ta fara magana a hasale tace "matsiyaciya kin kai mishi wayar ko yaya?"
Shiru yayi mata ya kasa amsawa yana mamaki tayi ta cewa hello hello yayi mata shiru, tsaki tayi ta kashe wayar sannan ya sake kira, this time da tayi picking bata ce komai ba shi ya fara magana ta hanyar kiran sunanta sannan
yace "rashin mutuncin naki har ya kai haka?"
Tace "me nayi kuma?" Yace "meya sa zaki kirata ki zage ta?", tace "ita wa kenan?", yace "Ameerah mana, meya sa zaki zage ta", cikin fushi tace "ba sai ka rama mata ba, kaje ka ajiye yar iskan yarinya sannan har kana da bakin da zaka hana ni zaginta, to hell with her!"
Abdul yace "to naji, amma there is this fact; I'm a man of honour Raheemah, idan ni dan bariki ne ai kema kin sani idan kuma akasin haka ne ma kin sani. I'm surely a man of honour, saboda haka ba zaki dinga kiran matata kina zaginta ba"
Tace "matarka ta ina?"
Deep sigh yayi yace " honestly speaking I can't stand it Raheemah matukar zaki dinga kira kina zagin min mata this relationship must come to an end"
Mamaki ne karara shimfide a fuskarta da har ya bayyana a muryarta, tace "Abdul dama ka iya aure? Dama yaudara ta kake yi? For how many years ina jiranka?"
Girgiza kansa yyi kamar yana gabanta, yace "Raheemah for how many years ina jiranki dai, kuma kamin ki dawo Allah ya riga da ya qaddara aure na, kuma bana tunanin hakan zai iya hana ki aure ni"
Hawaye ta fara yi, tace "amma pls kar ka fada min tsinanniyar yarinyar nan ce matarka"
Yace "I'm sorry Raheemah, it's my duty to protect my wife's dignity, ba zan iya jure yadda kike zaginta ba, ya kamata ki gane"
Tace "to ka kyauta, sai anjima"
Hanging up tayi yayi shrug ya mike ya shiga daga ciki. Ranan ya jima yana ba wa Jaleelah hakuri kamar shi ya zageta.
Ranan Wednesday tayi resuming schl ta cigaba da karatunta, bata da matsalar komai yanzu duk da ba auren soyayya suka yi ba amma suna kyautatawa juna fiye da wasu da suka yi auren soyayyar ga kuma son da mahaifiyar mijinta ke gwada mata da sisters din shi. Komai na tafiya mata cikin sauki.
After 3weeks......
0 comments:
Post a Comment