Fuskarta ya tallafo, yace "kina zargi na ne?", tace "ko ba zarginka nake yi ba, amma meya kawo Raheemah nan gidan, kuma me scarf dinta ke yi anan?" Yace "Jaleelah believe me, ba abinda kike tunani bane ya faru"
Shiru tayi mishi bata iya k'ara cewa komai ba, yace "kin ji?", nan ma tayi masa banza, yace "biyo ni gida tayi and I sent her away shine tayi fushi ta manta scarf din"
Tace "dan Allah I don't want to hear this and that, kawai ka barni haka, okay?"
Rugumota yayi ta janye jikinta tana fad'in "please Mr Airforce ka barni, kaina ciwo yake min and you are here adding salt to my injury"
Yace "okay then, let's go yanzu sai kije kiyi taking shower, sai ki sha magungunanki, ko kin sha?"
Tayi nodding kanta alamar eh, yace "baby bana son nodding, kin ji?"
Banza tayi mishi saboda ita a ganinta damunta yake yi, ga dukan data sha a wurin Mommy.
Tare suka wuce bedroom, suna shiga ta rage kayan jikinta ko kallonshi bata yi ba ta shige bathroom. Kallon kanta ta tsaya yi a mirror sannan ta fara karewa kanta kallo, burst dinta ya cika, idanunta were red and swollen, fuskarta duk ta kumbura sanadiyar kukan data sha. Bata tashi yin kuka ba sai da taga shedan dukan da Mommy tayi mata ko ta ko ina a jikinta. ko towel din bata cire ba ta sakar ma kanta shower tana kuka soulfully. Ta kusa 15mins tana yi, sosai taji zafin dukan, bawai physically ba amma emotionally touched.
Shi kuwa Abdul sai zaman jiranta yake yi amma shiru, har sai da ya gaji ya fara knocking sannan ne ta fara wankan that took her another 15mins sannan ta fito tana share ruwan fuskarta. Tana zama akan stool din dake gaban dressing mirror Raheemah na kira, ko nuna alamun ta san da mutum a inda take bata yi ba, shi kam sai tababa yake yi, bai jira call din yayi disconnecting ba yayi receiving, shiru yayi yana jira ta fara magana yana yi yana satar kallon Jaleelah ita kuwa bata ma san yana yi ba.
Raheemah ce ta fara magana, tace "hell..oo"
Ya mayar mata da "hello"
Tace "aw ashe kana ji na"
Yace "eh, ya kike?"
Tace "I'm good, miji na fa?"
Yace "yana cikin koshin lafiya", nan suka fara hira kadan kadan hankalinsa na kan Jaleelah dake ga sauri tana rubbing cream kamar ana jiranta, tana gamawa ta je gaban wardrobe ta ciro night dress dinta, yadda take yi kamar bata san da shi a wurin ba, cikin mintuna kalilan ta gama shirinta cikin short nightie dinta ta saka cap ta fice daga d'akin ta koma sitting room. A kan three seater ta kwanta ta runtse idanunta, a hankali ta fara hawaye, shi kuwa yana ganin ta fita yace wa Raheemah tayi excusing dinsa yana zuwa, ya bi bayanta yaje sitting room din ya same ta a kwance idanuwanta a rufe suna tsiyayar da hawaye, tana jinshi amma kuma bata fasa hawayen ba, har gefenta ya karisa ya zauna. Hannunta na dama ya riko yana kiran sunanta, "Jaleelah", can kasan muryarta ta amsa mishi, yace "can you please sit up?"
Cikin sanyayyar murya tace "please let me be"
Yace "ba maganar haka bane, just sit up muyi magana, idan mun gama I can even pet you to sleep", ta tashi daga kwance ta zauna tare da jinginar da kanta da backrest, tace "I'm all ears"
Yace "ok, amma first sai kin fada min me ya faru kike hawaye", tace "ba komai"
Yace "a'a, it can either be for joy or sadness, saboda haka ki fad'a min"
Ta share hawayen tace "kawai na tuno dukan da Mommy tayi min ne"
Yace "I'm sorry for that"
Lumshe idanuwanta tayi, tace "I'm the one supposed to say that, and... Ina jin haushi ka kawo wata gidanmu, and it's my fault, I wasn't there to serve you, da ina nan na san ba zaka kawo ta ba, kuma da komai ma bai faru ba, da I won't be rude kuma Umma ba zata yi fushi da kai ba, and.. Mommy ba da ba zata duke ni ba, can't you see I caused everything?" Ta karishe maganar tare da bud'e idanuwanta dake zubda hawaye.
Yasa hannayensa biyu ya share mata, yace "babu komai Jaleelah, babu laifin ki ko kadan a cikin faruwar hakan", with full confidence d'inta tace "noo Ameer, I caused it all, I caused everything! ba don ni ba you would have been happily married to the person you loved, yanzu ka ga saboda ni Umma ma bata son karin aurenka, Inteesar bata so, Aunty Safiyya da Aunty Mardiya ma haka, almost kowa ma, duk saboda ni, baka tunanin I'm hitch to your life?"
Rungemeta yayi yana patting dinta a baya, yace "I love you.. Ki manta komai, ke mata ta ce kuma ina k'aunarki, you're a part of me Jaleelah"
Rabewa suka yi ta goge hawayen fuskarta, tace "Still.. I'm sorry", ya dafa ta a kafada da hannayensa guda biyu, yace "ni bana son jin wannan I'm sorry din, instead kice I love you"
Murmushi tayi ta d'an tura mishi baki, yace "uhum, ina jinki"
Tace "ai kana da wacce kake so". Yace "duk da haka ni dai ina k'aunarki, kuma kema kiyi tunani Jaleelah, idan nace bana son ta saboda nayi aure kema kin San ban mata adalci ba, har alkawarin aure fa mun yi, and take yourself for example, da wane ido kike kallon Khaleefah? A matsayin wanda ya yaudare ki, ita ma haka take kallo na kuma duk da haka ta yarda zata aure ni"
D'an gajeran tunani tayi tace "it's okay"
Yace "to baki ce ki na qaunata ba", tayi murmushi tace "I love you"
Yace "I love you more"
••°••
A haka har suka kammala exams dinsu, kullum tana tare da Mrs Kiyawa a schl tana koya mata yadda ake wasu abubuwan, Ni'imah ma tana nan, duk lokacin da bata tare da Mrs Kiyawa to suna tare. Kusan kullum sai tayi waya da Umma da Mommy. AbdulHakam ma na kula da ita da nuna mata k'auna dai dai gwargwadon iyawarshi. Lokacin saura wata d'aya da 'yan kwanaki aurensu da Raheemah, ita ma dai yana kokarin ya nuna mata har yanzu tana nan a ranshi bai yada ta ba.
Wata ranan wednesday da yamma, Abdul yayi bak'i sai suka zauna a main parlour inda suke ta shan hirarsu, wayar Abdul kuma na wurin Jaleelah. Tana kwance tana surfing sai ga call din Raheemah, tunda ya fahimtar da ita akan aurenshi da Raheemar bata jin haushi yanzu sosai akan da, ta so bari ya yanke amma ko dan 'yar k'aramar drama ta d'auka, ta fara da sallama, Raheemah kuwa kasa amsawa tayi, tace "ke ina mijina?"
Jaleelah ta shek'e da dariya, tace "mijinki ko mijina?"
Tace "kin dai ji me nace miki, ina mijina?"
Jaleelah tace "yau ma dai ina ga wrong number din kika k'ara samu, wannan number'n Mijin Jaleelah ne, get it?"
Raheemah tace "na lura baki k'aunar gujewa fushi na"
Da sauri Jaleelah ta katse ta, tace "kece wa?"
Tace "idan na shigo gidan zan nuna miki ko ni wace ce"
Jaleelah ta sake bushewa da dariya, tace "to Allah ya kawo ki lafiya, ni shine fata na, kuma dama idan baka iya kama barawo ba shi zai kama ka"
Tace "wani kenan, amma wata ita ta iya kama b'arawon harda kayan da ya sata"
Gaba d'aya conversation d'in ma dariya yake ba Jaleelah, tace "ai wa'innan kayan sun dade da cin kasuwa, sai dai ko idan zaki lek'a kasuwa mafi kusa ki samo irinsu, wata k'il Allah ya sa ki dace"
Tace "ka ga min yar iskan yarinya?", Jaleelah ta tari numfashinta, tace "kar in sake ji, dama zan miki kashe din zagina tun kamin ki shigo mana gida, idan ba haka ba, zaki sha mamaki wallahi"
Tace "ka ga banza yar gidan talakawa jinin matsiyata"
Jaleelah ta k'yalk'yace da dariya, ta san hakan ba karamin batawa Raheeman rai yake yi ba, tace "oho dai, mun fi masu arzikin da ba zasu iya siyan sutura su rufe tsiraicinsu ba, mu kam Alhamdulillahi duk talaucin mu bamu yawo tsirara, kuma ba laifinki bane da kike kira na kina zagina, laifina ne da na bari ko wace shegiya take kiran mijina at her own will kamar bashi da aure, amma daga yau zaki gani", ta sake fashewa da dariya, ba ta bata damar yin magana ba tace "yar uwa sai anjima ko?"
Ta yanke kiran tana dariya, sai da ta shiga call log ta goge call history din. Da daddare bayan Abdul ya dawo daga masallaci, suna zaune a sitting room dinsu suna cin supper sai hira suke yi, bayan sun gama ta kwashe abubuwan da suka yi amfani da su ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito daga kitchen din, tun daga nesa yake kallonta har ta karisa inda yake ta zauna akan jikinshi, cikinta ya shafa da hannunsa, yace "Ameerah babyn mu nata girma ko?"
Kunya taji tace "cikin ya fara fitowa ne?"
Yace "eh mana, gashi kina gani, kalla ki ga", sunkuyar da kanta tayi ta kalli cikin nata, ta sa hannunta a kai ta b'ata fuska, tace "shikenan Ameer yanzu na gama fita"
Yace "meya sa?"
Kamar zata yi kuka tace "to baka ganin cikin ya fara girma"
Yace "and so?"
Tace "ni kunya nake ji, yanzu kaga ba zan iya zuwa gidan Mommy ba, kuma ba zan iya zuwa gidan Umma ba"
Dariya yayi, yace "to ai abun farinciki ne"
Tace "eh still ni kunya nake ji"
Yace "to ki sa hannu ki toshe kunnuwanki sai ki daina jin kunyar", turo baki tayi yayi dariya, yace "to me kike so nace miki? Kuma ranan friday zaki je gidan Mommy ki kwana, saturday zamu je Kano mu dawo sunday"
Tace "ahh.. Ba can zan koma ba?", yace "a'a, ina jin tsoron Umma, yanzu cikinki bai fi three months ba idan na kai ki na ajiye ki zata iya cewa sai kin haihu, dama haushi na take ji"
Tayi dariya tace "to mene ne?",yace "akwai wani abu gaskiya, almost six months fa zaki yi kuma bai zama lallai idan naje na ganki ba kuma ko da zan zo da weekend shima bai zama lallai na ganki ba bare mu je gidan mu"
Tace "toh... Yawwa...", don ya saurare ta da kyau tace "My love... Kasan mene ne?"
Yace "a'a. Sai kin fada"
Tace "ni dai, kawai ina so idan ka dawo gida ya zama time dina kawai kake dashi, you'll switch off your phone and be with me"
Ya girgiza kai yace "Jaleelah it can't be possible, idan daga wurin aiki na ana so ayi magana dani fa, ko yan uwa na ko abokanai na?"
Tace "to to to! Naji, ka sama new simcard for your family and friends, and call din wurin aikinka kadai zaka yi receiving idan ka dawo, promise?"
Girgiza kai yace "anything for my Prince's mother"
Tayi murmushi tace mishi "to chop knuckle"
Ya dungule hannunsa yayi forwarding suka yi, tace "that's my love"
Ya d'an mintsine ta a cheek dinta, tayi exclaiming "awch Ameer!!"
••°••
Tun daga wannan ranan kullum sai ta san yadda tayi ta amshi wayar AbdulHakam kullum idan ya dawo daga aiki, sai call din data ga dama take bashi yayi receiving. Ranan Friday nayi ya kaita gidan Mommy bayan sallar jumu'a, Saturday kuma yaje ya d'auketa suka wuce Kano. Umma kamar ta Goya ta a baya haka take ji, don bakinta Sam ya ki rufuwa yadda kasan shekara suka yi ba su ga juna ba, haka ma Inteesar musamman data ga cikin Jaleelah ya d'an ta sa. Yadda Umma ke farinciki yasa fushinta akan Abdul ya ragu, don bama ta da lokacinshi bare ma wani Abu ya hada su.
Da yamma suna zaune a kan rug a backyard suna hira, Abdul, Inteesar, da Jaleelah, Raheemah ta kira shi, ita dai Jaleelah ta san ko wane ne unlike Inteesar, ya wuce su sai da yaje can kusa da d'akin me gadi sannan ya zauna akan wani bench, ya kirata saboda then call din har ya yanke, tayi picking suka gaisa, tace "Abdul ka daina so na ne?"
Yace "a'a. Me kika gani?"
Tace "naga ka daina kira na unlike before"
Yace "ba haka bane Raheemah, commitments ne sai a hankali, kinga kullum na fita gida by 7am, na dawo past 5pm, wata rana ma nakan kai 6pm sannan na shiga gida, na huta, naci abinci, sometimes ko samun daman taking shower bana yi sai naje masallaci nayi sallar magrib da isha na dawo, nayi shower, by then dare ya fara yi, kuma mata na itama tana buk'atar lokaci na, dare ne Kadai lokacinta kinga I can't deny her her right"
Cikin fad'a tace "I didn't ask of your family, I asked of our relationship, kuma dama I just called to tell you a Kaduna nake son zama, period!"
Ya d'an yi yar dariya, yace "kiyi hakuri sai naji ta bakin mata na, sai ta fara zab'an inda take so"
Tace "to make things short, wallahi a can zan zauna"
Da sauri Mom ta fizge wayar daga hannunta ta yanke kiran, tace "amma ke wawuyar yarinya ce Baby, abinda zai kashe ki kenan, ke kullum sai kin bayyana rashin hakurin ki? Ko dan kissan nan irin na mata baki iya ba bare salon magana? A haka ne zaki ci galaba akan matarshi?"
Tace "Mom ai karamar yarinya ce"
Mom tace "to shikenan ki tsaya kina fad'in karamar yarinya ce"
Shi kuwa Abdul bai b'ata lokaci ba yaje ya samu Jaleelah, yace ma Inteesar tayi excusing dinsu, ya dubi Jaleelah dake jira taji me zai ce, yace "my love"
Tace "na'am my love"
Yace "uhmm... A ina kika fi son zama? Kano ko Kaduna?"
Ta kalli sama na yan sakwanni sannan ta kalle shi tace "Kaduna!"
Yace "why?"
Tace "nafi son zama kusa da kai, so I can serve you to my possible best"
Ya d'an yi murmushi, yace "ba za ki iya zama a Kano ba?"
Tace "zan iya mana amma nafi son zama kusa da mijina"
Yace "to zaki iya hakuri ki zauna a Kano?"
Tace "for how long?"
Ya d'an shafa kanshi, yace "for the rest of your life"
Ta zaro idanunta waje, tace "saboda me?"
Yace "Raheemah tace tafi son Kaduna, I tried to make her understand amma ta rantse ita a can zata zauna"
B'akin cikin da ke zuciyarta ta danne da murmushin takaici, tayi shrug tace "it's fine with me, kawai ka tafi ka barni a nan ma, I'll be okay"
Daga jin yadda take magana yasan she didn't mean it, yace "understand me please"
Tace "I do", daga haka ta tashi ta wuce shi ta shige ciki wurin Umma.
⚜Mijin Jaleelah⚜
42___46
By Linah Shams✍🏼
*let's do it paka`paka*👏🏼
Bayan sallar la'asar suka zauna a main parlour suna ta hira gwanin ban sha'awa, Inteesar ta rok'i Umma ta barta ta tafi Kwara state hutu wurin yayar Umman, Jaleelah tace "ki bari mu zauna a gidan mu mana"
Inteesar tace "wani gida? Kaduna?"
Tace "a'a nan Kano mana"
Tace "oh, ba gobe zaku tafi ba?"
Tace "eh amma zan dawo nan da zama gaba daya saboda amaryar shi tace ita Kaduna take so"
Inteesar ta tallafe hab'anta, tace "iyye! Ke kuma kika yarda? Wallahi kice a can zaki zauna ba zaki yarda ba"
Umma dake zaune tana saurarensu tace "ke bana son sakarci, ina ruwanki?"
Tace "Umma amma...", ta katse ta "nace ina ruwanki?"
Shiru tayi bata sake cewa komai ba.
Ita dai jininta bai hadu da na wannan amaryar ba.
Ba a jima ba sai ga Abdul ya shigo, ya zo d'aukan Jaleelah zasu je gidan Mustapha daga can zasu wuce gidansu a can zasu kwana. Faran faran suka gaisa da Umma, da shigarsa da dadewarsa bai yi mintuna Biyar ba, yace "Jaleelah ki shirya zamu wuce"
Umma tace "d'an Alhaji da wuri haka?"
Yace "eh Umma, zamu gidan Mustapha ne daga can zamu wuce gida"
Tace "to shikenan"
Jaleelah ta tashi ta sa hijab dinta sannan ta dauki yar handbag dinta, tace "Umma zamu tafi"
Umma ta mik'e, tace "to ku gaishe da Afaf d'in", har compound tayi musu rakiya, Abdul sai dadi yake ji yanzu Umma ta daina fushi da shi. A bakin motarsa suka tsaya, tace "d'an Alhaji"
Harda yar risunawa yace "na'am Umma"
Tace "ita yarinyar da zaka auro a ina zaka sakata?"
Shafa kansa yayi yace "Umma.. A Kaduna tace zata zauna"
Tace "to ai nayi tunanin matarka ce ya kamata ta fara zaban inda zata zauna, ko ita ce tace maka tafi son nan d'in"
Da sauri Jaleelah ta kirkiri murmushi, tace "eh Umma, ki bari kawai na dawo nan kusa da ke"
Umma tace "can nafi so ki zauna"
Murmushi ta sake yi tace "Umma ki bari kawai ita ta zauna a can d'in ni zan hakura na zauna a nan, ina ga hakan ma zai fi, ai duk d'aya ne da nan da can d'in"
Umma tace "kin tabbata?"
Ta girgiza kai tare da fad'in "eh Umma"
Tace "to shikenan, Allah yayi muku albarka" dukansu suka amsa mata da amin sannan suka shige mota ita kuma ta koma ciki.
A gidan Mustapha Jaleelah ta samu kyakkyawan tarba a wurin matarsa wacce bata wuce 22years ba. Afaf sai ina zata saka take yi da ita ga Ilham ita ma. Sai after isha sannan suka bar gidan.
Around 9:30 tana zaune a sitting room tana kallon TV Abdul kuma na ciki yana wanka Inteesar ta kira ta, ba tareda b'ata lokaci ba tayi picking tana fad'in "yan mata haffa?"
Tace "ai ni haushinki nake ji matar Yaya AbdulHakam, ni bazan boye miki ba"
Jaleelah tace "haba baiwar Allah me nayi?"
Tace "saboda kin bani kunya, wlhy kin bani kunya, kina mace har wata shemammiya ce zata fadama mijinki abinda take so? Tana waje sai abinda take so za ayi ina ga kuma ta shigo gidan?"
Tace "Inteesar kenan, to miye na jin haushi?"
Inteesar tace "ai na fada miki dalili, Allah seriously kin bani haushi"
Tace "to dana baki ba sai ki k'i amsa ba", ta d'an yi dariya sannan tace "nasan kema kallon yarinta kike min kamar yadda shima boss din yake kallo na, ai yarinta ba hauka bane kamar yadda shima yake fad'a min, kawai sai aka ce miki don ina da k'ananun shekaru shikenan sai aka ce miki bani da wayau? Kallonsu kawai nake yi, this is my first step"
Inteesar tace "to amma dai ki dinga sanin matsayinki, kece uwargida, ba wai don ta girme ki ba zata zo tana fadin yadda za ayi, ke ma matarsa"
Tace "to hajiya, nagode"
Tace "yauwa", suka yi sallama Jaleelah ta tashi ta shige bedroom wurin Abdul.
15days to the wedding day.
Ranan ne Jaleelah zata koma Kano gaba d'aya da zama saboda Raheemah tace sai an sake mata paint din gidan kuma anyi ma gidan sabon paint da kwaskwarima sannan zata shiga gidan. Gaba d'aya Jaleelah ta b'oye damuwarta, sai sha'aninta take yi, dama da yake gidan babu komai nata a ciki sai kayan sawanta da few kitchen utensils. Abdul yace ko me take so ta a gidan ta d'auka ita kuwa ta nuna mishi bata son komai.
Sai da tabi gidajen neighbours dinsu tayi musu sallama, duk da wasu bata saba da su kamar yadda ta saba da Umman Fadeelah.
Wannan karon tare da Hadiyya suka tafi Kanon, sun tafi thursday, Sunday Abdul idan zai koma zai koma da ita. A gidan Umma suka fara sauka daga bisani suka wuce gidansu.
Ranan Saturday aka kai lefen Raheemah akwati dozen, haka itama Jaleelah yayi mata, babu abinda yayiwa Raheemah da bai mata ba, sai dai fentin da aka sakewa gidan da Raheemah zata zauna, itama saboda bata cika zama a gidan bane kuma Umma tayi insisting a sake paint din Jaleelah tace a barshi haka, shiyasa kullum take kara kusantar zuciyar Umma saboda iya nuna kawaici.
Sai dai amma duk da haka ya zuba mata sababbin kujeru a main parlour din ta. Bayan Allah ya sauke ta lafiya kamin ta fara zuwa uni zai siya mata mota, don dadi fa taji dadi amma still tana jin kishi a ranta.
Ranan Sunday Hadiyya ta koma Kaduna tare da Abdul.
Tun ana saura kwana bakwai biki aka fara events na gani na fad'a. Anyi b'arna da nera. Ranan farko Nupe day suka yi, saboda Mom su nupawa ne, rana na biyu kuma suka yi kumbo day, rana na uku aka yi sa lalle, rana na hud'u kuma kamu, rana na biyar akayi Mothers' day, rana na shida kuma na su Dad ne, akayi Fathers' day da luncheon.
On the seventh day aka d'aura auren AbdulHakam Muhammad Jafar da Raheemah Adda'u Bello.
Ranan biki ya amsa sunansa biki, gidansu Raheemah shak'e yake da yan uwa da abokanan arziki, unlike gidansu AbdulHakam Wanda babu kowa a cikinsa sai Umma, Inteesar, Hadiyya, Jaleelah da matar baban Tarauni. Sai makwabta masu shiga da fita. Idan kaga Inteesar ba zaka rantse kace ana biki a gidansu ba, ranan ko wanka ma ta k'i yi kamar ita akewa kishiyar har sai da Umma ta zazzage ta sannan ta Shiga tayi wanka. Atamfa Riga da zani ta sanya fuskarta ko mai babu hakanan ta zauna. Ita kam Hadiyya ta cancad'a uban adonta, Jaleelah ma haka sai fara'a take kamar gonar auduga, amma deep down inside, it was killing her.
Mustapha ne kadai yayi mishi kara yaje daurin auren, amma Munawwar da Basheer sunki zuwa, sai abokanan aikinsa da suka je. Ya dai d'an ji haushi amma ba sosai ba.
Sai Da yamma sannan Aunty Safiyya, da Aunty Mardiyya da Sajida matar Khaleel suka samu daman isowa. Da Umma tace babu taron da zasu yi Baban Tarauni ya hayayyako mata yace dole sai anyi taro. Lokacin da suka iso lokacin Jaleelah ke shirin barin gidan, zata tafi gidanta ta d'auko kayan da zata sanya lokacin dinner, bridal gown din data siya na musanman domin wannan ranan.
Tare da Inteesar suka tafi suna tafe suna hira har suka isa. Ko da ta sawa gate din key jamlock ne kadai aka sa wanda hakan ya tabbatar mata akwai mutum a gidan kuma ba kowa bane illa Abdul.
A sitting room tayiwa Inteesar masauki ita kuma ta shige cikin bedroom duba Abdul yana kwance daga shi sai dogon wandon shadda da farar singlet yana amsa waya. Yana ganinta ya ware mata arms din sa daga kwance, tana murmushi ta karisa ta fad'a jikinsa yayi wrapping dinta da hannu d'aya. Sai after almost six minutes sannan ya gama call din, yana ajiye wayar tace "happy marriage life my love"
Yayi kissing dinta a forehead yace "thank you baby na, meya sa baki zauna a nan gidan ba?"
Tace "gidan Umma yafi mutane shiyasa"
Ta k'ara da cewa "to ina abokananka?", yace "ba su nan, wa'inda kuma suka zo min d'aurin aure duk sun tafi bayan anyi reception, kin san majority dinsu ba a nan Kano suke ba"
Tace "to ina Baban Ilham (Mustapha), da Baban Jazlaan (Basheer) da Baban Basbas (Munawwar)?"
Yar tsaki yayi yace "manta da su, wai they are busy amma zasu zo dinner, that's idan sun ga dama, yanzu dai I'm badly missing you"
Da sauri tace "da ni da Inteesar ne fa", yace "and so? Ita nake missing ko ke?"
Tace "amma ai ban ce mata zamu dad'e ba kuma kaga kaya na zo d'auka"
Yace "kayan me?"
Tace "na zuwa dinner'n aurenka", tashi zaune yayi, yace "what do you mean? Nufinki zaki je wurin dinner ne maza su kalle ki ga kuma cikin dake jikinki?"
Tace "kalla fa ka gani cikin ai bai yi girma da yawa ba, besides ita ma Raheemar ai matarka ce, kowa sai ya kalleta, yadda ma za a kalle ta ni ba za a kalle ni ba"
Yace "babu inda zaki, better take note"
K'asa k'asa tayi da murya tace "Dan Allah mana"
Yace "ba zaki ba nace". Ta riga da ta ci burin zuwa wurin dinner'n nan kuma ko ana muzuru ana shaho sai ta je shi. Tashi tayi ta bud'e wardrobe ta d'auko wata farar leda ta kalle shi a kaikaice tace "na tafi"
Bai iya ce mata komai ta fita suka yi wucewarsu ita da Inteesar. A hanya ta tambayeta "wai ke kayan mene ne wannan?"
Tace "duk inda kika ji kaya ai na sawa ne, kaya na na zuwa dinner ne"
Da mamaki ta kalleta, tace "kinga dalilin daya sa kike bani haushi ko? Har da wani d'inkin sabon kaya za ayi miki kishiya?"
Tace "eh mana, ai baki san dalilin daya sa zan je ba, nifa so nake na haska taron nan, ina so ta k'ara sannin cewa mijina yana so na saboda haka ina gefen damanshi tana na hagunshi, a tsakiya zamu sa shi, sai taga yadda auren kaddara ke komawa auren k'auna bama na so ba, kuma sai ta ga cikin nan", ta fad'a tana pointing cikin suna cigaba da tafiya zuwa bakin hanya samun abun hawa, ta cigaba da cewa "kece kike min kallon abin haushi, amma aka ce miki a banza ne zanje nayi wannan lallin da gyaran gashin kamar wata amarya? Ai yau dinner'n mutum biyu za ayi a lokaci d'aya, dama da zamu yi aure ba ayi ba"
Inteesar ta bata hannu tana dariya, tace "ban mu kashe nawa?"
Jaleelah ta bata palm d'inta suka tafa, tace "ke a hanya fa muke ba gida bane"
Tace "ni nama manta, to yanzu mene ne abun yi?"
Jaleelah tace "abun yi shine nifa sai naje dinner'n nan, kuma nasan Aunty Mardiyya da Aunty Safiyya ma zasu je, Maman Teemah (Sajida) ma zata je, Maman Ilham ma may be zata je, Izz nasan dole zashi to sai na roke shi ya kai ni"
Inteesar ta saki wani irin dariya, tace "babe kice yau akwai kashe kalaaa! Dafa nace babu inda zani amma yanzu wlhy sai naje"
Jaleelah tace "amma kin san mene?"
Tace "a'a"
Tace "yafa hana ni zuwa, amma idan muka koma gida zan marairaicewa Umma kamar zanyi kuka, nasan zata kirashi tace dole sai naje nima"
Tayi dariya tace "mata kenan, kuma kin kawo shawara, don yadda Umman ne ke ji dake nasan sarai zata kira shi tayi mishi fad'a"
Suna dira daga keke napep Jaleelah tayi cid'ucid'u da fuska ta wuce Inteesar, ita ta tsaya ta biya mai keke kudinsa sannan ta bi bayanta, abin ma dariya ya bata saboda ta san komai. Tsallake kowa dake parlour Jaleelah tayi bata zame ko ina ba sai bedroom din Umma. Ganin yadda fuskarta ba ko annuri yasa Umma tace "a'ahh, 'yar albarka, me kuma ya faru?"
A gabanta ta tsugunna ta d'aura kanta akan gwiwowin Umman, tace "yace ne wai ba zanje ba Umma, kuma kowa zashi amma banda ni"
Umma tace "shi wa? D'an Alhaji?", ta girgiza kai tana fad'in eh. Umma tace "ina za aje da yace ke babu inda zaki?"
Tace "dinner"
Tace "dinner kuma Jaleelah? Baki gani kina d'auke da juna biyu?"
Cikin shagwaba shagwaba tace "Umma ai ba rawa zanyi ba, kawai fa zuwa zanyi nima kar na zauna ni kadai a gida, kinga Inteesar ma zata je, kowa ma"
Tace "to shikenan, zaki je, amma sai kinyi min alkawarin ko kallon banza ba zaki ma matarshi ba, kina ji na?"
Tace "Umma to ni a ina ma zan ganta?"
Tace "na dai fad'a miki, ki je anjima sai Izuddeen ya kai ku ke da yar uwar taki"
Wani farinciki taji kamar ta tashi ta rungume Umma, amma duk da haka sai da tayi hugging legs dinta, tace "nagode Umma".
••°••
Quarter past 8pm Jaleelah ta gama shiryawa cikin golden gown dinta da ya sha ado da kyalkyali da bridal satin dinsa, fuskarta d'auke yake da kwalliya, ga lallenta da ya k'ara haskata, wuyarta sanye yake da sarkar gold da yan kunnayensa a kunneta, ga yatsunta da suka sha zobba suka karawa lallen kyau sai golden wristwatch din data sanya. Sai purse shima golden colour da wani d'an siririn veil data sagala a kafad'arta. Purse din cike yake da canjin sababbin yan naira hamsin wanda zata yiwa amarya da ango lik'i, ita dai burinta kowa dake wurin ya shaida zuwanta a matsayinta na uwargidan AbdulHakam. Kwalliyarta tayi matukar kyau don Ko amaryar sai haka. Duk Wanda ya ganta sai ya yaba da kwalliyarta musanman Umma, Inteesar kuwa sai rotsa mata kai take yi wai tafi amaryar kamar ta ganta.
Inteesar ma ba a barta a baya ba don ita ma ta sha ado dai dai misali. A motar Abba suka tafi wanda Izz ya tuka. Da Jaleelah, da Inteesar, da Aunty Mardiyya da Maman Teemah sai Aunty Safiyya.
Tare suka isa wurin da motarsu Abdul da Raheemah da motoci da dama suka marawa motarsu baya. Da gaggawa Jaleelah ta murd'o hannun motar ta fita ko sauraren kowa bata yi ba, Inteesar dake zaune a gefe ita ma ta fice tabi bayan Jaleelah, yau zata ga yadda ake k'arfin hali wai barawo da sallama. Kekketa mutane tayi ta wuce su ta tsaya daga gefen daman shi, shi sam bai ma ankare da ita ba duk a tunaninshi qawayen amarya ne. Sai washe baki suke yi dashi da amaryarsa. Inteesar kuma na daga bayanta.
A sannu suka taka kan red carpet din da aka shimfida tun daga entrance door har couples table. Duk inda suka wuce guda ke tashi. Su Aunty Safiyya sai kallon ikon Allah suke yi. Hakama mutane, su kam Abdul da Raheemah basu san dawan garin ba. Kowa sai mamaki don da ganin Jaleelah kasan matar aure ce saboda d'an k'aramin cikin dake jikinta.
Abdul bai tashi sanin Jaleelah na side d'inshi ba sai da suka zauna akan kayatacciyar kujerar da aka ta nada musu. Bayan ya zauna ta cire duk ilahirin kunyan da take da shi ta tsaya daga gabanshi, tasa hannayenta guda biyu a kowane side din fuskarsa ta tallafo, ta bashi light peck a goshinshi sannan ta sa index finger dinta na hannun hagu ta goge d'an jambakin daya taba mishi wurin.
Daga shi har Raheemah sai da suka rikice da mamaki, hakama kawayenta da suka mara mata baya da su Munawwar. Bata ko daga kai ta kallesu ba tace ma Abdul "happy marriage life once again my love", bata jira ya bata amsa ba ta kalli Raheemah tana murmushi tace "happy marriage life to you also sis", bata jira amsansu ba ta juya suka rike hannu da Inteesar suka wuce. Jama'a sai kallonsu suke yi sai kuma suka hau tafi ana shewa. Wannan Abu ba k'aramin dad'i yayiwa Inteesar ba, ko yanzu kasuwa ta tashi d'an koli yaci riba.
Da murmushi a fuskokinsu suka isa table d'in da su Aunty Safiyya suke. Dama six persons per table ne, suka zauna su shida abinsu. Kowa sai waigowa yake yi yana satan kallonta. Ita kuwa ko a jikinta. Inteesar ma kasa boye farincikinta tayi, sai washe baki take yi, Sajida ce tayi karfin hali tace "sannu da k'ok'ari Jaleelah", yar dariya tayi ta sunkuyar da kanta, tace "Aunty Sajida kenan", Aunty Mardiyya tace "wato abinda kuka kitso kenan dake da wannan yar banzar yarinyar"
Da ita da Inteesar suka fashe da dariya, Aunty Mardiyya tayi dariya tace "Allah ya shirye Ku, wato uwargida kenan"
Inteesar tace "sarautan mata ba. Ai kin ga yanzu kowa ya san akwai wata kamin wancan jar k'osan"
Afaf tace "ikon Allah, amma fa kin bada kala Jaleelah"
Tace "yawwa Ummin Ilham, kema kya gani"
Haka suka d'an dinga hira har lokacin yanka cake yayi.
Su Afaf Neman Jaleelah suka yi suka rasa, can suka tsinto ta a gaban Hall, ga ta ga Abdul ga Raheemah ya d'ayan gefen. Shima Abdul ganinta kawai yayi. Ai fa nan aka fara kashe musu hotuna ita kuwa sai washe baki take yi, murmushin karfin hali kawai Abdul yake yi banda Raheemah data b'ata fuska.
Hakanan suka yanka cake din su uku, Jaleelah harda dariyar mugunta. Abdul ya fara bawa Raheemah cake d'in a baki sannan itama ta bashi, Jaleelah dake gefe ta yanka ita ma ta mik'a mishi a baki, gudun kar ya dizgata yasa ya amsa, daga haka ya kawar da kanshi daga side d'inta, tasan ji yake kamar ya tsire ta da mashi, tana turo mishi baki tace "to nifa", yayi banza da ita, riko mishi hannu tayi cikin shagwaba tace "honey ni fa", this time around gudun kar ta jawo mishi mutane yasa ya bata yana mai galla mata harara kamar ya mare ta. Raheemah kuwa ji take yi kamar ta shak'e ta.
Dinner yayi dinner aka fara taka rawa, Jaleelah da Inteesar suka shigo fage aka fara dasu tana mak'ale a side d'in Abdul. Ita ta fara yi musu liki tana yi tana dariya itama ana lik'a mata. Lokacin da Abdul yaga mutane sunyi yawa ana ta rawa ya ja hannun Jaleelah suka fita, Inteesar ce kadai tayi nasaran ganinsu.
Suna tafe yana janta har suka isa parking lot suka tsaya cikin motoci, cikin fushi ya daka mata tsawa "me na fad'a miki akan zuwa wurin nan?"
Yadda yayi mata tsawan da yadda yayi mata magana yasa sai da taji tsoro, tace "ba komai", saboda tsoro ma rasa response din da zata bashi tace mishi ba koman, kafadarta ya rik'e ya jijjigata, saboda fushi idanuwanshi suka kad'a suka yi ja, cikin fad'a yace "tell me! Uban wa yace ki zo nan?", k'iris ya rage ta fara kuka saboda yadda ta d'imauce at once, yace "saboda kin raina ni? Har zanyi miki magana in baki umurni ki sa k'afa ki ture?"
Muryarta na rawa tace "Dan Allah kayi hakuri bazan sake ba"
Yace "da hakuri ta mutu sadakan uwar me kika bada?"
Siririn hawaye ne ya sakko daga idonta, ta sa hannu ta goge, tace "duk a saboda na zo dinner dinka ne ka zagi ubana da uwata?"
Duk sanda ya kalli kwalliyarta da d'an ficicin gyalen data sagala a kafad'a sai yaji b'acin ranshi na hauhawa kamar farashi, yace "if there's something worst than that I can do it!!! Kalli wannan tsinannan gyelen da kika sa"
Ta bud'e baki zata yi magana yace "idan na sake magana kika yi wlhy sai na baki mamaki a wurin nan"
Shiru tayi bata sake cewa komai ba har yayi fad'an shi ya gama, ya tambayeta Wanda ya kawo su ta fad'a masa Izz ne, nan ya kira numbern shi yace ya fito waje yana jiranshi, yana fitowa ya isa inda suke Abdul yayi masa umurni daya d'auketa ya mayar da ita gida. Bai ko sauraresu ba yayi wucewarshi cikin hall d'in.
Inteesar na ganin shigarshi ita kuma ta fita neman Jaleelah. A parking lot tayi spotting dinsu ta karisa cikin gudu gudu, nan da nan Jaleelah ta b'oye damuwarta, Inteesar tace "gida zaki koma", tace "eh ki zo mu koma tare mana", tace "ah haba ke kuwa, yanzu fa aka fara rawa", tace "eh ai mun d'anyi, ki zo kawai mu wuce", tace "to bari naje nayiwa su Aunty sallama kar su ga bama nan su hau nema"
In less than two mins ta dawo suka shige mota suka bar wurin. A cikin motar sai hiransu suke yi Jaleelah bata yarda ta nuna mata tana da damuwa ba. Ko da ta tambayeta dalilin da yasa zata koma gida yanzu ce mata kawai tayi Abdul ne yayi insisting ta tafi saboda cikinta.
Bayan Abdul ya koma ciki yaga sauyin fuska daga wurin Raheemah, sai sha mishi mur take yi muma yasan kome take mawa. A haka suna d'an tattakawa yace "I'm sorry baby"
Tace "you don't need to be, ka wulakantani a gaban mutane a ranan da aka daura auren mu. Har zaka iya fita da matarka a daidai wannan lokacin, na wannan lokacin ne kawai amma ba zaka iya boye zalamarka ba"
Bai iya ce mata komai ba sai I'm sorry, duk korafin da tayi sai dai ya bata hakuri don ba zai iya explaining kansa ba for now. Sai past 10pm sannan suka gama pate patensu, sai washe gari za akai amarya gidan mijinta.
Please bear with me🙏🙏
Love you loads💞
[4/15, 12:47 PM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
47
By Linah Shams✍🏼
Inteesar ta fara shigewa ciki ita kuma ta tsaya a waje, sai da ta tabbatar da ta shige ciki ta roki Izz ya dauko mata Hadiyyah yayi dropping dinta a can gidansu itama yanzu zata tafi, matukar ta kwana a nan gidan sai kowa yasan damuwarta. Tana shiga ciki ta d'auki bag d'inta da wasu 'yan tarkacenta ta harhad'a, Inteesar na d'akin Umma tana labarta mata dinner'n.
Kamar ana azalzala mata haka ta fito saboda ta k'osa ta koma gida tayi kuka. D'akin Umma ta shiga, Inteesar ta hangame baki tana kallonta, sosai ta danne damuwarta ta d'an shiga cikin parlourn, tace "Umma zan wuce", tace "zuwa ina da wannan daren"
Tace "can gidan zani", Umma tace "lafiya dai ko?"
Murmushi ta k'irk'iro, tace "eh ina son Hadiyya tayi min wanki ne gobe kamin ta tafi, kuma da wuri zata tafin shiyasa zan koma yanxu saboda tayi min da wuri"
Murmushi itama Umman tayi, tace "Inteesar tashi ki rakata bakin hanya to"
Ta mike ta d'auki mayafinta suka fita. Suna tafe suna d'an jefo yar hiransu har suka isa bakin hanyar Jaleelah ta samu keke napep ta shiga ita kuma Inteesar ta juya zuwa gida.
Sai da tayi tsayuwar mintuna fiye da goma sha biyar sannan Izuddeen ya iso tareda Hadiyya, sosai tayi masa godiya sannan ta bud'e gidan suka shiga tayi locking. Suna shiga bedroom Hadiyya ta fara kokarin rage kayan jikinta tana fad'in "Yaya Jaleelah kuna da ruwa a ban d'akinku kuwa"
Tace "eh akwai mana". Nan da nan ta shige cikin ban d'akin domin watsa ruwa. Ita kuwa Jaleelah a gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta, ko ita da kanta ta san bata tab'a yin kyau irin na ranan ba, kuma ta san ba don d'an cikin nan nata ba da wani sai yayi tunanin ko ita ce amaryar ko kuma aure biyu yayi a rana d'aya, b'akin cikin yadda Abdul ya dinga yi mata masifa tayi, sai ta tsinci kanta tana mai tsiyayar da hawaye, ko don albarkacin unborn child dinsu ai zai d'aga mata k'afa amma ya k'i sai da ya ci mata mutunci.
Share hawayen tayi ta cire kayan jikinta tana jiran fitowar Hadiyya itama ta shiga tayi wankar. Ta d'auko purse dinta ta bude ta ciro wayarta, missed calls uku ta gani kuma duka na Mommy ne. Ta bi call d'in amma kiran farko ba a d'auka ba sai a karo na biyu, lokacin data jiyo muryar Mommyn ji tayi kamar tayi tsuntsu ta ganta a gabanta, cike da farinciki suka gaisa suna hira sai ga Hadiyya ta fito. Nan ta mik'a mata wayar ita kuma ta tashi ta shige bathroom. Sai da taci kukanta ma'ishi sannan tayi wankan ta fito, lokacin har Hadiyya ta kammala shirinta na bacci tana kwance tana buga games da wayar Jaleelahn.
Sumi sumi take rubbing cream din kamar ba zata shafa ba. Har ta gama tana hawaye Wanda Hadiyya bata sani ba saboda d'akin was dim lit. Shirinta na bacci tayi sannan ta fita tayi locking entrance door, ta shiga sitting room shima tayi locking sannan ta dawo bedroom tayi musu locking k'ofar taje ta kwanta a d'ayan side d'in ta juyawa Hadiyya baya, tace "idan kin gama ki tabbata kin sa min wayata a chaji"
Ta amsa mata da "to sai da safe", ta ja bargo ta rufe jikinta ba don tana jin baccin ba. Hawaye ta cigaba dayi kamar ba zata daina ba tayi addu'ar bacci ta cigaba da abinta, in case ko da baccin zai sace ta, haka kuwa akayi don bata san sanda tayi baccin ba.
A b'angarensu Abdul kuwa ba k'aramin zafi Mom ta d'auka da shi ba da sauran yan uwanta. Hakan yasa bayan an kammala dinner d'in ta sa aka kira mata shi ya zo har gida ya same ta, fad'a tayi mishi na fitar hankali kamar zata cinyeshi, shi kuwa banda aikin bata hak'uri ba abinda yake yi, tace "kar ka k'ara fad'a min inyi hakuri, hakurinka na banza da wofi! Bayan ka dizga mu a bainin nasi sannan ka zo kana fad'a min hakuri?", ta k'ara da cewa "d'ago ta kalle ni AbdulHakamu kake ko wane ne? Mun fi k'arfin tsiya da raini, saboda mun baka auren yarinya har zaka iya wulakanta mu? Kaima kasan banda kaddara Raheemah ta wuce ma ajinka, sannan har zaku had'u da yar shilan da kake tak'ama ka aura Ku wulakanta mu? Ai kuwa kunyi kadan, dama nasan karya kake yi ba auren taimako kayi ba, da auren taimako ne ba yadda za ayi yarinyar nan ta samu 'yancin zuwa wurin nan, kuma gara kasan irin matakan da zaka d'auka a cikin gidanka, don bazan tab'a barin 'ya ta tayi rayuwar kunci a gidan ka ba", shiru ya biyo bayan maganarta na kusa five seconds, sannan tace "zaka iya tafiya", saboda matsanancin b'acin rai ko sai da safe bai iya ce mata ba ya fice.
Duk da yaji haushin Mom amma yafi jin haushin Jaleelah, ita ta ja mishi komai da duk hakan bai faru.
Bai yi tsammanin ta dawo gidan ba, yana zuwa shiga inner sitting room yaji kofar a rufe, ya tsaya budewa ma b'ata lokaci ne, ya bi ta dinning hall ya shiga ta kitchen, shima kofar locked. Hakanan ya hakura ya tsaya ya bude, ya shiga. shima kofar bedroom din sai da ya bude sannann ya shiga da zummar ci mata mutunci yaga su biyu ne da Hadiyya. Karisawa ciki yayi ya tsaya a gabanta ya haska mata fuska da wayarsa, murmushi yayi daya ga alaman tayi kuka, yayi kwafa sannan ya fice daga d'akin ya koma d'ayan bedroom din.
Washe gari ta tashi da mugun ciwon kai, don da kyar ta iya yin sallah a zaune. Bayan ta idar da sallahn ta koma gado ta kwanta, sai taji dama tayi zamanta a gidan Umma, yanzu gashi ta dawo ta sha kuka ya haifar mata da ciwon kai. Hadiyya ce zata had'a musu breakfast, ta fita zuwa kitchen ita kuma ta kwanta ta fara sobbing soulfully. Tana tsaka da kuka Abdul ya bud'o k'ofar ya shigo, tana d'aga kai ta kalleshi ta ji wani mummunar faduwar gaba da tsoro har sai da cikinta ya murd'a mata, sai da ta kudundune ko zata samu relief, a hankali yake tafiya har ya isa gabanta ya zauna, kasa d'ago da kanta tayi cikinta na kara juyawa, murmushin takaici yayi yace "jira kike yi in gaishe ki?"
Muryarta na shaking tace "ina kwana"
Yace "ban ganshi ba", cikinta ne ya kara juya mata tayi wani irin k'ara a hankali, shi kuwa duk a tunaninshi plan tayi saboda kar yayi mata fad'a, bai sake ce mata komai ba ya tashi ya fita daga gidan gaba d'aya.
Kuka mara sauti ta shiga yi, sai ga Hadiyya shigo tambayarta kwai nawa zata yi amfani da shi ta tarrar da ita tana kuka. Da sauri ta karisa inda take a durkushe kan gadon tana fad'in "Yaya Jaleelah lafiya?"
cikin kuka tace "ki kira min Umma"
Bata ba ta amsa ba ta d'auki wayarta ta shiga neman numbern Umma ta kira ta, bayan ta gaisheta ta fad'a mata Jaleelah bata da lafiya, ai fa hankalin Umma ya tashi, ba a k'ara minti talatin ba suka isa gidan ita da Inteesar. Jaleelah na ganinta ta sake barkewa da sabon kuka, saboda tasan akwai mai rarrashinta, Umma na zama tayi saurin d'aura kanta a jikinta, ta share mata hawayen fuskarta tace "meke damunki Jaleelah"
Cikin kukan tace "Umma ciki na da kai na". Umma tace "subhanallahi! Tun yaushe?", tace "jiya da daddare ne"
Tace "kin san baki da lafiya shine kika kama hanya kika dawo nan uhm?"
Tace "yanzu ne cikin ya fara"
Umma ta dubi Hadiyya tace "taci abinci ne?"
Tace "a'a ba abinda ta ci", tace "to zo ki samo mata wani abu taci sai mu wuce gida a kaita asibiti", ta fita zuwa kawo mata breakfast.
Umma tace "to shi d'an Alhajin fa? Ina ya tafi? Don banga motarsa ba Ko bai kwana a nan bane?"
Tace "ya kwana ban san inda yaje bane"
Umma ta d'aga wayarta ta kirashi, suka gaisa tace "kana ina ne?", yace "na d'an fita ne Umma"
Tace "matar taka bata da lafiya shine zaka ce ka fita, gidan wa ka tafi?"
Yace "naje gidansu Raheemah ne"
Cikin fad'a tace "uwarka da kai da Raheemahn, ka zo ina nemanka yanzu yanzu ba sai anjima ba"
Yace "insha Allah"
Daga haka Umma ta yanke call d'in.
K'awar Raheemah, Labeebah da suke magana da ita ya duba, yace "duk wa'inda suka zo da motocin sun san gidan so I don't think there's something left, xan tafi mata ta bata jin dadi, we talk later", ko sake kallonta baiyi ba ya shige motarsa ya kama hanyar gida. Ita kuwa Labeebah tana shiga gida ta labartawa Mom yadda suka yi da Abdul d'in, basu karishe magana ba ya tafi wai matarsa bata da lafiya, nan fa Mom ta dinga sauke ruwar ashar dana masifa, ita a dole yana wulakanta su, ba don ita ta kara karfafawa Raheemah gwiwan aurensa ba da yau sai tayi ta mata Allah ya k'ara.
Cikin bedroom din ya Shiga ya durkusa har k'asa ya gaishe da Umma. Inteesar da Hadiyya suka tashi suka fita. A gefen gadon ya zauna yana kallon Jaleelah, Umma tace "hala baka san bata da lafiya bane da ka d'auki k'afa ka bar gidan"
Yace "wlhy Umma ban sani ba, bata fad'a min ba"
Tace "ya maka kyau ai, yanzu sai ka zo ka mayar damu gida, sannan ka kawo kudin zuwa asibiti. Yarinya ma tana da juna biyu sannan kace har sai ta fad'a maka bata da lafia kai ba zaka iya yi mata sannu ba? Kasan wahalar d'aukan ciki kuwa?"
Shiru yayi sannan yace "to Umma su had'a kayan"
Tace "to, idan ka fita ka kira min su"
A sitting room ya tarar dasu, yayiwa Inteesar magana taje ta had'a kayan Jaleelah da zasu koma gida dasu, itama Hadiyya ta had'a kayanta kaf sannan Abdul ya d'auko 50k ya bawa Umman, ita kuma Hadiyya ya bata 5k.
Basu jima da isa gidan ba suka wuce asibiti a inda suka yi nasarar ganin likita yayi mata prescribing drugs. Zata dinga zuwa prenatal check up duk ranan Thursday har zuwa lokacinda zata haihu.
••°••
Ranan ango Abdul ya shiga d'akin Raheemah. Tun bayan dasu Umma suka rabu dashi bayan ya kaisu gida take ta expecting call dinshi saboda lokacin yayi mata sallama zai wuce Kaduna amma shiru, har 10pm. Ita Jaleelah ko damuwa ma batayi ba saboda matukar tana kusa da Umma bata damuwa da sha'aninshi bare kuma this time around sunyi rabuwar ba dad'i.
Inteesar kuwa dadi kamar ya nashe ta haka take ji saboda Jaleelah ta sake dawowa gidansu. Gashi sun fara expecting fitowar admission list.
Sai da akayi kwana biyu sannan Abdul ya kira jin lafiyar Jaleelah, shima ta wayar Umma ya kira ba ta wayarta ba. Ko Kadan Umman bata nuna mishi rashin jin dadinta ba akan rashin kiranshi, haka ma Jaleelah, ba yabo ba fallasa ta amsa mishi gaisuwarshi sannan tayi hanging up. Kullum cikin so da k'auna suke da shi da amaryarsa, matukar yana gida to suna nan manne da juna kamar cingam. Ita tana assuming she's the only wife, unlike him da ko da yaushe ya kalli gidan sai ya tuna Jaleelah, everything in the house reminds him about her.
Ranan Friday Jaleelah ta fara expecting zuwan Abdul, amma bai zo ba kuma bai kirata ba, ranan Saturday ma haka, Sunday ma bashi ba labarinshi. Sai da yamma ya kira Umma yace mata ba zai samu daman zuwa ba saboda ayyuka sun yi masa yawa.
Ranan Tuesday
Duk yadda Jaleelah ta so da taga ta b'oye fushinta akan Abdul ta kasa, hakan yasa tayi deciding ta kirashi taji matsayinta a wurinshi. Can backyard taje ta zauna akan bench tayi dialing numbernsa, sai da ta tabbata ta na da enough card a wayarta ta kirashi. Har ya gama ringing bai yi picking ba duk da ta san haka yake yi, bayan call din ya yanke ta sake dialing, ya yanke call d'in ya kirata, ita ma ta yanke nashi kiran ta kirashi da katin ta, hakanan yayi picking, cikin kuna kunai ta gaishe shi, a dak'ile ya amsa mata sannan yace "ya jikinki?"
Gyaran murya tayi tace "do you care to know?"
Yace "I don't!"
Nannauyar ajiyar zuciya tayi tace "nasan it will never bother you saboda you are now cold hearted, saboda ni bani da muhimmanci a rayuwarka, even for the sake of our unborn baby ai zaka kira ni kaji yaya nake, idan kuma saboda kaga ina d'auke da cikin babynka ne that's what gives you the ticket to treat me a trash to ni Jaleelah nayi maka alkawari wallahi sai na cire cikin ko da hakan yana nufin zan rasa rayuwa ta ne, and that shouldn't bother you just as it didn't"
A razane yace "kina hauka ne Jaleelah?"
Tace "ai baka ga hauka za dai ka gani, I'm living for you and your baby amma baka san ina yi, kaga idan na cire babyn I can freely move away, bani da matsala da kai henceforth, ka jira ka ji sakamako", bata jira yayi magana ba ta yanke kiran.
Kai ya d'aga ya kalli makeken agogon dake mak'ale a bango yaga ga karfe shida da rabi har ya gota, ba zai iya zuwa Kano yanzu ya dawo ba amma anyway gobe dole yaje ya ganta kamin ta illata rayuwarta.
[4/17, 7:00 AM] Leenah💋: ⚜Mijin Jaleelah⚜
48
By Linah Shams✍🏼
Washe gari da la'asar taje yin alwala a toilet tsautsayi ya auka mata ta zame a nan ta fad'i, kasa tashi tayi saboda azabar faduwa, da taji ba sarki sai Allah ta kwalla ihu mai k'arfi. Hankali a tashe Umma ta shigo d'akin don ganin musabbabbin wannan ihun, toilet din ta bude ta ganta a kwance tana bleeding, nan hankalinta ya kara tashi. Ciccibo ta tayi ta dawo da ita cikin bedroom ta fara kokarin gyarata amma kamar ana kara tsokano jinin. Rasa wanda zata kira tayi saboda Izz baya nan yaje wurin Abba. Ta fita ta lek'a kitchen ta kira Inteesar tayi mata umurni da ta zo ta tsaya ta duba Jaleelah ita kuma ta nufi makwabto nemo wanda zai taimake su ya kaisu asibiti, cikin nasarar ubangiji tana fita tayi kicibis da Munawwar kamar an jefo shi daga sama. Basu tsaya gaisawa ba tace "Alhamdulillah, zo mu shiga ciki", shi dai binta yayi da idanu yana mamaki, a baya ya dinga binta tana tafe cikin sassarfa har suka isa inda Jaleelah take tana kwance unconscious.
Inalillahi wa inna ilaihi raj'iun yayi ta fadi, tana kwance kamar mataciyya Inteesar na gefe tana zabga kuka. Da taimakon Allah Umma ta d'an gyara ta suka dunguma zuwa asibiti. A emergency aka amshe ta aka saka ta under ICU. Har magrib babu wani labari daga wurin likita kuma still Munawwar yana tare da su.
Abdul kuwa tun around six ya isa gida saboda before closing time ya tashi. Yana isa gidan yaga wayam babu kowa kuma ko da ya tambayi me gadi inda suka je ce mishi yayi shima bai sani ba don lokacin da suka fita yaje kama ruwa. Har yaje yayi sallar magrib ba su dawo ba kuma bai yi hausar kiransu ba.
Haka su Umma suka yi ta zama har akayi sallar isha, lokacin likita ya bukaci ganin mijinta, Munawwar yace mishi ba shi bane mijinta, yace "akwai wani abu ne?", Dr din yace masa "a'a it's okay". Suna gama magana ya d'aga waya ya kira Abdul, da kirari ya bude wayar "ango ango! Ango na Raheemah"
Abdul yayi murmushi yace "kaji matsalarka ai"
Dariya yayi yace "kana ina ne?"
Yace "wlhy gani nan a gidansu Umma, na zo dukansu basu nan kuma shima mai gadin wai bai San inda suka je ba"
Yace "ah to ai muna tare"
Cike da mamaki yace "ina kuka je?"
Yace "muna asibiti"
Gabansa ya fadi, yace "waye ba lafiya?"
Munawwar yace "matarka ce aka kawo ta rai a hannun Allah tana bleeding, dama yanzu doctor ya zo wai yana son ganin mijinta"
Salati yayi ya Sanar ma ubangiji, yace "wani asibiti ne?"
Yace "Kalthoum hospital"
Yace "to gani nan zuwa". Ya yanke call din ya shiga mota. "So this girl is mad, she killed our baby", ya fad'a a ranshi yana driving har ya isa asibitin.
Wurin Umma ya nufa kai tsaye dake zaune a reception ita da Inteesar sunyi zugum, a gefenta ya tsugunna. Mamakin ganinsa tayi, tace "d'an Alhaji", voice dinta ya tabbatar da lallai Jaleelah tayi musu asaran babaynsu, cike da damuwa yace "Umma ta cire cikin ko?"
Zaro ido waje tayi tace "ashe baka da hankali?"
Ya tari numfashinta "Umma hakane mana"
Lokacin doctor iso inda suke yace musu zasu iya shiga su ganta sannan ya juya ya wuce. Inteesar ta fara tashi ta bi hanyar d'akin sannan Umma sai Munawwar da shigowarsa kenan. Sai da suka shiga duka sannan Abdul yabi bayansu yana jin zafin abin da tayi.
Akan rubber armchair dake gefen gadon Inteesar ta zauna, dukansu fuskokinsu na na d'auke da murmushi. Haka ma Umma da taga alamar sauki a al'amrin. Inteesar ta d'an rik'e mata hannu, tace "ya jiki?", can kasan makoshinta tace "da sauki", Umma ta zauna a gefenta tana murmushi still, tace "'yata ya jikin naki?" Itama a hankali ta amsa mata da "da sauk'i", Munawwar ma yayi mata ya jiki ta amsa, amma banda Abdul dake tsaye a jikin k'ofa yana kallonta, saboda tsabar bakin cikin da takaici bai san lokacin da yayi slamming k'ofar ba ya fita, sai lokacin itama Jaleelah tasan akwai mutum a wurin. Ko tsayawa Neman doctor din da aka ce mishi na neman mijinta bai yi ba.
Tab'e baki Umma tayi ta mayar da dubanta ga Jaleelah tana tambayarta ko da kwai abinda take so. Munawwar yabi bayansa amma bai gansa a ko ina ba a cikin asibitin ba, hakanan ya dawo yayi wa Umma sallama ya tafi gobe zai wuce Jos inda yake da zama.
A gidansu yayi spending night d'in, amma zallan bak'in ciki ya hana shi ya runtsa. Tun da ya san tana da juna biyu ya kwallafawa ranshi son babyn, ko mace ko namiji shi dai yana masifar son babyn, har sites yake dubawa yana neman kayan babies wanda zai fara siya nan da k'arshen month d'in, tsattsaurar mataki ya d'auki aniyar d'auka akanta, washe gari da duku duku ya bar Kano ya koma Kaduna, b'acin rai bai barshi ko wanka yayi ba. Sosai Raheemah tayi mamakin ganinsa, sai dai mood dinsa gaba daya ya canja, duk yadda ta so taga ta shisshige masa kasawa tayi, daga karshe ma warning dinta yayi cikin fad'a, ita da yake ba kanwar lasa bace tuni ta watsar dashi ta cigaba da abubuwan da ke gabanta.
Tunda ya tafi bai sake waiwayar Jaleelah ba bare yaji tana nan a raye ko a mace. Kwanansu hudu a asibiti aka sallame ta, inda likitan yayi assuring din Umma cikin ta na nan bai fita ba, sai dai tana bukatar kulawa saboda tana da damuwa don har jinin ta ya hau.
Weekend din gaba d'aya bai zo ba kuma bai kira waya ba. Gabaki d'aya ya canja at once, ko Raheemah baya sakar mata fuska kullum rai a kicincine.
Gajiyan jira Umma tayi sai tayi deciding ita bari ta kirashi da kanta tunda shi yanzu yafi karfin ya kira tunda yayi sabon aure. Time din daya ga call din yana zaune a gefen yana sipping tea, gabansa ya d'an fad'i ya jira call din ya yanke sannan ya kira ta. Cike da ladabi ya gaishe ta, sannan tace "dama na kira ne naji lafiyarka, kasan ita uwa bata manta d'anta"
Shafa kai yayi kamar yana gabanta, yace "afwan dai Umma", tace "kana lafiya dai ko?"
Yace "eh Umma alhamdulillahi"
Tace "ka tabbata?"
Ya amsa mata da "eh", sannan tace "yau yaushe?"
Yace "yau laraba"
Tace "madalla. Jibi jumma'a kenan ko? To idan Allah ya kaimu da rai da lafiya ina son ganinka, kana ji?"
Yace "eh Umma"
Tace "idan kuma kaga dama kar ka zo"
Dafe kanshi yayi, saboda yasan dole idan yaje sai yaga Jaleelah kuma yanzu a halin da ake ciki baya k'aunar ganinta bare su zauna a inuwa daya, yace "insha Allah zan zo"
Tace "to Allah ya kaimu"
Ya amsa mata da ameen ita kuma tayi hanging up.
Ranan Friday nayi bayan ya dawo daga Friday service yayi shirin tafiya Kano, ko bi takan Raheemah baya yi tun ranan daya dawo daga Kano yayi mata masifa take jin haushinsa, shi kuma bashi da lokacin da zai iya rarrashinta a yanzu.
Bedroom dinta ya nufa bayan ya gama shiri, daya ke ba bedroom daya suke sharing ba unlike yadda suke yi da Jaleelah duk da akwai furnitures a dayan bedroom din. Daga gefenta ya tsaya tana kwance akan gado tana shafa waya, yace da ita "na tafi Kano", sai da ta juya masa baya sannan tace "to" saboda tasan wurin Jaleelah za shi kuma tana matuk'at kishi duk da ta san bai fiye zuwa ba. Bai sake bi takanta ba ya fice daga d'akin yayi tafiyarsa.
Yana fita ta da'ga waya ta kwalawa Mom kira. Tana picking tace "Mom"
Mom tace "na'am baby ya kike?"
Tace "lafiya k'alau Mom. Abinda dai kika fad'a min gashi yana ta tabbata"
Tace "mene kenan?"
Tace "zamana a Kaduna mana, gashi shegiyar yarinyar nan tunda muka yi aure bai tab'a zuwa ya kwana a gidanta ba, sai last week ne yaje shima da asussbahi ya dawo"
Mom tace "ai da kin tsaya kallon ruwa da yanzu kwado yayi miki k'afa, wannan ba boka ba Malam sarai zaki iya cin ubanata ki nuna mata ko da goma ta lalace tafi biyar albarka"
Tace "sosai mom, ko da coincidence ban taba gani sunyi waya ba"
Labari suka yi mai tsayi sannan call din ya cimma karshe inda Mom ke ta taya 'yarta murna.
Abdul na isa gidan da Jaleelah ya fara cin karo, tana zaune a main parlour ta d'aura kafafuwanta akan center table hannunta d'auke da remote. Sallama yayi ta amsa mishi ya kawar da Kansa bai ko kalleta ba, ganin yadda yayi mata yasa itama ko gaishe shi bata yi ba. Parlour'n Umma ya shiga da sallamarsa, tana kwance kan sofa tana shan iska. Da fara'a ta tashi zaune tana amsa mishi sallamar sannan tace "marhaba da d'an Alhaji"
Wuri ya sama ya zauna sannan suka yi typical gaisuwa cikin fara'a. Umma bata b'ata lokaci ba tace "sai na ji ka shiru d'an Alhaji, yarinya bata da lafia kai Baka sake dawowa ba kuma baka kira ba"
Dama ya riga ya ayyana a ranshi abinda yasa ta kirashi kenan, shiru yayi bai ce mata komai ba, tace "ka ganta a nan falo kuwa?". Yace "eh"
Tace "to, dama so nake yi ta koma can gidanta da zama idan ka zo hutun karshen mako ka dinga sauka a can alabarshi Inteesar ta dinga zuwa taya ta kwana daga litinin zuwa jumma'a"
Kansa a durkushe yace "Umma ai da kin barta a nan"
Tace "a'a kar a shiga hakkinta, zan dai dinga lek'ata jefi jefi"
Yace "ni Umma da so nayi kawai na sawwak'e mata auren nan taje ta huta hakanan"
Ba k'aramin mamaki Umma taji ba, tace "wai meya sa baka da hankali ne har yanzu?, me kake so ka zama? Sakarai ko me? Saboda kayi sabon aure shine zaka sake ta?"
Yace "a'a Umma, ko kusa"
Tace "to banji ba dai, lokacin da nace ka sake ta me ya hanaka sakinta? Sai yanzu da take da lalura har jininta ya hau sannan kace zaka sake ta?, to kayi kad'an bari in fad'a maka, wallahi ka kuskura ka sake ta sai fushina ya tabbata akanka"
Sai sannan ya d'ago da kanshi ya kalle ta, ya bud'e baki zai yi magana tace "bana son ji. Tashi ka d'auki matarka Ku bar min gida, idan kana iyawa idan kun koma gidan ka kashe ta, ta shi ka tafi"
Jiki a sanyaye ya fita still tana zaune tana kallo, bai ko kalli inda take ba yace "ki dauko hijab dinki" yayi ficewarsa. Ta ji shi amma sai tayi kamar bata ji ba ta cigaba da zamanta hankalinta a kwance. Yafi karfin minti goma yana jiranta a cikin mota amma bata fito ba, zuwa wani d'an lokaci Inteesar ta shigo gidan, ya tsayar da ita ya fad'a mata tace wa Jaleelah tayi sauri. Sai da Inteesar d'in ta shiga tayi mata magana sannan taje ta d'auki hijab d'in da jakar kayanta. D'akin Umma ta Shiga har kasa ta durkusa tayi mata sallama sannan ta fita.
Gidan baya ta bud'e ta saka jakar sannan ta bud'e gidan gaba ta shiga ya tada motar suka bar gidan. Ko nuna alaman akwai mutum a motar bai yi gashi ya b'ata rai sosai. Ita dai ko uffan bata ce masa ba har suka isa gida ta fita daga motan ta d'auki luggage dinta ta shiga ciki. Tunda suka rabu a nan bata sake sa shi a idanunta ba har washe gari da safe, duk tsoronta hakanan ta hakura ta kwana ita d'aya a d'akin duk da tasan watak'ila yana nan a d'ayan bedroom din.
Sai around 10am tana tsaye tana mopping din main parlour ya shigo, bata damu da mood dinsa ba tana mai murmushi taje kusa dashi ta zummar hugging dinsa, ture ta yayi da hannunsa saura k'iris ta fad'i yayi wucewarsa bai ko kalleta ba, a maimakon taji haushi sai ta fara mamaki, "ko dai ya fara shan wani abu ne?"
Itama bata sake bi takansa ba har tayi aikinta ta gama. Kitchen ta shiga ta fara preparing abincin rana, fried rice da salad. Tana yin aikin tana hutawa shiyasa it took her long kamin ta gama.
To 2pm ta gama komai, tayi iyakar kokarinta wurin ganin tayi setting table din da kyau, sannan taje tayi wanka tana fitowa ta gabatar da sallar azahar, sai da ta idar sannan ta yi rubbing Vaseline ta d'an shafa powder sai lip balm. Sanye da hijabinta ta nufi d'akin da Abdul ya kwana don duba shi sannan ta sanar da shi food is ready. Tana bud'e kofar ta shiga kamar ya ga mugun abu yayi sauri ya tashi ya shige toilet ya rufo kofan, sai yanzu taji haushin abinda yayi mata, itama ta fita ta bar mishi d'akin bata sake bi takanshi ba.
0 comments:
Post a Comment