Tunda abokansa suka rakoshi suka gama surutunsu da kawayen amarya bai ce uffan ba.
Asalima bazai iya maimaita magana daya da suka fada ba dan hankalinsa ba akansu yake ba.
Kallan yarinyar da take zaune kan gadon ya keyi baima san me zai soma fada mata ba.Ko kalar fuskarta bai sani ba tana zaune kan gadon lullube da mayafin da bashi da niyyar bude mata.
A hankali kaman mai koyon magana yace mata.
"Sannunki"
Tafi mintina biyar a zatansa ma bataji ba sannan cikin rawar murya tace masa.
"Nagode"
Hannunta tasa tana sake gyara mayafinta dai-dai lokacin da idanuwansa suka sauka kan hannayen nata da suka sha kunshi.
A gefe guda kuma zuciyarsa ta dauke shi ta watsa shi wani lokaci can baya.
*** ***
Da gudunta ta karaso inda yake.
"Yayana kaga kunshina yayi kyau?"
ta fadi da murmushi a fuskarta.
Shima murmushin yai mata yana fadin.
"Kai kai gaskiya baiyi kyau ba"
Fito masa da idanuwanta tayi lokaci daya ta tabare fuska tana shirin yin kuka.
Yana dariya yace.
"I am sorry. Just kidding, yayi kyau sosai. Waye yai maki?"
Juya bayanta tai alamar tayi fushi.
Rufe idanuwansa yai ya bude su a hankali in ba itaba bai fiye son yawan magana ba.
"kinga bara nai tafiyata since fushi kikeyi"
ya fadi yana mikewa. Riqo masa hannu tai sai da yaji wani abu har cikin kansa.
Bayaso tana rike masa jiki musamman in babu tsammani yaji hannayenta a jikinsa. Muryarsa can kasa yace.
"let go of my hand huddy"
Sake makalo shi tai. Saida yai mata tsawa sannan ta sake shi ta ruga kuma.
Yasan tabarar huddy kamar yunwar cikinsa. Kuka zatai kuma bashida zuciyar binta ya lallabata dan tana rikita masa kai da yawa.
*** ***
Idanuwansa da suke rufe ya bude. Hakan yasa zuciyarsa dakatar da inda ta dauke shi takaishi.
Sauke su yai kan yarinyar da take zaune kan tanqamemen gadon dakin.
Wani abu yaji ya soke masa zuciya. Jiyai sam bazai iya jurewa ba ya fice daga dakin yaja mata kofar a hankali.
*
Taji fitarsa. Kwantawa tai kan gadon ko kaya bata da kwarin tashi ta sake.
Kuka ne tayi shi har bata zatan tana da sauran hawayen da suka rage mata.
"Sannunki"
shine kalmar da tunaninsa ya bashi ya furta mata a darenta na farko a matsayin matarsa.
Wato kaddara dabance. Bata taba zatan auren wani bayan Ammar ba.
Fadar sunansa kawai a tunaninta yasa zuciyarta wani tafasa.
Ta gama tsanar mutumin nan tun kamin ma taganshi. Ya rabata da ammar dinta. Wai duk ma matan kano ya rasa wa zai aura sai ita.
Dan tsabar rashin adalci da rashin sanin darajar SO.
Kunshin hannunta ta kalla da bata ga amfaninsa ba can gefen zuciyarta ta tuno wani lokaci tayi kunshin jan lalle suna zaune da ammar.
*** ***
"Babyna ina son kunshi sosai. In munyi aure zaki dinga yimin"
ya fadi cikin karamar muryarsa da take so.
Murmushi tai a kunyace hadi da fadin.
"Saika biya tukunna"
Dariyarsa yai mata ya wani juya idanuwansa da yasan duk idan yayi yana burgeta sannan yace.
"Karki samu damuwa lokaci ne zaki fadamin ma.anar wannan maganar"
"Yaushe kenan?" Ta fadi muryarta da alamar dariya.
"uhm zakiyi bayani ne yarinya"
ya karasa shima da dariya a muryarsa.
*** ***
Wani radadi taji zuciyarta nayi tasan ta rasa Ammar da soyayyar nan tashi mai tsaya mata a rai.
Yanzun duk kulawar nan da alkawurransu sun tashi a banza? A wata daya kacal wani yazo ya ruguza masu soyayyar da sukai shekaru suna ginawa?
Ya tarwatsa musu farin cikinsu saboda sonkai irin nasa. Ta tsani koma waye wannan.
Kanta taji yana mata wani irin ciwo ga zuciyarta da take mata zafi.
Haka tai kwance shiru tana duk wata addu.a datazo bakinta ko zata samu saukin radadin da takeji.
A hankali bacci ya dauketa cike da mafarkin Ammar.
.
Ya rasa kwanciya zaiyi ko zama ko kuma tsayuwa. A duk yanda yai zuciyarsa sam babu dadi.
Auren nan ya sake fama masa ciwukansa yasa suna zubda jini.
Da su umma sunsan bashida sauran zuciya mai numfashi ta bangaren soyayya balle kuma aure da basu matsa masa ba.
ko da yake harda laifin yarinyar da bata gaya musu bata son shi ba.
Shi kam yayi iya kokarinsa na kaucewa auren fin karfinsa akai. Itama yasan kwadayin abin duniya ne yasa ta nace ma aurensa.
A wata dayan da akasa na bikinsu. Kin zuwansa yaga kalar fuskarta kawai ya isa ya tabbatar mata da bai amincewa aurenta ba.
Amman saboda naci da kwadayi irin na matan yanzun saida ta bari aka daura masa ita. Inda huddy ta sha banban da sauran kenan.
Zuciyarsa ta fada masa. Dafe kai yai. Baya son wannan matsayin nasa da wanda yasan yana shirin samunsa a lokaci na gaba.
Yasan bakomai bane zai zabarma kansa amman ya dauka cewar atleast matar dazai spending rayuwarshi da ita shi zai zaba.
Bawai daukarta za.ai a lika masa bada son ransa ba. Gaba daya kansa yai masa nauyi. Neman wanda zai likama laifin abinda yake faruwa dashi yake kuma a yanzun babu wadda tafi dacewa irin yarinyar can dako sunanta ma bai sani ba.
Inma an taba fada a gabanshi bai rike ba dan bata ransa. Baya mata kallan komai sai yar katsalandan da kara masa matsaloli fiye da wanda zuciyarsa take ciki.
Gani yai sai juye juye yake yi ya kasa bacci. Ga ciwon kai na damunshi yama manta cewar tun abincin safe ne a cikinshi da ummansa ta takura masa ya zauna yadan ci. Bacci sam yaki yazo. Dan haka ya tashi ya shiga bandakin shi ya dauro alwala.
Hakanne kawai zai masa maganin wannan tunanin da ya addabe shi. Kuma yasan zai samu nutsuwa ko yaya take.
*
Bude idanuwanta husna tai. Kanta ya wani sara mata. Lokaci daya komai ya dawo mata.
Dacin da take ji a zuciyarta yana nan daram. Wayarta ta lalubo kan gadon, jikinta ya mata wani irin nauyi.
Bata san ta makara ba saida ta duba agogon wayarta taga karge bakwai saura mintina sha biyar.
"Lallai nasha bacci"
ta fadi a hankali.
Sai da kanta yadan saki sannan ta mike zaune. Taja tsaki. Wata kofa ta bude daga cikin bedroom din taga hanya ce.
Ta rufe ta nufi wata ta sake budewa taga dakin canza kayane. Ta juya idanuwanta. Ta sake bude wata taci karo da tankamemen toilet.
Duk haduwa irin ta gidansu da gidajen yan uwa da take zuwa bata taba ganin kayataccen ban daki irin wannan ba. Duk da tsanar gidan da maishi da tai yawa a zuciyarta bai hana ban dakin burgeta ba.
Wanka ta fara yi sannan tai alwala. Sai bayan ta idar da sallah sannan yunwar da takeji ta soma addabarta. Rabon cikinta da wani abu tun safiyar jiya.
Sai da ta gama shiryawa cikin wani less ruwan toka duk da ba wata kwalliya tayi ba kayan sun karbi jikinta.
Fridge din da yake can gefen dakin ta nufa ta bude cike yake da kayan alatu. Fresh milk ta dauka da apple dan ba ma.abociyar cin abu mai nauyi bace. Musamman da sassafe haka.
Bayan ta kammala ta dauki katan mayafi kalar kayanta ta lulluba sannan ta koma kan gadon ta zauna.
Ta kudurta a ranta koda wannan Nataccen zai shigo kaman yanda ta yanke shawarar kiransa dashi tunda ba sunansa ta sani ba. Kuma ba damuwa tai da hakan ba. Bata shirya ya kare ma halittarta kallo ba.
Auren kaddara ne ta riga ta runguma ko da da hannu dayane. Bata san iya lokacin data dauka ba kamin taji an kwankwasa kofar a hankali.
Gabanta taji ya fadi a sanyaye tace shigo. Zuciyarta na dokawa ga mamakinta wata mata ce mai matsakaicin shekaru ta turo kofar hadi da sallama. Amsawa husna tayi.
Har kasa matar ta tsugunna ta ce.
"Ina kwana. Fatan kin tashi lafiya"
Wani irin nauyin matar ya kama husna. Ko bata haifeta ba zatayi kanwa da ita. A kunyace ta amsa.
"Ranki ya dade ko kina bukatar wani abu?"
matar ta tambaya wadda har lokacin tana tsugunne. Cikin sanyin murya tace mata.
"A.a bana bukatar komai nagode. Ya sunanki?"
"Sunana asabe ranki ya dade. An shirya abinci ko da kina bukata nazo ingani. Dan lokacin tashin yarima daga bacci baiyi ba."
Sai da tai jim sannan tace.
"A.a nagode da kulawarki malama asabe. Kije kawai"
"Hutawarki lafiya ranki ya dade "
Asabe ta fadi tana mikewa ta fita daga dakin.
Husna ta yamutsa fuska alamar komai yai confusing dinta.
Wannan girmamawar da matar take mata yai yawa. Duk idan tace ranki ya dade din nan sai taji wani iri.
"Yarima"
Ta nanata tana tabe baki.
"Wa abbana ya auramin ni husna?"
tai tambayar da batasan mai bata amsarta ba. Zuciyarta tace mata.
"da kin maida hankali lokacin da ake miki bayani ai da kinsan kowaye."
Girgiza kanta kawai tayi. Tagaji da komai ma. Tagaji da tunani kan wannan auren tunda an riga an daurashi.
Takuma gaji da tambayoyin da babu mai bata amsarsu.
Hade kai da gwiwarta tai tana sauke wani dogon numfashi......
.
Bai fito ba sai qarfe Goma na safe. Jikinsa sanye da shadda fara ya dora baqar alkyabba data sake taimakawa wajen bayyana kyawunsa.
Kai kawai yake dagawa duk hadiman gidan da suketa zubewa suna gaishe dashi.
Yau sarautar yake ji fiye da kullum magana ma wahala take masa.
Dining room ya shiga komai a shirye yake. Ya samu waje ya zauna.
Kaman yanda suka san tsarin cin abincinsa haka aka shirya masa komai.
Kadan yadan tattaba dan kawai kar ya zauna cikinsa babu komai.
Amman zuciyarsa bata da wadatacciyar natsuwar dazai ji dadin wani abinci.
Baibi takan natacciyar da aka kawo masa jiya ba dan hakan ya yanke hukuncin kiranta.
Ya yanke shawara da zuciyarsa babu ruwansa da ita.
Tunda bata gabanshi inta gaji zata gane hanyar gidansu da kanta danshi bashida wajen da zai mata a rayuwarsa.
Rigimar da yake ciki ma ta ishe shi ba saiya kara da tata ba.
Yana kammalawa ya miqe ya fita.
Bayan mota ya zauna driver dinsa ya tuqa shi zuwa gida.
Tun kamin ya fito daga motar hadimai ke tsugunnawa suna kwasar gaisuwa.
Wasu ya dan daga musu kai wasu kuma ya share abinsa.
Kai tsaye bangarensu ya nufa ya samu ummansa tana babban falo a zaune.
Har qasa ya tsugunna ya gaishe da ita ta amsa masa cike da fara.a ta dora da
"Babana har an fito kenan?"
Haka take fada masa kasancewar sunan mahaifinta da yaci.
"Nazo gaishe dake ne umma"
ya fadi yana murmushi duk da zuciyarsa babu dadi ganin mahaifiyarsa kawai ya bayyanar da murmushi a fuskarsa.
"Ya kwanan amarya?"
Ta buqata sai da yai jim sannan yace
"tana lafiya."
Ajiyar zuciya tai tace.
" babana saika yi haquri komai na rayuwa Allah ya riga ya gama tsarama bawansa. Ka zama mai rungumar qaddara. Kabawa auren nan lokaci sannu a hankali itama zata shiga zuciyarka."
Kawai shiga zuciyar data fada saida yaji ranshi ya sosu. In ya saka wata a zuciyarshi ita kuma huddy ya dauketa ya mayar da ita ina?
"Nagode umma"
ya furta yana ji zuciyarsa na wani tafasa.
ya za.aima wannan natacciyar ta shiga zuciyarsa bayan auren kwadayi tayi.
Ita kanta yasan badon kudinsa da matsayinsa ba babu yanda za.ai tai wautar auren wanda bata taba gani ba.
"Bara na qarasa mu gaisa da mai martaba"
ya fadi yana miqewa.
"Tam Allah yai maka albarka."
"Amin umma."
Fada cike take lokacin daya qarasa.
Fadawa na ta zuba masa kirari.
Gaisuwa ya miqa bai jima ba ya taso abinsa.
*
Yama rasa ina zaije shi ba ma.abocin yawo bane ba.
Babu wata hidima a gabanshi tunda an bashi sati biyu cewarsu ya gama amarci.
Duk idan ya tuna wani takaici kara kamashi yake.
Yai tunanin zuwa lambu sai dai wajen babu abinda zai qara masa illa rashin huddy.
Ashe akwai lokacin da rayuwa zatai masa haka?
Lokacin da zai rasa farin ciki. Lokacin da zaiyi murmushi iya fuskarsa bai kai zuciyaba.
Akwai lokutta da dama da akan bata mishi rai sosai. Amman huddy tana kwantar mishi da hankali.
A haka ya daure aka mai dashi gida.
A can qasan ransa yana fatan Allah yasa natacciya na bangarenta dan bai shirya haduwarsu yanzun ba.
Bai shirya ganin fuskarta ba. Baiki suyita zama haka ba. Dan ba karamar matsala za.a samu ba inhar tace zatai kokarin shiga rayuwarsa fiye da yanda tai masa yanzun.
Yako yi sa.a bata babban falo.
Yai maza ya wuce bangarensa ya kwanta.
Ta danna wayarta tayi game din harta gaji sam komai baya mata dadi.
Ta kunna kayan kallon da suke cikin dakin. Saidai duk wani channel da zata kalla taji dadinshi inta kai kewar ammar zata kara addabarta.
Wasu programs din ita ta koya masa kallonsu. Duk idan yai missing ko yana makaranta ko wata hidima yana dawowa saita bashi labari.
Haka idan ita tai missing zai bata labari. Wasu lokuttan kuma tare suke kallo.
Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Tasa hannu ta tarbesu zuciyarta na mata wani nauyi.
Yanke hukuncin fita ta dan zagaya gidan tayi amman ta kasa.
Duniyar ta hadu ta mata kunci.
Wayarta taji tana ringing. Ta dauka ta duba.
Da hanzari ta daga wayar ganin kausar ce take kiranta.
Bata san lokacin da kuka ya
qwace mata ba.
"Ya salam"
kausar ta fadi tana dorawa da
"lafiya kuwa? Husna meke ya faru?"
Har lokacin kukan bai tsaya ba daqyar ta sami muryar ce mata
"kausar bana son mutumin nan bana kaunar wannan auren.
Ammar nake so shi na tsara rayuwata dashi."
Cikin rawar murya kausar tace
"calm down husna please nasani amman kaddara babu yanda bata zuwama bawa dan Allah kiyi hakuri karki kara jan matsala tsakaninki da iyayenki."
"Hmm kausar bakisan yanda zuciyata take yiba ne shisa inama mutuwa nai na huta"
ta karasa cikin kuka.
"Dan Allah ki nutsu zan sake kiranki anjima inkin dan samu natsuwa kinajina?"
Jin bata da niyyar amsawa yasa kausar kashe wayar.
Ita kam husna jefar da tata wayar tai can gefen gado ta kife kan gadan tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Sai da tai mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet wanka ta sake yi.
Lokacin uku harda rabi dan haka tai alwalar la.asar. Tai mamakin saurin jan lokaci haka. Duk yaushe tai azahar kodan tana jin duk girman dakin ya mata kankanta ne shisa lokaci yake tausaya mata yana gudu?
Inama ace yanda lokacin nan yake gudu haka kaddararta ta wannan auren ta nisanceta.
Ta jima kan dadduma tana addu.o.i kamin ta miqe.
Asabe ta shigo ta sake mata maganar abinci yanke shawarar fita tai kodan taga yanayin gidan da zata kira na aurenta.
Gidan da duk lumfashin da zatai a ciki saita fito dashi da wani nauyi a zuciyarta.
Asabe ta rakata har qayataccen dining room din.
Chips kawai taci tadan sha fruits ta fito zuwa wani tanqamemen falo ta zauna kan kujera.
Daya bayan daya hadiman gidan sukaita zuwa suna gaishe da ita.
Bata qirga su ba amman tana yaqinin zasu kai su goma sha biyar.
Aljazeera take kallo tana ganin yanda duniyar taketa qarewa ko ina yaqi.
Ita kanta hatsaniyar ce take faruwa akanta. Saidai su yawancinsu mutuwa suke suna samun hutu da nutsuwa ta har abada.
Sabanin ita da take tunanin laifin datai take karbar horonsa da riba haka.
.
Ya sha bacci sosai dan jiya da dare sam bai samu wani baccin kirki ba.
Babban falo ya fita hankalin shi a kwance.
Bai zaci ganinta a falon ba.
Zuciyarshi ta wani doka a yan mintina kadan ya manta da damuwarsa idanuwansa suka natsu wajen aika masa da saqonni kyawun yarinyar da take zaune a falonsa.
Hankalinta gaba daya yana kan kallan da take da alama ma bata san shigowarsa ba.
Wannan ce natacciyar da aka aura masa kenan to kyawunta bazaisa yaji komai ba yake fadawa kansa. Dan ya tsani makwadaita masu son abun duniya.
Kujera ya samu ya zauna can nesa da ita.
sai lokacin ta dago ta kalle shi ta sake maida hankalinta kan T.V din kaman baya wajen.
Wani abu yaji ya tokare masa wuya. Sam bai saba mace ta kalle shi tai kaman baya nan ba duk min ajinta kuwa.
.
Yana da kyau shima yasan hakan.
Duk macen data kalle shi saita qara kallansa amman ta wani basar kaman bashi bane zaune a wajen.
Ballantana kuma in tasan koshi waye yanzun zakaga yarinya nasan yai mata magana ta shishshige masa.
Well nasan kudina da kuma matsayina yasa kika nace saikin aureni ya fada a zuciyarsa.
Yasan zata juyo ne ta sake kallanshi.
Ga mamakinsa miqewa tai ta gabanshi ta wuce batare da tayi koda yunqurin nuna yana wajenba tai gaba abinta.
Shi ya bita da kallo cike da mamaki yau shi prince Ishaq mace take wucewa kamar baya wajen.
Lallai akwai aiki a gidan nan. Zai iya jure komai dan tun daga huddy zuciyarsa ta daina numfasawa kowacce mace amman banda shariya.
Izzarsa da mulkin da yake yawo a jininsa bazai jure halin ko in kula ba.
Shi ya kamata ya share mata not the other way round. Domin ita ta nace ma aurenshi bawai shi ya nace ma ta ba.
*
Husna kam ganin natacce da tai a falo ba qaramin girgizata yaiba.
.
Kyakkyawa ne naban mamaki. Kallo daya zakai masa ka fahimci hakan.
Duk da kiyayyar da take masa tasan yafi ammar kyau amman hakan bashi bane zaisa ya burgeta.
Dan yanaji da kudi da kyau ba shi zaisa yai mata katsalandan da fin karfi ba.
Kyawunsa baya gabanta tunda shine silar rabata da farin cikinta.
Taga alamar yana ji da kanshi sai dai itama hakan take.
Ta dawo dakinta ne tabar masa falon saboda karta sake kallan shi ya dauka burge ta yai.
''Babyna bana son inji kince kina kallan indian film kar kije kiga wanda yafini kyau''
maganar ammar ta fado mata.
"Hmm kai bakasan zuciyata ta kulle ba bata ganin kowa sai kai dear idanuwana ne kawai suke ganinsu."
Wannan shine amsar data bawa ammar a lokacin amman gashi yanzun tana hada kyawunsa dana natacce.
Haushi ta bawa kanta hadi da alqawarin zatai qoqarin qin sake kallan fuskar natacce in Allah yaso ya yarda balle harta dinga hada shi da ammar.
*
Washe gari da safe wanda shine kwananta na biyu a gidan natacce.
Ta tashi zuciyarta da nauyi da wata irin kewa ta ammar data addabeta.
Jinta take kaman bata da rai a wasu wajajen na jikinta. Komai tana yinsa ne dan anayi.
Tun jiya bata qara ganin natacce ba ko yana ina shi yasani dan baya gabanta.
Ta kammala duk abinda zatai ta fita zuwa babban falo ko zata dan shaqi banbantacciyar iska da wacce take a dakin baccinta.
Ta tako kenan text ya shigo wayarta. Ganin kausar ce yasa ta dubawa taga tana tambayar ko tana lafiya.
Wani murmushin takaici ya tokareta. Reply take rubuta mata tana tafiya.
Karo taji takaiwa wani abu dabata san komeye ba saboda rubutun da takeyi yasa bata kallan inda zata saka qafarta.
Wani irin qamshi mai sa natsuwa ya doki hancinta. Sai lokacin ta kalla taga inda kafadarta ta doka.
Faffadan qirjinsa taci karo dashi da sauri ta daga kanta tako sauke idanuwanta cikin na natacce da yake mata wani irin kallo da yasa ta jin gwiwoyinta sun mata nauyin gaske.
Ga wani irin kwarjininsa da taji ya cika mata zuciya.
Lokaci daya ta sadda kanta qasa tana kallan takalmin qafarsa.
Zuciyarta na barazanar fitowa daga qirjinta.
A dake yace mata
"ki dinga kallan hanya karkiji ciwo."
Wani haushi taji ina ruwanshi da ita shi baisan ta tsane shi bane ba.
Ta tsani yanda deep voice dinshi tasa tsikar jikinta tashi.
A hasale tace
"nagode bana buqatar tunawarka."
Kamin ya bata amsa ta wuce ba tare data sake kallan inda yake ba.
*
Dakinta ta koma ta zauna kan gado tana maida numfashi kamar wadda tai dambe.
Duk jikinta ya mata wani iri.
Ga idanuwan natacce da takeji har yanzun kaman yana cikin nata.
Hakan yasata saurin rufe idanuwanta ta bude su.
Wasu hawaye masu dumi suka bi fuskarta.
Ta goge in shaa Allah ta daina zubda ma natacce hawayen aurensa dayake kanta.
Tasa hannu ta goge hancinta ko zata goge kamshin sa da take ji har lokacin.
.
Baisan yanda akai bakinsa ya furta masa abinda zuciyarsa take tunani ba.
Sam ba kalaman da kunnuwan natacciya ya kamata yaji bane ba.
Karon datai dashine ya tuna masa wani lokaci shida huddy hakan yasa shi yin irin furucin da yai wa huddy.
A karo na biyu da ta kalle shi ta sake dauke idanuwanta daga fuskarshi tamkar wacce taga wani naman ruwa.
Baisan abinda yasa hakan ya sake bashi haushi ba. Meye a fuskarsa da ta kasa jure kallanshi.
Who is she da zata kalle shi kaman shi din ba kowa bane.
Shin zaima iya tuna tsawon lokacin da wata mace tai masa magana da irin yanayin da natacciya tai masa.
Wai me take ji dashine? Kyau?
In kyaune shima ai yana dashi kuma bayajin tafishi.
Babu macen da zata ki girmama shi ko da bata son shi ballantana wadda ta like ma aurensa.
Well koma menene zai sauke mata shi.
Ba.ai macen da zata share prince ishaq ba ko da kuwa baya sonta ne dole ita ya burgeta.
Kawai ta bata mishi rai.
KiranNasir ne ya katse mishi tunanin da yake ya dauka yana fadin
"mutanen england."
"Yaya ni nayi fushi fa yau kwana nawa baka kirani ba? Tun ranar daurin aurenka"
Yasan bai kyauta ba kam. Musamman da nasir din ya fada mishi kwananshi biyu asibiti bashida lafiya ga exams zasu fara.
"Afuwan Kanina hidimomi ne sukaimin yawa shisa kaga ban kiraka ba. Ya jikinka?"
"Hmm it is alright"
nasir ya fada ya dora da
"Alhamdulillah naji sauqi. Ya gajiyar biki? Ya in-law dina? Kadai fada mata nace she should take care of you ko?"
Sai da yai dim sannan yace
"duk lafiya ya england? Ya karatun?"
"England gata muna ciki yaya,karatu yayi zafi mun fara exams jiya, na qagu inzo gida duk nayi kewarku."
Murmushi yai yana qaunar qaninsa kaman me duk a gidansu jininsu yafi haduwa in baka sani ba bazaka taba cewa baba kawai suka hada mama kowa data shi ba.
Shaquwarsu zata baka mamaki.
Cikin taushin murya Nasir yace masa.
"Are you really ok? I mean is she making you happy? If not yanzun na biyo available flight inyo gida"
Duk da wasan da yake yi bai hana prince ishaq yin yar dariya ba.
"Nas kai din nan ko!" ya fada da fara.a a muryarshi.
Haka suka ci gaba da hira na zuwa wani lokaci kamin suyi sallama.
*
Rayuwa take badan tanajin dadin ta ba. Jinta takeyi kamar wata zombie. Kaman wayar da take da full charge amman babu ko sim balle kai tunanin samun network.
Ga wani ciwon kai da baya sauka bata kuma damu data sha mishi magani ba.
Ga kirjinta data soma tunani sai ta dinga ji yana mata wani ciwo dakyar take tsugunnawa.
Yau kwananta bakwai cir a gidan natacce amman sau uku magana ta taba hadasu. Shima kuma duk kamawa hakan tayi.
Ta wanni fanin ta gode masa dabai yunqurin aiwatar da komai ba akanta da batasan yanda zata dauki hakan ba.
Kuma ta tabbata ba karamun rikici zasuyi ba.
Ta soma mamakin dalilin da yasa ya aureta.
Menene amfanin rabata da ammar ya kawota nan ya ajiye bayan ta kula bama damuwa yai da itaba.
Lokaci daya taji ta qara tsanar shi. Yanzun takan fita babban falo ta zauna banda nan bata zuwa kowanne fanni na gidan saikuma in zataci abinci.
Idan kewa ta dameta ta gaji da kallo Suna dan hira da su Asabe.
Hadiman gidansuna da kirki kuma suna matuqar bata girma.
*
Yauma kaman ko da yaushe yunwa ce takaita dakin cin abincin.
Tana shiga zuciyarta ta doka da qarfi. Ta tsani a gani na hudun nan datai masa zuciyarta ke son fitowa daga kirjinta.
Abu na farko da ya fara zuwa tunaninta shine kamshin sa da ta kasa mantawa.
Inba sharri bane irin na zuciyarta daga nisan da yake sai taji kaman ta jiyo kamshinsa.
Yana zaune kan daya daga cikin kujerun dining room din jikinsa sanye da wata alkyabba Ja.
Hannunsa rike da apple din dayake gutsura da wani irin yanga.
Ta kula duk ganin da tai masa da alkyabba a jikinsa.
Saurin sadda kanta qasa tai kamin ta gama fahimtar kyawun da yayi.
Da juyawa zatai ta koma daki idan ya gama ya fita saita dawo.
wata zuciyar tace nataccen zaki gudarwa?
Qarasawa tai taja kujera ta zauna.
Ko kallonta baiyi ba inma yaji alamar ta shigo bai nuna ba ko a jikinsa.
Apple dinshi yake tauna hannunsa daya kan tablet din shi da take kan table din wajen.
Kawai sai taji jikinta har wani kyarma yake ta kuma rasa dalili. Ga zuciyarta nata dokawa.
Yanayin da takeji bata tunanin wani abu zai iya zama a cikinta.
Dan jitai ya wani kulle ma. Haka ta dauki kankana guda daya da aka yayyanka da cokali mai yan yatsu tasa a bakinta.
Sai lokacin taji idanuwansa na mata yawo a fuska. Bugun da zuciyarta takeyi ya karu.
Sam taqi ta dago kanta duk da abinda idanuwanta keson yi kenan.
*
Yanajin shigowarta da zamanta wajen. Ta kasan ido yaga ta dauki kankana. Ya dago da kanshi ya kafa mata idanuwansa.
Kallanta kawai yakeyi yanda take tauna kankanar ma a yangance take yinsa.
Kanta a kasa. Badai ta dago ta kalle shi ba ballantana ma yai tunanin zatai mishi magana.
He is confused yanzun. Ya soma tababar anya kuwa kwadayine yasa ta nace wa auransa?
To inba kwadayi bane menene dalilinta da ba zata nace bata sonshi ba?
Kuma inda kwadayine zata dinga shishshige masa tana cusa kanta kaman yanda yan mata sukanyi masa.
Sai dai ya kula inda da yanda zatai karta ganshi ma gaba daya datayi.
Bata san koda kallan fuskarshi.
Tana yi kaman ma bata san yana waje ba duk idan sun hadu.
Hakan baqon abune a wajen shi bazai boye ba.
Yana daya daga cikin mazan da suke matukar son kulawa. Wata irin zuciya gare shi.
Yanajin rashin huddy fiye da ko yaushe ya tuna wani lokaci suna zaune.
*** ***
"Ke kaman baki taba ganina ba."
Dariyar nan tata da yake so tai masa tace
"yayana ni bana gajiya da kallan ka fa. Kana da kyau sosai."
Murmushi yai miqewa tai idanuwansa a kanta tace
"kace fa zaka koyamin doki."
"Ban manta ba huddy zan koya maki ba yauba kinga nagaji yanzun ki tafi wajen Nasir."
"Um um yaya nasir bazai yi hira dani ba yana karatunsa ne fa"
ta qarasa maganar a tabare.
Komai na huddy ya masa yana son yarinyar wani irin so da yake ji har jininsa ko dan akwai yan uwanta ka ta jini tsakaninsu ne shisa.
Tana rikita shi da yawa ya qagu watanni shiddan daya rage musu ya cika ya dauke kayarsa.
*
Wata ajiyar zuciya ya sauke.
Ajiyar zuciyar dayai ne yasa husna dagowa ta kalle shi.
.
A dai dai lokacin da shima ya dago daga tunanin da yake.
Ganin ta yasa shi tuna cewar yafa rasa huddy.
Wannan wata ce data shigo rayuwarsa ba tare da amincewarsa ba.
Kaman ko da yaushe saurin sauke idanuwanta tai kaman irin taso taga wani abune kuma ta fahimci baya wajen.
Husna kam bata san dalilin daya sa ya sauke ajiyar zuciya ba haka.
Kaman irin ya tuna wani nisantaccen abu.
Yanayin yanda ya kalleta da kuma yanda fuskarsa ta sauya lokaci daya ta daure mata kai.
Ya kalleta da sanayya a farko kaman taga yaso yai murmushi ne dayan yanayinne bata fuskanta ba.
Kema kike wahalar da kanki akan natacce zuciyarta ta fada mata.
Miqewa tai tabar wajen ba tare data yarda ta sake kallan shi ba.
Ya dafe kanshi. Baya son matsala amman da duk taku daya dazaiyi dan ganin ya guje mata da taku biyu da zatai don samun shi.
Dakinshi ya koma da fita zaiyi yaji sam ya fasa.
*
Kwance yake kan gadonshi maganar mai martaba na masa yawo a kwanya.
So yai ya tafi abuja abinsa yadan bar wannan shiga hanci da qudundunen da natacciya taiwa rayuwarsa.
Yadan samu nutsuwa ko ciwon kan da ke yawan damunshi zai masa sauqi.
Ko zai daina ganin natacciyar yarinyar can tana saka mishi jin rashin huddy.
Amman Mai martaba yace bazai tafiyar wata daya ba tare da iyalanshi ba.
Ko yaushe ta shigo rayuwarshi da har zata zama iyalanshi oho.
Shi baima san ta yanda zai fara ce mata ta shirya zasuyi tafiya ba bayan ko kallan fuskarshi bata son yi.
Bakuma ya son shige mata saboda bai manta da yanayin da tai masa magana ba rannan.
Komai zai iya faruwa in har ta sake daga mishi murya. Bai saba baba. Ba kuma zai fara daukar hakan daga wajenta ba.
Gashi jibi yake son tafiya abuja din. Ya gama shirya komai. Beside akwai abubuwan da yake son aiwatarwa da ba zasu yiwu ya soke tafiyar ba sam.
Duk da bata da wani matsayi a wajen sa. Darajar igiyar aurensa da take kanta ya wuce ace ya aika hadimai sun fada mata sako irin wannan.
Yanda baya son raini yake ji da izza baya son ya raina wani ta ko wanne fanni.
Dafe kai yai ya zama dole ya fada mata duk da baisan kalar zaman da zasuyi ba.
"Kalar zaman da kukeyi anan mana. Ko wa yai harkar gabanshi"
Zuciyarshi ta fada masa.
*
Yau satinta biyu kenan a gidan nan da take wahalar kiransa na aurenta.
Tun ranar da ta hadu da natacce a dining bata sake ganin shi ba. Hakan yafi mata kwanciyar hankali.
*
Tana zaune tana kallo kamshinsa ta soma ji wanda tun randa tai karo dashi ta kasa mantawa.
Ita kadaima in ta fito babban falo ko taje dining dan neman sharri irin na hancinta sai taji taji kamshinsa.
Jin kamshin ya fi na ko yaushe karfi yasata sanin da gasken shine ya shigo.
.
Cike da takaici ta ci gaba da kallonta zuciyarta na dokawa da sauri sauri.
Duk da tasan shine ya shigo bata ko motsa ba balle tai yunqurin kallan inda yake.
Tadai son nesa da ita zai zauna in zaman yazo yi kenan.
Jin zamansa gefenta kan kujerar da take yasa zuciyarta wani irin dokawa da karfin gaske.
Hannu tasa ta dafe kirjinta dan zata iya rantsewa natacce dake zaune gefenta yanajin yanda zuciyarta ke dokawa.
"Ki shirya zamu je abuja jibi in Allah ya kaimu."
Ya furta muryarsa a dake kuma can kasa.
Husna kamar zata kurma ihu. Akan me muryarshi zata dinga tayar mata da tsikar jiki.
Saboda me zaizo gab da ita ya zauna bayan kamshinsa takurata yake.
"Lallaima wannan ya qure rainin hankali sallama bata hadasu,gaisuwa bata hadasu sai yau zai wani ce mata ta shirya zasuje abuja jibi kaman wani ubanta."
Zuciyarta ta saka mata.
Shiru tai ta kyale shi tai kaman bataji shiba ma. Kanta akan tv. Tasa hannu ta dafe kirjinta kaman yana mata ciwo.
*
Wani abu yaji ya tokare masa wuya wai wannan yarinyar me take ji dashine haka da zai mata magana ta share masa.
Yar wacece ita da kamar shi zai mata magana tai kaman bataji shi ba.
Muryarsa a dake can kasan makoshi yace mata
"bana magana amin shiru."
Miqewa tai da niyyar bar masa wajen gaba daya.
Cikin wani irin zafin nama yasha gabanta saida ya tsoratata.
Ganinta tai can like da kasa dan ta tabbata in fuskarshi zata kalla sai ta daga kai. Saboda dogo ne.
Kanta a faffadan kirjinshi ya tsaya.
Kanta ta sadda qasa bata san ganin shi batasan yana mata magana ba taqi ya fita harkarta ba ya kasa gane hakan.
"Matsa in wuce ta fada"
muryarta na rawa kanta a qasa.
"Look at me... ki bani amsar maganar danai miki"
Ya buqata yana zuba mata idanuwansa. Ji yake kamar ya kwada mata mari sai ta dago ta kalle shi.
Baya son maimaita magana. Ko yaita fadar abu daya ka kasa ganewa. Bata mishi rai hakan yakeyi ba kadan ba.
Wannan natacciyar yarinyar ta kasa gane level din hakurin shi yakai karshe.
Numfashi yake ja yana fitar dashi a tsanake ko zai controlling bacin ran da yake ciki.
Husna tana jin hawaye na shirin zubo mata. Sam bata son takura ya kasa gane takura mata yake.
.
Kaucewa tai ya sake tare hanyar yaga alama yarinyar nan tana gwada haqurinsa.
Batasan waye prince ishaq ba harda rashin huddy ya sake mayar dashi haka.
Shi ya sashi zama so cool din nan. Da kudi akace tai masa hakan ba zatayi ba.
Gab da ita ya kara matsawa yau kome take ji saita sauke shi ta kalli fuskarsa.
Yanajin hucin lumfashinta a kirjinsa.
*
Husna kam zuciyarta ci gaba tai da dokawa tunda take bata taba yin kusa da namijin daba muharraminta ba haka.
Ammar ne yake mata yawo a kwanyarta ga kuma qamshin natacce daya addabeta so take ya kauce ta wuce yaqi.
Taga alama inba abinda yace tayi ba bazai barta ba.
"Ba zani abuja ba kabani hanya in wuce."
Ta fada da sauri dan batason yaji yanda muryarta ke rawa.
Murmushi yai duk da baikai zuciyarsa ba.
"I didn't asked you ko zakije ne. Nace ki shirya. And ki kalle ni kibani amsa"
Ya fada idanuwansa nakanta.
Ta soma qulewa a hasale tana shirin yin kuka tace
"wai kai wanne irin natacce ne ka qyale ni nace ba zani ba!"
Kuma sam taki dago fuskarta ta kalle shi.
Lumshe idanuwanshi yai ya bude su a hankali. Akwai rigima kenan ya fada cikin zuciyarsa.
Hannunsa yasa ya dago mata haba cikin idanuwanta ya kalla.
Ji tai duk wani karfi na jikinta yana narkewa. Duk wata gaba ta jikinta ta mata sanyi.
"In kina so zaman lafiya you have to take note of three things.
Ba.amin magana cikin hargowa.
Bana magana aimun shiru.
Bakuma nason gardama da maimaita abu."
Ya karasa yana kallonta deel cikin idanuwa.
Husna tana jib dumin hannun shi dayake kan habbarta a ko ina na jikinta.
Kamar habar tata tana da wani dangantaka da sauran inda take jin dumin nakai mata.
Hannu takai da niyyar ture mishi nashi dai-dai lokacin da mararta ta wani irin murda mata sai da ta ji lumfashinta ya na neman daukewa.
Hannunshin da zata ture ta kama ta rike gam tana kiran
"Wayyo mamina...."
Ji tai abin bawai na wasa bane ta sake kama hannun shi ta riko dam tana yin kasa.
Takan sha wuya ba kadan ba lokacin period dinta sai dai yau saura kwana biyu take tsammani ga abin yazo mata a bazata.....!
.
Prince ishaq kam hannunta yabi da kallo da wani yanayi a fuskar shi.
Gani yai da gaske takeyi cikin alamar tsoro yace mata
"ke meya hakan wai?"
Ta ma kasa magana kawai wayyoo mami take kira ta dafe ciki da hannu daya. Dayan kuma ya rike da na prince ishaq dam.
Baya son ganin wani cikin yanayi. Hakan na tuna mishi abubuwa da yawa.
Tsugunnawa yai Allah ya zuba masa tausayi musamman ma mata.
Cikin damuwa yace
"Are you okay? wai meke damunki?"
Daqyar tace masa
"cikina..."
.
Wani abu da ya dade bai motsa ba a jikinsa yaji. Koma menene yafi karfin zuciyarshi.
Baisan lokacin daya kai hannun shi kan cikinta ba.
"Dai-dai ina yake ciwo? Murdawa yake? Zafi?"
Kaman bata masan yanayi ba. Pillow din kujera ya dauko ya ajiye kasa ya samu ya zame hannunshi daga nata.
Kamata yai ya kwantar.
"Stay right here"
ya fada ya mike da gudu har kafarshi ta taka step din farko na benen zai hau sama kawai kamar wanda aka dokawa guduma akai.
Ya tuna da alkawarin dayai ma kanshi na kin sake taba wani patient a rayuwarsa.
Na barin career din daya so tun yarintarshi. Fasawa yai. Ya sauko da kafarshi.
Wajen husna ya dawo da take kwance ta hade jikinta. Ya tsugunna. Muryarshi a tausa she yace mata.
"Sannu kinji bara na kira doctor? Or we should go to the hospital? Can you walk?
Girgiza masa kai tai muryarta can qasa tace.
"zai tafi basaika kira kowa ba."
Hade fuska yai yace
"Ban fada miki ba.amin musu ba? Ko yan aikin gidan nan ne basu da lafiya hospital ake kaisu."
Duk zafin ciwon da husna take ji bai hanata harararshi ba.
.
A ranta tace wato ko yan aikin gidan nan. Itama ai ba catai tana da wani matsayi ba. Kaman yanda bata gabanshi bata kuma san me yasa ya aurota ba. Haka itama baya gabanta.
Tana kallonshi.Wayar shi ya dauko tana jinsa ya kira.
A wajen ya zauna duk motsin da zatai zai mata sannu.
Har doc din ya qaraso.
Cike da girmamawa taji sun gaisa kuma ya kira shi da prince ishaq.
"Prince ishaq" ta maimaita. Daman sunan shi ishaq kenan.
Tambayoyi doc din ya soma jero mata yanayin amsarta yasa ya fahimci period ne takeyin nata mai wahala.
Yadan rubuta mata magunguna yace bawani abu bane period dinta ne zai dai-dai ta inta sha wannan magungunan.
Ya maida hankalinshi kan prince ishaq yace.
"You know the rest.... "
"I quit. Sau nawa kuke son in fada maku?"
Yai maganar da wani yanayi a muryarsa.
Murmushi kawai doc din yayi yana daukar jakarsa. Yace ma husna.
"Allah ya kara sauki"
Ta amsa da amin muryarta can kasa.
"ka tafi da prescription din saika sa a kawomana"
Prince ishaq ya buqata.
"Alright Nabarku lafiya"
Doc din ya fadi yana ficewa.
*
Kallonta yake a nutse.
"sannu ya fada a cikin sanyin murya."
Tana jin shi. Yanda idanuwansa ke mata yawo a jiki. Shiru kawai tayi masa.
Bata so yana mata magana. Ita dazai tashi yabarta ma da taso.
Jin tayi shiru ga idanuwanta a rufe ya sashi daukar tayi bacci.
Ya sauke wani dogon numfashi. Sam baya son matsala.
.
Auren nan matsala ne a wajen shi. Yanzun idan irin wannan yana faruwa shi ya zai yi ne?
Jin tunani zai haye masa yasa shi miqewa ya fita daga dakin.
Cikin hadiman gidan ya tura mata guda daya don shi baida lokacin dazai bata yana kula da ita tunda bashi ya ajiyeta ba.
Kawai dai wata irin zuciya gareshi idan yaga mata cikin rauninsu.
Sai yanzun ma kalamanta suke sosa mishi zuciya.
Ya rasa meyasa natacciya bata son kallon fuskarsa kuma bata shakkarsa shi.
Wato yanda yake kiranta natacciya shiya bata damar ce masa natacce.
Ko dayake yafi ganin laifin mai martaba a wannan karin.
Shi ya takura masa ya aura masa ita kaman yanda yanzun ma yasa shi tafiyar nan da ita..
Sam baya son daukar kaya don ya tabbata shi zata zame masa.
Abinda zaije yi abuja yana bukatar sirri kuma mai martaba yafi kowa sanin haka.
Dashi kadaine zai zauna hotel abinshi. In yaje gida mutanen da yawa na iya sanin yana garin abuja.
Dafe kai yai ya sauke numfashi dai-dai lokacin da wayarsa ta dauki qara alamar kira ya shigo..
Sanin kowa keda ringtone din yasa shi fito da wayar daga aljihunsa ya lumshe idanuwansa sannan ya dannan wayar ya kara a kunne.
.
"Yaya wacece wannan data dauke hankalinka haka? Kar kasa in tsaneta tun kafin inzo.....baka da lokacina sam."
Cewar nasir da yake maganar kamar zaiyi kuka.
Yasan babu macen da ta isa ta dauke mishi hankali daga kan kanin nasa koda huddy ce balle wannan natacciyar duk kyan da take dashi kuwa.
Kawai dai damuwa ce tai masa yawa.
"Haba mana nasir. Wacece ma ta isa? abubuwane sunmin yawa babu lokaci sosai amman everything is gonna be alright karka damu."
"Yaya sune ko? Ba zasu barmu mu huta ma ranmu bane wai? Ko in dawo gida?"
Prince ishaq zai iya jin tsantsar damuwar da nasir din ya shiga.
Don haka yai kasa da muryarshi yace.
"No! Ka tsaya ka gama exams dinka kana jina ko? I am okay! Komai zai tafi dai-dai in shaa Allah"
"To fadamun what is going on? " nasir ya bukata.
Prince ishaq ya dafe kai.Sanna yace.
"Drop it nasir. I am serious ka kyale maganar nan"
"Hmm"
kawai ya furta ya kashe wayar.
Prince ishaq ya soma tunanin kila dai saiya dinga rubuta abubuwan daya kamata yayi saboda yawan mantuwar da yake yi these days.
Ya saba kiranshi a kullum yaji lafiyarsa da yanda komai na rayuwarsa yake tafiya amman a satikan nan ko dan text din baya samun damar tura masa.
Bayan damuwar da take zuciyarsa baya buqatar wata damuwar kuma dan haka text kawai ya tura masa ya kwantar mada da hankali.
Ji yai iskar wajen ta masa kadan. Ji yake kamar kar nasir su gama exams dinsu ya dawo Nigeria.
Zaman shi a England yafi masa kwanciyar hankali. Yasan masu farautar ransu da son gadon mulkinsu duk abinsu zasu bar masa kaninsa in yana can nesa...
.
Asabe tai zaune a wajenta har doc din ya dawo da magungunan daqyar ta tashi tasha.
Bata jima ba ta samu bacci cike da mafarkin ammar dinta.
Bata farka ba sai da yammaci sosai. A hankali ta bude idanuwanta....yanayin yanda taji jikinta ne tasan cewa ta baci ta dan gyara kwanciya da niyyar tashi taga Asabe a zaune cikin ladabi.
Tasan ita ta shigo wajenta bayan fitar natacce.
"Badai tun dazun kina nan ba?"
Husna ta tambaya da mamaki a muryarta.
"Ranki ya dade ina nan koda zaki farka ki buqaci wani abu....ya jikin naki?" ta amsa a ladabce.
Ita kam bata son wannan girman da suke bata nauyinsa takeji a kunyace tace
"da sauqi zaki iya tafiya abinki nagode."
"Ki huta lafia"
Asabe ta fadi ta mike ta fice,ciwon da takeji yayi sauqi sosai tashi tai ta nufi dakinta.
Kanta tsaye toilet ta nufa ta soma yin wanka don ta tsaftace jikinta.
Ta wanke kayan data bata ta dauro towel ta fito.
.
Wata er jaka data zubo abubuwan da tasan zata buqata ta dauko Always dinta ta duba saura guda biyu.
Ta dauki daya ta shafa farin almiski a jiki saboda yana dauke karnin jini kuma yana maganin ciwon sanyi da qwayoyin cuta da dama.
Bayan ta gama shiryawa tunani take tasan dole ma ta fita shopping tana buqatar kanan abubuwa na amfani.
Tsaki taja a fili tasan ba zata taba tambayar natacce zuwa unguwa ba don bai kai wannan matsayin a wajenta ba.
Shiru tai tana sake sake. Dazun da mararta ke ciwo sai taji kamar yasa hannu ya taba mata ciki.
Wani zafi taji kirjinta nayi. Inba tsabar naci ba inama ruwanshi da ita da har zai taba mata ciki.
Tama manta shi nashi hannun data kama ta rukunkume.
Dan rainin hankali wato jibi zamu tafi abuja ta nanata a zuciyarta wallahi yama rainani ta furta a fili.
Inba raini ba shi yana ma da qafafuwan dazai kwaso yazo wajenta yana fada mata zaiyi wata tafiya kuma har ma da ita.
Tunda a nata tunanin bata ga me yasa zai sanar da itaba. Babu ruwanshi da ita. Ko gaisawa basu taba yi ba.
Sai tai kwanaki bata ganshi ba.
Tome zatai masa in sun tafi taren ko kuma dai salon ya qara takurata fiye da wacce take ciki ne a yanzun?
Gabanta taji ya fadi. Kar dai ace so yake sai sunje abuja yace zai hada shimfida da ita.
Tunanin hakan kawai yasa taji hawaye sun cika mata idanuwa. Goge su tai. Tana tuna alkawarin datai.
Cewar ba zata sake zubda ma auren nataccen nan hawayenta ba.
Ko me zai faru kuwa. Tadai san akwai rikici kwance in har abinda take tunani yai shirin faruwa.
Wata irin kewar ammar take ji kaman zuciyarta zata fito. Wayarta ta dauko.
Tun satin bikinta aka qwace wayoyinta duka aka bata wannan aka kuma sake mata sim babu number din kowa saita yan gida da kuma kausar.
Ta sake jin wata tsanar natacce a zuciyarta. So take taga karfe nawa. Dan tana son fita sosai.
Idonta yakai kan date din wayar. Jitai kanta ya wani sara. Lokaci daya wani irin jiri ya kwasheta.
"06-03-2015"
Bangon wajen ta dafa tana kiran
"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un" babu adadi ko zuciyarta zata samu nutsuwa daga yanayin da ta shiga a wani bangaren kuma tunani yakaita wani lokaci can baya..............!
*** ***
Tana kwance kan gado wayarta ta dauki ruri.
Jin kidan kawai ya bayyana murmushi a fuskarta.
Dagawa tai ta kara a kunne hadi da yin sallama.
Ya amsa mata daga dayan bangaren ya dora da.
"Haba mana tawan. Sai anjamun aji za a daga wayar? "
Dariya tai wani son shi na sake shigarta tace.
"Nawan ni na isa kawai dai..... "
"Kawai dai me?" tanajin murmushin dake muryarshi.
Itama murmushin take a kunyace tace.
"Nayi kewarka ne nawan"
Ajiyar zuciya ya sauke da tanajinta har ta cikin wayar kamun yace.
"Idan na fadi nawa a fili zaiyi yawa tawan. In shaa Allah 06 ga watan 03 zan dawo"
Lumshe idanuwanta tai saboda hawayen da taji suna mata yawo.
Muryarta na rawa tace.
"Wata ukku kenan nawan"
Sai da yai jim sannan yace.
"Tawan ki mun addu.a ke dai. Randa na dawo ba zanyi awa biyu ba za.ai maganar aurenmu in shaa Allah."
Ba zata iya ci gaba da maganar ba. Dakyar tace.
"Nawan zamuyi waya anjima"
Shima shiru yai na wani lokaci kamun yace.
"Babu damuwa. Ina sonki sosai. Take care of you for me"
"You too" ta amsa tana ajiye wayar tasan zai kashe.......
.
Cikinsa yaji yana masa qara kuma yasan yunwace tun tea din daya sha da safe bai kuma samun natsuwar qara saka ma cikinsa wani abuba.
Abinda ya kara bata mishi rai tunanin waccan natacxiyar yarinyar daya fado mishi cikin jerin muhimman tunanin daya kamata ace yanayi.
.
Fada ma kanshi yake cewar auren shi dayake kanta bashi ya nema ba. Saboda haka ba matsalar shi bace. Ya fita hakkinta tunda ya kira mata doc. Ya kuma tura a kula da ita.
So baiga dalilin dazaisa ace yana tunanin ko taji sauki ba. Duk da hakan ba bakon abu bane wajen shi in har akan marar lafiya ne.
Ita din daice baya so tana kutso mishi kai cikin tunani.
Bai baro inda yake ba sai bayan la.asar.
kansa tsaye dining room ya wuce.
Plantain da qwai yaci yasha fresh milk ya fito.
Dakin shi ya shiga ya watsa ruwa ya saka wani farin yadi marar nauyi. Tunawa yai a dining yabar keys dinsa ya fita ya dauko.
A babban falo ya hadu da natacciya kallo daya yai mata zuciyarshi ta wani harba.
Rabon dayaji ta numfasa masa haka tun huddy.
Tayi kyau duk da bayason fadar haka cikin doguwar rigarta abuja style daurin dankwalinta simple sai mayafi.
Tunda can yana son yaga mace cikin shigar kaya purple kowanne irine.
Lokaci daya yaja wata qatuwar qofa ya kulle zuciyarsa baima san yanda akai qofar ta soma budewa ba.
Da alama fita zatayi don akwai qaramin mayafi a jikinta tasa shade shima purple.
Cike da mamaki yake kallonta....kaman koda yaushe kanta a qasa ko inda yake bata kallaba asali ma rabawa tai ta wuce kamar baya wajen.
Ficewa tai abinta.
Murmushi yaji ya qwace masa ya jima rabon dayaji ya bayyana a fuskarsa haka kawai inba mahaifiyarsa yake tare da ita ba ko suna waya da qaninsa..
Yasan ko qofar farko ba zata wuce ba,babu wanda ya isa ya bude mata gate batare da izininsa ba.
*
Hanyo yi taita bi. Bata san gidan nada girma haka ba sai yau.
Daya daga cikin hadiman gidan ta sa ta rakata har kofar gidan.
Sai da ta ganta a wajen gidan tukunna zuciyarta da take dokawa tadan dai-dai tu.
Tana saka shade in dai zata fita amman ba kowanne lokaci ba.
Yauma ta saka ne saboda ya boye idanuwanta dan kallo daya zakai mata ka fahimci ta sha kuka harta godewa Allah.
.
Date din data gani ne ya sake tunzurata ta fita bada izinin mijin da aka daura mata ta fin qarfi ba....duk da sanin hakan ba dai-dai bane bai dameta ba.
Tunda ba tada mota a gidan ta yanke shawarar daukar drop zuwa diamond bank ta ciri kudi sannan kuma ta zo stop and shop ta siyi abinda take buqata.
Mamakin girman gidan take yi harda titi a ciki kaman na estate dinsu ta dan soma gajiya da tafiya dan ba sabawa tayi ba.
Gate tagani a garqame kuma babu kowa a wajen taji wani takaici ya rufeta takai mintina goma a tsaye a wajen wai ko zataga wani ya bullo tasa ya bude mata amman babu kowa.
Juyawa tai idanuwanta cike da hawaye tanata qoqarin tarbesu karsu zubo kenan fita ma in zatayi komin buqatarta saita sauke ajinta ta tambayi natacce kenan.
Bata kaunar abinda zai hada su magana da juna.
Tana son fitar nan kam ko dan gyaran jikinta ma dole ta fita....tafiya take ga nauyi da zuciyarta tai mata.
Ko a wanne hali ammar yake? Allah kadai ya sani tana dai da tabbacin tsakanin jiya da yau ya tsaneta!
Tasan abinda ya kamata tayi....duk da kashe di da mahaifinta yai mata.
Ta tabbata inda shi ya tsinci kansa a halin data tsinta zai fahimci yanda takeji.
Da wani sabon qarfin gwiwar data jima bataji shiba ta juya ta shiga gidan.
*
Prince ishaq kam keys din shi ya dauka ya shiga dakinshi ya dakko system ya dawo babban falo.
Yana zaune a falon hankalinsa akan system dinsa husna ta shigo.
Ta tsane shi wata irin tsana dabata san kalarta ba ko ganinsa bata sanyi.
Ganinsa kuma datai sai yake kokarin ruguza mata dan kwarin gwiwar da take ji.
Abin takaicin ma sai da taji gabanta na faduwa. Ga wani kwarjini da taga ya mata.
Tsaki taja cikin zuciyarta. Batason wannan abin da yake mata ko kadan.
Cikin muryar dabata gane tata bace tace masa
"kazo kasa a budemin gate zan fita."
.
Yaji shigowarta sarai ya ci gaba da game dinsa.
Ya kuma ki abinda tace. Dame take ji da ba zata dauke shi da muhimmanci ba.
Dan shi bata gabansa bashi zai bata damar jin hakan game dasji ba. Ba ai macen da zata nuna masa iyakarsa ba. Ko da huddy ce kuwa.
Dole ta bashi girma ko bata so.
In tana son magana dashi ta zagayo ta kalli fuskarsa.
Husna kamar zata saka ihu don takaici.
"Magana fa nake maka kazo kasa a budemin gate."
Ta sake fadi cikin alamar qulewa.
System dinsa ya rufe ya miqe yana shirin nufar dakinsa.....tasha gabansa shade din idonta ta cire ta kalle shi cikin fuska sosai.
Tunda yake bai taba ganin kiyayya irin wadda yagani a cikin idanuwanta ba.
"Don na tambayeka abu zaka nemi wulaqantani?"
Da mamaki sosai yake kallonta. A. Lokaci daya kuma yana tambayar kanshi akan me zata aure shi.
Ta tsane shi!!!
Yagani cikin idanuwanta bata son shi. Ko da zaka auri mutum dan kudin shi da kalar tsanar datai masa kam zata hakura.
Sai dai duk wannan bai bata damar yi masa magana yanda take so ba.
Kamar wanda magana ke ma wahala yace.
"Not that i care. Ki rubuta ko me kike so aje a siyo miki"
Hawayen ta take iya bakin kokarinta wajen tarbewa. Da tana da bindiga harbe wannan nataccen zatai.
Me yasa baya ganewa ne. Me yasa yake son kara mata kunci har haka.
Muryarta na rawa tace.
"Kabarni da abinda yake damuna. Just kasa a bude mun gate"
.
Kallon nutsuwar nan ya tsaya yake mata.
Kallon da zaka rantse bashida wani muhimmin abun dazai daya wuce ya zuba mata idanuwan shi yana kallonta kamar yana hango har abinda yake bayan fatar jikinta.
Tun da ta kalli idon shi tai magana dazun ta sauke kanta kasa.
Tana jin yanda idanuwansa ke mata yawo. Saboda duk damuwar da take ciki bai hana kamshin shi damunta ba.
Bai kuma hana bangaren zuciyarta dake dokawa duk idan taganshi ci gaba da aikin shi ba.
Ganin suna shirin daukar mintina biyar bai ce komai ba. Yasa ta fadin.
"Bana son duk wata alfarma da zata fito daga wajenka zan je da kaina kuma zan shiga motar haya"
"Motar haya" ya nanata a zuciyar shi. Bawai bai san akwai bayin Allah da suke hawa motar haya bane.
Sai dai har ga Allah ya manta da wani abu waishi motar haya.
Saida yazo daf da ita wannan karon ma kanta a qasa hannu yasa ya dago mata da fuska ranshi ya baci.
Bakuma ya son ana bata mishi rai saboda bako yaushe yake iya controlling abinda yake aikatawa ba cikin bacin rai.
"Ba.a fadamin duk abinda ake so....idan kika qure haqurina ba zai maki kyauba. Daga randa kika tako kafafuwanki cikin gidan nan kike cin alfarmar da duk wanda yake karka shin sa yake ci."
Ganin yanda jikinta ke kyarma a hankali ta kuma kasa kallon idanuwanshi. Duk da idanuwanta akan fuskar shi suke.
Ya jinjina kai kamun yace.
"Ko hadiman gidan nan suke bukatar wani abu fita ake a siyo musu."
Ko ina na jikinta kyarma yake. Karo na biyu kenan daya kai hannun shi a habarta.
Kuma dumin hannun yana shigar mata wajaje da yawa a jikinta.
Hannunta tasa ta ture nashi hannun. Karfin gwiwar da take ji ya gama narkewa. Kawai so take ta samu abinda take bukata.
Karo na biyu da yai misalin matsayin yan aiki da nata.
Ta rasa abinda yasa hakan ya sosa mata rai.
Yana kallonta ta bude jakar hannunta ta dauko dan karamun diary da biro.
Ta rubuta always da recharge card. Ta rubuta pin din ATM dinta daga kasa taja masa layi.
Sannan ta rubuta 10k da take so a ciro mata.
.
Ta dauko ATM din 3k. Always ta 1k. Katin MTN na 2k.
Batare data kalle fuskar shi ba ta mika mishi takardar da kudin da ATM din.
Wani irin kallo yai mata sannan ya karbi takardar kawai yabar kudin da ATM din suka fadi kasa.
Bai jira amsarta ba ya wuce abinsa ya tsani wannan yarinyar da take ji da kanta.
Duk a yanzun ya tabbatar ba kwadayine yasa ta aure shi ba tunda yaga tsanarsa a idanuwanta.
Sai dai ya rasa dalilin dazaisa ta aure shi idan tana masa wannan tsanar.
Waya yai akawo always din guda goma da katin MTN na 5k.
Bai koma dakin shi ba saida ya bar umarnin in an kawo kayan akai ma natacciya bangarenta.
Yana shiga dakin shi ya sake duba list din yaga ta saka a ciro mata kudi.
Yaja tsaki. Baya son harkar karanta ko kadan da zubda mutunci.
Drawer din gadon shi ya janyo ya dauko rappers na kudi yan naira dubu dubu.
Na 50k ya dauka dan babu ma kudin sosai. Sai ya kira an ciro mishi.
Baya jin zai iya sake fita babban falo. Saboda yanda ranshi yake a bace.
Waya yai ma Kamala da yake kula da komai na gidan. Yasa a turo masa wata bangare shi.
Falon shi ya fito ya tsaya. Sai da tazo ya bayar da kudin a akaima natacciyar yarinyar can.
Kan kujerar falon ya zauna. Ya lumshe idanuwan shi yana karanto addu.o.in dazai samu nutsuwa a bisa koyarwar musulunci.
Sallama yaji. Ya bude idon shi. A ladabce hadimar da take tsugunne tace.
"Allah ya ja da ran yarima"
"Lafiya?" ya bukata muryarshi a dake.
A tsorace hadimar tace.
"Rankai dade. Uwargida tace a dawo maka da sakon nan"
"Kije da shi kawai"
ya fada yana kirga 1-10 cikin kanshi.
So yake ya nutsu ko yaya ne kamun ya fitar da kafarshi daga falon nan.
Cikin rawar murya hadimar tace.
"Rankai dade ban fahimta ba"
Cikin tsawa yace.
"ki dauki kudin nace yaren hausa ne bakya ganewa!!!"
Da sauri ta mike tana fadin.
"Allah ya huci zuciyar yarima"
Tana fita ya saka takalmanshi ya nufi sashin husna da tun ranar da aka kawo ta rabon da ko hanyar ya kalla.
0 comments:
Post a Comment