Bacci take sosai taji ruwa ya digo mata a fuska. Ta bude ido.
Prince ishaq ne ya sakar mata murmushinsa mai taushi.
"Lazy bones"
yace cikin sigar tsokana. Ruwan ya sake digo mata. Ta kalle shi. Da alama wanka ya fito dan rigar wanka ce a jikinshi ga gashinsa nan jiqe da ruwan dayake digo mata.
Takan jima batai magana ba inta tashi bacci da safe. Dan haka batace mishi komai ba.
Ta matsa gaba ta sauka daga kan gadon. Bandakin shi ta shiga taga brushes da yawa. Ta dauki daya ta bare tai amfani dashi.
Tai wanka itama sannan ta dauro alwala ta fito.
Ga mamakinta kayanta tagani kan gadon prince ishaq bama guda daya ba ba biyu ba. Sunfi kala goma a ajiye.
Shikuma yana tsaye sanye da jeans blue sai riga fara kal har shiga ido take kaman yanda kyanshi yake mata wasu lokuttan.
Gani yai tana kallonshi ya daga mata gira cikin alamar yadai?
Kaman ya fada a fili tace mishi
"kayana nagani anan"
"Ni ne na dauko"
ya amsa mata a taqaice yana dorawa da
"ki saka muyi sallah lokaci na wucewa"
Jikinta babu karfi ta dauki doguwar riga daya.
Duk yawancin kayan ma sababbi ne.Hanyar bandaki ta nufa taji muryarsa yace
"Ina zakije?"
"Kaya zan sake"
ta amsa mishi a sanyaye. Da murmushi a muryarsa yace
"nan zakibi to..."
Ta juyo ta kalli inda ya nuna. Bama ta taba kula da kofa a wajen ba.
Tazo ta gabanshi ta wuce ta shiga inda ya nuna mata. Dakin canza kayane. Babu komai ciki sai wardrobe da wajen shiri.
Inda zaka rarrataye kaya da wajen takalma. Dakin kanshi da tsarinsa abin kallo ne. Dan ta tabbata shagon wani ne a kasuwar sabon gari. Kaya ta sake.
*
Shi kam prince ishaq har lokacin murmushi yake. Yanzun har mamakin kanshi yake. Yana yawan fara,a kuma yanajin farin ciki har ransa. Husna alkhairi ce a tare dashi.
Dole ya tura mata sonshi kamun lokaci ya cika. Da duk ranakun da suke wucewa da kusancin alkawarin daya dauka. Ya sauke numfashi.
Dai dai fitowar husna. Ta mishi kyau. Namiji ne shi da baya son kwalliya mai yawa jikin mace. Baiqi yaga fuskarta fayau din nan ba. Babu ko powder balle wani janbaki.
"Barin sauri in dauko hijab"
ta fadi tana nufar kofa batare data jira amsarshi ba.
Murmushi ya sake yi. Batai minti biyarba ta dawo. Shiya ja sallar har suka idar. Husna tai azkar dinta na safe data saba tai addu.o.inta,taima nasir na samun sauki.
Saita tsinci kanta da yiwa prince ishaq addu.a da fatan tabbatar alkhairi a zamansu. Abinda bata taba yi ba.
Har wata nutsuwa ta daban taji ta shigeta. Mikewa tai takoma kan gadon ta kwanta.
Prince ishaq kam Qur.an taga ya bude drawer in kusa da gado ya dauko.
Tanata kallonshi ya bude yana karantawa a hankali yanda shi kadai zaiji sautin muryarshi. Sai taji zuciyarta na mata wani iri.
Tana son jin muryarshi yana karantawar. Dan haka tace
"gentle kayi yanda zanji Kaga kai ka samu ladan karatu nikuma na saurare ko?"
Bude murya yai yaci gaba da karatun. Ta nutsu tana saurarenshi. Kira.arsa na burgeta.
Muryarshi na shiga wasu wajaje a jikinta da bata san akwai su ba.
Harya idar yai addu.o.i sosai ya sauke idanuwansa akanta.
"Ina kwana"
ta furta a hankali.
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah"
ta amsa mishi. Bai sake ce mata komai ba.
Ya ja kafet din dayai sallah akai ya linke shi. Kan kujera ya koma ya zauna ya zuba mata idanuwanshi. Tama soma sabawa da yanayinshi.
Zasu iya awanni a haka. Yana kallonta baice mata komai ba.
Ba koyaushe magana ke damunsa ba. Bata san sanda bacci ya sake daukarta ba dan bai wadace taba daman.
Saidai tashi tai ta duba ko ina dakin bataga prince ishaq ba. Ta shiga bandakinshi ta wanke fuskarta da bakinta ta fito. Wajen falon ta fita baya nan.
Ta duba agogo goma harta wuce. Shisa take jin yunwa na damunta.
Dining ta nufa ta dibi iya abinda take jin zataji. Dan har mamaki take. Abincin da ake dafawa bata san ya zasuyi dashi ba.
Ko sun kai su goma ya masu yawa. Dan gashi nan kala kala. Saidai suci su bari. Ta gama tsaf. Ta je dakinta ta dauko wayarta. Ta dawo babban falo.
Prince ishaq ta kira ringing din farko ya dauka.
"Kin tashi?"
Ya tambaya.
Ta amsa da
"um banganka ba ka fitane?"
"Ina garden zaune ina kallon tsuntsaye sunata kukansu. Bakyaji ne?"
Ya fadi.
Sai lokacin ta nutsu take jin kukan tsuntsayen. Cike da mamaki tace mishi
"Ina garden din yake?"
"Cikin gidan nan zakizo ne?"
Ta girgiza kai kaman yana ganinta ta dora da
"Kazo mu tafi wajen Nas"
"Tam kin shiryane in taso?"
Ya fadi daga dayan bangaren.
"A.a barin tashi. Nan da minti talatin kazo nagama."
Ya amsa da
"Tam"
Ya kashe wayan. Tashi tai ta nufi bangarenta. Ta sake yin wanka ta shirya. Tana fitowa ta ga prince ishaq ya shigo.
Kinyi kyau ya fadi yana matsowa dab da ita. Zuciyarta taji tana dokawa tana jin kamshinsa ya cika mata hanci.
Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. Sumbatarta yai a kunci sannan yace
"Mu tafi ko?"
Kai ta daga masa dan bakinta ya mutu. Jikinta ma ba shida kwari. Ya kama hannunta suka fita.
*
Kan kujeru suke zaune sun tisa nas a gaba kaman kallon da suke mishi ne zaisa ya bude idanuwanshi.
Doc dinshi yace musu tun farkawar dayai bai sake ba. Amman babu wata matsala har yanzun.
Su duka bamai magana kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa.
Husna nata kallon Nas. Can taga kaman ya motsa. Matsawa tai da kujerarta kusa dashi sosai ta sake kallonshi aikam ya sake motsawa.
"Gentle!"
Yanayin yanda ta kirashi sosai yasa shi dagowa ya kalleta.
"Nas motsi yake fa ta sake fadi"
Shima matsawa yai kusa suka zuba mishi ido. A hankali ya bude idonshi yana kallon wajaje cikin dakin.
Kamun prince ishaq yace komai husna ta fice da gudu ta kira doctors.
Husna kam ba zata iya kallon koma menene zasuyi ba. Don haka ta fita ta zauna daga waje.
Ba afi minti ashirin ba suka fito. Akace ma husna zata iya shiga. Hamdala suke tayi daga ita har prince ishaq ganin Nas ya nata kallonsu duk da har lokacin baice kala ba.
Saidai murmushi dayake ta musu. Amman likitanshi yace ba komai bane. Zai magana idan ya shirya. Sunkai awa biyu a asibitin har saida bacci ya dauki Nas.
Daqyar prince ishaq ya lallaba husna su koma gida da yamma su dawo. Suna cikin motane ya kira gida yake fada musu.
Kowa yaji dadi ba kadan ba. Anata ma Allah godiya dan babu wanda yaba Nas din tashi.
.
Suna karasawa gida husna zata fita daga mota prince ishaq yace
"zanje wani guri i will call you ok?"
Tadanyi jim sannan tace mishi
"to please take car"
Murmushi ya kwace mishi.
Batasan lokacin data sa hannu taja mishi hanci ba hadi da fadin
"murmushin me kake?"
Ya daga mata girarsa cikin sigar dake kara masa kyau yace
"bakomai naji dadine kin damu dani"
Dariya husna tai kawai ta juya ta bude murfin motar zata fita.
Riqo mata hannu yai yana fito da idanuwa.
"Hussy ina zaki? Bawani a dawo lafiya kiss? Kawai zaki barni"
ya fada a tabare.
Wani lokaci har mamakin shi take. Fuskarshi ta tallabo da hannuwanta ta sumbace a kunci kaman yanda yake mata.
Ta hada da fadin
"tam a dawo lafiya"
"Ko kefa"
Ya fadi yana daria.
"Saina dawo"
Ta fita daga motar bata amsa shi ba. Saboda wani nauyi da bakinta yai mata.
Tasan kota tsaya gardama ko dai tai mishi koshi yai mata. Datai masa ma sai yafi mata sauki. Kamshinsa kawai taji.
Da shi yai mata kafafunta sanyi zasuyi. Ta kuma rasa dalili. Tana shiga daki alwala tayi.
Tai sallah sannan ta sake kayan jikinta ta saka doguwar riga dan duk kayanta sune ta koma babban falonsu ta zauna.
Bata jima ba prince ishaq ya shigo. Sallamarshi ta amsa yace kinyi kyau.
Ta kalli kanta cike da mamaki. Fuskarta dai ba kwalliya. Karasawa yai inda take ya zauna yana mata murmushin sa.
Hannu yasa ya zagaye lebenta sannan yace
"yes kinyi kyau. Ban cika son kwalliya a fuskar mace ba"
Kallon mamaki take masa a ranta tana fadin. Mutane iri iri. Kowa da kalar nasa ra.ayin.
Iska taji ya hura mata cikin fuska ta rufe idanuwanta tana dariya.
"Nagaji fa"
ya fadi da wani yanayi a muryarshi.
"Sannu gentle"
husna tace tana kamo hannun shi. Lokutta irin haka ita kanta mamaki take ba kanta. Haka suka zauna shiru dan ta soma sabawa ma.
*
Sun kai mintina talatin a haka kamun yace ma husn
"in tambayeki?"
Tace
"why not"
"Menene burinki a rayuwa?"
Dariya tai kawai dan burinta shine ta auri ammar kuma sai komai ya canza.
Hannunta taji ya dumtse cikin nashi kamun yace kinyi shiru. A hankali tace
"Najima banida wani buri saina ammar ya karasa karatu ya samu aiki muyi aure and komai saiya canza"
Lumshe idanuwansa yai yanajin wani daci a zuciyarsa. Duk da hakan bai hana ce mata
"i am so sorry hussy"
Kallon fuskarshi tai
"saboda me?"
Ta bukata.
Saida yaja numfashi ya sauke shi sannan yace mata
"saboda nasan yanda akeji in burin mutum bai cika ba. Zanyi komai dan kauce ma shiga tsakanin wani da burinsa"
Hannunshi ta sake dumtsewa sosai tana son fada mishi abubuwan data rasa kalaman da suka fi dacewa ta cikin hannuwan nasu.
Muryarta na rawa tace
"ba laifinka bane"
"Hmm"
kawai ya fadi yana sake kwanciya cikin kujerar abinshi.
Basu san lokaci yaja ba saida sukaji ana kiran sallar la.asar. Su duka suka tashi kowa yai bangarensa.
*
Alwala husna take zuciyarta cike da saqe saqe. Sallar la.asar ta yi ta zauna kan daddumar tana karatun Qur.ani. Data idar ma bata tashi ba.
Akai tai zamanta tana tunanin abinda ta rasa dakuma abinda takejin ta samu a yanzun.
Saidai batasan me zuciyarta take ciki ba game da auren su da ishaq. Kwankwasa kofa taji anyi kamun ma ta amsa ya turo kofar ya shigo.
Yai mata kyau sosai cikin shaddar shi light blue da alkyabba dark blue.
Kodan bata saba ganin shi da kaya masu kala bane. Shisa taga ya mata kyau haka.
Kan gadonta ya zauna.
"In shirya ko?"
Ta tambaye shi.
"Ki dora abu saman kayanki. You are more than ok"
ya amsata. Hakan kuwa tayi. Tare suka fita driver ya kaisu asibiti.
Suna shiga doc din nas suka gani. Da fara.a yace
"yanzun kaizan kira Nas ya tashi yana tambayarku"
Basuma amsa shiba da sauri suka nufi dakin Nas din.
"Antina"
Nas ya fadi muryarshi can kasa. Prince ishaq ya daquna fuska yana fadin
"ita ka soma gani Nas?"
Dariya husna tai ta juya ta mishi gwalo.Ta karasa ta zauna gefen gadon Nas.
"Alhamdulillah Nas sannu kaji Allah ya kara baka sauqi"
husna ta fadi muryarta na rawa saboda kukan da taji yana shirin zuwa mata.
"If you cry bacci zan koma Nas ya fadi"
Sukai dariya gaba dayansu. prince ishaq ya kama hannun Nas yama kasa cewa komai dan farin ciki.
Haka sukaita hira kadan kadan kamun wata likita tazo tace musu zasu gajiyar da Nas lokacin allurar shi yayi.
Fuska a hade Nas yace
"bafa maimun allura. Yaya kwanana nawa a kwance? Kumin alwala in rama sallolin da ake bina tukunna"
Husna tace
"Nas zaka iya kuwa? Jikinka babu karfi"
Prince ishaq yace
"yeah kana da gaskia a kira su su ciccire maka wannan tarkacen if motsaka babu matsala"
Haka kuwa akai. Daqyar likitocin suka yarda dan Nas din da prince ishaq sun dage.
Daga zaune Nas ya rama duk sallolin da ake binshi suna zaune suna hira.
Prince ishaq ya kamashi ya koma kan gado. Aka kira doc dinshi. Ana masa allura bacci na daukarsa.
Basu suka koma gida ba sai wajen 9 na dare. Kowa ya wuce bangarensa.
*
Wanka kawai prince ishaq yai dan sunyi sallolinsu tun a asibiti.
Ya saka kayan bacci ya kwanta. Wayarshi ya dauka ya kira husna. Ringing din farko ta dauka.
"Hello..."
ta fadi muryarta da alamar bacci.
"Hussy..."
ya ja sunanta.
"Gentle na fara bacci fa"
ta fadi a shagwabe.
"Kizo please"
ya bukata.
Husna ta girgiza kai kaman yana ganinta tace
"kayi baccinka nima bacci zan"
Kashe wayar yai. Baya son gardama ko kadan. Ta kira yanaji harta gama ringing bai dauka ba.
Yakai hannu ya kashe wutar dakin. Yai addu.a yaja bargo ya rufe jikinshi duk da yasan ba baccin zai ba.
Yanata tunane tunane abinshi sam baiji turo kofar ba sai motsin mutum dayaji.
Hannu yakai wajen switch din dakin ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina.
Husna ce kwanciya tai batace masa komai ba. Ya rikota jikinshi. Sam taki kallon fuskarshi.
Ya sumbaci goshinta yana fadin
"haba mana hussy."
"Kaine na kira baka dauka ba"
ta fadi da wani yanayi a muryarta.
Sauke numfashi yai yace .
"banason gaddama ne kuma banason takura miki"
Shiru tai tana kwantar da kanta a kirjinshi.
"Saida safe"
ya fadi. Ta daga mishi kai. Saida yai mata addu.o.i ya tofa mata sannan ya kashe wutar dakin yana gyara mata kwanciya a jikinshi.
Yana jin canzawar numfashinta alamar bacci ya dauketa.
Yai murmushi a zuciyarshi yana lissafa watannin daya rage masa ya tura mata sonshi.
Kamun shima ya rufe idanuwansa bacci ya dauke shi.
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Wata Bakwai 7
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Written by
Luβπα Sufyαπ
4⃣2⃣
Suna karasawa gida husna zata fita daga mota prince ishaq yace
"zanje wani guri i will call you ok?"
Tadanyi jim sannan tace mishi
"to please take car"
Murmushi ya kwace mishi.
Batasan lokacin data sa hannu taja mishi hanci ba hadi da fadin
"murmushin me kake?"
Ya daga mata girarsa cikin sigar dake kara masa kyau yace
"bakomai naji dadine kin damu dani"
Dariya husna tai kawai ta juya ta bude murfin motar zata fita.
Riqo mata hannu yai yana fito da idanuwa.
"Hussy ina zaki? Bawani a dawo lafiya kiss? Kawai zaki barni"
ya fada a tabare.
Wani lokaci har mamakin shi take. Fuskarshi ta tallabo da hannuwanta ta sumbace a kunci kaman yanda yake mata.
Ta hada da fadin
"tam a dawo lafiya"
"Ko kefa"
Ya fadi yana daria.
"Saina dawo"
Ta fita daga motar bata amsa shi ba. Saboda wani nauyi da bakinta yai mata.
Tasan kota tsaya gardama ko dai tai mishi koshi yai mata. Datai masa ma sai yafi mata sauki. Kamshinsa kawai taji.
Da shi yai mata kafafunta sanyi zasuyi. Ta kuma rasa dalili. Tana shiga daki alwala tayi.
Tai sallah sannan ta sake kayan jikinta ta saka doguwar riga dan duk kayanta sune ta koma babban falonsu ta zauna.
Bata jima ba prince ishaq ya shigo. Sallamarshi ta amsa yace kinyi kyau.
Ta kalli kanta cike da mamaki. Fuskarta dai ba kwalliya. Karasawa yai inda take ya zauna yana mata murmushin sa.
Hannu yasa ya zagaye lebenta sannan yace
"yes kinyi kyau. Ban cika son kwalliya a fuskar mace ba"
Kallon mamaki take masa a ranta tana fadin. Mutane iri iri. Kowa da kalar nasa ra.ayin.
Iska taji ya hura mata cikin fuska ta rufe idanuwanta tana dariya.
"Nagaji fa"
ya fadi da wani yanayi a muryarshi.
"Sannu gentle"
husna tace tana kamo hannun shi. Lokutta irin haka ita kanta mamaki take ba kanta. Haka suka zauna shiru dan ta soma sabawa ma.
*
Sun kai mintina talatin a haka kamun yace ma husn
"in tambayeki?"
Tace
"why not"
"Menene burinki a rayuwa?"
Dariya tai kawai dan burinta shine ta auri ammar kuma sai komai ya canza.
Hannunta taji ya dumtse cikin nashi kamun yace kinyi shiru. A hankali tace
"Najima banida wani buri saina ammar ya karasa karatu ya samu aiki muyi aure and komai saiya canza"
Lumshe idanuwansa yai yanajin wani daci a zuciyarsa. Duk da hakan bai hana ce mata
"i am so sorry hussy"
Kallon fuskarshi tai
"saboda me?"
Ta bukata.
Saida yaja numfashi ya sauke shi sannan yace mata
"saboda nasan yanda akeji in burin mutum bai cika ba. Zanyi komai dan kauce ma shiga tsakanin wani da burinsa"
Hannunshi ta sake dumtsewa sosai tana son fada mishi abubuwan data rasa kalaman da suka fi dacewa ta cikin hannuwan nasu.
Muryarta na rawa tace
"ba laifinka bane"
"Hmm"
kawai ya fadi yana sake kwanciya cikin kujerar abinshi.
Basu san lokaci yaja ba saida sukaji ana kiran sallar la.asar. Su duka suka tashi kowa yai bangarensa.
*
Alwala husna take zuciyarta cike da saqe saqe. Sallar la.asar ta yi ta zauna kan daddumar tana karatun Qur.ani. Data idar ma bata tashi ba.
Akai tai zamanta tana tunanin abinda ta rasa dakuma abinda takejin ta samu a yanzun.
Saidai batasan me zuciyarta take ciki ba game da auren su da ishaq. Kwankwasa kofa taji anyi kamun ma ta amsa ya turo kofar ya shigo.
Yai mata kyau sosai cikin shaddar shi light blue da alkyabba dark blue.
Kodan bata saba ganin shi da kaya masu kala bane. Shisa taga ya mata kyau haka.
Kan gadonta ya zauna.
"In shirya ko?"
Ta tambaye shi.
"Ki dora abu saman kayanki. You are more than ok"
ya amsata. Hakan kuwa tayi. Tare suka fita driver ya kaisu asibiti.
Suna shiga doc din nas suka gani. Da fara.a yace
"yanzun kaizan kira Nas ya tashi yana tambayarku"
Basuma amsa shiba da sauri suka nufi dakin Nas din.
"Antina"
Nas ya fadi muryarshi can kasa. Prince ishaq ya daquna fuska yana fadin
"ita ka soma gani Nas?"
Dariya husna tai ta juya ta mishi gwalo.Ta karasa ta zauna gefen gadon Nas.
"Alhamdulillah Nas sannu kaji Allah ya kara baka sauqi"
husna ta fadi muryarta na rawa saboda kukan da taji yana shirin zuwa mata.
"If you cry bacci zan koma Nas ya fadi"
Sukai dariya gaba dayansu. prince ishaq ya kama hannun Nas yama kasa cewa komai dan farin ciki.
Haka sukaita hira kadan kadan kamun wata likita tazo tace musu zasu gajiyar da Nas lokacin allurar shi yayi.
Fuska a hade Nas yace
"bafa maimun allura. Yaya kwanana nawa a kwance? Kumin alwala in rama sallolin da ake bina tukunna"
Husna tace
"Nas zaka iya kuwa? Jikinka babu karfi"
Prince ishaq yace
"yeah kana da gaskia a kira su su ciccire maka wannan tarkacen if motsaka babu matsala"
Haka kuwa akai. Daqyar likitocin suka yarda dan Nas din da prince ishaq sun dage.
Daga zaune Nas ya rama duk sallolin da ake binshi suna zaune suna hira.
Prince ishaq ya kamashi ya koma kan gado. Aka kira doc dinshi. Ana masa allura bacci na daukarsa.
Basu suka koma gida ba sai wajen 9 na dare. Kowa ya wuce bangarensa.
*
Wanka kawai prince ishaq yai dan sunyi sallolinsu tun a asibiti.
Ya saka kayan bacci ya kwanta. Wayarshi ya dauka ya kira husna. Ringing din farko ta dauka.
"Hello..."
ta fadi muryarta da alamar bacci.
"Hussy..."
ya ja sunanta.
"Gentle na fara bacci fa"
ta fadi a shagwabe.
"Kizo please"
ya bukata.
Husna ta girgiza kai kaman yana ganinta tace
"kayi baccinka nima bacci zan"
Kashe wayar yai. Baya son gardama ko kadan. Ta kira yanaji harta gama ringing bai dauka ba.
Yakai hannu ya kashe wutar dakin. Yai addu.a yaja bargo ya rufe jikinshi duk da yasan ba baccin zai ba.
Yanata tunane tunane abinshi sam baiji turo kofar ba sai motsin mutum dayaji.
Hannu yakai wajen switch din dakin ya kunna wuta haske ya gauraye ko ina.
Husna ce kwanciya tai batace masa komai ba. Ya rikota jikinshi. Sam taki kallon fuskarshi.
Ya sumbaci goshinta yana fadin
"haba mana hussy."
"Kaine na kira baka dauka ba"
ta fadi da wani yanayi a muryarta.
Sauke numfashi yai yace .
"banason gaddama ne kuma banason takura miki"
Shiru tai tana kwantar da kanta a kirjinshi.
"Saida safe"
ya fadi. Ta daga mishi kai. Saida yai mata addu.o.i ya tofa mata sannan ya kashe wutar dakin yana gyara mata kwanciya a jikinshi.
Yana jin canzawar numfashinta alamar bacci ya dauketa.
Yai murmushi a zuciyarshi yana lissafa watannin daya rage masa ya tura mata sonshi.
Kamun shima ya rufe idanuwansa bacci ya dauke shi.
.
A hankali komai yake tafiyar musu. Sauqi kam ya samu wajen nas watanshi biyu kenan cif a asibiti.
Dan harya soma musu korafin ya gaji shi kam.
Saidai likitanshi yace ba zasu sallame shi ba sai sun tabbatar internal injury din daya samu a kanshi bazai bada wata matsala ba.
*
Prince ishaq da husna kam da duk ranakun da suke wucewa wani irin shakuwa me karfi ce take kara shiga tsakaninsu.
Yanzun kam sai tai kwanaki ma bata tuna da wani ammar ba. Zasu kwana waje daya da prince ishaq. Dan tama saba da duk rikicinsa yanzun.
Suje unguwa tare, wasu lokuttan in yasan zai fita ya jima saiya dauketa ya sauketa asibiti wajen Nas suyita hirarsu in ya dawo ya biya ya dauketa su koma gida.
*
Yauma kaman kullum tana zaune falo tana kallon mbc 3 ya fito jikinshi sanye da farar shadda. Da kyanshi da shaddar suka shigar mata ido. Murmushi tai.
Ya daga mata gira hadi da fadin
Say it hussy"
Ta kalle shi cikin ido tace
"mezan fada?"
Ya sake fadada murmushinsa.
"Kice nayi kyau mana"
ya fada yana karasawa inda take ya zauna.
"Shaddarka tamun kyau"
ta fadi tana dariya ganin yanda ya tabare mata fuska kaman karamin yaro.
Ja mishi hanci tai tace
"sorry gentle kayi kyau kama fi shaddar"
Dariya yai shima ya matsa daf da ita ya sumbaci kuncinta.
Ya bude baki zaiyi magana kenan wayarshi ta soma ringing.
Yasan Nas ne saboda ringing dinshi dabanne dan haka ya zaro wayar daga aljihu ya daga hadi da fadin
"Hello Nas..."
"Yaya kuzo ku daukeni an sallameni"
ya fadi daga dayan bangaren muryarshi cike da farin ciki.
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Wata Bakwai 7
💝💝💝💝 💝💝💝💝
Written by
Luβπα Sufyαπ
4⃣4⃣
Tare sukaje suka dauko Nas. Su duka ukkun kallonsu zakai ka tabbatar fuskarsu dauke take da farin ciki.
Sai hamdala sukeyiwa ubangiji. Haka sukaita hira bayan sun dawo gida. Zaka rantse sun shekara ne basu ga juna ba.
Sai can husna ta kalli Nas ta sake duban agogon dakin. Karfe tara harta dan gota.
Ka tashi ka sha magani kaje ka kwanta lokaci yayi. Husna ta fadi tana kallonshi.
Nas ya wani shagwabe fuska.
"Nikam kinga wallahi bangaji da hirar nan ba"
"Kana son komawa asibiti ne ko?"
Prince ishaq ya fadi muryarshi babu alamun wasa.
Aikamun husna tace wani abu nas ya mike da saurinshi yabar wajen.
Suka hada ido ita da prince ishaq sukai dariya. Miqewa tai itama a kasalance prince ishaq yace mata
"ina zakije?"
"Daki"
ta amsa mishi yanayin yanda yake kallonta na kashe mata jiki.
Hannunsa ya miqa mata alamar taje. Batai masa musu ba tasa hannunta cikin nashi ya dumtse nata sosai kamar zata gudu.
A hankali yajata ta zauna jikinshi. kamshin sa na wani rikitata. Ajiyar zuciya ya sauke ya saka hannuwansa duka biyun yana riketa sosai.
"Hussy naji tsoro sosai"
ya fadi a hankali. Shiru tai dan batasan amsar da zata bashi ba.
Jin hakan yasa shi ci gaba.
"Allah yaga zuciyata ba zata iya daukar rashin Nas ba shisa yabar min kanina."
Ya karasa maganar cikin sanyin murya. Hannunshi ta riqo cikin nata tana kokarin gaya masa kalaman da batasan ta ina zata soma hadasu ba.
Sun jima zaune a haka. Kamun tace masa
"muje mu kwanta ko?"
Kai ya daga mata alamar eh. A hankali ta zame jikinta daga nashi tana miqewa.
Shima tashin yai tare suka nufi bangarenshi. Kan gado ya kwanta da full kayanshi yana wani tabare fuskarshi me kyau.
Husna ta girgiza kai kawai ta shiga toilet ta watsa ruwa. Ta sakko bath robe ta fito. Prince ishaq ta kalla bacci yake
Rabin jikinshi akan gado rabi a kasa. Tai murmushi kawai tasan ya gaji.
Gama shiryawa tai tsaf tasa kayan bacci sannan tazo inda yake ta zauna ta zuba mishi ido.
Zuciyarta na dokawa. Har kasan ranta batason tashin shi. Saidai yanayin kwanciyar dayai zata iya saka mishi ciwon jiki.
Dabara tazo mata nata kamashi ta juyashi ya kwanta kan gadon sosai.
Kafafuwanshi ta kama daqyar ta cicciba su ta dora kan gadon tana uban nishi.
Komun nauyin baccin dayake kana tabashi saiya farka. Husna na tabashi ya tashi saidai ya rufe idonshi kawai yana jinta da nishin da take.
Dariya na son kubce masa. Sake juyashi tai daqyar ta kama hannunshi ta zare alkyabbar dake jikinshi. Ta sake mirgina shi ta zare dayan hannun.
Gefe ta zauna tana maida numfashi. Ta kare mishi kallo. A ranta tace Allah ya kera mazaje a wajen nan.
A fili kuma fada take tiqa a hankali.
"Mutum shi badan dambe ba yabi duk ya tara tsoka. Yanzun da ace baida qiba kamar ni juyashi kawai zan in rage mishi wannan kayan nauyin.
Ai shikenan ka huta. Saikaita baccinka da wannan shaddar nikam dai nagaji"
Prince ishaq baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba. Husna ta zaro ido. Lokaci daya ta hade fuska
"ashe kana jina daman"
Pillow ta dauka ta kwada masa a kirji tana fadin.
"Kasa inata nishi kana jina kai lamo"
Ta sake kwada masa a fuska ya tare yana dariya. Kwace pillow din yai ya rama.
Husna ta dauki dayan pillow din ta sake kwada masa. Fadan pillow suka ci gaba dayi inta kwada masa ya rama. Yanata mata dariya.
Gajiya tai ta ajiye ta kwanta gefe tana maida numfashi. A hankali yakai hannu ya juyo da fuskarta ta kalle shi.
Idanuwanta ta sauke cikin nashi tako yi saurin maida nata kan kirjinsa. Murmushi yai.
Yanajin dadin yanda idanuwansa ke da tasiri akanta. Bata jure kallonsu.
Sauka yai daga kan gadon ya shiga toilet shima ya watsa ruwa ya fito.
Ya shiga dakin canza kaya ya fito daga shi sai boxers da farar singlet.
Ya hau gadon ya kwanta yana janyo husna zuwa jikinshi.
Kaman ko da yaushe sai da taji wata kasala ta saukar mata. Ta kasa sabawa da yanayin nan.
"Nagaji da abuja"
yace mata.
Hannu tasa ta danna mishi kumatu daidai inda dimple dinshi yake.
Sannan tace
"mukoma gida mana gobe indai babu wata matsala"
Ya jinjina kai yace
"haka nake planning nima nasa kamala yai booking mana"
Saida safe tace mishi tana rufe idanuwanta. Addu.o.i yai musu kamar koda yaushe ya sumbace ta a kumatu da goshi sannan yace mata
"Allah ya tashe mu lafiya"
.
Washe gari tunda wuri suka hada abinda suke bukata. Dan husna ma akwatinta datazo dashi shi tadan zuba wasu kayan.
Wasu kuwa nan tabarsu. Daga prince ishaq har nas babu abinda suka dauka sai kayan jikinsu.
Jirgi sukabi zuwa kano. Karo na farko a rayuwar husna data taba hawan jirgi.
*
Daga airport mota suka samu ana jiransu aka dauke su zuwa gidan su prince ishaq. Husna taga karamci ranar.
Takuma ga duk yan uwan prince ishaq masu kyau saidai duk basukai shi kyau ba.
Sun jima sosai gidan dan nan sukai sallar la.asar. Komai husna takeyi a kunyace take yinshi.
Haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyinsu. Musamman mahaifiyar prince ishaq din.
Hakan umma ta kula dashi yasa ta kira prince ishaq din tace
"Babana kazo ku tafi gidanku ko?"
Da murmushi a fuskarshi ya amsa mata ya maida dubanshi zuwa kan husna yace ta taso.
Har kofar falon aka rakasu sannan suka fita zuwa harabar gidan inda motar su take ajiye.
Bude musu akai suka shiga. Sai bayan an rufene husna tace
"gentle banga nas bafa har zamu tafi."
"Yana can bangarensu. Zaizo har gida indan Nas"
ya amsa batare daya kalle taba. Kanshi ya jingina da kujera yai shiru.
Ta kalle shi yau sarautar ta motsa kenan ta fadi a ranta.
Duk da yangarshi a jininsa take. Wani lokaci tana kula in sarautar ta motsa magana ma kan dole yake yinta.
Sai su wuni shiru saidai yai ta amsata dakai kome zatace inyai kokari yace mata um ko um um ko hmm.
.
Satin su biyu kenan da dawowa daga abuja. Komai na tafiyar musu yanda ya kamata.
Saidai prince ishaq baya zama. Sai ya wuni baya gida wanda husna ke bala.in kula dashi a yanzun.
Dan ba zataima kanta karya ba. Ta fara damuwa dashi sosai da sosai. Balle data san masu son illata shin sunfi kusa dashi a kano kan abuja.
Duk idan yai cikakkun awa biyu a waje bataji ya kirata ba ita zata neme shi taji ko lafiya.
*
Ta idar da sallar la.asar ta sake kiran prince ishaq wayar shi har lokacin bata shiga.
Tun karfe biyu take nemanshi shiru haka. Ta nemi number din Nas shima a kashe.
Ta koma dakin prince ishaq din ta kwanta. Gaba daya a tsorace take. Jitai ba zata iya ba ta fito babban falo ta zauna.
Num din shi ta kara nema shiru. Tai rau rau da ido. Saboda bata san wa kuma zata kira taji ko lafiya ba.
Ta yanke shawarar inhar magrib tayi zata fita akaita gidansu ta dubo.
Ta mike kenan ta sake komawa sama yai sallama. Batasan lokacin data karasa inda yake ba da gudu ta fada jikinshi.
Riketa yai yana fadin
"Easy hussy....."
Hawayen da take ta kokarin tarbewa ne taji sun zubo. Ya dagota daga jikin shi yana kallon fuskarta.
"I am so sorry wallahi charge dina ya kare. Hankalina ba a kwance ba. I should have call......"
Batace komai ba ya sake rungumeta tsam a kirjinshi yana jin wani abu game da ita daya girmi so yana kara shigarshi.
Da ita a kusa dashi sai yake jin komai na masa sauki.
"Kinci abinci?"
Daidai lokacin dayai tambayar ne cikinta ya zabi yai wani kuuu alamar yunwa.
Girgiza kai kawai yai ya kama hannunta suka hau sama zuwa bangaren shi.
*
Tana nan zaune ya fito wanka ya shirya. Suka sake sauka kasa zuwa dining din.
Abinci take ci ita. Shikam tana kula da tun zamansu wasa kawai yake da cokalinsa cikin abincin.
Abincin dake bakinta ta hadiye sannan ta kalle shi sosai tace.
"Gentle what is wrong?"
"Kici abincin ki karya huce"
Ya fadi maimakon ya amsa mata tambayarta. Dakyar ta kara cokali biyu saboda ji tai abincin ya fita a ranta.
Kallonta yai. Da gajiya hadi da damuwa a fuskarshi yace.
"Kin koshi"
"Na koshi"
Ta amsa shi tana mikewa.
Magrib sukaji ana kira. Ta kalle shi yace mata suhau sama kawai. Yai musu jam.i dan bayajin fitar ne kwata-kwata.
Sai da suka idar da sallah suka gama addu.o.in da zasuyi. Ya juyo ya fuskance ta sosai yace.
"Hussy ban dawo ba yau. Saboda muna asibiti da Nas..... "
Yana ambaton sunan Nas taji gabanta ya wani fadi. Katse shi tai da fadin
"Me ya same shi kuma? Bayaji sauki ba?"
Hannunta ya riko yace.
"Ki nutsu kiji ni okay? Just calm down"
Kai take daga masa cikin kosawa yaci gaba da fadin.
"Tun rand muka dawo yake fama da ciwon kai sosai. Yana ma mumy korafin kanshi kaman ana hura wuta.
Sunje asibiti sau hudu dawowarmu. Basu fadamin bane sai yau da abin yai girma"
Ajiyar zuciya ya sauke kamun ya ci gaba da fadin.
"Yana da wani ciwo cikin kanshi. Buguwane sosai. An bamu 100% tabbacin zai warke. Amman za ai masa aili a kasar india"
Bama tasan hawaye sun zubo mata ba sai da taga ya matso kusa da ita sosai yasa hannuwanshi duka biyun ya goge mata fuska.
Hannuwanshi tallabe da fuskarta yace.
"He is going to be okay in shaa Allah. Ni dakaina naga file din binciken da sukai"
Muryar ta can kasa tace.
"Yaushe zaku tafi?"
Dan husna kewarshi taji ta soma yi. Yanda take jinma ya danne damuwar Nas.
Ganin yanda idanuwanta suka sake kawo ruwa ne yasa shi fadin.
"Gobe in Allah ya kaimu da yamma. An gama arranging komai....... "
Bata iya tace komai ba. Hannun shi ta cire daga fuskarta tana jingina bayanta da bango.
Takai tsahon mintina biyar tana kokarin hadiye abinda ya tokare mata a wuya kamun tace.
"Allah ya kaimu goben ya bashi lafiya and........ And..... "
Kasa karasawa tayi saboda kukan dake shirin kwace mata.
Kallonta yai yana dakuna fuska saboda bai san me yake bata mata rai banda damuwar Nas ba.
Kokarin karantar fuskarta yake ba saiya tambaya ba. Ya kasa saida tace.
"Ka kula da kanka sosai"
"Husnaaa..... "
Ya fadi da wani yanayi ya dora da.
"Kin dauka zan tafi inbarki ne? Kwana talatin fa. Tare zamu tafi"
Wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki. Duk da damuwar da yake ji bai hana shi sakin mata wani tattausan murmushi ba.
Cikin sigar tsokana yace.
"Hawayen missing dina ne nan aka zubdo?"
Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta saboda wata kunya takeji. Tun tana mamakin damuwarta akan shi harta daina.
Prince ishaq dinne akwai shiga rai ba kadan ba. Yanayin kulawar shi da komai.
Suna nan zaune shiru har akai isha.i. Ta mike dan ya sake jan su sallar isha.i sai taga ya nufi hanyar toilet.
"Ina zakaje?"
Ta bukata.
"Alwala zan"
Ya bata amsa a takaice.
"Oh...... "
Ta fadi da dariya a muryarta. Hakan ya sashi zaro idanuwan shi dan yagama gane me "Oh..." dinta take nufi.
Fuskar shi datai wani ja take kallo. Batasan sanda dariya ta kwace mata ba. Gentle da tusa.
Abin ne taji shi wani gingirin gin. Ga kunyar da tagani a fuskarshi ta sake bata dariya.
Yai tsaye shiru yana kallonta. Bawai dan baya abinda take tunani bane. Yadaiji kunya ne kawai. Kuma taba tan dayaine ya karya masa alwala.
Dakewa yai ya soma takawa inda take yana fadin.
"Hussy ni kike ma dariya...."
Matsawa take tasa hannuwanta tana kokarin tsayar dashi har yakaita bango.
Hannuwan ya rike da duk nashi biyun ya matse ta da bangon sosai.
Gaba dayanta a jikinshi take. Da kamshinsa daya cika mata hanci. Ya sunkuyo da kanshi saitin fuskarta.
Kasa yai da murya sosai dai dai kunnenta yace.
"Dariyar me kike?"
Jikinta ya dauki dumi. Kafafuwanta na mata kashedin kasa daukar nauyinta.
Sumba ya manna mata a fuska da wuyanta ta cikin hijab din dake sanye jikinta.
Jiyai abin na neman fin karfinsa. A hankali ya janye jikinshi daga nata batare daya saki hannuwanta ba.
Dan ya kula batada wadattacen karfi a jikinta. Daya zuwa goma yake kirgawa cikin kansa.
Dan juriyarsa akan husna ta soma kadan. Shi kadai yasan abinda yake ji.
Murya a dishe yace.
"Wuce mu sake alwala"
"Jeka fito tukunna.... "
Ta fadi dakyar. Bai mata musu ba ya saki hannunta ya wuce.
Bango tabi ta zauna kan gado tana maida numfashi.
*
Suna tashi da safe. Sukai sallar subh. Husna ta shiga wanka.
Data fito wanka prince ishaq taga yana cire bedsheet. Abin ya bata mamaki.
"Gentle da kanka. Da saika bari in fito ai. Ko kasa ai maka"
Dagowa yai ya kalleta yace
"Um um fa. Bamai shigarmun bedroom. Ni nake gyara abuna in share. Iyakacin yan aiki babban falo shima sai da dalili"
Kallon shi kawai take cike da mamaki. Ta girgiza kai tace.
"What kind of a prince are you?"
Tambayarta ta bashi dariya. Shiru yai mata ya karasa cire bedsheet din. Ya dauka ya nufi fita da alamu zai bayar ne a wanke.
Mai husna take shafawa sanda ya dawo. Dakin da suke sake kaya taga ya shiga ya fito da wani zanin gadon da rigunan pillow.
Man da take shafawa ta ajiye. Ta mike tana fadin
"Kawo kaje kai wankan ka"
Ba tare daya kalle ta ba yace
"Ki sa pillow case din kawai. I will make the bed"
Sanin baya son gaddama ne yasa tai abinda yace din. Ta taya shi suka gyara gadon tsaf.
Zaka rantse ba tafiya zasuyi yau ba. Hakan daya fado mata a raine yasata fadin.
"Bazai yi kura ba kamun mu dawo?"
Yadan yi jim sannan yace
"Kamala zaizo asa ledoji a rufe komai"
Kamun tace wani abu ya wuce ya shiga toilet.
Fita tai ta nufi dakinta tana mamakin kalar rayuwarshi. Yana da jin kai amman nasa kala dabanne akan yanda take jin labarin yaran sarauta.
*
Ita ya bari ta hada musu kaya. Akwati daya suka dauka. Ta zuba duk wani muhimmin abu data san zasu bukata.
Yan kana na kuma ta zuba cikin jakar hannunta. Karfe uku yai mata waya ya turo kamala yazo ya tafi da ita zuwa airport.
*
Nas take kallo a yanayin shi zaka rantse lafiyarshi kalau. Shi kadai yasan abinda yake ji.
"Oh sannu Nas. Allah ya baka lafiya"
Ta fadi tana jin duk ba dadi.
"Antina amin. Yaya har wani murmushi yake. Nifa nace ya taho dake"
Kwalo idanu husna tai cikin mamaki. Tace
"Allah sarki kanina nagode"
"Idan kun gama ku wuce mu shiga ciki"
Prince ishaq ya fadi. Dan bashida lokacin tsokanarsun nan. Bayajin maganar.
Karfe hudu jirginsu ya tashi zuw india.
.
INDIA.
A bala.in gajiye suka sauka. Musamman Nas da shi kadai yasan yanda yake ji cikin kanshi.
Suna sauka airport ya kira doc din suka sake magana. Zama sukai akazo da motar asibitin aka dauke su.
Hankalin shi bai nutsu waje daya ba sai da aka shiga da Nas checking.
Yaje yagani da idanuwanshi. Gabanshi sukai sedating din Nas din bacci mai nauyi ya dauke shi.
Addu.o.i yai mishi sosai sannan ya fito ya samu husna zaune a waiting room tana jiran shi.
Murmushi yai mata.
"Gajiya ko?"
Ya tambaya yana nazarin fuskarta. Kai kawai ta daga mishi dan bata saba irin wannan tafiyar ba.
Ga yunwa na cinta. Akwatinsu ya dauka cak. Husna ta bishi da idanuwa tana mamakin karfin shi.
Jan akwatin tai dazun amman harda nishinta. Hannu ya mika mata. Ta kama ya dago ta.
Har lokacin murmushine a fuskar shi. Yanda yaga gaba daya husna tai laushi.
Lifter suka shiga ta saukar dasu zuwa kasa. Suka fita daga asibitin. Hannun shi damtse danata kaman wadda za.a kwace.
*
Taxi suka hau. Turancin ba ibdiyan mai taxi din dakyar yake haduwa yace mishi ya kaisu wani hotel mai kyau.
Amman indai da mai kyau kusa kusa da asibitin yakai su nan. Haka kuwa akai wani dan hotel yakai su.
"Hotel ka mubarak" baiyi nisa can da asibitin ba. Kuma yana da dan kyau.
Husna sai dai idanu dan tagama gajiya gabaki dayanta.
*
"Yunwa ko?"
Ya fadi yana zama kusa da husna.
Kai ta daga mishi ya bata fuska alamar baya so. Hakan ya sata cewa
"Eh yunwa fa"
Mikewa yai.
"Barin samo mana abinda zamuci"
Kwanciya tai kan gadon kamun ya dawo.
*
Yanayin yawancin abincin yagani yasan da wuyar gaske ya ciyu wajensu. Dan haka ya siyo musu kaji da lemuka.
Kwankwasawa yai ya tura da sallama ga mamakin shi husna har tai bacci.
Badon yunwar da take jiba sam da bai tashe ta ba. Ajiye kayan yai a kasa. Ya zauna gefen gadon.
Hannunshi yasa ya shafa kuncinta. Ta ture hannun shi tana sake gyara kwanciyarta.
Hannuwanshi yasa duk biyun ya dagota kaman yarinya karama. Ya tallabota jikinshi.
A hankali yake jijjigata yana fadin.
"Hussy mana. Tashi kici wani abu"
Sake langabewa tai jikinshi. Ya lumshe idanuwa yana jin wani yanayi da yake wahalar dashi.
Ya sauke numfashi yana sake girgizata. Amman ina gajiyar datai tasa baccin yaci karfinta.
Yana son ya tasheta da salonshi sai dai shi zai wahala. Yanda yake ji ma a yanzun kawai ya ishe shi.
Dakyar ya samu ta tashi kaman zata saka mishi kuka.
Ya kama hannunta zuwa toilet. Ruwa ya zuba mata yace ta wanke fuska da bakinta.
Ya sake riko ta zuwa bedroom din. Zaunar da ita yai tana wani murza idanuwa da hannuwanta.
Ta wani burge shi. Ya nutsu yana kallonta kamun ya dauko ledar ya bude musu.
Tare suka ci. Tana gamawa ta lallaba tahau gadon ta kwanta.
Prince ishaq sai da yai wanka sannan yazo ya kwanta.
Matsawa yai sosai kusa da husna yanajin wani abu na fisgarsa.
Adduo.i yai musu ya dora kanshi a kafadarta yana sauke numfashi. A haka har bacci ya dauke shi.
*
Da safe da suka tashi. Tana jinshi yana kiran yan gidansu suna gaisawa.
Saita tsinci kanta da jin wata kewar mamanta ta rufeta. Yaushe rabon da ko taji muryarsu.
In sun waya da maheer ne takan ce ya gaishe mata dasu. Ita ta kasa kira.
Su kuma tasan fushin sune bai gama hucewa ba shisa basu neme ta ba.
*
Magana yake ta mata yaji shiru. Karasowa yai ya zauna kusa da ita. Ya taba mata kafada hadi da fadin.
"Hey.... "
Dagowa tai ta kalle shi tana sauke numfashi.
"Tunanin me kike?"
Ya tambaya yana tsareta da idanuwanshi.
"Bako..... "
Hannu ya daga mata alamar baya son ji. Shirun kuwa tai. Sosai ya kalleta cikin fuska sannan yace
"Feel free idan ba zaki iya gayamun damuwarki ba. But yau yaza ma na karshe da zakimun karya"
Mikewa yai dan haka kawai yaji ranshi ya baci. Yasan bashida matsayin da zaice saita fada masa komai dake damunta.
Yana dai fatan wata rana tazo da bama saiya tambaya ba zata fada mishi.
Husna taga alamar ta bata mishi rai. Bawai gaya masa ne ba zata iya ba. Bata son damunshi ne da damuwarta.
Hidimomin shi sun masa yawa. A hankali tace
"Ba haka bane gentle bana son damunka ne fa"
Agogon shi yake daurawa baice mata komai ba. Tasan yana jinta hakan yasa ta ci gaba.
"Yanda kake waya dasu umma ne ya sani missing nawa family din. Shine kawai"
Yanda ta karasa maganar da wani sanyin murya yasa shi fadin
"Crap"
Cikin kanshi. Dan baima san yanda akai tunanin suje gidansu baizo masa ba.
Ya kamata ace koda sau dayane sunje tare ma. Yaga kalar family dinta ya gaishe dasu.
Batare daya juyo ba yace mata.
"Zamu kirasu anjima mu gaishe dasu. Idan mun koma gida zamuje"
Dan kunyarta ma yaji ta wani saukar masa. Gaskiya bai kyauta ba. Ko da sanda aka bashi ita baya so.
Wanda yai maka karamcin aura masa yarka ya cancan ci mutuntawa.
"Allah ya kaimu"
Ta furta. Baya son maganar don haka yace
"Mu tsaya mu karya ko sai munje wajen Nas?"
"Muje din. Kaga munbarshi tun jiya karya farka bakon waje"
Juyowa yai ya kalleta alamar ta shirya. Ya kuma daga mata kai cewar ya ji me tace.
Wani hade fuska tayi yanda yakanyi. Cikin kwaikwayon muryarshi tace
"Bana son magana da kai. Ka bude bakinka ka amsani"
Towel din dake gefenshi ya dauka ya cilla mata a fuska. Yana rufe tashi fuskar da hannuwanshi.
"I love the way you blush"
Husna ta fadi tana sake kwashewa da dariya. Kunyar shi na bata mamaki.
Sai kaga fuskar nan mai kyau tayi wani ja. Bata ga tahowar shi ba saboda dariyar da take.
Jinshi kawai tai kusa da ita sosai. Dariyar ta tsaya mata a wuya.
Idanuwanshi ya zuba mata.
"Kika ce menene?"
Ya fada can kasan makoshi. Ji tai jikinta ya dauki dumi duk wata kalma ta tsaya mata.
Fuskarshi ya matsar kusa da tata. Tanajin numfashin shi saman fuskarta. Ya wani ja iska yana lumshe idanuwa.
Gaba daya yagama saukar mata da kasala. Sumba ya manna mata a wuya da kumatu da kan hancinta.
Tayi luf da ita. Tanajin yanda jikinta ke amsa duk wani sakon da yake tura mishi.
Hannu yasa ya zagaye mata lips sannan ya saka hannun a baki yana tasting kalar man leben data saka.
Dakyar ya samu ya mike. Yana azabtuwa da yanda yake ji din nan. Sai dai inba tabbatarwa yai da son shi a zuciyarta ba.
Bazai iya wuce fiye da yanda yake yin nan ba yanzun. Ko baki bazai iya hadawa da macen da bata son shi ba balle a wuce hakan.
"Tashi ki shirya mu tafi" ya fadi yana maida numfashi.
Yanda ta amsa
"Uhummm"
Din dakyar ya sa shi dariya. Yana kallon yanda take sunkuyar dakai a rashi yace good.
Yanzun ta sa yaji kunya.
*
Suna isa asibitin kuwa Nas yace yanzun ake shirin kiransu saboda za.a shiga dashi aiki.
Prince ishaq ya kalla idanuwan shi cike da wata kaunar yayan nashi yace.
"Yaya ka yafemun. Just incase ko da wani....... "
Girgiza masa kai prince ishaq yake. Muryarshi a dake yace
"No Naseer. No and i mean NO bana son ji. Allah zai baka lafiya munyi addu.a"
"Antina"
Ya fadi yana maida hankalin shi kan husna. Kuka take.
Nas yace
"Haba mana super anty. In kina haka wazai kulamun da yayana"
Hannu tasa tana kokarin goge hawayen fuskarta amman ta kasa.
Prince ishaq ne ya kamota. Tako yi luf jikin shi tana kuka. Dakyar ta samu nutsuwa ta dago.
Tace
"Kanina Allah yasa a fito lafiya. Allah ya baka lafiya"
Ya amsa da amin. Suna kallo akazo aka tafi da Nas din.
Shi kanshi prince ishaq daya tambaya akace masa awanni takwas za.a dauka ana aikin. Sai da yaji jikinshi yayi sanyi.
Nan suka zauna husna ta kwantar da kanta saman cinyarshi.
Shikuma nashi kan na saman kafadarta. Suna jiran hukuncin Allah.
0 comments:
Post a Comment