Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba nace da ita ina dubanta. Yar budurwa ta daga girar idanunta sama cikin rashin fahimta can kuma saita girgiza kai gamida wani alakaron murmushin.
Oh kana nufin daga inda nake? Daga maiduguri nake motar mu ce ta baci ahanya shiyasa mukayi dare yanzun ma direban motar na roka Allah da Annabi shine yakawo ni har nan tayi shiru tana dubana.
Jarumi Hilal ina fatan dai yanzu ka gamsu.....shin na iya shigowa?
Sanyi nakeji Wallahi hilal akwai wani abu a tattare da ita dake damuna fiyeda yawan murmushinta gashi kuma ko ganina azahiri bata taba yi ba sai yanzu yanzu ma kuma acikin Duhu.
.
Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane. Ta ajiye akwatin sannan ta juyo ta dubeni.
In baka damu ba don Allah nuna min bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf.
Gabana yafadi ras na bude baki cikin kaduwa nace Ki shanya kayanki? Na tambayeta adolance. Ta gyada kai. To ke kuma ki zauna dame? Tayi murmushi lokaci guda tasa hannu ta yane jikakkken lullubin dake kanta nan da nan siraran gashin kanta baki sidik suka zubo kan kafadarta koda walkiya ta hasko cikin dakin sainaji zuciyata na harbawa da sauri na dade banga gashi da kyawun nata ba.
Saina zauna aciki idan sun sha iska na maida kayana nafito. Na sunkuyar dakaina kasa a rude kai yau na gamu da gamona. Nace cikin zuciyata koda na daga kaina sainaga ta kura min idanu kamar zata hadiye ni.
Oh hilal yau dai Allah ya nuna min kai. Wallahi kada kaga irin son danakeyi maka duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nace ma acan maiduguri akwai kawayena da yawa da suke kirana da suna HILAL.
Tayi shiru tana dubana me yiwuwa ko don ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata bane.
Hilal yaya kakeyi min irin wannan kallon ne haryanzu baka amince dani ba. Akaro na farko sainaga ta dan hade fuska amma duk da hakan saida idanunta suka nuna alamun murmushi.
Bahaka bane malama abin da haryanzu ke rudani shine zuwanki cikin wannan talatainin dare kuma..... Ta katseni.
Nace dakai motar muce ta lalace haba hilal nifa bakuwarka ce in kuma korata kakeyi shikenan bari natafi nagode. Ta yi nan tsaye bata dai motsa ba akaro na farko saina sassauta murya nace da ita a tausashe.
Toh naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana?
Yar budurwar ta dubi akwatin dake kwance atsakar dakin sannan ta dawo da dara daran idanunta kan fuskata.
Hilal kaga in bakaji dadin zuwana ba simple ce kawai na fita saina fice ma daga daki ko a tasha na kwana da safe na koma garinmu yaya zaka sani agaba da irn wadannan tambayoyi kamar wani tsohon dan sanda. Ta harareni gamida murguda min baki ta danyi shiru tana maida numfashi.
In banda abinka hilal mutane nawa ne suke zuwa ziyartarka arana daga jihohi daban daban ? Kawayena ma nawa ne suka zo gurin ka? Ai kwatancen gidan fitacce kamar ka ba wahala bane musamman agidaje irin wadannan na gwamnati kasan fa kowane gida yanada lamba...kodayake dai zuwana ne kawai baka so. Ta juya min baya tana kallon kofar dakin.
Allah baki hakuri nace da ita a tausashe juyo mu fuskanci juna basai kin juya min baya ba yar budurwar ta juyo da faffadan murmushi.
Lah hilal menene kuma na bata rai nifa ba fushi nayi ba ai ko ina fushi da mutane hilal kai ka wuce nayi fushi dakai idanunta suka kai ga agogon dake makale abangon dakin. Na dubeta nima karfe biyu da rabi na dare 2:30am
.
Lah wannan ai hotonku ne na fim din Daren Mutuwa. Budurwar tace cikin karaji sannan cikin hanzari ta matsa kusa da agogon ta kura masa idanu.
Nikuwa hilal daman inason na tambayeka na dubeta cikin mamaki.
Me zaki tambayeni? Yar budurwar ta dora dan yatsanta na hagu akan hoton ta nuna fuskar Lauriyya tace. Amma wannan yarinyar ko agaske ba'a fim ba budurwar kace ko? Naji gabana yafadi ras na girgiza kai.
Kokusa kada kiyi tunanin haka fim ne kawai kinsan ku yan kallo kusan ko yaushe kuna da wannan kuskuren fahimtar.
Irin kallon datakeyi mane a fim din na lura ya wuce na wasa..... Na dubeta akaro na farko sainayi mata murmushin yake..bakya rabuwa da kame kame baiwar Allah bakisan yan dirama bane yanzun nan sai suyi miki abu kiga kama da gaske nan kuwa karya suke. Bata juyo ta kalleni ba haryanzu kallon hoton take amma na lura da murmushinta ba zato ba tsammani saita juyo ta fuskance tace.
Ai kuwa kyakkyawa ce. Mukayi shiru na tsahon lokaci muna duban juna.
.
Nuna min bandaki hilal kada mura ta kamani da wannan jikakkun kayan dake jikina.
Zo muje nace da ita domin nagaji da jayayya.
Nashiga gaba tana bina abaya kamar bawa da balarabe bandakin acan bayan falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin ta cikin falon batareda k fita waje ba.
Ga kofar nan nace da ita ina duban yala yalan gashin kanta. Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta shige bandakin gamida rufo kofar gararam da karfin gaske karar rufr kofar suka cakude da rugugin aradun nayi sauri na rufe kunnena.
Akwai lokuta da dama da bana son sautin aradu domin ji nake kamar ni zata fadowa......
.
Domin ji nake kamar ni zata fadowa..
.
Na juya ahankali na nufi dakin ina shiga saina janyo kofar dakin amma ban rufe ta gaba daya ba. Na zauna abakin gado nafara jujjuya batun wannan kyakkyawar budurwa mai ziyarar tsakar dare cikin zuciyata.
Akwai wani abu atattare da ita dake bani tsoro na lura da ita ko kusa ko alama batada tsoro haka nan batada kunya kuma babu alamar bakunta ajikinta bugu da kari kuma acikin amsoshin tambayoyin danayi mata akwai amsa daya na tabbata karya takeyi.
.
Shin duka duka wata na nawa da tarewa awannan gidan da har maziryata na zasu kwatonta mata inda nake? Nidai a iya tunanina tun dana tare agidan bansamu wani maziyarci daga bakuwar jiha ba ina nan zaune ina jiran fitowarta na dubi agogo karfe uku saura kwata 2:45am nasan ni da sake samun wani isashshen barci kuma sai abinda hali yayi tunda dai nan sa sa'o'i biyu da motsi zamu fita sabon fim dinsu Alhajiji. Nayi murmushi sa'ar dana tuna yaudarar da Lauriyya tayiwa alhajiji kai wannan al'amari da daure kai yake nace da kaina saikayi mamakin yadda kudi da mata suke tsananin tasiri azuciyar Mazaje.
Naji gabana yafadi sa'ar da wani tunani ya fado min nan da nan naji gumi ya fara sartu agoshina yanzu idan garin Allah ya waye wani kokuma kawuna yazo ya sameta adakin nan me zance dashi? Kirjina yafara dakan uku uku tuni nasan mutanen unguwa sun dade suna zuzzuga kawuna akan wai dole sai ya hanani harkar wasan kwaikwayo domin wai duk yan wasan kwaikwayo yan iska ne marasa mutunci da kyar nasamu na shawo kansa. To yanzu kuma bayan duk wannan idan yasami mace ta kwana adakina fa?
Gumi yaci gaba da sartu akan goshina kaga dan samari wata zuciya tace dani abu mafi sauki shine data fito daga bandaki katafi da ita gidan kawunka ka kwankwasa masa kofa nasan in nayi masa dogon bayani yana iya fahimta sai su kwana tare da matarsa.
Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji wani abu kamar sautin mota wajen gidan na dubi agogo karfe uku harda kusan rabi 3:30am kai amma dai ta dade cikin bandakin nan kodana lissafa sainaga kusan sa'arta guda aciki na mike tsaye cikin sauri na nufi falon ina zuwa saina wuce kai tsaye zuwa kofar da zata kaini har bandakin ga mamakina sainaga kofar a bude. Gabana ya ya fadi na mtsa ahankali na kara kunnena ajikin kofar bandakin ko zanji motsi shiru sai sautin zubar ruwan sama akan kwanuka zuciyata na harbawa saina kwankwasa kofar bandakin. Malama haryanzu kina ciki? Shiru ta gaida kunnuwana.
Malama ina kike ne? Na sake kiran sunanta to saidai kuma ni kaina nafara tunanin bazanji amsar komai ba.
Na bude kofar bandakin ahankali sainaga WAYAM. Babu ita babu alamarta. Nan da nan na ruga aguje zuwa kofar gidan. Ina kike ne? Adaidai lokacin ne to naji sautin injin mota an tuka anbar gidan. Nakarasa aguje amma ni kaina nasan bazan taba samun motar ba na tsaya sororo ruwan saman na dukana ina hangen danjar motar tana daukar idona kamar gauta acikin rana.
Sannu ahankali har na daina hangota.
.
UKU 3
.
Nadawo cikin dakin jikina na rawa kamar tsohuwar data sami kwarto karkashin gado. Na zauna jagwaf atsakar dakin kamar tsohuwar saniya na kurawa akwatin data bari danu sama da tambayoyi dari suka fara turereniya cikin zuciyata.
Shin wacece ita? Daga ina take? Menene dalilin zuwanta? Yanzu kam dana tabbata TA GUDU na tabbata duk abinda ta fada abaya karya takeyi. Sannan babu zato babu tsammani saina tuno da akwatin datazo da ita.
Na mike zumbur kamar an sokeni da kibiya na nufi inda akwatin take jikina na tsuma na daukota na dora akan gado sannan na fara kokarin budeta. Atunanina acikin akwatin ina iya samunwata shaida da zata sanar dani ita wacece. Allah ma ya taimakeni data bar akwatin nace cikin zuciyata.
Na danna mabudan akwatin ina mai wasi wasin budurwar ga mamakina sainaga ta bude fayau. Na dubi cikin akwatin ina mai mamakin ganin babu komai ciki sai wani dan kyallen yadi fari lullube da wani abu. Jikina ya dauki rawa kamar mazari. Nasa hannuna kan farin kyallen sannan na janye farin kyallen.
Numfashina ya kauracewa kirjina yawun bakina ya kafe kana yar autar cikina ta manne jikin hanjin cikina. Akwance male male akasan akwatin.
DAN JARIRI NE.
Sabuwar haihuwa kyakkyawa dashi kamar dan larabawa akusa dashi kuma takarda ce ko liketa ba'ayi ba ajikinta sakone a rubuce kamar haka........
.
HILAL.
Na dade ina ganin fina finanka kuma kana matukar burgeni hakan nema yasa begenka yafara mamaye zuciyata. Hakika tun danake arayuwata ban taba ganin jarumin danake kauna ba kamar kai ka iya shiri kwararrene kai mai burge yan kallo to saidai kuma katsam sai gashi acikin fim dinka na DAREN MUTUWA ka bani haushi kasa na tsaneka. Lokacin da ka dauki jaririn nan acikin fim din zaka jefa shi cikin rami sainaji kamar da gaske zaka jefa ciki.
Baka dade ba da gama fim din sai nima na sami nawa jaririn abin dai kamar acikin dinka na daren mutuwa CIKIN SHEGE NE don haka sai naga abinda ya dace shine na sako shi cikin akwati na kawo maka shi tunda dai ka saba jefa jarira acikin rami me yiwuwa kana iya rabani da nawa abin kunyar ka taimaka ka Jefar min da shi. In kuma kana so to gashi nan nabaka shi kyauta a matsayin ka na kwararren jarumin fim din
DAREN MUTUWA.
Sai anjima kada ma ka nemeni domin bazaka taba samuna ba domin GARIN MU DA NISA.....!
.
NA ajiye takardar cikin akwatin jikina na rawa sannan na dubi jaririn dake kwance cikin akwatin sainaga kamar yanayi min dariyar kuda. Na dafe kirjinsa da tafin hannuna na girgiza kai cikin Kaduwa lallai kam kyauta ta musamman. Hakika kam nayi dace da kyautar kyakkyawan jariri in da ba don MATACCE BANE.
.
*********** ************ ******************
Idanuna suka fara zafi banyi mamaki domin gumin dake sartu akan fuskata kamar ruwa tuni yafara shigar min idanu.
Nasake duban kyakkyawan jaririn dake kwance acikin akwatin na tsahon lokaci sannan sannu ahankali saina janyo farin kyallen na lullubeshi gami da rufe murfin akwatin ahankali kaikace tsoro nake kada na tashe shi daga barcin dayake. To saidaikuma nasan shi da farkawa sai ranar da aka busa kaho.
Kafin na rufe akwatin saida na dauke wasikar da budurwar tasa aciki na tura ta cikin aljihuna sannan na mike tsaye ina muzurai ni kadai kamar tsararraren kwarto.
Shin wace mata ce wannan? Shin danta ne? In kuma bana ta bane menene alakata da jaririn menene kuma dalilin dayasa ta rasa wanda zata kaiwa gawar jaririnin sai Ni? Kai wannan rashin imani na mutanen duniya da yawa yake.
Haryanzu ba'adaina tsugu uban ruwan saman ba haka nan lokaci lokaci saikaji an ruguza aradu kamar ta tsaga dakin. Ama ni duk wannan ba ita bace agabana babban abinda yafi tayar min da hankali shine yaya zanyi da jaririn?
Ka kirawo yan sanda wata zuciya ta shawarce ni. Acan kuma wani bangaren na zuciyata akace dani.
Kai shashashan banza idan ka sake ka kirawo yan sanda ka kashe kanka daman tsammani zasuyi sato shi kayi ka rude shine ka kirasu.
Basai kayi musu bayanin yadda budurwar ta kawo maka shi ba? Wata zuciyar ta sake kwabata in ka sake ka kira yan sanda ka karasa rusa kanka a harkar fim domin dole ne labari ya watsu abokan hamayyarka kuwa sun sami makamin da zasuyi ta yakarka har sai sun kai ka kasa.
Can kuma sai wata zuciyar tace dani
kai dan samari rufawa kanka asiri tun wuri ka dauki jaririn nan yadda ta baka shi kaima kaje ka jefar dashi ka hutawa kanka tonon silili.
Kokuwa na tashi yayana na sanar dashi? To sai dai kuma haryanzu zuciyat nan nata kururuwa cikin kwakwalwata kai fa baka rabuwa da sakarci Wallahi mutumin da tuni mutanen unguwa sun gama zuzzuge kawun naka ana cewa yan iska ne ku yan shirin fim bakajin cewa idan yaganka da jariri zai iya tunanin ko naka ne aka kawo maka shi har gida dan bariki?
Ai kawai ka dauki jaririn nan bakinka alaikum ka jefar dashi.
Abinda yakama nayi kenan nace da kaina. Nasan dai yanzu babu jami'an tsaro akan tituna ballantana kuma mutane na mike tsaye cikin sauri ina mai fargabar kada gari ya waye min akamani da jariri dumu dumu ahannu.
Wani zazzafan gumi yayi zarya tun daga kan doro wuyana har zuwa bayana. Kagafa hakane. Nace da kaina. Lallai kam mafita ta daya ce kawai na hanzarta na dauki jaririn nan na jefar dashi na huta in yaso daga baya na nemi uwarsa. Amma tabbas in har maganar ta fito fili to ko kawuna bai zargeni da komai ba sai mutanen sunyi ta yawo da zancen me yiwuwa ma wata rana yazama abin gori ga 'ya'yana.
Akaro na farko tun bayan da akayi min kyautar jaririn sai naji sanyi sanyi araina. Kwakwalwata kuma tafara tunani sosai da sosai.
Na nufi kofar dakin ahankali sannan na shiga falon. Na duba hanyar da zata kaika har bandaki saina girgiza kaina. Lallai budurwar tayi kyan dan maciji na wuce kai tsaye na nufi kofar da zata kaini har waje na budeta kadan. Sassanyar iskar dake ta faman watangarariya da kwayoyin ruwan dake zubowa adoron kasa daga sararin Subhanahu Wata'ala ta bugi fuskata yan sa'o'i kadan da suka wuce bazan iyayin maraba da iskar ba amma ayanzu saita zame min tamkar na'urar sanyaya daki alokacin zafi.
Na juyo dakin cikin sauri na sunkuya abakin gadon sannan na tura hannuna na dauko katuwar rigar leda ta ruwa wacce azamanin danake tashe aharkar fim idan zamu tafi daukar shirin fim lokacin damina da ita nake fita.
Koda na dauko rigar na karkadeta saina dorata akan rigar dake jikina sa'annan na fara balla maballin rigar bugun zuciyata yafara dawowa daidai ayanzu na sake sunkuya karkashin gadon akaro na biyu na dauko takalman ruwana nasa sannan na duba akwatin da mataccen jaririn ke ciki na tambayi kaina da cewa...
To yanzu kuma ina zaka jefar da akwatin waje na farko daya fara zuwa zuciyata shine wani katon kango dake bayan gidan wani attajiri wanda ya saye ginin kwamnatin gidaje uku ya hadesu ya kera katon gida.
Katon kango ne yadade ahaka an zagaye shi ba'a gina ko daki daya acikinsu ba. Lokacin damina kamar yanzu kangon cike yake da dogayen ciyayin tafasa da rai dore awani lokacin dan daya wuce zamanin muna yara acikin kangon muke bata lokaci muna wasan boyayyeniya idan mun taso daga makaranta. Bazan manta ba maciji ya taba cizon abokina Sani Ayuba acikin kangon. Nayi sauri na kawar da tunanin hakan daga zuciyata tabbas nan ya dace nakai akwatin.
Na sunkiya ahankali na dauki akwatin mai tsaya wacce jaririn ke ciki na nufi kofar dakin cikin sauri.
Koda na bude kofar dakin sainayi murmushin yake cikin duhun daren kamar awani fim din Daren mutuwa.
Allah sarki jiya ba yau ba nace da kaina.
Na dade akofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi. Daga karshe dai sai......
.
Na dade a kofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi daga karshe dai sai na saduda naga tsoro da fargaba basu amfana ta awannan lokacin sai kawai na jefa kafata waje na shige cikin ruwan ina mai Addu'ar Allah yasa duk wanda muka hadu dashi yayi kuskurena a matsayin jami'in tsaro.
Naci gaba da tafiya ruwan saman dake zuba kamar da bakin indararo sai dukan bayan rigata yake fas fas. Duk dayake dai nayi sa'a duk kusan bangaren gidajen an dauke wutar lantarki amma Hakan bai bani kwarin gwiwar fitowa nayi tafiya kai tsaye cikin takama ba
Ina tafiya ina bin inuwar bango kamar Kadangare wata sa'ar ko Walkiya akayi sai na rabe kadan kafin naci gaba da tafiya.
Ina nan tafe lokaci guda kuma duk Addu'ar da Tazo bakina sai in karanta... Kwatsam sai nafara hango gidan attijirin tsakanina da gidan akwai yar tazara kafin ka kai ga kangon dake jikin gidan saikayi tafiya cikin wata yar farfajiya wacce babu gine gine a cikin ta sai ciyayi haka nan kuma anan filin wasan kwallon kafa na samarin Unguwar yake.
Gabana ya fadi sa'ar dana hango fitilun lantarki naci a kofar gidan dakuma kan katangar reras dasu kamar taurari tabbas injin wutar lantarki ya kunna.
Ganin hasken ne ya sani sauya shawara na kauce nabi wata yar siririyar hanya wacce ta ratsa ta cikin filin wasan kwallon kafar takuma bi ta bayan gidan attijirin zuwa cikin kangon da nake hari.
A daidai lokacin ne to najiyo sautin abin da ya kusa sa akwatin dake hannuna ta subuce....
Ko shakka babu mutum ne abayana. Nayi mutuwar tsohuwa a tsaye tsoro da fargaba suka hanani juyawa. Wani abu ya dunguri dunduniyar takalmina na dauke numfashi cak ina kokarin zama gunki har yanzu wanda ke bayan nawa bai ce Dani uffan ba sannan ne to naji wani gurnani abayana marar dadin ji
Gashin jikina ya mimmike tsaye kamar gashin bushiya tuni wani zazzabi zazzabi yafara kokarin rufeni nayi ta yan maza na juya a hankali na dubi bayana sai mukayi ido hudu da bawan Allah mai bakaken idanu kamar ifritu yana gurnani wani dankareren kare ne mai jajayen idanu da zako zakon hakora kamar tarko babu alamar farin gashi a jikinsa.
Wani katon kare ne ya kwada min uban haushi WAW-WAN Nayi tsallen gefe guda sai yakawo min sura santsi ya kwashe ni nafada cikin cabin ruwan nagama gigicewa maimakon na Jefar da jakar saima na sake mikewa tsaye da ita kankame a kirjina kai kace wasu makudan kudade ne aciki.
Mukayi tsaye cirko cirko nida karen ya dube ni na dube shi saina juya da gudu karen kuwa yace da wa Allah ya hadashi bada ni ba.
Tun kafin tafiya tayi nisa karen ya fara kawowa dunduniyata sura. Allah ya taimake ni da takalman ruwa a kafata akaro na biyu ne ya sami Nasarar farka rabin rigar ruwan dake jikina.
.
Wayyo Allah.
Na kwalla ihu na manta da abun da ke dauke a hannuna na sake juyowa a firgice na kaiwa karen duka da jakar dake hannuna Saidai kuma dukan na matsoraci ne domin bai iya kwantar da ko da yar budurwa ba ballantana mahaukacin kare alokacin ne to
TAFARU TA KARE. Wani abu mai kamar guduma ya sulalo ta cikin duhun daren ya daki tsakiyar kaina kafin na gama warwarewa sai wani abu kuma mai kamar katakon duka ya daki bayana naji kamar an soke ni da mashi.
Wayyo Allah na kwalla ihu.
Zakayi ihu ma sai agaba shege BARAWO Meka sato acikin akwatin?
Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren...........
.
*************** ************* ***********
Zakayi ihu ma sai agaba shege barawo.
Me ka sato acikin akwatin? Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren....
.
********* *********** ********
.
Adaidai lokacin dana sulalewa zan fadi acikin cabalin ruwan ne sai wani busashshen hannu mai kamar iccen makera ya cafi kwalata ya dagoni sama da karfin tsiya ya girgizani.
Me ka sato aciki Barawo? Aka sake tambayata akaro na biyu sannan sai busashshen hannun ya damki makwogorona.
Idan baka fadi abinda ke cikin akwatin nan ba kasheka zanyi shege azzalumi kudin wa ka sato?
Wallahi ba kudi bane.. Nace dashi cikin karaji.
Uwarka ce to aciki? Shege Allah ya tona asirinka kananan barayin unguwa daman jira kakeyi afara ruwa saika biyo dare ka dauki wannan ka zari wancan kamar mayen karfe ko?
Haryanzu ba'a daina tsuga uban ruwan saman ba na hadiye yawu da kyar ba karamin riko yayiwa makoshina ba dakyar nake numfashi gashi ya daga hancina sama ruwa sai shiga yakeyi kamar bututu.
Busashshen hannun ya dada girgiza ni zuciyata sai harbawa takeyi Tam Tam kamar tamaula tsakanin hakarkarina akwatin kankame akirjina na san idan na sake ya bude akwatin kashina ya bude.
Daureka zanyi yace dani yau Allah ya toni asirinka bazan buda akwatin daka sato ba amma da zarar gari ya karasa wayewa zan mika ka ga hukuma.
Mutumin ya tura ni riki riki da akwatin ahannuna muka nufi katon gidan attajirin nan mai katanga dauke da fitilun lantarki burjuk kamar hasken rana.
Mutumin yaci gaba da jana kamar mushe rabi ina tafiya rabi kuma kafata na jan kasa kamar kafar gawa.
Wani lokacin idan aka kwantsama aradu mai karfin gaske sai mutumin ya dan dakata da jana yace.
Shege dama ta fado maka azzalumi.
Nayi mamakin ko wanene azzalumin tsakanina dashi.
Bayan wasu yan tsirarrun mintuna muka kawo ga kofar gidan attajirin nan. Na dubi dankareren gidan kana na dubi yan mitsi mitsin kwayoyin ruwan dake ta zubowa bila adadin daga sararin Subhanahu Kamar hazo lokaci guda kuma na juyo akaro na farko nayiwa mutumin kyakkyawan kallo.
Banyi kuskuren fasaltashi cikin zuciyata ba.
Domin kamar dai yadda nayi tunaninsa haka nan yake saima abinda ya dadu kato, baki, jajayen idanu, fankaceciyar kafada, kamar kofar shagon kasuwa. Abin dayafi bani mamaki ga halittarsa shine duk da girman jikin nan nasa kansa dan kankanine haka kuma fuskarsa tsukakkiya ce fatar bakin siririya kama an tsaga wanda da tsinin wuka.
Koda ya dada fizgata muka dada matsawa daf da kofar gidan sai tangamemiyar kofar ta bude wasu dogayen mutane suka fara fitowa daya bayan daya har suka zama su uku. Basu damu da ruwan da ake kwararawa ba.
Mutanen uku duk Buzaye ne sirara masu dan rakeken wuya kamar kasan almakashi ka dauke.
Kowannensu dauke da dakon katon rawani kamar mushen tunkiya rike da takobi tsirara.
Wa Allah kuma ya hada ka dashi MAMUDA?
Daya daga cikin masu gadin ya tambayi katon mutumin dake tike da wuyan rigata.
Irin yan kananan barayin unguwannin nan ne dake damun unguwa da yan sace sace yanzu ma dubunsa ce ta cika na zagaya cikin ciyayin can sainaji DUNA yana haushi nakai masa agaji nakamo wannan karamin marar kunyar.
Yana gama fadin haka saiya hankadani gaban buzayen da karfi na fadi ricaaa agabansu.
.
Wannan akwatin fa dake rungume akirjinsa?
Buzun maigadin ya tambaya
ban budata ba babu ruwana da abinda ya sato ku barshi kawai idan gari ya waye saimu mika shi ga jami'an tsaro domin irin kananan barayin nan annoba ce ga al'umma dan irin su ne idan suka rika sai su zama yan fashi da makai.
Yasa kafa ya daki Duwawuna da karfin gaske na kwalla kara.
Au dan dan wannan ma? Ai somin tabi ne kawai na baka ladan kamu ne saima gobe idan kaje hannun yan sanda kayi mai dalili Ya fashe da dariyar mugunta.
Ku jefa min shi cikin dakin injin bada wuta yace da buzayen.
To! Suka amsa baki daya sannan kowa daga cikinsu ya kama inda yafi rainawa ajikina sukayi sama dani kamar gadon kara suka nufi cikin gidan dani.
Kada ma ku damu kanku da sai kun daure shi kudai ku kulle shi kawai aciki karamin barawo ne babu abinda zai iya yi.
Suka karasa dani kofar wani dan daki dake manne ajikin bangon gabas na farfajiyar gidan dan dakin kusan duk akere yake da shuke shuken furannin alfarma haka nan duk farfajiyar gidan. Nayi bakin ciki domin duk da mummunan halin danake ciki basu barni na kashe kwarkwatan idanuna ba.
Muna isa kofar dakin sai suka ajiyeni akasa biyu daga cikinsu suka rikeni yayinda dayan ya bude dakin jannaretan nan da nan karar injin dake cikin dakin gamida hayaki suka gauraye gurin.
Anan zaka kwana in kuma kaso ma to kana iya sace injin gaba daya duk ribar kafa ce wai giwa ta taka kwado. Suka jefani cikin dakin kaina ya bugi jikin injin. Sannan na mirgina gefe guda ina murkususu.
Masu gadin suka mako kofar garam!!! Sannan naji karar kwadon sun kulle dakin.
.
Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda karajin inji sannan kuma idanuna kamar zasu fito waje saboda hayakin injin dake shigo min.
To amma fa duk wannan bai sa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba
.
Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda Karar injin sannan kuma idanuna kamar su fito waje saboda hayaƙi injin dake shigo min.
Toh amma fa duk da irin wannan wahala baisa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba na yunkura Dakyar sannan na nufi kofar kofar dan karamin dakin injin bada wutar lantarkin adaf da kofar dakin akwai wasu yan kananan tagogi ajere reras guda shida don haka ina Karasawa ga tagogin Saia tura hannuna ta cikin kofar daya daga cikin yan kananan tagogin hakan danayi shi ya bani damar shakar tsaftatacciyar iska sannan kuma sassanyar iskar ruwa ya bugi fuskata nan da nan naji na dan fara dawowa hayyacina akusa da kofar dakin daga hannun hagu akwai wai katon duro na mai.
Na matsa kusa da durom din na ajiye akwatin akai na jingina dashi sannan kuma wani lokaci guda fuskata na cikin yar Jafar tagar ina shakar iskar tsaftatacciyar iskar ruwan Saman ahaka ko barcin gajiya ya dauke ni.
Bansan iya sa'o'in dana share ina barci ba Nidai kwatsam ba zato ba tsammani sai ji na nayi nadaku da kasa. Sannan naji wani abu ya Fado min awannan sa'ar na tashi firgigit cikin tsoro sannan ne to na fuskanci ashe barci ne ya daukeni a tsaye harna ture durom jakar dana ajiye da kuma akwati.
Na tashi tsaye da kyar jikina na rawa ga mamakina sai Naji gidan yayi tsit wannan shi ya tabbatar min da cewa an Dade da dauke ruwan saman acan wani bangare kuma na Unguwar nasu wani ladan mai zakin muryar gaske yana kwada kiran sallah asuba tayi nace a zuciyata kashina kuma ya bushe kenan. Na sake cewa a zuciyata Daman nasan da gari ya waye marasa imanin masu gadin nan zasu Mika ni hannun yan sanda shin anya kuwa haka zata yiwu? Yafa kamata ka motsa ko zaka samu hanyar tsira wata zuciya tace dani.
Na nufi kofar dakin ahankali kafata kamar zata balle saboda ciwo nasa hannuna a jikin kofar na dan jijjigata sannan ne to naga kofar dakin......... Karshen abubuwan........ Ne.
.
Karfe da gilashi kuma gilashin dake daf da inda nake masakalin dan makullin yake a daya sakon. Nan da nan zuciyata tafara harbawa inama ace zan iya murde dan makullin na ce da kaina. Namika hannu naji hannun ya taba kwadon dakin kamar wasa sai kawai naji kwadon ga mamakina ya bude gumi yafara sarara agadon bayana sannan ne to wata zuciyar tace dani shashasha mai gadin bai balle kwadon ya shiga daidai ba. Nan da nan na murde kwadon na tura shi sama sai ya fadi can kasa Tim. Jikina kamar mazari na rawa na dauki akwatina sannan na tura kofar ahankali sai ta dan bude nayi shiru ina saurare ko zanji motsi shiru babu motsin komai sainaga hanya yakin bishiyoyin gidan da iska ke kadawa banyi mamakin jin shirun ba domin nasan hankalin masu gadin a kwance yake tunda dai a tunanin su ina nan a kulle abu na farko da ya fara zuwa zuciyata shine hanyar da zan bi na tsere to Saidai kuma tuni na tabbatarwa da kaina cewa bashi yiwuwa na tsere ta kofar da suka shigo dani idan nayi gangancin bi ta kofar to kamar na tura kaina ga halaka ne da gangan.
.
Tsakanina da inda dakin yake dakuma tangamemiyar kofar gidan yake akwai tazara don haka sai wata zuciya tace dani tunda dai kofar bata biyuwa me zai hana ka lallaba ta cikin duhun shuke shuken da suka kare dakin ka zagaya ta baya? Nan da nan sai na koma ina mai amincewa da shawarar zuciyata tunanin daya fara zuwa min shine na zagaya bayan gidan saina haura katangar indira cikin tsohon kangon dake makwabtaka da gidan wanda Daman tun farko anan nayi niyyar jefar da akwatin mai JARIRIN.
Na tura kofar dakin ahankali sannan na fito waje.
Sannan ahankali ina bin lungu lungu sako sako dake cikin shuke shuken har na kawo ga ginin gidan adaidai lokacin to naga yar siririyar hanyar data bi ta bayan ginin dakunan gidan har zuwa katangar arewa wacce itace ke makwabtaka da gidan.
Fasalin ginin dakunan gidan irin Fasalin nan ne da zaka iya ginin dakunan su kadai ne a tsakiyar gidan batareda an jingina koda gini daya da katanga ba wannan shi ya baiwa rufanin damar yin yado ajikin katangar hakan nan kuma yan dukur dukur fitilun alfarmar suma suka kai kusurwar katangar kudu ta gidan abin gwanin ban sha'awa me yiwuwa hakan ce tasa akayi ginin tsakiyar gidan batareda an jingina shi da koda katanga daya ba.
.
Na lallaba ahankali kirjina na Dakan shida shida na bi yar siririyar katangar ta tsakanin shuke shuken na nufi katangar.
A daidai lokacin ne to sainaga tagar daki ta bude nayi sauri na sunkuya acikin shuke shuken dake daf da tagar kadan ya rage tagar dakin ta buge min kai domin jikin ginin dakin nake bi bantaba zaton za'a bude tagar din ba haka nan shiyasa ni tunanin ko na koma da baya na sake hanya domin a baya na akwai jerin wasu tangagogin har guda biyar kafin nakai ga katangar danake hari. Bangama shawara ba sai na sake jin abin da yasa zuciyata harbawa da karfin gaske. Wata shakakkiyar muryar magidancin mutum tace.....
Ke FADILA tashi munafuka INA KIKA JE DA DADDARE naji shiru na dan lokaci sai Naji an sake cewa
Ke ba ke Nake yiwa magana ba? Shiru ba'a amsa ba can sai Naji an amsa
BABA NI WALLAHI BABU INDA NAJE........
Jin muryar shi yasani mikewa zumbur kamar wanda aka sokawa kibiya na sake saurarawa dakyau
To don iyayen ki ni zakiyiwa karya ina kallon ki fa jiya ana wannan ruwan kika fice dauke da akwati a hannun ki Ina Kika kai akwatin ina kuma kika ajiye motar da kika dauka? Wani abu mai Kamar gizo gizo ya biyo tun daga babban dan yatsana har zuwa bayana.
Bab...... Don Allah tafara kuka na Mike tsaye ahankali na leka tagar dakin sannan ne to naji numfashina ya dauke ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI NE
.
Ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI ne.
.
Tana zaune abakin gado ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta gashin kanta awarware wani katon mutum ne dattijo tsaye akanta sanye da babbar riga bana raba daya biyu mahifinta ne. Naci gaba da saurarensu jikina na rawa.
Ina kika kai jaririn munafuka? Mutumin yace sannan ya matsa kusa da ita ya gaura mata mari tas
ina kuka kai jaririn iye? Wato jefar dashi kukayi ko? To zakici gidanku.... Yau daga ke har shegiyar uwarki data bataki sai kun fice min daga gidana ke kuwa ahannun yanda zan mika ki.
Kai Allah wadaran haihuwar irinku haihuwar bakin ciki. Adaidai lokacin ne to naji budewar kofar acan cikin dakin.
Kada ka zageni. Wata sassanyar muryar mace tace duk abinda yafaru akan FADILA kai ka janyo ai sai da nace dakai kada ka riga sakarwa fadila kudi tun tana karama nayi nayi dakai ka ki
kasai mata mota har guda uku don shagwaba har kasashen turai kake tafiya da ita tokuma shin ayanzu don.....idonta ya bude da iskanci har ta sami nasarar ba wa... DAN GWARZO shine kuma zaka zargeni ? Matar tayi shiru tana maida numfashi ai saida nace dakai a zubar da cikin ka ki yo kuma yanzu don ta haifi dan ta jefar shine zaka zo kahauta da duka ka dagata don Allah Alhaji kada ka kashe min 'ya ba fa taka bace kai kadai.
Mutumin ya dubi matar a fusace yace.
Allah wadaranki Wallahi nima kaddara ce tasa na aure ki rabon dai in sami wannan tsinanniyar yarinyar da zata janyo min abin kunya agari kema kafin na aure ki ciki nawa kikayi aka zubar?
To kace ma fadilar ba 'yar ka bace mana.
Matar tace a fusace nan da nan sai maigidan ya sake shake yarinyar yahauta da duka.
Wayyo Allah baba na shiga uku fadila ta fada cikin kuka.
Baki shiga uku ba ma tukunna sai ma na dora wuka a mokogoronki don ubanki. Ina kika jefar da jaririn.
.
Batare da na sake jiran komai ba sai kawai na dauki akwatin na koma... Da gudu ban damu da ko masu gadin zasu ganni su sake kamani ba. Ina zuwa saina nemi kofar shiga babban falon na tura kofa na shiga bayan nayi yan dube dube saina jiyo hayaniya awani daki. Hakan shi ya bani damar gane cewa shine dakin da nake nema.
A ina kika jefar da jaririn? Ya sake tambayarta banyi wata-wata ba saina tura kofar na fada cikin dakin babu sallama. Gaba daya mutanen uku miji da mata dakuma 'ya suka juyo a firgice suka dubeni kamar wani Aljani.
Kayi hakuri alhaji da shigowata babu sallama.
Nace dashi. Zuwa nayi na ceci ran 'yarka domin ba sai ka dora wukar a makogoronta ba. Ga Jaririn nan bai yi nisa ba dazun nan tayi min kyauta dashi amatsayin kyakkyawan jaruminta na shekara.
Nayi musu murmushin yake su kuma suka dubeni saroro kamar wadanda suke tunanin na tabu. Na ajiye akwatin agabansu sannan nace.
Jaririnta yana cikin nan yana barci ni zan koma Alhaji saidai kuma don Allah kayiwa masu gadin nan magana domin su Barawo suka kamani jiya da daddare adakin injin dake baku wuta na kwana. Allah ne ma yasa zan raba wannan rikici shiyasa na fito.
.
Karya yake Wallahi baba shine ya sace jaririn wallahi shi ya sace min fadila tace.
Yi min shiru munafuka mutumin ya buga mata tsawa na dubeta nayi murmushi sannan na lalubi aljihuna na dauko wasikar datayi min na mikawa mutumin nace.
Duba min nan Alhaji shin wannan rubutuna ne ko nata? Ni sauri nakeyi domin muna da fim din da zamu fara idan an jima. Idan kuma kana bukatar karin bayani to saurareni da kyau.
Mutumin ya amshi wasikar daga hannuna nikuma saina dubi Fadila itama ta dubeni nayi mata murmushi nace.
Kadan ya rage ki kai labari yan mata to saidai kuma kyautar da kikayi min tayi girma dayawa. In banda abinci ina ke ina yi min kyautar Jariri? Ai tayi min yawa ina laifin ma ki bani Kyautar
KWALBAR TURARE KO FULAWA
Adaidai nan naji sautin sawun masu gadin suna ta guje guje atsakar gidan.
Lafiya meye haka? Mutumin yace yana dubana nayi masa murmushi nace dashi
kada ka damu masu gadinka ne suke nemana.
Fadila ta daga kai idanunta cike da kwalla tace.
HILAL nace Na'am FADILA
Tace don Allah ka yafe ni. Na dubeta na tsawon dakiku sainaji tausayinta ya kamani saina dubeta da tattausan murmushi nace.
Na yafe miki Fadila saiki nemi kuma gafara agurin Ubangijinki dakuma mahaifinki.
Fadila ta fashe da kuka.
Adaidai lokacin ne masu gadin suka kwankwasa kofa.
Ku shigo nace dasu.
Waya saka? Mutumin yace dani na dubeshi nayi masa murmushin ko in kula.

0 comments:
Post a Comment