HUDU 4
.
Kusan minti guda muka share tsaye muna duban kofar kodayake fadila bata kallon kowa sai ni.
Kofar dakin ta fara budewa ahankali kamar iskace ke turota sannan sai kakkausar muryar kartin nan tace.
Salamu Alaikum....Alhaji mu shigo ne?
Mahaifiyar fadila wacce ke tsaye rike da tsantsa tana huci kamar kububuwa.
Mamuda ne? Shigo kai kadai. Maigadin yace bakinsa na rawa
Garsakeken katon ya shigo dakin cikin sanda yana zuwa saiya dubeni ya rusuna agaban maigidansa yace.
Kayi hakuri don Allah Alhaji Wallahi adakin injin bada wuta muka sashi ya gudo.
Bari inyi waje dashi na hada shi da yan sanda. Yana gama fadi saiya yunkuro DAMKE NI............
.
17
Yana Tafe Anjima Insha Allahu Zan Biya Bashin jiya I banyi ba saboda balaguron da mukayi
[13:00, 1/24/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-17
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Yana gama fada ya yunkro zai Damkeni...
.
Uhm Uhm mamuda kada ka taba shi.
Maigidan yace cikin karaji. Mamuda yayi cak kamar ruwa ya cinye shi.
Alhaji barawo ne...
Kada ka damu mamuda jeka waje kaci gaba da aikinka kawai.
Toh yallabai katon yace cikin girmamawa lokaci guda kuma ya nufi kofa.
Af mamuda... Maigidan ya kira sunansa katon ya juyo cikin sauri na lura duk a rude yake me yiwuwa tunda yake gadi agidan bai taba shiga wannan dakin ba.
Wannan maganar daga kai sai mu ka.
Kafadawa abokan aikina ma bana so ta wuce tsakaninku. Kakuma kawo min akwatin daya bari adakin injin wutar. Katon ya gyada kai cikin fahimta sannan saiya dubeni. Kallon dayayi min na iya nufin komai.
Nayi masa murmushi cikin sanda ya juya kamar yadda ya shigo ya sulale daga dakin.
.
Muka sake yin shiru na tsahon mintuna akaro na biyu mahaifin fadila na kallon tattausan kilishin dake dakin yayinda fadila ke kallon. Nikuwa idanuna na kallon mahaifiyar fadila wacce ta kurawa fadila idanu bata ko kiftawa. Azuciya na yarda da maganar mahaifin fadila dayace da mahaifiyarta tun farko itace ta bata fadila domin na lura da alamun damuwa karara a fuskarta dakuma kauna ga fadila yarta.
Ku shiga daga ciki RASHIDA. Maigidan ya kira sunan matarsa akaro na farko. Nayi zaton zata hau masifa amma maimakon hakan saita dubi Fadila tace. Taho mu tafi. Fadila tayi min kallon gefe idanu tabi mahaifiyarta suka bi ta wata yar tsukakkiyar kofa suka shige ciki. Maigidan ya dubeni gamida sassauta yanayin dake fuskarsa yace.
Zauna bawan Allah ya nuna min kujera araina sainaji na kaunace. Hakan shi yasa nayi biyayya na zauna batareda nayi jayayya ba. Ya danyi shiru gamida sakin wani tattausan tari kana sai ya dago kansa..
.
Tun tana karama muke fama da ita kadarar yarinya ce ka ganta nan gashi da babu abinda ta rasa agidan nan na daga kayan alatu amma bata iya zama sai shegen yawo. Mahaifiyarta ce ta bata tun tana karama.... Yayi shiru akwai alamar takaici karara a fuskarsa. Na tausaya masa.
Babu daman nayiwa yar cikina fada sai mahaifiyarta ta hauni da masifa. Haka kullum nake fama kwatsam ran nan sai muka fahimci yar banzar yarinyar tayi ciki mahaifiyarta tayita uzura min sai a zubar da cikin. Nikuma ina tuna mata yin hakan barna ce domin kisan kaine saimu bata goma biyar bata gyaru ba. Haka mukayi ta fama har zuwa ranar data haifu shine yanzu don tsabar rashin imani suka hada baki ita da mahaifiyarta suka kashe dan jaririn wata daya kawai da haihuwa....hawaye ya fara kwarara akan fuskarsa.
Na yunkura akan kujerar cikin damuwa ni duk maganganun sun fara gundurata duk da dai basu shafeni ba ni abinda kawai nake so shine yabar ni na tafi dan na lura tuni har gari yafara haske. Duk da yake banga agogo ba ina kyautata tsammanin biyar na safe ta wuce. Fita fim dinsu Alhajiji ne araina.
Alhaji.... Allah ya sawwake.. Nace dashi ina ganin in babu wani sauran abu to ni zan tafi alhaji domin kaga duk wannan abubuwan da kake fada bai kamata na sani ba domin sirrinku ne ku kadai bai shafe ni ba. Mutumin ya dago kai yana girgiza shi.
Ya shafe ka bawan Allah. Awannan karon ni na dube shi cikin mamaki.
Tayaya ya shafeni? Mutumin ya sunkuyar da kai na tsawon lokaci yana girgiza kai. Can saiya dago alamar damuwa a fuskarsa a fili. Ga mamakina sainaga ya mike tsaye ya nufo inda nake ya sunkuya akaina ya dafa kafadata yace.
Bantaba neman alfarma agurin kowa ba tun da nake.... Amma yau zan fara. Abinda yace sai ya daga rudani.
Ban fahimce ka ba. Ya daga girarsa sama kamar biri na lura karfin ikonsa da kwarjininsa na attajiri sun fara dawowa gare shi.
Abinda nake nufi shine ina neman kayi min alfarma guda biyu bawan Allah.
Ni kuwa zan saka ma da abinda baka taba zato ba. Numfashina ya dauke abinda ban taba zato ba? Indai ba kuskuren fahimtarsa nayi ba nasan abinda kalmar ke nufi muddin ta fito daga bakin ATTAJIRI.
Wa.... Wacce alfarma kake so? Ya dubeni na tsawon lokaci kana yace.
So nake ka rufa min asiri maganar jaririn nan ta zama daga kai samu don Allah na rokeka ka rufa min asiri domin idan ta fito fili nagama yawo... Kaga shekara mai zuwa nake son tsayawa takarar GWAMNA zuciyata ta harba tsakanin hakarkarina. Bakina na rawa nace dashi.
Indai don wannan ne Alhaji kada ka damu in Allah yaso babu wanda zai kara jin ta abakina. Nayi tsammanin zai saki fuska cikin jin dadi amma sainaga haryanzu dai tana nan yadda take babu yabo babu fallasa.
Sai kuma alfarma ta biyu bawan Allah yace. Lokaci guda kuma naga akwai alamar razana a fuskarsa.
Fadi muji ranka ya dade. Nace dashi ina dada kwantar da murya domin kalaman dayayi ne zaiyi min abinda ban taba tsammani ba yasa zuciyata lissafe-lissafe,,,, na tuna da dimbin bashin da ake bina.
.
Bawan Allaj me ye sunan?
Sunana Hilal.
Yawwa hilal.
Alfarmar danake nema tanada nauyi amma kamar yanda nace dakai abaya zan saka ma. Ya danyi shiru sannan saiyace,
Zaka iya hilal? Na dubeshi cikin mamaki nace to ai bansan me zanyi ba Alhaji.
Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya daga kansa ya dubeni ido da ido yace.
SO NAKE KA AURI 'YA TA FADILA.
.
************ ************** ************* *********
.
KU HUTA TUKUNNA SAI MUCI GABA
.
NA SADAUKAR DA WANNAN KASHI NA 17 GA DUK WAYANDA SUKA JE KADUNA TA'AZIYAR ABOKIN HULDA AWANNAN DANDALIN IBRAHIM TAREDA DUK WAYANDA SUKAYI TA BUGO WAYA SUNA MIKA TA'AZIYAR SU TA HANNUN MU DAKUMA MASU COMMENT A CIKIN POSTING DINA NA RASUWAR DA TAFIYA TA'AZIYAR ALLAH YAYI MANA RAHAMA DA RAHAMARSA BADON AIKIN MU BA
[13:22, 1/27/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-18
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya.
.
Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya dago kansa ya dubeni ido da ido yace.
SO NAKE KA AURI 'YA TA FADILA.
.
********* ******** ***********
.
Ba karamar girgiza nayi da kalamansa ba. Kaduwar danayi ita ta sani zaune nayi mutuwar tsohuwa na kasa cewa dashi komai domin bansan me zance dashi ba. Na auri fadila? Chab babbar magana.
Yaya kayi shiru Hilal ko baka sonta ne? Na girgiza kaina cikin kaduwa.
Bahaka bane Alhaji... Kaga dai yan sa'o'in da suka wuce na santa kuma.... Ya daga min hannu.
Hilal basai ka fada ba nasan abinda kake tunani. Auren yarinyar banza kamar fadila ko?
Yarinyar data yi cikin shege ko? Ya danyi shiru sannan yaci gaba.
Abinda yasa na baka duk tarihinta abaya shine so nake ka aure ta da halinta. Kuma ko da yake baka dade da saninta ba kai kasan fadila kyakkyawa ce bata da wani aibu in ya wuce na dabi'unta na banza.
Hilal inason ka sani cewa in dai kana sonta zaka aureta da halinta to zan saka maka da babban alheri domin tuntuni na gaji da zamanta agidan nan. Ganin sharrin dataso ta dora ma shi yasani tunanin babu wanda yadace ya aureta sai Kai.
Na gama rudewa zuciyata sai dum dum dum takeyi duk abubuwan dake faruwa ji nake kamar amafarki.
Mecece sana'ar ka hilal? Mutumin ya tambayeni hakan dayace shi ya sani dada gyara zama.
Harkar shirin fim nakeyi... Nace dashi cikin gaggawa mutumin ya shafi kansa da tafin hannunsa na dama yace.
Saurareni da kyau hilal zan baka lokaci kayi shawara zan kuma sami Fadila nayi mata maganar.
Ya danyi shiru sannan yaci gaba. In dai zaka yarda zaka aureta da halinta nayi maka alkawarin zan sayo maka duk abubuwan da kake bukata na harkar shirin fim idan nafita kasashen ketare. Ko gobe ka amince kazo ka sameni ka fada min zan aika cikin sati guda a sayo maka duk abinda kake bukata inason kuma ka nemi gida mai girman gaske a ko ina ne zansa arugujeshi agina maka kamfanin fina finanka zan kuma zuba maka jarin naira Milliyan biyar kyauta. Na shiga uku nace cikin zuciyata. Milliyan biyar?
.
Alhaji zanyi shawara.... Abubuwan sunyi yawa akaro na farko sai ya saki wata tattausar dariya yace.
Ai kadan ma ka gani ya mike tsaye sosai zo muje in rakaka. Jikina na rawa na bishi abaya.
Ruwan saman ya tsaya cak. Tuni gari har yafara haske naji sa'ar da agogo ya buga karfe shida na safe. Muka bi ta wata yar kofar sai na ga mun bulla a filin ajiye motoci.
Motovi bakwai ne ejere kusan duk sababbi ne akwai jeep guda biyu Lexux daya marsandi biyu da honda shudiya da ja. Ga mamakina sai naga ya tsaya ajikin motocin.
Alokacin ne fa nayi masa kyakkyawan kallo dogo ne siriri fari mai gashi irin na buzaye yalo yako me yiwuwa bafilatani ne kokuma mutumin Mali. Allah masani. Sa'ar daya dubeni yayi dariya sainaga hakorinsa na sama guda daya a bantare.
.
Zan baka sati guda kayi shawara hilal abinda ka yanke saika zo ka fada min ni da kaina zan sami iyayenka.
A ina kake ne? Ya tambayeni hannunsa na dama akan rufin motar lexux.
Anan unguwar nake can ciki nake (No 106)
Af ashe ma makwabvina ne. Ya fadada murmushinsa ya laluba aljihun doguwar jallabiyar shudiya dake jikinsa ya dauko dan makullin mota sannan ya nufi shudiyar motar honda.
Alha..... Alhaji bama sai.... Ka bari kawai saina karasa ma akasa. Murmushinsa ya fadada.
Uhm hilal kenan kaifa nace dakai yanzu ka dan ma ka gani. Ungo rike wannan. Ya miko min dan makullin mota ya nuna shudiyar motar da baki yace.
Gata nan nabaka kyauta. Wannan kyautar bata cikin wancan yarjejeniyar tamu koda baka amince ba wannan motar dai taka ce... Na bude baki cikin kaduwa da mamaki chab. Dan saurayi hilal anya kuwa ba mafarki kake ba?
Bansan irin godiyar da zanyi maka ba alhaji na gode Allah... Ya katse ni ta hanyar daga min hannunsa a fuska..
Kada ka gode min Domin asirin dakayi alkawarin zaka rufa min yafi dahaka. Da'ace ciniki zamuyi.
Ya dan saurara yana dan dukan saman motar da yan yatsunsa.
Shikenan hilal sainaji daga gareka kana iya shiga motarka Allah yabamu alheri nakuma gode domin nine da godiya. Yana gama fadi saiya juya yayi ciki da sauri. Yakoma cikin gidan ta inda muka fito.
.
Na dade anan saroro a rude domin abin kamar a mafarki awani bangare kuma na zuciyata sai cewa akayi dani wannan yaudarar ce irin na aljanu.
Amma sa'ar dana bude hondar na lume acikin kujerar direba sai na gaskata faruwar dukkan al'amarin.
Ada na dauka dana shiga motar zan ga ta bace saina tsinci kaina kwance akan tsohon gadona. Amma tabbas ko shakka babu duk abinda nagani tun daga dare har zuwa wayewar gari gaskiyane babu zancen aikin aljanu KAMAR A FIM.
.
Nayiwa motar key na tashi sannan na fara tukata ahankali na nufi kofar gidan azuciyata nace Allah mai yadda yaso yan sa'o'i kadan nine ke yawo da mataccen jariri ina neman inda zan jefar dashi sannan lokaci guda kuma na tsinci kaina amatsayin barawo sai gashi akarshe cikin ikon Rabbana motovina da bashi ya cinye daya ta dawo daga cikinsu.
Koda na fara tuka motar sai na juyo da nufin na yiwa ginin gidan kallon karshe gabana yayi RAS. Sa'ar dana hangi.....
.
AKWAI CIGABAN ANJIMA IDAN KUNA SO
.
Gabana ya fadi ras sa'ar dana hangi FADILA tsaye agindin taga tana daga min hannu ba ganin nata ne yasa zuciyata ninkaya ba sai tunanin cewa ayanzu abinda ke tsakanina da zama miloniya shine kawai na yarda zan aureta. LAURIYYA ta fado min arai.
Ga koshi ga kwanan yunwa nace araina.
Koda masu gadin suka hangoni tafe sai sukayi sauri suka bude min kofa atunaninsu ubangidansu ne koda suka fahimci nine sai suka bi ni da kallo bakunansu a bude cikin kaduwa. Dankareren katon daya kamoni amatsayin barawo idanunsa suka firfito cikin kaduwa kamar idanun kwado. Na daga masa hannu harda murmushi na take sabuwar motata abina na nufi gida.
.
********** ********* *********
.
Tun daga nesa na hangesu tsaye akofar gidana motoci biyu da mutane biyar kowannensu nata waige waige suna ta duban hanya akwai alamar damuwa a fuskokinsu.
Nayi fakin da dalleliyar hondar adaf dasu ina ganin alhajiji ta cikin gilashin motar yana duban agogo baiko damu daya kalli motar data tsaya afad dasu ba domin nasan babu wanda acikinsu yake tsammanin nine na bude kofar motar ahankali.
Sannunku da zuwa furodusa. Nace dasu da faffadan murmushi. Duk su biyar din suka juyo acikin mamaki ganin nine sai fuskokinsu suka washe.
Dan Banza daga ina a ina ka kwana? Tun dazu karfe biyar da rabi muke nan muna jiranka duk sauran yan wasan sunyi gaba kai kawai ake jira na dubeshi bayana jingine da motar ina karkada dan makulli.
Kun aika gidan kawuna ne nemana? Na tambayesu gabana na faduwa.
A'a bamu aika ba daman USMAN ne ma yace mu aika nikuwa nasan da wahala in kana ciki. Nayi ajiyar zuciya da sun aika gidan kawuna nemana da sun janyo min jaf'i.
Bari in shiga gida in dan wasa ruwa sai mu tafi ko? Usman dake ta kallona tun zuwana yasaka magana saboda kullewa sai kawai safa da marwa yake.
Kaga malam tun dazu da muke jiranka fa anan sai zamuyi ta jira har rana tayi mana dubi fa karfe shida da rabi. Na fashe da dariya.
Dubi rigata fa usman ka gani gaba dayansu suka zubo min idanu sabodar tsabar kaguwa da sukayi basu ko kula da yanayin da rigar ruwan dake jikina take ba.
Me ya sami rigarka haka naga duk a yayyage... A'a kaima ai duk a jike kake da chabi. Duk jikinka tun kafin suyi tambayar nagama tsara amsar da zan basu cikin zuciyata.
Ai jiya muna rabuwa dakai lokacin daka bar mu da Lauriyya sai wasu suka daukeni muka tafi daukar wani fim. Da Allah da Annabi suka janyeni domin wai jarumin da sukayi niyyar fim din dashi baya gari kuma daukar da zasuyi suna bukatar ruwan sama. Shiyasa suka takura sai mun tafi acan na kwana. Kai jiya munyi fim da wuya. Don nasha dukan ruwa....
To indararo.... Don Allah alhajiji barshi yaje ya shirya yafito mu tafi inka biye tashi sai yayita zuba kenan daga nan har azahar. Kasan ba gajiya yake da magana ba.... Usman yace cikin fada. Na dube shi nayi masa gwalo... Sannan da gudu gudu na shige cikin gidan.
.
Bayan mintuna ashirin nafito nayi wanka na sanya kayana tsaf dani inka dauke zunzurutun tunanin dake raina. In banda na amsa musu tun jiya da ba zanje fim din ba milliyan biyar.
.
Mu tafi nace dashi cikin sauri na nufi sabuwar motata.
Hilal mota ka sake ne? Alhajiji ya tambaya na san gatse yake son yi min ya dauka arota nayi domin duk fadin duniyar fim babu inda labari bai watsu ba cewa taurarona ya daina haske.
Daman ai chanji zanyi shine yasa na saida wadancan nan da sati guda ma za'a kawo min marsandi daga kwatona.
Alhajiji ya dubeni cikin kaduwa akwai alamun hassada karara a fuskarsa. Hakanan kuma na lura da cewa kamar dai na barshi cikin wasi wasin gaskiyar abinda nafada. Ganin ya kasa magana saina ce dash.
Ina lauriyya? Fuskarsa ta washe nan da nan. Ai ka fini kusa da ita.
.
BIYAR 5
.
Ina ganinta tsaye sa'ar dana nufo ofishin ta raba hannuwanta ajikin kofar tana ta hange hange ko shakka banayi ni lauriyya take hange taga ta inda zan bullo to amma har sa'ar danayi fakin da sabuwar honda akofar foshin Allah bai nuna mata ni ba domin atsammaninta akasa zata ganni na bullo.
Nayiwa kaina murmushi sa'ar dana fara rufe gilashin tagogin motar duk yadda akayi masu karbar bashine cike suke jirana. Don na lura da yanayin fuskar lauriyya hankalinta atashe yake. Babu mamaki ma duk hange hange da take kokari take taga ta inda zan bullo tayi min inkiya na gudu batareda masu karbat bashin dake ciki sun sani ba.
Na dubi bakar jakar dake ajiye akan kujerar motar. Kudin da kamfanin Sinad produtions ne suka biyani na fim din danayi musu aranar. Naira dubu talatin da biye ne cif cif.
Fim din da muka dauka aranar ya burge duk ma'aikatan amfanin musamman ma alhajiji. Domin ya yaba da kwazona. Da wannan ne ma tasa sa'ar da aka kammala saiya kirani yace.
Hilal akwai sauran kusan gurare hudu da zakayi mana sati mai zuwa amma zan biyaka kudinka yanzun nan baki daya.
Godiya nake furodusa. Nace dashi.
A'a ai ni nake da godiya domin Wallahi Hilal na dauka ka gama mutuwa domin tuni ake yawo da labarin wai tauraronka ya daina haske sai yanzu ne na lura da cewa ashe duk hassada ce.
Ya danyi shiru...
.
TAKUN FARKO NA RIKICIN KENAN
Tuni ake yawo da labarin wai tauraron ka ya daina haske sai yanzu ne na lura cewa ashe duk hassada ce.
Ya danyi shiru na yan dakiku sannan ya ci gaba.
Dubu ashirin da takwas mukayi da kai ko?
Na gyara kai sai yace
Toh ga dubu talatin da biyar nan saura kyauta ce ta musamman daga kamfanin sinad production domin baka taba yi mana fim ba sai yau ina kuma dada tabbatar maka in Allah ya yarda wannan fim din sai ya dada haskaka ka domin mu muna da labarai masu kyau sauran kuwa duk shirme ne dahaka ai suke so su kashe ka.
Har na baro gurin alhajiji bai daina Yabona ba da zan baro gurin ma har kyautar shadda mai tsada yadi goma yayi min Don haka sa'ar dana gama rufe gilasan motar sai na dauki kudin da jakar yadin shaddar na nufi kofar ofishina.
Lauriyya bata tashi ganina ba sai dana zo daf da ita sai tace cikin rada.
Lahh ta Ina ka biyo? Na kalli motar ina murmushi acikin wannan motar nazo lauriyya ta waiga bayanta a tsorace bayan ta tabbata babu mai ganina daga cikin ofishin saita kifta min idanu akan na gudu
Wanene aciki? Na tambaye ta a tausashe.
Emeka ne tun safe yake nan har yafara fada yana cewa yau ko zai kwana nan sai ya same ka in kuwa bai ganka ba toh gobe da yan sanda zai zo lauriyya ta dada waigawa tana dubana.
Mu shiga daga ciki kada ki damu ai yau a shirye nake da zuwansa hakan dana ce shiyasa lauriyya ta kalli jakar ledar dake hannuna nan da nan sainaga fuskarta ta washe cikin mutanen murmushi ta matso inda jakar take ta karbi jakankunan guda biyu daya ta kudi daya kuma ta shadda.
Har naji dan dadi Wallahi Hilal.
Tun dazu gabana ke ta faduwa Wallahi bana son naga kana ta guje guje akan bashi. Allah sarki lauriyya nace cikin zuciyata irin wannan kulawa tata ita take dada rura wutar begen ta cikin zuciyata. A da can ban dauketa a komai ba amma a Yan kwanakin nan dana shiga masifa lauriyya ba karamin tallafi bace agare ni.
Tana gaba ina binta Abaya har muka shiga cikin ofishin.
Hello Emeka barka da zuwa ya juyo firgigit kamar an tsikare shi da kibiya.
Kada ka karya min kujera a banza da wacce kazo naji ance kusan kullum sai kazo nemana ko? Emeka ya Harareni.
Ai kafi kowa sanin abunda yakawo ni tun yaushe ne alkawarin cikon kudin kaset din mu ya cika? Kasa sai kashe kudin mota Nakeyi a banza duk ribar ta tafi ga masu mashin da mota.
Huta da nunfashin ka kada hauhawar jini ta hau ka a banza. Nace dashi ina murmushi Lauriyya ta ajiye kullin jakankunan daga can bayan teburina sannan ta fice cikin sauri ta koma can dakin karbar baki.
Nawa ne cikon kudin naka? Emeka yabata rai dubu ashirin da biyar.
Na bude baki cikin mamaki kai kace da man can bansan yawan kudin ba.
Dubu ashirin da biyar? Ashe dai kudin naka Emeka da yawa. Ya Harare ni.
Kaga Hilal ni kada ka bata min lokaci in banda lalacewar ka nawa ne dubu ashirin da biyar agurin ka. Na dube shi gamida girgiza kai.
Sanin da kayi min yanzu abubuwa ne sai a hankali. Ina gama fadin haka saina sunkuya kasan teburina na zaro naira dubu goma sha biyar na Riga nasan teburin yakare Emeka bazai ga daga inda nake zaro kudin ba
Nawa ne nan? Emeka ya Kalleni fuska a yatsine sa'ar daya ga kudin basu cika ba.
Nawa ka gani?
Dubu goma sha biyar.
To ka godewa Allah daka sami wannan kayi min hakurin dubu goma sai bayan sati guda.
Tsawon lokaci Emeka na nan zaune yayi jim kamar ruwa ya cinye shi can saiya nisa yace ba jiran sati guda ne aiki ba cika alkawarin ka
Kada ka damu zama sami cikon kudin ka.
A haka na lallaba shi muka rabu a zuciyata nace shashasha baisan ba a yanzu tsakanina da miloniya kalma daya ce tak kawai.
.
Bayan na raka Emeka saina dawo kan kujerata na zauna sannan sannu ahankali kamar a hoton majigi sai abubuwan da suka faru adaren jiya har zuwa asuba suka fara dawowa garai garai a faifan zuciyata.
Fadila ta zame min ALAKAKAI.
hakika ga dama ta sameni nace cikin zuciyata na farko dai idan na amince zan auri Fadila saina rabu da duk bashi da ake Bina saina zama gagara gasa acikin duk kamfanonin shirya Fina finan hausa. Na dubi hannun rigata sainaga har yafara kodewa sainayi tsaki fitaccen jarumi kamata yana bukatar kayan sawa akalla kala dari biyu a talauce.
.
Zan saya maka duk abin da kake bukata na harkar fim. Kalamansa suka Fado min a zuciya.
To amma duk wannan da zarar na tuna da halayarta sai inji duk al'amarin Yafita daga raina hakika ina matukar son kudi a halin danake ciki a yanzu domin basussukan da ake Bina sun kusan miliyan guda to amma acan cikin zuciyata ni nasan auren fadila ba daidai bane na farko dai ba dole bane tace tana sona in kuma ma ta amince Dani ba itace irin uwar daya kyautatu na samarwa 'ya' yana ba domin ayanda ubanta ya bani labarin halin ta ko na aure ta zaiyi wuya in zata daina bin maza.
A dacan kuma wani bangare na zuciyata nasan duk kwane kwanen da nake na abu daya ne hakika na kamu da son lauriyya tabbas in har zan auri wata mace a duniya toh lauriyya ya kamata na aura nace da kaina.......
.
NIMA YARIMA NACE KA HAKURA DA FADILA KA AURO LAURIYYA TALAUCI YACI GABA DA SUBURBUDAR KA.
.
NI KAM INA JAM'IYYAR FADILA DA BABANTA
.
Idan har zan auri mace a duniyar nan toh lauriyya ce nace da kaina.
.
To sai dai fa ga fadila ga miliyan biyar. Wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina acan wani bangare na ofishin agogon bango ya fara buga kararrawa karfe biyar da rabi na yamma.
Zuciyata tagama shiga rudani abubuwa uku agabana.
Lauriyya
Miliyan biyar da fadila
Biyu nafi son na mallaka daga ciki to Saidai kuma daya daga cikinsu yashiga tsakanina da guda daya tabbas in har Inason lauriyya to sai dai in hakura da miliyan biyar.
In kuwa kudin nake so dole ne saina hada da Fadila. Allah kiyaye nace cikin zuciyata. A can wani bangare kuma wata zuciya sai cewa takeyi dani kai shashashan banza saikace ba wayayye ba ka manta kawai da lauriyya ka auri fadila ko ka rabu da talauci da wulakancin Abokan harkar ka na shirin fim yanzu in banda shirmen ka har akwai wani abun kunya da aibu da miliyan biyar bazata iya lullubewa ba?
Hilal..... Naji muryar lauriyya ta daki dodon kunnena na dago kaina firgigit ina shafar fuskata da hannu.
Tunanin me kake yi? Ta tambaya lokaci guda kuma ta matsa kusa dani ta zauna akan teburin dake gaban kujerar danake zaune kadan ya rage gwiwarta ta gogi tawa.
Akwai alamun damuwa karara a fuskar ta.
Uhm.. Bawani tunani nake ba gajiya kawai nayi lauriyya ta zuba min idanu na tsawon lokaci na lura karyar dana shirya bata samu matsugunni ba.
Mintunan ka ashirin fa kenan kana zaune cikin ofishin nan kai kadai kuma kace ba tunani kake ba? Sai fa dana kira sunan ka har sau hudu kafin kaji ni... Ban amsa mata ba dan banida abin cewa Gaskiyar ta tabbas tunani nake.
Lauriyya ta ci gaba da wasa da Biron dake hannun ta tana kida dashi a tausashe akan teburin.
Da wata shawara nazo da ita Hilal... Kokuma ince neman alfarma. Nan da nan na juya na kalle ta cikin mamaki sai a lokacin ne na lura ashe akwai jaka rataye a kafadarta.
Ina zaki tafi ne naga kin dauko jaka? Lauriyya ta girgiza kai.
Babu inda zani muka sake yin shiru.
Ni Nafara magana. Wacce shawara ce.... Kokuma ince wacce alfarma kike nema? Na tambaye ta zuciyata na harbawa abin na da rudarwa. Yan sa'o'i kadan fa kenan da attajirin ya nemi alfarmar na Auri 'yarsa to ko itama alfarmar na aure ta zata nema?
.
Hilal nasan ana binka basusuka dayawa wadanda na tabbata bazaka iya biya ba a kwana kusa.
Lauriyya ta dago kanta ta dube ni sainaga kwalla ta taru cikin idanun ta.
SHI Yasa nazo neman alfarma. Alfarmar itace zanyi Maka kyauta ta musamman da wani abu wanda zai taimaka maka ka rage mafi yawan bashi da ake binka.
Idan na baka so nake ka karɓa kada ka juya hannun kyauta baya shine kawai alfarmar..... Wani abu mai kamar gare gare yafara zaryar cikin kwakwalwata.
Me kike son ki bani? Na tambaye ta a iya tunanina lauriyya bata da wani abu da zai iya biyan koda rabin bashin da ake Bina.
Jikinta na rawa ta sauke yar madaidaiciyar jakar dake makale a kafadarta ta dorata akan bencin dake gabana sannan saita daga jakar sama ta zazzage abubuwan dake ciki akan teburin. Alokacin sa al'amarin ke faruwa duhu ya gauraye dakin domin tuni har an fara kiran Sallar magariba kuma bamu kunna kwan lantarkin dake cikin ofishin ba. Amma duk da hakanan sai kyalkyalin abubuwan ya haskake dakin sarkokine yan kunnaye da sauran tarkacen kayan karau na kwalliyar mata duk dayake bansan darajar su ba amma nasan sunada tsadar gaske bakina na rawa na girgiza kai.
Lauriyya.... Baza ta yiwu ba bazan iya raba ki da kayanki ba... Kuma ina kika same su ban taba ganinsu ajikin ki ba dan abin da kike samu kuwa a kamfanin nan bai isa ko iya tarawa kike balle har ya sayi wannan ba. Lauriyya ta matso gareni ta dafa kafadata tace.
Kayiwa Allah Hilal kayiwa Annabi ka karɓa tunda nake ban taba neman alfarma agurinka ba sai wannan idan kaki karɓa ka gama bata min rai ka konan zuciya.
Toh amma dai lauriyya bai kyautu ba ace in har ni ban yi miki ba ke ki..... Ta katse ni ta hanyar daga hannayen ta.
Kada ma kafara wannan zancen Hilal tunda nazo garin nan wake wahala dani in ba kai ba Kaine uwata Kaine ubana Kaine abin kaunata ka kadai ne ka iya sani dariya har cikin zuciyata. Ta danyi shiru tana kokarin share hawaye.
Farin cikin ka shine farin ciki na tunda nazo garin nan baka taba sanin tarihina ba baka kuma takura min saina fada maka sirrina ba amma kake taimaka min iya karfin ka yau juyi nane na taimake ka don Allah kwashe su Hilal ko a kasuwar barayi ka sayar dasu akalla zasu kai dubu dari shida. Ta dafa hannuna ta kankame.
Kaji Hilal don Allah kwashe su Narasa abin da zance da ita. Wata zuciyar nacewa dani kada ka yarda ta rudeka dubu dari shida basu kai miliyan biyar ba.
Karkari dai su biya ma bashin amma zata kare babu komai a hannun ka
Nayi fatali da kururuwar zuciyar. Hakika abunda lauriyya tayi min bazan taba mantawa da ita ba har iya rayuwata nasan cewa a yadda take da Matsalar ta sa komai tabani kadarar ta cancak ta makudan kudi zata iya bani naira miliyan dari inda ita tana da shi.
Hilal... Hilal kayi magana mana ka zura min idanu in kuma banida matsayin da zan nemi alfarma kayi min saika fada na kwashe kayana na tafi.
Kada kice haka lauriyya ki kuma daina cewa alfarma kike nema ai nine kika yiwa alfarmar bakisan wani abu ba lauriyya nace da ita ina duban ta ido da ido.
DUK duniya a yanzu banida wadda tafiki in babu ke lauriyya bansan inda zan sa kaina ba kece garkuwa ta mai tallafa min na yarda zan karɓa amma ki ajiye min su agurin ki daga nan zuwa sati guda kawai.
Lauriyya ta dada kankame hannuna saita fashe da wani tattausan KUKA.
Ban taba farin ciki irin na yau ba Hilal kuma.....
Kwankwasa kofar da aka yi shine ya katseta nan da nan ta Mike tsaye cikin sauri ta share hawayen dake idanun ta muka dubi kofar lokaci guda aka dada Kwankwasawa.
Bari in je in gano tace dani a tausashe. Na gyada mata kai sannan nayi sauri na boye sauran kudin dubu ashirin da suka rage me yiwuwa wani mai karbar bashin ne nace cikin Raina.
Bata dade da fita ba sai ga lauriyya ta dawo ta tsaya gabana ta rike tsantsa akwai alamun damuwa a fuskarta.
Wata ce wai take son ganin Ka nayi ajiyar zuciya nasan aduk masu Bina bashi babu mace ko daya.
Kice da ita ta shigo nace da ita... Ina Nan zaune sai Naji motsi ina daga kaina sainagan ta tsaye agabana. Nan da nan dakin ya hade da kamshi doguwa ce sanye da doguwar riga ruwan Hoda kanta lullube dan kyalle irin launin rigar. Baba iya ganin fuskar ta Sosai domin haryanzu ban kunna kwan lantarkin dad ofishin ba.
Sannun ki da zuwa malama ga mamakina sainaga ta matso ta zauna a bakin teburina daidai da inda Lauriyya ta zauna.
A'a MALAMA ga kujera nan koma can ki zauna mana ta fashe da dariya cikin wata zazzakar murya.
Hilal Wallahi kabani mamaki daka kasa gane ni.
Ko na kara kyau ne? Naji gabana ya fadi rasss nan da nan sai ta girgiza kanta lullubin dake kanta yafado kan kafadarta siraran gashin ta suka bayyana suna sheki.
Me yiwuwa kafi gane ni ahaka ko haryanzu baka Gane ni ba JARUMIN JARUMAI.
Ta sake fashewa da dariya.
NICE FA FADILA......
.
SHIDA 6 Loading.........
.
ALAKAKAI-22 Loading.......
.
KAI ANYA KUWA NIMA BA JAM'IYAR LAURIYYA ZAN KOMA BA

Me yiwuwa kafi ganeni ahaka ko haryanzu baka ganeni ba JARUNIN JARUMAI.
Ta sake fashewa da dariya.
NICE FA FADILA....
.
SHIDA 6
.
Fadila nakira sunan ta a sanyaye ko shakka babu ta sani bala'in kaduwa domin ban taba tsammanin zan sake ganin ta kwana kusa ba Hilal kenan manyan gari ta tashi daga kan teburin ta nufi kujerar dake fuskantar teburina ta zauna.
Babu wuta a ofishin ne ko kafi son zama acikin duhu ne? Na muskuta akan kujerar na fara farfadowa daga cikin kaduwar danayi.
Akwai..... Wuta ban kunna bane ga makunnar nan a bayan ki Fadila ta Mike tsaye ta lalubi makunnar lantarkin ta kunna dakin ya gauraye da haske numfashina ya dauke yawun bakina ya kafe. Nashiga uku nace cikin Zuciyata ashe kyakkyawace ta gaske kamar ta karanta abin da ke zuciyata saita kashe min idanu tace.
BAKA dauka na kai haka ba ko? Kallon tsoro kayi min jiya ta matso kusa da bakin teburin tana tafiya tana girgiza jikinta da gangan kusan ko ina a jikinta rawa yake ta dafa kan teburin da hamnayen ta na dubi yan yatsunta sirara ne farare sol babu wani alamar tabo ko kwarzane atare dasu kamar jikin maciji.
Tsawon lokaci tana tsaye akaina ta lullube ni da kamshin turare da man dake jikinta bansan sa'ar data dauke hannaye ta daga kan teburin ta Mike tsaye ba.
Hilal yaya naga kayi shiru ko bakaji dadin zuwana bane? Nayi kokarin na tattare hankalina guri guda nace.
Da wacce yau kika zo kuma? Wata sabuwar kyautar kika kawo Min?
Fadila ta bata rai
KA cika rikon magana wannan zancen ya fita daga bakin ka Hilal.
Abinda ya wuce ya riga ya wuce jariri dai tuni an gama binne shi an riga an binne shi tun da safe. Tayi shiru tana tsuke baki muka sake yin shiru.
Amma.... Dai kinsan ai abunda kikayi baki kyauta ba ko? Ko kina ganin daidai ne Abinda kikayi? Fadila ta dauke kai gefe guda.
Da zamu bar zancen nan dai da zaifi.
Don me yasa kika ce haka?
Saboda tone tone bashida dadi. Na Mike tsaye daga kan kujerar na jingina da bang.
Fadila Gaskiya al'amarin ki sun dame ni kin.... Ta katse ni.
Hilal Inason ka sani cewa duk abin da nayi adaren jiya nayi ne saboda mahaifina in baka sani ba kasani duk da cewa kuwa mahaifiyata tafi kaunata da shagwaba ni duk duniya babu wanda nake kauna kamar sa.
A zuciyata nace duk yadda akayi yarinyar nan tanada tabin hankali babu mamaki Hakan ne yasa ake kokarin bani auren ta.
Nasan Abinda kake tunani banida hankali ko? Ta dubeni. Na girgiza kai.
Kada ka boye min jarumi Hilal naga alamu a idanunka amma yana da kyau ka yi tambaya kafin ka yanke hukunci.
Toh..... Amma saiki kashe jariri kice wai saboda kaunar mahaifin ki kikayi? Ta kada min idanu tace.
....... Nan da wata bakwai mahaifina zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna babu abin da nake buri irin ace yau mahaifina ne Gwamnan garin nan. Tayi shiru tana rangaji agabana kamar bishiya.
Ina Fatan yanzu ka fara fahimtar hoton da nake kokarin zana ma? Kaga Hilal ciki dai nariga nayi Munso mu zubar da cikin nida mahaifiyata tun yana ƙarami mahaifina ya hana lokacin Dana haihu sainaga in har na bari dan ya girma nagama kunyata mahaifina kuma idan zancen yafito Abokan hamayyar siyasar sa na iya yin amfani da damar su bata mahaifina.
Amma kuma bakya ganin yanzun ma bata sauya sani ba tunda dai ai jama'a da dama sun sani kinada cikin shege?
Jama'a kamar su wa? Ta tambaye ni gamida daga girar idanunta sama.
In banda kai dakuma likitan mu da ya auna ni ya tabbatar ina da cikin duk duniya babu wanda yasan inada cikin kai ko wanda yayi min cikin baisan inada shi ba domin tin yana dan wata daya aka hanani fita ko ina aka sa masu gadina har sai dana haife dan.
Kawaye na da Abokan Arziki idan sun zo ne mana sai ace dasu bana Kasar.
.
Nayi shiru ina sauraron shashashan zancen ga mamakina sianaji duk da kyawunta nafara tsanarta ko kadan bata da kunya.
Ina ganin idan babu sauran wani abu da zaki fada ni zan fita nayi sallah kinga har an idar sa sallah a masallaci nafara yar tafiya a cikin ofishin.
Au harma korata kake yi? Ta bata fuska.
Babu zancen kora kora in kina iyawa jirani nayi sallah sai muci gaba da hirar daga nan zuwa asuba.
Muga abunda Allah zaiyi nasaki Murmushi nafara Jin dadin badakalar.
Wai dan Allah da gaske kike yi baki kawo min kyautar komai ba? Ta kawo min duka cikin wasa na kauce.
Ya ishe ka haka kaga bana so.
Ta juya ta fara tafiya akwai alamun farin ciki a fuskar ta.
Muje to ka rakani.
Muka ratsa ta cikin dakin karbar baki.
Ban iya yarda na kalli inda lauriyya ke zaune ba.
Toh amma na lura zaune take ta kifa kanta akan teburin dake gabanta.
Nayi tsammanin zata biyo bayan mu da man Ga al'ada duk bakon da ya zo tare da ita muke raka shi amma Sam Sam bata biyo mu ba tun kafin mu Gama fita na hangi katuwar marsandin tana kyalkyali acikin hasken farin kwan lantarkin daya haskaka kofar ofishin......
.
KAI NIFA NA RIKICE NA RASA WACCE ZAN GOYA WA BAYA
LAURIYYA KO FADILA ????

0 comments:
Post a Comment