Wani irin dad’i maras misaltuwa Mama taji a ranta a yayinda hawayen jin dad’i suka soma gangarowa daga idanunta. Finally Allah ya amsa mata addu’arta ya shiryar mata da Zeezee a lokaci guda. Ba ita kad’ai ba harta Baba yaji dad’i matuk’a, saboda yadda Zeezee ta tsara maganan bame sanin wai duk plan ta had’a ga yadda take kuka me tsuma zuciya full of regret. “Come here Sweetheart” Mama tayi beckoning nata over. A nitse ta miqe, hugging nata Mama tayi suna kuka tare duk anan kallonsu Baba yake seda Mama tayi releasing Zeezee yaja hannun Zeezee tare da hugging nata shima. “Alhamdulillah! My old Zainab is back na yafe miki K’anwata, Allah ya cigaba da shiryar mana dake.”
“Ameen” shida Mama suka fad’a.
“Baba ina me sake baka hak’uri.”
“Kema kiyi hak’uri K’anwata for what happened am sorry kinji?”
“Ni baka min komi ba Baba, I love you so much.”
“Allah cigaba da raya mana ke.”
“Ameen” nasiha sosai Mama da Baba suka ta mata a yayinda take ta sheqe kuka, sun gama mata ta musu godiya ta fice a d’akin tana mejin dad’in completing first mission of her plan. Sosai Mama da Baba sukaji dad’i se sawa Zeezee albarka suke duk sun d’au dagaske ne Zeezee ta shiryu musamman ma Baba da abin yafi damunsa nunawa ne kawai bayayi.
Washegari Zeezee na tashi da safe bayan tayi wanka ta nufi d’akinsu Mama ta gaishesu cike da ladabi sannan d’akin Omar bayan nan ita da Mama suka shiga kitchen for the first time. Dukda kwa6a take amman yau ta shiga kitchen d’in da sunan yin aiki. Sun gama breakfast Zeezee ta ari wayan Mama da sunan zata gaishe da Al’ameen. Ba tare da Mama ta kawo wani tunani a ranta ba ta bata wayan, seda ta rufe k’ofan d’akin nata ta zauna kan kujera sannan tayi dialing number’n Al’ameen. Bejima ba ya d’aga.
“Hello Ya Alameen ina kwana?”
“Wow! Zainab kece?”
“Nice mana, ina kwana?”
“Lafiya hope you slept well?”
“Yes I did I hope you too.”
“Alhamdulillah so you called? Am startled anya kuwa kece?”
“Nice mana, na kira ne dama na baka hak’uri game da rashin kunyan dana maka a baya, am so sorry hakan ya faru ne bisa rashin tunanin da banyi ba amman I promise it’ll never happen again. Kayi hak’uri please na amince zan aure ka, I welcome you to my life wholeheartedly.” Al’ameen was left dumbfounded, anya kuwa Zeezeen daya sani ce? Kode she is possessed by some kind of evil spirit ne? Kokuwa shiryuwa tayi, but anya?
“Hello Ya Alameen? I know its hard for you to believe me but believe it or not na tuba kuma ina neman gafararka.”
“Masha Allah Zainab, I think am the most happiest man on earth right now.”
“Am glad I made you feel that, so ka yafemin?”
“Ni bakiyi offending d’ina bama ai Zainab bale ki nemi yafiya na.”
“Hakane?”
“Sosai ma Zainab.”
“Toh nagode mesa kake cemin Zainab?”
“Isn’t it your name?”
“It is amman Zeezee ake cemin ai.”
“I prefer your actual real name, yana min dad’i sosai.”
“Thank you kaima sunanka na min dad’i.”
“LOL hakane?”
“Yes, so ya aiki?”
“Nad’an kar6i leave but alhamdulillah.”
“Toh masha Allah, ya kowa da kowa a gida? Kanada sisters? If yes meh sunansu?” Haka Zeezee tayita jan Al’ameen da surutu ranan gabad’aya mamaki ya rufesa he can’t believe actually its Zeezee. Shiko biye mata yayi ko breakfast ma beyi ba ranan seda airtime na Mama ya k’are. Take ya kirata back tayita mai hiran shirmeh bayan sunyi sallama yayi wa Mama VTU transfer’n 10k.
Wani maqirin murmushi Zeezee ta saki “ai wallahi Soldier seka gommaci kid’a da karatu bakai wai Zeezee kakeso ba? Ha!” Ta cize lips nata. Haka nan tun daga ranan Zeezee bayan 2-2 days take kiran Al’ameen. Atimes in bata kira ba shi yake kira suyita hira kaman dagaske, Al’ameen could’nt ask for more, Zeezee is the most happiest and sweetest thing that has ever happened to him. Tunda yake be ta6a son ‘ya mace kaman Zeezee ba kullum cikin zancenta yake wa elder Sis nasa Sadeeyah da younger sisters nasa Salmah and Ayshah duk they are so eager suga Zeezee. Mamanshi Hajiya Ameenah kam couldn’t ask for more finally Allah ya amsa mata addu’arta her son is in love. Kullum Al’ameen cikin zancen Zeezee yake duk friends nasa sunsan da zaman Zeezee, sonta yake tsakani da Allah, fiye da tsammanin d’an Adam, wannan kenan!
****
Har a yanzu Zeezee bata sanar da Adeel halin da ake ciki ba kamar yadda tayi hani wa Lubiee da komin rintsi karta fad’a mai itama when the right time comes she’ll let him know. Everybody a gida believed Zeezee da Al’ameen soyayya suke saboda har sau biyu yake zuwa mata Baba da kansa ya basu parlour’n shi suyita hira, aduk zuwansa kuwa seyayi wa Zeezee kyautan kud’i wanda kaman dagake ta d’auka duk ta baiwa Mama. Al’amura sun daidaita ras tsakanin Zeezee da Baba sun dawo kaman yadda suke da sede har yanzu Baba bece ze sai wa Zeezee waya ba kamar kuma yadda kuma be miyar mata da motarta ba.
*~ * ~*~
Yau ranar ta kasance Wednesday, 11:27AM Zeezee ta ari wayan Mama as always ta kira Al’ameen bayan sun gaisa take cemai, “Ya Al’ameen tun d’azu naso kiranka Mama bata tashi da wuri ba.”
“Ayyah ba komai My Princess, how are you?”
“As you are, did you sleep well?”
“I did I also dreamt of you.”
“Oh really?”
“Yeah” hira suka tayi chan yake fad’a mata ze koma aiki Abj anjima.
“Ayyah I will miss you.”
“Zanzo muyi sallama karki damu we’ll keep in touch.”
“Da wayan Mama da kullum ke hannuntan? Ina ma ace inada waya na sabida muna waya kullum”
“Kuma haka fa yakamata ace kema kinada wayarki.”
“I use to have one.”
“Ya 6aci ne?”
“A’a Baba ne yayi seizing ya fasa lokacinda na ta6a yin wani laifi.”
“Will he agree if I buy you a new one?” Dad’i sosai taji finally her plan is working.
“Ban sani ba seka tambayesa.”
“Toh karki damu My Princess zan taho miki da sabon wayanki yau in shaa Allah.”
“Really Ya Al’ameen?”
“Don’t you trust me?”
“Yes I do Ya Al’ameen thank you so much.”
“Shh! Lemmi take my shower my flight is by 1:30pm.”
“Tam sekazo see you” nan ta katse. “Mschww gaskiya na miji anyi soko wallahi yanzu koshi Ya Al’ameen ne kome sunansa hankali baze basa duk faking nake ba? Ni ina zan kai tsoho kaman sa? Anyways his own wahala my new phone is coming soon can’t wait to skype my very own!”
12:19PM Al’ameen ya iso gidansu Zeezee da sabuwar wayarta cikin leather suna zaune a parlour da Baba bayan sun gaisa yayi clearing throat nasa “Brother ina fatan banyi gwaninta bako?”
“Name fah Maj-Gen?”
“Waya na siyo wa Zainab namu tace she is not confortable amfani da wayan Madam.”
“Oh hakane? Ba matsala toh.”
“Toh nagode Brother yauma zan koma Abj nazo muyi sallama da ita ne.”
“Toh bari nayi mata magana” Baba da kansa yaje ya kirawo Zeezee “K’anwata Maj-Gen yazo wajenki.”
“Toh Baba ina zuwa” ta amsa tana murmushi, gyalenta taja sannan ta fice a k’asa kamar yadda ta saba kullum ta zauna tare da mai sannu da zuwa. Duk da haushinsa da takeji takasa ignoring kyan da Al’ameen ya mata, bata ta6a ganin hot man in uniform kaman shi ba, farin fatarsa dake bata haushi ma yamata kyau yau amman ba hakan yasa taji tana sonsa ba ita Adeel nata kawai takeso.
“My Princess bazaki zauna kan kujeran ba yanzu?”
“A’a Ya Al’ameen nanma yayi.”
“A’a ni ki hau ki zauna please.”
“Seriously nanma yayi karka damu.”
“Ni sekin hau toh.” Seda yayi dagaske sannan kaman dagaske Zeezee tahau kujera ta zauna se wani kakkare fuskarta take. Hira kad’an suka ta6a yace ze tafi leather’n wayan ya ajiye mata kan cinyarta. “As promised My Princess in colour’n be miki ba let me know zan turo wani yaro na ya sai miki sabo.”
“Toh meh aciki Ya Al’ameen?” Tayi maganan tana bud’e leather’n black jet iphone 7s taga ciki “wow! Ya Al’ameen thank you!”
“Nifa na gaya miki banason godiyan nan, do you like it?”
“Yes I do thank you.”
“Am glad toh ni zan wuce.”
“Toh bari nafad’awa Baba” sede data duba alokacin Baba yashiga wanka dan haka ta rakasa har waje tana ganin guards nasan ta wani had’a rai seda Al’ameen ya gano hakan.
“Bakison ganinsu ne?”
“A’a” ta k’irk’iro murmushin k’arya “kawai tsoro suke ban da wannan guns d’in.”
“Next tim zanzo barasu zoba tunda baki son ganinsu.”
“Oh common karka damu Allah ya kare toh.”
“Ameen My Princess” Seda taga ficewarsu ta koma ciki wayar ta bud’e a garin haka airtime na 10k da new sim card ya fad’o. Murmushi ta saki “wai! Zanyi skype da Very Own har sena gaji!” Had’a wayar a charging tayi. Baba na fitowa daga bayi taje ta fad’a mai. Nasiha sosai yayi mata and like a good girl tayi godiya ta fice.
****
Life couldn’t be better tun daga ranan da Al’ameen ya sai wa Zeezee waya ta rage kiransa as 24/7 tana kan video or voice call da Adeel nata. Shima Al’ameen dake ya koma aiki yanzu seya jera kwana uku be kirata ba in se in yasamu free time yake kirantan, ita kuwa seta mai k’arya wai gari ba wuta shiyasa bata samun kiransa itama wayarta ba chargi. Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa, wani new chapter’n love Zeezee da Adeel suka bud’e. Da k’yar ranan Baba yabar Zeezee tajeta gidansu Lubiee nan ma Omar yasa yayi dropping nata. Achan suka had’e da Adeel nata, wani k’war jini taga ya sake mata cause she can’t remember when last ta sasa a ido tun birthday’nsa se inde a video call. Hira da shafe-shafensu suka ta sha like never se 5:30pm da Omar yazo d’aukanta sukayi sallama nanma da Adeel yayi hugging nata ji take kamar ta bisa su gudu karta koma gida remembering she has a better plan in mind sukayi ba-bye ta fice.
Da daddare tana ta chatting abinta da Adeel da Lubiee. Lubiee tayi messaging nata _Babe nifa har yau kink’i nuna min hoton Ya Al’ameen na k’osa naga angon namu._
_Gaja ai Ya Al’ameen kome yake ba shine real ango naba ko kin manta Adeel ne? Ya Al’ameen is the ladder that will take me to my dreams._
_Hmm nide ba ruwana kimin sending pic nasa kawai abinda na tambaya kenan._
_Yo ai banida pic nasa nikam Adeel ya hanani barin hotunan maza a waya._
_Babanki dake da Adeel d’in Babe please show me his pic or kishinsa kike ne?_
_Over my dead body wallahi banida pic nasa amman bari na duba dp’nsa ko yasa na hankad’o miki._
_Yauwa do please._ Zeezee na dubawa aiko Al’ameen ya cire daman wani hotonsa ne da uniform ya bala’in yin kyau.
_Ke Babe seki d’au na annabawa yacire pic nasan._
_Dang it! toh ask him mana ai he is your boyfriend._
_Fake boyfriend FYI plus a dalilin meh zan tambayesa pic nasa? Ba seya d’au sonsa nake ba._
_Oh! Toh Allah shiryaki nide na gane rowansa kawai kike min._
_LOL Allah ya mayar zan miki sending._ chan dare kafin ta kwanta taga yayi changing dp nasa ya miyar dana d’azun take tayi saving ta turawa Lubiee nanfa Lubiee tayita hauka ita sam Al’ameen yafi Adeel kyau kuma ai in bawai an fad’a bane baza’a d’au ma yayi 42 ba sede 38 haka. Zeezee mafa tasan da zaman haka amman dan iskanci da neman take gaskia sam tace ita ba haka ba Al’ameen is too old.
_Several months later..._
Al’ameen har ya dawo daga Abuja angama magana ansa date na bikin aurensa da Zeezee in 3 months time. Jin haka kuma Zeezee ta kariya ta soma kuka sosai ita bata son auren. Karap Mama ta bud’e k’ofar d’akinta da wuri ta share hawayen nata. “Kuma kukan me kike?”
“Niba kuka nake ba.”
“Banida ido ai nace kukan me kike?”
“Mama ni banason auren wallahi.”
“Baki so?! Dama bason Ya Al’ameen d’in kike ba?”
“Ina sonsa auren ne banaso.”
“Kinga banason shashanci kina jina ko? Auren ki nanda 3 months ba abinda muka fara gobe zamu wuce Kano chan za’ayi maki siyayyan, kinji koh? Seki fara shiri.” Shiru Zeezee bata amsa ba. “Bada ke bane?”
“Dani ne.” tayi murmuring. Washegari suka biya ta air to Kano achan suka gama wa Zeezee siyayya, kud’i in abundant Baba ya bawa Mama ba abinda basu sai mata ba. A guest house na Baba aka sauk’e kayakin kasancewar har yanzu Zeezee bata yanke hukuncin wani gari take so ta zauna ba.
_Morning hours..._
Tana zaune a d’akinta damuwa sun mata yawa wayarta ya shiga ringing acewarta ma Lubiee ce tana kai dubanta taga Al’ameen wani dogon tsuka taja haka tana gani har ya yanke bata d’aga ba se a karo na biyu. “Hello My Princess” kamar wacce baza tayi magana ba tace, “na’am ina kwana?” sede daga yadda tayi maganan yagano da akwai matsala “any problem Zainab?”
“Babu” tayi stating sama-sama.
“Are you sure ko auren ne bakiya so a fasa?”
“Eh” ta fashe mai da kuka.
“A fasa?” yasa dariya.
“Am serious Allah dan Allah karka rabani da Mama da Baba kuma ka bar min dariya.”
“Toh nadena theres nothing to worry kinji? I’ve got you Zainab, I love you so much.” Wani haushinsa ta sakeji sannan dan dole tace, “thank you.”
“So kinyi making up mind naki? Zaki zauna a Kaduna a family house kokuma anan Bauchi alone ke kad’ai? Kinsan a Abj nake aiki Kaduna is more closer and zanfi samun visiting naki frequently.”
“Chabd’i! A family house? Nice zan zauna da in-laws? Lallai kuwa! Ka sake tunani”
“Excuse me?” Yayi maganan suprised. Ita kanta Zezee batasan lokacinda tayi maganan ba. “Uhm Ya Al’ameen I mean zama da in-laws d’innan gaskiya bana so problems yake haddisawa.”
“Trust me, my family don’t have that problem.”
“I know kawai nice banaso gomma nan Bauchin ina kusa da Mama kai kuma koda jifa jifan ne kana visiting d’ina its okay by me.”
“Are you sure?”
“I am ”
“Toh shikenan hakan za’ayi, I love you.”
“I know, thanks.” Tunda Al’ameen yake be ta6a jin Zeezee tace mai I love you ba amman dake shiyasan yana sonta ne don Allah badan wani abu ba be ta6a damuwa ba.
“Toh semun sake waya, take care.”
“Bye” tayi hanging take ta kira Lubiee.
“Hello Matar Soja” cewar Lubiee.
“Babe ya zanyi dan Allah? Taya zan fara sanar da Adeel aure na is in three (3) months time? I really dunno how please help me out.”
“Kefa Zeezee banza ce wallahi, forget Adeel wallahi Ya Al’ameen loves you.”
“That will be the last thing I’ll ever do kefa bakisan yadda nakeji da Adeel bane.”
“Toh ya zakiyi yanzu? Kinason na fad’a mishi ne?”
“A’a please don’t zan fad’a mai da bakina.”
“Toh suit you well ni ya batun ashobe ne? Wanda muka fitar d’in sunyi?”
“Yeah leave that to me wallahi kap ashoben Ya Al’ameen ne ze biya tunda shi yace yana sona.”
“Haba! Zeezee set ukun duka zakice shi? Pity him mana.”
“Shi yayi pitying d’ina ne daya kama yace yana sona seya auren? Ki ajiye kalman pity agefe friends d’in duka ku nawa ne?”
“Mu 18 ne.”
“Tam karku damu kede kawai ki sanar musu a group namu na LYS STARS kan in three weeks time suzo su karb’i ashobensu gidanmu.”
“Toh Matar Soja! Angama.”
“Mschwww! Banza kawai” tayi hanging. Al’ameen ta kira and har ya tsinke be d’aga ba kasancewar bai kusa, itama missed call d’aya tamai dan iskanci.
****
Da daddare ta sake trying nasa be jima ba ya d’aga “hello My Princess you called earlier bana kusa sorry.”
“Its okay dama batun ashoben friends d’ina ne a kace na tuna maka.”
“Okay, nawa kike buk’ata all in all?”
“Kaga friends d’ina are 18 in number each person kuma ten thousand five hundred (N10,500) ne making one hundred and eighty-nine thousand (189,00) altogether.”
“Okay zan baki 200k incase kinsamu additional friends.”
“Tam sekuma na makeup artist, nida Lubiee kad’ai za’a mana.”
“Shikuma nawa?”
“Nawa 60k na Lubiee 25k through out the 5 events all together is 425k plus na ashoben making 610k.”
“Wow! My Zainab is such a great mathemathecian zan miki transferring 650k hope thats all koh?”
“Eh shikenan and karka min ta acct na Mama kayi ta nawa.”
“Toh My Princess anything for you shikenan?”
“Eh shikenan for now.”
“Okay feel free to call me up whenever your need arises.”
“I’ll thanks” tayi hanging. “Baho ai seka tsiyaye wallahi mschw ni yanzu ta ina zan fara sanar da Adeel for God’s sake?” Tana cikin wannan tunani alert na 650k ya shigo wayanta maqirin murmushi ta saki.
3 WEEKS LATER (2 months one week to Zeezee’s wedding) LYS GROUP CHAT.
Lubiee; _Announcment! Babes y’all invited zuwa gidansu Zeezee yau kuje ku amshi ashobenku kala uku which is worth N10,500. Ba a buk’atan kud’inku saboda Soldier’n mu which is our ango to be yariga ya saya muku._
Sumayya; _what?! You mean to say Zeezee zatayi aure? Tsaya wata Zeezee tukuna?_
Miss Aysha; _help me ask o bangane wata Zeezee ba nima._
Lubiee; _Zeezee nawa kuka sani a garin Bauchi? Zeezee Isma’il Yosouf FYI in ashoben ne bakuso a baiwa wasu, mschww!_
Miss Xoxo; _weehoo!! Kuce angon namu DON ne ashoben N10,500 ya siyewa kowa?_
Lubiee; _abinku da Maj-Gen! So sekunzo wacce batazo a yau ba za’a baiwa nata ma wata._
Sumayya; _LOL sekun ganmu toh su Zeezee amarya muna jiran pre wed._
Ilhamerh; _kefa gulmanki ya miki yawa Sumayya angon kike son gani kome?_
Mjay; _barta deh shegen gulma ne da ita._
Sumayya; _no bayan cika bakin da tayita yi kan seta gama degree tayi aure ne ai nakeson ganin wazata auran wait guys ina Adeel nata fah?_
Rumaysa; _kema kinsan Zeezee bazata auri gaja anyhow ba ko bakiji Soldier bane?_
Lubiee; _ke wallahi Sumayya gulma ya miki yawa mschw! Ba wanda yasan destiny’n sa kuma thank god ma had’ad’d’en miji zata aura wanda yafi Adeel_ pic na Al’ameen ta musu sending ai sam Sumayya da k’awarta Ameena suka k’i amincewa da wannan kyakkyawan soldier’n ne mijin Zeezee don black belle.
Miss Aysha; _can’t wait!!!_
*~ *~ *~
Da yamma friends na Zeezee suka hallaro amsan ashobe, bikin Zeezee de yazama talk of the town sabida basu ta6a jin bikin da ango yayi ashoben 10,500 wa each friend ba. Har rana me kaman na yau Adeel besan me ake ciki ba as Zeezee bata sanar dashi ba bekuma ji rumor a gari ba.
*© MIEMIEBEE Team #YGC!*
👄👄👄👄
wwww.beeenovels.blogspot.com
[1/7, 3:04 PM] 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣2⃣
Jere aka shiga yiwa Zeezee achan gidanta dake New GRA layin Sunday Awoniyi road, wannan gida shi ake kira da mansion I don’t have to go in details sanin kanku ne gidan Maj-Gen ba wasa. Ana cikin haka Zeezee takai Lubiee gidanta suka duba se yaba gidan Lubiee ke, gida sekace ba a Bauchi ba. A month to biki Mama ta d’aukowa Zeezee me gyaran jiki daga Maiduguri wacce tayi wa su Mariam da Yasmeen. Sam Zeezee tace ita bataso seda Mama tayi dagaske ta amince, magunan gyaran jiki da Mama ke bata kuma har ayau ba wanda ta ta6a sha da an bata seta wulla cikin side drawer’n gadonta.
Yau ma as usual da safe Mama ta shigo d’akin nata rik’e da roban drugs d’in “ina kwana Mama?”
“Kin tashi lafiya?”
“Eh sannu.”
“Kinga yadda skin naki ya k’ara haske kuwa? Ai kin kamoni fari yanzu koma ince kin fini, amman kice wai ke ba ruwanki da gyara? Bansani ba ko jiki kaman na k’adangare kikeson kije dashi gidan Maj-Gen. d’in yadda zeji dad’in sako ki.”
“Ai daya kyauta.”
“Kika ce meneh?”
“Eh man ai gaskiya ne wallahi shiyasa banason wannan shirmen gyaran jikin ayita miyarwa mutum fata ja sekace fuskan Ya Ibraheem.”
“Aww Baban nawa kike zaga?”
“Toh ai gaskiya ne, ayita murjewa mutum jiki sekace Aljannah za’a kai sa mschw!”
“Toh ya isa ke dama baki gaji mutunci ba, ga maganinki.” K’afa ta shiga shurewa “wai Mama kullum magani magani sekace rashin lafiya nake ni wallahi na gaji banaso.”
“Wawiya wannan ba shine ze gyara ki ta ciki ba, ko cemiki akayi gyaran waje kawai ake?”
“Nide banaso.”
“Amshi nace banason zancen banza” haka Zeezee na gunguni ta amshi maganin ganin Mama bata kallonta ta wurga goran k’ark’ashin gado. “Yauwa ni ranan ina na ajiye makullin gidan naki ne?” Mama tayi maganan tana k’ok’arin jan side drawer’n kan Zeezee wanda take tara duka magunan nata aciki. Ganin haka da wuri Zeezee tace, “Mama baya cikin chan karki b-” bata idda maganan ba Mama taja kawai gani tayi maguna suna mata sallama. Baki ta sake wide in shock totally out of words wato duk aikin banza take kullum tayita kawo mata magani tayita kashe kud’inta duk a iska, lallai Zeezee!
“Me wannan?!” Ta tambaya a fusace. Lamo Zeezee tayi zaune kan gadon tana kallon k’asa. “Magana nake miki, meh wannan? Bazakiyi magana bane?”
“Mama kiyi hak’uri dan Allah.”
“Meh wannan nace?!”
“Magunan ne.”
“Magunan dana ke baki?” A hankali ta gyad’a kai mari lafiyayye Mama ta kai mata a bare back nata seda shatin hannunta yafito nan Zeezee tasa ihu “dan k’aniyanki inyita asaran kud’i na inasai miki abinda ze amfane ki ashe duk tarawa kike ba sha kike ba? Iyye?!” Tana murza bayan nata ta kad’a kai “kiyi hak’uri kar Baba ya sani dan Allah.”
“Inba rashin wayo irin naki ba dry d’inki haka kikeso ki jewa shi Maj-Gen d’in? Ana baki abinda ze taimakeki kina shashanci? Ina wanda na baki yanzun?”
“Na shanye” tayi k’arya.
“K’arya zakimin? Ina yake nace?” Tsugnawa tayi ta zaro goran daga k’ark’ashin gado “maza bud’e kisha ina ganinki.”
“Mama wallahi banaso da Allah kiyi hak’uri.”
“Bazaki bud’e bane ko sena kira Omar ya baki kashi?” Haka Zeezee na hawaye ta kurb’e goran tas tun daga ranan Mama ke tsayawa akanta seta shanye maganin tas sannan tabar kanta.
2 weeks to bikin aure Mama ta soma batun pre wedding pics saboda yadda sisters na Al’ameen sunka k’osa kullum cikin kiran Mama suke awaya. “Zeezee! Zeezee!” Mama ke kiranta.
“Na’am” ta amsa tare da zuwa ga koran “gani.”
“Ehem kinada labarin gobe zamu wuce Abj ko? Achan zakuyi pre wedding pics nakun.”
“Har Abuja?! Kuma ma wani pre wedding? Shi baze zoba sede ni na bisa? Ni wallahi banason bidi’ancin nan ayi aure kawai ba shikenan ba.”
“Lallai kam! Keda shi waye babba? Ko bakisan he is busy bane yanzun ma squeezing time nasa zeyi bama wannan ba se in in-laws nakin suka kiraki kice musu ke baza kiyi ba nide na gayamiki anjima Omar ze amso miki d’inkunanki daga gun tailor seki had’a akwatinki.” Tana kuka ta koma d’akinta, babban tsoronta shine kar Adeel yaga pre wed’s d’in saboda tasan muddin akayi hoton dole ze gani, takira shi ta sanar dashi yanzu kuma batada courage. Ta shiga contacts neman numban Lubiee Adeel ya soma kiranta seda ta sa lock a d’akintan ta d’aga tare da clearing throat nata “hello Very Own.”
“Sweetest Love ya kike?”
“Lafiya” ta amsa sama-sama.
“Why whats wrong? Muryanki sounds not okay.”
“Bakomai kawai na buga k’afa na ne jikin gado.”
“Awcchh! Sorry Hun.”
“Its okay so ya kake?”
“Am good Sweetest Love anya kuwa buga k’afanki kawai kikayi? Something sounds really not okay.”
“Seriously...” Sekuma ta fashe da kuka. “Gosh! Did I say something wrong? Please stop crying” kukan ta tayi da k’yar ya samu tayi shiru. “Yanzu zaki fad’a mun mesa kike kuka?”
“Very Own babu.”
“So kike muyi fad’a abee? Tell me.”
“Very Own please no matter what happens know that I love you morethan words could ever tell and that I can die for you.”
“I know that Babe and I love you as much but why the sudden words?”
“Babu I just want you to know that no matter what you are the only love of my life.”
“I love you Babe, so much.”
“I love you too, what of now? In nazo gidanku neman auren ki still Baba will suspect?”
“He’ll Adeel mubari nan da months ahead haka.”
“Babe what if before then wani ya rigani zuwa fah? I can’t lose you.” Wani kukan ne yaso fin k’arfinta da k’yar ta danne sanin Al’ameen ya riga ya rigasa, batasan da wani bakin zata soma fad’awa Adeel aurenta saura sati biyu ba.
“I’ll call you later, I love you.”
“I love you too” jira tayi yayi hanging sannan ta koma kan gado ta cigaba da kuka. Da yamma kayakinta suka iso Mama da kanta ta had’a mata akwati a washegari suka wuce Abj ita da Mama achan suka had’u da Al’ameen, he couldn’t take his eyes off Zeezee dan yadda skin nata ke wani glowing. The following day best makeup artist na Zeezee wato Oshewa Beauty ta cancare mata makeup sannan suka wuce studio’n George Okoro sukayi pictures. Pictures are just lit and fire! Zeezee bataso 6ata pre wed’s nata ba saboda mutane irinsu Sumayya masu bacci da ido d’aya. Kafin ace me pictures se yawo yake a social media.
Kwana d’aya suka k’ara suka juyo ita da Mama.
3 days to biki Mama ta kawo wa Zeezee wani pepper soup na kazan daya sha had’in maganin gyaran jiki banda rashin dad’i bakomi tattare da shi. Zeezee na kai bite d’aya baki tace ita sam bazata ci ba, tsaye Mama tayi akanta da belt haka seda Zeezee ta cinye kazan tas wane zatayi amai.
****
Adeel ne miqe kan gadon d’akinsa yana viewing pics a instagram, yashiga ta explore kawai yaci karo da biggest and most shoking suprise of his life wato pre wed pic na Zeezee da Al’ameen wanda take sanye da hulansa na soja akanta sun rik’e da hannun juna suna dariya. Idanunsa ya shiga murzawa danko ya kasa believing what he is actually seeing, gashi de a zahiri Zeezee yake gani a hoton amman ya kasa believing itance. Tapping hoton yayi nan name nata da akayi tagging yafito assuring him itance ba me kamanninta ba.
“No! No! It can’t be possible it just can’t, this is not Zainab me kama da ita ne” yayi maganan yan kad’a kai still not believeing. Wani irin ciwo yaji a zuciyarsa wanda be ta6a witnessing ba wurgi yayi da samsung J7 dake hannunsan seda ta tarwatse. Wasu zafaffun hawaye ne suka soma sauk’owa daga jajayen idanunsa a yayinda kansa ke masa wani irin sara. Da k’yar ya iya mik’ewa ya ciro iphone nasa daga wardrobe ya kira Lubiee.
***
Tana shirin zuwa gidansu Zeezee ta tsaya tayi picking “hello Adeel?” Kawai jin sautin kukansa tayi “omg! Adeel are you okay?” Shiru be amsa ba “kana ina ne? Hello Adeel?”
“Lubiee tell me it aiint true kinji? Dan Allah tell me its not.”
“Whats not true? Ban fahimce kaba.”
“Z... Z... Zeezee.”
“Meya samu Zeezee kuma?!” Tayi maganan hankali tashe a cewarta ma kowani abunne ya samu Zeezee.
“Aure Zeezee zatayi?” Dum! Zuciyarta ta buga ina kuma Adeel yasamu wannan labari kode Zeezee ce ta fad’a mai? Kai No halan yaga pictures d’inne a instagram. “Answer me please pre wed nata nagani dawani soldier, itace? Is she really the one? Is Zeezee getting married to someone else? Ke kad’ai zaki iya amsa min wannan tambaya.”
“Adeel calm down okay?”
“How can I calm down Lubiee? Zeezee zatayi aure and wani zata aura for all this while she’ve been cheating on me shiyasa koda nace mata zan tura Uncle Abdul gidansu take tamin corner-corner ashe this was it, she have someone already. I should have guess.” ya k’are maganan sounding disappointed.
“Omg! Adeel stop saying all these kaima kasan kalan son da Zeezee ke maka, its not what it seems.”
“Ni just answer me itace ko ba itace ba?”
“Itace amm-” katse wayan yayi a kanta koda ta shiga gwada line nasa kuwa bayi shiga. Yini Adeel yayi ranan yana kuka indeed this is the biggest heartbreak daya ta6a witnessing a rayuwansa.
Lubiee kuwa koda ta isa gidansu Zeezee takasa fad’a mata abinda ya faru sabida batasan ta ina zata fara ba.
Da daddare Zeezee tayi trying both lines na Adeel sede switched off yake ta cemata, sanin ba halinsa bane switching off phones nasa hankalinta ya matuk’ar tashi. Lubiee takira right away “hello Babe meya samu line na Very Own bayi shiga? Inason mishi magana, its high time I tell him the truth.”
“Ermm.. Ni... Nima ban sani ba fa tun d’azu nake trying.” Sede don yadda Zeezee tasan Lubiee ta gano k’arya Lubiee ke. “Babe you are hiding something from me dan Allah ki gayamun meya samu Very Own d’ina? Yayi accident ne? Is he badly injured?”
“Zeezee enough of the panicking please ba abinda yasamu Adeel nima nayi trying line nasa it aiint going through.”
“Babe please don’t lie to me on this, I can sense it ba lafiya ba dan Allah meya samu Very Own?”
“Zeezee wallahi babu abinda ya sami Adeel just that... Just that...” sekuma tayi shiru.
“Just that what? Tell me please.”
“He has find out the truth already Zeezee.”
“Truth about my wedding? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” sekuma ta fashe da kuka “Babe how? I intended on telling him everything tonight dan Allah tell me its not true, please...” ta sake rushewa da kuka.
“Please ya isa kuka is never a solution I know Adeel he’ll calm down soon enough, if he does nida kaina zan mai explaining komi please kibar kukan haka.” Har anan Zeezee kuka take, “Lubiee na fiki sanin Adeel wallahi baze ta6a sauk’owa ba, koda zeyi ma ba nan kusa ba nikam na mutu na lalace, Al’ameen be kyautamin a rayuwa ba” tana kaiwa nan ta katse wayar. Wurgi tayi da kanta bisa gado ta shiga rera kuka tana sumbatu ahaka Mama tazo ta tarar da ita ba kalan tambayan duniyan da batayi wa Zeezee ba amman Zeezee tak’i tankata. Daga k’arshe ma kawai tayi suggesting halan kukan shagwa6an barin gida Zeezee ke.
Kwana ranan Zeezee tayi tana trying layin Adeel sede sam its not going. Washegari Lubiee itama ta gwada line na Adeel bai shiga tana gama shiri tazota gidansu Zeezee inda ta sameta se kuka take Mama na a tsaye a kanta ta zuba mata ido. “Ina kwana Mama?” Lubiee ta gaisheta.
“Barka ma da kika zo Lubabatu, shin meke damun k’awar taki? Ba kalan tambayan duniyan da ban mata ba tak’i fad’amin. Tun jiya take wannan kuka ga gida ya soma cika da mutane banason a fara k’ananun magana cewa auren dole Babanta keson mata.”
“Shikenan Mama zan mata magana kije ba damuwa.”
“Yauwa please.” Mama na ficewa Lubiee taja crying Zeezee jikinta “Babe its okay please kinga kukan nan baida amfani bashi ze dawo da Adeel ba, yau zanje gidansu in samesa in person kinji?” Take Zeezee ta d’ago kai “please kije ni ko yanzu nema kije ki samesa I need him badly.”
“I will amman sekin bar kukan nan.”
“Wallahi na bari” tasa hannu ta share hawayen nata. Sosai idanunta suka kumbura sukayi water bags a k’asa.
“Toh bari naje na same san” anan Lubiee ta fice zuwa gidansu Adeel.
Mamin shi kad’ai ta tarar bayan ta gaiaheta ta tambayi ko Adeel na gida.
“Ai Auta na baya nan Lubabatu, be fad’a miki zeyi tafiya bane?”
“Tafiya Mami?!” Lubiee tayi exclaiming.
“Eh fah.”
“Amman lafiya dai ko?”
“Toh kinsan halin Auta baya son sanar dani problems nasa, nide all I know is tun jiya ko lunch yak’i fitowa yaci yau da safe kuma na gansa fuskansa duk a kumbure yana rik’e da akwati. Dana tambayesa ko lafiya kuma yacemin lafiya kawai ze wuce Florida ne yaje ya huta achan yanzu haka yana Abuja d’azu ya kirani kan sunyi landing.”
“What?! Florida ze wuce?”
“Eh wai.”
“Toh Allah sa lafiya ya kuma dawo dashi lafiya amman Mami ya gaya miki for how long he’ll be staying there?”
“A’a gaskiya nima ban tambaya ba becika son tambaya haka ba.”
“Toh numbansa nakeso zan kirashi.” Bayan Mami ta bata layin tayi godiya sannan ta fice a bakin gate ta kira layin Adeel thankfully ya d’aga “hello Adeel?”
“Lubiee?” Ya tambaya not sure.
“Eh ni, kai haka akeyi ne Adeel? Yanzu ka kyauta kenan tun jiya Zeezee ke kuka-”
_Disconnected_ taji tana dubawa taga hanging call d’in Adeel yayi kafin tace zata sake kiransa har ya cire sim d’in ya karya. Tashin hankali! Kasa komawa gidansu Zeezee tayi. Zeezee ko tun d’azu jiran Lubiee take jin shiru ta kirata da kaman Lubiee bazata d’agaba sekuma ta canza mind nata “hello Babe I’ve been waiting for you since, ina kika shiga?”
“Uhn Ummi ce ta kirani wallahi I had to go back home.”
“Oh ayyah kinsamu kinje gidansu Adeel d’in?”
“Uhm-”
“Please don’t lie to me, komin d’acinta ki gayamin wani yanayi kika tsinci Adeel please.”
“Zeezee I’m terribly sorry, I went Adeel bai gida yana Abj as we speak now daga can ze wuce Florida for a break regarding what happened.”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! No! No! No please!!!” jefar da wayan nata tayi ta ruga aguje zuwa bayi tasa lock. Bajewa tayi k’asan toilet d’in tana kuka wane don shi aka turota. Hakan ta cigaba dayi seda hawayenta ya kusa k’arewa. “Adeel why do you have to leave me please, why? You know right I can’t leave without you please come back it doesn’t have to be this way.” Seda tayi calming kanta ta fito ta d’au wayar several missed calls na Lubiee ta tarar nan ta kirata back “thanks Gee!” Lubiee tayi exclaiming.
“Lubiee kimin sending digits na Adeel if kinada please.”
“Wallahi bani dashi sabo wanda Mamin shi taban ma yabar shiga maybe ya karya koya kashe wayan. Yanzu ba lokacin damuwa da Adeel bane it might follow afterwards kinsan fa jibi za’a fara wedding events naki inhar kikayi ruining su Sumayya sun samu abin magana akai kenan. Please ba don ni ba don Allah ki manta Adeel for now kinji? Kiyi hak’uri.”
“Thank you sekinzo gobe” nan tayi hanging. Haka koda Mama ta kawo mata maganinta yau tasha ba tare da sunyi long drama ba takoma gado ta kwanta. Mama de harta gaji da tambayan Zeezee whats her problem.
A washegari Yasmeen, Fateemah da mazajensu suka hallaro.
_PROGRAMS OF EVENT Starts..._
Da Tea party suka fara, event ya had’u iya had’uwa sede Zeezee sam ba walwala tatattare da ita su Lubiee kad’ai sukayi enjoying party’n through out the event tunanin Adeel Zeezee ke. The following day akayi English dinner Zeezee and Al’ameen nailed it a wajen ba’a cewa komi se wanda yagani, naira yayi kuka. Bayan english dinner akayi Kamu se sword crossing wanda yafi dukannin events d’in so far had’ewa. The next day which is Friday aka d’aura auren MAJ-GEN. MUHAMMAD AL’AMEEN SHETTIMA da ZAINAB ISMA’EEL YUSOUF akan sadaki naira dubu d’ari biyu.
Zeezee najin an d’aura aurenta da Al’ameen ta rikice musu a gida ranan. Kuka tayita yi wane zata cire ranta. Ita abubuwan ma sun taru sunyi mata yawa. Na farko ba wanda takeso zata aura ba, na biyu ga barin gidan da zatayi and above all rashin Adeel nata. Su Mariam sun bata hak’uri har sun gaji, haka Lubiee, Fateemah da Mama ma. Wani kukan ma seda dangin Ango sukazo d’aukan Amaryarsu. Zanin Mama ta kama k’ememe tak’i sakewa se rusa kuka take tana sumbatu tana ita ta fasa auren. Ba yadda basuyi ba a fito da Zeezee sun kasa daga k’arshe Baba aka kira tana ganinsa ta ruga aguje ta nufi kansa tare da tattara jamfansa a hannu tana kukan cire rai tana basa hak’uri dan Allah ya barta ta cigaba da zama a gida ta tuba bazata sakeyin wani rashin hankali ba. Seda Zeezee tasa idon Baba yayi ja saboda yadda take kuka sosai har se ji yake kaman yasa Al’ameen ya saketa a fasa auran amman hakan bame yuwuwa bane.
“Yi hak’uri Zeezee, everything will turn out perfect kibi su Ayshah kinji? Muma zamu taho daga baya, muna tare ai Hafsah zoki jata.”
“Baba dan Allah kayi hak’uri Mama please karku fitar dani daga gidan nan.” Haka da k’yar aka fitar da ita aka sata mota zuwa gidanta, su Lubiee se hak’uri suke bata. Not long enough aka hau shirin dinner, makeup na ranan shine beyi kyau ba saboda yadda fuskan Zeezee ya kumbura bayan nan kuma tak’i ajiye fuskan nata se kuka take. 8:30pm suka wuce Zaranda Hotel inda za’ayi program d’in. Ai ganin hotel d’in kawai ta sake tunawa da Very Own nata. Suna zaune da Al’ameen a motar ta shiga rusa mai kuka, beso mata magana ba saboda yasan theres no point doing so and koda hak’uri ya bata ma sake worsening situation d’in zeyi dan haka kawai ya zuba mata ido se aikin kukan take. Dai-dai driver yayi parking Al’ameen juya ya kalleta “My Princess all shall be well kinji? Stop crying haka, our families awaits us.” Wani wutan tsanansa ne ke ruruwa a zuciyarta ko kallonsa batayi ba, da k’yar su Lubiee suka fito da ita daga motar. Tabari ya rik’e hannunta ma tak’i haka through out the event tak’iyin murmushi bale dariya se tissue take sawa a idonta tana tare hawaye.
*™ MrAndMrsMuhammadAl’ameen.*💑
*© MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣3⃣
_Hummm! I can smell my birthday tomorrow☺😋_
_This page is in honour of *Zaynab Anka, Ummee, Feedy G Muh’d, Kabo Daughter, Mom Nu’aym, Umm Aneesah, Maryam,* and *Maryam Wasagu* #OneLove❤_
Ana gama event su Zeezee suka dawo gida gabad’aya kowa ya watse a gidan daga ita se Al’ameen se soliders kota ina suna gadi. Driver na parking ta bud’o k’ofa ta fita gaban entrance door ta tsaya tana jiran Al’ameen ya bud’e mata k’ofa har anan bata bar kuka ba wanda hakan ba mugun damun Al’ameen yake ba. Har tambayan kansa ya somayi anya kuwa Zeezee na sonsa? Da guards nasa biye dashi ya k’arisa ya bud’e mata k’ofan kai kawai tasa se a d’akinta ta tsaya ta baje kan gado tana me cigaba da rusa kuka. Bayan Al’ameen ya bud’e kazan amarchi yasa mata a plate da farm fresh a cup ya nufi d’akin nasu, sallama yayi ganin batada niyyan amsawa yasa kai ciki kawai. A kan side drawer ya ajiye “Princess?” Ya kirata a hankali cikin sark’ak’k’iyar muryansa. “Princess kukan ya isa kinji? Yi hak’uri” hannunsa ya d’aga a hankali ya aza kan bayanta, jikinta ta ja da wuri tare da d’ago kanta tana mai wani mugun kallo. “Don’t touch me Al’ameen don’t! Bak’in cikin daka jefani kad’ai ya isheni ba seka k’ara min da wani ba. Ka rabani da iyayena and above all ka rabani da saurayi na Adeel kasa yayi nesa dani kasani bazan ta6a yafe maka ba Al’ameen. Ka cuceni I wish I’ve never met you.” ta k’are maganan hawaye na bin k’uncinta.
“Zainab what are you talking about? Weren’t you the one that agreed to thsi wedding in the first place? Dama ba sona kike ba kika bari akayi auren?” Ya tambayeta suprisingly.
“Nayi ne saboda in farintawa Baba rai amman badon wai ina sonka ba, ban ta6a sonka ba kuma bazan ta6a sonka ba. I hate everything about you, your skin and that sweet irritating voice of yours Adeel nakeso I want you to stick that to your head and please excuse me just looking at you disgusts me.” Ta k’are maganan tare da watsa mai harara.
Mamaki ne sosai ya cika Al’ameen da har ya zama lost of words amman be damu ba saboda gani yake har yanzu yarinya ce batasan ciwon kanta ba eventually al’amura zasu daidaita tsakanin su, he believe. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki “naji toh My Zainab amman tashi kiyi having dinner seki kwanta kinji?”
“I am not yours and ba ruwanka da abinda zanyi tunda ba zaman ka nake ba, kuma ka tattara kajinka kayi waje dasu banaso bazan ciba.” Tana kaiwa nan ta mik’e tare da jan akwatinta ta ciro night gown nata ta nufi bathroom. Kai kawai Al’ameen ya kad’a ya wuce d’akinsa shima ya watsa ruwa, koda yafito be koma d’akin nasu ba atunaninsa bari ya bata space. A parlour ya zauna yaci ragowar kajin. To twelve (12) ya lek’a d’akin nata yana sanye da ¾ wandon soldiers zalla, hakan ya sake fiddo da how muscular and built up his body is making him worth more looking. Kwance tana bacci ya tarar da ita tana sanye da wani pink sleeping dress me hannun spaghetti da ¾ wando. Kajin data ce bazata cin bama ta cinye tas harda fasa k’ashi. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki sannan ya k’arisa d’akin tare da gyara mata kwanciya yaja comforter ya rufeta sannan ya kashe musu wutan d’akin ya hauro suka kwanta. Sam beyi niyyan mata wani abu ba a daren ranan saboda yasan koda had’a sama da k’asa zeyi ba basa had’in kai Zeezee zatayi ba she needs some space.
12:50am Zeezee ta farka gabad’aya takasa gane meke damunta, tunda tasan kanta bata ta6a jin abinda takeji ba yau, juye-juye tahau yi kan gadon duk anan Al’ameen bacci yake peacefully besan meke faruwa ba. “Wayyo Allah na! Mama me kika samin a maganin d’azu?” Sauk’a tayi daga kan gadon tana me cigaba da juye-juyen a k’asa wani irin sha’awa kawai take jiyowa ita kad’anta ta rasa dalili. K’ara ta saki sosai seda Al’ameen ya tashi ganinta kawai yayi se juye-juye take. A hanzarce ya nufi kanta tare da sa hannunsa akan bare back nata kasancewar sleeping dress natan show me your back ne, “My Princess are you okay? Meke damunki?” Da wuri taja jikinta don d’an ta6a tan da yayi ba k’aramin affecting nata yayi ba kawai jin wasu electric sparks suna bin jikinta ta tayi a yayinda degree na sha’awan nata ya sake k’aruwa.
“Wayyo Allah zan mutu Mama kin kasheni dan Allah karka sake ta6ani I can’t take it.”
“Mama kuma? Me ta miki?”
“Dan Allah kabarni in kanayi wa Allah karka sake ta6ani muryanka ma dad’a min abinda nakeji yake in kanayi wa Allah ka tashi ka fita kokuma kasa kaya.” So take ta miqe amman takasa se juyi take wajen, tuni Al’ameen yagano meke faruwa. “Tashi toh muje mu kwanta.”
“Wai ana dole ne? Wayyo Allah na! Dan Allah ka tashi kabarmin kaina, Mama kin kasheni yau! Nashiga uku!!” Murmushi kawai Al’ameen ke ba yadda beyi da ita ba ta tashi suje su kwanta tak’i haka ya koma ya kwanta yana kallonta. Juyi Zeezee ta cigaba dayi agun ganin abin bana sauk’i bane taja pillow ta danne kanta har anan bata barjin abinda takeji ba. Ga sauk’i nan kawai taje ta samu Al’ameen amman batajin zata iya basa kanta tayima Adeel alk’awarin budurcinta. Haka tayita wahalar da kanta a daren ranan da k’yar d’in k’yar takoma normal ta haura gado ta kwanta.
Da Asubah ya tashi yayi alwala sannan ya zauna gefen sleeping Zeezee yana k’arewa kyakkyawan fuskanta kallo then back to d’an mitsitsin bakinta me uban tsiwa. Kallonta kad’ai na sanya masa farin ciki baze iya kwatanta yadda yakeson Zeezee ba. “Zainab” yayi whispering name nata. “Zainab tashi muyi Sallah kinji? Zainab!” yayi tapping nata. A hankali ta bud’e idanunta tare da kallonsa sekuma ta juya mai baya. “Tashi muyi Sallah ko inyi nawa ni kad’ai?”
“Ban sani ba” ta amsa a takaice ganin batada niyyan tashi ya miqe ya hau yin Sallansa. Seda ya kusa idarwa ta tashi itama tayi alwala. Koda ta idar bata gaishesa ba ta koma gadon ta cigaba da bacci. Al’ameen kuwa na gama Azkhar nasa ya fita waje ya samu men nasa ya hau training nasu har safiya be koma bacci ba.
Amarya kuwa se 10am ta tashi, bayi ta fad’a tayi wanka tana zaune gaban mirror da towel zallah a jikinta tana shafa mai Al’ameen ya shigo ganin batada kaya yad’an tsaya gun tare da clearing throat nasa ko zata gyara. Aiko maras kunyan yi tayi kaman bata jisa ba ta cigaba da wangale santala-santalan cinyoyinta tana shafa mai. Cikin d’akin ya k’arisa tare da zama bakin gado yana kallonta a yayinda wutan so da sha’awanta ke running a veins and atteries nasa. Tana gama shafa man ta d’au inner wears nata tasa sannan kayanta ko kunyansa bataji. “good morning My Princess tunda bazaki gaisheni ba” yayi speaking up finally. Ko kallon direction nasa batayi ba tafice izuwa kitchen tana tunanin dame zatayi breakfast. Tana cikin wannan tunani idanunta sukayi tozali da take away akan counter. Ba tare da 6ata lokaci ba taja ta bud’e chips da omalet taga ciki. Ai kujera kawai taja tahau ci seda tayi nak sannan ta koma d’aki alokacin Al’ameen na gun wanka. Wayarta ta d’au taga missed call na Lubiee take ta kirata tare da barin d’akin. “Hello Babe.”
“Matar Soja good morning.”
“Banaso ni na gaya miki banaso.”
“Toh yi hak’uri ya jiki-jiki?”
“Jiki-jikin k’aniya ce miki akayi banida lafiya?”
“Kamar ya?”
“Wai da kin d’au zan bawa Al’ameen kaina ne?”
“Aww yanzu ko Ya d’inma babu.”
“Bansani ba ai dana basa budurcina na gommaci na baiwa mahaukaci akan hanya.”
“Haka kika ce?”
“Eh mana.”
“Amman tsaya jiya kinsha maganin da Mama tabani na baki?”
“‘Yar iska daman kinsan abinda maganin zemin kenan kika k’i gayamun? Wallahi jiya da k’yar na samu nayi bacci.” Dariya Lubiee tasa “kinshan ne kuma shine kikeson nayi believing kan ba abinda ya shiga tsakaninki da Al’ameen?”
“Wallahi babu pillow nad’au na tare kaina.” Nanma wani dariyan Lubiee tasa “wallahi ‘yar iska ce ke.”
“Niba abinda ke damuna ba kenan ya zancen Very Own fah? Line nasan ya soma shiga?”
“A’a wallahi Babe.”
“Oh no! Na shiga uku.”
“Babe gomma tun wuri kin miyar da hankalinki kan aurenki kina jina ko?” Nasiha Lubiee ta shiga yima Zeezee wanda tana cikin yi Zeezee ta katse wayar abinta. D’akinsu ta koma ta tarar dashi yana shafa mai, la6ewa tayi bakin k’ofa tana kallon yadda muscles nasa suke moving in sync in yana shafa man haka kawai take depriving pleasure from staring at his naked body. Ta mirror Al’ameen ya ganta, murmushi kawai ya saki ya cigaba da abinda yake chan yayi clearing throat nasa “My Princess ki shigo mana.” Kunya taji sosai sannan ta fito daga la6en “nifa ba kallonka nake ba k’ofan ne ya kama min kayana naga kana wani murmushi.”
“Toh ai bance kallo na daman kike ba, inma kallon nawa kike ai ba damuwa tunda am all yours.”
“Kai kaji wajen kuma wai kai haka muryanka yake ne kokuwa iyayi ke saka magana haka?” Dariya sosai ya tsaya yi in which Zeezee find him cute “meh muryan nawa ya miki kuma?”
“Bayamin dad’i.”
“Nikuma naki na min dad’i sosai My Princess. ”
“Sau nawa zan gaya maka kadena cemin My Princess? I am not yours I belong to Adeel kuma ka sa kaya banason ganin na miji other than my Adeel ba kaya, sannan kuma kasa wad’ancan useless guards nakan da suke waje su kaini gida inason inje inga Mama.”
“Toh dama Amarya tana fita unguwa ne?”
“Wai kai baya damunka ne idan na kira sunan Adeel da baza kayi zuciya ba kace zaka sakeni?”
“Mesa ze damen Zainab? Duk wanin da kikeso nima dole in sosa ai.”
“Seka tayi ai wallahi da kanka zaka gaji ka sakeni, kuma ba amarya ceni ba cause as far as am concerned banida aure.” Ignoring what she said yace, “kibari ko zuwa next week ne seki fara fita kinji? Yi hak’uri.”
“Har next week?” Tahau tsiwa, “mezan tsaya yi a wannan gidan naka har zuwa next week? In ganinka da wad’ancan useless guards d’inne na gaji dayi, wallahi ka kaini gida” tasa mai kuka. Kai kawai ya kad’a “naji toh bar kukan shirya driver yayi dropping naki nima zan d’an fita dama.” Tana share hawayenta tace, “da yafi ma kam.” Wardrobe nata ta nufa ta ciro mayafinta tare da nannad’esa a one side of her shoulder yadda ‘yan mata keyi bayan ita gata matar aure. Al’ameen na gama shiri ya kalleta “mu tafi ko?”
Miqewa tayi tare da jan wayanta “wait haka zaki fita Zainab?” yayi maganan a hankali.
“Ni wallahi muryankan nan...” ta zumburo baki “kuma da ya kakeson in fitan?”
“Ki rufe jikinki da gyalen mana Zeezee na, bakiga duk gidan maza bane?” Kishin Soja ya k’osa!
“Toh ni nace ka d’ibo gang of soldiers ka tarasu a gidanka ne? In kaga bakason kaga matar ka tana fita haka is simple seka sakeni daman niba san auren nake ba.”
“Yi hak’uri ki gyara kinji? Yi hak’uri bakisan beautiful things are left covered ba? You are too beautiful to expose your body like this” ya k’are maganan some inches away from her. Shiru tayi tana kallonsa, hannunsa ya miqa a nitse ya d’ago gyalen daga kan kafad’arta tare da bud’ewa ya yafa mata shi me kyau sekace mace. Juyata yayi yadda take kallon kanta a mirror “bakiga kinfi kyau haka ba?”
“Ni ka sakeni toh” taja jikinta. Murmushi ya saki sannan yace mata “lets go” ganin ya shiga tafiya ta sake bud’e gyalen sannan tabi bayansa. Soldiers d’in suna ganinsu suka hau saluting nasu wani dirty look Zeezee tashiga binsu dashi ita haushi ma suke bata yadda sukeyi ma Al’ameen sekace wani god, mschw! D’aya daga cikin prados na gidan d’ayan soldiers d’in ya bud’e mata tana shiga Al’ameen ma yashiga aka rufe sannan suka fice.
Not long enough suka isa gidansu Zeezee. Nan soldiers na d’ayan motan suka fito tare da jeruwa ta side na Zeezee d’aya daga ciki ya bud’e mata. Tazo fita Al’ameen ya rik’o hannunta “ki gaishe da mutanan gida kinji? Da La’asr zanzo in d’aukeki.” Kaman bazata amsa ba ta gyad’a kai tare da ficewa. Mama na zaune tsakar gida ita da Omar Zeezee ta shigo.
“Amaryar! Lafiya dai ko?” Mama tayi exclaiming. K’arisowa tayi tare da gaishesu “baki amsani ba lafiya?”
“Lafiya mana Ya Al’ameen ze fita ne shine nace yayi dropping d’ina nan gida tunda ba abinda zanyi and yace yana gaisheki ma.”
“Kaman ya ba abinda zakiyi Zeezee girkin rana fah?”
“Nace zanyi yace no need ya d’aukemin girki wai.”
“Abun nema ya samu ba, dama ba son girkin ake ba.”
“Uhm ina Baba?”
“Ya fita kasuwa” cewar Omar.
“Ohh ni zan wuce d’akina.” Kallonta kawai Mama ke har seda ta fice “uhm su Zeezee amarya.” Omar na murmushi yace, “kede bari kawai Mama Allah sa de auren yasa tayi hankali.”
“Ameen Omar ya ko ka fasa fitan ne?”
“Eh zan koma d’akina kawai.”
****
Yini Zeezee tayi tana trying line na Adeel da Lubiee ta turo mata sede sam bayi shiga. Gabad’aya ta rasa ina zata sa kanta se bayan La’asr Al’ameen yazo d’aukanta har anan ma Baba be dawo ba, d’aya daga cikin guards nasa ya tura yayi ma Zeezee magana kaman karta bisu takeji amman dolenta taje kada Mama tayi suspecting wani abu. Sunyi sallama da Mama ta fice koda ta shiga motan bata ce da Al’ameen ko k’ala ba shine ma yace mata sannu nanma banza dashi tayi. Dagangan dan neman magana ta bud’e wayarta ta ajiye a tsakiyansu yadda Al’ameen na lek’awa yaga pic na saurayi kan wallpaper’n nata wanda he is sure shine Adeel d’in. Kallonsa Zeezee ke a yayinda yake kallon pic na Adeel a zatonta ma zeyi magana segani kawai tayi ya kawar da kansa daga direction d’in, hakan ba k’aramin haushi ke bata ba, shikenan shi ba aikinsa se ignoring nata? Mschww tafison suyi ta yinta har seya saketa tukun, bata da burin dayafi wannan.
★*★*★*★
Ahaka fa har Al’ameen da Zeezee suka samu sati biyu da aure. Ba abinda ya ta6a shiga tsakaninsu saboda ko gwada ta6ata bayi yi idan sun kwanta. Cikin sati biyun nan Zeezee bata ta6a d’aga tsintsiya ba da sunan shara banda rashin kunya da yarinta ba abinda take na Al’ameen, shikuwa duk abinda take mai overlooking kawai yake saboda uzurin yarinta dayake mata for sure yasan da tasan ciwon kanta bazata na hakan ba. Har a yau Zeezee bata ta6a hura wuta ba, breakfast, lunch and dinner kullum siyo musu yake randa yace sufita suci ma gar da gar setace mai ita batason aganta da tsoho. Rashin kunya kwando-kwando Al’ameen ke sha.
Yau Sunday Al’ameen ze koma aiki Abj leave nasa ya k’are. Zeezee dad’i kasheta finally zata samu tafita yawo abinta. Koda Al’ameen keta had’a akwatinsa batayi yunk’urin tayasa ba as she is busy playing game a wayanta har a yau kuwa kullum setayi trying numban Adeel sede ko so d’aya be ta6a shiga ba. 1:30pm Al’ameen yagama shiri da trolley’nsa rik’e a hannunsa ya kalli Zeezee da tayi banza dashi “My Princess ni zan wuce toh ga pocket money naki nan incase need yayi arising bana nan tho duk wani abinda zaki buk’ata ma na riga na tanadar miki, anytime you’re hungry na bar miki two of my men they’ll be at your service.” Wayar nata ta ajiye ta nufi gabansa tare da d’ago bundle na d’ari biyar daya ajiye matan. “Yanzu zakayi tafiya shine d’an wannan zaka ajiye min? Nasan shekaru nawa zakayi a Abujan? Wallahi bazan yarda ba ka k’aramin kokuwa k’afanka k’afana, taya agida Baba be barni da yunwa ba kai kace zakayi hakan?”
“Yanzu wannan ya kasa Zainab?” Ya tambayeta suprisingly yana murmushi.
“Seka tambaya ne? Ya kasa mana me ‘yar dubu hamsin da ina iya kashewa a minti biyar zata min?”
“Nawa kikeso toh?”
“Double mana” ta amsa a takaice. Be sake cewa komi ba ya k’ara mata wani bundle d’in “shikenan?”
“Eh kuma se yaushe zaka dawo dan ba zaka ajiyeni a wannan k’aton gidan naka ni kad’ai ba wallahi kai kaje chan kana mu’amala da mutane kabarni da wasu sojojinka nan.”
“Shiyasa nace miki in kaiki chan family house a KD kika k’i.”
“Toh a dalilin me zan zauna da in-laws haka kawai abi a sawa mutum ido.”
“Uhm toh ni natafi ko?” Yi tayi kaman bata jisa ba “ba rakiya Zeezee?”
“Lallai baza kayi tafiyan ba kenan inhar ni kake jira nama rakiya” ta kai da juyawa ya rik’o hannunta tare da pecking forehead nata “I love you My Peincess” freezing Zeezee tati a wajen sabida wani sparks da takeji suna tashi a jikinta, peck na Adeel be ta6a sata feeling haka ba. Kasa cewa komi tayi daya gano hakan se kawai ya mata murmushi ya fice.
Tafi minti biyu tsaye a wajen immobile sannan tasamu ta dawo hayyacinta, hannu tasa wajen tana murzawa in an tambayeta peck nasan take gogewa. Koda Al’ameen yayi landing Zeezee bata damu ta kirasa tamai ya gajiya ba. Haka shi yazo ya kirata daga baya nanma seda ta gama jan aji sannan ta d’aga “hello My Princess?”
“Nifa bacci nakeji.”
“Har kin kwanta ne? Its just 9:20pm fa My Princess.”
“Toh mezan tsaya yi awannan gida naka?”
“Uhm toh sleep tight Beautiful, I love you.”
“Naji” nan tayi hanging. Addu’an Al’ameen a kullum bayyafin Allah ya kawo rananda al’amura zasu daidaita takaninsa da Zeezee. Lubiee Zeezee ta kira kan tazo mata yini gobe Al’ameen bai gida.
Washegari tun 8am kasancewar Lubiee tanada lecture free day ta iso gidan Zeezee. Ko breakfast batayi ba. Aikan d’ayan soldiers d’in Zeezee tayi ya siyo musu breakfast suna cikin karyawa Lubiee ta ta6e baki “amman Zeezee kin ta6a share gidan nan naki kuwa?”
“Zamansa nake da zan share mai gida? Ya saken ya auro matar da zata mai kokuwa ya kawo me aiki.”
“Oh! Zeezee fa kina jin dad’i wallahi har yau baki soma girki bakuma ko?”
“Yo da wace boyi-boyinsa da zemai girki? Karki 6ata min rai please.”
“Se ke matar Soja se yaushe ze dawo?”
“Ohonsa ni yaga dama ma kada ya sake dawowa ba nemansa nake ba.”
“Hmm ma farin sojan kike ma wannan iskanci? Ma nawa ya ajiye miki tukunnah?”
“100k ofcourse yaban 50k nak’i amsa dan dolensa ya k’are kuma inhar yakai two weeks be dawo ba seya k’aramin wani.”
“Haba! haba! Zeezee kinajin tsoron Allah mana.”
“Kanki akeji ni bud’en wayanki.” Ba musu Lubiee ta bud’e mata pictures Zeezee ta shiga gani suna karyawa, mistakenly hannunta yashiga call logs nan taga sunan Adeel gun as last person da Lubiee tayi waya dashi ayau. Kai ta d’ago tana kallon Lubiee da mamaki. “Ya da wannan kallo haka?”
“Kinzo kin samu numban Adeel d’in kuwa? Kinsan wanda ke waje na bayi shiga.”
“Ermm... Uhm...” Lubiee ta shiga kame-kame “nima har yau bamu sake waya ba.”
“Hakane? Babe k’arya kika soma min yanzu? Number’n waye wannan? Wato d’azu ma kunyi waya dashi kinsan how crazy I went looking for his number kin samu bazaki gayamun ba, kin kyauta.”
“Zeezee yanzu da da fa ba d’aya bane matar aure ce ke yanzu be dace ace da mijinki ba kina waya dawani. Its high time ki mance da Adeel saboda Adeel ya miki nisa.”
“I will never forget about Adeel I believe zamu kasance tare someday and kaman ya yamin nisa? Ba a Abj yake ba?”
“A da kenan, 4 days back ya wuce Florida achan yake yanzu kinga ko ya miki nisa just forget about him.”
*© MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣4⃣
_I *Miemiebee* want to use this medium to say a very huge *THANK YOU* to each and every single special soul that made my birthday worth it, indeed this is a birthday I will forget never. Thank you all so much for making my birthday a memorable one, I love y'all oceans and galaxies from the bottom of my heart. #OneLove❤ ™YGC!🎀_
Kai Zeezee ta shiga kad’awa “no Babe thats not true, it can’t be true, it just can’t.”
“It is Zeezee kiduba numban nasa kiga international number ne shiyasa nake son ki manta da zancen Adeel kibawa Ya Al’ameen chance.” Zeezee na dubawa ta tabbatar da hakan kuka ta shiga rusawa sosai bata d’au Adeel yad’au abin da zafi haka ba. “Wai ko kukan me kike?” Copying numban Adeel Zeezee ta shigayi ba yadda Lubiee batayi da ita ta bari ba tak’i. Se chan Maghrib Lubiee ta tafi gida bayan Zeezee ta idar da sallan Isha tayi dialing line na Adeel har ya yanke be d’aga ba kasancewar bai kusa da wayan, 2 missed calls ta masa sannan ta hak’ura.
Around 9pm yayi calling nata back and ba tare da 6ata lokaci ba ta d’aga “hello?” Cewar Adeel. Muryansa kad’ai taji ta shiga zubda hawaye “hello??” Yayi maganan a bit tensed this time around.
“Very Own...” Se kuma ta rushe da kuka.
“Zeezee?!” Yayi exclaiming sunanta cike da mamaki dakuma k’in yarda.
“Very Own its me your Zainab-” kawai ji tayi yayi hanging daman she knew this was coming. Tana hawaye ta shiga nemansa ta masa missed calls ba iyaka amman yak’i picking. Messages tayita mai sending tana had’a sa da Allah kan yayi picking. Seda tasha wuya tasamu ya d’aga ba tare da yace komi ba “thank you for picking up.”
“Why did you call? Bayan na fara mancewa dake why do you have to ruin my life again? A ina ma kika samu number na?” Daga yadda yake maganan za’a san cewa a 6ace ransa ke.
“Haba Very Own I thought you’ll be the last person to believe that I’ll ever cheat on you, kai kanka kasan yadda nake sonka kuma har rana me kamar ta yau sonka a zuciya na be ragu ba se ma de k’aruwan da yayi.”
“Really? In ma dragging d’ina into trouble kikeson yi kisani I’ll not fall into your trap ko a jinki bansan solider kike aura bane?”
“Adeel please trust me this once wallahi tallahi ban ta6a son soldier’n da aka aura min ba, kafa san komi amman kake bani wahala haka. Wannan hukuncin da ka yanke min yayi tsauri dayawa Allah kad’ai yasan the kind of hell that I went through for the past few weeks da banji muryanka ba.”
“Aww! Ma aura miki shi akayi? LOL am not dumb Zeezee, you can fool your parents amman you can’t fool me da idanu na naga pre wed naku and the way you were smiling at him said it all, you love him.”
“Adeel me kakeson nayi maka ka yarda cewa auren dole akayimin da Al’ameen? Friend na Baba ne shi, admission yafito bada jimawa ba yazo gidanmu ya ganni yace he wants to marry me and Baba gladly gave me to him.”
“Why didn’t you tell me then?”
“I didn’t want you worried Very Own but wallahi believe me I've always had the intention of telling you.”
“And meya hanaki?”
“A ranan da kayi discovering truth d’in daman naso sanar da kai se kuma kayi finding out already please believe me Adeel wallahi ba k’arya nake maka ba, ban ta6a son wani na miji kaman ka ba sonka a jini na yake, I love you morethan you can ever imagine and am ready to sacrifice anything for your love.”
“What now? An riga an miki aure and nasan kin riga kin bashi kanki theres no US again.”
“And thats where you are wrong, I’ve once promised you that my pride (budurcina) belongs to only you and har yau promise d’innan na nan, ban bawa Al’ameen kaina ba, bazan ta6a bawa wani na miji kaina ba se kai Adeel please believe me.” Dad’i sosai Adeel yaji amman ya dake;
”If you want me toh mesa baki fad’awa Baba ke kinada wanda kikeso ba in the first place kikayi agreeing to marriage d’in?”
“Adeel I tried, I really did amman Baba wouldn’t listen he even threatened me ze aura min me shago” ta k’are maganan cikin sautin kuka.
“Is okay I believe you stop crying kinji?”Wani sanyi maras misaltuwa Zeezee taji a ranta “you really do Very Own?” Tayi maganan tana share hawayenta “yes Sweetest Love, I do.” Tana murmushi wane yana gabanta tace, “thank you, thank you so much I can’t tell you just how much you mean to me.”
“So what do you plan on doing now? I don’t think we can be together anymore.”
“Sure we can Very Own just trust me.”
“How?” Ya tambayeta a takaice.
“Adeel I have a plan in mind, I won’t rest har se in Al’ameen ya gaji dani ya sakeni.”
“Are you sure Babe?”
“I am cause all I want is to be with you.”
“And I promise to take care of you till my last breathe Sweetheart, I love you so much.”
“I love you even more so are we good now? You are no more mad at me?”
“Had it been am mad at you will I tell you I Love you?”
“No kayi gaskiya” ta amsa tana murmushi, “amman yaushe zaka dawo 9ja you’re so far away from me.”
“It won’t make any difference Babe, is better I stay here in har mukayi accomplishing mission namu sena dawo right away muyi aure.”
“I can’t wait to be with you in your arms.”
“Me either” hira sosai sukata sha kan ba gobe shide Al’ameen ya rasa da wa take waya sau biyu yana trying nata at different intervals amman se ce masa ake line is busy with another call.
Cikin kwanciyan hankali Zeezee tayi bacci ranan. Wayarta dake k’ark’ashin pillonta ne ya farkar da ita daga bacci sanadin ringing da yake. Da k’yar ta samu ta ciro ganin wake kira ta ja doguwar tsuka sannan tayi picking “My Princess good morning, kinyi Sallah?” Kaman baza ta amsa ba tace, “a’a.”
“Ahh to ki tashi kiyi kinji?”
“Waikam ina ruwanka da yin Sallah na ko rashin yinsa? In kuma bana Sallan fa?”
“Uhm-uhm to am sorry take care, I lobe you” Nan ya katse wayar. Doguwar tsuka taja sannan ta koma bacci se 6am ta tashi ta idar sannan ta koma baccin.
*~ *~ *~
Tun rana me kaman na ranan Zeezee ta soma enjoying life nata. A rana seta fita yawo sau biyu zuwa uku, ga kuma koda yaushe tana kan video or voice call da Adeel, kafin ya kirata sau d’aya tayi sau biyu ko uku ita amman ko mistakenly ne bata ta6a kiran Al’ameen ba. Ahaka har yayi sati biyu da tafiya Zeezee bata ta6a d’aga tsintsinya da sunan shara ba kwatsam rana d’aya Mama tace mata gata a hanya tana zuwa ita da Mariam da kids nata nan Zeezee tayi wur-wur ta samu ta share parlour da d’akinta se kitchen da kuma dining space. Yini Mama sukayi mata ranan sosai Zeezee taji dad’in zuwansu. Bayan tafiyan Mama Zeezee ta d’au waya for the first time after their marriage ta kira Al’ameen. Mamaki sosai yasha ganin _My Princess_ na flashing akan screen d’in.
“Hello My Princess.”
“Na’am ina wuni?”
“Lafiya ya kike?”
“Am good ya aiki?”
“Alhamdulillah ya Bauchi?”
“Cool nace se yaushe zaka dawo?”
“Wow are you missing me?” Yayi maganan yana dariya. Wani haushinsa takeji amman ta danne zuciyarta “yeah sort of.”
“Shine baki ta6a kirana ba?”
“Uhm amman ai na kira yau ko?”
“And thats why I still can’t believe it!”
“Toh you better do, dama nace akwai auren friend d’ina ne da za’ayi jibi inason zuwa.”
“Is that why you called?”
“Yes”
“Toh ba matsala My Princess na baki izini.” Ita dariya ma ya bata wai ya d’au ta kirasa ne don ta tambayesa izini? Lallai kuwa yayi kad’an, ita kanta batasan sau nawa take fita unguwa ba bayan tafiyansa ba kuma tare da izinin sa ba “Toh nagode” tayi speaking finally “se kuma kud’in gudumawan da nakeson kai mata da kuma na ashobe kasan nice best friend nata.”
“Wow! Ashe farin jinin Zainab d’inan ba gun maza kad’ai neba harda mata, kece best friend ya kamata gudumawan ki yafi na kowa ko My Princess?”
“Yes Ya Al’ameen.”
“Nawa kikeson ki kai mata toh?”
“Zan d’an mata siyayya ne haka nasu dinner set da bedsheets haka.”
“Okay... Kaman nawa kike buk’ata?”
“Zan samu 50k?”
“Why not? Zan tura miki 100k seki k’ara akan pocket money naki.”
“Ba yanzu zaka dawo ba kenan?”
“Eh toh zan d’an k’ara koda two weeks ko one haka se hak’uri My Princess auren soja seda hak’uri, kinji?”
“Bakomai Ya Al’ameen” a ranta kuwa cewa take ai hakan yafi dad’i. “Toh senaji alert.”
“Yauwa My Princess take care I love you.”
“I know” ta amsa sannan ta katse. “Mschw! Ya Al’ameen ko baho? A dad’i na nide” neman contact na Lubiee ta shigayi se gashi itama tana kiranta “hello Babe yanzu fa nakeda niyyan kiranki.”
“Matar Soja! Sekuma na rigaki.”
“Toh ya kike?”
“K’alau wallahi ya preparation na bikin Hajar?”
“Gamu nan dai kud’in ashobe nason ya gagareni har 15k fa gakuma na d’inki again gana gudumawa.”
“LOL karki damu zan biya miki na ashobe dana d’inki what are BFF’s for?”
“Se Matar Soja godiya nake, kice Ya Al’ameen ya baki kud’i kenan.”
“Ba dolensa ba, 100k yace ze turon.”
“Wallahi kina jin dad’i Babe I envy you Allah bani miji kaman Ya Al’ameen nima such a gentleman.”
“Mschw! Sekiyi kuma gomma kin nitsu kin miyar da hankali kan karatun ki ehe.”
“Kefa baza kiyi ba? Ko remedials ne kiyi applying mana.”
“Haka Al’ameen ma yace nide ba abinda zanyi in turanci ne inaji na yafe karatun Baba ya riga ya ciremin interest.”
“Toh Allah kyauta.”
“ Ameen semun had’u gobe” anan sukayi sallama.
****
Zeezee sekace ba matar aure ba gun bikin Hajar, gyalen ma ajiyesa tayi a gefe se rawa suke ta takawa. Tarewa ma gabad’aya tayi zuwa gidan bikin yadda baza tayi missing d’in koda event d’aya ba. Ranan Kamu da misalin k’arfe 5pm Mama ta turo Omar kan ya kawo wa Zeezee miyan Eghusin da tayi sanin Eghusi is one of Zeezee’s favorite. Omar yaje guards suke sanar dashi ai Madam bata gida ana bikin friend nata so ta tare chan da mamakinsa ya dawo gida ya fad’awa Mama.
“Zeezeen?!” Tayi exclaining.
“Ita de, haka guards nata suka cemin.”
“Lallai yarinyan nan bata da hankali, agidan uban wa ta ta6a jin anyi haka? Bama wannan ba shin mijin nata ya bata izini ne?” D’aki ta koma ta d’au wayarta tare da kiran Zeezee, Zeezee ana ta cashewa bata ma san ina ta jefa wayar nata ba se chan bayan Maghrib prayer taga missed call na Mama nan takira ta back. Masifa Mama ta hauta dashi “ke bazaki ta6ayin hankali bako? Dan k’aniyanki kin ta6a gani na nayi wannan rashin hankali da kika tafka? Saboda Maj-Gen bayi gari seki tare zuwa gidan biki? Da izinin wa? Shi ya baki izinin?”
“Eh mana Mama seda na tambayesa ai.”
“Aww k’arya zaki yimin?”
“Mama ba k’arya bane Allah na tambayesa.”
“Kin tambayesa izinin zaki gidan biki kokuwa zaki tare gidan biki?” Shiru Zeezee tayi tana nazari. “Dake fa nake?”
“Na tambayesa yace zan iya zuwa.”
“Bari na kirasa yace min ba haka ba kiga abinda zan miki.”
“Mam-” katse wayar Mama tayi ta shiga neman Maj-Gen.
Cin faracu Zeezee ta shigayi shikenan nata ya k’are inhar Baba yaji wannan batu nata ya k’are sallama tayi da ‘yan gidan biki takira driver yazo ya d’auketa ASAP ta koma gida, gabad’aya ta kasa samun sukuni.
Around 9pm wayarta dake kan centre table a parlour ya shiga ringing, har 6ari take da take k’ok’arin duba wake kiran, ganin Maj-Gen akai ta sauk’e ajiyar zuciya “thanks Gee ba Baba bane” ta furta tare da picking “Ya Al’ameen ina wuni?”
“Lafiya Zainab, ya hidiman biki?”
“Alhamdulullah gobe ma za’a d’aura aure.”
“Allah bada zaman lafiya toh.”
“Ameen.”
“Why did you do it?”
“Menayi Ya Al’ameen?” Binsa take a hankali karya tona mata asiri gun Baba.
“Lets not play games why did you do it?”
“Ya Al’ameen am sorry dan Allah kayi hak’uri karka fad’awa Baba wallahi dukana zeyi.”
“Kinsan kinyi ba dai-dai ba kenan.”
“Eh nasani wallahi sharrin shed’an ne it’ll never happen again Mama ta kiraka d’azu?”
“Yes she did.”
“And meka ce mata? Baka bani izini ba?”
“Eh.”
“Haba mana Ya Al’ameen kafasan dole zata fad’awa Baba.”
“Am kidding ban fad’a mata ba.”
“Amman nagode plenty phew!”
“It shouldn’t repeat itself again okay? Nan gaba duk inda zakije let me know its for your own safety kinji?”
“Naji” tayi maganan tana murgud’a baki. “Seda safe.”
“Kina ina ne yanzu? Gida?”
“Eh na dawo.”
“Tam sleep safe and sound, I love you.” Yana katse wayar ta sake sauk’e ajiyar zuciya atleast she’s save now.
Washegari bayan Zeezee ta dawo daga wuni ta kira Al’ameen a waya kaman dagaske tana hawaye sosai. “Subhanallah Zainab whats wrong?” Kukan take har yanzu takasa amsawa “Zainab are you there? Speak up please.”
“Ya Al’ameen...” Se kuma ta sake sa wani kukan.
“Zainab where are you right now?”
“Gida.”
“Alhamdulillah! Tell me meya faru? Mesa kike kuka?”
“Ya Al’ameen dan Allah kayi hak’uri wallahi ba dagangan nayi ba.”
“Yi meh? Calm down and tell me kinji? Don’t worry.”
“Ya Al’ameen a gidan biki ne yau...”
“Ehem ina jinki.” gabad’aya tasa hankalinsa ya tashi matuk’a.
“A gidan biki yau aka sace min white gold d’ina both d’ankunne da sark’a wallahi bawai carelessness nayi ba.” Shi dariya ma tabasa “subhanallah amman yanzu dan an sace miki gold naki kike wannan kukan Zainab?”
“You are not mad at me?”
“Why shall I? Qaddara baya wuce ranansa haka Allah ya qaddara za’a sace miki.”
“Na d’au fa zakamin masifa, na ajiye zan yi alwala kafin na fito an d’auke am sorry please.”
“Stop apologising kinji? In zan dawo in shaa Allah zan taho miki da wani sabo don’t worry.”
“Dagaske Ya Al’ameen?”
“Sosai My Princess your happiness means the world to me.”
“Thank you so much Allah dawo dakai lafiya” kaman dagske ranan suka sha hira sosai se chan tace mai tana jin bacci, suna sallama ta 6arke dawani dariyan shegantaka, wajen bag hanger ta nufi tare da zaro case na d’ankunnenta se kawai ga white gold nata complete aciki meaning ba satan da aka mata duk plan ta had’a don ta damfaresa. “Bari na 6oye wannan yanzu kafin yagani ya fasa sai min sabo ai wallahi seka tsiyaye inde ni ne don kanka zaka gaji ka sakeni.” Tace da kanta sannan ta bud’e kit nata tasa ciki ta rufe da key.
*~ *~ *~*
One week 3 days Maj-Gen ya k’ara sannan ya kira Zeezee musamman yace mata ze dawo yau. Mutumiyar ko a bakin zaninta yau mijinta ze dawo daga tafiya, ba shara ba mopping bale ayi maganan girki. Wankanta kawai tasha tasa wata shegiyar fiited electric blue lace gown nata me black torches. Sosai tayi kyau dake kayan yad’an bayyano da cleavage nata, video taping kanta tai tayi tana sending wa Adeel. 3:47pm Al’ameen ya shigo gida alokacin Zeezee na zaune a parlour akan kujera se chatting da Adeel take. Koda taga Al’ameen bata cemai komi ba se cigaba da chatting nata take kai kawai ya kad’a ya k’ariso cikin parlourn ya zaua gefenta yana k’are mata kallo a yayinda so da sha’awanta ke building a jikinsa. “My Princess am home.”
“I know” ta basa takaicaccen amsa.
“Kinyi kyau sosai My Princess.”
“Nasani ba seka fad’a ba.”
“Toh kina hutawa ne haka?”
“Ni ka dawo da suratan nan naka ko da wannan muryan naka, baka ga ko sannu da zuwa ban maka bane ai kamata yayi kaima kayi zuciya karka min magana.”
“Ashe baki min sannu da zuwa ba!”
“Lallai ma! Wato baka ma san banyi maka sannu da zuwa ba?”
“Toh irin wannan shan kyan da kikayin ai gabad’aya ya tafiyar min da hankali.”
“Suit you well.”
“Bari na watsa ruwa toh” yana kaiwa nan ya fice doguwar tsuka ta bisa dashi. Not long enough ya fito da white towel d’aure a waist nasa d’aya kuma ya ya6a a wuyansa yana goga gashin kansa dashi kaman ance Zeezee d’ago kanki ta tsaya tana kallonsa jaw dropped wide open. Theres no more denying Al’ameen is hot itama ta amince da hakan yanzu, kasa dena kallonsa tayi kawai ji tayi yaja dogon hancinta. Da wuri ta kyafta ido. “Kallon beyi yawa ba My Princess?”
“Nifa ba kallonka nake ba, I mean yes ina kallonka amman hankali na ba’a kanka yake ba tunanin Adeel d’ina nake.”
“Hakane? Toh ina lunch d’ina? Am hungry.”
“Lunch ba a baku snacks bane a jirgin? Danni ba abinda na girka.”
“But I told you I was coming.”
“Meaning? Dan zakazo sena hau shiga kitchen? Lallai fah Soja dagaske kake.”
“I don’t mean kiyi girki but atleast ki tura koda guards ne su siyomin lunch am your husband Zainab.”
“Toh banyi ba inji bugi da duka, nifa surutu ne banaso, ina zaman zaman na qalau ka dawo zaka fara cikani da surutu, ai dama na gaya maka you must regret marrying me gwara tun yanzu da kake da dama kayi whats right ka sakeni aikin banza kawai” tana kaiwa nan ta nufi d’akinta. Binta kawai yayi da kallo sannan ya aika d’aya daga cikin guards nasa ya siyo mishi lunch ya samu ya kora yunwa.
Koda Maghrib yayi shi kad’ansa yayi Sallansa sabida yasan there is no point yace mata suyi tare don bayi zatai ba. Tana zaune a parlour tana kallo ya shigo ko d’aga kai ta kallesa batai ba leda ya ajiye mata kan centre table nanma bata ce komi ba “open it, its all yours.”
“Me aciki?” Tayi maganan cike da rashin kunya.
“Kede bud’e mana yi hak’uri.” Kaman bazata bud’e ba ta miqa hannu ta bud’e ganin white gold d’an kunne, sarqa harda zobe tayi ciki wanda yafi nadan tan ma girma da kyau. “Wow! Nawane wannan?”
“Naki ne Zainab ba an sace miki d’ayan ba?”
“Wow! Thank you Ya Al’ameen.” Shide yagane Zeezee yanzu idan yanason suna shiri yana suprising nata da gifts. “You’re welcome My Princess ko kinason zuwa shopping gobe ba inda zani se muje.”
“Dagaske?”
“Sure Dear.”
“I’ll have to think about it.”
“Toh My Princess ina mijinki ma sekin jamin aji? Anyways thank you for liking the gift ni zan kwanta.”
“Toh seda safe.” Kallo ta cigaba dayi seda ta k’are series d’in sannan taje ta canza zuwa night gown ta kwanta gefensa daga chan nesa, sede me? Ta fara bacci sama-sama taji Al’ameen ya matso da pillonsa kusa da nata, batace dashi komi ba seda taji furry hand na Al’ameen zagaye akan cikinta wani electric shock taji na bin jikinta, ba kad’an ba every single touch na Al’ameen yake affecting nata. “Meh haka Ya Al’ameen? Ka d’agani mana.”
*MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣5⃣
_Get well soon *AUNTY SIS* wishing you a jet recovery, ILY. I solemnly dedicate this page to you alone *Queen Beelqees* you’re such a great fan and an amazing sister, ILY._
“My Princess until when zaki bani hak’k’i na? Bakiya tausayi nane?”
“Kaman ya hak’k’in ka nifa bansan me kake magana akai ba kabar ni kurum bacci nakeji.”
“Nikuma hak’k’i na nakeso My Princess, bakiya tausaya min neh? Yaufa watan mu d’aya da aure ban ta6a nema ba se yau yi hak’uri kinji?”
“Ai nice abar tausayi ba kai ba dan Allah kayi hak’uri wallahi ba ‘yar iska ceba ni.”
“My Princess kaman ya iskanci kuma? We are a couple fah.”
“Ni wallahi banaso, ba tarbiyyan da Baba yaban ba kenan.” Dariya sosai tabasa da k’yar ya danne dariyan yace, “toh aina akace miki yin hakan iskanci ne?”
“Ni de wallahi banaso dan Allah kayi hak’uri.”
“Toh My Princess naji I’ll go easy on you.”
“Ai wallahi k’arya ne nasan halin soldiers ni dan Allah karka min wani abun, na tuna ma wallahi bana Sallah ina kan period d’ina.” This time around kam seda yayi dariya, “d’azu fa kikayi sallah My Princess.”
“Bb.. Bayan Sallan ne yazo Allah ba k’arya nake maka ba” Ignoring what she said ya ja hannunta seda ta fad’a jikinsa, hugging nata yayi gagam wane za’a k’wace masa ita, ihu da kuka Zeezee ta shiga rusawa tsakaninta da Allah badan komi ba kuma don wai tayi promising wa Adeel pride nata. “Ya Al’ameen dan Allah kayi hak’uri wallahi na tuba bazan sake ba” riganta ya shiga raba ta dashi nan ta k’ara volume na kukan nata “wayyo Allah! na nashiga uku dan Allah ka rufa min asiri wallahi bazan sake ba.” Shima Al’ameen baida niyyan mata komi kawai so yake yayi mata horo ko halan zata d’an rage yimai rashin kunya. Yi yayi tamkar baya jinta seda ya rabata da kayanta gashi daman shi kad’ai ne a jikinta nan ta shiga kare k’irjinta tana kuka sosai har wani sama-sama nishinta take. “Ya Al’ameen wallahi bazan sake maka rashin kunya ba kace sekayi abinda kakeso wallahi gawana za’a cire gobe a gidan nan. Ka tausaywa min yarinya ceni wallahi bansan komi ba.”
Dariyansa ya danne da k’yar, “baki sanin ba yasa nakeson na koya miki yau ai, I’ll go easy on you.”
“Wallahi banason sani ka rufa min asiri don Allah.” sam be saurareta ba ya shiga sarrafata iya son ransa danko da hannu d’aya ya iya ya danneta. Ihu tasa “Mamana na mutu yau! wallahi Ya Al’ameen bazan sake maka rashin kunya ba kaji na rantse dan Allah ka rufa min asiri ka dena.” daman ya take k’arewa da slight touch nasa bale yau da yake mata uwa uba. Kukan ga cigaba dayi amman Al’ameen be saurareta ba seda ya kashe mata jiki lik’is yazamo jan numfashi kawai take sannan ya tambayeta;
“Are you sure bazaki sakemin rashin kunya ba?” da wuri sekace me jiran tambayan ta amsa;
“I am pretty sure, na sake kamin duk abinda kaga ya dace bale ma bazan sake ba.” Se anan ya saketa da wuri taja riganta ta miyar tana share hawayenta. Gani yayi ta d’au pillonta tana neman barin kan gadon. “My Princess ina kuma zakije?” A farko tayi niyyan sharesa remembering ze iya tarke ta yamata abinda take tsoro tace, “zan kwana a k’asa.”
“Mesa?”
“Babu kuma dan Allah karka hanani.”
“LOL zo ki kwanta nan ba abinda zan miki.”
“Wallahi k’arya ne ni kabarni in kwana acan d’in kawai.”
“Ko ki hauro mu kwanta kona biki har k’asan na miki.”
“A’a dan Allah kayi hak’uri” gabad’aya ta gama tsorata da kalan abinda Al’ameen yayi mata sede theres no denying she enjoyed every part of it. Ranan bakin yin rashin kunyan ma babu.
“Kizo mu kwanta kinji? Ba abinda zan miki.”
“Ya Al’ameen ka rantse ba abinda zaka min wallahi yarinya ceni ka rufa min asiri.”
“I swear bazan miki komi ba.” Se anan ta koma gadon ta kwanta daga chan nesa gabad’aya ranan ta kasa bacci seji take kaman ze danne ta yayi mata wani abun, ina ita ina soja?!
****
Da wajajen 11am Zeezee da Al’ameen suka shirya tsaf zuwa Jifatu Store siyayya kaman ba gobe Zeezee tayi, sauran abubuwan ma ita kanta batasan me zatayi dasu ba amman dan ta raba Al’ameen da kud’insa tayita d’iba duk haushinsa takeji da abinda yayi mata jiya inda kuma yaci nasara akanta fah? Mezata cewa Very Own? Koda suka isa gida fitowa tayi daga motan ta nufi ciki, guards nasa yasa suka fiffito masu da kayakin. Miqe kan gado tana sanye da vest da skirt na lace da ta fita dashin ya tarar da ita “My Princess lunch fah are you not hungry?”
“Toh ka siyo mana ne kaga banci ba?”
“Ni se yaushe zanci girkin Princess d’ina? Naki nakeso ba na waje ba.”
“Lallai ko zaka bushe, kaga na farko ni ban iya girki ba na biyu koda na iya ma bazan ba, so tun wuri gwara kayi whats right, ko ka sakeni ka kawo wacce zata na maka kokuwa kaje ka siyo mana.” Ba tare da yace da ita komi ba ya aika one of his men, daya dawo seya zauna a parlour. Zeezee kuwa seta d’au ko ya fita ne nan ta bud’o kit nata tare da ciro old white gold nata ta ajiye sa kan gado. Kwatsam! Taji shigowan Al’ameen ba notice kafin tace zata b’oye har ya gani. Kallon gold d’in yayi sannan back to her wanda tuni ta sunkuyar da kanta, murmushi kawai ya saki tare da kad’a kai. “Toh ki adana mana My Princess kafin ya 6ata kinji?” Cike da kunya ta gyad’a kai ita wai wani irin mutum ne Al’ameen? _Kode be gane cewa tsohon gold nawan bane?_ Ya gane mana wata zuciyar tace mata. _Toh mesa bemin masifa ko magana akai ba?_ Sabida halinsa ne hakan ignoring duk wani rashin hankalin da kike mai ko kin manta me Lubiee tace miki ne? Duk abinda kike yanzu zena kallonsa ne a matsayin yarinta, zuciyar ta sake amsata.
Kai ta kad’a da wuri “chan maka” ta furta a hankali. Bako kunya ta d’au gold d’in ta miyar cikin kit nata. Abinci na isowa kuwa ita ta fara bud’ewa ta hau ci. Bayan tacinye naman dake kan nata ta bud’e take away na Al’ameen ta cinye naman nasa shima.
Yana fitowa daga bayi ya nufi dining space tare da bud’e nasa gani yayi ba nama akai. “My Princess haka suka kawo abincin ba nama akai?”
“Ni na cinye dan na yau nama uku ne kacal akai nikuma in banci biyar zuwa sama ba bana jin dad’i” tana kaiwa nan tabar masa dining table d’in. Kamar yadda ya saba ignoring nata yayi ma yau sannan a hankali ya cinye abincinsa.
Da yamma da yunwa ya korata ta shiga kitchen tana tunanin mezata dafa. Fridge ta bud’e ta ciro froze chicken tasa a ruwa bayan k’ank’aran jiki ya tafi ta d’ago wuk’a zata yanka sede sam bata san how ba, cinya kad’ai tasamu ta cire sauran duk yankan ganin damanta tayi. Tagama ta tafasa kamar yadda taga Mama nayi nanma ta manta batasa albasa dan kora mata k’arni ba. Yana tafasa ta shiga soyawa anan tayita k’ona kanta, bayan nan ta dafa indomie sannan ta nufi dining tahau ci. Dai-dai nan Al’ameen ke dawowa ciki daga training men nasa “humm! me Princess ta girka mana haka?” Yayi maganan yana k’arisowa inda take.
“Abincin yara na girka.”
“Manya basuwa cin indomie koh Princess?”
“Nide ban ta6a ganin Baba yaci ba.”
“Toh nida Baba waye babba?”
“Ai duk kanwan ja ce, me marabar dambe da fad’a?” yana dariya yace “to aci lafiya” ya juya ze tafi kenan idanunsa sukayi tozali da k’uran da farin kayansa ya d’iba wanda he’s sure jikin dining chair d’in ya kwasa. “Princess kin ta6a dusting kujerun nan kuwa?”
“Meka ga?” Kayan nasa ya nuna mata. “Toh dama aiki na ne yin dusting? Ai wallahi kamar yadda na gaya maka zan sake nanata ma yanzu ba tsaftace maka gidan da zanyi inkaga bakason zama cikin dotti seka sallameni nakoma gun saurayi na aikin banza kawai ni kayi ka koma Abujan ma ko zan samu iska.”
“Allah kaimu tonight” yace kad’ai da ita sannan ya fice. Jin haka kad’ai seda yasa ta saki fitsari a panties nata. Koda dare yayi yau hijabi babba me hannu ta 6urma sannan ta d’au pillonta ta nufi kan couch dake d’akin ta kwanta tare da lullu6e kanta. Not long enough Al’ameen ya fito daga bayi sanye da towel. Tana ganinsa taja bargon ta rufe fuskanta dashi, batason ganinsa ba kaya saboda hakan ba k’aramin affecting nata yake ba.
Cikin nitsuwa yagama kimtsa kansa sannan ya nufi inda taken nan tahau shaking kafin yace ze yaye bargon ta mik’e zaune “Ya Al’ameen dan Allah kayi hak’uri karka min wani abin na tuba wallahi.”
“Bani kikeyi wa rashin kunya ba d’azu? Ai yau ba abinda ze hanani amsan hak’k’i na.”
“Wayyo Allah Mama na! wallahi kace zaka kar6a kana iya kaini lahira ba shiri ka tausayamin wallahi yarinya ceni.”
“Ai ke kikace idan kika sake min rashin kunya namiki duk abinda ya dace wannan hukuncin ne kuma ya dace ga duk wani me yima soldier rashin kunya.”
“Kuma nace kayi hak’uri bazan sake ba.” Ignoring nata yayi yashiga neman kwaye mata hijabin, nannad’esa tayi gam a jikinta tana mai kuka tana had’a sa da Allah “gobe in kika sake namiki meh?”
“Kamin duk abinda kaga ya dace amman banda wannan dan Allah bale ma bazan sake ba.”
“Naji toh tashi muje mu kwanta.”
“Baza kamin komi ba?”
“In kika sake tambayana sena miki.”
“Toh nayi shiru muje mu kwantan.” Pillon nata ta d’aga tabi bayansa suka kwanta sannan ya kashe musu wuta.
*~ *~ *~
Life moved on, rashin kunya de na yau daban na gobe daban duk yadda Al’ameen yayi don daidaita tsakaninsa da Zeezee abin ya gagara. The only way is ya bud’e mata ido ya fara discpline nata tunda dama ya karanci matsoraciya ce, kurun baki ne kawai da ita bayan nan kuma na k’arfi da yaji ya amshi hak’k’insa anan ne zata soma ganin girmansa amman dake kullum sede yayi warning nata shiyasa take abinda taga dama amman meh? Shi bayison hakan bayason yayi taking nata da k’arfi yafison inma abu ze shiga tsakaninsu yazamo da concent nata ne sabida he values her alot duk wani abinda ze ta6a ta bayaso. All he knows for sure is he’ll never rest trying to make her happy se har rananda tayi accepting nasa as mijinta tunda dama time heals.
The only time suke shiri da Zeezee shine in ya siya mata abun daya burgeta anan kam zesha fara’a kaman ba gobe. Tun dawowansa kuwa yau kusan sati uku kenan Zeezee kullum cikin yimai wak’an ya koma Abuja take saboda tasamu tayi waya da Adeel nata. Ana sauran sati ya koma Abj bayan ya dawo daga training men nasa ya tsinci Zeezee zaune kan dressing mirror da wani nickers iya saman cinyarta da kuma vest ajikinta tana trying on lipsticks data siyo ran chan. Se aukin zama da k’ananun kaya tabi ta tada mishi sha’awa dazaran yace ze neme ta kuma tak’i. “My Princess tashi ki shirya zamu fita.”
“Kai kam ko maye albarka wallahi wai shin yaushe ne zakayi sticking it to your head that I don’t love you Adeel nakeso? Ina kuma zamuje ni gaskiya banason yawo da tsoho.”
“Yi hak’uri kinji?” ya fad’a cikin omg voice nasa.
“Ina zamuje ka fad’amin.”
“Its a suprise.”
“Sekuma Allah yayi banson suprises so save it.”
“Zakije kiyi passport ne.”
“Nameh? Haka kawai ana zaman k’alau sena hau yin passport? Thank God ba mahaukaciya ceni ba.”
“Trust me kinji? Ko bakiya son kije aikin Hajj this year?”
“Hajj!” Tayi exclaiming tare da miqewa tsaye.
“Sosai ma next week zan koma aiki and zanyi morethan a month kinga ba amfani kiyita zaman banza anan gomma kinje kinga d’akin Allah ko?”
“Dagske kake Ya Al’ameen zaka kaini Saudi?”
“Am damn serious Princess.” Bako kunya ta hau rawa wajen tana jin dad’i kallonta kawai yake kaman doll baby. Nan da nan ta shirya suka fice inda tayi passport and other stuffs acikin sati kafin ya koma Abuja ya samu yagama mata all processes daya kamata. Zeezee de ta cika wa ‘yan gida da friends nata kunne kan zata tafi aikin Hajj. Acikin sati biyu Zeezee ta samu tafiya, d’ankaren nan an had’a list na abubuwan da za’a siya a Saudi tun kafin a isa. Mak’udan kud’i Al’ameen ya bata wanda ita kanta seda tasha mamaki.
Zeezee de ba aikinta achan Saudi se yawo anan yawo achan da d’aukan selfies. Tunda ta tafi sau biyu ta kira Al’ameen amman Adeel kam wai! 24/7 tana kan mai waya dan sokanci ma idan tana d’awafi cewa take Allah sa Al’ameen ya saketa ta auri Adeel, haka through out har suka gama aikin Hajj. Siyayya sosai Zeezee tayi wa kanta kaya sekace na siyarwa bayan data gama da kanta ta tabbata bata buk’atan wani abu ta sai wa su Baba da Mama dasu Lubiee harda ‘ya‘yen Mariam da d’an Yasmeen kayaki amman ko k’asan Makkah ne bata d’iba ba da sunan wannan na Ya Al’ameen ne.
Safe and sound Allah ya dawo dasu Zeezee gida. Washegari su Mama sukazo sukayi mata sannu da zuwa. Gifts kad’an ta basu kasancewar kayanta na kago. A ranan da kagonsu ya iso a ranan Al’ameen yamata waya kan ze dawo, shi da kansa ya biya ya amso mata akwatunan nata. Shi kansa mamakin ina Zeezee zata kai wannan kayaki yake.
Ya isa gida guards suka shiga ciki da kayaki sede yayi ta sallama Zeezee bata amsawa. D’aya daga cikin guards nasan ne ya sanar dashi kan Madam ta fita bata gida.
“Bata gida where did she go?”
“I really don’t know Sir all she told me was that she won’t take long.”
“Okay you are free to go.”
“Thank you Sir” ya fad’a tare da saluting nasa sannan ya fice, ciki Al’ameen ya koma yana mamaki irin hali na Zeezee. Ace ya sanar da ita yau ze dawo amman ta d’ibi k’afa ta fita? Bayan bata ajiye mai komi ba gakuma fita yawon da tayi, mawai da izinin waye? Toh Allah shirya masa ita. Ba Zeezee ce ta dawo gida ba se bayan Sallan Maghrib. Koda ta gansa zaune a parlour bata mai magana ba illa ma had’a ran datayi, wucesa tayi takai ga shiga d’aki ya kirata kaman bazata amsa tace, “meh kuma nayi?”
“Zoki zauna anan”yayi beckoning nata over.
“Ni gaskiya fitsari nakeji.”
“Jekiyi koma meh ki dawo ina jiranki” harara ta galla mai sannan ta k’arisa ciki chan ta tarar da akwatunanta. Sallah ta idar da wuri-wuri sannan ta shiga bud’e kayakin gabad’aya ma ta mance da kiran da Al’ameen ke mata shida kansa yagaji da jiranta ya k’ariso ciki ya tarar da ita se gwada kayaki take. “Ban kira kiba Zainab?”
“Ka kira” ta amsa ba tare ta nuna damuwa ba.
“Meya hanaki zuwa?”
“Na samu abinda yafi kiranka daraja, kai shikenan yau ka dawo zaka hau tak’ura min ni wallahi bank’i ka koma bama a gobe.”
“Zainab this should be the last time zaki sake fita baki sanar dani ba clear? Ba fata ba amman in fitanki wani abu ya sameki fah? Sede akirani acemin ga abinda ya sameki ni banida masaniya akai?” yayi maganan in a serious tone wanda be ta6a using da ita ba seyau amman dake rashin kunya yayi mata yawa ko damuwa batayi ba ta dake;
“Jimin bawan Allah? Nifa surutu ne banaso, da yini kakeso kullum inayi a gidan nan naka da bakomi aciki? Kokuwa so kake kowani fita na nakira ka na gaya maka inda zani? Lallai kuwa banida katin asara. Kaga rashin hankalin dana ke maka yayi yawa its simple kana iya sallamata daman ni tun farko ma bason auren nake ba.”
“Haka kikace?”
“Haka yake kuma ni excuse me ina gwada kaya.” Bece da ita komi ba yafice yabar gidan gabad’aya. Gwada kayakin ta cigaba dayi don kanta tagaji tabar sauran se gobe, sannam tayi sorting out tsaraban da tayi ma mutanen arzikinta. Da safe bayan ta had’a breakfast na iyaka bakinta ta fad’a bathroom tayi wanka tsaf sannan ta shirya cikin d’aya daga cikin arabian dresses data siya. Dining ta nufa ta hau karyawa da chips da omalet, tana cikinyi Al’ameen yafito shima all dressed up kamar yadda ta saba da k’in gaishesa haka ma tayi yau. “Har kin had’a breakfast ne baki jira sun kawo mana ba?”
“Inada inda zani ne shiyasa.”
“Toh yayi kyau ina nawa?”
“Ban girka ba.”
“Kaman ya baki girka ba bayan ga abinci a gabanki?”
“Eh toh na girka amman na baki na ni kad’ai in yunwa kakeji,kana iya aikan guards naka su siyo maka.” Nan da nan ta kur6e tea’n ta ta k’are breakfast ta bar mai wajen. Tsaraban su Mama ta tattara ta fito “toh ni na fita sauran kace ban tambayeka izini ba.” Bece mata komi ba ta fice achan gida ta rabawa su Omar tsarabansu, sosai Baba yaji dad’i se albarka yake ta sa mata haka Mama ma. Bayan ya kira Maj-Gen. Ya tambayesa izini kan ze iya miyar wa Zeezee da motanta, Maj-Gen yace ba damuwa Baba yad’au key’n motar ta ya bata bayan nasihan dayayi ta mata. Ita de Zeezee dad’i kasheta.
Suna zaune a d’akinta ita da Mama, Mama ta tambayeta “mijinki fah? Me kika kawo masa?”
“Da har da shine a tsaraban Mama?”
“Kaji ‘ya! Kar kisa na zageki Allah, ya biya miki kud’in Hajj gabad’aya amman kice baki kawo masa komi ba? Haba Zainab mesa kike hakane? Wannan rashin hakali dame yayi kama?”
“Nikam gaskiya hankalina beban haka ba.”
“Toh kina jina ba? Kina komawa gida ki d’au agogo da darduman da kikace zaki bawa Ya Ibraheem ki bawa Maj-Gen kinji ko bakiji ba?”
“Naji” tayi murmuring.
“Bayan nan zan d’au d’aya daga jallabiyan Babanku ki had’a duka ki kai masa sannan kuma ki basa hak’uri, ke ashe rashin hankalin kin har ya kaiga haka? Toh Allah shiryeki Zainab don nabar zaginki da yi maki baki yanzu saboda bashida fa’ida addu’a kad’ai zan miki Allah ya shiryeki.”
“Ameen ,harda jallabiyan Baba? Wallahi masu tsada ne kuma wa Baba na siyo wa.” Bige bakinta tayi “ungo naki nan da masu tsadan.”
****
Tuni Zeezee ta tura driver’nta gida. Gidansu Lubiee ta wuce da motarta sannan lastly gidan Mariam daga chan se gidanta. A parlour ta tsinci Al’ameen data shigo sannu da zuwa yayi mata sannan ta amsa sama-sama ta wuce ciki. After a while ta fito da tsaraban dole da Mama tace seta basa, a gefensa ta ajiye “gashi wai inji Mama na baka.”
“Name fah?”
“Tsaraba daga Makkah.”
“Mama ne tace kibani?”
“Eh ko baka so ne?”
“D’auki abinki My Princess karki damu nasan bawani kikayi niyyan kawowa ba, tattara kinji?”
“Aww wai bakaso? Aikuwa tafi nono fari wallahi daman agogon Ya Ibraheem ne kayan kuma na Baba, karka kar6an.” Binta yayi da kallo seda ta 6ace sannan ya kad’a kai yacigaba da kallon sports nasa.
*© MIEMIEBEE Team #‘YGC!*
www.beeeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣6⃣
_Just to let you know👌🏿 Masu karatu wai shin kun d’au ni kaina dad’i rashin kunyan da Zeezee keyima Al’ameen d’inmu yakemin neh? Kusani Mahak’urci Mawadaci, kuma me hak’uri shi kan dafa dutse yasha romo. Ita kuma Zeezee acewarku haka zan barta ne taci bulus bayan dukkanin aikin haramun datake aikatawa? Ofcourse no dole zata gir6e abinda ta shuk’a wataran. Duk wanda yayi ba dai-dai ba dole zega consequences so nomore bina private ana cemin abinda Zeezee keyiwa Al’ameen yayi yawa I know right what am doing ™YGC!💞_
_Ahh! Almost forgotten this page is honoured to *D Queen, Humairah,* and *Ummi Ayshatu* #OneLove💞_
Few days later yar Maj-Gen. wato Hajiya Sadeeyah ta mai waya kan zata zo nan Bauchi bikin ‘yar k’awarta zata kuma sauk’a a gidansa. Bayan sun k’are wayan yaje ya samu Zeezee mik’e kan gado tana chatting da Adeel tunda ba halin yin waya Maj-Gen. na gida. “My Princess” banza dashi tayi se a karo na biyu ta amsa “menayi kuma yanzu?”
“Haba Princess give me a break mana ni bansan mena miki ba kullum kike cikin 6atamin rai, in wani abun na miki lemmi know sena gyara ko ke marital life namu na miki dad’i? Kullum babu jituwa a tsakanin mu? Its hightime ki gyara ko ba haka ba?”
“In gyara? Me zan gyara? Kai babba bakace zaka daidaita komi ba seni zaka wani cemin na gyara.”
“Me zanyi toh Princess? Duk yadda nasan zanbi dan daidaita tsakaninmu nayi kink’i bada had’in kai.”
“Lallai kuwa, ka kama ka barni da outdated mota kam ai dole kace kabi anyway you know how, ni kaga ba dogon surutu nakeson yi ba, uban nawa in Allah ya sake hore mai ze canza min motar.”
“So kike a canza miki mota Princess?”
“Eh mana waye bayison sabon abu?”
“Shine kad’ai dalilin dayasa kike duk abubuwan da kike, akan mota ne kad’ai?”
“Kafa dena cewa kad’an nan Malam Soja tunda ka kasa canza min.”
Yana murmushi yace, “toh ai baki ta6a cemin na canza miki mota ba Princess.”
“Komi ne sena gaya maka? Hankali bayi gayawa mutum whats right ne?”
“Yana yi Princess toh am sorry it never blinked into my mind, za’a canza miki mota inhar shi kikeso anything for My Princess.”
“Wani iri zaka sai min toh?” Tayi maganan finally tana murmushi.
“Duk kalan wanda Princess take so za’a sai mata.”
“Dagaske Ya Al’ameen?”
“Sosai ma Princess, wani iri kikeso?”
“Kalan Ford Jeep naka 2016 d’innan nakeso.”
“Irin nawa?!” Yayi exclaiming.
“Me wani kake zaro ido ba zaka iya sai min bane? Kokuwa kaima kana sahun mazajen da suke cewa matansu basu hawa mota iri d’aya da nasu?”
“Ko d’aya Princes naga kaman wancan ya miki girma da yawa ba gara irin simple cars haka ba, inaga jeep nan ya mik’i kato kona miji ma ya ake ganinsa ciki? But inhar jeep d’in kikeso why not try out prado ko LR-3?”
“Banaso in bazaka saimin kalan naka ba shikenan dama haka kake ba abinda ka ta6a min tunda ka auroni, agida ban ta6a neman abu gun Baba na rasa ba Allah ze sak’a min ai” se ta 6arke da kuka tana Allah zeyi mata sakayya. Kallon yarintan ta kawai Al’ameen yake yana murmushi, “toh ya isa haka Ford Jeep kikeso?” Kai tayi saurin gyad’awa tana hawayen har yanzu. “Toh stop crying zan sai miki.”
“Dagaske Ya Al’ameen? Irin nakan nan fa nakeso amman fararta banason bak’ar mota.”
“Ko pink kikeso za’a sai miki stop crying I don’t want you to think bana miki komai, I’ll use the last kobo I have to make you happy.”
“Yeyy!! Nagode toh se zuwa yaushe toh zaka siyamin d’in?”
“Nan bada jimawa ba Princess, I want a favor from you also kinji?”
“Ahap ai dama nasani ba tsakani da Allah kace zaka sai min motar ba, nasani zakace yau sena baka hak’k’in kane toh inhar haka ne ka riqe motar taka tunda kai bakada tausayi ‘yar ni d’innan zaka ce zaka sa a gaba seka k’wato abinda yana iya kaini lahira.”
“Ohh Zainab! Ashe haka masu sunan naku suke? Ki kwantar da hankalinki in hak’k’i na ne na jima da yafe miki sabida banason tsinuwan mala’iku akanki se rananda kika yarda tukuna, yanzu that aside gobe Hajiya Sadeeyah tace zata zo nan Bauchi bikin ‘yar friend nata.”
“Wata Hajiya Sadeeyah tukun? Sis naka babba?”
“Eh ita kuma na mata masauk’i anan-”
“Anan?” Tayi saurin katsesa “haba kaikuwa, mesa baka barta ta sauk’a a hotel ba.”
“Haba Princess wani irin magana kike? She is my blood sister fa, ke yanzu zakiso ace in Yasmeen namu zatazo Bauchi takama hotel ne?” Kai ta kad’a da nufin a’a “toh nima ai kinga be kamata nabar Hajiya Sadeeyah bako?”
“Eh be kamata ba kam amman kaga ai in Yasmeem ce zata sauk’a anan ba girkin da zan mata komi ita zata na yiwa kanta amman incase of Hjy Sadeeyah kuma kaga fa dole sena hura wuta kuma ni ban iya ba wallahi ba abinda na iya girkawa aside from indomie da chips se dama-dama suyan kaza.”
“Duk ba matsala neba wannan Princess abinda nakeso dake shine kawai ki ajiye wannan rashin kunya da yawon na kwana biyu har seta tafi kinji?”
“Haba! Haba! Daddy kayi adalci mana, shikenan don ita se a tauyemin hak’k’i? Rashin kunya kuma in zakamin abinda nakeso ka sakeni ba wanda ze ji kanmu.”
“Its a favor am asking yi hak’uri kinji? Ko bakiya son Ford Jeep naki ne?”
“Inaso amman de-” hannunsa ya aza bisa lips nata;
“Yi hak’uri just this once.” hannun nasa ta cire;
“Naji Allah sa kar wani abin ya taso toh don gaskiya da sakel.”
“Nagode kinji Princess? I love you so much.”
“Naji toh, excuse me.” Be sake ceda ita komi ba ya yai finding way nasa out.
****
A washegari Hjy Sadeeyah ta iso, a tare Zeezee da Al’ameen sukaje suka d’aukota daga airport. Se admiring nasu take, a rayuwa batada burin da yafi taga her only brother da matarsa, hakan yasa takeson Zeezee sosai. Tin a mota se yaba Zeezee take har suka iso gida. Bayan Zeezee takai mata akwatinta d’aki ta zarce ta had’a kan dining sekace ita tayi girkin. Bada jimawa Hjy Sadeeyah tafito suka ci lunch sannan Zeezee ta tattara wajen instead tayi wanke-wanke seta jibge kayan gu d’aya kawai abinta ta dawo ciki.
Ganin Al’ameen nacan parlour da sis nasa suna hira tasa lock a d’akinsu ta hau skyping Adeel.
“Very Own.”
“Yes Sweetest love howayou?”
“Am good and you?”
“Also, is it my eyes or kin k’ara weight ne?”
“K’iba? Well maybe.” tayi maganan tana checking kanta.
“Am jealous that soldier is finally making my woman happy tunda har take k’ara weight.”
“Oh common Very Own please don’t say that kaima kasan no one will make me happy than you will.”
“Hakane?”
“Yes Baby, ya Florida?”
“As it always is, party here party there.”
“Very Own nasan kana chan kanata shafa jikin sluts d’incan ko?”
“Toh kema ba kina chan ba kinayi da mijinki ba?”
“Wallahi thats not true ko ta6ani ban bari yayi.”
“LOL am kidding you ni naki ne ke kad’ai kinji?”
“Yauwa Very Own.”
“So har yanzu be sake kinba?”
“Am still working on it, mutumin ne bansan dame zanyi describing nasa ba, komin me nayi masa baya gani yace ze d’au mataki akai he keeps on ignoring me.”
“Meaning baze iya sakin kiba kenan bale mu kasance together?” Yayi maganan haushi yana building a voice nasa.
“No Very Own calm down ba haka bane, I will never rest until ya sakeni you have my solemn words.”
“Alright Babe I trust you amman fa kiyi a hankali banason naji shima ya ta6amin lafiyarki as Baba did kinsan soldiers d’innan.”
“Don’t worry wannan I don’t think ze iya d’aga hannu ya ta6ani.” Jin motsin mutum tayi sauri tace mai “am cutting off he is here.” Da sauri ta katse sede daga yadda take raba ido ana iya gano batada gaskiya.
“Princess me kike haka?”
“Mekaga? Babu ofcourse.”
“I thought I heard you on the phone with someone.”
“Toh shikenan yanzu ko waya ban isa inayi ba? Classmate d’ina ne ya kiran ko shima zaka hanani waya dashi ne?”
“Are you sure?”
“Yoh jimin mutum kanason kaji da wa nayi waya? Da sauarayi na Adeel ne, nifa tak’ura ne banso duk ladabin danayi wa Hjy Sadeeyah baka gani ba kanason 6atamin rai shikenan ka rik’e motarka na rik’e ladabi na aikin banza kawai” tana kaiwa nan ta bar masa d’akin. Binta kawai yayi da kallo.
****
Washegari da safe Zeezee ta tashi sid’ak-sid’ak tayi wanka ta shirya tsaf ko karyawa batai ba wai seta isa gidan su Lubiee tukunnah. Motarta ta ja ta fice yawon banzan data saba.
9:20am Al’ameen ya tashi yayi wanka ya shirya, d’akin Zeezee ya wuce kasancewar ranan a nasa ya kwana, dabe ganta ciki ba se yayi tunanin ko tana kitchen ne sede da yafito ya dudduba Zeezee was nowhere to be found. This is serious! Yaushe ta fitan?
Yana juyawa yaci karo da Hjy Sadeeyah, “little bro ina kwana?”
“Ina kwana Hjy har kin tashi ne?”
“Eh kasan zuwa anjima zan fita” tayi maganan tana bin kitchen d’in da kallo, gani tayi wanke-wanke kota ina kuda suna bi. “Maj-Gen!” Tayi exclaiming.
“Me wannan nake gani haka? Karka gayamin wanke-wanken jiya ne?”
“Erm..” Ya shiga kame-kame.
“I knew it all along, ko me kakeyi a kitchen d’in kuma yanzu? Ina fatan bawai wankewa zakayi bako?”
“Oh common Hjy! Nazo d’aukan abu ne.”
“D’aukan abu ko neman matarka? Karka damu naga ficewarta d’azu.” Hannunsa ta rik’o “zo nan” a parlour suka zauna “what is going on a gidanka Maj-Gen?”
“Seriously babu Hjy itama Zainab d’in biki suke dashi shiyasa tafita yau.”
“And you expect me to believe that? Yau ma ni kake yiwa k’arya Little Bro?”
“Ba haka bane Hjy please lets drop this topic.”
“What is going? Wahala Zainab take baka shine baka sanr dani ko Mama ba? Meye amfanin family toh?”
“Gosh! Hjy enough please ba haka bane.”
“Toh yaneh? Gashi nan its written all over your face da akwai matsala, nikuma ba haka nasanka ba, abu bai ta6a damunka inba wai yakai maqora ba. Waye ne? Zainab ce?”
“Hjy I don’t know either I just can’t get her. Inason Zainab you know that.”
“I know Little Bro fiye da tsammaninka so meke faruwa?”
“Tunda aka d’aura mana aure ta canza gabad’aya, she is not the Zainab I use to know, narasa dalilin dayasa take hakan bayan ban ta6a tauye nata hak’k’inta ba, duk wani abinda takeso shi nake mata na kaita Hajj yanzu haka tace tanason na sai mata irin Ford Jeep d’ina I agree zan saya mata but I don’t get anything good from her tun abun bayi damuna ya soma. Hjy akwai wani abinda nake lacking ne as a man? Ko kuwa akwai abinda mazaje keyima matansu ne don su sosu wanda ni bansani ba baniyi mata? Let me know please.” Ya k’are maganan abin tausayi.
“Is okay kaji? Ba abinda ka rasa as a man Maj-Gen sabida haka kuma ‘yar yarinya bazata tsaya tana baka wahala ba. Adalilin me? Allah dawo da ita gida I’ll confront her myself wannan ai bayi bane.”
“No please don’t let her be time heals, eventually zata gano kuskuren yin hakan wataran please karki mata magana kinji?”
“Kamar ya kar na mata magana Al’ameen? Yarinyan da ina iya yin jika da ita ne zakace kar na mata magana bayan tanayin ba dai-dai ba? Wallahi k’arya ne. Tasan ina nan zata kama ta fita ba tare da ta tanarda min breakfast ba? Haka akeyi?”
“Nasan tayi laifi am apologising on ber behalf kiyu hak’uri please but karki mata magana kinji Big Sis?”
“Al’ameen...”
“Please for me.”
“Toh shikenan but promise me kai zaka mata.”
“I do, zan mata in shaa Allah nagode.”
“Gaskiya amman inhar bata shiryu ta shiga hankalinta ba dole a raba auren nan don ina raye bazan bari wata tasawa Brother na hawan jini ba, I can’t take it.”
“Is okay ki shiga kiyi wanka bari na aika a siyo mana breakfast.”
****
Ba Zeezee ce ta dawo gida ba se bayan Maghrib a dai-dai bakin k’ofa ta kasa kunnenta sanadin jin muryan dake tashi a parlour da tayi.
“Allah ka barni da ita senayi mata magana wannan rashin hankali har ina? Ace yarinya ta fita tun safe har yanzu bata dawo ba kuma bawai ta tambayeka izini ba?” cewar Hjy Sadeeyah a fad’ace.
“Hjy I said enough let her be please.”
“Shegiya munafuka irin kune koda kunje Makkah baku ganin Ka’abah ina ruwanki da inda naje dakuma lokacin dawowa na gida mschww.” Zeezee tayi maganan a fusace a kuma cike da rashin kunya sannan ta bud’e k’ofar, tsaye ta tarar dasu. Ba tare da tace da ko d’ayansu uffan ba ta wuce ta nufi d’akinta binta kawai Hjy Sadeeyah tayi da kallo.
“Ahakan kake cewa kar na mata magana? Matsa min tunda kai dama haka Allah ya yika da shegen hak’uri, anason mutum me hak’uri amman ba irin naka ba.” Bin gefensa tayi yana binta a baya suka shiga d’akin Zeezee alokacin harta rage kayan jikinta ta ragar da vest da short zallah, koda taga Hjy Sadeeyah batayi niyan rufe jikinta ba wayar hannunta ta cigaba da latsawa.
“In shi mijin naki ya saba ganinki haka don ni aikuma seki rufe jikin naki ko ya?”
“Toh ai ba sallama akayi ba bale nasan da mutane akai na.”
“Ke Zainab! Ki kalleni ni zaki yiwa rashin kunya? Waye sa’anki anan?” Se k’ok’arin janta baya Al’ameen yake a rayuwa inda akwai abinda ya tsana shine tashin hankali. “No ka barni da ita tasamu waje ne ai, waye sa’an ki anan?”
“Aini ba rashin kunya nayi ba akan gaskiya ta nake naga nan gidan mijina ne duk shirin dayamin zanyi amman haka kawai kizo gidana ki had’a kaina da mijina? Sanin da haka ai tun farko nace bazan zauna a family house naku ba wallahi Allah ya isa na, Allah ze sak’amin. Don kun ganni k’arama kuke d’aukan alhak’i na” tasa kuka shark’af-shark’af kaman dagaske “kimin k’aninki yamin, in kinason Allah ki had’a k’anin naki da Allah ya sakeni na koma gidan ubana nima inada gatana ai, dan ina auran k’aninki bazaki tsaya kina gayamin magana son ranki ba kice mishi ya sakeni a daren yau na koma gidan Baba na inhar kun isa ‘ya‘yen halak.”
“Enough ZAINAB!!” cewar Al’ameen a tsawace cikin wani erin kakkausar muryan da ba wanda ya ta6a saninsa dashi apart from his soldiers se yau. Ba Zeezee kad’ai ba harta Hjy Sadeeyah seda ta razana. “Hjy lets leave please let her be” da k’yar ya ja Hjy waje akwatinta ta had’a tabar gidan at that instant saboda bazata iya ganin ‘yar datayi jika da ita ba tana gaya mata magana son ranta. Zama a parlour Al’ameen yayi gabad’aya ya rasa meke masa dad’i, shin meyayi wa Zeezee take punishing nasa haka? All he did was to love her. Yafi minti talatin a parlour sannan ya miqe ya nufi d’akin nasu tana miqe akan gado ko uffan bata ce mai ba. “Tashi ki zauna Zainab.” yayi ordering nata.
“In zauna kamin meh? Ka sake cin zali na?”
“Tashi ki zauna nace” yayi maganan in a serious tone da shegen tsoronta tuni ta zauna “ki gayamin mena miki kika za6i ki wulak’anta sister na haka?”
“Ma har yanzu tambayana kake mekamin? Auro ni dakayi shine laifin daka min kuma wallahi tallahi kaji rantsuwa ba kaffara inhar bakayi gaggawar saka na ba wataran akan Mamanka ze fad’a.” Tsaye yayi wajen lost of words yana kallon Zeezee, abun nata ba yarinta bane yanzu sarai tasan abinda take dagangan kawai take. Be iya yace mata komi ba ya nufi d’akinsa inda ya kwana awajen ranan ma. Da safe ya shirya yaje yasamu Hjy gabad’aya ranta ya 6aci ko kallonsa batason yi taya ze bari ‘yar yarinya ta rainasa haka? Da girmansa. Dukda nature’nsa ne hakan hak’uri dakuma juriya amman na Zainab is too much ita tsoronta befi Zeezee tasa ma k’aninta hawan jini ba tunda be ta6a so ba se akanta. Ba yadda batai dashi ba kan ya saki Zeezee koda horata zeyi, in mata ne tanada dubun da zata yimai amman yak’i bayi jin ze iya sakanta ya lalata mata future at her very tender age ace tazama bazawara dukda de har yanzu da budurcinta take amman ba kowa bane zesan da hakan bayan nan kuma yayi believeing kan wataran komin dad’ewa Zeezee zata gano kuranta ta shiryu su fara zaman lafiya shide baze gaji da farinta mata ba har se inda k’arfinsa ya k’are.
Tun lokacin wannan incident Al’ameen ya rage shiga harkan Zeezee as yanason ya bata enough space ko hakan ze taimaka mata. D’akin nasu ma gabad’aya bar mata yayi ya koma nasa inda yake kwana ya yini ciki. Ita ko wawiyar dad’i kasheta haka zata hana kanta bacci da daddare tata waya ko video call da Adeel, atimes har abinda take cewa da Adeel Al’ameen naji amman haka duk kalan kishi irin na soldiers dayake dashi zeyi hak’uri ya danne zuciyarsa. Ana sauran sati biyu ya koma Abuja ya tahowa Zeezee da sabuwar Ford Jeep nata fara k’al 2016 cikin ledarta.
Tana miqe akan gado as always da vest da nickers ya shigo d’akinta wanda baze iya tuna when last yayi hakan ba “My Princess” yayi maganan cikin sark’ak’k’iyar muryarsa. Ita kanta tayi missing sweet voice nasa “na’am” ta amsa.
“Kizo I have a suprise for you.”
“Takardan saki na ne? Inhar bashi bane save it banaso.”
“Yi hak’uri ki fito kinji? Seda ta gama 6ata mai lokaci sannan ta mik’e “muje” tayi maganan tana mai dirty look.
“Toh kisa hijabi mana Princess kinfa san yadda gidan yake da maza kullum.”
“Toh ni nace kana kawo sune? Ai laifinka ne ga guards sannan ga ‘yan maula ni gaskiya zafi ake banajin zan iya sa hijabi.” Da kansa ya nufi wardrobe nata ya ciro hijabk ya miqa mata “yi hak’uri kisa sa” kaman bazata amsa ba sekuma ta kar6a tasa tabi bayansa suna fita kawai taga sabuwar mota na mata sallama ita kanta bazata iya descriing how motan ya birgeta ba amman dan ta k’untata mai ta dake “se yau motan ya iso? Ina key’n?” Mamaki sosai tabasa wato ko d’an godiyan da take d’anyi adan ma babu shi yanzu. “Gashi” ya miqa mata “My Princess ko motan be miki bane?”
“Me kaga?”
“Your face didn’t show and bakiyi godiya ba.”
“Daman don nayima godiya ka siyo? Ashe ba tsakani da Allah bane anyways kayi kok’ari” tana kaiwa nan takoma ciki Lubiee takira tayita mata hauka kan Maj-Gen ya sai mata Ford Jeep 2016. Lubiee de tun tana yiwa Zeezee wa’azi bataji har ya zammana yanzu kawai sede tajita ta kad’a kai saboda Zeezee batajin magana kona k’alilan.
*© MIEMIEBEE ™YGC!*
www.beeenovels.blpgspot.com
👄👄👄👄
[1/20, 9:01 PM]
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣7⃣
_Assalamu Alaikum, literally I don’t even know where to start from my family, to friends, to fans, supporters, readers and to everyone who missed either my book or me, know that I missed you guys as much and am so sorry for keeping you people in such a non ending but now ended suspense and also that I can't reply back to each and everyone of you that cared and stopped by to ask for me privately, or on the blog or in groups or even tried calling me. The messages are over Alhamdulillah I have such awesome people that care for me, nagode sosai for your maxi support, care and love I love y'all oceans and galaxies❤❤. With your prayers, Allah ya dawo dani safe and sound se muyi firing on da *™YGC*💞_
_2 days later..._
Ba inda Zeezee bata taka ba da sabuwar motarta a garin Bauchi tana bawa mutane assignment. Duk mutan arziki sun taya ta murna barin ma Baba da Mama they can’t ask for a better son-in-law than Al’ameen. They are sure ko bayan ransu ze cigaba da kula da Zeezee, nasiha again Baba yata mata amman haka baiwar Allahn nan ta ajiye mai abinsa a wajen da tazo tafiya.
_Afternoon hours..._
Kasancewar Al’ameen be ta6a jimawa haka a gari ba se wannan karan yasa mutanensa da suke Bauchi duk suka soma hallaro gidan nasa suna zuwa yimai gaisuwa. Duk yadda yayi dan kada su san yana gari abin ya gagara babban mutum kamanshi se a hankali. Suna zaune da mutanen nasa a parlour yayi excusing kansa ya shiga d’akin Zeezee alokacin ma waya da Adeel take wanda da sauri ta katse ganin Al’ameen. Kai kawai ya kad’a yace da ita, “Zainab white rice nakeson ki dafa wa bak’in danayi sekiyi slicing carrots akai dakuma peas da za’a sa akai kinji?”
“Kut! Nice zanma duka wannan aikin? Wallahi k’arya ne ni banida lafiya.” tayi maganan cike da rashin kunya.
“Ki dafa white rice shine bakida lafiya Zainab? Bance fa zakiyi stew ba, na riga nasa an siyo stew shinkafan kawai zaki dafa thats all.”
“Yo dama kace nayi stew’n mana in bakayi asaran kayan miya ba kuma ma wai su abokan naka basuda mata ne kokuwa iskanci da son sa mutum aiki ne ke hanasu zama a gidansu suci abinci se sunzo gidan mutane? Allah wadai d’in mutane kaman su wallahi mschww.”
“Ya isa haka toh wuce kije ki dafa kiyi sauri.”
“Kuma wallahi in shinkafan be dahu yadda kakeso ba don’t blame me bani nace ka kawo bak’i ba aikin banza.” Mayafinta ta taje ta fice mai, in less than one hour shinakfan ya dahu yadda Al’ameen ya buk’ata sede ruwa yaso yi mata yawa kad’an amman de tayi k’ok’ari. Ita bama haka taso ba, taso ace shinkafan yayi fate-fate yadda ko a mafarki baze sake sata dafa mai abu ba.
A food warmer ta juye ta basshi a kitchen d’in sannan ta nufi parlour inda yake zaune da mutanen nasa ta bisu da dirty look sannan tace, “Daddy kaje ga abincin bak’in naka yayi.” Da mamaki friends nasan suka juyo suna kallonta taya zata kira mijinta da Daddy? Ignoring this thought suka gaisheta kusan a tare dukansu tunda ita tak’i gaishesu. “Ba gaisuwarku nake buk’ata ba ni, inda hali daga yau karku sake zuwa gidana tunda kwad’ayin abinci ke kawo ku.” Tana kaiwa nan tayi d’akinta binta da kallo duka sukayi wide in shock sannan back to Al’ameen “kuyi hak’uri dan Allah, kuyi mata uzuri yarinya ce har yanzu.”
“Bakomai Maj-Gen Allah rufa mana asiri” cewar d’aya daga cikinsu. Haka dan kansa yaje ya d’auko wa bak’in nasa abinci sukaci bayan tafiyansu ya tara plates yakai kitchen. Banda kuda dake yawo suna bin wanke-wanke tun na shekaran jiya ba abinda ke gudana a kitchen d’in. Beso ba amman dan dolensa ya nufi d’akinta be sameta ciki ba kasancewar tana wanka zaman jiranta yayi. Kaman me haihuwa seda tayi spending numerous minutes ta fito da towel nata iyaka tsakiyan cinyarta.
“Haka kawai ba sallama seka na fad’omin d’aki inda kuma ba komi a jikina na fito fah?”
“Am sorry, in kin gama shiri kije ki rage wanke-wanken kuma its hightime ko sau d’aya ne kibi gidan nan da shara Zainab, ko ke zama cikin dottin na miki dad’i sede kiyita tsaftace jikinki amman banda na muhalli.”
“Look at who’s talking dan Allah” tayi maganan tana tafe hannu “bakason ganin gidanka da dotti fine and good kana iya saka na right now ka auro wacce zatayi maka wannan bauta. Kafa sani niba boyi-boyi bace bazaka na kawomin so called friends naka suna taramin wanke-wanke ba and expect me to be washing the dishes for you, uh-uh baka da wannan gatan Daddy.”
“Zainab mesa kike haka ne? Baki tsoron tsinuwan mala’ikun Allah ne ke? In ni ina barinki sufa bazasu barki ba.”
“Ai tsoronsun yasa nake tambayar takarda na saboda in samu wanda zan na mai bauta wanda nake so ba kai ba.”
“Naji bakiya sona but you can’t change the fact that am your husband koba haka ba? Kije kiyi wanke-wanken nace” yayi maganan this time a bit tensed.
“Bazan yiba inma zan wanke se wanda nida kai mukaci abinci akai ba wanda wad’ancan bak’in naka suka ci abinci akai ba in kanason ana maka wanke-wanke kana iya kawo me aiki.”
“Naji zan kawo me aikin amman yanzu kije ki wanke na kitchen d’in in shaa Allah zan d’auko miki me aiki.”
“Ma kanka de ba mani ba yanzu excuse me zan sa kaya.” Be sake cemata komi ba ya fice. Nan da nan tagama shiri tafito kitchen kenan taji an danna door bell tana dubawa taga Mama salati kawai tahau yi har anan Al’ameen na zaune a kan sofa be motsa ba. “Ki bud’e k’ofan mana Zainab waye ne? ”
“Mama ce nawa ya k’are!” tayi maganan hankali a tashe. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki seda dimples nasa suka lotse sosai sannan ya kad’a kai ya kawar da kansa daga kallonta. “Aww ma dariya kake min ko? Mugu kawai, mutum babba amman wai da dimples mschw” Da k’yar ta bud’e k’ofan atare ita da Al’ameen suka yima Mama sannu da zuwa. Drink da snacks ta kawo tayi serving Mama dashi.
“Ai na d’au ma ko ka koma Abujan ne Maj-Gen.” Maa tayi maganan tana cin kad’an daga cikin cin-cin dake gabanta.
“A’a wallahi se next week in shaa Allah.”
“Toh Allah ya kaimu, bazan gaji da maka godiya bafa naga sabuwar motar da ka sai wa Zeezee Allah k’ara bud’i mungode sosai.”
“Ba komai Mama an zamo d’aya ai yanzu, barin shiga ciki toh.”
“Nazo na koreka ko? Kayi zamanka de zamu shiga ni da ita.”
“A’a please kuyi zamanku anan” yana kaiwa nan ya fice. “Ke kin mai godiya kuwa daya sai miki motan?”
“Nayi mana Mama nayi sosai ma.”
“Toh ki rik’e mijinki hannu bibbiyu Zeezee aljannarki a tafin k’afafunsa yake ba a nawa ba yanzu duk lokacinda ya nemi had’a kwanciya dake karki hanasa sannan duk abinda kika san bayaso ki kiyaye wanda yakeso kuma kina mishi kina jina ko?”
“Eh Mama inayi sosai nagode.” Hira kad’an suka ta6a can Mama tace zata kai plate nata kitchen nan Zeezee ta dage atapir ita zata kai mata sanin kitchen natan bamai ganuwa bane. “Kibari mana meh haka? Bak’uwa ce ni?”
“A’a amman kibari zan kai da kaina.”
“Matsa min da Allah kaman dagaske.” ta tureta ta shiga kitchen d’in, baki kawai ta sake wide in shock tama kasa believing abinda idanunta ke gane mata. “Ke! Me wannan? Kitchen d’in mahaukaciya komeh?”
“Mama wallahi nad’anyi rashin lafiya ne kwana biyu shiyasa wanke-wanken ya taru.”
“K’arya zakiyi min? Ba two days back bane Maj-Gen ya sai miki motan kika rik’a fita yawo anyhow shine zaki cemin bakida lafiya iyyeh?” Mari lafiyayye Mama takai mata a baya. “Rashin hankalin da kikeyi agidan naki kenan ko wanke-wanke bakiyi?” K’walla na cika a idonta ta kad’a kai “wallahi a’a da Allah karki gayawa Baba wallahi ze kasheni.”
“Me ze hanani gaya mishi? Ke bazaki ta6a shiga hankalinki bako? Wannan wanke-wanke tun na yaushe?”
“Mama wallahi be jima ba kuma yau ma nakeda niyyan wankesu, MP ne ya sani gaba shiyasa.”
“Na yaushene nace? Bazaki amsa bane? Kuma wallahi kimin k’arya kiga inban kira Maj-Gen. ba na tambayesa, na yaushe ne nace?!”
“Wallahi na shekaranjiya ne.”
“Innalillahi! tun shekaran jiya? Yanzu na shekaran jiyan ne be jima ba? Ma’ana har na sati kina tarawa kenan ko?”
“Wallahi a’a Mama wannan d’inma sharrin shed’an ne” Ajiye cup d’in Mama tayi ta jawo hannun Zeezee sannan ta shiga kai mata mari kota ina, ihu Zeezee ta shiga rusawa har seda Al’ameen ya fito da mamaki yayi sauri ya k’wato Zeezee yana bawa Mama hak’uri.
Kama shirt nasa Zeezee tayi gagam tana b’oye jikinta a bayansa. “Ni zakiyi wa abin kunya iyye? Kalan tarbiyyan dana baki kenan, tunda kike kin ta6a ganin wanke-wanke ya kwana a gida na dake zaki bar har na shekaran jiya? Maj-Gen in kanayi wa Allah dan Allah ka fita kabarni da wannan maras kunyan.”
“A’a Mama dan Allah kiyi hak’uri duk beyi zafi haka ba ita kanta tanada niyyan wanke dishes d’in yau.”
“Aww ai dama nasan kai kake d’aure mata gindi, haba Maj-Gen. kai da ya kamata ka gyara mata zama se kuma ka zuba mata ido tana rashin hankali iya son ranta gaskiya am very disappointed in you. Wannan abu dame yayi kama?”
“Kiyi hak’uri Mama.”
“Ka gayamin bayan wannan wani rashin hankali kuma take again?” Shirt nasa Zeezee ta shiga tukiukuyawa tana mai nufin kar ya tozarta ta.
“Babu wannan ne kad’ai kuma shima zata gyara ko Zainab?” Tana riqe da shirt nasan ta gyad’a kai “eh eh wallahi.”
“Zan samo mata me aiki ma tana taimaka mata tunda gidan yayi girma da yawa.”
“Me aiki?” exclaimed Mama. “Wallahi bame aikin da zaka nemo ma wannan ‘yar, shara da mopping d’inne shine se an nemo mata me aiki? Da wanke wanken da befi a k’irga ba? Inhar kana k’aunan Allah kaja baya da wannan zance, ban yarda ba. Koda wasa karka d’aukan mata me aiki, kajini ko?”
“Naji Mama amman-”
“Don Allah nace Maj-Gen kai wai bakasan halin Zeezee bane? ka fara mata da haka by the time kuka zo kuka haifafa fah? Ya gidan naku ze kasance tunda yanzu da take ‘yar amaryarta ma baka barinta tayi aiki.”
“Toh Mama za’ayi kaman yadda kikace kiyi hak’uri.”
“Yauwa yanzu inason kabani waje kuma kabarni da ita kad’ai.”
“A’a Ya Al’ameen dan Allah karka fita wallahi dukana zatayi” Zeezee tayi maganan tana sake matsesa a jikinta.
“Mama please kiyi hak’uri karki ta6ata zatayi wanke-wanken.”
“Naji bazan ta6a ta ba ka fita to mu samu mu had’a kitchen d’in.”
“Ya Al’ameen wallahi kafita duka na zatayi.” Seda Mama tayi dagaske tasamu ta fito da Al’ameen. “Maza kama yin wanke-wanken wawiya kawai.” Nan da nan Zeezee ta shiga washing dishes d’in sama-sama kaman yadda ta saba ashe duk kallonta kawai Mama take, ta gama zata fara jerawa Mama tace, “dawo dawo dasu nan” cup d’aya ta d’aga ta shafa jikin se maik’o kawai malam sekace be shiga cikin ruwan kumfa ba. Lafiyayyen mari Mama ta kai mata a baya kafin tasa ihu Mama ta aza hannunta akan lips nata tana mata alaman tayi shiru. “Wallahi kika bari Maj-Gen ya fito kinji na rantse sena gayawa Babanki har nan ya biki ya baki d’ankaren duka” jin haka ta had’iye ihun nata tare da shanye hawayen nata.
“Hakane kin wanke? Bazaki bar aikin cuwa-cuwan nan da kika saba bako? Kanki ma yanzu zaki cutar tunda tun chan agida haka kikeyi.” Mama na tsaye a kanta Zeezee ta sake bin wanke-wanken seda suka fita k’al sannan ta share kitchen d’in tayi mopping ta goggoge kan counter dasu gas cooker and microwave. Bayanta kan ze 6alle, tunda tasan kanta bayan aikin wankin da Ya Ibraheem ya ta6a sata bata sake aikatuwa kaman na yau ba. “Shara fa kinayi?”
“Mama dan Allah kiyi hak’uri ki tafi gida wallahi nayi shara yau bayana yana iya 6allewa.”
“Ma’ana bakiyi kenan?”
“Zan fara gobe dan Allah kiyi hak’uri.”
“Maza d’ago tsintsiya ki bini ashe ba sharri idona suka miki ba tun shigowana na karanci gidan naku da k’ura” haka Zeezee tana tura baki tana matse k’walla tabi bayan Mama, kap gidan ranan seda Mama ta sata ta share ta kuma yi mopping harda dusting sannan tabi gidan duka da turaren wuta. Tanayi tana kuka amman hakan besa Mama ta k’yaleta ba.
“Wayyo Allah zan mutu!” tayi maganan baje akan tiles tana riqe da bayanta.
“Tashi kije ki kiramin Maj-Gen. d’in.”
“Mama wallahi bazan iya tashi ba.”
“Aww na saki share cikin gidan naki kenan ko?”
”A’a zan tashi zan tashi” tana bud’e d’akin nasa ta tarar dashi akan laptop yana aiki “wai kaje Mama na maka magana.”
“My Princess ya haka da riqe baya?”
“Ban sani ba ai wallahi ka kyauta nikan kazo.” Bayanta yabi suka fice akan kujera opposite na Mama suka zauna “gani Mama.” yayi maganan gentlemanly.
“Yauwa Maj-Gen ka bud’e kunnuwanka da kyau ka saurareni don Allah nace.”
“Toh Mama.”
“Take a look at your house now what can you say?” Yadda Mama ta buk’acesa yayi. He couldn’t believe it ko ina se sparkling yake ga k’amshin turare na tashi. A rayuwa yanason yaga muhallinsa da tsafta kaman haka “wow” yayi breathing “its sparkling yayi kyau sosai.”
“Good toh haka nakeson gidanka ya kasance a kullum, alk’awarin abu d’aya nakeson kamin, ka tabbata ko wani safiya Zeezee tayi shara tayi moppkng after each 3-4 days kuma tayi dusting, wanke-wanke kuma ban yarda wanke-wanke ya kwana a gidanka ba inba wai rashin lafiya take ba. Kar ya zamana takai sati bata wanke muku toilets ba. Zancen me aiki kuma banason ka d’au ma Zeezee me aiki dukkanin aikin nan dana lissafo ita nakeson tanayi can I count on you?”
“Uhmm Mama you see-”
“Bazaka iya min ba kenan?”
“A’a bawai haka bane-” saurin katsesa tayi “then can you promise me all that?”
“Yes Mama, I promise in shaa Allah.” wani mugun kallo Zeezee ke binsa dashi sannan ta sauk’a har k’asa tana kukan munafirci “Mama dan Allah kiyi hak’uri wallahi inhar na cigaba da aikatuwa haka kullum wataran gawa na zaku cire daga gidan nan, kiyi hak’uri dan Allah kibar Ya Al’ameen ya d’aukomin me aiki I promise tare zamuna yin aikin da ita Allah wallahi.”
“Zainab banason sakarci kina jina koh? In kinga Maj-Gen. ya d’au miki me aiki toh wallahi se in kin haifafa hidiman yara ya fara miki yawa, kana jina ai Maj-Gen?”
“Eh Mama naji.”
“Good ke kuma addu’a zan yita miki Allah shiryeki don zagi bashida amfani, amman kisani duk ranan da garin Allah ya waye baki aikata wannan aiki dana lissafo ba bakuma dan wani k’wararren dalili ba Allah ya isa na yana kanki.”
“A’a Mama please, kiyi hak’uri in shaa Allah ma zata nayi ba sekin ja Allah ya isa ba.” cewar Al'ameen.
“No ka barni da ita nasan halinta sarai ina barin nan bazata sake d’aga tsintsiya ba tunda kai na lura baka mata magana.”
“Kin jini ko bakiji ba?” Shiru Zeezee tayi not ready to talk.
“Aw in kira Babanki na fad’a
mishi.”
“A’a wallahi naji, naji karki kirasa dan Allah” tayi maganan fear na building a tare da ita. Da mamaki Al’ameen ke kallonta ashe duk rashin kunyarta tanada weak point, da kyau. Hak’uri Mama ta sake bawa Al’ameen akan rashin hankali irin na Zeezee sannan kuma a gabansa tayita yiwa Zeezee fad’a sosai sannan ta bisa da nasiha.
Bada jimawa ba tace zata tafi wanda Al’ameen yasa driver’n sa yayi dropping nata. Tana tafiya Zeezee ta zarce d’akinta tana me rusa kuka tsakaninta da Allah yanzu shikenan ita hutunta ya k’are kenan? Kukan ta cigaba dayi koda Al’ameen ya ganta be mata magana ba sabida yasan theres no point doing so in banda rashin kunya ba abinda zata masa don haka ya zarce d’akinsa shima.
*~ *~ *~
Washegari Zeezee ta tashi da sassafe ta gama ayyukanta tas, ji take wane bayanta ze 6alle dan azaba. Al’ameen na fitowa yaga ko ina sparkling clean ga kuma k’amshin turare d’akin Zeezee ya nufa ya sameta miqe kan gado tayi ruf da ciki. A nitse ya k’arisa ya zauna kan side drawer nan ta juya mai baya. “My Princess?”shiru ba amsa, “My Princess sannu da aiki kinji? Everywhere is sparkling clean ga wannan tukuicin aikin da kikayi.” ya ajiye mata bundle na N50.
Juyawa tayi don ganin meye tukuicin tana ganin kud’in ta d’aga bako kunya. “Bayanki na miki ciwo ne?” Kaman bazata amsa saba se kuma ta gyad’a kai. “Do you need a massage?” Tana so tana kaiwa kasuwa “ni banaso kafita min daga d’aki ai duk kaine.”
“Yi hak’uri toh.”
“Ni kafita min.” Besake ce mata komi ba ya miqe, ya kaiga bakin k’ofa ta tsayar dashi “kazo kamin wallahi bayana kaman ze 6alle” murmushi kawai ya saki yana kallonta da take rage kayan jikin nata, bajewa ta sake kan gadon tana jiran ya fara mata tausar. A hankali taji sauk’an hannunsa akan bare back nata, take heart nata yayi skyrocketing ita kanta ta rasa dalilin da yasa every single touch na Al’ameen yakeda strong influence akanta.
Massaging mata baya ya shiga yi a hankali wanda don dad’i har wani bacci Zeezee ta soma ji, hakan ya cigaba da mata har seda tayi bacci. Kwanciyarta ya gyara mata sannan yaja comforter ya rufeta da shi tare da rage speed na AC’n tunda batada kaya. Dawowa yayi ya zauna akan side drawer yana k’are mata kallo a yayinda wani irin wutan sonta ke sake ruruwa a zuciyarsa, he can’t wait for the day Zeezee zatayi accepting nasa as her husband, surely that day will come shiyasa baze gaji da trying to make her happy ba. What a gentleman!
Hannunsa ya d’aga a hankali ya aza akan fuskarta yana shafawa sam bata motsa ba seda yaja hancinta. Hannun nasa ta kama tasa k’ark’ashin kumatunta duk a cikin baccin, ta sake kuma tak’i ta sake hakan ya sanya Al’ameen murmushi sosai. Haka ya cigaba da zama a wajen yana k’arewa beautacious innocent while at sleeping face nata kallo, da k’yar ya samu ya iya ya zare hannun nasa tare da pecking forehead nata yayi whispering “I love you Princess” sannan ya fice.
_5 days later..._
Gabad’aya rayuwan kanta tabar yiwa Zeezee dad’i dalili kuwa shine wannan aiki da Mama ta aza mata shi na dole, domin haka tayi coming up da plan. Tana idar da sallan Asuba yau ta d’au towel ta tsoma cikin warm water sannan ta mammatsa a jikinta seda ya d’au zafi. Tana jin dawowan Al’ameen daga masallaci ta ruga gado ta kwanta tare da jan comforter ta rufe duka jikinta dashi harda kanta ciki tana kakkarwa. Not long enough ya shigo d’akin nata as usual don duba ko tayi Sallah tunda yanzu ba kwana d’aki d’aya suke ba.
“Princess kinyi sallah?” Yayi maganan some inches away from her bed har anan bata motsa ba. “Zainab?” Cike da kasala wane wacce batada lafiya ta leqo da fuskarta waje “Ya Al’ameen...” Ta fad’a cikin wani irin muryan dake nuni da mutum baida lafiya.
“Subhanallah! Princess are you okay?” Ya k’are maganan yana zaune akan gadon a gefenta. “Meke damunki Princess?”
“Zazza6i nakeji.”
“Zazza6i?” Ya miqa hannu tare da feeling body tempreture’nta extremely high ya jisa. “Subhanallah! Princess you are sick, sannu kinji?” Wutan d’akin ya kunna ya shiga toilet tare da fitowa da bowl cike da ruwan sanyi kad’an. Matsa mata jiki dashi ya shiga yi da towel d’in idan ya tsoma cikin ruwan. Ahaka har fake hot tempreture’n nata ya sauk’o se kukan shagwa6a take ta mai.
“Sannu kinji? First thing in the morning za muje asibiti, sannu koh?” Comforter yaja ya gyaggyara mata kwanciya, ya miqe ze fice kenan ta riqo hannunsa “Ya Al’ameen Mama nakeso, dan Allah ka kaini wajen Mama ita kad’ai zata iya taking care of me.”
“Toh karki damu sleep now, later on semu kaiki gida kinji?” Dad’i kasheta finally her plan has finally worked out! Kai kawai ta gyad’a mai kaman dagaske. Yana barin d’akin tahau daka tsalle sauk’a tayi daga kan gadon tare da jan d’aya daga cikin trolleys nata tahau had’a kayakinta ciki. Ai ba jaka bace ita da zata riga shara kullum tana dafa farin shinkafa, spaghetti kokuwa macroni wa bak’in Al’ameen gwara taje gida chan ta huta abinta.
*© MIEMIEBEE ™YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
[1/20, 9:01 PM]
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣8⃣
_09:34AM_
Zeezee ta gama shiri tsaf sekace wacce zata gidan biki. Tana kan pancaking face nata Al’ameen yayi knocking bisa k’ofa tare da shigowa “My Princess har kin shirya ne? I thought kina bacci ai.”
“A’a na tashi since.”
“Jikin da sauk’i kenan.”
“A’a wallahi kawai de na dage ne yanzu haka kaina ciwo yake min just now nayi amai ma.”
“Subhanallah sannu ko? Muje mu karya toh muje asibitin yaso daga chan se nayi dropping naki a gida zuwa Maghrib na d’auko ki.”
“Wai kai ka d’au yini kawai zanje inyi? Rashin lafiya fa nake” akwatinta ta fiddo daga lungu “ina kuma zakije da wannan?”
“Gida mana.”
“Lafiya daiko?”
“Kaman ya lafiya zanje gida Mama ta kula dani mana.”
“Zainab yanzu sabida fever’n da be kwantar dake ba shine zaki had’a akwati zaki gida?”
“Kamar ya be kwantar dani ba? Dan ya d’an sakeni yanzu sekace haka? Ai zuwa anjima ze dawo.”
“A’a baza ayi haka ba, tunda ina gida i’ll take care of you yanzu muje asibitin.” Bajewa tayi k’asa gun tahau rusa kuka haka kawai ze kama yayi mata ruining plan wallahi k’arya ne. “Wallahi ni se ka kaini gida, ni Mama nakeso ba kai ba wayyo Allah!!” Ihu ta cigaba dayi wajen tana kururuwa a yayinda yayi tsaye wajen kawai yana mamakin yarintarta.
“Is okay toh naji tashi mu kaiki gidan bar kukan haka.” Hannu tasa ta share hawayenta “anya kuwa Zainab ba faking rashin lafiyar nan kike ba?”
“Kaman ya faking? Ana k’aryan rashin lafiya ne? Kai kanka fa kaji yadda tempreture na yahau d’azu Allah banida lafiya.”
“Toh get well soon.”
“Yauwa kuma ni bazan je wani asibiti bafa Mama zata kula dani.”
“As you wish lets have breakfast” nan da nan suka karya aka fito mata da akwatinta, acikin mota Al’ameen ya kalli Zeezee daketa buga Candy Crush a wayanta sannan yace, “Princess sekuma yaushe zaki dawo?”
“Idan fever’n yayi sauk’i kaman nanda one week haka.”
“Har one week?”
“Wani har nema? Dan bance zanyi wata ba?” Bada dad’ewa ba suka isa gidan nasu. An bud’e mata k’ofa ta fita kuma seta k’i. “Any problem?” Ya tambayeta.
“Yanzu na taho gida bazaka d’an bani kud’i na rik’e a hannu na ba?”
“Yaushe ne na baki 20k Zainab?”
“Ni ba abinda na tambaya ba kenan in kud’in ne bazaka bayar ba shikenan.”
“Toh ni ban fito da kud’i ba” sarai da akwai kud’i a pocket nasa dakuma motar ma in whole amman baze bata ba tunda rashin kunya tasa a gaba.
“Kar Allah yasa ka bayar d’in.” Buga masa murfin motan tayi wane zata 6alla sannan guard yabita da akwatinta ciki, binta da kallo Al’ameen yayi tare da kad’a kai.
****
Koda ta shiga ciki bata tarar da Mama ba saboda ta fita unguwa ana sunan ‘yar k’awarta. Sallama tayi Baba dake shirin fita kasuwa ya fito “a’a K’anwata ya da akwati? Lafiya dai ko?”
“Ina kwana Baba?” tayi maganan wane maras lafiya tare da tsugunawa har k’asa.
“Amsani de tukun meya faru?” acewarsa ma sakinta Al’ameen yayi, his biggest fear.
“Lafiya k’alau Baba nice bana jin dad’i zazza6i yasani gaba chan kuma bame bani kulawa Ya Al’ameen kullum bai gida shine yayi suggesting nazo nan nad’an huta.”
“Toh hakane? Amman don zazza6i shine har sekin dawo gida K’anwata?”
“Toh Baba bazan iya kula da kaina ba yanzu haka daga asibiti muke ammin allura.”
“Wai wai har allura? Sannu K’anwata sannu, k’ariso ciki toh.” Da kansa yaja mata akwatinta (iyayen d’aure ma k’arya gindi ba.) Bada jimawa ba ya fice kasuwa nan Zeezee ta samu kanta. Waya tahau yi da Adeel kaman ba gobe. Harda La’asr ba wanda yadawo cikin su Baba. Se chan 5:46pm Mama ta dawo gida all exhausted ganin Zeezee tayi a kitchen tana soya k’wai aikin kenan kullum, kafin tace zata 6oye plate d’in har Mama ta ganta. “Zainab!”
“Na’am Mama sannu da zuwa.”
“Sannu de tun yaushe kike nan?”
“Tun safiya fah Baba yace kin tafi gidan suna.”
“Eh wallahi Fateey’n Maman Fateey ce ta haihu.”
“Ayyah sannu da zuwa, arghh! wayyo kaina!” Tayi faking exclamation.
“Me kuma ke damun kankin?”
“Oh! Ban fad’a miki ba ko? Wallahi zazza6i ne yasani gaba for the past three (3) days shine Ya Al’ameen yace na taho gida zanfi samun kulawa.”
“Ban fahimci wai kidawo gida ba wai kina nufin harda akwatinki?”
“Eh toh achan bame kula dani.” Tafe hannu Mama tayi in suprise tana mamakin gut irin na Zeezee “yanzu don zazza6in k’aryan da am sure kika k’irk’iron shine kika dawomin gida da zama?”
“Mama wallahi ba k’ar-”
“Rufa min baki” ta katseta da wuri, “ni zaki raina ma wayo ko jinki bansan wannan d’an banzan halin da kuke developing bane ‘ya‘yan yanzu? Da zaran kunga kun fara aikatuwa a gidan aurenku seku d’ibo k’afa ku dawo gida da sunan wai bakuda lafiya ko ba haka ba? To ki bud’e wannan kunnuwan k’ashin naki ki saurareni da kyau wallahi ba a gidana za’ayi wannan iskanci ba kina jina ko? A da dabaki fara su shara ba ai baki ta6a cewa bakida lafiya ba se yanzu. Maza-maza ki had’a kayakinki kiyima Maj-Gen waya yanzu ya turo a d’aukeki.”
“Mama wallahi ba haka bane Allah banida lafiya ai Baba ma yaga shigowa na kuma ya amince na zauna anan har sena samu sauk’i.”
“Babanku kam dama ai komi ma amince miki yake tunda shi har yau be koyi darasinsa ba, maza ki kira Maj-Gen ba a gidana za’ayi wannan sakarci ba wallahi, kin ta6a ganin Mariam ta dawo gida da sunan bata lafiya ne? Koda ta haihu batace zata dawo gida ba nice naje na sameta mesa baza kiyi koyi da yayyun ki ba? Bazaki motsa bane?”
Kuka Zeezee tasa gun ita a dole batada lafiya. “Wai jiranki nake ne?” Tana tsugune gun tana ta k’irk’iro kukan k’arya tace, “wallahi Mama banida lafiya ki kira Ya Al’ameen ki tambayesa abinda har allura mun d’auka min.”
“Wato se kinji na jaki zaki tashi ko?”
“Wallahi Mama banida lafiya dan Allah kibarni na zauna anan, ina warwarewa zan koma gida na.” Ana cikin haka Baba da Omar suka dawo suka samu su Mama in the act. “Sannu da zuwa Alhj, Omar sannu.”
“Yauwa sannu Mama.”
“Sannu Hafsah meke faruwa haka kikasa patient agaba?”
“Patient? Wace patient d’in?”
“Zeezee mana ko bata gaya miki ba tada lafiya bane?”
“Baba wallahi na gaya mata wai sam k’arya nake.”
“Ai k’aryan nema, rashin son aiki yasa kika gudo nan koba haka ba?”
“Wallahi ba haka neba.”
“Haba Hafsah! Ana k’aryan rashin lafiya ne? Kuma munyi waya da shi mijin nata ma ya shaidamin batada lafiya.”
“Yo Maj-Gen kam ai dama haka zece maka tunda Zeezee tafi k’arfinsa amman wallahi ‘yar nan k’alau take.”
“Allah banida lafiya.” Omar dake tsaye wajen yana kallonsu don kansa ya nufi site nasa saboda shima yasan k’arya Zeezee take.
“Ya isa haka Hafsah tunda ba’a kanki ‘yar nan zata kwana ba, ba ruwanki musamman mijinta ya kawo ta saboda batada lafiya kice k’arya take?”
“Nikuma kaji na rantse da Allan da raina ke hannunsa baza ayi wannan rashin hankali a gida na ba, wani rashin lafiya ne anan yarinya duk tayi kumatu saboda yadda takejin dad’i a gidan miji amman don rashin son aiki ta gudo wai batada lafiya? Wallahi bazan bari ba yanzu, yadda ka lalata tarbiyyan yarinyan nan ada kayi ma yanzu, Zainab zata koma gidanta ko tana so ko bataso ni na gaya maka.” Ta k’are maganan in a serious tone sosai tabawa Baba mamaki be ta6a jinta tana d’aga murya haka ba hakan na nuni da yadda ranta ya matuk’ar 6aci kenan.
“Me yayi zafi haka Hafsah na? Yi hak’uri mana” yayi maganan in a soothing tone.
“Ai ba zancen hak’uri bane ‘yar nan bazata kwana gidan nan ba.”
“Naji toh yi hak’uri kinga Maghriba ya riga yayi yanzu kiyi hak’uri kibarta ta kwana nan yaso gobe da safe seta koma chan gidan nata. In rashin lafiyan ya sake tak’urata yaso sekije ki sameta ko?”
“Har se gobe ta koma gida? A yau d’innan zata koma, yarinya sam batasan ciwon kanta ba ke bakisan da haka zakiyi creating space wa Maj-Gen. ya soma kula matan waje bane? Saboda time da ya kamata kina tare dashi baki nan as kinzo nan kina faking rashin lafiya ni na gaya miki a gobe zaki koma gidanki aikin banza kawai.” Mama na kaiwa nan ta fice, kuka Zeezee ta shigayi shikenan Mama ta rusa mata plan nata yanzu haka zata koma ta cigaba da bauta wa Al’ameen? Wayyo ita.
Hak’uri Baba yata bata da alama har ya mance da kalan rashin hankalin da Zeezee tamai a baya be koyi darasinsa ba har yanzu. Zeezee na kwance a d’akinta se turo baki take gabad’aya ji take kaman ta gudu taje somewhere tasamu Adeel nata. Video call da sukazo sukayi da Adeel nema ya d’an farinta mata rai.
Kafin Al’ameen ya kwanta seda ya kirata don yi mata ya jiki amman dake a cike dashi take, gani take duk laifinsa ne yasa ko d’aga wayan ma batayi ba.
*~ *~ *~
Washegari tun 8am Mama ta kira Al’ameen da kanta ta buk’acesa da ya turo driver’nsa yazo ya d’auki Zeezee maza-maza kuma koda wasa kada ya sake bari ta baro gida inhar Zeezee batada lafiya ne dagaske nan gaba ita da kanta zataje ta zauna akanta, fad’a sosai tamai da yadena zubawa Zeezee ido tana abinda taga dama yana mata fad’a sede shi yana ganin baze iya ba, ansan soldiers da fad’a da zafi but when it comes to their loved ones they are damn sweet, calm and quiet!
Tara saura driver’n Zeezee ya iso, sam bata so tafiya ba. Fad’a Mama tata mata kaman ba gobe.
***
Su Zeezee suna isa gida tafito daga motar a fusace not minding ta rufe k’ofar, zaune bisa dining table yana having breakfast ta tarar da Al’ameen, wani d’an banzan harara ta watsa masa sannan ta nufi d’akinta direct inda ta baje tayita kuka kaman ba gobe. Seda tayi ta godewa Allah sannan ta nufi bayi ta wanke fuskanta tafito ta zauna bakin gado tana tunani ya zatayi tasa Al’ameen ya saketa, shin wani rashin hankalin zata mai da zesa ya rabu da ita? Gabad’aya ta shiga damuwa yanzu saboda yadda Adeel kece mata bata damu dashi ba yanzu don kuwa da tayi da tuni ta kashe auran nata (wa'iyya zubillah!) Dabara ce ta fad’o mata, wata maqirar murmushi ta saki. A ranan gabad’aya word be had’ata da Al’ameen ba saboda ko shiga d’akinta beyi ba shima.
Washegari bayan ta k’are chores nata sun karya Al’ameen ya shirya tsaf sannan yazo yayi mata sallama kan ze fita ko ta kansa batayi ba banda dogon tsukan data ja mai. Yana fita taja mayafinta itama ta nufi gidan k’awarta Hajar datayi aure recently, bayan ta fayyacewa Hajar plan natan tayi promising nata 100k inhar tabata had’in kai suka gudanar da wannan plan, kasancewar Hajar money monger ce tuni ta amince.
_2 days later..._
Ana sauran kwana hud’u Al’ameen ya koma ABJ, yana zaune a parlour as usual yana kallon sports aka danna door bell yana dubawa yaga bak’in fuskoki guda biyu amman sede yana da tabbacin k’awayen Zeezee ne. Ya bud’e yayi musu sannu da zuwa sede meh? Take Hajar tahau sa da tsiwa “ina matar taka take? Wallahi ta fito ta biyani kud’ina ai ba haka mu kayi da ita ba, kota ban kud’i na kona kai k’aranku duka police station tunda kaine mijinta.”
“Wait, wait what is going on here guards!” Take suka mammatso “kunsan wannan faces?” ya tambayesu in an authoritative voice.
“No Sir sunce mana de k’awayen Madam ne.”
“And mena ce muku about letting strangers in?”
“We are very sorry Sir but they told us they are friends.”
“It shouldn’t repeat itself, am I clear?”
“Yy.. Yes Sir thank you” sukayi saluting nasa tare da ficewa.
“Baiwar Allah kode kinyi 6atan kaine?” yadawo da kallonsa akan Hajar dake ta admiring kyansa ita bama wannan ba muryansa ne ke tafiyar mata da imani, me bawan Allan nan ya rasa da Zeezee ke neman ya saketa? Ai ita wannan ma ya fiye mata Adeel wallahi, dake wa tayi;
“Ba wani 6atan kai ko ba nan bane gidan Maj-Gen Al’ameen me mata Zainab?”
“Nan ne nine ma maigidan.”
“Good so nake ka fito min da matarka ta biyani kud’i na wallahi.”
“Kud’i you mean kina bin Zainab bashi? Since when?” yayi maganan damn suprised.
“3 weeks back.”
“Subhanallah, nawa kuma?”
“500k.”
“What?!” yayi exclaiming jaw dropped.
“Ai ka jini de kuma ba sharri nake mata ba wallahi tafito taban kud’i na ace babban mutum kaman ka amman kabari matarka tana cin bashi awaje Allah wadai wallahi, nide aban kud’ina konayi kururuwa in tara maku jama’a.”
“Ko kinsan a gidan soja kike kike wannan batu? And how can you accuse my wife?”
“Aww ma tambaya kake? Zainab!” ta shiga k’wala wa Zeezee kira “Zainab kifito nan.” A farko Al’ameen yayi niyyan yasa guard nasa suyi mai waje da Hajar da k’awarta amman ganin yadda ta dage kan sam wallahi da akwai bashinta gun Zeezee ya shiga duhu shin har yaushe Zeezee taci bashin 500k besani ba? Wani irin kud’i ne bai bawa Zeezee da zata nemi ta tozarta sa a idanun jama’a da girmansa da komi zata mai haka meya mata? A gaban k’ananun soldiers nasa bujakai wanda basu kai sun kawo ba sun tsaya suna gaya mai magana gaskiya abin Zeezeen kuma ya soma yin yawa “ina zuwa” kad’ai ya iya ce dasu sannan yaje yasamu maqirar zaune kan gado, yi tayi kaman bata da masaniya kan abinda ke faruwa.
“Zainab?”
“Meh? Menayi kuma yanzu?”
“Shin dagaske ne kin ranta bashin 500k gun k’awarki baki biya ba?”
“Sosai ma kuwa anyi haka.”
“Sabida mesa?”
“Kaman ya sabida mesa? Baka bani kud’i ishasshiya ba ba dole naci bashi ba.” Magana ya soma a fusace sabida ransa ya matuk’ar 6aci, bayason abinda ze ta6a masa suna.
“What nonsense Zainab? wani irin kud’i ne ban baki ba? White gold naki be 6ata ba kince ya 6ata na sai miki sabo, I heard you the other day on the phone kina ciniki zaki siyar da shi duk ban miki magana ba, yanzu kuma seki nemi tozartani ki 6atamin suna agari ace babban mutum kaman ni nabar matana tana cin bashi a gari?”
“Wow! Wow!” Ta tahau yin tafi “I like where this is going finally kafara fighting back ai da hakan kakeyi tunda a baya da warhaka mun tarwatse, bakason sunan ka ya 6aci a agari? Fine and good seka bani takarda na yanzu-yanzun nan ko minto d’aya kada ka k’ara aikin banza kawai baka bani kud’i ba ya kakeson nayi? Ko ka ta6ajin Baba yace maka naci bashi lokacinda nake gidan shi ne? Kai ka d’aukoni ka kawo ni nan dole kayi hak’uri da dukkanin abinda zan maka kuma believe me this is just the start wallahi I will never rest until da hannunka ka d’au takarda na ka miqa min mschwww!”
“Haka kikace?”
“Ai hakan nema, ko ka biyasu kud’insu kokuwa ka sakeni Baba na ya biya min tunda ba matsiyaci neba shi.”
“Ya miki kyau” kad’ai yace mata sannan yaje ya rubuta wasu Hajar cheque na 500k tare da basu hak’uri on behlaf of Zeezee.
Su Hajar suna isa gida tama Zeezee waya “Babe ga cheque nan fa har Ogan naki ya bamu.”
“Aikinki yayi kyau gobe zan taho miki da 100k d’inki.”
“Toh ya yanzu? Yace ze sake kin?”
“Wannan mayyen? Ai inba maqora na kaisa ba, baze ta6a saka na ba.”
“Toh amman Zeezee meyasa kikeson rabuwa da miji kaman Maj-Gen.? Bawan Allan nan banga abinda ya rasa ba ga kyau ga hankali most of all ga sweet voice.”
Allah ko? bari Ahmed (mijin Hajar) ya jiki ba ruwa na.”
“LOL but seriously.”
Toh ni duk feautures d’in ba burgeni suke ba, Adeel kawai nakeso.”
“Allah baki shi toh sena ganki goben.”
“Ameen bye!” nan tayi hanging yau ma kaman jiya word be sake had’ata da Al’ameen ba ko duba ta da Asuba beyi ba saboda abinda ta masa ya mugun 6ata mai rai.
****
A washegari kaman yadda ta saba fita bada izininsa ba da sassafe ta tashi ta gama ayyukanta ta karya sannan ta fice yawonta. Ba Al’ameen ya tashi ba se to 10am nan yayi wanka shima jin ba motsinta yasan tafita yau ma, breakfast ya aika aka siyo mai yana cikin karyawa wayansa ya shiga ringing yana kai dubansa kuwa yaga Hjy Sadeeyah, batare da 6ata lokaci ba ya d’aga “halo Big Sis.”
“Na’am Little one kana gida?”
“Eh ban koma aiki ba tukun se jibi.”
“Oh to gamu da Mama mun yanko kwanan gidanka.”
“You mean kuna Bauchi?!” yayi exclaiming.
“Yes gamu nan ma a bakin gate yanzu.” Mumunar fad’i gabansa yayi yasan halin Sadeeyah sarai ba shakka taje ta irgawa Mamansu halin da yake ciki ne Mama ta ibo k’afa all the way from Kaduna ta taho nan. Tunanin me zeyi ya soma wanda beyi nisa ba Sadeeyah ta danna doorbell. Jiki na k’yarma ya miqe ya bud’e musu. Salati kawai Mama ta saki ganin yadda fuskan Al’ameen nata yad’an fad’a ba shakka Sadeeyah batayi k’arya ba matar Al’ameen na basa wahala saboda ta samesa shiru-shiru bayi magana. Al’ameen mutum ne da abubuwa basu cika damunsa ba inhar ko aka soma ganin damuwa tattare da shi to abu ya 6aci ne kwata-kwata ba kanta.
“My Only Son?!” Mama datayi ageing about 67 tayi exclaiming tana shafa fuskansa pathetically.
“Ai na gaya miki Mama, kinga yadda ya rame kuma believe me wallahi time dana zo bekai haka rama ba.” Hannun Al’ameen taja suka shiga ciki suka zauna kan kujera d’aya a yayinda Sadeeyah ke zaune oppsite them. “Al’ameen Babana meke faruwa? Meke damunka?” Hannunta ya sauk’e da k’yar daga fuskan nasa, “babu Mama” sannan ya maida kallonsa kan Sadeeyah, “Hjy me kikaje kiga gayawa Mama kika sa tazo all the way from Kaduna, bakisan its bad for her health bane?”
“Akwai abinda yakai min rashin kwanciyar hankalinka tashin hankali ne Al’ameen? Yanzu ace da raina amman bazaka sanar dani halin da kake ciki ba sede a bakin Sadeeyah? Itama da Allah be kawo taba sede rana d’aya inji matar taka ta sa maka ciwon zuciya ka fad’i ka mutu?”
“Mama what are you talking about? Bafa abinda ke faruwa ki kwantar da hankalinki please ni banason abinda ze tayar miki da hankali.”
“Ai ka ajiye kalman kwanciyar hankali a gefe, ina matar taka take?”
“Uhm... Erm-” katsesa Sadeeyah tayi da wuri “ta fita yau ma kaman kullum ba? Ai na gaya miki Mama, wallahi kullum da safe seta fita yawo kuma karki manta ba breakfast take ajiye mai ba sekuma Magrib take dawowa.”
“Thats not true Mama karki jita, Hjy enough please” yayi defending kansa.
“Aww nice nake k’arya Lil Bro? Well lets see” dining space ta nufa sega take away nasa dayake having breakfast with, kai ta kad’a ta d’ago ta kai wa Mama, “ba gashi ba aikin kenan kullum cikin siyan takeaway, bata ta6a mai girki ba Mama meye amfanin wannan auren? Wallahi ina raye wancan shegiyar bazata wahalar min da k’ani ba, I just let her go kwanaki but not now not ever.”
“Barni da ita Sadeeyah, haka kawai tasa min Only Son a gaba sabida taga baya magana? Ina matar taka take nace?”
“Sekin tambaya ne Mama? Ofcourse ta fita yawon banzan data saba mana.”
“Ina take Al’ameen answer me.”
“Mama bata gida ta fita amman da izini na ta fita.”
“Al’ameen yanzu ni zakayi wa k’arya? Ka kalli cikin idanu na kamin k’arya?”
“Mama please...” Sekuma yayi shiru.
“Da izinin ka tafita koko a’a? Karka min k’arya am damn serious.”
“Bada izini na ta fita ba but pl-” katse sa Mama tayi “Sadeeyah d’au waya ki kira min iyayen yarinyar both baban da maman now! Za’a yita ta k’are yau.”
*© MIEMIEBEE ™YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄?
[2/3, 9:32 PM] 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*Febuary, 2017*
3⃣9⃣
Nan da nan Sadeeyah ta kira Mama as a matter of urgency kan ita da Baba suzo yanzu-yanzu, ta fad’i ko lafiya kuma tak’i. Cike da tashin hankali Mama ta kira Baba yana d’agawa tayi stating, “Alhj kana ina yanzu?”
“Ina hanyan zuwa kasuwa ne, lafiya?” Ya amsa.
“A’a wallahi ba lafiya ba ka juyo yanzu Sadeeyah yar Maj-Gen ta kirani kan ita da Mamansu suna gari suna gidan Zeezee haka wai we are needed urgently.”
“Subhanallahi! Allah yasa de k’alau to gani nan zuwa.”
“Yauwa kayi sauri please.”
***
“Mama you are not doing this.” Al’ameen yayi maganan still not believing abinda ke gudana.
“Ka tsaya kaga aiki da cikawa.”
“No Mama please drop all this Hjy call them back kice musu su fasa zuwa ni banason tashin hankali, let Zeezee be eventually zata zo tayi learning truth, yarinya ce har yanzu.”
“Yarinya fa kace Al’ameen? D’an yaron shekara d’aya ma ya iya ya tantace dad’i da rashinsa sekace min zank’aleliyar mata kaman Zainab batasan ya kamata ba? Wallahi k’arya ne raba auren nan za’ayi kowa ya huta ba yadda za’ayi ka kai yarinya Hajj ta tsaya tana maka wannan iskancin.” Ta fada rai a b'ace.
“Ai Mama ban fad’a miki bane har mota ya sai mata kuma karki d‘au wai k’aramar mota ce, sak irin nasa Ford Jeep d’innan ya sai mata.” Hjy tayi stating.
“Karki gayamun Sadeeyah!” Exclaimed Mama.
“Wallahi gashi ki tambayesa, kuma ina da tabbacin ita tace se kalan nashi takeso.”
“Al’ameen kalleni, kalleni nace!” Ta tsawata masa a hankali ya d’ago kai yana kallonta “ya kukayi da ita?” Shiru yayi not ready to talk, “aww bazaka gayamin ba kenan? Kode asirce ka matar taka tayi?”
“Mama ni bata asirceni ba, wai ina baki hak’uri bazaki hak’ura ba yanzu? Please kuyi dropping maganan nan I beg of you please.”
“Kanason in sa6a maka koh? inba asirce kan tayi ba then mesa bakason aga fault nata? Ina maka tambaya bazaka amsani ba? Nace ya kukayi da ita?!”
“Tace tanason kalan mota na ne inda hali na sai mata thats all bawai forcing d’ina tayi ba.”
“Lallai yarinyan nan batada kunya, Allah kawo iyayen nata.” Mama tayi maganan unbelievably.
“Ameen” Sadeeyah ta amsa.
“Mama please inhar kina sona call them back kice su fasa zuwa, zamu iya mata gyara within us base mun sa iyayenta ciki ba, karmu had’a kanta da parents nata please.”
“Kai abinda ke damunka kenan? Kaji na rantse yau se an raba auren nan billahillazi.”
“No Mama please dan Allah don’t do this to me, karki raba aurena da Zainab you know how much I love her.”
“But she doesn’t love you Al’ameen zuciyarta bata tare da kai kadena wahalar da kanka akan wacce is not worthy of your love.”
“I believe in US I believe wataran al’amura zasu daidaita tsakani na da ita, its just a matter of time.”
“Time? Yau da bikinku watanni nawa? Beyi hud’u ba?”
“Yayi sosai Mama” cewar Sadeeyah “in beyi biyar bama kenan.”
“Akwai time dayafi wannan ne? watanni biyar da aurenku ko 6ari banji ‘yar nan ta ta6a yiba kome dalili ban sani ba.”
“Mama wannan kuma wace irin magana ne? Haihuwa kam bana Allah bane?” Al’ameen yayi saurin tararta.
“Wai Al’ameen in haifeka sannan kake tunanin zaka iya min wasa da hankali? Nace meye dalili?”
“Nima ban sani ba gaskiya.”
“Lil Bro why defending her? ‘yar nan ba sonka take ba, she don’t deserve you, she isn’t worthy of your love. Mama wallahi koda nazo kwanaki ba a d’aki d’aya suke kwana ba and that means ita ta koresa daga d’akin tunda batason basa kanta, can you deny it?”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Al’ameen! Amman da hankalika kuwa? Mahak’urci mawadaci amman naka hak’urin yayi yawa, Sadeeyah tell me this not true.”
“Wallahi it is Mama gashi ai seyayi denying inhar k’arya nake”
“La’ilaha illallahu! Ni Ameenah naga duniya, kai! Amman da hankalinka kuwa? Ka biya sadakin yarinya sannan tak’i baka hak’k’inka kuma still ka tsaya kana farinta mata rai da gifts? Are you that stupid Al’ameen? What is wrong with you? Dakai nake magana!” Tun daga nan Al’ameen ya kasa fad’in komi again, kansa ya sunkuyar ayayinda masifan Mama da Sadeeyah keta scattering masa k’wal’kwalwa take ciwon kai me tsanani ya rufesa.
*~ *~ *~
In less than 30 minutes su Mama suka sa iso hankali tashe, gaisuwa sama-sama sukayi da Mamansu Al’ameen. “Hajiya you called for us ina fatan lafiya?” Cewar Baba. Zanin Mama Al’ameen ya shiga ja da nufin dan Allah tayi shiru amman ta fisge zanin nata.
“Inason kafin mu fara komi ku kira min Zainab awaya ko wala Allah zataji magananku ku iyayenta ta dawo gida tunda ta saba fita bada izinin mijinta ba.”
“Mama please thats enough” Al’ameen yayi pleading a hankali amma kota kansa batayi ba
“Hajiya ban fahimci inda kika dosa ba” Baba yayi maganan with bewildered look on his face, Mama kanma kasa cewa komi tayi.
“With time zaka fahimta Alhj, amman nafison ayi komi a gaban Zainab kada kuce sharri akeyiwa ‘yarku.” Tuni ran Baba yahau tafasa waya ya zaro daga aljihunsa a fusace ze kira Zeezee sanin halinsa Mama ta sauk’e hannun nasa “a’a Alhj kabari na kirata da kaina dan Allah nace.” Kai kawai ya gyad’a mata yana wani irin zakin nishi.
** _After a while..._
“Hello Zeezee?”
“Na’am Mama ina kwana?”
“Lafiya qalau nace kina ina ne? Ki dawo gida yanzu gani na zo.”
“Toh Mama I’m on my way.” Tana ajiye wayan tayi sallama da Hajar. Zama shiru sukayi wajen ba wanda ya sake cewa komi seda suka jiyo k’aran bud’e k’ofan Zeezee tana maida k’ofan ta juya taga biggest suprise of her life, idanunta na tozali dana Baba ta tabbatar tana cikin babban tashin hankali yau, meke faruwa? Me tayi? Wayyo nata ya k’are.
“Kinyi tsaye akan mu bazaki k’ariso bane?” Cewar Baba harshly. Jiki na rawa ta k’arisa parlourn tare da zama a k’asa daga wani angle, cikin sauti me rawa ta shiga gaidasu sede kowa ya amsa banda Baba, nan fa cikin Zeezee ya sake d’aukan ruwa.
“Masha Allah, Sadeeyah kiyi ma Saje (one of Al’ameen’s soldiers) magana.” Cewar Mama Babba. In a minute taje ta taho da Saje, cike da girmamawa yabisu duka da gaisuwa babu kaman yadda ya gaishe da Al’ameen. Shi kansa Al’ameen is confused me kuma yasa za’a kira Saje acikin family matter’nsu? Bade su Sadeeyah sun had’a baki dashi ba yana kai masu rahoto a kullum ba?
“Good ina son dukkannin ku nan kubani aron kunnuwanku wannan” tayi nuni da Zeezee da tuni cikinta ya sake tsabagen rud’ani “Zainab ce matar Al’ameen d’ana. Inason Alhj kaida Hjy Hafsah ku kalli Al’ameen ku kuma kalli Zainab ku gayamin inji cikinsu waya k’ara weight bayan aurensu da akayi wanda ke neman watanni biyar.”
Mama kad’ai ce ta d’aga kai ta kalli Al’ameen banda Baba dake ta bin Zeezee da dirty look tun beji dalilin dayasa aka tarasun ba yasan rashin hankali tai. Se anan Mama taga kalan fad’awan da fuskan Alameen yayi whereas Zeezee kuma ta k’aru, ita daman tasan Zeezee na bawa Al’ameen wahala proof ne kawai batada.
“Hjy its crystal clear Al’ameen ya fad’a ba laifi.” Mama ta fad’a finally.
“Good base na sake nanata muku ba, you guys are aware yaron nan ya kai Zeezee hajj koba haka ba? Kuma inba wai yana sonta bane baze ta6a asaran sama da miliyan biyu akanta ba am I right?”
“Hakane sosai ma” Mama ta amsa ayayinda Baba ya gyad’a kai “Al’ameen na son Zainab sonda bana tsamannin akwai d’a na mijin da zeyi mata irinsa. Tun da nake da Al’ameen ban ta6a ganinsa acikin damuwa ba se alokacinda yakeson Zainab, abun mamaki anan shine kalan abubuwan da Zainab take yima Al’ameen d’ina har yasa ya zube haka, tun bayi bin abin a zuciya har ya fara damunsa wanda ba haka nasan Al’ameen d’ina ba kaima Alhj kasan halinsa tunda kuna zumunci.”
“Sosai Hjy ki gayamin me wancan ‘yar iskan tayi.” Cewar Baba.
“Alhj calm down dan Allah inma zakayi mata fad’a kabari se munje gida” Mama tayi maganan yadda Baba kad’ai ya jita.
“Abubuwan da tayi kuma take kan yi suna da yawa tunda ta samu Al’ameen me hak’uri take iya son ranta a gidan nan, tunda akayi musu aure bata ta6a aza mai girki yaci ba, tana fita bada izininsa ba, be ta6a gaya mata magana tayi ba gar da gar take zaginsa tana gaya mai magana iya son tanta, bata ta6a had’a kwanciya dashi ba ga kuma wayan da takeyi kullum da sauarayinta wai shi sunansa Adeel, yanzu haka fitan ta yau Al’ameen baida masaniya. Mota tace se irin wanda yake hawa takeso haka yaron nan ya sai mata amman ta saka mai da butulci irin wannan? Don ita yaro na gabad’aya ya zube ya sauya kamanni, it isn’t fair! Just recently taje taci bashin 500k gun k’awarta badon komi ba don ta 6atawa Al’ameen suna a gari, haka tasa k’ananun yara wanda basu kai ba suka zo suna gaya mai magana iya son ransu kan ya bari matarsa tana cin bashi a waje wanda ba haka bane. White gold na ‘yar nan be 6ata ba tamai k’arya ya 6ata haka ya sai mata sabo ta samu ta siyar da tsohon toh ni wallahi gaskiya ina raye bazan bari a cutar min da d’a ba. Na kiraku nan ne badon komi ba se dan ayita a gabanku ta k’are am cutting off this marriage Al’ameen baze cigaba da zama da Zainab ba tana cutar dashi tunda daman ba sonsa take ba tanada saurayinta wanda takeso as said.” Ta k’are maganan anger na building within her.
“Inalillahi wa inna ilaihi raji’un!” kad’ai Mama da Baba ke ambata, they are both totally speechless wannan rashin hankali dame yayi kama? Tun auran Mariam da Yasmeen in-laws nasu basu ta6a kiransu suka masu magana akan halayensu ba se Zeezee da dududu auran ta befi watanni biyar ba? Gabad’aya Zeezee ta kasa cewa ko uffan wajen all she knows is that nata ya k’are dan yankata Baba zeyi tun anan ta shiga rera kuka a hankali. Al’ameen kuwa tun da Mamanshi ta fara magana bece ko uffan ba infact tunda su Mama suka shigo ya gaishesu be sake d’aga kansa ba.
“In kuma har baku yarda ba inada proof, Saje kunna audio’n.” Cike da mamaki Al’ameen da Zeezee suka d’ago kai suna kallon saje wani audio kuma? Suka tambayi junansu a zuciya se yanzu suka gano Saje ne source of all informations da Mama ta samu batun zaman aurensu wannan na nufin akwai recorder’n daya ajiye a d’akin Zeezee dakuma parlour kokuwa kullum yana eavesdropping ta window anytime yaji Zeezee akan waya seyana recording, this is serious!
“I’m very sorry Sir, please forgive me for intruding, it was an order from your Mother” Saje yace da Al’ameen sannan ya kunna audio’n seji akayi muryan Zezee na tashi tana waya da Adeel ba a samun jin abinda Adeel ke fad’a se nata love words d’in har inda take sake ce mai budurcinta nasa ne kad’ai seda ya fito. Yana k’arewa aka sa na wanda take cinikin white gold nata Baba be gama jin audio’n ba zuciyarsa ta gama tafasa a zuciye ya miqe kafin Mama tace zata taresa yahau kan Zeezee tare dayin wani d’an banzan ball da ita seda gun ya 6ullo take. Wani irin rikicaccen ihu cike da azaba ta saki hakan yasa Al’ameen yayi saurin miqewa ya jata a yayinda Saje ya ja Baba baya shima yana me basa hak’uri, idon Mama kuwa tuni suka kad’a sukayi ja wannan wace erin rayuwa ce? Shin se Zeezee ta bata heart attack tukun zata huta? Cikin wani irin dishasshiyar murya numfashi na seizing Baba ya shiga magana.
“Al’ameen ka saki yarinyan nan ka saketa nace! Shi saurayin naki Adeel ko wa yake shi zan bashi sadaqar ki amman kisani Zainab bazaki gama da duniya lafiya ba na rantse miki.”
“Subhanallahi Alhj calm down please karka illata ta hakan baida amfani” cewar Maman Al’ameen a yayinda su Sadeeyah suke basa hak’uri.
“Wallahi seya saketa kunji na rantse seya saketa. Ai auran Al’ameen gata ne a gare da wannan ‘yar iska la’ananniyar, da kai nake Al’ameen maza ka d’au takardan sakinta ka rubuta mata shi yanzun nan kuma ba saki d’aya ko biyu nake so ba uku-” tari ya shiga yi sosai, “saki uku zaka rubuta mata, ita wai saurayinta har yanzu tafi fifitawa akan kowa ba? Shi za’ayi mai sadak’ar ki wallahi bazaki gama da duniya lafiya ba Zainab” Baba yayi mata baki again. Salati Mama ta hauyi sabida shi kad’ai ke fitowa a bakinta, har anan Zeezee na abayan Al’ameen tana rusa kuka.
“Alhj calm down please kaga har numfashinka na neman d’aukewa” cewar Maman Al’ameen “nima na goyi bayanka ayi sakin nan amman ba uku ba, saki d’aya ma ya wadatar tunda dan a hora Zainab ne.”
“Wallahi uku za’ayi bazan yi rantsuwa a iska ba, kuma ko ke kad’ai ce ‘ya a gareni na yafeki Zainab na cireki daga cikin jerin ‘ya‘yan dana haifa ko a lahira kika ganni ki canza hanya. Ni? Ni zaki nemi ki 6atan suna a idan jami’u ki tozartani, na d’au miji me hankali da hak’uri kaman Al’ameen na baki amman ki tauye masa hak’k’i bayan nan ki ringa waya da saurayi a gidansa kinayin abinda kika ga dama? Bazan ce zan miki duka ba dan wallahi-” ya tsaya yana tari sosai a yayinda idonsa suka kad’a sukayi ja wur “ya isa haka haka Alhj dan Allah kayi hak’uri” cewar Saje har anan Mama datake zaune jugum a kan kujera ta kasa fad’in komi ko motsi ta kasa seda taji fad’uwan abu rigijib! A k’asa. Take dukkaninsu mutan wajen suka kai dubansu ga inda sukaji k’aran, sumemmen jikin Baba suka gani, innalillahi wa inna ilaihi raji’un kad’ai ke tashi a wajen “Alhj!!!” Mama tasa wani erin d’ankaren ihu tare da rugawa a guje ta nufi kan Baba ta aza kansa a cinyarta tana hawaye sosai tana tapping kumatunsa sede sam bayi motsi, nishinsa ma wani sama-sama yake fita. Nan da nan duk sauran suka nufi wajen banda Zeezee dake sprawled a k’asa tana kukan cire rai daga inda take. “Ta kashemin miji, ta kasheshi wayyo Allah na! Na mutu na lalace!!” A 360 aka kinkimi Baba se Teaching Hospital gabad’aya hankalin kowa ya matuk’ar tashi, Mariam ma tuni Omar yasanar da ita ta taho ba shiri a corridor’n emergency room da Baba ke ciki ta tarar da kowa da gudu taje ta rungume Mama datayi jugum wajen banda hawaye ba abinda takeyi, kuka suka shigayi a tare a yayinda su Sadeeyah ke basu hak’uri daga bisani Mariam ta d’ago kai tare da watsa wa Zeezee dake tsaye acan ita kad’ai tana kuka harara. Kamar a kyaftawan ido ta risketa tare da bata wani irin hot slap cike da tsana da haushi, wajen Zeezee ta riqe da k’yar tana hawaye endlessly kafin ta farfad’o daga marin Mariam ta k’ara mata d’aya a other side d’in. Da wuri Omar yajata baya a yayinda Al’ameen ya kare Zeezee “kin kyauta kenan? Kin kashe mana Baba kin kyauta? What kind of a sister and a daughter are you Zainab? Wallahi kisani inhar wani abun ya samu Baba none of us your family will forgive you, bazamu ta6a yafe miki ba” ta k’are maganan tana kuka sosai, rungumeta Omar yayi yana bubbuga bayanta.
_45 more minutes..._
A dai-dai nan ne red globe dake a bakin k’ofan da Baba ke ciki ya mutu and within second counts k’ofar ya bud’u tare da bayyano da wani Dr. daga ciki. Kusan a tare dukansu dake wajen suka nufa gun Dr’n da gudu kowa da abinda yake tambaya which is none other than ya jikin maras lafiyan yake banda Zeezee dake baje a k’asa achan inda Mariam ta tsinka mata mari tana kukan cire rai. “Calm down okay? Ku kwantar da hankalinku haka in shaa Allahu ze samu sauk’i we pray so.” Salati ne ya biyo baya, “Dr. Ka gaya mana meke damunsa dan Allah, am his wife please tell me wani hali mijina yake ciki dan Allah karka 6oye mana wani abin dan Allah nace” Mama ta k’are maganan tana jan hanci.
“Toh muje office d’ina tunda kece matar tasa please.”
“No Dr. I can’t wait till then duk nan family ne ka gayamana wani hali yake ciki please.”
“Yes Dr please” cewar Omar da Mama Baba. Clearing throat Dr yayi “kaman yadda kuka sani shi patient d’in nada hawan jini ko?”
“Eh amman rabuwan jinin nasa daya hau ya jima Dr.” Mama ta amsa immediately.
“Yasamu heart attack ne wanda a dalilin haka yayi leading masa to heart failure-”
“Heart failure?!” Sukayi exclaiming in unison. “Dr dan Allah karka cemin ya mutu I can’t afford to lose him” jan Mama Mariam tayi a jiki tana bubbuga bayanta.
“Calm down be mutu ba mun bashi kulawan gaggawan daya kamata yana bacci yanzu in shaa Allah zuwa anjima ze farfad’o sede inason jin meya jawo attack dayasa har heart nasa yayi failing, saboda munyi all tests is not as if yana suffering from wani infection ko disease kokuma yana shaye-shaye.”
“Baya shaye-shaye Dr. ‘yar sa ce ta tsinka mai zuciya abinda ya faru kenan” Mama tayi explaining in a crying tone.
“Shikenan Hjy kibar kukan haka in shaa Allah mijinki ze samu waraka zamu d’aurasa akan diuretics da cardiac drugs sede yazamo dole abar breaking masa sad news kuma if possible koda ya tashi kar kushiga cikin d’akin nasa da ita ‘yar nasa data jawo mai attack d’in sabida by just looking at her zuciyan nasa tana iya tsinkewa again.”
“In shaa Allah Dr. Mungode mungode sosai” Maman Al’ameen ta amsa.
Komawa duk sukayi suka zauna atleast Baba be mutu ba yanzu, har anan ba wanda yayi takan Zeezee.
_20 more minutes..._
Alokacin har Mama Baba da Sadeeyah sun koma gida, Nurse ta sanar dasu Mama kan Alhj ya farka, godiya dukkanin su sukayi wa Allah sannan Mama kad’ai ta shiga d’akin, hawaye tasoma zubarwa wane lalacaccen famfo ganin har oxygen seda akayi supplying wa Baba. A nitse ta k’arisa wajen taja kujera ta zauna, “Al... Alhj?” Hannunsa yakeson d’agawa amman ya kasa data gano hakan seta d’aga ta had’a da nata “Alhj Allah ya baka lafiya, Allah baka lafiya Alhj” cikin wani dishasshiyar murya ya amsa da “ameen kukan ya isa haka, Al’ameen ya saki Zainab?” Abinda ya fara tmbaya kenan.
“Alhj kabar damuwa da zancen Zainab its not fit for your condition.”
“Ki gayamun ya saketa?”
“Ya saketa Alhj” tamai k’arya ganin hannunsa ya soma shaking.
“Hafsah nayi nadama, nayi nadaman maida Zeezee *_‘YAR GATA_* gata bashida wani amfani, tabbas da naji maganarki da a baya da duk hakan be faru ba, ina alfahari da Mariam da Yasmeen Allah ya cigaba da musu albarka.”
“Ameen Alhj duk wannan ba abinda zaka damu kanka dasu bane yanzu, lafiyanka ne a gaba su Mariam suna nan kanason ganinsu?”
“Eh ki shigo min dasu” sauk’e hannunsa tayi a hankali taje ta kira su Mariam inda ta sanar da Al’ameen komin rintsi yacewa Baba ya saki Zeezee saki uku kaman yadda ya buk’ata. Bayan Mama suka bi suka shiga ciki da gudu Mariam da Omar suka nufi kan Baba suna kuka sosai a yayinda shi kansa yake hawaye, “‘ya‘yan albarka ku yafemin, ku gafarceni na rashin adalci danayi a tsakaninku ku yafemin please.”
“Baba dan Allah kabar neman yafiyanmu ba abinda ka mana mude fatan mu Allah ya baka lafiya” cewar Mariam
“Sannu Baba” cewar Al’ameen “Allah ya baka lafiya”
“Ameen” Omar da Mariam suka amsa.
“Al’ameen nagode Allah saka maka da alkhairi.”
“Ameen Baba bakomai.”
*** Tsaye Mama ke a bakin k’ofar d’akin Baba tana bin Zeezee dake ta kuka har a yanzu da harara, wani wutan tsanan Zeezee ne ke ruruwa a zuciyarta. Jiki na k’yarma Zeezee ta doso inda Mama ke tsaye tare da kneeling a gabanta tana kuka me tsuma zuciya, “Mama dan Allah kiyi hak’uri, kiyi hak’uri dan Allah na tuba bazan sake ba.” One more dirty look Mama ta watsa mata sannan ta bar mata gun tare da shigewa d’akin domin batajin zata iya mata magana.
*© MIEMIEBEE ™YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄
[2/3, 9:32 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*Febuary, 2017*
4⃣0⃣
Wani irin kuka Zeezee ta rushe dashi, kanta har wani sara yakeyi mata. Tafi minti goma tsugune a wajen tana kuka, seda su Al’ameen suka bud’e k’ofa taja gefe har anan su Mariam basu ce mata ko uffan ba. Gida Mama ta aika Omar dan kwaso mata abubawan da zata buk’ata tunda a asibiti zata kwana yau. Sallama duka sukayi sannan Mariam ta koma gida. Al’ameen yazo tafiya ya kalli Zeezee dake ta aikin kuka har yanzu sannan a hankali yace mata “Zainab tashi mu tafi gida.” Da kaman bazata miqe ba sekuma ta tashi ta share hawayenta tabi bayansa, kuka ta cigaba dayi cikin motan wanda ko k’ala Al’ameen bece mata ba, sun isa gida ya faka suka fito. Tsaye suka tarar da Mama da Sadeeyah a parlour wane jiransu suke dama.
“Ya jikin Baban nata?” Mama ta tambaya.
“Alhamdulillah da sauk’i.” Al'ameen ya amsa.
“Allah k’ara mishi lafiya toh” cewar Sadeeyah atare Mama da Al’ameen suka amsa da ameen. “Yauwa Al’ameen ga biro da takarda maza ka rubuta ma Zainab takardanta tabar min gida yanzun nan, yarinyar data iya tasawa Mahaifinta hawan jini har kashe mijinta zata iya, wanda nikuma bazan iya affording rasa kaba, maza amshi ka rubuta mata saki d’ayanta ta tattara kayakinta tabar gidan nan at this instant.”
“Mama do I have to do this?” Ya tambaya a maraice.
“Yes Al’ameen inhar bawai so kake na sa6a maka ba, na baka nan da minti ashirin inhar baka saki yarinyan nan ba forget it that am your mother” tana kaiwa nan ta wuce ciki, kafad’ar Al’ameen dake riqe da biro da paper Sadeeyah ta dafa “do whats right Maj-Gen.” itama daga nan tabi sahun Mama. Waje ya nema ya zauna ta ina ze soma rubutawa Zeezee takardan saki yanzu? Kai ya d’ago yana kallonta a yayinda take kallonsa itama da jajayen idanunta. “Me kake jira? Ka rubuta min ka huta mana tunda kasa Baba ya la’anceni ya cireni daga jerin yaran daya haifa its what you've ever wanted dama” One more look yamata sannan ya rubuta mata takardan sakinta as
_Ni Muhammad Al’ameen na saki mata ta Zainab saki d’aya._ folding yayi a nitse sannan ya tashi ya miqa mata “gashi Zainab, amman kisani it was never my intention to divorce you, duk abinda na miji keyiwa matarsa don farinta mata nayi miki, Allah sheda na ne ban ta6a cin zalunki ba a iya zaman mu, kuma I want you to know that duk rashin hankalin da kika min na yafe miki Zainab, Allah fiddo da alkhairi daga wannan lamari, I love you so much and I’ll continue to do so till my last breathe.” Ita kanta taji ba dad’i amman ta dake tare da share hawayenta ta wabje takardan “finally am free.” D’akinta ta nufa ta had’a akwati har guda uku sannan tafito, cikin booth na motanta tasa boxes d’in sannan taja motarta ta fice.
_Back inside..._
Zaune Al’ameen yake shiru akan kujera gabad’aya ji yake inama ba’a k’addaro masa da rana kaman ta yau ba, yana son Zainab be ta6a kawowa a ransa zasu rabu ba. Duk da kalan rashin mutuncin da take masa he still loves her and so much. 20mins later on the dot Mama da Sadeeyah suka fito dag ciki ta tambaya “ka saketan?”
“Na saketa saki d’aya kamar yadda kika buk’ata Mama, har ta tafi ma.”
“Yar banzan yarinya ko hak’uri bata iya badawa ba.” Cewar Sadeeyah.
“Ai gwara da bata badan ba hakan yafi sauk’i yanzu ba shikenan ba” Mama tayi maganan tana neman zama gefen Al’ameen. Matsa mata yayi kad’an ta zauna “kayi hak’uri Baba na ni kaina nasan what you did was not an easy thing, I know how you love Zainab amman its hight time kayi hak’uri ka gane cewa bata sonka, don da har tana sonka da bazata bari ka rubuta takardan nan ba but see ko hak’uri bata bamu ba. Fatan mu shine Allah yasa rabuwan ku shi yafi alkhairi ina nan ina kan yimaka addu'a a kullum d’ana.”
“Nagode Mama, I love you so much."
“I love you more My Son” tayi hugging nashi.
***ZEEZEE
“Hello Very Own? Ban ganka ba har yanzu ganifa gaban Wikki hotel d’in.” Zeezee tayi maganan tana zaune cikin motarta da wayarta maqale a kunnenta.
“Sweetest Love am on my way” answered Adeel, daga nan tayi hanging. In second counts sega sabuwar maroon Genesis G80’n Adeel ya shigo htl d'in tare da parking not too far from Zeezee's car. Da gudu Zeezee ta fito daga motan nata ta nufi nasa yana fitowa ta fad’a jikinsa tana kuka sosai hugging nata yayi tightly, he can’t remember when last yayi hakan. “Shhh! Sweetest Love I’ve got you okay? Stop crying.” Kukan ta cigaba dayi da k’yar ya samu tayi shiru sannan ta d’ago daga jikinsa tana kallon cikin idanunsa a yayinda wani sabon sonsa yake shiganta. “Very Own Baba yayi disowing d’ina banida kowa sekai yanzu, Mama dasu Adda Marima duk they are extremely mad at me, you are the only one I have” ta k’are maganan tana kuka.
“I’ve got you Baby its okay, I love you so much, kikace Al’ameen d’in ya sakeki?”
“Yes" ta amsa tana gyad’a kai takardan ta zaro daga jakarta ta miqa mai bayan ya karanta ya yayyaga into pieces “a gobe Uncle Abdoul zeje ya samu Baba ayi mana aure mubar hell dayake nan and go back to Florida.”
“I love you Adeel” tayi hugging nasa. Hotel room ya mata booking inda ta sauk’a achan se bayan La’asr Adeel ya tafi dan zuwa ya sami Uncle nasa.
Cikin sauk'in kai Adeel yama Uncle nasa magana tare da stating masa conditions d'in kan sadaqar masa da Zeezee Babanta yace zeyi dalili kuma shine dan taje birthday'n sa. Da wannan reason Uncle Abdoul ya samu Mama ya zana mata komi itama ta amince don kuwa yadda Adeel ya tsara maganan se kaman Baban Zeezee wani Malami ne ustaz da bayison yahudanci ko kad'an, maman Adeel kuma datayi girman London bata d'au zuwa party wani babban laifi ba don haka tayi welcoming Zeezee wholeheartedly.
Kwana biyar Baba yayi a asibiti aka sallamoshi, alhamdulillah yasamu sauk'i da k'arfin jiki sosai ba laifi. Har ayau Mama batasan ina Zeezee ke kwana ba saboda ta tambayi Mariam ko ta mata masauqi a gidanta Mariam ta sanar da ita a'a. Labarin sakin Zeezee kuwa tun a daren ranan da Al'ameen ya saki Zeezee, Mama Babba ta kirata ta sanar da ita.
A yau su Mama suka dawo hida suna isa abinda Baba ya soma buk'ata shine akira masa Zeezee tazo da saurayin nata dakuma magabantansa yayi ya sadaqar da ita ya huta.
“Alhj dade ka fita daga harkan 'yar nan ina gudun maka ciwonka, kade ji abinda likita yace” Mama dake 6allowa Baba meds nasa tayi maganan a nitse.
“A'a Hafsah hankalina baze ta6a kwanciya ba se ranan da naji shi Adeel ne ko waye ya bawa Zainab kashi ya illata min ita kokuwa ya kasheta ya kai ta lahira.”
“Subhanallahi wai Alhj bazaka share maganan Zeezee ba se ciwon naka ya sake worse tukuna? Kuma da kake magana haka baza tayi zaman idda bane? Ko haka kawai zamu sake mata wani auren?”
“Zaman idda fa kikace Hafsah? Ko kin manta la'ananniyar bata ta6a had'a shimfid'a da mijin nata ba?”
“Amma-”
“Ki kiramin Zainab nace” ya fad'a in a serious tone. Shiru tayi ta gama 6alla masa Meds nasan sannan tad'au wayarta ta shiga kiran Zeezee.
Wayan nata (Zeezee) na a hannun Adeel suna zaune akan gado a htl room wayar ta shiga vibrating kasancewar a silent take. “Babe Mama is calling you” ya sanar da ita in an I-dont-care tone.
“What Mama???” Ta fad'a unbelievably.
“Yup” ya amsa tare da miqa mata wayar. “Pick it up” yayi instructing nata, ba musu ba gardama ta d'aga tare da sawa a handsfree ”Assalamu Alaikum Mama? Ina kwana?”
“Wa'alaikumus-salam kizo Babanki na nemanki, ki taho tare da Adeel nakin da magabatansa kinji?” Zuciyarta na har6awa ta amsa da “toh” tare da jira Mama tayi hanging. A hankali ta zare wayan daga kunnenta. Kallo d'aya Adeel yamata ya gano hanklinta ya tashi matsowa kusa da ita yayi tare da kwantar da kanta a chest nasa “all is going to be well okay? I've gotchu.” Kai kawai ta iya ta gyad'a mai.
****
Bada jimawa ba Zeezee, Adeel da magabantansa suka hallara gidansu Zeezee saidai shi sam Adeel d'in yak'i shiga ciki. Har parlour Zeezee takai in-laws to-be nata sannan taje tayo sallama d'akin Mama inda iyayen nata suke. Mama kad'ai ta amsa murya na rawa tana kare jikinta a bayan k'ofa tace, “sunzo suna parlour Mama.”
“Naji kije waje ki jirani.”
“Ta fita min daga gidana gabad'aya ta k'ara koda minti d'aya ne Allah ya isa ban yafe ba.” Hak'uri takeson basa amman jin haka ta d'ibi k'afa tayi waje ta samu Adeel. Cikin mintuna k'alililan Baba yayi sadaqar Zeezee wa Adeel da shaidu uku kacal se waliyai ya amshi sadakinta ma yak'i. Suna kammala duk abinda ya kamata Zeezee da mijinta dakuma in-laws nata suka dawo gida. Achan Mamin Adeel ta had'a grand celebration nata luncheon sukayi na kece raini wanda gun event d'in seda Zeezee tayi kuka kasancewar duk inda ta juya bata ganin nata sena Adeel seta tuna bikinta da Al'ameen dangi har sunyi mata yawa ga kuma sisters nata uwa uba mahaifiyarta nan kome aikin gidansu babu. Anyi event lafiya sumul ba yadda Mami batai da Adeel ba yabari su kwana nan gida da Zeezee yak'i shi sam se a hotel, can d'in suka nufa suna isa d'akinsu suka watsa ruwa one after the other sannan sukaci abinci.
Sede daga yadda Zeezee ke acting Adeel yagano she is missing home tana zaune a one end of the bed tayi shiru ya k'ariso ya zauna kusa da ita, “Sweetest love?” Jikinsa kawai ta fad'a tare da sa wani irin kuka me tsuma zuciya, solacing nata yayi tayi seda tad'an rage kukan, cikin sautin kuka tace, “Very Own please promise me that you'll never leave my side, and that you'll love me forever.”
“Ofcourse yes Sweetest Love you know how much I love you right? Add more to it, I'll never leave your side for better or for worse.” D'an sanyi aranta taji batasan cewa na miji ba d'an goyo bane. Hira sosai Adeel ya riqa janta dashi seda ta warware, ba wanda yayi tunanin yin sunnah raka'a biyun da ma'aurata suka saba yi. To twelve yace su kwanta kafin nan seda ya 6allo wasu capsules k'waya biyu da ruwa a cup ya miqa mata. Tana miqe kan gado ya tada ta, “Sweetest Love here tashi kisha kinji?” Tana miqewa ta tambayesa “magani kuma Very Own?”
“Yes” ya amsa.
“What for?”
“Don't you trust me Babe?”
“I do very well Very Own but what are they for?”
K'arya ya mata “pain killers.”
“But am in no pain Very Own.”
“Come on! Sweetest Love” yayi maganan tare da zama a gefenta “must I dictate it out? Ko kin manta tonight will be our...” Sekuma yayi shiru. Gano abinda yake nufi, seta saki murmushi kad'an “don't worry I can bear that pain.”
“Nahh you can't, and even if you can I wont let you kar6a kisha kinji lets sleep.”
“Anything for you Very Own, thank you” amsa tayi ta had'iye seda yaga wucewan k'wayayin a gullet nata ya miyar da cup d'in tare da kashe musu wuta suka kwanta warm and close inda a daren ranan Adeel ya kar6i hak'k'insa as yadda Zeezee tayi promising nasa. Ba k'aramin dad'i yaji ba jin shi ya bud'e ta shine first man to know her, dama its what he has ever wanted pride nata. A daren ranan jinsa yake on top of the world. Wahala sosai yabawa Zeezee amman don yadda takeson sa takuma keson ta farinta mai rai bata nuna masa sosai ba. Seda ya gamsu iya gamsuwa sannan ya barta alokacin har wani sama-sama nishin Zeezee ke don azaba da wahala hawaye se ambaliya suke a fuskarta.
A jikinsa ya kwantar da ita tare da pecking gashinta yana share mata hawayen, “thank you Sweetest Love you made me the most happiest man on earth today, I wont ever forget this, I love you.” Da k'yar ta iya zagaye hannunta akan cikinsa “I love you more Very Own morethan you can ever imagine.” Yana rubbing bayanta back and forth har ya samu tayi bacci sannan shima yayi.
****
Basu suka tashi sallan Asubah ba se kusan to 7am. Nanma da k'yar yasamu ya d'aga Zeezee ya kaita bathroom sukayi wanka sannan alwala sukayi Sallah, pain killer ya bata suka koma bacci se after 11 suka tashi Zeezee is feeling a bit better yanzu. Wanka Adeel ya shiga yayi yana fitowa Zeezee itama ta shiga alokacin ne Mami ta turo musu breakfast, shi da kansa yayi feeding nata. Da suka gama ci ne y juya ya kalleta anan ya gano she is weak k'arfin hali kawai take. “Sweetest love?” Ya kirata romantically. “Na'am Very Own” ta amsa a kasalance.
“Are you still feeling the pain?” kai ta kad'a masa amman yasan k'arya take sekuma ta basa tausayi daya tuna yadda yayi forcing kansa a cikinta jiya. “Am sorry” ya fad'a a hankali.
“For?” Ta tambayesa all confused. Hannunta ya had'a da nasa sannan yace, “for last night-” da sauri ta katsesa “you don't have to Very Own I'm all yours, my pride is yours and you've taken it away why are you apologising?”
“Is that so?” Ya d'aga mata gira teasingly, d'an murmushi ta saki ”yes Very Own.”
“Thank you okay? Yestarnight was great I can't tell you how happy you made me I love you.”
“I love you too” ta amsa shi nan ma a hankali. Wuyansa yayi bending tare da owning lips nata for some time sannan yace mata, “are you ready?”
“For?”
“To fly to Florida.”
“Florida kuma how?” Ta tambaya confused.
“Yup there I promised you, zamu bar nan for now muje chan and get a break from all these... You know tension.”
“Very Own but how-”
“How did I got ur passport?” Ya katse ta. “Don't worry acikin jakanki na d'auka the other day, so are you ready?”
“Are you serious Very Own?”
“Yes Sweetest love are you ready?”
“Definately” ta amsa all excited. Pecking nata yayi a lips “good then flight namu is by 1am tonight.” Hugging nasa tayi “I love you so much.”
“And I do too.” Yayi responding.
*~ *~ *~
Through out Zeezee ta wuni ranan tana expecting call from Mama amman shiru abun ba k'aramin damunta yake ba amman batason ta nuna wa Adeel. A rayuwa in akwai abinda ta tsana shine tashin hankalin Adeel, wannan kenan!
Zuwa 9pm na dare tana maqale jikin Adeel ta d'aga wayanta for the 1000th time don ganin ko Mama ta kirata, da Adeel ya lura da frequent duban screen da take se yayi deciding da bazi ya tambayeta. “Babe?”
“Yes Very Own?”
“Are you expecting a call?”
“Nnn... No” ta fad'i finally.
“Are you trying to lie to me?” Ya tambaya a hankali.
“Am sorry is just that na d'au ko Mama zata kirani amman shiru Very Own Mama dont care about me anymore.”
“But I do Sweetest Love, you have me, I shall never turn my back against you I promise.”
“I know Very Own but it still isn't enough she's my mom.”
Gashinta ya shiga shafawa a hankali in a soothing manner “I know Babe am sorry kinji?”
“Its not at all your fault.”
“I can be anything for you Babe, a father if you need me, a mother, a brother and also a sister so kidena tada hankalinki let them be and move on okay?” Kai ta gyad'a tana share hawayenta “should I call her instead?”
“You don't have to ita da kanta zata kiraki idan ta jiki shiru.”
“Are you sure Very Own?”
“You don't trust me then , idan na samu misunderstanding da Mami ko Papa before he died da kansu suke nema na ko suban hak’uri ma so karki damu, or dont you trust me?” Take ta d'ago daga jikinsa tare da rik'o hannunsa “stop saying that you know I do alot.”
“Thats my woman get some sleep zuwa 12:00 zamu wuce airport.” Har ta miqe sekuma ya riqo hannunta “but first your medication.”
“Very Own am really okay no more pain.”
“I insist” kad'ai yace mata sannan ya b'allo capsules d'in ya bata yauma kaman jiya seda ta had'iye yabar wajen. Kamar yadda ya fad'i 12am d'in ya tasheta suka shirya zuwa airport kafin su fara boarding Zeezee taso kiran Mama atleast ta sanar da ita amman duk tsoro take kar Adeel ya kamata idea'n tura text message sam bezo kanta ba haka tana ji tana gani ya amshi wayan nata ya musu switching off tare da nasa.
*****
Few days later, jin shiru Mama ta saci jiki ganin Baba na bacci tayi site na Omar ta gwada kiran layin Zeezee don jin ko lafiya tunda tun ranan da aka bata wa Adeel bata sake jin motsinta ba. Abun mamaki kota kira switched off takeji Lubiee ta kira a k'arshe inda take sanar da ita ai Zeezee na Florida ayanzu haka. Mamaki ne ya ziyarci zuciyan Mama, har Florida? Ta tambayi kanta. Shin Zeezee wacce irin d'iya ce ace zata tafi har Florida amman bazata sanar da ita ba, ba k'aramin b'aci ranta yayi ba wanda yakaiga koda da Lubiee ta tura mat digits na Zeezeen ma k'in kirarta tayi, aga wanda ze nemi wani.
*~ *~
Life moved on, Maj-Gen yakasa moving on se a hankali al'amarinsa ya soma dai-daita ya fara rage tunanin Zeezee if not ata farko-farko har Mama Babba ta soma regreting sasa sakan Zeezee da tayi saboda ita sheda ce akan kalan son da Al'ameen keyiwa Zeezee but tasan hakan is for the best shiyasa koda yasamu ya kar6i leave a office tasasa ya dawo gida a wajenta ita da sisters nasa ya zaun suna kula dashi, alhamdulillah yanzu an samu massive improvemet physically tunda har ya koma office amman psychologically kullum seyayi tunaninta always all the time saidai bayi nuna musu.
Adeel de a kullum be fasa baiwa Zeezee capsules dayake bata ba wanda koda zatayi mar tambayan duniya ba fad'amata zeyi ba ganin ransa na 6aci anytime tA tambayesa maganin menene yasa tama dena tambayar nasa yanzu ita wai she trusts him. Duk wani abinda tasan yana iya had'asu ma hasali avoiding take, bata chatting kap dakowa inbanda friends nata mata sanin kishi irin na Adeel. Hakan yasa basu ta6a samin wani understanding dashi Adeel ba, kullum saidai suyi wanka su fita yawo shikenan, duk abinda yagani me kyau ne yana k'ok'arin siya mata suna zaman lafiyansu lau, ahaka har suka samu 3 months Zeezee bata sake ji daga gida ba.
Koda Mama ta bawasu Ya Ibraheem labarin abinda Zeezee tayi mata fusata sosai yayi yace sam se Mama tabasa digits na Zeezee ya kirata yaci mata mutunci amman Mama ta hanasa surely one day she'll need them saboda jini ba abu bane na wasa.
Su Adeel sun samu 3 months 1 week a Florida yace shi zaman chan ya ishesa yanason ya dawo gida. Zeezee tafison zaman chan sabida gabad'aya ta manta da problems nata har wani kauri ta k'ara, tanason cemasa sud'an sake prolonging zaman nasu amman tasan halinsa bayi son ana questioning actions nasa. Haka cikin kwanciyar hankali suka shirya suka dawo Bauchi, Nigeria inda ya d'au musu d'aya daga cikin 2 of his inherited houses as duk sauran ya siyar dasu ya k'arar da kud'in a hosting parties, siyan motoci and other useless expences. Bayan sunyi settling Zeezee ta samu time ta kira Mama a waya suka gaisa ko nuna mata abinda tayi ba dai-dai bane Mama batayi ba saboda there is no point ai ba yarinya bace. Lafiya k'alau suka gaisa sukayi sallama.
0 comments:
Post a Comment