wai ana kiran amira inji wani yaro amira ce
kwance a kan tabarma tana danne-danne a
'wayarta tamkar ba ta ma san yana yi ba.
_Ummansu da ke cikin dakinta ta fito ta
duBi‘yaron. “Kai je ka ce masa tana zuwa' Amira
ta yi saurin juyowa ta ce da yaron. ' ‘ ' “‘Ka ce
waye yake sallama?” Ummansu ta kwada mata'
harara’. “‘Au. da kina ma jinmsa ki ka yi masa
shiru saboda ba ki san muhimmancin sallamar da
yake yi ba k0?”
Amira ta mike tana murtsike idanu. “Umma ban ji
shi ba ne, game din nan ce ta dauki hankalina”.
Umman ta-sake Watsa mata kallon rashin yarda,
sannan ta ce'. “Allah ya kyauta miki: Tayi kicin
tana duba miyar da Amira ta dora. Yaron ya
daWo ya ce “Wai Alhaji Saminu ne Amira ta dan
yi wani tsaki a‘ ciki, sanna tacewa yaron. kace ga
ni nan zuwa”. mayafinta ta tita. ta yafa' ta isa
soran gidan kamshin turarensaya mamaye ,wajen
Yana ‘tsaye tsadaddiyar shigarsa da ya saba yi.
Wannan karon blue din shadda ce mai daukar ido
'da' taushi ga sheki, ya: Sha‘ aiki da hula a.
kanshi,’ :kyakkyaWar fuskarsa mai dauke da
murmushi' a .koda yauShe na
' nuna Kuruciyarsa ko ba a fada ba za ka
gane yana‘ 'cikin ganiyar kuruciya ne da'
zaman dirshan da naira ta yi masa‘ Amira
Gimbiya; Amira ' zonan_sarauniyar mata”.
' Ya ’furta’ da salOn' Wake‘Sun'dukima suka yi
dariya, abin da ya; f1 komai barge ta; da shi
kenan,‘ Sanya mutum nisha'di ga barkwancinsa
yadda ta fito
' da ya yi dariya.
‘ Ta gyara tsayuwa hade DA bude masa; fararen
idanunta masu ta lumshe su. ‘ Kallonta Yake“Yi‘
babu KO kibtawa
'komai nata sake kidimashi yake‘yi
cikin wani‘yanayi ya ,ke amsa gaisuwar da
take yi masa.‘ Ita kanta ta lura da kallon da
yakeyi mata ta 'hadiye Wani ya tsaya' mata ta
mai da idanunta kasa. Ya Kara taku biyu 'zuwa
inda ta ke
motata kadai zai gani ya gane ina nan, kin ga
kuma hakan ba girmana bane a idon jama’a, ki
amince min mu shirya wajenda” za mu dinga
haduwa kawai, kinada ilimi ya kamata ki gane
cewa wannan zancen ya zama tsohon yayi ko
ince“ na talakawa ne, amma ga gurin hutawa
kala-kala, ki zabi ko’ina a fadin Kasar nan mu je
mu tattauna Amira in har kina kaunata; wannan
duk ba Zai gagara ba”; Tunda ya soma fadar
bukatarSa kanta ya soma daukar zafi tana
matukar son Alhaji Saminu a ranta,‘ amma .irin
wadannan wayayyun kalaman nasa. ke. bata,..
mata rai da Shi. . ‘ Ta hasala sosai, ta sauke
nannauyar“ ajiyar zuciya, sannan ‘tadago ido ta
dube' shi na tsawon Sakan biyu. Ya kasa 'dauke
nasa idon a kanta, yana binta,_.da kallon karfafa
gwiwa a kan manUfarSa..
“Alhaji ina ganin wannan ba shi ne - abu mafi
muhimmanci a tsakaninmu ba , saboda haka bai
kamata ka kira shi rashin
kauna ba”. Ya wani "Ware idanu yana fadin. . “Ya
ya za ki kira lokacin da za mu ’ samu damar
tattauna mara muhimmanci a gare mu? Lokacin
da za mu sake ne fa mu fahimci juna fa, haba
Amira
‘ Ta hade yatsun hannunta biyu har sukayi ‘yar
Kara.
“Babu wani abu da baki zai furta wanda ba zamu
iya yinsa a nan ba... ba mu tSaya bata lokacinmu
zuwa wani waje. Wanda waje ne da addininmu da
al’adarmu basu koyar‘ da mu ba...”
motsin shigowar da suka ji ne“ya sa . shi'yin
shiru daga abin’ da yake shirin fada mata,
mai'Shigowar ta shigo soron ‘ sannan tai
sallama. Dukkansu' Suka amsa mata Alhaji
Saminu ya gaishe ta ganin‘
tana kallonshi.
Ta amsa, ta shigesu, Alhaji Saminu ya ce.
“Kun yi kama sosai, yayarki ce?”
Ta girgiza kai, tace
“Kanwar'Babana ce”, "
Ya ce, “Ya yi kyau”. ’
Sannan ya gyara tsayuwa ya ci gaba.
“Kin ,kasa fahimtata saboda ba kya sona, kina
son yi min kora da hali ne kawai, amma ya dace,
ki gane bambance-bambance masu yawa a
tsakanin tsayuwarmu a nan da samun -
keBantaccen waje na musamman, amma' zan ba
ki lokaci ki yi shawara, sai dai ni daga yau din
nan idan har ba ki sauya
ra’ayi ba ba zan sake zuwa na tsaya a nan ba.
Irin ‘zamanin da ki ke fada‘tuni ya jima da
wucewa; komai ai tafiya yake da .zamani, ki yi
shawara da ,zuciyarki ni
zan wuce. Duk abin da kika yankesai na ji ki a
waya
Ta bi shi da kallo, ya fice ba tare da ya
waiwayota ba. Ita ma sai ta juya ta shiga gida,
ita kam ta dauki wannan rana ranar rabuwarsu ta
har abada, domin ba za ta taBa yarda ta bi abin
da yake nufi din ba.‘
Tana shiga tsakar gida ta tarar da Aunty Ummce
da. Ummanta a kan tabarmar da ta tashi, » suna
hira har da Kyalkyala dariya'. Abin da ya sata
cikin mamaki kenan, domin Aunty Ummee idan ta
zo gidansu ban da harara da tsaki babu abin' da
ta keyi wa Ummansu ita din ma ba haka ta ke
shiga ba, daga gaisuwa za ta shiga sabgar
gabanta.
:‘Ba ta gama wannan mamakin ba Aunty Ummi
ta Kwala mata kira. ‘
“Zo, ya ,‘yar nan mai Kashin . . arziki, ashe Alhaji
Saminu ne yake Zuwa Wajenki?”
Yarinya kin yi gadon arziki”.
Ta soke kudinta~ a, jaka, sannan ta soma duba
kayan kwalin atamfoii ne super guda biyu, da
leshi guda biyu, kowanne da kalar mayafinsa. Sai
takalmi da jakunkunansu guda biyu hade da kudi
dubu ashirin a kai.
. Daya kwalin kuma mayukan shafaWa ne da na
Wanke gashi da turaruka,
komai saiti. Ta dubi Umman Su Amira, ta ce
“Wannan lefe kuma sai, ya ya?” Murmushi
Umman tayi tare da godiya ga'Allah a
cikinzuciyarta, da Allah ‘ ya kawo ranar da za a
ga wani abu a yaba a
tare da ‘ya’yanta. Malam Bashir ne ya shigo da
sallama. Hayaniyar me ku ke yi haka?”
Aunty Ummee ce ta dago kai fuskarta cike da
mujrmushi.
“Kayan da aka kawo wa Amira muke gani
Malam Bashir ya sauke ajiyar Zuciya, domin ya
dauka fada ake yi da Umman kamar yadda aka
saba.
Kallo daya ya yi wa kayan ya dauke kai. Can ya
zauna a kan wani tudu da ya
saba‘ zama, Ummansu ta tashi ta shiga kicin dan
ta ba su waje Yaya, Amira ma ta mike ita ma ta
shiga daki.
Aunty Ummee sun gaisa da Alhaji Bashir ta fada
masa sakon da mahaifiyarsu ta turota ta fada
masa, wato zuwa gaisuwar mutuwa a can garin
mahaifisu da ke karamar hukumar "‘Kura gobe da
safe, sannan suka yi sallama ta tafi
Malam Bashir mahaifin Amira su shidda iyayensa
suka haifa, daga babbar yayarshi Halima, sai
wanshi Alhaji Musa
sannan shi da sauran kannenshi duka duk da
mala bamai hali bane
Yana da rufm asiri domin gidan da suke ciki
gidansa ne na kansa. Yana sana’ar sai dakayan
masarufi a kasuwar Kurmi, Allah ya ‘azurta _shi
‘da ‘ya’yanshi takwas Wanda matarsa’ Amina ta
haifar masa Amira ita ce babba, sannan Saifullahi
da Mukhtar, Hauwa, Aina’u, Mahmud Fatima tana
goyon Umar.
.Rayuwar gidan rayuwa ce wadda iyayensu suka
shimfida musu ita bisa‘ doron tarbiyyar addinin
musulunci musamman 'Amina da ke kula da
mijinta da ‘ya’yanta cikin rufon asiri da
mutumtaka wannan ‘ne 'ya janyo mata
kyakkyawar tsana wajen dangin Malam
Bashir.
Suna ganin ba ya shawara da su bisa dukkan
lamarinsa .sai matarsa. Kalmar nan ta ta shanye
shi. ta dora daram akanta. _
‘ Shi‘, kam ~hankalin Aminatu da nutsuwarta shi
neya fizgi hankalinsa, su
duk sun yi bacci, tunanin da ya addabi zuciyarta
shi ne ,ya hana idanunta runtsaWa.
Hakika tana matukar son Alhaji Saminu tana
kuma mafarkin ace shi ne mijin aurenta, domin ba
ta hangi makusa a tare da shi ba, sai dai a yau ta
gama tabbatar da zargin da zuciyarta ta ke yi a
kan irin son da Alhaji saminu yake' yi mata ya
sauya tunaninta a kansa na son ya Kulla
kyakkyawar alaka ta aure a tsakaninsu.
A yau kam ta tabbatar da Alhaji Saminu yana son
ya bude idonta ne da soyayyar zamani, yana
neman ya yi mu’amalar banza ne da ita duk
bayyanar soyayyarsa gare ta sha’awa ce kawai!
Babu batun. so na gaskiya a tare da shi, ta
matso wasu guntayen Kwalla daga idanunta
lokacin da ta tuna da _irin farin cikin da Ummanta
ta ke ciki a ,yau tun zuwan Alhaji Saminu wajenta
yadda
Aunty Ummce ke kwarzanta dukiyarsa da
kyawawan halayensa tare da iya rike iyalinsa.
Sai dai duk wannan ya zamo ta baya ta rago- a
gare ta, domin tana ganin yau rana ce ta karshe a
tsakaninsu, rabuwarsu tazo
Ta sake yin juyi tabbas tana son ta zame wa
mahafiyarta mai share mata hawaye a kan gorin
da dangin miji keyi mata, musamman a ‘ cikin
‘yan kwanakin nan a kanta wai su yarinya ba ta
taBa gama sakandire ba mijinta a hannu ba, duk
cikin danginsu sai dai ita suna ganin nauyin jinin
da ta yi ta kwaso shi ne a dangin uwarta, su kam
farin jini gare su.
Ba Ummanta kadai ba har ita kanta maganar ta
daki qirjinta, kuma sanadiin furucin ne ta warware
duk shirin da ta yi na ci gaba da karatu. Wannan
shi ne dalilin da ya‘sa ta Ki ba wa samari fuskar
da 2a su
zo da maganar manya gidansu, ba wai rashin
manema ba kamar yadda suka zata.
' Mahaifiyarta ta san burinta na son karatu mai
zurfi tun tana ‘yar Kankanuwarta, sai dai ta kan
gargadeta a kan kada ta mayar da wannan
buquta fiye da yin aure, sam aure ba ya hana
neman ilimi. . ’ - “Amira kada ki kori manemanki
idan Allah ya sa kina da rabo a karatu sai ki yi
shi a dakinki”.
Duk lokacin da ta ji Ummansu na fadan haka
tana jinta ne kawai, amma Kudirinta na sai ta yi
digiri ta soma aiki sannan za tayi aure yana nan
a cikin ranta. Tunaninta na nuna mata mazan
yanzu mayaudara ne :zasu' iya amincewa da
maganar karatu sai kun yi aure ‘su Ki amincewa,
ita kam ba ta son abin da zai hana ta cikar nata
burin na karatu
Lokaci daya ta sassauto daga nata burin zuwa
namahaifiyarta, domin gorin da aka yi wa
mahaiflyarta gori a kanta‘ sai da ta zubar 'da
hawayen baqin ciki, sannan ta sha alwashi za ta
yi aure aure kuma na nunawa sa’a domin a can
ma ba ta taBa yin ragon saurayi ba, rashin
amincewane kadai ya sa 'suka kasa gane tana da
farin jinin masu hali ma kamar‘yadda Kawayenta
ke fasa mata kai da cewa, ita matar manya ce
Kamar ba su yi Karya ba, idan ka dubi diri da
kyan surar da Allah ya ba , Amira sunan- da mafi
yawancin jama’a ke kiranta da shi, amma usulin
sunanta Khadija. Ta ci‘sunan kakarta ta wajen
uba ne shi ya sa ake kiranta da‘ ‘ Amira.
- Fara ce tas, mai .matsakaicin tsawo,‘ tana da
dirin jiki mai daukan hankali ba ta” da kiba can,
jikinta a murje yake, Tana da dara—daran
idanu wadanda ke kara fitar da sirrin kyan :
fuskarta.
Hancinta bai fiya tsawo can ba, _ amma ba gajere
bane tana da dan karamin baki, kallo daya za ka
yi wa Amira ka gane " kyakkyawa ce.
Tun tana ‘yarinya Karama mutane da dama ke
cewa, kamannin kakar Babanta ta dauko Ladi
buzuwa, har ‘tsayin gashinta Usulin Ladi Buzuwa
a can Agadaz kakan Babanta ya auro ta k0
‘ya’yanta ba su yi kama da ita kamar Amira ba,
inji wadanda suka yi wa Ladi Buzuwa farin sani
Amma dirin jikin na mahaifiyarta ne. domin ita
Ladi siririya ce matuqa, tun Kuruciya har tsufanta
ba ta yi kiba ba.
Sun hadu da Alhaji Saminu a wajen bikin kawarta
Nafisa,ne yana daya daga cikin ', abokan ango,
ya kuma ziyarci 'wajen
dinner din da ake. Tun da ya kyalla ido ya
ga Amira hankalinsa ya gaza kwanciya, ya yi
dace da ta amshe shi hannu bibiyu karo na hudu
kenan yana kawo mata ziyara bayan waya da ya
ke kiranta sau hudu k0 sau uku a kowacce rana.
Komai na Alhaji Saminu abin burgewa ne shi ya
sa cikin kankanin‘ lokaci ya shiga ranta sai dai a
zuwansa na biyu kadai ya soma rikita lissafinta
da buqatunsa da suka yi wa kanta girma, har ta
ke nazari a kansu.
Daga karshc ta ajiye shi a matsayin ba abokin
tafiyarta ba, domin ita aurensa ne burinta. '
Dukkan yadda zuciyarta ke azalzalarta da tunanin
Alhaji Saminu ba ta taBa sha’awar kiransa a
waya ba, haka shi ma bai sake bi ta kan tunanin
sake zuwa wajenta ba, musamman a halin yanzu
da ya sake haduwa da wata yarinya Sa’adatu
da ta mallaka masa komai nata su ke
sheqe ayarsu kaman ba gobe
Bankada
Chapter2
watsewarsu gaba daya ma ya manta da batun
Amira a rayuwarsa
Tsawon watanni. biyu ba ‘kira ba sakon Alhaji
Saminu, a gidansu‘duk saurayin da Amira ta
kwatanto sai ta ga bai kai Alhaji Saminu dacewa
da‘ ita ba, saboda haka ta dawo da dabi’arta ta
Kin "
kula samari k0 an yi sallama da ita ba ta fita. “
Wannan lamari ya dami Umnmnsu tana ta saka
da kwancewa a kan ‘yartata na abin da ya sa ta
ke korar samari ita tafi son ‘karatu
kuma,.Babanta ya ce ba a ‘gidanshi ba sai dai
gidan mijinta. Abin ya'dame ta sosai, har wata
‘rana suna tsaka da ninke kayan kannen Amira
Ummansu ta‘dube ta. ‘
“‘Amira Wai ina mutuminnan na na kwanaki da
yake zuwa "wajenki, ya daina zuwa? K0 shi ma
korar tasa kika yi. ne?”
Amira ta 'dago ‘kai kamar Ummanta
san zanccn data ke yi kenan a zuciyana, ta ce.
“Umma kina nufin Alhaji Saminu?”
Ummansu ta ce, “Eh ina ga shine mutumin da
Umme ta ce ta sanshi”.
Amira ta dame fuska ranta ya sosu, domin yanzu
nadamar haduwama da Alhaji Saminu kawai ta ke
yi, ta ce
“Umma tafiya ya "yi, ba ya Kasar ba korarsa na
yi. ba”
' -- Umman ta‘ ce “Eh to Allah ya sa da gaSke ki
ke yi 'Amira, domin lamarinki mamaki ya ke ba
ni. Abin da yasa na yi miki maganarsa‘ na ga
kamar kin fi sonsa a cikin. manemankine, ba
kuma dan kudinsa ba, domin idan kudi ne baa
kya Ki Alhaji Auwalu ba, abin da nake so ki gane
Amina, aure shine mutumci' da martabar duk diya
' mace, idan ba da gaske shi Saminun yake ba, to
ki daure ki amshi maganar Sulaiman
a yi auran nan naku hankalina mayafi
kwantawa dashi. Tace “To Umma’.
. NURADDEN
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, san‘nan ya yi
miqa tare da salati ya murza _ yatsun hannunsa
ya dora su a kan sitiyarin' motarsa tare da
hamdala. Ya dubi agogo Karfe biyu da rabi na
rana, ya yi sauri ‘kamar yadda ya So, amma ya
gaji liKiS tunda ya dauko hanya daga Abuja k0
sau daya bai‘ tsaya hutu a hanya ba, har ya iso
garin na Kano ta dabo tumbin giwa. '
Yunwa da gajiya, babu abin da babu a jikinsa,
uwa~uba kewar matarsa da ta
hana zuciyarsa sukuni, har sai da ya yi asubancin
zuwa gare ta. Ya shafi tsakiyar kansa yana
tunanin
irin yadda zai gan ta, da irin farin cikin da. za ta
yi idan ta gan shi da wuri haka,
saBanin yadda ya saba zuwar mata da la’asar.
Ya tsaya a wani store ya siya mata cake da ice
cream sannan ya jidar mata turaruka masu tsada
ya hada a cikin sauran tsarabar da ya yi mata
tun a Abuja ya nufi hanyar gidansa. _
Samarin da ke zaune a kofar gidan suka yi masa
barka da zuwa, ya amsa ciki- ciki domin shi ba
don Son ransa suke tare masa a gida ba.
Ya ajiye motarsa ya nufi ciki, sai dai tunda ya
doshi Kofar shiga ciki yake jin hayaniya kamar‘
ana ‘wani sha’ani‘ a gidan ya sa kai da sauri dan
idonshi ya gane masa abin da ke faruwa.
. Wadansu yara ‘yan samari- ne a kofar kicin din
suna ferayar doya su biyu, daya kuma na gyaran
kayan miya.
Duk da bai san sunan yaran ba, ya san
fuskokinsu almajiran malam ne Ya bi tsakar gidan
da kallo ledar ' pure water, bawon rake da na
gyada ban da na doyar duk ya tsallake su ya
shiga tsakar gidan. Hango kofar dakinsa a bude
DA yayi ne ya hana masa amsa sannu da zuwa
da ' yaran. suke yi masa. Ya hada da sauri har
da sassarfa domin ya shiga. ‘
Sabi’u ya gani tsaye da tsintsiya a hannunsa da
alama motsin shigowarsa ne . ya sa shi dagowa
daga Sharar da yake yi.’ . '
Ya daka masa tsawa.
.“Kai malam fita ka ba ni waje”
" Sabi’u na kokarin gaida shi ya juya gwiwarsa a
sage ya fita' da tsintsiya a hannunsa.
zuciyarsa ta gama hasala yanzu wannan jibgegen
katon ne baligi a dakin baccinsa da sunan yana yi
masa Shara? Yana da iyali ba babu ba. .
Ya‘ ajiye ledar hannunsa, sannan ya juya
zuciyarsa na tafasa. Falonta ya nufa,
sai dai ta tarar da shi har ya shiga bandaki jikinta
ya yi sanyi ta zauna bakin‘ ‘ gadonshi tana sake
—saken yadda za' ta yi'ta taushi zuciyarsa daga
dukkan zafin donta lura ya yi. fushi Ya turo Kofar
ya fito da alama alwala‘ ya yi bai k0 kalli inda ta
ke ba ya shimfida darduma ya tayat da sallah. ‘
'- Tana nan a zaune ta rafka tagumi wasu
addu’o’i ta ke karantawa a zuciyarta, har lokacin
da’ ta fuskanci ya idar da sallar‘ ~
Ta mike tSaye zuwa inda ya ke. “ “Nura kayi
hakuri, ban san. zaka dawo yanzu ba..” ' Ya
katse ta,“‘Sai zan dawo za ki san ” abin da ya
dace da ke da wanda bai dace ba? Ina ilimin da
kike da shi yake k0 dama ba‘ don ki yi aiki; da
shi aka koya miki shi ba da za ki dinga kawo min
Katti gida ' kina. zama a cikinsu‘!” Nan da nan
"ta'hade fuska, ‘abin.zuciyarta
ta raya mata so ya ke yi ya raba ta da kowa ba
ya kaunar wani ya rabeta idan kuwa ta sakar
masa fuska haka zai - korar mata duk ja‘ma’a ya
tafi can wani gari ya bar ta a gida ita kadai
kamar mayya.
Ta sake hade fuska, ta ce.
nura su Sabiun ka ke kira Katti'sai ka ce baka
sansu ba? Ni fa ba za ka raba ni da su ba tunda
tare ka ganni da su...”
“Shut up!” ya yi furucin da har sai da hantar
cikinta ta kada. _ ’tafi ki bani waje_,>bana son
irin wannan shirmen naki
"“Zan bar. maka. daki amma ka sani yadda ka
ganmu da su haka za ka bar ni da su”. Ya dauke’
kansa.kawai .._yana ‘ maimaita hailala, domin
yadda ~yake ji- ‘ a, ‘ zuciyarsa' ba‘don girman
mahaifinta a , WAjenshi da babu- abin" da zai
hana“ shi
sakin aurenta k0 ya lakada mata dukan da .‘ za
ta kasa tashi, sai dai, kash 'tana da matsayin
‘yar malaminsa da yake da girma da kwarjini a
idonsa, ai k0 kare ya ba shi ba zai dakar masa
shi ba bare mutum mai darajar mace kuma ta
aure
Yunwa da gajiyar da ya yi duk sun kau, sai dai
bacin Bacin ran 'da ya keji a cikin‘ kirjinsa. .
Malam Balarabe mahaifin Bahijja malamin
mahaifinsa ne domin duk 'a yammaci yana zuwa
wajensa karatu. Babban malami ne da
shahararSa ta? mamaye Bangarenssu, ' yana da
yawan dalibai‘ almajirai amma , ya daina ‘
karantarwa, sai dai har zuwa‘ yanzu ana'
karantar da almajirai a wani fili nasa da ke: kusa
da gidanshi yana dai zama a dakin soron gidan'
yana’ kar‘Bar bukatu na maza da mata masu
neman bukatu na neman, taimako da addu’a.
Yana da matan aure har hudu da tarin ‘ya’ya
maza da mata nasa da na ruKO.
Yana da matukar girma a idon jama’a sosai, ana
ba shi girma domin idan yana tafiya da Wiya ka
ga mutum sama da biyu a bayansa, sai abin da
ya zana hakan.
Yadda mahaifin‘ Nuraddcn Alhaji Lawan ke
girmama Malam Balarabe shi ya sa Nuradden shi
ma bai dau lamarin Malam Balarabe da‘ sauki ba.
Bai dada ganin girman lamarinsa ba, sai da
mahaifinsa ya kai shi akan buKatar yi masa
addu’a a kan neman aikin da yake yi domin
lamarin yake tafiyar masa
daidai ‘yadda ya dace. “ Cikin kwana biyu wanda
ya ke wajensa ya tura shi zuwa Dubai zaBo musu
wasu kaya da ake so. ‘
Komai na tafiyar nawa Nura ,daidai har yaz0 shi
ma yana zuwa ya dauki karatu a
wajen malam in yana gari.
Sun shaku Kwarai da Malam har ya zama Nuran
kan yi 'Wasu shawarwari da Malam don shi ma
haka ya zama ba shi da shamaki a ko’ina gidan
Malam tamkar dan cikinsa haka ya dauke shi
wani yammaci bayan sun gama karatu da Malam
ya dubi Nuradden ya ce
“Kai ma fa kana daga cikin angwayen wannan
shekarar, zan aurar da kai tare da ‘yan uwanka,
amma ba dole zan yi maka ba idan kana da wani
hanzari sai ka fada min shi, idan kuma babu ni
na zaBar maka matar da zata dace da kai”.
Duk kunya ta lulluBe Nuradden, kansa na kasa ya
ce.
“Malam ba ni da wani hanzari a kan abin da ku
ka zaBar min”.
Malam ya yi mumushi har ya dafa'
kafadarsa, ya ce. , “Allah ya yi maka albarka
Nuraddcn."
Bahijja ita Ce yarinyar da na“hada ku
Isyaku kuma Maimuna, Basiru kuwa Hamida”.
Nuraddcn cikin zuciyarsa ya soma laluben wacece
Bahijja cikin yaran gidan, duk da yawan shigarsa
gidan bai tantance ‘ da sunan ‘ya’yan Malam din
mata ba, domin babu wani abu da ya ke hada su
duk Shigar da yake yi yawanci saman malam din
yake hawa, sai dai k0 shi ya aike shi wajen
matansa k0 ‘ya’yansa maza, da ya . fadi aiken
ya ke fita ba ya zama cikin gidan.
Zuciyarsa ta soma hasko masa wace ce Bahijja a
cikinsu, ya dinga addu’ar Allah. ya sa ‘yar gidan
Hajiya Kaltume ce, domin yana son matar tana da
kirki sosai, sai dai ya kasa samun zaBi a cikin su
ukun, k0 wace ce ma a hada shi da ita, ya san
bai yi zabe tumun dare ba.
Iyalan Malam zasu zamo ababen
alfaharin mazajensu, duk da ba lokacin ya
zabarwa kansa aure ba, amma ya ji dadi kwarai
da ganin Bahijjarsa ta kwanta" a ransa sosai,
musamman da ya luratana cikin farin ciki, ta
karBe shi a matsayin mijin aure. A taKaice tana
sonsa.
Yadda ya tsara wa kansa, zai soma gininsa-kafin
lokacin biki, amma Malam din ya ce kada ya
daga hankalinsa, ya yi gininsa a sannu domin ya
tanadar musu gidan zama a bayan gidansa ya
kuma ce ya yafe duk wani kaya da za a yi na
bidi’a, sadaki kawai yake bukata.
Mahaifinsa tamkar ma yaf1 shi murna da faruwar
wannan lamari, domin son da yake nuna wa
Nuradden ya sake kusanta shi jikin Malam din, ga
shi kuma yau suna shirin hada zuri’a da shi, duk
nasiharsa da Nuradden‘ ba ta Wuce ‘ya rike
Bahijja da kyau, domin ita wata baiwa ce a
tare da shi Allah ya ba shi‘
'Shi ma 'haka ya dauki lamarin da ' girma a
ransa shi ya sa bai taBa jin wani abu na kin
hadin ba, duk da akwai irin type dinsa da yake ta
kissimawa zai ajiyc a matsayin matarsa ba irin
Bahijja ba.
Nuraddcn mutum ne wayayye, yana kuma
sha’awar auren mace mai wayewar addini da ta
zamani, musamman Bangarcn ado da kwalliya shi
kam mace mai yawan ado tafi daukar hankalinsa
fiye da mai kyau
Abin da ya lura Bahijja bai dame ta ba kenan k0
ma yace irin tsarin gidansu . babu bayyana
kwalliya a wajen kowacce budurwa. Girman
lamarin Bahijja ya sa bai dauki wannan a bakin
komai ba, abin da zuciyarsa ke gaya masa
saukakken lamarinc idan ta zo hannunsa zai
tafiyar da ita yadda yakeso. _ :
Anyi komai. cikin farin' ciki da karamci da
mutumci, sai dai tun farkon aurensu. ya ,soma
haduwa da matsaloli
masu tsayawa a rai. Ya danne, ya kuma hadiye
yana kuma Kokarin nusar da ita irin: yadda ya ke
so har zamansu ya kai tsawon; shckaru hudu,
inda k0 'da yaushe abubuwan ci gaban rayuwa
keta Samunsa, kasuwancinsa na tafiya sosai. Ya
mallaki abubuwa da dama na ci gaba tuni ya bar.
KarKashin wani yana cin gashin kansa ne.
Sai dai abin da yake dakusar da ci gaban nasa
Bahijja wanda ya lura har yanzu babu wani sauyi
daga nata Bangaren har yanzu duk yayin da yake
son kawo gyara na ci gaba irin wanda yake so, to
sai ta kawo masa wasu shirmammun dalilai da‘
za ta kafa hujja dasu ta Ki amsa gyaransa.
Idan ya ji‘ kamar ya ‘kai karanta gurin
mahaifinta, sai ya ji nauyin yin haka ba ma ya iya
tattauna matsalarta da‘ kowa, hadiyewa kawai
yake yi yana tunanin duk; wanda "ya ji zai ce
bata samu kyakkyawar tarbiyya ba ne, a rage
ganin Malam da,
’Kima. Yanzu ma haka ' ya ke ta hadiye
fushinsa‘, duk da tunzurar zuciyarsa da ta ke yi,
yana ji kamar ya mike ya bi ta har cikin dakinta_
ya lakada mata duka, domin shi' ne kadai abin
da'ya' rage ya yi mata horon da za ta hankaltu
ta gane _ abin da - yake so; da wanda ba ya so.
‘
Ya ci- gaba da nanata hailala tunda da ma idar
da sallarsa kenan, har ya kammala a hankali
komai ya soma lafa masa, take yunwa da gajiya
suka bijiro masa, jikinsa babu Kwari ,ya mike
yana tunanjn mai ya kamata yaci da alama ba a
k0 kammala girkin gidan' ba, k0 ma da sun
kamala ba ya jin zai iya cin abincin da almajirai
masu tarin Kazanta irin wadannan suka 'yi
hidimar girkawa ba. ' ' " Ya fito ya nufi kicin dan
har lokacin suna tsakar gidan sharar tsakar gidan
suketayi
tana tsakikyar kicin tana. kokarin dora Katuwar
tukunya a kan cooke.
Kallo daya ta yi masa ta dauke kai kamar yadda
ya yi mata, butar shayi ya dauko ya wanke da
ruwan roba da yake hannunsa, sannan ya kunna
cooker ya‘ dora lokacin har ta fice daga kicin din,
yana jin tafasar tattasai kamar 'zai yi amai Sai
dai ya Ki fita daga kicin din ne gudun kada wani
yazo ya yi masa kazanta a cikin shayinsa.
Har ya tafasa ya juye abinsa, ya fita zuwa
dakinsa ya debo kayan shayi ‘ya yi hadi mai
kauri, sannan ya dauko kek din
da ya yi 'mata tsaraba yasoma ci,_shi kam kayan
zakin nan ba cimarsa bane'sai ya zamo turawa
kawai 'yake yi, da haka cikinsa ya daga bai san
lokacin da bacci ya kwashe shi a wajen ba.
***************
Umman su Amira ne a tSakar gida
tana tankaden garin tuwo ta ji sallamar surukarta
Hajiya Khadija da sauri ta ajiye rariyar tana mata
sannu da zuwa, har suka isa falo ta zauna tana
dai 'cike da mamakin ganinta, domin ba kasafai
ta ke Zuwa gidan ba. , Bayan sun gaisa Hajiya
Khadija ta ce. ‘ ‘ ' ‘
‘ “Wai 'ina yaran. ne na ji gidan- shiru Sai
wannan sarkin rigimar?” 1
Ta mika hannu' za ta dauke shi,’ ya ki
yarda Umman ta ce “Suna makaranta”.
Hajiyar ta ce
“Ni ma wucewa nazo yi ta nan na ce bari na leko
biki naje gidan- Alhaji Mamuda’
Umma ta‘ mike, “Bari na kawo miki ruwa
A“A’ bar shi yi 'zamanki, na' cika Cikina da lemon
gidan biki”.
Sun ' dan‘ yi shiru’ na ‘yan daKiKai
Haj iy‘a Maryama ta ce.
- “Ya ya maganar 'takwarata (Amira), har yanzu
babu wata : magana tsayayya? Auntynsu Umme
ta zo min da maganar Alhaji Saminu yana zuwa
wajenta, har ya, . yi mata kyautarkudin mota’
‘ Aminatu taja ajiyar zuciya, ta ce. “Haka ne Inna,
amma ni lamarin yarinyar nan ne na kasa gane
mata, ina tsammanin da kanta ta ke korar
samari, da mutum ya yi zuwa daya biyu wajenta
sai ta daina fita, k0 da ya 20 idan kuma na
matsa mata ta fita, to ba zai sake zuwa‘ba Alhaji
Saminu ne ma nake dan tsammanin ta amince
masa sai-"gagashi ma tun daga ranar da ya zo
har‘Ummee ta ganshi bai sake zuwa ba, da na
matsa mata da .tambaya, sai cewa ta yi ya yi ta
fiya ne, ba ya Kasar”. ‘ ‘ salatin da.Hajiya Khadija
ta ke yi
ya katse wa Aminatu maganar da ta keyi, jikinta
ya yi sanyi tana zaton ba karamin - laifi ta yi ba
dalilin fadar hakan. Ita dai ta san manufarta guda
daya ce su gane ba wai rasa manema Amira ta yi
ba, ita din ce ba ta damu da kula su ba.
Bayan' Hajiya Khadija. ta karasa sallallami ta
sake duban Amina ta 'ce
“Ai gara da ki ka fada min, , wannan lamarin ba
na zama ba ne
Aminatu ta sauke ajiyar zuciya da ta' ji ba laifi ta
yi ba.
“Yaushe ne za a‘ zauna da yarinya irin haka na
faruwa, _ ba a~ san dalili ba? Arzikinki na zuwa
tana hamBarar da shi da
kanta”. Hajiya Khadija ta mike tana cewa- '
“Nizan tafi amma ki turomin
Basiru gobe mu tattauna abinda‘
yadace
Aminatu ta yi mata rakiya ta
ta dawo cikin zuciyarta tana . juya maganganun
Hajiya Khadija, ita kam ba ta taBa rainon
budurwar ‘ya‘ ba sai a kan amira tabbas akwai
yiwuwar akWai matsala a tare da' Amira don, ita‘
ceta kasa ganeWa, amma yanzu sai ta ji dadi. da
Hajiyar ta sanya ' baki, ta kuma ce za ta binciki
matsalar. Hankalinta ya kwanta da hakan, duk
da- ba ta san ta hanyar da za su bi a warware
matsalar-ba, ' ’ ’ ‘Haka Amira ta dawo daga
makaranta ta same ta, kallo daya ta yi mata ta
fahimci akwai damuwa a tare da ita; ta ajiye
alkur’aninta a inda ta ke ajiye ,shi.. K0 hijabi ba
ta cire ba ta zauna gefenta. ‘ “Umma lafiya na
ganki kamar kina tunani?’:’ Aminatu ta dago kai
da murmushi a fus'karta. . . , . “Lafiya Kalau nake
Amira, yanzu Hajiya Kaka ta zo”. "
Sunan da jikokinta ke kiranta kénan. Amira ta kau
da fuska. mtws
“Ni gara ma da bana nan ta zo me ta
fada miki Umma?”
Ta mike, “Babu komai gidan biki ta je ta biyo ta
dai tambaye ku”
“ “Uhum”. Kawai Amira ta ce, ta mike ta soma
cire kayan makaranta.
‘Mama ki daina damuwa da surutun mutane a
kaina, duk abin da Hajiya Kaka za ta fada kada
ya dame ki”.
“Na fada miki ta ce min wani abu ne, da za ki sa
ni a gaba da surutu‘? Ni lafiya muka rabu da ita”
. Amira ta raunana murya,‘ta ce.‘Yi hakuri Umma
gani ‘na yi da naa shigo kin yi jugum...” '
Umma ta katse ta da cewa.
“To babu komai, ni ba mu. taBa yin hira mai dadi
ba irin na yau”. “To Shi' kenan Umma, ' me ‘ake
dafawa Yunwa nake ji yau sosai”.
Umma ta ce “Tuwo ne, Sai ki Shiga kicin din ki
kwashe? '
Washegari Alhaji Basiru ya je wajen mahaifiyarsa'
do’min ya sami sakonta Wajen Aminatu. '
Bayan sun gaisa Hajiya Kaka ta gyara zama, ta
ce
“Da ma a kan maganar yarinyar nan ne Amira”.
Duk ta fayyace masa abin da ta ji daga Bakin
Aminatu, da labarin Alhaji Saminu da Ummce ta
ba ta. Sannan ta dora ' da cewa. '
“Irin wannan idan ha a lura ba sai tafiya ta yi
nisa a." gane aljanune suka shiga jikin yarinya
budurwa ta dinga tsanar duk wanda ya‘ ce yana
sonta, suna korarsa..To shi ya sa na ce ’kaZo mu
yi shaWara”.
Shima "jikinsa ' yayi' sanyi, hankalinsa- ya tashi
dan bai dau wannan a
matsayin matsalar da mahaifiyarsa ta hango ba
sai yanzu. Ya sauke ajiyar zuciya. “Kan wannan
Hajiya har sai kin
nemi shawarata kiyi abin da ya dace a kan Amira
duk abin da kika yanke ya yi daidai”;Hajiya
Kaka‘tace. “Eh haka ne. Basiru,‘amma shawarat
ma ai tana da dadi, ni abin _da nake ganin ya
dace a yi shi ne, a kai ta wajen 'Malam Balarabe,
na lungu biyu’ ya duba lamarin nata ya gani, idan
tana da matsalar aljanu sai ya korar matasu.
Idan kuma babu sai a yi mata addu’a har Allah
ya kawo manemi da wuri’
Alhaji Basiru ya ce
“ai wannan babu -laifi,:yaushe ya _ ka mata ku je
sai na turo ta?? Hajiya Kaka ta nisa, tukun ,ta ce
“Ina ganin gobe ma za mu je saboda
jibi za mu bikin ‘yar wajen Lantana”_
Ya ce “To sai ta z0 da safe kodan kuji saukin
samunjama’a. - '
Ya zura hannu a alj‘ihunsa ‘ya 2aro
dubu daidai guda uku, ya ce ‘ '
“Ga shi ku rike a hannunku”.
Haj iya Kaka ta amsa. '
“To sai goben duk yadda aka yi kuma idan ka zo
sai ka ji”.
Yace“Ba damuwa”.
Ya fita, maganar ta kwanta a ransa sosai, domin
ya 'san Malam Balarabe shi ma ya taBa zuwa
wajensa ya kuma yaba da .Kokarinsa; domin
matsalar da ta kai shi wajensa tuni ta zama
tarihi. ‘ ' ,
. Lokacin da ya koma gidanshi ya kammala' ‘cin
abinci, Aminatu na zuba masa ruwa yana wanke
hannunsa, ya ce
- “Kin ji' shawarar da Inna 'ta. yanke game da
Amira?” ' Aminatu ta buds idanu na razana,
sannan ta ce‘
“Me ya faru?”
Ya yi murmushi, “Babu komai, ta dai yi min
maganar korar samari da Amira ta ke yi, ta ce‘sai
an taimaka mata da ' addu’a saboda haka gobe
za su je wajen Malam Balarabc tare da ita”.
Aminatu ta zauna, tana fadin
“Kayya Malam, ni bana zaton tana da wata
matsala illa iyaka hangen wani abu ta. ke yi ya
sa ta haka, da a hadu ayi mata fada ta daina k0
a bata duk wanda aka ga dama da ya f1”
Alhaj i Basiru ya Bata fuska.
“Kina ganin kinf1 Hajiyarmu sanin abin da ya
dace kenan k0 kina son ki nuna mata iko a kan
Amira ne?”
Amina ta yi murmushi, ta cc.
“Haba dai duk bana nufin abu daya daga cikin
wanda ka fada, ina dai ganin kamar matsalan ba
a kai ga zuwa
wajen wani malami ba ne, amma na san Hajiya
tafini hangen nesa da sanin halayyar mutane,
yara nawa ne suka girma ta aurar da su a
gabanta”.
Ya Ce,‘ :“Yauwa, ke ma kin fahimta idankuma aka
samu' wata matsala ta Billo a kan maganar nan
to ke ce tunda tun farko kin nuna Kin
amincewarki za kuma ki iya zuga ta ta ki bin
umarnin mahaifiyata”.
Aminatu' taji' zafin maganganun,
domin ‘ba su kai ‘yadda zai dinga sauya mata‘
manufa haka ba, ta dai dake kawai ta
ce ‘ “Insha Allah ba za- ka ji bakina ba,
Allah ya tabbatar 'da alkhairi”. -;‘Amin’~~ Ya
fada tare da mikewa ya dauki buta yayi bandaki.
Washegan' da safe, Amira na sharar dakin
Ummansu ta ji kiran mahaifinta. - Da sauri ta
ajiye tsintsiyar ta nufi dakinsa da sallama.
Ta durkusa a gabansa, yayin da ya ce. “Amira za
ku je unguwa da Hajiya yanzu, saboda haka ki yi
sauri ki shirya ki jeki same ta kuje da wuri kafin
mutanc su cika”. . ‘
“To”. Kawai ta ce masa zuciyarta na tunanin ina
zasu je da Hajiya Kaka haka da har Baba ya
sanar da ita da kansa, ya ke kuma gargadinta da
ta yi sauri?
Tana shiga dakin ta dauki tsintsiyar ta ci gaba da
sharar da ta ke yi. Tana sharar zinccn zuci ya yi
mata yawa. Nan da nan ta ji tana cikin-
matsananciyar faduwar gaba. Harta gama ta
shiga can dakin Umma; ta tarar da ita a zaune a
bakin gado tana lallaba Umar da ta ke so ya yi
bacci, ta ce
“Umma yanzu Baba ya ce na shirya za mu je
Wani-waje da Hajiya Kaka, ina za mu?”
Ta fadi hakan ne dan ta kwantar mata da hankali
daga wasu-wasi k0 firgici, amma Amira sai ta
Zauna. " a
“Kai Hajiya Kaka da'rigima ta ke, ni ‘ kam bana
son yawan shige—shigen nan”. '
Aminatu na jinta ta dai tayi shiru, dan kada Amira
ta fadi wani, abin a ce ita ce ta saka ta.
Amira tana shiryawa amma sai mita ta kce yi, da
jan dogon tsaki kuma har
lokacin gabanta faduwa yake yi. Amma ta‘“ san
babu yadda za ta yi'ta guje wa zuwanta tunda
Babansu da kansa ya kirata ya fada mata.
' Har ta kammala shirinta ta nufi gidan Hajiya
Kaka. Ba ta jima a bakin titi ba ta samu mota"
Wannan ya ba ta damar kai wa gidan da wuri, -
Amma ga mamakinta Hajiya Kaka
har ta kammala nata shirin, tana zaune a tsakar
gida kan kujera ‘yar tsugune Ta
“Kin san shirin namu sai a hankali
Hajiya Kaka ta amshe da cewa.
“Ana ta kaKalen saka hoda da jambaki ba,
kwalliya ba miji”.
Amira ta mike daga tsugunnen da ta yi. _ “Haba
Hajiya Kaka, yaushe na isa . ~auren da za ki kira
min miji?” '
Haj iya Kaka ta watsa mata dakuwa. “Un go
wannan, ja’ira kawai Shekara sha taran ki ce ba
ki isa aure ba, kin zama uwar mata a gida?” .
Amira ta ce, “Hajiya a birni fa muke . ba a kauye
ba, kamar ni a dinga yi min zancen aure, ga masu
shekaru arba’in nan ma a gida, ai ina da sauran
lokaci”.
Hajiya Kaka ta sake watsa mata
dakuwar tana fadin.
“Ungo wannan rasa kunya beran tanka. Idan ma
shekara dari aka yi to ba a gidan nan ba, ni ba,
k0 kin taba ganin yarinyar cikin gidannan da ta
kai shekara sha biyar ba ta yi aure ba?”
’ “Zamaninsu daban 'nawa daban’; .. Amira ta
fada murya.KaSa'Kasa
Haj iya Kaka tace me "kike cewa?”
Amira ta ce, “Ba komoi
Dan ta .kawo KarShen fadan Hajiya,‘ Kaka ba don
tsoron fada mata' abin da ta" fada din ba. ‘
Hajiya Kaka 'ta lulluBa mayafi‘- a kanta, ta ce
“Mu je kin ji, ke yarinya ce har yanzu ba ki' san
abin «da yake yi miki ciwoba, aure shi ne
mutumcin duk' diyar da ta kai minzalin yinsa,
Amira ta yi shiru kawai: tana
sauranon Hajiya Kaka duk rabin hirarta a ‘ kan
hanya a kan nusar .da ita ne
muhimmancin kama mijin. aure a hannu da yadda
iyaye ke fadi—tashi a~ wajen ganin ‘ya’yansu
sun‘sami gidan daular da za -a rike musu ‘ya. a .
Shiga wannan lungu, fita wancan sai " ga su a
gidan Malam Balarabe, Hajiya Kaka ta ce.
' “Yauwa”. Ganin mutum daya, biyu suka tarar.
'Dayar na zaune a kan benci, daya kuma na‘
-ciki suma suka ‘zauna a kan bencin sama masu
jira.
Bugun zuciya da fargabar Amira ya tsananta
lokacin‘ da’ layi ya zo kansu, wanda ita kanta ba
2a ta iya cewa ga dalili ba, tunda wadanda suka
shiga suka fito da fara’arsu suka yi musu
sallama.
Babban mutum ne mai girman jiki, tsawo da Kiba
sosai,.fari za a kira shi. Yana da ‘dogon gemu da
'yaWan saje da suka hadu da gemun suka kame
masa Shekarunsa kuwa ba za su‘ gaza hamsin
ba, yana sanye da manyan 'kaya ya dora ‘mayafi
a kafadarsa da hula a kansa, duk yawan
Kasumbar da ta 'mamaye ‘ fuskarsa ba ta Boye
dogon hancinsa da manyan idanunsa masu
kwanrjini ba. ' '
,Kallo. daya ta yi masa ta lura da wadannan
abubuwan da ke tare da shi, sai dai lokacin da ta
durkusa idanunta nakasa ba ta son sake hada ido
da shi, tana ji suna gaisawa da Hajiya Kaka,
sann‘lan ita ma ta
dago ta soma gaida shi,
Idon da ya zuba mata ya tsananta faduwar gaban
da ta keji, ta sauke 'nata idon tanaji Hajiya Kaka
na cewa
Wannan jikata ce malam’ yar
wajen Alhaji Basiru ce ita ce babba”. Malam ya
shafi gemu tare da cewa.
. ,“Masha Allah”,
TaCe, “TO malam wata ‘yar matsalace ke tafe da
mu game da wannan yarinyar. . . Tana da tarin
manema manyan mutane, sai dai har yanzu a
cikinsu babu wanda ya zo da batun maganar
aure, shi ne nake so ai mata addua ta samu
gwani daya ya tsaya”. " Malam ya‘ ce “Kin yi ’
tunani .mai kyau Hajiya, za kuma a bincika
lamarin ’ Ya dubi Amira, ya ce, ,“Ke yarinya ya ya
sunanki?” Ta fada masa, ya ce ” “Mu ga
hannunki
Ta bude masa tafin hannunta, ya matsa sosai ya
sa 'nasa yatsan ya soma yi mata Zane a ciki.
Amira ta dauke numfashi saboda wani irin abu da
ta ji yana yawo a jikinta.
Ya. dauke hannunsa ya koma kan wata takarda
ya tambayi sunan mahaifiyarta da mahaifinta.
Duk Hajiya Kaka ta ‘fada masa, sannan ya rubuta
a jikin
‘yar takardar ya mike ya shiga wani daki.
Daga ita har Haj iya Kaka babu wanda ke iya
magana, babu jimawa ya fito
ya sake haWa kan dardumar da yake zaune
dazun, ya dubi Hajiya Kaka ya ce
“Haj iya yarinyar nan babu matsalar aljani k0
sihiri a jikinta, matsalar dai daga masu zuwa
wajen nata yake musamman shi wanda na ga
kamar zuciyarta tafi so a cikin manemanta, akwai
Saminu da
Sulaiman, duk wadannan da gaske suke yi a cikin
binciken da na yi, na ga dukkansu a
shirye suke da aurenta.
Sai dai rashin samun 'goyon bayanta ‘ abin da na
gani zuciyarta ta f1 karkata ga shi Saminu,“sai
dai shi matSalarsa iyalinsa duk matar da ya so
da aure sai ta lalata maganar ta zama shiririta”.
Hajiya Kaka ta jinjina kai, sannan ta ce
“To Malam yanzu ya kake’ ganin za a yi? Su dai
yaran yanzu 'ba a-musu dole, kuma 'shi. zaman
aure da 'soyayya ya f1 dankO inda zuciyana ta f1
karkata kenan
Malam ya ce, “Haka ne”.
Yana duban Amira da ke ‘ta raba idanu tsakanin
Malam da Hajiya Kaka zuciyarta ciike da dumbin
mamakin abin da Malam ya fada tunda ya
bayyana sirin ' zuci’yarta ne da babu wanda ya
san da shi, ita kadai ta san samarinta da yadda
suka Zautu da son ta ba su damar turowa a
gidansu a yi maganar aure ta ke zullewa. Malam
ya ce “Duk wannan abu ne mai sauki Hajiya, za a
yi aiki a kansa, zai zo da maganar aure ba da
jimawa ba, za kuma ta. samu alkhain' a jikinsa
mai tarin yawa, wani nata ma zai ji dadinsa”. ‘
'ba Hajiya. Kaka kadai ba, har ita ma sai data yi
murmushi. Ya ci gaba da cewa. “Za ta dingazuwa
tana karBar rubutu tsawon kwanaki uku da kanta
za ta dinga zuwa, akwai‘ Wanda sai ta 20 '2a a
rubuta mata ta .shanye, akwai kuma wanda» za
ta
tafi da shi cikin dare ta sha ta, shafe jikinta da
shi”.
Hajiya Kaka ta ce, “Za ta zo ai ta ga gurin”. Ta
bude ‘yar Karamar jakarta ta zaro dubu biyu ta
ajiye wa Malam suka mike suna godiya: Malam
ya" bi bayansu da kallo, ya lashe“ busassun
laBBansa.
“TabbaS da ina ‘da wajen ajiye
wannan yarinyar da na ajiye ta, a gidana na more
da baiwar da Allah ya yi mata”; Abin da ya raya a
zuciyarsa kenan, sanin ba shi da sauran gurbi
domin matansa na aure hudu ne, cikon ta hudun
k0 shekara daya ma bai yi da aurenta ba.
Asha karatu lfy
Daga qaninnan naku
Bankada
Chapter3
Nuradden ya farka daga baccin da ya dauke shi,
yana kuma jin dadin baccin sai dai kiraye—
kirayen sallar la a'sar “‘ne ya ‘ farkar da shi, ya
mike jikinsa babu kwari
*** *** ***
sai dai ya rage radadin zuciyar da ya
kwantadashi.
Ya yi alwala a dakinsa, wannan karon jam’i yake
son bi tunda lokaci bai qure masa ba, don haka
ya fito daga dakin.
Yana fitowa suka hada ido da ita, da alama
dakinsa ta nufo. Ta sakar masa murmushi. Tare
da fadin. harka
“sha baccin yanzu nake shirin
zuwa na tashe ka saboda lokacin sallah ya
yi”. Duk yana jinta duk da gaba daya ya
mai da hankalinsa a kan saka takalmansa, amma
sai ya basar da ita tamkar ba da shi ta ke ba.
Sai dai ya dan kura mata ido~ kamar mai son
gano Wani abu a cikinsu, sannan ya juya ya hada
da sauri domin ya ji an tayar da sallar. Sai dai
yana jin zuciyarsa a washe tas, da ya fahimci
fushin na Bahijja yau ba‘ mai zurfi bane
Tsawon kWanaki biyun da Nuraddcn ya yi a cikin
gidansa ya yi su ne cikin kunar zuciya, saboda
fushi mai tsanani da Bahijja ta ke dauke da shi.
Abu daya ne yake dan lafar masa da zuciya ganin
raguwar yawan zuwan almajiran da ke wunin
musu a‘ gida. Yaran ne kadai ke zuwa, su ma
daukar abinci kawai suke yi su fita, hakan sai ya
sa ya dan ji sanyi har ya soma zargin Bahijja ta
fara gane kuskurenta
ta kore su ne Girman kai irin nata ya hanata ta
ba ‘ shi hakuri', k0 ta nemi sulhu da shi, hakan
ma ya yi Wa ' zuciyarsa dadi, domin ya samu
nutsuwa cikin hutun da yake shirin yi na kwanaki
bakwai a gidan sa ba tare da ya fita kasuwa ba,
har zuwa‘ lokacin da jirginsu zai daga zuwa
ka‘sar Dubai, domin sarin kaya.
Yadda gidan ya yi shiru ya yi masa dadi kwarai,
duk da da ma Sun rage shi cikin jin dadin
kwanakin, amma zaman gidan shiru ba hayaniya'
Shi ma yana da tasa babbar gudunmawar ta jin
dadinsa.
Yana cin abincinsa cikin kwanciyar hankali tunda
ya san ba almajirai bare su yi masa jagwalgwalo,
daga ci sai bacci sai zuwa masallaci.
Sai dai a ranar ta yau yana dawowa daga
masallaci suka hada ido da Bahijja, tana tsaka da
kwankwatsa attarugu‘a cikin
no“Yar rigima kenan, kin San gaskiya kike takewa,
yanzu gidan nan haka daga ni sai ke bai fi miki
dadi ba, ga shi har kin samu damar da za ki yi
wa mijinki irin ' kwalliyar da ya ke so. Kin ga
kyau da kayan suka yi miki kuwa?”
Ba ta tanka masa ba, ya janyo fatar gefen cikinta
a hankali, ta sa dariya.
. “Ka gani‘ ba na so”.
Ya rike hannayenta. ‘
“Kina so Bahijja, miskilancinki ne ya hana ki bin
mijinki ki ba shi haquri”.
Ta juya ido, tace ‘
' “Ni na yi maka laifi ka koreni daga dakinka, in
na sake shiga ai sai na yi wani...
‘Abin da yake ne ya sa ta kasa karasa abin data
ke shirun fada, sai dariya da kyar ta kwaci kanta,
ta soma gudu yana binta suna zagayen gidan. '
A yammacin nan ya samo cikon
farin cikinsa da jin dadi da ya rasa na kwana
biyun DA suka wucw
Ya manta da komai, lallai komai ya shafe a ransa
Kaunar Bahijja ke ninkuwa a ransa, yana girmama
son da yake yi wa Bahijja. Duk abin da ta ke yi
masa ba ya tunanin rabuwa da ita k0 sau daya,
burinsa ta gane irin rayuwa da yakeso su
shimfida ta ba shi hadin kai a burinsa na
dauwamman zamansu.
A cikin daren ranar ya baje tsarabar dinkunan da
ya yo mata a Abuja, atamfofi ne masu kyau da
tsada. Yana kallon yanayinta lokacin da ta ke
kallon dinkin. ’
Zuciyarsa ta ba shi ba za ta saka su kamar
yadda yake so ba, tunda ya ga tana kallon dinkin
tana yatsina baki. Cikin karfafa gwiwarta ya ce
mata.
“Kin ga irin dinkunan da ‘yammatan Abuja harda
na nan Kano ma ke yayi”. Ta yi sa ar tararsa da
cewa.
“Shi ne kuma ka kawo wa matarka ta aure, abin
da marabarsu da tsirara kalilance?
Ya dan yi murmushi, ya ce
“Ai ina ganin da ‘yammata ne kadai dinkunan ba
su dace ba, matan aure ya fi dacewa su mai da
su kayan saka wa mazajensu a gida. Idan kuma
za su fita sai su sanya sutura mai yalwa da duhu
mai rufe jiki domin dinkunan na da daukan
hankali musamman idan suka samu jikin
kyakkyawa kamarki”. “Oh na gane abin da ka ke
nufi, kana
so na dinga shigar da karuwanku suke yi?”
Ya dago da sauri daga kishingiden da ya yi, ya
Kankantar da idanunsa yadda ya ji maganar
kamar shigar mashi.
,“Karuwai?” Ya sake nanatawa kamar mai son ya
tabbatar.
Ta murguda baki.
“In ba karuwa ba ta ya ya aka yi har ka iya yi wa
mace kallon tsanaki a kaya na
jikinta?” . . .. '
“Bahijja ni ki ke gaya wa ina tare da ‘karuwa
saboda baki da mutumci, ba ki san qimata ba?”
Ta ja dogon tsaki, ta dauke kai tana
‘yan guna—gunin da ba ya jin abin da ta ke fada,
amma tafasa zuciyarsa take yi, yana jin kamar ya
’ faffalla wa fuskarta kyawawan mari yadda
zuciyarsa ta hasala, amma sai ya koma ya lafe
jikin kujerar da yake kishingide yace Bahijja duk
yadda ki ka fassara ni a ranki haka nake, duk
abin da za ki yi sai ki yi
Ta mike tsaye ta ce.
“To ni mai zan yi maka? Kaya ne dai
na ce bana so, ba ma zanyi irin shigar da 'zai
nuna tsiraicina ba sai akai kasuwa”. Duk da
fushin da yake ciki bai san
sanda ya kwashe da dariya ba, kalamanta na
karshe ne suka sa shi dariya, har da rike ciki
yana nunata da dan yatsa.
Duk da bai ce komai ba‘, ta gano kalamanta yake
yi wa dariya. Wani abu ya taso ya tsaya mata a
wuya na takaici. Ta juya ta soma tafiya, ya janyo
ta da karfi ta fada jikinsa.
A kunnenta yake rada mata.
“Bahijja ban da abinki wane dare ne kuma
Jemage bai gani ba?” '
Kai tsaye ta amsa masa.
“Sai ranar mutuwarsa mana”.
Ya ce “To shi kenan amaryata, duk yadda ki keso
haka 2a a yi, amma ina rokon alfarma a wajenki
ki daure ki dinga - tauna magana kafin ta fita
daga bakinki.
Idan ki ka yi haka za ki kara kima da
mutumci a wajen duk Wanda za ki yi magana da
shi”.
Ita ma ta hango kuskurenta, amma
kana ta saisaita murya.
“Nura ai kai ne wani lokacin ka ke tabo ni, ka san
yadda kuwa na ji. da ka ambaci kana ganin
kayan nan jikin wasu mata? Abin da ka fada fa
yana nufin sun ba ka sha’awa kenan?” '
Ta yi masa tambayar tana kallon tsakiyar idonsa;
Ya sauke ajiyar zuciya.
' “Ba zan yi miki karya ba Bahijja, ni : din nan da
ki ke gani ina miki kaunar da ba na hada ta da
duk wata diya saboda kaunarki ta gauraye da
girma da martabar Malam da nake gani a idona.
Ban Boye miki komai ba, ina sha’awar dinkin a
cikin idona, amma ina SO na yi masa kallon
sha’awa a jikin iyalina shi ya sa na yi na kawo
miki da ina da wadanda zan yi wa kallon'
sha’awar da zan gan .su da ban kawo miki su
ba”.
Wani almajiri-ne ya yi sallama, sun shagala da
tattaunawa ba su amsa ba, shi
kuma ya shigo falon nasu. Ta mike da sauri ta ji
kunyar yadda yazo ya same su sosai, shi ma
yaron ya juya da baya. Ta kasa k0 magana,
Nuradden ne ya ce“Kai mene ne?”
Yaron ya ce, “Na zo kawo allona
ne
Nuradden ya ce, “To ajiye shi a nan”. .
Sai da ta ji fitar yaron ta sauke ajiyar zuciya
idanunta har sun kawo Kwalla saboda wani irin
takaicin Nura da ta ji, duk shi ya janyo mata
tunda ba ya iya zama sai ya Kwakume jikinta duk
yaran da suke zuwa yi mata aiki, da wadanda
suke taya ta hira duk zuwansa ya sa sun daina
zuwa gidan sai ya yi mata shiru. Duk ba dadi a
take ta soma‘addu’ar Allah ya sa Nura-ya tafi ko
sa wataya.
Ta dube shi,’ “Ka gani k0?”
Ya dauke kai, ya ce.
Na gani duk kin wani diririce kamar
wadda aka kamada kwarto. Ni mijinkinefa ‘
Ta ce, “Amma ko k mijina ne
bai kamata ya ganmu a haka ba, sai ya rage
ganinmu da kima”. Idan wannan ya dame ki, to ki
koyi rufe fadarki, wai ma allunan me ya zo kawo
miki cikin daren nan?” “Rubutu na sa shi ya yi
min”. Ya gyada kai, “Ya yi kyau”.
***
Tun lokacin da Amira suka bar gidan Malam ta
gama aminta ‘da lamarinsa- ta yadda ya gama
sanin bayani game da sunan samarinta ba tare da
wani ya gaya_ masa ba.
A hanyarsu ta komawa gida sai ya zamana Amira
ta ke damun Hajiya Kaka da tambaya, saBanin
lokacin zuwanta da ta,
*** ***
ke jin matsa mata Hajiya Kakan kawai ke yi.
Karin bayanin da Hajiya Kaka ke yi mata game da
ayyukan da Malam din yake yi shi ne ya ke dada
sa ta aminccwa da aikin da zai yi mata a kan
Alhaji Saminu.
Tana jin kamar ta same shi ta gama 'ta hanyar
auren da ta lura ba ya so, ba ta Bangaren
shashanci ba.
_ Ta dauki ‘yancinta da martabarta ta ‘ya mace a
matsayin abu mafi daraja a tare da ita, shi ya sa
k0 Kuwa wadda kanta 'ya waye da soyayyar
zamani ta rage zafin k0 shan minti ba ta yi, duk
kuma yadda ta dauki yarinya da daraja a idonta
da zarar ta samu labarin tana irin wannan harkar
shi kenan ta daina ganin Kimarta, haka za ta
dinga jin kyamarta da tsanarta a zuciyana, irin
yadda k0 a hanya ba ta son haduwa da ita bare
kuma da namiji. ‘
Ba ta taBa yin saurayin da ta zarge
shi da manufar nuna mata soyayya- irin ta
zamani ba ta sake saurarensa, wani ma ba
nufinsa ‘ kenan a kanta ba, amma wayewarsa da
zakewa a kan soyayyarta idan ya yi mata yawa
tana musu kudin goro tace duk ‘yan iska ne,
mayaudara.
Alhaji Saminu shi ne kadai mutumin da ya nuna
mata maitarsa a fili ta kuma ji ya yi tsayuwar da
ta kasa cire shi daga ranta. Hangen samun
nasara a wajen Malam na sauya manufarsa daga
mummunar manufa ‘ zuwa kyakkyawa ya sa ta ji
a yau zuciyarta ta yi wasai tamkar an sauke
mata wani nauyi daga Kirjinta.
Sun rabu da Hajiya Kaka tun a hanyar da zata
:shiga mota tana jaddada mata, kada ta yi
sakaci‘ gobe, ta yi sammakon zuwa wajen
Malam.
Ta‘ shigo Ummansu na kicin, sai Umar fake
tsakar gida yana rarrafe, ta dauke shi ta daga
sama, tana cilla shi ~suna‘ kyalkyala dariya daga
shi har ita. Tunda
Ummansu ta ji muryarta ta ke tai sauri ta.
kammala da zuba abinci dan ta zo ta ji abin da
ya faru a gidan malam, domin tun fitar Amira
hankalinta ya kasa kwanCiya, musamman idan ta
tuna da» kalaman Amirar kafin fitarta.
Ita ma sai nata gaban ya dinga" matsanancin
faduwa, jikinta ya yi sanyi Kalau, ta ke ta sake-
saken abubuwa da dama har ta soma bawa
kanta laifi
Sai dai jin yadda Amira ké Kyalkyadariya ya‘ sa
ta sauke ajiyar zuciya, ta ‘ fahimci ba a yi mata
wani abu da zai dami zuciyarta ba.
Amira ta nufi hanyar kicin din, ita ma Umma
nakokarin fitowa ta. tsaya tana
mai da numfashin daga Umar saman da ta
yi ta yi.
“Umma sannu da aiki”.
“Yauwa Amira, kun dawo?”
“Mun dawo Umma, ashe wajen da kafa ma ake
zuwa daga gidan Hajiya Kaka? Lunguna dai muka
yi ta bi can wani waje wai shi Saran ban taba
zuwa wajen ba sai
yau . .Uma ta ce “kun same shi dai k0?” “Yana
nan Umma, yace‘ matar Alhaji Saminu cekeyin.
asiri a kan duk matan da ya ke cewa yana so ya
janye”. Ummanta ta sauke ajiyar zuci’ya har
lokacin da Amira ta gama ba tar labari hankalinta
bai kwanta sosai da, ita abin da ta tsorata da shi
tun kfin ma a shiga gidan sai an soma bin
malamai a kansa, idan an shiga kuma sai ya ya?
Haka za a ai ta biye-biye saboda kawai ana son
zama da shi? Sai dai yadda ta ga Amira na ta
_farin ciki wanda rabon da ta yi irinsa har ta
manta a gidan, ya kure duk wani abu ta ke hange
a zuciyarta, burinta na son ganin auren Amira ya
sake ninkuwa.
Washegali da wuri Amira ta shirya zuwa wajen
Malam, tun da Aminatu ta yi ' wa Babansu
bayanin duk abin da Amira ta" fada mata, saboda
haka da ta shiga ta gaida shi da safe ya ce
,“Amira ga kudi ki shiga mota,Ki tafi wajen Malam
ki kuma tafi da wuri bana son biye- biye gidan
kawaye kin ji na fada miki”.
Tace “To Baba insha Allahu ba zan jima ba zan
dawo”.
Ya dauko dari biyar ya miKa mata.
“Ga shi”.
Ta karBa ta duke domin kudin ya zarta na mota
kadai.
Amira ta isa gidan Malam a yau mutum daya
kawai ta tarar a shimfidar da ta ke soron gidan,
ta yi wa matar sallama ‘ suka gaisa ta zauna,
matar ta dube ta. ‘
“Yau Malam din, ya yi jinkirin fitowa da tuni ma
na tafi dan na dan jima da zuwa”.
Amira ta dubi kofar 'dakin‘ da'yake zama din,
ashe bai ma fito ba, motsin fitowarsa ne ya katse
musu hirar‘ tare suka dubi kofar fitowar daga
gidan, shi din 'ne kuwa yana sanye da manyan
kaya.. Ya yi yafe da farin mayafi kansa da hula,
fuskarsa cike kwarjini. ‘
Suka soma-‘rige rigen gaishe shi yana amsawa
idanunsa na kan- fuskar Amira. Ya sakar mata
murmushi ya shiga dakinsa, bai jima da shiga ba
ya'yi‘ gyaran ‘murya ya ce
a shigo da wadda ta soma zuwa. ' ‘ Ta tashi ta
shiga, ya rage Amira ita kadai. Ba ta jima sosai
ba ta fito, Amira ta shiga. ‘ Ta durkusa ta. sake
gai‘she shi, sannan ta zauna ya daukowani
madubi da aka yi wa rubutu a kai, ya ce.
“Yarinya ai tun jiya na kammala da rubutunki”
Ya dauko tawada yana'Wasu rubutun a kan
wanda ya‘yi a jikin madubin wanda ba ta fahimci
abin. da yake rubutawa ba. Kalmomin ba Shi yi
mata kama da wasu ayoyi na cikin alkur’ani
amman zaif1 kyau a ‘ kira rubutun nasa da
jagwalgwalo ba don kada na yi saBo ba. Abin
data ke ta fada azuciyarta kenan lokacin da ta ke
kai mafara wajen hada baki ba larabci k0 2a ta ‘
gane wani abu mai ma’anar da ta sani, ba ta
gane komai ba har ya kammala, sannan ‘ ya ce
ta miko masa hannunta. .
Ba tare da musu ba ta miko hannun nata ya
dangwali tawada ya dora alkalami a kan tafin
hannun nata ya soma rubutu.
Wani irin abu ta dinga ji yana yawo a .jikinta
tamkar wadda ake‘ yi wa tafiyar kadangare,
amma haka ta sa wa kanta
juriya har ya gama ya dubeta.
“Amiran tauraronki mai haske ne aikinki zai 20
min da sauki k0 da kuwa shi saminun ba sonki
yake yi ba, idan har na soma aikin da wuri zai ci,
tunda kina haska idanun duk wani da namiji”, Ya
mika mata madubin da yayi rubutun a kansa.
“KarBi wannan”.
‘ Ya tura mata wata roba da ruwa a cikinta, ya ce
“Ki wanke madubin nan da hannun da na yi miki
rubutun nan daidai yadda za ki iya shanye ruwan,
ki shanye”. ‘
Ya jingina da bango yana lumshe idanu kamar
mai bacci, jikinasa_ ya gama mutuwa ido yasa
mata yake sake kare wa Amira kallo tana .wanke
rubutun.
Tun zuwansu Amira jiya da ya dora ido a kanta
babu matar da yake iya tunowa sama da ita.
Babu tunanin da yake illa nata. Wuni ya yi yana
sakawa da
kwancewar yadda zai yi ya mallaki Amira, sai dai
duk tunanin da yake yi a kanta yana saurin
warware shi da kansa. Yana ganin ba abin ma da
zai yiwu bane, sai ya watsar. ‘
A yanzu da ta ke zaune a gabansa- ’tana wanke
rubutun da lallausan hannunta da ya gama
kidima lissafinsa tun a jiya komai ya gama
kwance masa, yana ji kamar a zabce shekarunsa
a kan wanda yake da su Yana laluben
maganganun; da ya dace ya soma da su dan ya
sace zuciyarta sai dai yana ganin kada ya fada;
mata Wata maganar da za ta daina zuwa ya
kuma zubar da damarsa a wajenta ba tare; da ya
ci gaba da samun wani abu daga gare ta ba, k0
da na xaman da ‘ya yi ne yana kare mata kallo.
ne
Saboda haka ya ja bakinsa ya yi‘ shiru, ita kam
hankalinta na kan abin da ya sa ta bata kula da
kallon da yake yi mata ba
Ta yi tsammanin ma gyangyadi yake yi, shi ya sa
da ta gama ta ce masa.
“Malam na gama”.
Ya dago kamar mai baccin gaske.
“Yauwa kin shanye? To sake wanke ki dura
ruwan a wannan ledar, idan kin je gida sai ki
shafe gaba daya jikinki da shi”.
Ta zuba rubutun kamar yadda ya ce, ,' sannan ta
daga ‘yar karamar jakarta, ta mike tana ce masa,
to ta tafi.
Kasa magana ya yi, kai kawai ya daga mata
saboda irin abin da yake fama da shi na
matsananciyar sha’awarta.
Wunin ranar cikin farin ciki ta yi shi, saboda
yadda Malam ya karfafa gwiwarta ' .a kan
nasarar aikin da ake yi, da ta ke hanga.
3l' Washegari ba ta samu zuwa da wuri ba kamar
kwanaki biyun da ta yi tana zuwa a baya saboda
Ummansu za ta fita gidan
aminiyarta wajen kaI kayan lefen ‘yarta
da za a yi a yau. Amira sai da ta tsaya ta
kammala wa- 'qannenta abincin makaranta ba ta
iSa gidan Malam ba sai Karfe daya da minti
goma‘na rana, ta cika da mamakin ganin yadda
wajen ya cika da mata da maza. .
Ta samu wurumi ta zauna matan nata hirarkinsu,
amma hirar wasu'
mata guda .‘ biyu ta fi daukan hankalinta. .Dayar
nanbawa dayar labarin yadda kishiyarta ta yi
mata wani irin mugun asiri da ta dinga zubar da
jini ya Ki tsayawa sai da ta zo gurin Malam aka
dace jinin ya tsaya.
Dayar ta numfasa, ta ce
“Sharrin kishiya ai na da yawa, ni kuma ban tarar
da ita ba tun kafin ya aure ni ya sake ta, amma
ta hana mu zauna
lafiya da shi da mugun asiri irin nata, 'sai
da muka zo gurin Malam a ka karya asirin, -'
yanzu ba ki ga yadda ya ke ji da ‘ni ba
Amira ta sauke ajiyar zuciya, ta kawar da kanta
tana dada girmama lamarin Malam, suka ci gaba
da hirarsu wadda yawancinta a kan matsalokin
zaman kishi sukeyi.
Ta gode wa Allah da ya sa ta zo _. wajen Malam
ta kuma sake kudiri na shirin " karBar maganin
tsarin jiki a wajen malam ’ tun kafin ta shiga
gidan Alhaji Saminu, tunda matarsa a tsaye ta ke
ba ta son kishiya.
Layi na tafiya har ya zo kanta, amma ta kosa da
zaman ta yi nadamar rashin zuwanta da wuri da
tuni tana gida.
Ta yi sallama ya amsa, yana zaune a kan
dardumarsa tunda ya ji muryarta ya dago da
sauri dan tabbatarwa ita din ce domin harya fitar
da rai da zuwan nata.
Ta durkusa ta Soma da gaida shi, ya
amsa yana shafa’dogon gemunsa idanunsa na
kanta; har sai da ta zauna ya sauke numfashi
min tsallake next page sbd yayi damege
makoshi ya ce ; ‘
“Ya kamata' gobe ace,kiyi sammako takwas tayi
miki a nan saboda aikin da za a yi miki goben
yana‘da yawa, kuma shi ’ne zai zamo na_ qarshe
da ,an kammala ‘shi Alhaji Saminu" zaizo, duk
kuwa a inda yake fadin kasar nan zai neme ki”.
’Duk da Sauyin muryar'da ta ji daga Malam‘bai
sa ta gano '_Wani abu a tare da shi ba. Kwarjini
yake yi mata da'ba‘ ta iya hada ido da, shi dalilin
da ya sa ba ta hangi kallon da yaake yi mata ba
har ta fita daga dakin. "
”-*** *** ***
Dare ya soma nisa cikin baccinsa ya dinga jin
shesshekar kUka, bacci ne sosai a. kansa yakasa
bude idonsa, sai dai ya kai hannu yana laluben
gefenSa da take a
kwance ya ji babu ita, sai filin wajen.
Take ya mike ya bude ido yana mitsitssika su dan
ya tabbata: da zargin da ya soma yi.
Ya kai hannu ya kunna fltilar gefen gado,
hankalinsa ya tashi sosai da ya ganta zaune a
bakin gado ta hada kai da gwiwa tana ta kuka da
shessheka.
Ya rarrafa har zuwa inda ta ke ya rike kafadunta
ta baya.
“Bahijja me ya same ki, mene ne?”
Maimakon ta ba shi amsa, sai kukan ya Kara
tsanani, hankalinsa ya qara tashi ya zuro
qafafunsa zuwa kasa ya sake janyo ta jikinsa a
hankali ya ke rada mata. '
“Haba Bahijja mane ne amfanin irin wannman
kukan cikin dare? Idan wani abu ke damunki sai
ki fada min idan kuma wani abu ne ya faru sai ki
fada min,
kin san babu abin dana tsana irin ‘na' ga
damuwarki, bare 'zubar hawayenki. Ki‘ fada, min
k0 mane ne hankalina fa ya gama tashi”,"
~Yadda ya ke lallaBa ta ya sa har ta rage
kukanta, ta dago, ta dubi yadda ya birkice gaba.
daya, tabbas ‘abin da ya fada har cikin zuciyarsa
yake
Da Kyar ta iya daga baki cikin muryar kuka‘,‘ta
ce
“Al’adata na gani”.
Ya sauke' dOguwar ajiyar zuCiya, ya hade yatsun
hannayenSa wuri guda, ya zuba wa kafet din da
ke shimfide ido, shi da kansa ya ji wani abu na
rashin jin dadi ,matuka, domin iya wannan lokacin
ya soma qaguwa da son shi ma ya ga dansu
shekara hudu da yin aurensu duk yayye da
Kannenta da aka yi daurin aurensu a tare sun
haihu~daga masu ‘ya’ya'biyu sai ma su uku, shi
ya sa da ta fada masa ta dora
kWanaki goma a‘ kan kwanakin dawowar
al’adarta ya cike da farin . ciki tare da addu’ar
Allah ya sa ta samu ciki ne
Jikinsa ya yi sanyi sosai, ya dago ya _ dube ta
har lokacin kukan ta ke yi.
“Bahijja ita' ma Wannan matsalar
kuka ba zai yi maganinta ba, ni ina‘ ganin abin da
za a yi, mu dage da .addu’a da kuma binciken
matsalarmu mu nemi maganinta. Idan kuma ba
mu da wata ' matsala sai mu tsaya ga addu’a
har Allah
ya ba mu”.
Duk da kukata ke yi, sai da ta juyo idanunta sun.
sauya launi, ta watsa masa‘ wani kallo mai kama
da harara, sannan ta ce ”
“wai me ka ke nufi da mu yi' binciken
matsalarmu?”
Ya gyara' ya fuskanCéta:
“Bahijja ina nufin mu je asibiti‘a yi mana wasu
gwaje-gwajen dan a gane muna
da matsala k0 babu?”
Ganin har lokacin irin kallon data keyi masa dazu
shi ta ci gaba da yi masa sai ya dora da cewa.
“Ina ganin wannan ba matsala ba ce Bahijja”.
Ta gyara zama, “Idan kana ganin babu' komai a
cikin yiwa Ubangiji shisshigi cikin lamuranSa kai
sai ka jeka yi, amma ni ba ciwo nake ji a jikina ba
ba komai ba, ba zan je wajen wani likita neman
haihuwa ba. Ba a wajensa mu ke
' nema ban,”
Ya yi saurin katse ta.
“Haba Bahijja ya ya zaki jahilci maganata? Babu
abin aibu a- cikin zuwa wajen likita dan binciken
matsala da maganinta, ana iya rashin samun
haihuwa dan matsalar ciwo, ana kuma Kin
samunta haka kawai ba tare da ciwo ba.’ Menene
laifi dan mutum ya binciki lafiyarsa?”
Ta mike tsaye tana fadin.
“A . wajenka, da irin jahiltacciyar fahimtarka ba
Ya janyo ta da qarfi' ta zauna ba Shiri ransa ya yi
mugun Baci da‘abin da ta fada masa.
“To tunda ke kina da ilimi sai ki fada 1 min ayar
k0 hadisin da ‘ya ke nuni da kada mu binciki
lafiyarmu, k0 kada mu nemi magani?” ‘
yayi shiru, domin ta lalubo amsar . Jin ta yi Shiru
ya juya ya kwanta abinsa. Zuwa cam ta nisa tace
“Taka dai fahimtar kenan, da wayona Kafata ba
ta taBa taka asibiti ba, kuma ba za ka sa ni zuwa
dole ba”.
“‘Saboda dalilin kin mai da mijinki jahili, k0
saboda girmama al’ada kin danne abin da ya
halatta' saboda toshewar basira irin taki, da take
sane. To kada ki sake yi min kuka a kan maganar
haihuwa
kin ji na fada miki”. .
Ya janyo bargo ya lulluBe jikinsa, zuciyarsa na yi
masa kuna, shi kam ya rasa baudadden ’hali irin
na Bahijja, dukkan abin da‘ yake kwadaituwa da
shi na
wayewa irin ta addini daga babban gida na
malamai ya kasa samu daga Bahijja, wata irin
tarbiyya ta dauka a gidansu haka ta take gaskiya
a fake da addini a. girmama bidi’a da al’ada.
Tabbas ya zama tilas ya yi wani abu a kan irin
zaman da sukeyi da Bahijja hanya mafi sauki ya
kai ta har gaban Malam da kansa ya fada masa
zuwansu ‘ .' asibiti ba kuskure ba k0 ta dauka ta
daina ganinsa wani wanda ba shi da ilimi mai
zurfi a kan addini. Ita kuma ta sauya irin wannan
baudaddiyar fahimtar tata;
Da tunani da Bacin rai bacci ya dauke shi, har
cikin baccin ma mafarkai ne
barkatai duk a kan matsalar da ya kwanta
da ita.
**********
Tunda Alhaji Saminu ya farka daga‘: baccin da ya
yi ‘cike da mafarkin yarinyar da ya manta da
maganarta tunda ya fahimci ba zai samu abin da,
yake,” so da ita ba, bayan rabuwarsu da ita ma
har: ya yi wata sabuwar yarinya Husna.
Ya sosa‘ tsakiyar kansa dan tunawa da fadan da
suka yi da matarsa NA’IMA kafin kwanciyarsa
bacci. .
Ya dai san shi ne ‘da lafi'ta .kuma‘ , kama shi
dumu—dumu .a.’ cikinsa, kwanaki uku 'da ‘suka
wuce ya yi mata Karyar ya-yi' tafiya zuwa Abuja.
Ya yi haka ne domin ya ; more huta’wa da'
sabuwar; yarinyarsa Husna‘, Sam ba ya san abin
da'zai raba sho da ita, tunda ya same ta yadda
yake so, ba kuma tare da ya sha wahala kamar
Amira ba.’ '”
Husna yana sakar mata bakin aljihu, ta mallaka
masa komai nata har ta yi masa alkawarin yi
masa kwanaki biyu a hotel din da ya kama dan
ya huta. ' .
Yammacin kwanakinsu daya suka fita super
market dan ya yi mata siyayya. A daidai inda
danja ta tsayar da su matarsa Na’ima ta ganshi
yana tare da Husna.
Duk da tana zargin mijin nata da neman mata
hankalinta ya yi mugun tashi, ‘ ba ta taBa
tsammanin zai yi mata karyar
tafiya ya tare a wajen karuwa ba.
Hannunta yana rawa ta lalubi wayarta ta danna
kira, tana hangenshi ya dauka, ta _yi Kokarin
daidaita nutsuwarta sannan ta ce. ,
“Sweety‘ kana ina ne? Yau'sam baka samu ka
kira ni a waya ba?”
Yace “Hankalina na kanki my lOVC ayyuka ne
suka yi min yawa, yanzu haka ina ofice,din Alhaji
Kabir na nan Abuja.
idan na gama da shi ma gidan Alhaji Amadu‘ Zan
WuCe"-Saboda’ ina so a _yi clearing din
kayannan
Ta sauke ajiyar zuciya, ganin yadda ya ma raina
mata hankali sai ta daure ta sake cewa da shi. ‘
“To yaushe kuma zaka dawo?
Ya juya ya dubi 'HUsna da 'ta ke watso masa“
harara'a fakaici ta gefcn ido, ya sa hannu ya riko’
nata hannun, idanunsa da sigar lallashi.
“To ga mu nan dai, amma inaga ’ sai na Kara
kwanaki uku nan gaba”.
Wani' abu ya
Cika matar, “idanunta da har saida ta zubar da
hawaye
“Kin gane k0 Na’ima?” Ya fada a diriricc, sai dai
ya makara,
tuni ta kashe wayar danja kuma ta ba su
hannu. Husna ta ce da shi.
“Lafiya dai Yallabai?”
Ganin duk hankalinsa a tashe yake,- yace. ‘“Kalau
kawai ‘yar matsala na gidana ne, matata ba ta da
lafiya”.
Ya yi karya yana bin Bayan motar Na’ima da ido.
Ya tsorata da irin gudun da ta ke yi', amma ba ya
son Husnah ta fuskanci wani abu dan haka ya ‘yi
mata Karya, ya kuma juya da ita zuwa hotel din
da suke ya ba ta hakuri zai je gida ya ga
‘ halin da matarsa ta ke ciki. , Yana fita ta doka
masa harara hade ‘ da jan dogon tsaki.
“Wannan shegiyar matar tasa duk ta
bata mana tsari, amma zan yi maganinta da
sannu”,
Yana isa gida ya tarar da Na’ima ta hargitsa
cikin dakinta da kaya tana zubawa a cikin
akwatuna.
Hawayen da ke zuba daga idanunta sun kasa
tsayawa, tana jin shigowarsa, amma k0 kallon
inda yake ba ta yi ba.
Hankalinsa ya tashi tunda suke fada ba ta taBa
yunkurin barinsa ba 'sai yau, k0 da ba ta fada ba
yagane manufarta. ‘ *
“Na’ima wai me ki ke shirin yi ne‘?”
-“Na yi shirin barinka Saminu tunda ba ni da
amfani a gidanka, har kana iya yin Kafiya dan
kawai ka yi kwanaki da karuwa? To ni mene ne
amfanina‘? Ai ba ni da amfani gara na barka ka
watayawarka ba tare da nauyina a kanka ba bare
harka ‘ shirya karyar tafiya”. ‘
Duk maganganun da suke yi ba ta yarda sun
hada ido ba, ya .karasa da sauri ya finciko jakar
da ta ke zugewa. .
“Na’ima na yi miki laifi, kuma
karbi laifina, ki taimaka min ki yafemin”.
“Ka nemi gafara gurin Ubangiji, ka tuba daga“
aikata mummunan saBon da kake aikatawa,‘-da
me-na rage ka da shi? Idan maba na gamsar da
kai me zai hana ka kara aure da irin wannan biye
—biyen da kake yi wanda barazana da lafiyarmu
gaba daya kake yadda cututtuka suka yi yawa”.
Ta yi furucin zuciyatta na zafi, duk
‘, da ba yau kadai ta soma zarginsa ba, amma na
yau‘ ya tsaya a ranta‘, yana mata matuKar Kuna
ta kasa iya danne kishinta har cikin ranta“ ta ke
‘ji gara Alhaji Saminu ya ,Kara aure
Ya soma lallashinta da magiya da rantse—‘rantse
da. shan alwashi na dainawa har ya samu ta
sauko. Sai dai tuban muzuru Saminu ya yi', wata
dabarar ya
'Sake shiryo mata. Ya_fita a can ya kai karfe sha
daya na daré bai dai kwana ba ya dawo
Ya farka da matukar jin sha’awar Amira a ransa
ya zana siffofinta na zahiri da ya gani cikin
mafarkinsa kadai ke yi masa gizo, burinsa nason
kasancewa da ita kadai ya dinga ninninku a
zuciyarsa. Ya tuna da yadda suka rabu da Amira
ya sani duk wata hikimarsa da dabarunsa sun
kare a kan Amira, ya kasa samun kanta.
Amira da Umma suna zaune a tsakar gida,
dawowar Umman nasu kenan daga wajen karBar
kaya, kamar yadda Amira keyi duk lokacin da ta
dawo daga gurin Malam tana ba wa Ummansu
labarin wani abin al’ajabin da Malam ya yi.
Haka ma yau ta ke ba ta labarin hirar matan da
ta ji sunayi a wajen zaman jiran Malam.
Ummansu ta ce
“Ai haka ne Amira, wasu mutancn Allah ya ba su
sanin lakani, wasu kuma baiwa ce da su saboda
kyakkyawar zuciya
da sun yi addu’a. Allah sai ya amsa. Ni dai burina
a ce kin yi aUre tun da kuruciyarki, da ma ga shi
dai Umaima da .muka je karBar ‘kayanta ba ki ga
kaya ba, abin gwanin sha’awa”. ‘ Ta soma lissafo
wa Amira yawan kayan lefen‘. wayar Amira ce ta
katse hirar ‘ saboda Kara'data ke yi, Amira ta
daga tana Korafin waye wannan da magribar
nan? Lokacin 'da -ta ga sunan Alhaji Saminu
akai, sai da numfashinta ya tsaya ta ja ajiyar
zuciya "kafin ta daga, sai da ta kalli Ummanta da
mummshi. ’ “Alhaji Saminu nefa”. Ta fada,
sannan ta daga wayar tare da mikewa tsaye
zuwa cikin dakinsu. “Hello ranki ya. dade”. “Tare
da naka. da ma anajinku?” Ya ce, “Ya' ya za ki
fada haka bayan kin sa wa‘ zuciyata «dabaibayin
da ki ka san
ba za ta iya nesa da keba
Ta yi murmushi mai hade da sauti
“Haka dai ka ce, amma wane ni?
Ya ce, “Kin isa har kin yi Yawa Amira, shi ya sa
ma kika Ki kirana lokaCI mai tsawo kin san zan
dawo ne-
Ta ce, “Ka manta sharadin da ka gindaya min ya
yi tsauri shi ya sa ka ji shiru.
Ya yi dariya, sannan ya ce
“Amira kenan ‘yar rigimata. Na janye wancan
sharadin, amma na samar mana mafita”.
“Wacce mafita ce wannan? Allah ya sa ba 2a ta
yi min tsauri ba”.
Ya ce “Idan ta yi miki tsauri Amira
dole na hakura, sona ne kawai ba kya yi”.
' “To ka fada min”. ' ~ “Kada ki damu zan zo mu
tattauna”. “To shi kenan, sai na ganka”. .‘suka yi
sallama, ta doka tsalle
rungume wayar tare da yin godiya ga Allah,
sannan ta nufi dakin‘Ummansu. “Umma Malamin‘
nan kamar' yankan wuka tun-ma bai gama aikin
ba kenan”....; ~ Daga nan ta fada wa Umman
gobe zai zo, Umma ta yi addu’ar Allah ya sa
alkhairi, ita ma farin ciki duk ya kamata. Washe
gari tun. da Amira ta idar da sallar asubahi ba ta
koma bacci ba saboda gudun .kada ta koma
lokaci ya qure mata zuwa wajen Malam, tunda
,ya ce ta zo da_ Karfe bakwai. harta ' yi wanka
ta shrya, bakwai da 'minti goma ta; dauki hanya
***************.
abun da ya yi matuqar Bata wa Nuraddcn rai
shime farkawa da ya yi ya
tarar da Bahijja a nade a gado ya ‘yi zaton
k0 ba ta da latiya ne, sai da ya tambaye ’ta' ya
fuskanci fushi ta ke yi da shi,‘ fushi kuma mai
tsanani, har ta kai duk maganar da ya yi mata ba
.ta ko tanka masa ga Bacin ran abin da ya faru
tsakaninsu, ga kuma abin da ta tashi. Da wannan
ya hadu ya sake tunzura zuciyarsa, yana yin
wanka k0 karyawa bai yi ba ya nufi gidan Malam
Balarabc. -
**********
Amira ta shiga soro na farko shiga na biyu babu
kowa, kamar yadda ta" zata sai dai ta ga Kofar
dakin Malam din a budw
ga shi ba kowa a wajen, don haka ta kwada
sallama a bakin kofar dakin.
Ga mamakinta sai ta ji muryar Malam din ya
amsa mata, kuma ya ba ta izin ta shigo cikin
zuciyarta ta ce
“Yauwa ya ma fito”.
Ta shiga dakin da sallama saBanin:
inda ya saba zama ta hango shi, daga can kurya
akan dardumarsa.
Ta gaida shi' idanunta a Kasa fuskar nan tasa
cike da kwarjini, ya nuna mata wajen zama kusa
ne sosai da shi.
“Ki zauna a nan, aikinmu na yau yana da ‘yar
wahala, ya bambanta da sauran shi ne kuma
mahadin na Rarshe
Ta ce “To”.
Ta tashi ta matsa sosai, ta ce masa.
“Jiya ma Alhaji Saminu ya yi min waya”.
Ya yi dan murmushi, “Zai 20 da kafafunsa, ‘aikun
da za mu yi miki a yau aiki. ne daza ‘ki mallaki
zuciyarsa, k0 bayan an ‘yi auran ma sai yadda
kika yi da shi. Amma fa sai kin ba mu' hadin kai,
rubutu ne za a yi miki a wasu Bangarori na jikinki
za a wanke a ba ki duk sanda ya zo ki ba shi ya
sha a cikin lemo k0 wani abin sha.
Idan kika yi haka sau uku shi kenan an gama da
shi sai yadda kika yi da shi”.
Ta ce“To”. Ba tare da wata fargaba ba, ta dai san
wanda aka yi mata wancan a tafin hannu ne,
wannan kuwa ba zai wuce
a bayan hannu k0 a tsintsiyar hannun ba.
Malam ya tashi ya yi dabarar fita ya‘ leka ba
kowa a wajen kamar yadda ya Sani, duk yaransa
suna wajen Malam Yahya
daukar karatu, ba kuma wanda zai fito sai wajen'
karfe tara da rabi kuma yana da cikakken tsarin
wannan dakin nasa na ganawa da baki, babu mai
shigowa cikin'sa sai wanda ya ba wa izini. : '
' Gudun kada Amira ta firgita da shi, shi ya sa bai
rufe kofar gaba daya ba, ya dai dan turata ya
dawo ya zauna, sannan ya dauko taWadarsa ya
Kara gumtse fuska.
“Yarinya bude kirjinki”. Wani irin faduwar gaba ta
ji. “Kirji kuma?” Ta nana a a zuciyarta,
wani Bari na zuciyarta ya ce.
“To me_ wannan babban malamin zai yi miki na
cutarwa? Kawai aiki ne ya kama a haka tunda a
.gaban Hajiya Kaka ya yi rubutu a hannu ba ta
hana ba, ai rubutu zai yi miki kawai”.
Abin da zuciyarta ta saka mata kenan, bayan
wani irin kwarj ini da Malam din yake yi mata. Ta
yaye mayafinta, sai a_ lokacin ta yi da na sanin
saka rigar da wuyanta ya dan bayyanar da wani
sashi na Kirjinta, ta soma kiciniyar jan rigar ta
rufe
Malam ya ce “Barshi haka, ai aikin zai zo bar
zuwa nan din”.
Haka ta zuba ido, Malam ya dinga rubutu da
hannunsa, tun daga wuyanta har
zuwa saman kirjinta, gaba daya Malam ya gama
rikicewa, idanunsa sun gama rufewa. Ya riKe ta
gam ya hada ta da Kirjinsa ganin ta soma ja da
baya kada ta kuBuce masa. Cikin wata irin murya
ya ce
“Yaya zaki gudu, wannan aikin idan aka fara shi
ba a bari sai an gama, idan ba haka ba baKar
Jaka za ki koma, ni kuma na
zam'a Alade”. “To...to”. Ta fada tana lumshe
baki, duk
jikinta rawa yake yi, ganin yana neman- keta
mata mutumci ya sa ta bude baki za ta yi Kara
ya sa hannu ya toshe mata baki. Ta soma ture
shi tana duka', amma kamar dutse k0 gezau ba
ya yi, burinsa bukatarsa ta gama biya. ‘
Nuraddcn ya shigo gidan ganin babu kowa a
kofar gidan ya sa shi shiga ciki ya ga babu kowa
ya daisan san Malam bai fitowa a daidai wannan
.lokacin - ‘ ‘ matsin da a yaji a cikin dakin
Mallam ,sai ya yi zaton shin wanene zai "masa
sallama da Malam din a cikin gida saboda shi
yana ganin rashin dacewa ya shiga cikin gidan a
daidai wannan lokacin,
za a iya zargin ba lafiya ba.
Yadda ya kejin zuciyarsa na suya ba ya bukatar
Bata lokaci a wajen Mallam, yana son ya ji daga
gare shi, sannan ya kawo masa Bahijja ya
tsawatar mata da kansa
Ya tura kofar hade da sallama, abin da idanunsa
suka gane masa Malam din na aikatawa da
yarinyar da bai san k0 wace ce' ba tana kiciniyar
kwatar kanta ya rufe mata baki. shi yai matuqar
tarwatsa kwanyar kansa
Juyawa ya yi da sauri ya ja da baya kansa ya
gama daurewa, ya ma rasa me ya . kamata ya yi
har ya fito waje bai san ya
fito ba, kafafunsa ne suka kasa daukarsa. Ya
durkushe a inda yake tsaye
mamaki da al’ajabi, bakin ciki da fargaba
su ne suka taru suka cunkushe a
jwakwalwarsa. Ya dafe kai ya runtse ido,
kirjinsa na bugawa da sauri. DA
0 comments:
Post a Comment