Dawowar ta daga Dumpeen Art Gallery kenan a matukar gajiye, rungume take da Al-Ameen wanda ta biya ta makarantar yara da take kaishi ta dauko shi. Har yanzu babu maganar aiki, ta rasa dalili ko ina taje sai sunce ta dawo nan da kwanaki kadan idan kuma ta koma sai dai su ce tayi hakuri basu da wajen ajiye sabbin ma'aikata, bata kawo komi a ranta duk da cewa abin yafi karfin ace coincidence ne saboda taje neman aikin yafi waje biyar Anna kullum maganarsu daya ce; babu space. Amma tana kyautata zaton zata samu da Dumpeen Art tunda su sabon guri ne budewar last week tasan karya ne su ce suna da cikakkun ma'aikata. Tana fitowa daga cikin art gallery din ta nufi inda tayi parking din motar ta, a bayan motar ta taga motar kamfanin su Uncle, ta dan tsaya jimm tana tunani can kuma sai ta girgiza kai, no way! Me zai kawo Uncle nan?? Ta shiga motar taja ta tafi.
A galabaice kwarai ta isa gida saboda yunwa, a falo ta samu Anti tana amsa waya da alamun daga Najeriya ne, ta kwantar da Al-Ameen akan kujera saboda yayi barci, ta maida dubanta ga Anti data kashe wayarta tace da kyar, "Anti yunwa!.... Akwai abinci?" Anti tace "yana kicin, yanzu na sauke" da sauri ta shiga kicin din ta fito hannunta dauke da kula, plate, fork, cokali, bowl da goran ruwa da cup a cikin wani babban tray, ta ajiye su akan karamin table taja shi har kusa da kujerar da Anti take zaune. Wani hadadden kamshin farfesu ya daki hancinta lokacin data bude kular, ba shiri ta hadiye yawu ji kake mukut!! Ta figi cinyar kaza data dahu luguf ta fara ci tana lumshe idanu kunnuwanta har motsi suke kan dadi, taci iya cinta ta sha romon kazar sosai tayi gyatsa ta ture kwanon gefe, anti tace har kinyi me? Tace koshi mana of course. Anti tace Aikuwa sai kin cinye kazar nan tass! Ajiye ta zanyi anjima na miki warming dinta, Ameenah murmushi kawai tayi, ta bude plate din da aka rufe da wani kyakkyawan kyalle, wainar kwai ce aka yi sharbebiya ta sha veggies kala-kala, tana kaiwa bakinta tauna daya tayi ta dakata tana son tuno inda tasan taste din wainar kwan, ganin anti bata nuna komi a fuskarta ba yasa ta basar kawai. Hatta da ruwan data sha lokacin sai data ji ya canza taste.
Washegari da safe bayan ta kai Al-Ameen makaranta ta dawo, anti ta kai mata breakfast dinta har daki, farfesun kifi ragon ruwa da yasha ganyen spinach da Irish potatoes a ciki, sai kuwa wainar kwai irin ta jiya. Ta kalli Antin da mamaki, "amma ya abincina ya banbanta da naku? Na ga tea da fried Irish kuka karya dashi yau?" anti tace "ahhh, yayi kadan ne shi yasa na miki naki daban" ta dan gyada kai cikin doubting, ta janyo abincin ta fara ci yayin da anti ta fita ta bar mata dakin. Da dare kuma ba sai ta kai mata gashin nama ba? Ya sha tumatiri da farar albasa yayi ruwa-ruwa yana ta tashin kamshin spices. Ta kasa hadiye mamakinta tace "wai ko dai kun cire ni daga girkin kune Anti? Naga ba abnd kuka ci ba kenan yau da dare!" Anti ta danyi dariyar yake tace kusan haka, tace me?? Antin ta basar, "ke kici abincin ki kada ya huce..., bari in dauko Al-Ameen yayi barci a dakin su Asleem" tasa kai ta fita daga dakin.
Kwana biyu abubuwa suka cigaba da tafiya a haka, tana tunanin abin zai ragu amma inaa! Karuwa ma yayi. Yanzu hatta da ruwan wankanta sai Anti ta zuba wasu ganyayyaki da wani abu mai dan banzan kamshi. Haka duk bayan kwana biyu sai tayi tsuguno, Anti tace wai maganin sanyi ne. Kai daidai da ruwan shanta ya zama na daban, jin shi take zaki cauu kamar zuma. Ta tuna lokacin da zata auri Marwan irin wannan abubuwan Anti ta dinga bata sai dai bai yi yawa irin haka ba, zuciyarta ta kasa natsuwa da wannan abun nasu Anti, bata fahimce su ba. Sai dai bata son zarginta ya tabbata, shi yasa a duk lokacin data bude baki da niyar tambayar su tsoron irin amsar da za a bata take yi. Shi yasa tayi shiru kawai ta zuba musu ido.
Har ta kwanta amma bata yi barci ba idanunta a bude suke tangaras tana kallon ceiling zuciyarta na mata sake-sake, Anti Jameelah tayi sallama ta shigo dakin hannunta dauke da mug, Ameenah ta zuba mata ido yayin da bakinta kadai ya motsa wajen amsa sallamar. Ta mika mata mug din, Ameenah ta amsa. Tatacciyar madarar shanu ce sabuwar tatsa kila ma ta yanzu ce, ta kai bakinta da niyar sha sai kuma ta fasa, tace "Anti in tambaye ki mana don Allah!" anti ta dan sha jinin jikinta, tace ehh, ina jinki. Tace me yasa kike bani kayan karin ni'ima ne? Ko dai kina da wata masaniya akan cewa Kawu zai min aure??" ta fada cikin faduwar gaba da tsoron irin amsar da Antin zata bata, ta gaji da nuku-nukun da ake mata, idan ma auren ne za ayi kawai a fito fili a fada mata sai ayi ta ta kare.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:04 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�45&46鈥⒙梆煇�
Aunty ta kalleta da mamaki, "ya aka yi kika sani??" a tsorace kuma a diririce ta kalli Antin cikin zaro ido, duk da cewa tayi tsammanin jin hakan amma kuma da taji sai taji abin yazo mata a bazata, unexpected as if Antin ta watsa mata dalma a kunne haka taji saukar maganar a kunnuwanta. Cikin kyarmar murya tace "kenan.... kenan.... Hakan yana nufin.... Da gaske aure za a min??" tausayinta ya cika Anti kamar zata fashe da kuka, tace kiyi hakuri Ameenah, muma waya kawai aka mana aka sanar damu zancen auren, kiyi hakuri ki rungumi zancen auren nan hannu biyu kuma da zuciya daya. Idan kika yi hakan zaki ga ribar biyayya ga magabata. Ki sanyawa zuciyarki salama Ameenah kin san halin Kawu Hamza sarai, ko ba tsoron abinda zai biyo baya idan kika ki amincewa da auren ba, kina ganin ya dace ki sa kimarsa da mutuncinsa su zube a idanun mutane??" taji jikinta ya danyi sanyi, gabadaya Anti ta daure ta da jijiyoyin jikinta. Ta sadda kai kasa tana kwararar da hawaye, bata damu wai tasa hannu ta share ba haka ta barsu suka yi ta zuba. Anti ta dafa kafadarta ta cigaba da mata magana cikin kwantar da murya, "kada kiyi fushi da zabin Kawunki Ameenah, Allah kadai yasan alherin dake ciki. Marwan is no more! You have to face the reality and move on with your life, nasan cewa ba zaki taba mantawa da Marwan ba. Amma Ameenah, ita 'ya mace kimarta da mutuncinta suna gidan aurenta, har zuwa yaushe ne zaki zauna a haka without a life partner? Shi auren nan yana da benefits da dama a gareki da Al-Ameen, ko babu komi zai bude ido ya ganku ku biyu and call you his parents! Zaki ji dadi ya bude baki da ido watarana yace miki Maah, wher is dad? Will u b fresh in it??" Ameenah tayi saurin girgiza kai, anti tace to ko don wannan, Ameenah na roke ki kada ki watsa mana kasa a ido, m begging youhh....!!
Sai kawai ta kece da kuka ta fada jikin Antin, kuka take ba kakkautawa. Anti ta dinga tapping bayanta a hankali cikin sigar lallashi, a ranta kuwa fadi take, "Ya Allah! Yaa Ladeef!! Rayuwar baiwar nan taka taga kaddarori iri'iri, ka tallafi rayuwarta data marayan d'anta kayi mata zabin miji nagari, Ya Allah ka albarkaci rayuwar aurensu Ameeen!" ta lumshe ido hawayen tausayin Ameenah na kwararo mata.
Anti ta cigaba da rarrashinta har sai data ga ta nutsu ta daina kukan da take yi sai dai shessheka. Ta tashi jiki a sanyaye ta mata sai da safe ta fita. Madarar da Ameenah bata sha ba kenan ta koma ta kwanta. Ta rasa yanayin da zuciyarta ke ciki, ita dai tasan cewa bata na'am da zancen auren nan. To amma kuma wani sashe na zuciyarta yayi na'am da hakan. Da taci gaba da tarawa da debewa sai taga ai kashi sittin na sassan gudanar da tunani na jikinta sun fi kawo dalilan ya kamata ta amince da auren. Ta tashi zaune dangargar a tsakiyar gadonta tana sake-sake, me yafi dacewa tayi yanzu? 'Neman zabin Allah!!" Wani sashe na zuciyarta ya rada mata hakan. Tsam ta tashi kamar wadda aka tsikara ta je ta dauro alwala tazo ta fara nafilah.
Daya daga cikin manyan kyawawan halayen Ameenah kenan, sam bata barin zuciya tayi ruling dinta. Ta kan nemi zabin Allah a duk wasu al'amura da suka cunkushe mata. Bata samu ta runtsa ba sai data sallaci asubahi.
喙涒櫏喙涒櫏喙涒櫏喙涒櫏
Lambu ne mai tsananin kyau, yana ta tashin kamshin kyawawan nau'ikan furanni da aka shuka a wajen ga bishiyoyin fruits dangin su peach, strawberries, mangoes, guava, berries, dama wasunsu da dama sun nuna sosai. Hadari ne ya gangamo sosai aka fara walkiya mai karfi da rugugin tsawa, kafin kace me! An kece da ruwan sama kaman da bakin kwarya.....
Cikin sauri ta tashi daga kan kujerar da take ta ruga da gudu tana neman mafaka. Daga can nesa ta hango wani kyakkyawan farin mutum tsaye cikin furanni yana shafa su da kyawawan fararen hannayensa yana murmushi mai kayatarwa, inda yake sam babu ko dishin ruwa. Sai ta kara karfin gudunta har ta cimma shi...., cike da murna, tsantsar mamaki da tsananin farin ciki take kallon mutumin daya rikide ya dawo MARWAN!! Yayi fari sosai, yayi wani irin haske mai ban mamaki, gassu tausasa shimfide a kyakkyawar fuskarsa da kuma hannayensa, fuskarshi na fitar da wani irin sheki mai tattare da annuri... Sai ta fashe da kukan murna ta afka jikinshi gabadaya, yayi saurin kaucewa rungumar data kawo mishi yana girgiza mata kai a hankali, yace "A'ah Ameenah!! M not ur Muharram, m no more ur husband kin manta ne??" sai ta tsaya ta ta kura mishi ido a nutse, tace Marwannn....! Ya saki kyakkyawan murmushin nan nasa yace "nazo ne na miki godiya akan irin rikon da kike yiwa gudan jinina Al-Ameen, ki sani duk addu'o'in da kike yi mun suna zuwa gare ni kuma Ina jin dadin hakan. Sai dai ki sani bana farin ciki ko kadan da gudun aure da kike yi, me yasa kike yin haka Ameenah??" sai ta zube bisa gwiwarta tana kuka a hankali mai tsuma zuciya, tace "ina jin tsoron in sake yin wani auren in rasa damar sake haduwa da kai a gidanmu na gaskiya a matsayin ma'aurata!!" ya sake yin wani murmushin yace "Ameenah!! Kowane dan Adam da kike gani yana da kaddararsa, tamu kaddarar kenan muma don haka dole mu rungumeta da hannu biyu, kiyi hakuri ki daina kuka. Kin ga mata na sun zo, zan koma tare dasu..." ta daga kanta a hankali ta dubi wadanda Marwan ya kira da MATAN SHI! Duk iya kwatancen ta da lissafinta ta kasa kwatanta siffofin MATAN MARWAN! Abinda ta sani kawai shine matane masu wani irin haske marar misali wanda bata taba ganin kwatankwacinsa ba. Suka matso gare shi kowace ta kama hannunshi ya dubeta fuskarshi na dauke da murmushi yace "bye Ameenah, sai watarana.... Kin ga mijinki can, wanda zai kula dake fiye dani yana jiranki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku!!" Ameenah ta shiga girgiza kai tana kuka tana rokon shi akan kada ya tafi, wata sansanyar iska mai ni'ima ta fara hura ta, ta lumshe idanunta kadan. Budewar nan da zata yi sai wayam! Babu Marwan babu Matan shi!! Ta tashi da sauri tana waige-waige tana kwala mishi kira, ruwa ya fara jigata amma bata yi yunkurin neman mafaka ba.
Tana cikin waige-waige ta hango wani giant mutum ya juya mata baya hannunshi rike da bazara, a gefenshi wasu kyawawan yara ne suna ta wasanninsu cikin nishadi. Kamar wadda maganadisu yake ja haka ta ji ta tunkari mutumin kamar ba kafafunta take takawa ba. Tun kafin ta karasa gare shi ya juyo fuskarshi cike da annuri. A tsaye yake sosai, mutum ne wanda ilimi da baiwarwaki suke baiyane akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da kwarjini, kalar fatarshi kuwa za a iya kiranta baka. Bayan wannan babu abinda zata iya karaswa game dashi...
Mutumin ya tare ta da wata runguma mai laushi, suma yaran nan sai suka rugo da gudu suka rungumeta suna kiranta da MUMMY!! Mutumin ya dauki daya daga cikin yaran ya sumbaci goshinta, ya mikawa Ameenah yace "karbeta ta Ameenatu.... Hasken idaniyar mu ce, gudan jininmu!" sai ta samu kanta da sakin murmushi, yayin da taji kaunar yarinyar ta mamaye mata zuciya. Ba musu tasa hannu ta amshi yarinyar ta rungumeta, mutumin ya kamo hannunta suka juya suna tafiya a nutse, wani kyakkyawan kerarran gida suka nufa dake cikin lambun, sauran yaran suka rufa musu baya.....!!
*******
A hankali ta fara bude idanunta, maimakon cikin lambu, sai ta ganta a dakinta, kwance akan gado! Tayi-tayi ta tuno fuskar mutumin nan amma ta kasa amma jikinta na gaya mata cewa tasan shi. Anti data jima a tsaye akanta tun dazu tayi gyaran murya tace Ameenah lafiya? Tayi firgigit ta kalli wajen da taji sautin ya fita, ita din ce dai. Ta bude baki a hankali idanunta cike da kwalla tace "mafarkin Marwan nayi Anti" ta zauna a gefen gadon ta kamo hannuwanta duka biyun ta damke cikin nata tace Marwan kika ce? Ta gyada kai kafin ta bata labarin duk abinda ta gani a cikin mafarkin.... Anti tayi shiru tana kallonta cikin nazari, can kuma ta nisa a hankali ta dubeta tace "me kika fahimta game da wannan mafarki? Ta runtse idanu a hankali tace "na fahimci kara yin aure na yana daya daga cikin dalilan da yasa Marwan ya tafi ya barni! Kuma shi kanshi Marwan din yana farin ciki da kuma na'am wa auren da zan sake!" Anti tace bayan wannan da?! Ta girgiza kanta a tausashe alamun babu. Anti tace tabbas auren nan yana nufin abubuwa da dama ciki har da mutuwar Marwan. Rabo! Rabo ajali!! (Aysha Kurah) ,kuma wani baya haihuwar dan wani. Don haka ki kara hakuri Ameenah kina jina? Ta gyada kai a sanyaye, jikinta yayi laushi tubus tun daga mafarkin da tayi. Anti ta shafa kanta tana murmushi tace to tashi kiyi wanka, it's past eleven already. Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta, tayi saurin kallon gefenta, wayam! Babu Al-Ameen, ta kalli Anti zata yi magana ta tare ta ta hanyar cewa "Uncle ya kaishi makaranta tun dazu" sai ta dan saki murmushi kawai ta tashi ta fada toilet. Yanzu ma haka ta tarar da bath tub cike da ruwa, an zuba wasu irin furanni a ciki yana ta tashin kamshi mai sanyi. Ta dan ja wani siririn tsaki don tasan aikin Anti ne, rariya ta bude ruwan yabi ta ciki ya fita ta sake hada wani ruwan ta matso kumfa ta shiga ciki. Kwanciya tayi a cikin ruwan ta lumshe idanunta, bata san iya adadin lokutan data bata ba sai da taji Anti ta kwankwasa mata kofa sannan ta bude rariya ruwan ya fita, ta dauraye jikinta ta fita. Ko mai bata tsaya shafawa ba ta saka jallabiya ta fito falo. Anti ce kawai a falon, ta karbi hutun karshen shekara ne a wajen aikinta. Kai tsaye dinning ta wuce ta hau daga kuloli, tsaki kawai take yi don kuwa gashin kifi ne da yasha magungunan data tsana, da wani irin kunun alkama da yasha hadin data rasa ko na menene, haka nan dai ta zauna ta dan tsakura ta tashi ta koma dakinta. Gyale ta yafa ta saka wani flat sandal na roba ta fita, unguwan ta shiga zagayawa da kafa saboda damuwa da kadaici da suka dameta. Anti Rukky ta kira ta suka sha hirarsu amma bata yi mata zancen daya danganci aurensu ba, itama sai bata tada maganar ba. Sai data je makarantar su Al-Ameen ta dauko shi sannan ta koma gidan. Da dare duk suna falo tana koyawa su Asleem assignment, Al-Ameen na gefe ta tura mishi puzzle piece na haruffan larabci yana ta bugawa. Uncle da Anti suka fito daga dakin Uncle din, Anti Jameelah ta wuce kicin zata hada mishi dinner shi kuma ya zauna akan kujera yana kallon Ameenah fuskarshi dauke da murmushin tsokana, yace "Amarya... Amaryah....!!" nan da nan annurin fuskarta ya bace bat kamar daukewar ruwan sama. Ta wani cune dan bakinta gaba kamar gidan tsutsa tana kunkuni, Uncle ya fashe da dariya. Anti ta fito daga kicin da tray a hannunta ta zauna a gefen Uncle ta fara serving dinshi, jefi-jefi suna hirar bikin Ameenah. Haushi ya cikata yazo mata wuya, sai kawai ta tashi ta sungumi danta ba tare data kara kallon su Uncle din ba ta nufi dakinta. Uncle ya kira sunanta, "Ameenah!" yana kokarin danne dariyar data kamo shi. ta dakata ba tare data juya na, yace "ki fara shiri nan da kwana uku zamu tafi Nigeria saboda kwanaki shida suka rage daurin aurenku" ta juya tana kallonsu kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa kawai ta gyada kai ta tura kofar dakinta da sauri ta fada, suka bi bayanta da kallo cike da alhini. Bayan kofar tabi ta sulale a hankali, tasa duka tafukan hannayenta a fuskarta ta fashe da wani irin matsanancin kuka zuciyarta na mata zogi, sai da tayi ya ishe ta kafin ta lallashi zuciyarta ta tashi daga bayan kofar. Ta shimfide Al-Ameen akan gado, ta zauna a tsakiyar gadon ta kura mishi ido tana kallonshi cikin tunanika daban-daban, iri-iri, kala-kala.....!!.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:05 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�47鈥⒙梆煇�
Ana washegarin zasu tafi Nigeria, komi na tafiyarsu ya kammala. Duk wasu kaya na sakawa a gida tun daga kan furnitures, kitchen wares, kai hatta da cokali daga India aka saye shi, tuni Uncle ya auna su zuwa Kano. Anti kuma ta dage da kimtsa ta abinda ya danganci gyaran jiki ciki da waje, jiya ma a Dulhania Saloon suka yini, wata shahararriyar mai gyaran jiki Xehrah Mahendi ta yaryarawa Ameenah kunshi sannan ta mata gyaran jiki dana gashi. Ta fito sak a amarya kuwa. Yanzu ma tana zaune ne kawai tana karewa lallen hannunta kallo, ya zanu ya matukar yin kyau. Anti ta shigo dakin hannunta rike da silver bowl karama data dama tukudi a ciki yasha kwakwa da dabino, zuma har dasu cikwi. Ta mikawa Ameenah, maimakon ta amsa sai ta cuno baki, tace kina yiwa Allah Anti ki daina dura min kayan nan haka, baki san irin wahalar da nake sha ta dalilinsu bane. Anti tayi dariya tace ashe dai suna aiki, daidai kenan. Ke kin fi so ne kije masa salam ba taste kamar ruwa? Ina so ne in sa surikin nawa ya gigice, ya kasa tantance wai Budurwa ce ne ko kuwa Bazawara??!
Ameenah ta kara turo baki tana wani hura hanci, tunda taji cewa Abdul-Rasheed Modibbo ne angon ta sanya ranta a inuwa akan abinda take kulafucin kada wani ya dandana bayan Marwan. Tace Anti kina yin abu kamar baki san halin Modibbo ba? Anti tace sanin halin nasa ne yasa nake so na rikita shi da fatar jikin ki ma kawai kafin akai can ciki.... Ai ke dai Allah ya nuna mana ranar auren nan lafiya mu sha bidiri. Maza ki shanye tun kafin ya sha iska. Ta amsa tana yamutsa fuska kamar wadda ta amshi kashi, Anti tace eyh, koma me zaki yi dai sai kin shanye shi tass kin bani kwanon nan Ina tsaye a kanki!! Ita karfin halin Antin ma sai ya dawo bata dariya, dole ta murmusa ba don ta shiryawa hakan ba, Anti tace to ko ke fa, Amaryar mu??!.
*GOMBE....*
kwance yake akan irin wooden couches dinnan na hutu da aka tanada a gefen swimming pool din dake cikin Vomella Hotel dake cikin Gombe, Modibbo ne yake sana'ar tashi (tada hayaki). Da yammar nan ya iso Gombe bisa aikowar mahaifanshi, sun ce yazo su kara fahimtar juna shi da amaryar tashi su kuma tsara yadda bikin nasu zai kasance. Wannan wata babbar dama ce a gare shi ta wargaza zancen bikin cikin ruwan sanyi ba tare da sunan shi ya fita ba, don haka koda ya karaso Gombe bai tunkari gidan su amaryar ba ya nemi babban hotel ya kama. Ya bari sai gobe ido na ganin ido zai je ayi ta ta kare, ya huta da wannan makalallen auren, in yaso daga baya sai ya nemo mace wadda yake ganin ta dace dashi, karfaffa ba irin wannan er shalau din ba kamar igiya, wadda yake ganin duk ranar da tsautsayi yasa ya rutsa da ita ya dora mata nauyin kirjinshi, sai dai wata amma ba ita ba, don kuwa raga-raga zai yi da ita. Don haka Allah-Allah yake gari ya waye yaje su hadu, shi kadai yasan kudirin dake ranshi.
*****
Ta 6angarenta ma jiran zuwan shi kawai take yi, tana tunanin cewa tana da wata dama ta karshe da zata kashe zancen auren nan ya mutu murus, tana jin cewa zata iya zaman aure da kowa amma banda mai baudadden hali irin Modibbo!
Koda sakon zuwanshi yaje mata a washegarin ranar, bata ji ko dar ba ta zari gyalenta ta tafi har wani harbin iska take yi, zuciyarta na gaya mata wannan shine 'The End' na zancen aurenta. Tasan cewa Modibbo baya daukan raini ko kadan, kuma baya son wulakanci, to abinda tayi niyar yi mishi kenan, tasan cewa idan tayi haka to babu yadda zai ci gaba da auren nan tunda tasan cewa shima ba son auren yake yi ba. Anti ta bita da kallo cike da faduwar gaba, Ameenah must be up to something, tasan ruwa baya tsami banza. Farin cikin dake shimfide akan fuskarta abin tambaya ne, sai ta shiga addu'ar Allah yasa ba ruwa zata ballo musu ba don tasan halin su biyun kamar yunwar cikinta.
Yana cikin motar da yazo a cikinta Discussion Continues sanye da suits na wani cotton mai tsananin taushi maroon color, yasa bakin tie da bakin cover shoe, rigar ta sama ya ajiye akan kujerar mai zaman banza ya bar er ciki fara kawai, fuskar nan tasha wani makeken sun glass na Prada wanda ya mamaye rabin fuskar. Kafarsa daya na cikin motar daya na waje, idanunshi nakan kofar sashen su yana jiran fitowarta.
Can sai gata ta bullo tana takun nan nata mai daukar hankali, cike da natsuwa.....
Bai gasgata abinda idanuwansa ke hango masa ba har sai daya kai ga zare gilashin idonsa ya runtse ido na dan lokaci, ya sake budewa, but still, ita din dai yake gani tana tunkaro shi. Yarinyar nan fara... mai zubi da kira mai kyau... Aljanar shi... Wacce gani biyu ya taba mata a rayuwar shi amma ta cigaba da zuwar mishi cikin mafarkinshi!! Kar dai??... Ko dai....???! Ya shiga girgiza kansa cikin wani irin yanayi, sam ya gaza tantance halin da zuciyar sa ke ciki, farin ciki ko akasinsa??
Gare ta kam, tunda ta tunkaro shi taji gabanta na bugawa sosai, wani irin kwarjini ya mata marar misali. Sai dai ta kasa tantance ma'anar kallon da yake jifanta dashi wanda tafi kyautata zaton shine ya haifar mata da faduwar gaban. Har ta matso kusa dashi idanunshi na kanta cikin wani mayataccen kallo kamar wanda ke son gano wani abu a fuskarta, ba zato ba tsammani taga yaja murfin motar ya rufe garammm! Kamar tashin duniya, ya kuma warci motar a dari da tamanin ya bar gidan. Sai tayi turus tabi motar da kallo bakinta a bude, da salon rashin mutuncin da yazo dashi kenan? Ai kuwa daidai kai ka samu. Tana daga idonta ta hango Kawu Hamza a tsaye daga can kofar sashen shi, babu mamaki ya ga duk abinda ya faru a tsakanin su, bata nuna alamun ta ganshi ba ta hau matse hawayen karya zuciyarta fal farin ciki, tasan Kawu Hamza will not stand it.
Kawu Hamza kam iya shaka ya shaka sosai, wannan wane irin wulakanci ne surikin nasu yazo dashi? A fusace ya koma cikin gida ya lalubi waya ya dannawa Mukhtar kira, yace lallai-lallai ya nemo Modibbo duk inda yake a garin Gombe yana nemanshi, bai kara ko a ba ya kashe wayar ya bar Mukhtar cikin faduwar gaba da tambayar kanshi lafiya???
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:05 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�48鈥⒙梆煇�
Modibbo kuwa Allah ne kadai ya kaishi masaukin sa lafiya, ya shige dakinsa ya kulle da makulli ya hau kan gado ya kwanta ruf da ciki idanunsa a runtse gam. He still couldn't believe what he'd seen, did he really saw ha? Was it not illusion?? Kai ko dai mafarki yake yi ne? Nan ya tashi zaune ya fara mintsinin tattausar fatar hannunshi, da alamun dai da gaske ne hakan ya faru.
Yana cikin wannan halin kiran Uncle Mukhtar ya shiga wayarshi, a kasalance ya daga, ya tambaye shi yana ina? Sai ya rasa abinda zai ce, babu mamaki yayi witnessing rashin mutuncin daya zabgawa Ameenah ne yanzu, da kyar ya lalubo abin fada, yace "ina nan asibitin fata na Gombe, dama akwai wasu ayyuka da zanyi acan din to kuma yanzu har na shigo gida zan ga Ameenah sai aka min emergency kira, shine na tafi tun gabanin mu gaisa., yanzu haka ina shirin shiga tiyata ne ka kira ni!" Uncle yace to Allah ya kyauta, dama Kawu Hamza ne yace a kira ka yana nemanka, bari in sanar dashi. Suka kashe wayar a lokaci daya. Modibbo ya sake wata kakkarfar ajiyar zuciya fuskarshi dauke da murmushi, so it's her! Yarinyar data hargitsa mishi tunani ta mayar dashi wani gaula! Ashe bakar yarinyar nan ce, ita ce Ameenah. Farin ciki ya cika shi ya rasa me ma zaiyi? Ba zato ya kwala wani kakkarfan ihu, ya fara birgima akan gadon yana ihu kamar wani sintacce, daga karshe ya diro daga gadon dalilin kiran sallah da aka yi, ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita zuwa Masjeed. A can ma bayan an gama sallah mikewa yayi ya fara jero nafilfili yana mai godewa Allah bisa wannan kyauta daya mishi, da ace ya 6ata auren nan tuntuni da hakika ya kasance cikin dana sani mara amfani for the rest of his life, and he wouldn't be able to forgive himself idan yayi hakan!!
Da misalin karfe biyar na yammacin ranar, tsaye yake a gaban dressing mirror. Wata shadda ce getzner ruwan makuba da aka mata dinkin Abacha a jikinshi, ta mishi kyau sosai yadda kasan bashi ba, ya dora karin hula ta zauna mishi das, turarukan daya fesawa jikinshi kuwa basu da adadi. Kanshi yake karewa kallo yana son ganin ta ina zai ga wata makusa? Amma bai gano komi ba, ya saki kayataccen murmushi tare da daukar makullin motar shi ya fita. A nutse yake tukin zuciyar shi na azalzalarshi da son sake ganin Ameenah. Tunanin ta sigar da zai je mata yake yi, matsayin masoyi? Ko kuwa wanda zai aureta kawai? Da wadannan tunanikan ya tura kai falon Kawu Hamza bakin shi dauke da sallama, Uncle Mukhtar ya biyo shi a baya.
Tana sashen Yaya Abdul-Hadi ana ta shirye-shiryen walimah da za ayi gobe da safe anan farfajiyar gidan. Tana zaune ne kawai, amma sam tunaninta baya tare dasu, ta cilla wata duniya ta daban. Imran dan gidan Ya Abdul-Hadi ya shigo inda suke da gudu yana kwala mata kira, ta dube shi tana dan murmushi tace ya aka yi ne Imu na?? Yace Kawu Hamza yana kiran ki. Gabanta kam ya fadi sosai, ta tambayi kanta me ya faru? Haka nan dai ta mike ta tafi cike da taraddadi.
A falon na Kawu durkushe take a gabanshi cikin dar-dar kamar ace mata at! ta fece da gudu, ta dan saci kallon Modibbo daya nutsu sosai a gaban Kawun kamar wani kamilin gaske, shima ita din yake kallo. Tayi saurin kau da kanta gefe bayan ta auna mishi harara. Kawu yayi gyaran murya ya dubesu yace "dalilin tara ku anan wajen ba wani dalili bane sai don na kara tambayarku game da ra'ayin juna musamman ke Ameenah, bana so daga baya wani abu yazo ya faru a kuma zo ana kuka gani. Don haka Ameenah menene ra'ayin ki game da wannan aure? Kina da matsala dashi ko kuwa??" ta ciza tattausan lebenta na kasa cike da wani irin murmushi, babu mamaki Allah ne ya dubi halin da zata shiga ya kawo mata wannan kyakkyawar damar. Babu jin ko dar game da hukuncin data yanke tace "zan amince Kawu, a bisa sharadi daya; idan har ya amince da zaman Al-Ameen tare dani, ba kuma zaman agolanci ba to babu damuwa daga bangare na, na amince!" Kawu ya maida kallonshi ga Modibbo da zufa ta yanko mishi, yace to kai kaji abinda Amaryar taka tace, shin ka amince??
Ya saci kallon inda take zaune, kanta na kasa amma yana hango wani kwantaccen murmushin mugunta a bisa fatar bakinta, nan ya kamo bakin zaren. Ya dage gira sama, wato abinda ta kulla kenan? Tana tunanin idan tayi hakan zai ki amincewa ne? Ai kuwa idan hakane u're wrong Ameenah! Ba wai da daya na, idan ma duka duniyar ne zaki tare da ita a gidana I will accept u, as a wife and they, my children.., ganinki kawai tare dani babban makami ne na kare kaina daga bacin rai.
Sai yayi murmushi ya kalli Kawu daya zuba mishi ido yana jiran amsar shi, yace Kawu na amince, na kuma yi alkawarin rike shi amana tamkar dan dana haifa a cikina!.
Fuskar Kawu ta washe da farinciki sosai, yace Masha Allah! To ke Ameenah kin dai ji abinda yace. Allah ya gani na fita hakkin ki, don haka aure babu fashi. Jibi war haka an daura In shaa Allah!! Ku tashi kuje na sallame ku, Allah ya muku albarka. Yadda kasan wadda aka bugewa kafafu haka Ameenah ta mike da kyar, jiki a sanyaye ta fita. Ya kara dukawa yawa Kawun sallama ya rufa mata baya da sauri. Kawai ganin mutum tayi ya tari gabanta, taja ta tsaya ta kama kugu tana kallon shi fuskar nan kamar wadda taga mala'ikan mutuwa. Tace malam lafiya? Ya daga kafada, ita ta kawo haka malama! Naga Kina shirin wucewa ne ba tare da kin tsaya mun tattauna yadda zamu tsara bikin mu ba. Ta kara tamke fuska tace "Malam ni babu wani biki da zanyi, idan kai kaga zaka iya sai kayi amma fa ba dani ba" yace "ahhhh! Sai Yanzu kika tuna min. Ashe fa matar tawa ZAWARA ce! Su kuma Zawarawa ba ayi musu biki irin na 'YAN MATA..... Well, ki godewa Allah ma zaki samu albarkacin 'yanmatan da za a hada ku tare dasu ayi shagalin biki mana, don haka dole zaki je duk bukukuwan da za a gudanar" tace dalili?? Zuciyarta cike da takaicin kalmar Zawara daya kira ta da ita. Yace "dalili? Saboda nima zan je, idan har zan je ya zamar miki tilas kema kije!" taja tsuka, "to ba zan je din ba, sai dai idan gawana za a cicciba akai wajen bikin". Ta bi ta gefenshi zata wuce, ya janyo hannunta da karfi ta dawo gabanshi suna fuskantar juna, ya maida fuskar shi ya dinke tsaf daga sassauta din da yayi. Yace watch your mouth Ameenah, don ina shirin zama mijinki ba wai yana nufin zan zauna ne ina fadar magana kina mayar min gatsar babu respect ba kin gane? Yasa hannu a aljihun shi ya ciro bundles na dubu ya kamo hannunta ya dora mata su, "ga wannan kiyi hidimar biki dasu ke da kawayen ki, ni yau zan koma Kano in shaa Allah gobe zan juyo tare da abokai na, Jibi a daura aure in dauki er Bazawarar Amarya ta mu tafi Kano....!" Haushi ya kawo ta wuya, anya yasan irin dafin dake tattare da kalmar nan tashi ta zawarci? Ba zata iya jura ba..., da gudu tabi ta gefenshi tayi part din Yaya Abdul-Hadi. Ya bita da kallo yana jin kamar ya bita ya kamota ya rungumeta ya lallashe ta don yasan ya bata mata rai sosai, sai dai idan yayi hakan ya bada kanshi da wuri, ya kula yarinyar sai an biyo da ita ta bayan gida kafin a daidaice da ita, ya kada kanshi ya fada mota ya mata key ya dauki hanyar Kano, to sauka lafiya!
Can kuryar dakin Anti Nadiya ta shige tana huci kamar wata tsohuwar zakanya. Anti Jameela ta biyo bayanta don ganin yadda ta shigo a gigice, ita kuma daidai lokacin tayi jifa da kudin, Anti ta cafe su ta waro ido a kansu tace "yauwa! Angon nan naki yasan yayi abu at d ryt time, kamar dama yasan tunanin inda zan lalubo kudin da za a sayo kulolin da zaa raba a wajen walimah nake don na hannunmu sun kare tun a cikin gida, kin ga sai a karo da wannan!" ta juya ta fita tana kwalawa Sadi kira. Ameenah ta bita da kallo cike da takaici, tana jin kamar taje ta kwace kudin ta yayyaga su gutsi-gutsi.
鈽�**鈽�**鈽�**鈽�
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:05 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�49鈥⒙梆煇�
Karfe takwas da rabi na daren ranar a cikin farfajiyar gidansu ta mishi, ya kashe motar ya fito cikin wani nutsattsen taku fuskar shi na dauke da kayataccen murmushi, jinshi yake kamar wanda aka yiwa albishir da gidan Aljannah. Yayi sallama a kofar falon tare da tura kofa ya shiga a lokaci guda, Ummie da Safeenah ne kawai a falon da alamun suna sirrantawa ne, baki en biki wadanda suka zo suna sashen baki har sun kwanta. Ya zauna akan kujera kusa da Ummie yana wasa da makullin motarshi, farin ciki da dokin dake fuskar shi sun kasa boyuwa. Cike da mamaki suke binsa da kallo, kamar kuma suna doubting anya Modibbo ne kuwa? Yanayine da basu taba ganin irinsa a tattare dashi ba, hatta da mahaifiyarshi kuwa a iya tsawon rayuwar ta. Safeenah tace Yaya wat happened? U look so happy, jubilated...me ya faru ne hmm?? Ya kara sakin wani tattausan murmushi triumphantly, feeling so high. Sai Biebie ta kara sake baki tana kallonshi cike da mamaki marar misaltuwa, bata taba ganin Yayan ya murmusa haka ba. Mutumin da sam ganin murmushi a fuskarsa na en sakanni ne amma ji yadda yake ta murmushi tunda ya shigo, kana iya hango tsabar Farin ciki da murna shimfide a kwayar idanunsa, gashi nan kuma zane baro-baro a fuskarsa. Ta tabbata koma meye ya faru ba karamin al'amari bane. Yace babu komi Safeenah Amarya, kawai ina cikin muuudu mai kyau ne kawai. Ummie tace ya aka yi ka dawo yanzu? Yace gobe in shaa Allah zan koma tare da abokaina. Tace to Allah ya kaimu ya amsa da ameen Ummie, bari in je in kwanta, m extremely tired wallahi, very tired!! Ummie tace gashi Mukhtar yace a tambayeka a inda za a kai kayan Ameenah, gobe zasu iso daga India. Yace a kaisu gidana na Lamido crescent, acan zamu zauna. Ummie ta gyada kai, "amma da kake cewa ba zaka zauna acan ba?" dariya kawai yayi ya tashi ya musu sai da safe, Safeenah tace Yaya Ango!! Cike da tsokana, tasan cewa harara ce zata biyo baya don kuwa baya son sunan ko kadan. Amma ga mamakinta sai ya watso mata fararen hakorannan nashi tas-tas dasu har wani reflecting suke, yace haka yake amaryar mu Safeenah...! Ya fita daga falon yana en wake-wake cikin nishadi. Suka bishi da kallo suna tattaunawa game da canjin da suka gani tare da Modibbo kamar bashi ba.
Yana shiga daki ruwa ya fara watsawa, bayan ya fito daga wanka ya zura kayan barci ya dauki waya ya samu gefen gado ya kwanta ya shiga kiran abokanshi yana fada musu daurin auren shi Jibi ne, duk sun sha mamaki suka yi ta mishi korafin kin sanar musu da wuri da yayi, hakuri kawai yake basu yana cewa daurin auren ne yazo kai tsaye shi yasa. Wasu sun ce a goben zasu bishi, wasu kuma suka ce sai ranar daurin auren zasu je, wasu kuma suka ce idan amarya tazo zasu je su gaisa. Dariya yayi yace ko basu zo ba ya gode da fatan alkhairin da suka mishi.....
Farfajiyar gidan ta Wakili's estate cike take da manyan canopies marassa adadi, babban guri ne da aka tanada musamman saboda shagulgula irin wannan. Amaren guda uku sun sha adon riga da siket na wani tattausan yadin silk sky-blue, Anti Jameelah ce tayo musu shi daga can India, sai aka dora musu alkyabba baka a jikinsu. Suna zaune akan wasu kujeru na alfarma sun fuskanci dubban jama'ar da halarci taron walimar auren su zazzaune akan fararen kujerun roba a karkashin canopies din. En jaridu da masu daukar hoto na gefe suna daukar hotuna, Wakili's Family babban family ne daya tara manyan en kasuwa, en siyasa, ta bangaren army ma ya tabo manya, family ne wanda ciki da wajen Gombe babu wanda bai san da zaman su ba, daidai gwargwado mutane suna girmama su. Muryar Malama Atika Abubukar ta karade wajen da sautin Wa'azinta ta hanyar lasifika, tayi magana akan hakkin miji akan matarsa da hakkin mata akan mijinta da kuma hakkokin da suka rataya akansu su duka, ta tabo mafi yawan matsaloli da ma'aurata suke fuskanta a wannan zamanin da kuma hanyoyin da take gani yakamata abi domin a magance su. Da yawan matan dake wajen jikinsu yayi sanyi sosai da wa'azin malamar, suma amaren jikinsu a matukar sanyaye yake saboda tunawar da suka yi cewa gobe war haka fa wani nauyi ne zai hau kansu wanda shi zai yi sanadin zuwansu Alanna idan sun sauke shi ta hanyar data dace, kuma dai wannan nauyi zai iya kaisu zuwa wuta idan har basu kiyaye dokokins sa ba. Ameenah kuka take yi sosai, tana rokon Allah akan yasa ta yiwa mijinta biyayya irin wadda Malama Atika tace mace na yiwa mijinta, tana tsoro! Tana tsoron zuciyarta, tana tsoron zuciya ta hana ta bin mijinta Allah ya jefata cikin azabarsa.
Daga karshe Malamar ta rufe taron da addu'a da fatan alkhairi ga Amaren, aka watse daga taron bayan an bi duk wanda yazo wajen da jaka irin ta biki mai dauke da sunayen duka amaren da angunansu, akwai kula a cikin jakar itama da sunayen couples din, kowa ya tafi yana musu fatan zaman lafiya mai dorewa.
Aka bar Ameenah a zaune har zuwa lokacin tana kwararar da hawaye cike da alhinin irin sabuwar rayuwar da zata shiga gobe. Sauran amaren kuwa tuni sun shige cikin kawayensu suna gaisawa dasu don haka babu wanda ya kula da halin data shiga. Ta mike a hankali take tafiya, kanta na masifar sara mata sam bata da karsashi. Can kuryar dakin Anti Nadiya ta shige ta kulle kofa ta kwanta ba don tana jin barci ba, Al-Ameen yana wajen Ya Faruq don haka bata damu data nemi inda yake ba. Har zuwa lokacin da nata angon ya iso tare da zugar abokanshi cike da dokin sake dora ido akan kyakkyawar fuskar ta, yau kawai da bai ganta ba zuciyarshi a matukar galabaice take. Amma neman duniya aka rasa Ameenah a cikin gidannan, an kuma kira wayarta aka ji a kashe. Sai jikin shi yayi wani irin sanyi, duk yadda yaso ya boye damuwar ranshi game da ita abin yaci tura, bai san me yasa ba yarinyar na da wani irin tasiri a ranshi wanda yasa sam bashi da wani katabus muddin akanta ne. Abokanshi sun lura da halin daya shiga a take, very disappointed, missing his bride very badly. Sai suka shiga mishi tsiya, wai ya daure mana, yau ne kawai ya rage, gobe war haka suna tare ta zama tashi. Hakora kawai ya dinga watsa musu cikin yake, don kuwa can kasan zuciyar shi is aching him, ita kawai yake son gani. Kawai sai suka shiga cikin sauran angwayen ana ta hirarraki da en matan amare, Sai bayan magariba suka bar gidan.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:05 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
*A LOVE STORY SEALED WITH CHALLENGES.....*
馃惥掳鈥�50鈥⒙梆煇�
Ameenah bata fito daga dakin ba sai da tara na dare ta gota, tun lokacin tana kwance babu abinda take yi sai kuka da tunanika, idan an kira sallah zata tashi tayi tunda akwai toilet a cikin dakin. Dama dai ba a zancen abinci, rabon data saka wani abu a bakinta tun wani tukudi da Anti Nadiya ta takura mata tasha da safiyar ranar, bayan shi bata ci komi ba, kuma bata sha'awar cin komi.
Su Anti Jamila na falon suna hira lokacin data fito daga dakin, idanunnan nata sun kada sosai. Cike da mamaki suke bin ta da kallo, sam basu yi tunanin tana dakin ba, ko kadan ma hankalinsu bai kawo zata je wajen ba tunda ba a cika ta'ammali da dakin ba. Anti Jamila ta kalleta tace baki da lafiya ne Ameenah? Ta girgiza kanta a sanyaye amma bata ce komi ba, Anti Nadiya tace tun dazu Ammie da Faruq ke neman ki, Al-Ameen yayi ta kuka da bai ganki ba. Sai lokacin tayi magana cikin shakakkiyar murya kamar wadda mura ta kama, tace can zan je yanzu. Ta juya a sanyaye zata fita, Anti Jamila tace kin kuwa ci abinci Ameenah? Ta juyo tana kallonta fuskarta dauke da dan murmushi duk don ta kore damuwar data hango zane baro-baro akan fuskokinsu, tace manta da abimcin nan Anti, a koshe nake. Sai da safen ku.... Ta karasa fita da saurinta.
tun daga nesa ya hango ta tana tafe a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, ya saki wata irin doguwar ajiyar zuciya wacce bai ma san yayi ta ba. Tun komawarsu hotel din da yayi masauki shi da abokansa, gabadaya zuciyarshi ta rasa sukuni. Iya dauriya yayi amma abin ina, kasa daurewa yayi wai har sai gobe ne zai ganta, gani yake yi idan ya wayi garin gobe ba tare daya saka Ameenah a kwayar idanunsa ba, babu mamaki a tarar da gawarsa a daki. Ya rasa irin mayataccen son da yake yi mata, da dai abin bai kai haka ba amma tunda ya sake ganinta for the third time, ya sake rasa sukunin shi, daidai da sakan daya tunanin Ameenah yaki ya kyale shi, komi yake yi tare da tunaninta yake yin sa. Ba shiri ya dauki makullin mota ya taho gidan don Anti ta tabbatar masa cewa lallai Ameenah na cikin gidan.
Ba zato taji an ja hannunta anyi gefe da ita, baki ta kware da niyar kwala ihu taji ansa hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka ce "shhhh!!!" manyan idanunta da suka canza kala ta daga a hankali ta kalleshi, inda suke babu wadataccen haske. Duk da cewa bata ga fuskarshi ba, amma ta dauki muryar shi. Cikin sauri ta ture hannunshi daga bakinta ta fita fili wajen haske, ya biyo bayanta ya tsaya a gabanta suka fuskanci juna. Ya matsa daf da ita kamar wanda ke son shigewa jikinta, yace ina kika shiga tun dazu muke ta nemanki? Ta dan matsa baya kadan, cikin tamkewar fuska tace bana tunanin abu ne wanda ya shafe ka sanin inda naje din!. Ya daure fuska, "ban gane ba? Kin kuwa san irin kunyar da kika bani dazu? Nazo da tarin abokaina suna son ku gaisa amma aka neme ki aka rasa, kin san irin muzancin dana shiga lokacin?" tace Wannan ba damuwa ta bace Modibbo! Plss idan baka da wani abin cewa excuse mee... Kaina yana sara min. Ya bude manyan idanunshi akanta, hakan ya janyo mata jin wani irin kasala a jikinta. Yace me yasa ne baki da kunya ko kadan Ameenah? Me yasa sam baki san inda ya dace da wajen da bai dace kiyi rashin kunya ba??" baki ta murguda tace ina ga ai kai ka tari rashin kunyar, Kai ka shiga harkata da rayuwata don haka indai rashin kunya ne to yanzu kuwa ka fara gani!. Ya dage gira sama, "Allah da gaske? To Dan Allah sake yi mun rashin kunyar yanzu mana ki gani, zanyi maganinki anan take wallahi, don't try me Ameenah I don't tolerate sh**t da kike gani na nan!!". Kashedin ya shige ta sosai ya kuma fadar mata da gaba, amma hakan bai hanata bude baki cike da jarumtaka ba tace anyi maka rashin kunya din, kayi duk abinda zaka yi....!!" babban yatsan hannunshi na hagu ya hada da yatsan tsakiya ya sakar mata su a baki, ba shiri ta sanyawa bakinta kwado, tasa hannu ta dafe wajen Saboda tsananin zugin da yake mata. Kan kace meye wannan? Hawaye sun fara zarya akan kumatunta kamar an bude famfo, dariya ce ta kusa kamoshi, lallai yarinyar nan a shagwabe take. Murya irin ta wanda ke son fashewa da kuka tace "Allah ya isa na mugu! Kuma ma auren an fasa tunda kai mugu ne!!".
Ya saki murmushi sosai yace "very good! Da kin kyauta min sosai kuwa, kuma Ke zaki yiwa kanki babun badinahu. Kin dai san ko yanzu kika fasa aure na to a goben ko mata hudu nace zan aura ba zan rasa ba, saboda ni saurayi ne sabon jini, fresh guy babe! Sabanin second hand. Ke kanki kinsan bacin kaddara babu abinda zai yi hadin saurayi da Bazawara!!". Sai ta damke bakinta da hannu ta falfala cikin gida da gudu don kuwa ta tabbata idan ta bude bakin to kuka zata fashe dashi, abinda kuma bata so kenan; ya gano weak point dinta.
Shi kam binta yayi da kallo har ta shige cikin gidan, ya shafa sumar kanshi yana murmushi cike da nishadi marar misaltuwa, yace "yarinya ki gama duk kewaye-kewayen ki da rashin kunyar ki, gobe war haka nasan tuni na kashe bakin tsanyar" ya fada motarshi ya fita daga gidan a nishadance.
Sai data tsaya a bakin kofar falonsu ta share fuskarta sannan ta shiga ciki, ba kowa a falon don haka ta shiga dakin Ammie. Tare ta same ta da wasu daga cikin en uwansu da suka zo bikin, ta gaishe su suna ta tsokanarta. Alfarmar ta musu yaken murmushin data saba ma yau basu samu Ba. Ammie ta dinga bin ta da kallo har ta iso wajenta, tace Auta nah kin kuwa ci abinci? Karya ta mata tace Ehh. Ta gyada kai tace to Maza kije ji kwanta dare yayi, da ganin ki kuma kina bukatar hutu. Sai da safe ta musu ta juya ta tafi dakinta, akan gado ta samu Al-Ameen a kwance yana barci, tayi murmushi ta shafa sumar kanshi tare da sumbatar goshin sa. A hankali ta haura kan gadon ta kwanta tare da rungumoshi zuwa jikinta, fatan ta daya Allah yasa kada Ammie ta hanata tafiya da Al-Ameen idan zasu tafi Kano gobe, ta lumshe idanunta har barci ya dauketa.
*_Washegari...._*
Qarfe goma sha daya na safe aka daura auren Amaren hudu, da yake gabadaya aka hada auren aka daura har na Safeenah saboda Alhaji Abbas yace kada a wahalar da mutane kawai a daura anan, Ana daura auren maza suka zarce da reception a Vomella Hotel, yayin da aka dauko Amarya Safeenah daga Kano aka taho Gombe da ita saboda ta samu ta halarci dina da za ayi da dare.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:06 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�51鈥⒙梆煇�
Tunda taji an daura aure jikinta yayi wani irin sanyi marar misaltuwa, gado ta haye saboda zafi da jikinta ya dauka ta dukunkune a cikin bargo tana rawar sanyi. Anti Jameela ta shigo dakin ta same ta a halin da take ciki, tayi salati tana tafa hannu ta nufeta da sauri, ta tsorata da halin data ganta. Tace Ameenah kan ki kike so ki kashe ne?? Ta fita da sauri sai gata ta dawo da kwano da magani, ta taimakawa Ameenah ta tashi zaune, da kanta ta dinga bata abincin tana lallashinta cikin tausasa murya. Ya Faruq ya shigo dakin sanye da bugaggiyar bakar shadda, ta daga ido a hankali tana kallon Yayan. Wani irin haske da annuri ne kawai ke fita a fuskarshi, lallai shekin angonci daban yake. Ya zauna a gefen gadon ya dan dafa goshin Ameenah yana tambayar Anti ya jikin nata? Tace mishi zazzabin ya dan sauka yanzu. Ya amshi magani a hannun Anti ya durawa Ameenah a baki Anti tabi da ruwa, suka shiga bata kalamai masu taushi sai gata tana murmushi. Shi da Anti suka yi dariya a lokaci guda, Faruq yace toh ko ke pha Auta?? Maza tashi ki wa baby wanka a shirya min shi, mu je mu taro amarya ta dashi tana kan hanya. Ameenah tayi dariya ta sungumi Al-Ameen dake barci a gefenta ta shige toilet, su Anti suka fita suka ja mata kofar dakin.
Ta wanke Al-Ameen tas wanda sanyin ruwa ya farkar dashi ya bude ido tangararas yana kallonta yana mata wasanni wadanda suka saba idan tana mishi wanka. Ta biye mishi itama, baka jin komi a lokacin sai sautin dariyar su. Ta nade shi cikin towel suka fito, daidai lokacin Anti Hadiza yayarta ta fado dakin, tace yauwa Anti ga dana ki shirya min shi, bari inyi wanka" ta koma bandakin Anti kuma ta dauki Al-Ameen ta fara shirya shi.
Lokacin data fito har Anti ta gama shirya shi cikin tattausar farar shadda irin ta jikin Faruq, sai tashin kamshi yake. Ameenah ta rungume yaron tana jin kaunar shi sosai a jikinta. Ta dago shi daga jikinta tace kayi kyau yaro na! Yayi dariyar shi mai kyau dimples dinshi suka lotsa sosai, yace Ke ma mommy. Dariya tayi ta nutsa yatsar ta a kumatun shi inda ya lotsa tace Love yah baby. Gaban mirror ta koma ta shafa mai, ta zira rigar sallah a jikinta ta sallaci azuhur. Sannan ta dawo gaban mirror ta zauna ta fara shafe-shafen hoda, duk da ba wata kwalliyar azo a gani tayi ba amma kyawunta ya fito sosai. Tana cikin zira gown din atamfa da Anti Hadiza ta fitar mata na ankon su, Antin ta sake shigowa da plate a hannunta, tace baby Al-Ameen Faruq yana jiranka a falo. Ya fita da gudunsa yana wa Ameenah bye.
Ta mikawa Ameenah plate din tace "amshi ki cinye yazo Auta" ta kalli plate din farfesun kaza ne yana ta kamshin daddawa da tafarnuwa mai dadi, ta cuno baki kamar zata yi kuka tace "wai farfesun ne again?? Ni pha na gaji da cin abubuwan nan!" Anti Hadiza tace ba zaki gane irin gatan da muke kokarin yi miki bane yanzun har sai kinje gidanki Auta, wannan shine martabar ko wace 'ya mace. In dai kina son kiyi gashi a idon wannan mijin naki to ina tabbatar miki wadannan sune manyan makamai daya kamata ki yake shi dasu musamman da ba a budurwa zai aure ki ba" tace to wai ni dama nace miki ina son yaso ni ne? Anti tayi murmushi tace baki ce ba, yi hakuri kici wannan ne na karshe kinji? Tana kumbure-kumbure da gunaguni haka ta amsa ta cinye kazar ta shanye romon. Anti ta dauki kayan kwalliya ta kara gyara mata kwalliyar ta, ta dauki dankwalin atamfar ta mata wani irin nadi a kai sai ta fito kamar wata African queen. Anti Hadiza tayi murmushi tace Masha Allah!! Kin yi kyau sosai kanwata. Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, Ameenah mutum ce mai tsananin son compliment. Anti tace yauwa, just continue smiling like this for the whole day, promise?? Ameenah ta gyada kanta da sauran murmushi a fuskarta. Anti tace good! Muje ku gaisa da baki. Ba musu ta bi bayan Antin. Falon nasu a cike yake da mutane, tana fitowa sai kowa yayi caaa a kanta, masu guda nayi, masu tsokana nayi, da kyar ta samu ta fita daga sashen ta tafi na Ya Almu inda a can sauran amaren da kawayensu suke. Tana shiga hasken flashes na camera ya dallare mata ido, tayi saurin saka hannu tana karewa. Muhibba daya daga cikin cousins dinsu ta riko hannunta suka shiga daukar hotuna kamar ba gobe, suna yi suna shakiyancin su kamar dai yadda kawayen amarya suka saba yi, Ameenah sai dai tayi murmushi kawai idan suka tabo ta.
Sai karfe hudu na yamma amaryah Safeenah da tawagarta suka iso, Ya Faruq ya kamo hannun matarshi dake lullube cikin lafaya ya jata har sashen ta inda zata zauna, bai kuma saki hannun ba sai daya kaita har kan gadonta ya zaunar da ita, mutane suka bi bayansu masu shewa nayi masu daukar hoto nayi. Abokan wasa suka mishi caaa akai dole ya bar gidan. Nan sashen amaren suka koma aka cigaba da gashi.
Da misalin karfe takwas na daren ranar, amaren na zazzaune a gaban mirror sanye da dinner gown, masu kwalliya na tsaye a kansu kowacce na gwada basirar da Allah yayi mata ta wannan fannin. Kada ku so ku ga amaren a wannan lokacin, yadda kasan a sace su a gudu saboda tsananin kyawun da suka yi kamar wasu masu modeling. Doguwar riga ce har kasa a jikinsu ta wani silk yadi, sai dai kowannensu kalar shi ta banbanta, wani net aka yi amfani dashi aka yi tattara a bayan rigar inda sauran ya zuba har yana jan kasa. Da yake dukansu suna da gashi Masha Allah, sai suka kitsa gashin jela daya bayan sun bar wani style a gaban goshin su, suka nade jelar gashin ya bada wani style na daban kamar nadin fure, suka yi amfani da pin suka nade karshen, sai suka dauki siririn gyalen kayan suka dan zizaro shi daga sama sauran gyalen ya sauka a gadon bayansu. Kamshi suke fitarwa mai sansanyan kamshi. Kafin a gama shirya su tuni Abokan anguna sun kwashe kawayen amarya, saura angunan kawai da amaren.
Kowacce wadda ta shiryata ta kama hannunta suka fita, motoci ne bakake har guda hudu anyi parking dinsu a kofar falon, angunan na tsaye cikin shiga ta yadi mai taushi wadda ta hau da kayan dake jikin amaren. Kowane Ango ya tafi ya taro amaryar shi cike da tattali ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, amma shi Modibbo tsayawa yayi cak kawai ya kurawa amaryar tashi ido cike da maita. Ji yake kamar ya hadiyeta ko ya samu ya huta da wannan azababben son da yake mata, kanta a kasa haka suke tafiya amma tana jin idanuwansa akanta, don haka koda wasa bata yi kuskuren daga idanuwanta ba, sai da suka isa daf dashi kafin ya samu kuzarin dauke idonshi daga kallonta, yayi azamar sa hannu ya bude murfin motar na baya, matar ta taimaka mata ta shiga, ya maida murfin ya rufe. Daya gefen ya zagaya ya shiga ya zauna a gefenta, direba yaja motar a hankali suka bar farfajiyar gidan.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:06 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�52鈥⒙梆煇�
A cikin motar babu wanda yace da dan uwansa ci kanka, ita gefe guda ta juyar da kanta tana kallon hanya tana tunano wani lokaci da aka mata kwalliya cikin saree zata je dinar auren su ita da Marwan, irin tattalin daya dinga mata da kulawarshi a gareta, farincikin daya shiga a wancan lokacin...., sai zuciyarta tayi saurin ce mata kul! Yanzun ke matar aure ce, matar wani... Tayi saurin lumshe idanunta tana jan a'uziyyah tana istigfar. Yayin da Modibbo ya jingina bayanshi da seats din motar ya dafe kanshi, a zahiri idan ka ganshi zaka yi tunanin stress da gajiya ne suka tarar mai, though yes akwai gajiya wadda kusancinshi da Ameenah ya saukar mishi yanzun nan. A kaikaice kuma hanci ya ware yana shakar daddada kuma tattausan kamshin da Ameenahr keyi wanda yake jin kamar duk shaka daya da zai yi yana kara mishi tsabar son ta da sha'awar kasancewa da ita, hakan ya saukar mishi da wata irin kasala marar misali. Jikinshi lakwas haka suka isa Vomella Hotel inda za ayi dinar. Wajen ya kawatu sosai, haske tarr yadda kasan rana ce ba dare ba, mutane dankam suka tarar a bakin shiga wajen suna jiran isowarsu. Da isar su kuwa en jaridu da masu hotuna suka taro su da ruwan flashes har kan mazauninsu sannan kowa ya nemi waje ya zauna, babu bata lokaci aka fara gudanar da events na dinar. Muhseen babban abokin ango Modibbo shi ya bada tarihin ango na karshe (Modibbo), bayan ya gama bada tarihin ya kara da cewa shi bai taba ganin taro ko biki wanda ya kayatar dashi irin wannan ba, ya kuma ce bai taba ganin ango da amarya da suka dace da junansu irin wadannan ba. Ya kara da cewa akwai yiwuwar shima zai zagayo ya lallabo cikin Wakili's Family ya nemi wadda zai yi plan B da ita don ya kula duk kyawawan 'yanmata ne masu cike da zati a cikin familyn. Duk sai aka kwashe da dariya a wajen sosai, yayin da enmatan wajen suka ji kansu ya fashe sosai. Sai wajen karfe goma sha biyu aka tashi, daga nan aka wuce da amare Rukky da Maimunah gidajensu don dama tuni sun yi sallama da iyayen su, suka rungume Ameenah su ukun suna kukan rabuwa da kyar aka samu aka janye su.
Wannan karon ma Modibbo ne ya bude mata motar ta shiga, direba yaja motar suka tafi. Har suka bar wajen idanunta basu daina zubar da hawaye ba, akai-akai ta kam sa yatsa ta dauke hawayen. Ido ya zuba mata jikinshi a sanyaye, zuciyarshi na tsikarin shi wai ya rungumota ya lallashe ta, amma sam yaki ba kanshi damar yin hakan. Baya so yarinyar ta samu damar raina shi tun yanzu, yanzun ma har suka isa gida bata kalli inda yake ba, direba yana gama gyara fakin ya musu sallama ya fita daga cikin motar.
Cike da wata irin takama ya bude motar ya zagaya ya bude gefen da take, ta zuro kafarta ta fito a hankali, ya maida murfin ya rufe. Yaki matsawa ya bata hanya ta wuce, taku biyu ya kara ya isa dab da ita har suna jin numfashin juna don itama Ameenah ba baya bace wajen tsawo, ta dan ja baya a hankali, ya kara matsawa shima, haka suka yi tayi har sai daya dangana ta jikin motar. Ya kai bakinshi saitin kunnenta kamar mai rada yace "so, ina kike shirin tafiya ba ko sai da safe? Me yasa ba kya respecting dina ne Ameenah?? Dazu fa ko gaishe ni baki yi ba.... Kin kyauta kenan??" dan karamin bakinta ta tabe tace zancen kyautawa da rashin kyautawa bana zaton akwai shi a tsakaninmu... Gaisuwa kuma ban ga dalilin da zai sa na gaishe da kai bane. Yayi kasa da muryarshi yace ko albarkacin ina mijinki ba zan ci ba kenan?
Ta daga idanunta tana kallon tsakiyar idanunshi tana murmushin da yafi dangana shi dana takaici, tace da ka ambaci kalmar miji sai naji ka bani dariya, ko ka manta cewa kai da bakinka Ka fada min cewa aurena kawai zaka yi don ya zamar maka dole ba don kana sona ko kuma kana maraba da auren ba? Ina ganin kamar idan ka kira ni matar ka baka yiwa kanka adalci ba don ban cancanci na zama matar ka ba.... Shima murmushin ya saki sosai cikin kara kaurara idanunsa cikin nata, kallo mai ma'anoni da dama, sai ta rusunar da nata kwayar idanun don ba zata iya jure kallon kwayar idanunsa ba yanzun. Yace to yanzu ya za ayi kenan? Gashi kuma ina so ki zama matar tawa! Ta dago ido da sauri ta kalli fuskarshi, kafin ta kawar da nata fuskar zuwa kallon wani sashen daban tace babu abinda za ayi, saboda ni bana so ka zama mijina... U're lacking so many things as a husband! Yace like what??... Tayi shiru bata amsa ba. Hannu ya saka ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, cikin zafin nama ta buge hannun nashi tace "don't u dare touch me again Modibbo! Plss don't!!" ya kalleta da mamaki yace bana tunanin na aikata wani sabo don na taba fuskar matata! Cikin daga murya tace "sau nawa kake so na fada maka cewa yadda maka dauke ni a mata ba nima ban dauke ka a matsayin miji ba? Stop putting all dat shows and get lost!! Nasan you r just pretending, but baka sona kuma baka so ka aure ni ba!!" ya gyada kanshi, you r ryt! Bana sonki, sai dai abinda ya faru ya riga daya faru, aure dai an riga an daura bamu da yadda zamu yi haka ne? Don haka na yanke shawarar zama dake a matsayin mata duk da cewa bana sonki!" ta ja tsaki, "matsalar kace ka soni ko kada ka soni bai dameni ba ka gane? Abinda kawai na sani shine ni dai ba zan so ka ba! I've already given my heart to someone who deserves it!..."
Idanunshi cike da bacin rai yake kallonta, "me kike nufi kenan?" ta murguda baki, "abinda kaji shi nake nufi!!". Hannu yasa ya shafo tattausar sumar kanshi tun daga goshi har keya, bata ankare ba sai jin saukar lebensa tayi akan nata.....
Ta zaro ido cikin tsabar shock din da hakan ya haifar mata, jikinta yayi wani irin sanyi lakwas ta rasa duk kuzarin ta. Gare shi kam jin sa yayi kamar wanda yake ziyartar duniyar Neptune saboda wani irin feeling mai dadi da yaji yana ratsa shi har tsakiyar kansa, feeling wanda bai taba experiencing irinsa a duniyar sa ba. Tsananin taushin lebunanta da wani kamshi mai sanyi da suke fitarwa, ya taimaka kwarai wajen fitar da AbdulRasheed-Modibbo a hayyacinsa, wani irin hadamammen kiss ya dinga mata mai zurfi, gabadaya ta rasa kuzarin ture shi daga gareta. Shi da kansa yayi tunanin nan ba muhallinsa bane, a hankali ya fara janye bakinsa daga nata amma bai janye daga jikinta ba. Ya bude idanunsa dake lumshe ya sauke su a kanta, idanunta a bude suke rass cikin shock din da bata fita daga cikinsa ba. Sai lokacin wani karfi yazo mata, tasa duka hannuwanta biyu ta tura shi baya da karfinta. Yayi taga-taga kamar zai fadi don sam babu kuzari a tattare dashi, Allah ya takaita ya tsaya cak.
Ya nunata da yatsa yana magana a wahalce don har zuwa lokacin numfashinsa bai daidaita ba, yace "next time, try and mention anoda man in front of me again, ko kuma ki murguda min baki, I promise you that ba tsotsar bakin zanyi ba, cinye shi zanyi duka in ga karyar rashin kunya!!".
Ta daga baki kamar mai son tace wani abu amma maganar taki fita, sai ta hutar da kanta ta juya ta bar wajen cikin sassarfa. Ya bi bayanta da kallo idanunsa na lumshewa, ji yake kamar ya kara kamota ya cigaba da kissing lebunanta don bai gaji da tsotsar su ba. Ya jima sosai a wajen kafin ya shiga mota ya tafi masaukinsa.
Lokacin daya isa karfe dayan dare ta wuce, abokansa dake tare dashi har sun yi barci. Wanka ya fara yi yayi shirin barci ya kwanta, amma barci yace bai san idanunsa ba. Yayi-yayi abin ya gagara, juyi kawai yake a gadon, Ameenah kadai yake bukata a lokacin, ita kadai. Sai dai baya tunanin ko an kaita gidanshi zai iya yin wata mu'amalar aure da ita, zai jure ko wace wahala ce ya kauda kai daga gareta har sai ya tabbatar daya saka mata zazzafan son shi a zuciyarta.
Ta bangaren Ameenah ma bata samu barci ba, da taga tunanika sun addabeta sai ta daura alwala ta kalli alkiblah. Tana kan sallaya tana karatun Al-Qur'ani mai girma aka kira sallah, ta mike tayi raka'atanil fijr ta sallaci asubahi. Sai lokacin taji wani irin mayen barci ya mamaye mata idanu, tana gama sallar ko abin sallar bata dauke ba ta koma kan gado ta kwanta, ta janyo Al-Ameen ta rungume tsam a jikinta kamar wadda take tsoron a kwace mata shi, a haka barci ya dauketa.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:07 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�53鈥⒙梆煇�
Karfe goma daidai na safiyar ranar Ameenah na gaban motar da zasu tafi Kano, cikin rakiyar duka yayyenta da wasu da yawa daga cikin jama'ar gidan, tuni en rakiyarta zuwa Kano sun nabba'a a cikin mota har da Anti Fati wadda a daren ranar zata bi jirgi ta koma Ghana. Sauran yayyenta mata duk a ranar zasu koma gidajensu. Ameenah kuka take yi sosai kamar wadda za a kaita kabari ba gidan aure ba, Ammie na kara yi mata nasiha akan wadda Kawun nan ta suka yi mata. Ya Faruq da kanshi ya bude murfin motar ya saka ta ciki, ya leka kanshi ta cikin murfin motar yace a sanyaye Auta menene abun kuka kuma? Kar ki jawo wa kanki ciwon kai fa... Ta daga baki cikin kuka tace Yaya, Al-Ameen.... Yace kada ki damu, zamu kula dashi in shaa Allah, kina yin wata guda acan zan kawo miki shi da kaina I promise you. Oyaa maza ki goge hawayenki, it's hurting me. Tayi murmushi tana goge hawayen, amma tana share su wasu suna kara gangarowa. Daidai lokacin angon nata ya bude bayan motar ya shigo, Safeenah ta leko ta tagar motar tana musu fatan a sauka lafiya. Muhseen abokin shi ya shigo ya tashi motar, daukacin jama'ar wajen suka daga musu hannuwa suna musu fatan a sauka lafiya. Ameenah ta kara bin farfajiyar gidan su da kallo idanuwnta cike da kwalla, karo na biyu kenan data bar gidansu zuwa gidan aurenta, wancan karon tana so kuma tana muradi da dokin kasancewa da wancan mijin, yayin da wannan karon kwatakwata bata son kasancewa da wannan mijin, bata kuma kaunarsa. Zuciyarta kuma na cike da tsoron kalar zaman da zasu yi da Modibbo, a yadda take ganin take-taken sa namijin duniya ne na gaske, tasan ba zai bata damar suyi zaman doya da manja irin yadda take so suyi ba. Tafi-tafiya ta daina kukan da take yi sai dai lokaci zuwa lokaci tana share hawaye dake zarya a kumatun ta. Modibbo kanshi na ga wayar hannunsa yana latsawa amma hankalinsa kacokam yana gareta, wani irin kuna zuciyarsa keyi saboda kukan da take yi babu sassauci, zuciyarsa na gaya mishi saboda bata son shi ne take yin wannan uban kukan. Anya a duniya akwai abinda yafi son maso wani kuna da kuma ciwo kuwa? Sai yaji kamar shima ya fashe da kukan, ya daure zuciyarshi ya cigaba da latsa wayar shi cikin kunan rai, idanunshi suka kada jawur. Muhseen ya lura kamar couple din basu cikin annashuwa irin ta sabbin ma'aurata, he was curious. Sai dai kasancewar sa wayayyen mutum wanda bai cika son shiga cikin harkar da babu ruwansa ba, sai ya juya ga Amaryar ya fara tsokanarta, wae ko bata son zuwa Kanon ne su juya ya maida ta Gombe yanzun nan? Tun dai tana mishi dan yake har ta ware tana tikar dariyar tsokanar Muhseen, yana da barkwanci sosai. Zuciyar Modibbo ta fara rage zugin da take ganin yadda Ameenah ta saki jiki sosai suna hirar kasar India ita da Muhseen da yake dukansu a can suka yi karatu shi da Modibbo. Bai saka musu baki cikin hirar tasu ba, ya kan dan murmusa dai kawai idan Muhseen ya tabo shi. A hankali ta fara jero hamma, barci sosai ya cika mata idanu ta dan kwantar da kanta akan Kujera barci yana fizgarta kadan-kadan, cikin dan kankanin lokaci ya kwasheta.
Ya dan saci kallon inda take, ta dan takure alamun iskar dake shigowa ta cikin tagar motar yayi mata waya, yanayin yadda kwanciyar da tayi ma kanta ba comfortable bace ba mamaki ta tashi da ciwon wuya. Sai ya mika hannu cikin tsanaki ya jawo ta ya saka cikin jikinsa, ya maida gilasan motar ya rufe, ganin haka sai Muhseen ya kunna musu AC yana dan murmushi.
Tsabar farincikin da Modibbo ya shiga a wannan lokacin baya misaltuwa, yau Ameenahr shi ce kwance a cikin jikinsa me ya kai wannan farin ciki da alfahari a garesa? Lallen hannunta yake kallo, ya fito sosai a farar fatar hannunta kamar a lokacin aka zana shi babu alamun disashewa, ya kamo duka hannuwan nata ya kai bakinsa ya sumbata cike da wani irin shauki. Muhseen yayi gyaran murya, harara ya jefa mishi, "Malam bi a hankali kada ka tasar min mata daga barci da wannan katuwar muryar taka" yayi er dariyar tsokana yace ahh, ni kawai ina tuna maka cewa ba ku kadai ne a motar ba don naga kana kokarin wuce gona da iri. Ya maida kallonshi gareta data dan motsa, yace ai ni ba dan iska bane irinka!! Muhseen ya kyalkyale da dariya yana dukan sitiyari yace banza je ka dai, na kyale ka ne kawai saboda kai farin shiga ne a harkar, so zan yi maka uzuri..." Modibbo ya gyada kai kawai yana dan murmushi ba tare daya tanka shi ba, tun asali shi mutum ne mara son magana sosai, shima Muhseen din yana cin darajar shakuwar su ne, abokansa ne tun yarinta. Ga Muhseen da dan banzan surutu da son tsokana, amma a haka ake abotar. Sanin hali sai shima Muhseen din yayi shiru ya maida hankalinsa ga tuki yana bin sautin wakar dake tashi a hankali daga cikin radion motar.
*KANO TA DABO.....*
Karfe daya na rana a cikin kwaryar garin Kano ta musu, Ameenah na dukunkune a jikin Modibbo tana barcinta cike da natsuwa har zuwa lokacin. Kai tsaye Lamido Crescent gidan amaryar suka wuce, hadadden gida ne hawa daya mallakin Modibbo. A wani zamani da aka tura shi Pondicherry yin wani course, ya ci karo da irin gidan a can, gidan yayi matukar birgeshi. Ya ga dacewar ya gina shi a matsayin gidan da zai rayu da masoyiyar shi a ciki, don haka ya dauko zanen gidan gabadayansa ya kawo aka fara gina mishi, lokacin da aka gama ginin ya ma cire rai da samun ta a rayuwarshi kwatakwata, don haka ya rufe gidan da kudirin ko da ace zai yi wani auren sai dai ya nemi wani gidan su zauna da matar amma ba dai wannan ba. To da yake shi mutum baya taba rasa abinda yake rabon sa ne sai gashi wadda aka gina gidan domin ta da kuma sunan ta ne zata shiga gidan, Allah Kenan!!
Tsayuwar da motar tayi a cikin gidan ne ya farkar da Ameenah daga barcinta. Tayi shiru tana so ta tantance a inda take kwance, ta dago a hankali ta kalleshi ba tare data janye daga jikinshi ba. Idanunshi fes a kanta ya ja fuska kamar bashi ba, kunya da takaici suka dirar mata sosai, kenan tunda ta fara barci a jikinsa take duk wannan tsawon lokacin? A hankali ta janye jikinta daga nashi ta gyara zaman gyalenta ta bude murfin motar ta fita, ya bita da kallo amma bai yi yunkurin fita ba. Muhseen dake kokarin fita ya dubeshi yace malam a cikin motar zan barka koh? Ya doka mishi harara yace idan kai kafiri ne toh ni musulmi ne, masallaci zan wuce. Ya dan dafe bakinshi yace awwwh! Na manta ashe anyi azuhur. Cikin motar ya koma ya tasheta yabi ayarin sauran abokansu da suke fita daga gidan bayan sun sauke en rakiya.
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:07 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�54鈥⒙梆煇�
Wasu cousins din Modibbo su biyu suka fito daga can wata siririyar hanya suka tari amaryar da en rakiyarta, suka musu jagora har cikin gidan. Ameenah ta saka kafarta ta dama a falon bakinta na dauke da bismillah da addu'ar da Ammie tace ta dinga yi. Babban falo ne wanda ya sha saitin wasu genuine Italian leather seats manya, kofofi biyu ne kacal a falon kasa sai babban dinning table orange color da kujerunsa. Falon babu wani tarkace, daga katuwar plasma, sai wani katon flower vase baki da aka dora bisa dan karamin center table din dake tsakiyar falon. Gabadaya falon lullube yake da wasu mahaukatan marbles masu sheki sama da kasa, komi na falon a bisa tsari yake irin dai na cikakkun en boko da suka san ma'anar bokon. Fuskar amarya na lullube a cikin gyalenta babu abinda ta gani a falon ta dai ji suna ta zuzuta tsaruwar falon. Suka taka steps din bene suka hau sama, dan karamin falo ne a saman da dakuna guda shida reras. 'Yanmatan nan suka kai baki inda aka tanadar musu don su huta su kuma ci abinci, Anti Fati da amarya suka shiga dakin amaryar. Suna shiga ciki kafafunsu suka nutse cikin wani tattausan carpet bugun hannu, dakin babba ne sosai. Daga can gefen kudu na dakin katon gado ne wanda ke barazanar lashe mutane biyar ba tare da sun matsi juna ba, kafin ka kai ga gadon sai ka taka matakalar hudu, an lailaye gadon da wani lallausan bedsheet beig color, gadon rufe yake ruf da wani shara-sharan material mai kama da net shima beig. Sai toilet, dressing mirror, da wardrobe. Komi na dakin beig ne yana ta fitar da kamshi mai dadi.
Anti ta umarci Ameenah data shiga toilet ta dauro alwala, sai lokacin ta yaye rufar da tayi tana karewa dakin kallo a nutse. Zuciyarta ta karye sosai, wace irin kauna su Uncle suke yi mata a duniyar nan? Duk wata kauna da da yake bukatar samu daga wajen iyaye to ta samu fiye da irinta a wajensu. Da kyar ta iya daga kafa ta shiga toilet din, nan ma wani sabon babin kallo ne ta bude baki a hangame. Duk shige-shigen ta da yawace-yawacenta bata taba ganin toilet daya tsaru irin wannan ba, fadar abubuwan cikinsa ma bata baki ne kawai dai tasan ya hadu sosai. Alwala tayi ta fito, har Anti ta shimfida mata abin sallah. Ta tada kabbarar sallah ta fara da nafilah kafin ta sallaci azuhur. Kafin ta gama aka shigo musu da abinci mai rai da lafiya, Ameenah dai bata samu ta ci ba, gabadaya a koshe take jinta. Da kyar Anti ta samo kanta ta dan tsakuri abincin. Da suka gama suka fita har amarya din suka zagaya gidan, ashe basu ga komi ba dazu, yanzu ne suke ganin asalin gidan; kicin dinta kawai da kayan dake cikin kicin din sun isa su sa mutum ya sare da lamarin mutanen nan. Sai da suka zagaya ko ina na gidan har da su lambu a bayan gidan da wajen hutawa, gida dai yayi dari bisa dari sai fatan Allah ya ba maxauna gidan zaman lafiya mai dorewa, addu'ar da suka dinga yi musu kenan.
Anti Fati ta ja Ameenah suka kule a daki ta dinga mata nasiha tana kara nusar da ita game da falalar dake cikin aure da amfanin aurenta a garesu, tace "ki duba irin gatan da Mukhtar ya miki Ameenah, kina zaton akwai abinda zaki yi a duniya ki rama irin halaccin da yayi miki?" Ta girgiza kai, Antin tace "to wannan dama ce kika samu ta rama halaccinsa a gare ki, don Allah Ameenah kada ki rama alkhairi da sharri. Nasan duk wahala jinin Uncle Mukhtar yafi karfin kallon banza daga gareki, kada ki manta Abdul-Rasheed dan gidan yayar Mukhtar ne uwa daya uba daya, ko don darajar Uncle don Allah ki zauna lafiya dashi ko da ba kya son shi, kada ki saba umarnin shi, kada ki guje shi a shimfida don Allah da mala'ikun sa na fushi da masu aikata haka, ki daure ki ba mara da kunya kinji Auta?? Yadda na sanki a yarinya mai biyayya da jin maganar na gaba da ita don Allah kar ki sauya daga haka, Yanzu Abdul-Rasheed shi zai zama komi naki, sai kinyi masa biyayya ne zaki shiga aljannah kin fahimce ni?" ta girgiza mata kai tana hawaye. Anti ta fara janta da hira data taimaka wajen sanyaya mata rai har zuwa lokacin da direban da zai kaita airport ya iso, Ameenah ta rike Antin tana kuka riris har tana hadawa da ihu, da kyar ta saki Antin ta fita itama tana matse kwallar kewar Autar tasu.
Ana kiran magriba wata motar tazo ta kwashe en rakiyarta zuwa gidan Ummie, umarnin Ummien ne wai saboda kada su takurawa amarya da angon, gobe tun da safe zasu juya Gombe kenan ba lallai su sake haduwa da amaryar ba a goben, don haka suka mata bankwana suka tafi bakinsu dauke da addu'ar fatan sake saduwa da junansu cikin Alkhairin Allah, aka bar Amarya-Ameenah cikin tangamemen gidan AbdulRasheed-Modibbo ita kadai kwal kamar mayya. Har ta sallaci ishai da misalin karfe takwas na dare amma bata ji duriyar angon ba. Sai ta koma can karshen gado ta takure kanta a jikin bango, tana cike da kewar Ammie da Al-Ameen, amma tsoron kasancewarta ita kadai a cikin gidan ya danne kaso tamanin na kewar dake cin ranta, a tsorace take sosai.
Sai wajen karfe tara taji alamun bude gate, mota ta shigo an rufe, bata motsa daga inda take zaune ba amma jikinta ya bata kila ko Modibbo ne da abokansa. Ba a dauki wasu lokuta masu tsawo ba taji an turo kofar dakinta an shigo. Har zuwa lokacin kayan dazu ne a jikinsa wato babbar riga da er ciki kalar teku, kowa dai yasan yadda kalar sea ocean ke fitar da kyawun baki, ga bakin nashi ya hadu da shekin angonci don haka yayi kyau sosai ba kadan ba. Fuskarsa dauke da wata irin fara'ah ya shiga dakin yana mai zabga mata kirari, "amaryah... Amaryah ta buda sha kallo.... Amarya ba kya laifi sai kin kashe dan masu gida!!!" tayi gaggawar kawar da kanta can gefe guda zuciyarta na tambayarta dalilin daya hana ta kulle kofarta tun dazu cike da da-na-sani.
Ya ajiye ledar daya shigo da ita bisa dan karamin teburi dake tsakiyar dakin, ya janyo resting chair kusa da teburin ya zauna akai tare da mike kafa daya akan daya ya kalleta, "taso ki ci kazar amarcin kafin ta huce, kin san da zafi tafi dadi" ba ta tashi ba, hasalima kwanciya tayi ta juya mishi baya. Hular kanshi ya cire ya ajiye akan kujerar ya tashi ya nufeta cikin wani irin taku na cikakkun maza!.... Kafin ya isa inda take ya zare babbar rigarsa ya saura er ciki kawai, ya dora rigar akan gadon. Hannu yasa ya juyo ta suna fuskantar juna, yace ba dai jan aji ne zaki yi ba? Ina jan aji bai kamace ki ba tunda wannan ba shine karon ki na farko ba, ni nine farin shiga, in kika ja min aji ba ki min adalci ba. Da kyar ta bude baki tace sanin cewa kai farin shiga ne ya sanya naki jerawa da kai don kwatanta adalci, Farin shiga ai sai farin shiga ba tsohon hannu ba. Ya fadada murmushin dake fuskarsa sosai yace yeah! U're ryt! Buh kada ki damu, farin shigar ma na nan zuwa, but for now zanyi maneji da tsohon hannun.... Ya juya zai tafi, "....ki taso ki ci abinci fa ina fada miki" komawa tayi ta sake kwanciya, sai daya kai tsakiyar dakin ya juyo ya ganta a kwance. Komawa ya sake yi ya tsaya a gefen gadon, "Ameenah ki tashi ki ci abinci ko in ciccibe ki Allah-Wallahi...." Kara lafewa ma tayi akan gadon, yayi kwafa yana balle links din hannun rigar shi ya nannade hannun, ba tare da zaton ta ko tsammani ba taji an daga ta sama cimak kamar wata er tsako......!
漏Jeedderh馃惥
[5/2, 11:07 PM] 鈥�+234 816 492 9724鈥�: 馃挄馃惥鈥⒙扳€⒙� *BAYAN*鈥⒙扳€⒙梆煇攫煉�
馃挄馃惥掳鈥⒙扳€� *RAI...*掳鈥⒙扳€煇攫煉�
馃惥掳鈥�55鈥⒙梆煇�
Duk zille-zillenta ko a jikin Modibbo, sai daya kaita har kan kujera ya zaunar shima ya zauna a gefenta. Ba tare daya nuna ya damu da irin kallon takaici mai cike da tsana da take jifansa dashi ba ya janyo ledar daya ajiye yana kokarin juye abinda ya shigo dashi a cikin plate, duk da cewa a can kasan zuciyar shi kallon yana mintsinin ranshi. Gashin peacock ya juye a cikin plate din tangaran, yaji albasa da tumatiri da dan attaruhu gashi ya danyi ruwa har tiriri yake yi alamun ba a jima da sauke shi daga kan wuta Ba. Yayi amfani da fork da wuka ya yanko naman ya nufi bakinta dashi, tayi saurin janyewa. Ya kura mata ido cike da tuhuma yace me nufinki kenan? Kai tsaye tace ba zan ci ba! Yace wasa kike yi koh? Me kika ci ne? Ya fada yana kokarin taba cikinta, ta ja baya da sauri tana watsa mishi harara. A fusace tace idan ma ban ci abincin ba ina ruwanka, cikin ka ko nawa? Yayi kasa da murya cikin sigar lallashi wanda bai ma san ya aka yi yayi hakan ba, abinda ya sani kawai shine yana so ta saka wani abu a cikinta don ya tabbata babu wani abin kirki data ci, hakan kuma ya dame shi zai yi komi kuma don ganin ta ci abincin ciki har da lallashinta. Yace da ruwana Ameenah, saboda kula da cin ki da shan ki duk yana karkashin iko na ne yanzu, ba zan so Allah ya tambayeni dalilin barin ki da yunwa ba.
Ta tashi tsaye daga kan kujerar, tsakaninta da Allah tace in dai wannan hakkin ne na yafe maka duniya da lahira, kai har dama duk wasu sauran hakkoki nawa dake kanka kaje na yafe... Hannu yasa ya dawo da ita ya zaunar inda ta tashi, ya kara dauko naman ya nufi bakinta dashi yace "naji nagode, amma ni ban yafe miki nawa hakkin dake kanki ba, umarni nake baki yanzun.... Karbi kici tun kafin na miki dura kin dai san zan iya!". Kwalla ta ciko idanunta kamar ta kece da kuka haka take ji, da wannan damar ta hakki zai yi amfani yana kwararta. Abinda ta dinga fada a cikin ranta kenan, ta bude bakin a hankali ya saka mata naman, shima ruwane ya tasattsafo a nashi idanun, yayi saurin maida su. Ya dinga bata naman zuciyarsa cike da alhini, ga dai Ameenah macen daya jima yana mafarkin kasancewarta matarsa a gabanshi yau, kuma a matsayin matar tashi, sai dai ita bata dauke shi a matsayin mijin ba. Wai har sai yaushe ne shima zai dandana zakin so kamar sauran mutane?
Bai kyale ta ba sai daya tabbatar data koshi, sannan ya fara cin naman shima jiki a sanyaye. Bayan ya gama ya shayar da ita tatacciyar madara shima ya sha, da kansa ya hada kayan da suka yi amfani dasu ya fita ya kai kicin, ya sake dawowa dakin. Tana zaune inda ya barta a zaune zuciyarta na luguden daka cike da tsoron abinda zai biyo baya. Rigar shi dake kan gadonta ya dauka tare da hularshi ya tsaya a kanta, ya jima yana kallonta ba tare da yayi magana ba ita kuma bata daga kanta ba. Ya saki ajiyar zuciya a sanyaye cike da tausayin kansa da zuciyarsa, muryarsa a shake yace ki je kiyi brush ki kwanta Ameenah, sai da safe! Ya juya cikin sauri ya bar dakin babu ko waiwaye, sai da taji ya maida kofar ya rufe sannan ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya ta samun relief tayi hamdala, a nutse babu fargabar komi ta fada toilet da niyar watsawa jikinta ruwa don yanayin garin akwai zafi.
Dakinshi ya shiga ya lalubi gefen gado ya zauna ya dafe kanshi, ya fada nannauyan tunani na neman mafita game da zamansu da Ameenah. Ya kula sosai zasu sha dabi da yarinyar wanda baya jin zai iya aminta da hakan. Yadda zuciyarsa take bukatar soyayyar ta, haka gangar jikinsa ke bukatar nata jikin. Ya dade sosai cikin zuzzurfan tunani na neman mafita, me ya kamata yayi yanzu? Soyayyar zai fara nema ko kuma gangar jikinta? Ko kuwa duka a lokaci guda?? Daga karshe dai ya lalubo mafitar da yake ganin itace mafi a'ala a gareshi. Bai san lokacin da wani tattausan murmushi ya subuce masa ba, ya mike da kuzarin shi cike da kwarin gwiwa ya fada wanka.
Barci har ya fara daukarta lokacin da taji an turo kofar dakin an shigo tare da kunna hasken dakin, cikin sauri ta kalli kofar, Modibbo ne a tsaye jikin kofar ya harde hannu a kirji yana kallonta. Cikin wani irin rawar jiki da sauri ta yayimo bargo ta rufa akan dan karamin wandon jikinta wanda da kadan ya kai mata cinya da wata half vest mai hannu daya. Yayi fuska kamar bai ga komi ba duk da cewa gabadaya babu inda baya rawa a jikinsa saboda kyakkyawar kirar Coca-Cola bottle daya gani ta Ameenah. Ya karasa shiga cikin dakin ba tare daya kara kallon sashen da take ba yace idan kina da alwala taso muyi sallah. Ta bishi da kallo cikin alamun tambaya, har ya dauko abin sallah ya shimfida bata samu ta motsa ba. Ya juya ya kalleta, murya a dan kaurare yace ke fa nake jira. Tace ban gane sallar da kake nufi bane. Ya ja fuska sosai yace "kuma so kike yi ki san ko wace iri ce koh??".......
0 comments:
Post a Comment