Kai tsaye tanufi pallow tana tafiya tana girgiza tana yanga,
A can ta hango mutane Zazzaune a kan kujera,
Mahmud yana tsiyaya masu lemo a cup,
daga ganin alama kasan suna da fahimmanci gareshi."
Sai da tazo dafdasu a can tayi tozali da Abba,
fara'a tasaki a fuskarta, ta nufi wurinsa domin ta gaida shi,
don shi kad'ai tasani a cikin mutanen da tagani zazzaune a pallow,
amma daga ganin mommy ta fahimci cewa itace mahaifiyar mahmud sai kuma Khalil wanda ta sanshi tun a wurin partty kasancewar ya gabatar mata da kanshi a matsayinsa na k'anen Ango,
Bayan hakan kuma da zarar ka kalli Khalil da mahmud zakaga suna matuk'ar kama da junansu sosai."
Sai kuma kyawawan 'yan mata da tagani guda biyu wad'anda suka ci kwalliya, musamman dijama data hard'e k'afa d'aya kan d'aya tana mata wani kallo na bakida tarbiya."
Mahmud yayi saurin doka mata tsawa tun kafin ta kai da zuwa wurin Abba, yana Jifanta da wani kallon tsana,
Wanda yasa tayi saurin dakatawa da zuwa wurin, jikinta ya soma rawar tsoro."
Ya nunata da hannu rai b'ace yace "dibeki kidibi jikinki, ki kuma dibi kayan da ke sanye a jikinki a hakan zaki tunkari mahaifana da sunan zaku gaisa dasu?"
Kina so ki nunawa duniya cewa bakida tarbiya kenan, kina kuma so ki nunawa mahaifana cewa banyi dacen matar aureba."
Ya kuma doka mata tsawa yace "Dan Allaha malama kije ki suturta jikinki, ki sanya kayan mutumci snn kifito Ku gaisa."
Sai a lokacin taji kunyar kayan dake sanye a jikinta, jiki sab'ule ta juya tana tafiya ko ina na jikinta yana motsowa."
Gaba d'ayansu saboda jin kunyar shigar da tayi ko wannensu ya kauda kai daga kallonta amma banda Khalil,
Da ya karkace kai ya k'ureta da ido yana k'arewa surar jikinta kallo a zuciyarsa yana fad'in brother yayi dacen mata amma gaskiya zai huta a wurin can."
Tsohuwa kuma saboda mamaki da Al'ajabi kasa magana tayi, xaune take wuri d'aya a kan kujera ta rafka tagumi, tarasa abin fad'a,
Can ta nisa ta kalli mahmud dake zaune daga ganinsa akasan ransa a b'ace yake tace "kai kuma irin matar da KA aura kenan?"
Ta rik'e baki tace "Allah mai iko yau naga abinda mmki, naga abinda bantab'a gani ba a duniya."
Kowa yayi shuru yana sauraren tsohuwa a zahirin gaskiya kuma kowa da abinda yake tunani a ransa musamman mommy da tun farko bataso aurensa da Yusra ba sabida rashin tarbiyarta da kuma sangartarta uwa uba rashin kamun kai,
Dan dai ba yanda zatayi ne,
Abba ya riga da ya goyi bayan sai anyi auren."
Abba shima abin mmki yake bashi Ashe Dama Yusra bata da kunya hakan bai saniba?"
Ashe bata da tarbiya bai saniba?" Da yasan hakan take gudanar da tarbiyarta da bbu abinda zaisanya ya amince da buk'atar Alhaji Atiku, na aurawa mahmud ita."
Amma yaji dad'in tsawar da Mahmud yayi mata akan taje ta suturta jikinta wnn shi zaisanya tasan ba dai dai ta aikataba ko da a nan gaba idan wasu bak'in sukazo bazata tab'a tunanin ta fito a hakan ba."
Mommy taja dogon numfashi daga tinanin da takeyi ta kalli mahmud dake zaune tace "meyasa KA dokawa matarka tsawa wanda har ya sanyata tayi saurin firgita a gabanmu?"
Karka kuma yimata tsawa hakan Idan tayi wani abin da ba dai dai ba janta zakayi wuri d'aya KA zaunar da ita cikin hikima da kwantar da hankali ka nuna mata abinda tayi bata kyautaba, KA Nuna mata yanda kakeso ta kasance, zatafi fahimta
Baka dinga yi mata tsawa kana disgata a gaban bainar jama'a ba, hakan da kakeyi bayada kyau ko a addini."
Sunkuyar da kai yayi yace "mommy kiyi hak'uri bazan kuma ba."
Murmushi tayi tace "Allah yashi maku Albarka ya Baku zaman lafiya da hak'uri a zaman aurenku."
Aka amsa da Ameen amma banda dijama da tsohuwa."
Tsohuwa ta mik'e tsaye tana gyara mayafinta
tanufi hanyar waje, tana fad'in "ni da yake ba uwarka bace Wanda ta tsungunna ta haifeka, A lokacin da nake magana ai kyaleni kayi, kayi banxa dani,
Amma da uwarka tayi maka magana sunkuyar da kai k'asa kayi kana saurarenta daga k"arshe kuma kashiga bata hak'uri."
To na bar maka gidanka, na barka da marar kunyar matarka mai yawo tsirara a gaban bainar jama'a. Kai kan bakayi dacen mata ba, a hakan za'a aura maka 'yar uwarka a kawo maka ita, wnn fitsararriyar matar taka ta b'ata mata tarbiya,
Gaba d'ayansu kowa ya d'aga kai yana kallon tsohuwa Abba da mommy sai rok'on Allah sukeyi Allah yasa kadda tsohuwa ta furta abinda ba yanzun sukayi Alk'awarin fitar dashiba."
Tsohuwa na ganin kallo ya dawo kanta komai ta tuna ohoo tayi saurin Jan bakinta tayi shuru."
Shima mahmud d'in yashiga mmkin wace 'yar uwa tashi za'a aura mashi?"
Idan kuwa da gaske ne,
So akeyi a kashe masa rayuwa baza"a barshi ya zab'i wacce yakeso ba?"
A gaskiya a wnn karon sai dai Abba ya hak'ura domin bazai tab'a Amince masa ba."
Dijama najin hakan sai da gabanta ya yanke ya fad'i, tashiga tashin hankali,
Wace 'yar uwace tashi Wanda za'a kuma aura masa?"
Khalil kuma da yasan kwanan zancen ya kuma had'e rai, yana kallon tsohuwa yana jiran ta furta wata magana wanda batayi masa ba a tsakanin dijama da mahmud a nan take zai bata amsa domin kuwa babu wani Wanda ya isa ya aure dijama bayanshi, a yanda yakejin dijama a ransa komai yana iya aikatawa in har zai sanya ya sameta ya aureta tazama mallakinsa."
cike da mmki mahmud ya Mik'e ya nufi wurin tsohuwa
yana fad'in "yi hak'uri tsohuwa kidawo ki zauna ba kyaleki nayiwaba, ai ke kinsan bana kyaleki."
Fad'amun naji wacece kuma za'a aura mun?"
Tsohuwa tace "bazan fad'aba sainaji shak'a da bak'ura."
Mahmud yace "Allah yabaki hak'uri 'yar tsohuwa mai ran k'arfe."
ganin kusan minti 30 yusra bata fitoba,
Mommy da Abba suka mik'e tsaye Abba ya riga fita yana masu sallama snn mommy tare da su dijama,
Mahmud y bisu da kallo yace mommy bazakujira tafito Ku gaisa ba?"
Mommy tace idan tafito KA gaida ita sai mun sake dawowa, tafita SU fateema suka bi bayanta tareda Khalil, wanda duk yaji haushin tafiyar da akayi batare da Yusra tafito ya kuma kallonta ya tattacewa brother irin matar da ya aura."
Hakan ya rakasu mota Khalil yajasu suka nufi gida kowa da abinda yake sak"awa a ransa."
A fusace ya juya ya shiga gida, kai tsaye d'akinta ya nufa yana huci, kwance ya tarar da ita kan gado tana latsar wayarta hankalinta a kwance."
Zuciya ta kuma rufeshi ya fisge wayar yayi jifa da ita saida screen d'inta ya farfashe snn ya fincikota da k'arfi ya kwad'a mata mari har sau biyu yana furta , " na tsaneki bana sonki ko a lahira bana fatan nayi tozali da macce irinki nakashashiya marar tarbiya."
Kin wulak'anta mun iyaye wad'anda darajarsu kikaci har aka d'auramun wulak'attacen Aurenki,a kaina amma a yau sune kika bari zaune a parlour suna zaman jiranki."
kisani iyayena k'annena kakata wlh sune farin cikina, kuma yanda kika wulak'antasu sai na wulak'antaki na kuma wulak'anta ubanki."
Ya kuma kwad'a mata mari a karo na uku, ta rik'e kunci tana kallonsa tana kuka,
Ta nufoshi ta shige a jikinsa ta cimuimuye shi,
tana "fad'in KA kasheni mahmud KA kasheni nace Domin kawai nace ina sonka?
,KA kasheni na huta, amma kasani ko yanzun KA kasheni nacika burina na aureka, kai mijina ne ni matarka ce sai dai bak'in cikina d'aya da har yanzun ban......
Bata iyar da maganar da takeyiba taji saukar belt a jikinta abinda tunda uwarta ta haifeta bata tab'a jiba."
Kuka takeyi sosai tana Neman d'auki dakyar tasamu ta fita d'akin da gudu ta fad'a d'aya d'akin ta rufe ta sanya key tashiga kuka tana birgima, a maimakon tayi nadamar aurensa da tayi sai ma wani sabon sonshi taji yana taso mata. A zuciya."
_Hmmmmm so hana ganin laifi_
Da zuwansu Abba gida suka hau shirya kayansu zuwa gida, Amma banda Khalil da yace sai zuwa anjima zai taho idan Ahmad ya shirya."
Cikin ikon Allah suka sauka gida lafiya,
Washe gari tsohuwa itama ta hau shirya kayanta harda na dijama zasu koma Tofa, Abba da mommy suka shiga bata hak'uri dakyar aka samu tsohuwa ta hak'ura amma da sharad'in za'a fitar da dijama makarantar kwana."
Abba ya ameence da hakan, Dama kuma saura mako d'aya sufara jarabawar k'arewa."
*************
Sulaima da matarsa Fareeda kud'i sun zauna hankalinsu ya kwanta har fareeda ta kuma haihuwar 'yarta mace fadila."
Babu abinda zai iya cewa Abba da mahmud sai godiya domin A yanzun Abba ya wuce mahaifin Abokinsa, ya zama mahaifinsa mahmud yawuce Abokinsa ya zama d'an uwansa,
Tin lokacin da sulaima ya d'ora ido a kan dijama yaji yakamu da sonta,
Kuma duk irin rashin ji da yakeji mahmud yana fad'a akanta bai ganshi a tare da itaba.
Asalima na tsuwa ya gani a tare da ita da kamala,
Macce Wanda bata son yawan suruto da damuwa,
Bai taushi hannu ba kai tsaye ya same Abba ya fad'a masa k'udurinsa a kan dijama,
Abba yanuna jin dad'insa sosai a kan hakan kuma ya Amince a kan yaje ya nemi so a wurinta."
Alhaji Atiku hankali ya kwanta shalelensa ta aure Wanda takeso,
Amma wata damuwa d'aya da take damunsa tun lokacin da ya kori sulaiman daga wurin aiki bai kuma samun nutsuwa da kwanciyar hankaliba."
Da zarar ya shiga ofice d'insa zaiji gaba d'aya hankalinsa ya tashi baya iya zama yayi aikin da ya kawoshi, a cikin tashin hankali zai fita daga office d'in ya koma gidansa
A yanzun abin ya cutara kwata kw zauna ata baya k'aunar yabi Kota kusa da ofice d'in bare ya shiga cikinsa ya yayi aiki."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )
*42*
~~ Gaba d'aya yaransa abin yana damunsu,
sun shiga cikin damuwar canzawar da oga yayi, a lokaci d'aya,
amma banda Mahmud, dako a jikinsa aikinsa yakeyi ba ja da baya."
Yanzun kimanin shekara d'aya kenan Alhaji Atiku office d'insa ya gagaresa zama
Ga kuma lokacin siyasa ya kunno kai ana buk'atar taimakon commandan d'in sojoji, domin a bawa k'asa tsaro."
a duk lokacin da shugaban k'asa yayo aike a sanar ya tura jami'an tsaro sojoji ba'a tarar dashi a office."
Anan take sak'o ya iso wurinsa daga shugaban k'asa, akan cewa andakatar dashi daga aiki har sai zuwa lokacin da yaje ya nemo lafiyarsa snn yadawo bakin aikinsa."
Cikin kwana biyu aka Dora mataimakinsa mai adalci, ai kuwa cikin sati d'aya komai ya fara tafiya dai dai akan gaskiya."
Tun lokacin da sak'on sallama daga aiki ya tarar da Alhaji Atiku ya shiga rud'u da tashin hankali, babu abinda yafi d'aga masa hankali sai ce masa da akayi yaje ya nemo lafiyarsa."
Kuwa yakeyi yana d'aga murya tare da kai komo paloow zuwa birdromm yana fad'in " naje na nemo lafiyata hauka akace inayi ne?" ko zaucewa akace nayi?"
Sam bazai yiwoba inaji ina gani da raina da lafiya ta a saukeni daga kan kujerata,
Da k'arfi yashiga doka Kansa a bango,
mommy mahaifiyar Yusra tana gefensa tana magiya akan yayi hak'uri yabi komai a sannu, sai k'ok'arin fisgoshi takeyi amma ina yafi k'arfinta."
Sallamar mahmud taji yashigo pallow wanda rabon da yazo gidan tun kafin a d'aura masa auren Yusra."
Hango Alhaji Atiku yayi yana magagganu yana doka kansa a bango cikin hanzari ya nufeshi,
Yana fad'in subahanallahi Daddy meyake faruwa?"
Mommyn Yusra tace "Dan mahmud KA taimakamun ka janye shi daga wurin KA zaunar dashi."
Da kyar Mahmud ya samu ya janyeshi ya kwantar dashi a kan kujera,
Ya kafeshi da ido yana fad'in sannu daddy,
"Mommy meya sameshi?"
Alhaji Atiku ya zabura ya tashi zaune yace "mahmud wai ni za'a dakatar daga wurin aiki, ni Alhaji Atiku, sai kuma yayi shuru."
Shuru mahmud yayi ya yana tunanin irin dubban mutanen da shi ya kora da kansa, ashe
Ba dad'i."
"Daddy kayi hak'uri KA barwa Allah komai, idan kayi dibo da irin mutanen da kayita sallama daga aiki, ina ganin suma hak'urin sukayi suka barwa Allah,
Kaima ya kamata kayi hak'uri tunda kaine mai sallama gashi sallamar tazo kanka."
Magagganun da mahmud yakeyi sune suka dawo da tinaninsa,
Ashe dama hakan akeji idan aka dakatar da mutum da ga aiki?"
Yanzun duk wad'anda ya kora haka suka zauna cikin bak'in ciki da tashin hankali?"
Babu wanda ya fad'o masa a rai sai sulaiman wanda tun lokacin da ya koreshi ya kasa zama cikin kwanciyar hankali, gaba d'aya natsuwa ta k'aura cemasa,
Hakan sulaiman ya tsinci Kansa a cikin tashin hankali,a lokacin da ya koresa?"
yana da labarin irin wuyar da yasha kafin ya samu aikin, ba dan komai sai dan yayi dogaro da kansa ya kuma tallafi mahaifansa."
Mahmud ya katse masa tunani da yake cewa, daddy kayi amfani da shawarar da suka baka kaje asibity a diba lafiyarka ko ba komai kana buk'atar ganin likita ko Dan ayi test din jininka a fad'a maka halin da kake ciki domin kuwa silinda maiyi maka hidima a office ban yarda da lafiyarta ba."
Yana kaiwa nan ya mik'e tsaye yace "Allah ya tsare gaba daddy,
Shalele tana gaida kai."
Yyi wuce warsa."
Tashin hankali Alhaji Atiku ya kuma shiga da yaji kalaman da Mahmud ya fad'a masa yana nufin bai yarda da lafiyarsa kenan?
Wai mai yasa mahmud yake tunkararsa gaba da gaba ya fad'a masa magana,
Ya tsinci kansa da kasa d'aukar masa mataki?"
Wacece silinda kuma?"
kaddai ace yana ganin lokacin da yake hutawa da abokiyar aikinsu?"
Rud'u ya kuma yashiga, yana fad'in karya ne, lafiyata glau babu abinda yake damuna."
mommy ta matso kusa dashi ta zauna tashiga kwantar masa da hankali cikin kalamai masu taushi snn da kyar ta samu ya kai kwance akan kujera bacci b'arawo yayi awon gaba dashi."
****************
Yau ake yin bikin kammala makaratun su dijama Wanda za'a had'e tare da walimar saukarsu, Khalil sai kai da komo yakeyi, duk wani abinda dijama da fateema suke buk'ata Khalil ya sawo ya ajiye masu."
Hakan sulaiman shima ya taka rawar gani wurin tashi gudunmawa."
Khalil yana lura da take taken sulaiman a kan dijama, ya fahimci sonta yakeyi, wnn dalilin yasa idan zasuyi had'uwa goma wuri d'aya baya iya masa magana sab'anin da,
Idan suka had'u har hira sukeyi har da 'yar wasa a tsaka ninsu."
Shima sulaiman hakan ya fahimci khalil ya fad'a matsananciyar soyayyar dijama wanda yake ganin dijama a yanzun alurace cikin ruwa mai rabo ke d'auka, Dan haka duk wani shariyarshi yaje yayi abarsa bai damuba Allah ya ba mai rabo sa'a."
Wanda ita kuma dijamar gaba d'aya duk abinda ake baya gabanta burinta d'aya Allah yakawo yaya mahmud lafiya wanda tun asuba da sukayi waya ya sanar da ita cewa gashi a kan hanyar zuwa,
amma kadda ta fad'awa Mommy da Abba sai dai kawai su ganshi yazo."
Gashi yanzun har kusan k'arfe 10am bai isoba,
kowa ya hallara a wurin amma banda dijama wanda ta shirya cikin wani lesi ruwan madara wanda Abba ya d'unka masu iri d'aya tare da fateema, d'inkin riga da saket ne, sunyi matuk'ar kama jikinta k'ugunta ya fito tare da k'irjinta wad'anda suka bayyana a cikin rigarta sunyi tsaitsaye sun cika cikin rigar,
Fateema ta dubeta tace kai sister kinganki kuwa yanda kikayi kyau?" Dijamah ta d'an saki murmushi tace "nagode sis aikema kinyi kyau kinma fini kyau."
Fateema ta rik'e baki tace wace ni, aini nasan kinfini komai bama zan had"a kaina da keba."
Dijama ta d'an ya mutsa fuska ta dubi wayar hannunta,
Snn tace "daina fad'ar hakan dani dake duk d'aya,
Ganin lokaci yana tafiya Abba ya soma kiransu suyi sauri sufito,
Fateema ce bata iyar da kammala shiryawa ba,
Ta dubi dijama tace "lah kinga sister hijabanmu suna d'akin Momy kije ki d"auko mana kafin na sanya kayana."
Mik'ewa dijama tayi da waya a kunnenta tana gwada kiran yaya mahmud ko Allah zaisa kiran ya shiga,
Amsa d"aya ce ake bata wayar a kashe take."
Ta cikin babban falon gidan ta wuce zata shiga d'akin mommy bata lura da mommy da Abba da Khalil da sulaiman ba, gaba d'aya hankalinta baya tare da ita yana a wayar ta, zaune suke suna jiran fitowarsu."
Tafiya takeyi tana wani juyi, idan kagani sai KA d'auka da gaggan takeyi kuma ainahin tafiyar ta kenan,
Ga k'irjinta a cike Dana shanu gata doguwa fara kyalkyawa, masu karatu duk yanda zan misalta maku dijama ta wuce nan."
Duk yanda Khalil yake tunanin dijama sai ma gani yayi ta wuce nan,
Haka sulaiman da ya k'ureta da ido yana kallo."
Wani kallo Khalil yake mata irin nasu na 'yan duniya wanda suka San qualities d'in cikakkiyar mace."
Wani kishi ya tasowa Khalil ganin yanda sulaiman ya kafeta da ido yana kallonta,
Shima sulaiman hakan,
Atare suka juya suka kalli junansu suka sakarwa junansu harara."
*IYA COMMENT D'INKU IYA TYPING D'INKU*🤷🏻♀🤷🏻♀🤷🏻♀
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )
*43*
Abba na ganin hakan yayi gyaran murya ya kuma dibonsu a tare gani yayi ko wanne jiyakeyi kamar ya had'iye d'an uwansa,
Yace "ya kamata kutashi Ku isa wurin kafin muk'araso."
Gaba d'ayansu suka kalli Abba,
Mommy tace "ya kamata ku isa wurin tin yanzun domin kuga yanayin taron gamu nan zuwa yanzun idan suka kammala shiryawa."
Jiki ba kwari kowannesu ya mik'e ya d'auki key din motarsa ya fita, domin zaman da sukeyi a wurin ko wanne yaci Alwashin a motarsa dijama zata shiga."
Tsohuwa ce tafito daga d'akinta wanda yake masauki ne a gareta a duk lokacin da tazo,
Itama cikin shirinta na zuwa walima."
Tana fitowa taga Abba da mommy zaune, a pallow
Sai da ta lalubo goronta a Jakarta ta gutsara snn ta kalli Abba tace "wai tun d'azun me ake jirane, ba'a tafiba
Har na kwanta bacci na tashi,
Duk a tinanina har kuntafi kun barni."
Mommy tayi murmushi tace "wamu nan ai bamu isa mutafi mu barkiba, Inna."
Abba ya k'ara da cewa "sai dai a fasa walimar."
Tun d'azun zaman jiran fitowarsu mukeyi."
Tsohuwa bata ce komaiba illah ta nemi wuri a kan kujera ta zauna, tana kallon TV tana cin goronta."
Da sauri dijama ta fito d'akin mommy sanye da k'atuwar hijabi mai hannu ruwan madara kalar lass d'inta,
Hannuta rik'e da d'aya hijabin fateema zata kai mata,
Sai a lokacin ta lura da Abba da mommy da kuma tsohuwa dake zaune a gefe d'aya."
Mommy tace "karfa kub'ata mana lokaci, Ku muke jira tun d'azun kun barmu a zaune."
Ta had'a da d'an saurinta tanufi d'akinsu domin ta mik'awa fateema hijabinta tana fad'in "yi hak'uri mommy ai mun kammala shiryawa."
A kofar d'akin ta tarar da fateema ta mik'a mata hijabin snn suka fito suka shiga motar Abba, tsohuwa ce gidan gaba,
snn gaba d'ayansu har da mommy suka shiga gidan baya Abba yajasu suka nufi makarantar."
Motar Khalil ce a gaba snn mortar sulaiman, a tare suka shiga makarantar ko wanne yanaji da kansa suna nunawa junansu isa."
Khalil ya fara fitowa cikin isa da gadara, ya nufi office d'in shugaban makarantar domin ya biya kud'in duk abinda ake buk'ata, gaisawa sukayi da shugaba,
Ya shiga tambayarsa nawa ne kud'in?" Dame dame ake buk'ata?"
Shugaba yace "ai tuni, Yayanka yazo yabiya harda kyauta ya mana mai tsoka, kai munji dad'i sosai ubangiji Allah ya biya yayanka shima ya bashi wad'anda zasu taimakesa."
"Ameen yace a tak'aice, tare da mayar da kud'insa a Aljihu."
Yafita yana mamakin wanne yayan NASA?"
Shi dai yasan brother bai zoba, to kodai sulaiman ne yayi masa rigage."
Hmm lallai kuwa zai nunawa sulaiman ba'a ja dashi a fagen Neman macce."
Motar Abba ta tsaya a harabar makarantar taro yayi taro mutane an hallara manya da 'yan siyasa, Abba yana d'aya daga cikin manyan bak'i wad'anda ake jiran isowarsa,
Haka itama mommy da tsohuwa suka nufi wurin mata iyayen yara suka zauna cikin manyan mata 'yan gayu."
Suma su Dijama suka nufi wurin d'alibai 'yan uwansu suka zauna."
Anan aka fara gudanar da abinda ya tarasu a wurin."
Ko wanne d'alibi yana cikin farin ciki amma banda dijama da sai murmushin yak'e takeyi hankalinta na wurin yaya mahmud, rashin ganinsa da batayi ba."
Abinda batasani ba shine,
tun k'arfe 8am mahmud ya dura garin kano, bai zame ko ina ba sai makarantarsu kai tsaye wurin malaman ya nufa wad'anda dama sunsanshi sunsan matsayinsa a wurin su dijama.
Anan yashiga tambayar shugaban makaranta duk wani abin da ake buk'a."
Shugaba yashiga yimasa lissafi, anan take ya cire kud'in ya biya, tare da tashi gudunmawa."
Gefe d'aya yaja ya zauna yana kallon kowa d'aya bayan d'aya,
A can ya hango motar Khalil da sulaiman,
Har zuwa lokacin da Khalil yashiga office d'in shugaban makaranta,
mahmud yana ganinsa ya shiga office d'in yyi murmushi yace "yaro man kaza."
Jim kad'an yaga Abba ya shigo tare da mommy da tsohuwa."
Snn ya hango dijama ta fito tare da fateema, ko wanne ya tafi wurin zamansa ya zauna."
Cigaba akayi da bikin,
yana gefe d'aya yana kallon kowa d'aya bayan d'aya."
Nana khadija hassan yaji ankira domin ta bud'a taro da karatun AlQUR'ANI Dijama ta fito jiki a sanyaye tana tafiya a hankali,
Ta gefen tsohuwa tabi zata wuce tsohuwa ta d'an mangareta a k'afa tana magana k'asa k"asa "ki d'aga k'afa kiyi tafiya,
Kina tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki."
Dijama ta waiga ta kalli tsohuwa tasaki murmushi,
Snn ta kuma juyawa taci gaba da tafiyarta a hankali mai cike da yanga da rangwad'a."
Khalil da sulaiman ko wanne ya kafe ta da ido cike da birgewa,
Hakan shima mahmud wanda tun tasowar ya kafe ta da ido yana kallonta domin gani yayi tayi masa wani irin fitinannin kyau, wanda baya misaltuwa
d'aga ido yayi yaga duk ilahir mutanen dake wurin kallonta sukeyi."
Wani abin yaji ya taso masa, a zuciya bai San lokacin da
Yaja dogon tsaki ba tare da had'e fuska yace "dama tasan za'a kalleta ne shiya sa tak'i sanya lik'abi."
Tunaninsa ya tsinke a lokacin da yaji k'ira'ar Alqur'ani yana tashi cikin wata siririyar murya mai dad'in sauraro."
Lumshe idonsa yayi ya kuma bud'esu ya kalli wurin tabbas dijamace 'yar gidan tsohuwa ke karantun Alqur'ani,
Wayarsa ya Ciro daga Aljihunsa yana murmushin farin ciki ya shiga d'aukarta camer videos."
Bayan ta kammala karatun qur'anin ta kuma bud'e taron cikin harshen turanci."
Duk wani masoyin dijama a wurin idan ya ganta sai yaji ta burgeshi ta kuma Shiga ransa."
Mahmud bai San lokacin da ya mik'e tsaye ya nufi motarsa ya d'auko babban kyautar da yazo mata da ita wanda shi kad'ai yasan kome a ciki."
Fuskarsa cike da farin cikin da baya misaltuwa ya nufi cikin taron,
Sai da yazo daf da ita wanda yayi dai dai da kammala warta,
Fuskarsa cike da annuri, ya
Mik'a mata kyautar. Ganin hakan gaba d'aya wurin a kad'auki tab'i, domin sun burge mutane, kuma shine mutum ba farko da ya fara bata kyauta girmamawa."
K'ureshi da ido tayi cike da farin ciki snn ta sauk'e ajiyar zuciya snn ta d'an runsuna alamar girmamawa ta k'arbi kyautar tana godiya "
Hakan da sukayi ba k'amin burge mutanen wurin sukayi ba, aka shiga d'aukar photo na Abba da mommy da tsohuwa sai murmushin jin dad'i sukeyi suna mamakin yaushe yazo?"
Hakan shima sulaiman murmushi yakeyi,
Wanda khalil yacika saima yatashi daga inda yake kallonsu ya koma motarsa yayi zamansa, zuciyarsa na tafasa."
Hakan kowa yayita bata kyauta yana jinjina mata da yaba mata a kan k'ok'arinta."
Taro yayi taro mutane anci ansha an wadata dijama da fateema sunsamu kyauta ta ban mmki, wanda da zarar anbawa dijama kyauta idan ta k'arb'a tayi godiya Mahmud take mik'amawa, yin hakan ba k'aramin dad'i yake yiwa Abba da mommy ba."
Bayan antashi daga taron kowa yana k'ok'arin shiga motarsa tareda iyalansa domin su isa gida."
Sama da k'asa aka nemi Mahmud da dijama aka rasa,
Abba ya shiga kiran number mahmd yaji ko da suna tare amma gaba d'aya daga number shi harta dijama a kashe take."
Acan bakin get Abba ya hango wucewar motar sa tare da dijama a gaban motar,
Itama tsohuwa ta hangosa ta nuna da hannu da baki tace "wncan ba mamuda bane?"
Gaba d'aya kowa ya juya ya kallesa mommy tace "shine kuma ina ganin kamar a tare suke."
Khalil ya cika ya burzar da iska mai zafi cike da jin haushi yace "amma bro meyasa yyi hakan ya kamata ya sanar zai tafi da ita."
Tsohuwa tayi karaf tace "ina ruwan ka?" Yak'i ya sanar d'in, meye naka a ciki?"
Ta dubi Abba tace "Hassan shiga mota KA kaimu gida,
Ai shima mahmud d'in zurfin cikine dashi wanda ba inda zai kaishi."
Sulaiman yana gefensu a tsaye, FAREEDA sai waya take masa, akan yyi sauri ya dawo ta kammala abinci,
murmushi ya saki ya d'an runsuna yyi wa su Abba sallama ya shiga motarsa yyi tafiyarsa."
Khalil yanajin tsohuwa ta dakatar dashi,
Cikin jin haushi da takaici shima ya nufi motarsa, Abba ya lura da yanda yake wani ciccira idonsa yayi ja,
Ya dakatar dashi yakira sunansa tare da nunashi da hannu yace "Khalil muddun kasake kayi mugun gudu to kasani da kai da mota sai dai kagani a abokananka."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )
*44*
*DEDICATED TO MSS HAFSY stylishlady*💋
Turo baki yayi yace "to ni Abba ya akeso nayi ne?"
Sai nake ganin kamar duk an tsaneni, kawai a kasheni a huta."
Mommy tace "khalil mu kake fad'awa magana?"
Abba yayi shuru ya k'ureshi da ido yana kallonsa."
Tsohuwa tace "eh lallai yaro ka girma wuyanka ya isa yanka, ai abinda ya rage maka d'aya ne kazo KA dake mu kawai sai ka huta."
Fateema tace "kefa tsohuwa baki kashe wuta sai dai ki kuma rurata."
Tsohuwa tace "yi mun shuru,
rufemun baki me kika sani ke kuma?"
Mommy tana gefen mota tsaye tana kallonsu batayi magana ba."
Snn Abba ya bud'e mota ya shiga, dukansu suka shiga harda tsohuwa da har yanxun masifar takeyi bakinta yaki yayi shuru."
Khalil yana ganin Abba ya Shiga mota shima ya mirgina kai cike da jin haushi, ya tayar da mota suka fita a tare."
Motar Abba ke gaba Khalil na biye dashi a baya,
Abba yana kallonsa a dubi."
Hanyar makaranta Abba yaga khalil ya nufa yana tafiya da mota a hankali kamar wanda baya da lafiya."
Girgiza kai Abba yayi,
Yashiga magana a zuciyarsa dole ne a sake sabon zama domin kuwa Khalil ya fad'a matsananciyar soyayyar ummie, wanda a yanda yake gani a idonsa komai zai iya faruwa idan baisameta ba."
Dogon nishi yaja wanda yayi dai dai da karya kwanar gidansa."
Duk a tunaninsu zasu tarar da motar mahmud ajiye a kofar gidan amma abin mmki basu ganshi ba, bai isoba."
Ko wanne yaja bakinsa yyi shuru, daga ciki kuwa har da tsohuwa, da ta mere baki tayi shigewarta gida."
Mahmud kuma bayan antashi daga taron idonsa na wurin dijama, yana ganin irin malamai da d'alibai ko wannesu k'ok'ari sokeyi sukawo jiki wurin ta domin suyi photo, kasan cewar makarantar had'e take da maza da mata."
Duk inda dijama ta wurga sai biyarta sukeyi suna hotuna, can ya hango wani malami wanda tun d'azun ya kame wuri d'aya cikin wasu k'ananun kaya, duk motsin da yayi idonsa na kanta, wurinta
Yanufa yana murmushi yana kuma gyara kwalar rigarsa, dijama tana ganinsa itama ta sakar masa murmushi tace uncle Salis ina wuni."
Ya kuma sakar mata murmushi ya amsa tareda matsowa kusa gareta yana fad'in Nana khadija yar farar yarinya kyakkyawa makaranta zatayi rashinki da kewarki inama zamuyita zama dake hakan."
Zaro ido tayi alamar shagwab'a tana murmushi "karka damu uncle ai ba'a rabuba ana tare."
D'an sunkuyawa yayi kusa da ita ya d'aga wayarsa ya d'aukesu photo suna murmushi."
Mahmud yana ganin hakan ya taso daga inda yake zaune ya nufo wurinsu, a dai dai lokacin da uncle ke cewa nana khadija ki amince na dinga zuwa gidanku mudinga gaisuwa."
D'aga kan da zatayi tana murmushi domin tana matuk'ar ganin mutuncin uncle salis,
ya taimaketa sosai a kan karatunta,
ido biyu sukayi da mahmud tsaye a kusa da ita ya sanya hannuwansa biyu a aljihun wandonsa,
Yana kallonta tareda wurga mata wata kalar harara."
Jikinta ya fara rawa ta soma ja da baya tana fad'in "dan Allah yaya kayi hak'uri."
Uncle ya juya ya dubi Mahmud dake tsaye wurin d'aya kallo d'aya yayi masa sai da antar cikinsa ta motsa,
Tare da fad'uwar gaba,
kasancewar mahmud namijine jarumi k'akkarfa mai kwarjini."
Sulalewa uncle yayi yayi tafiyarsa bai kuma yin magana ba."
Ita kuma dijama sai hak'uri take bashi Tana ja da baya. Ganin ba wanda ya lura dasu, tana Neman tara mashi jama'a ya doka mata tsawa,
Sai gani tayi ya zamar mata mahmud dinsa wadda tasani ada."
ya zaro mata rinanun idanunsa yace "duk kika kuskura kika kuma d'aga k'afa daga inda kike,
Babu abinda zai hana na kakkarya k'afafun idan na kamaki."
Tsayawa tayi cak."
ta k'ureshi ido cike da tsoro jikinta na rawa "dan Allah yaya mahmud kayi hakuri."
Ya d'aga k'afarsa cike da k'asaita yana tafiya guda guda, ya isa wurinta ya rik'o hannunta ya jefata a mota ya zagaya mazauninsa yaja motar suka fita makaranta."
Gudu yake da mota kamar zai tashi sama, wanda gaba d'aya hankalin dijama ya tashi ta sadakar kasheta kawai zaiyi domin ganin b'acin ransa wanda bata tab'a ganiba."
Hankalinta ya kuma tashi a lokacin da taga ya d'auke hanya wanda bata gida ba."
"Yaya dan Allah kayi hak'uri na tuba, wlh Allah Uncle d'inmu ne, idan k'arya namaka ka tambayi FATEEMA zata fad'a maka."
Wani wawan murki yaja a gefen titi a can cikin uguwar GRA unguwarda ko kasheka za'ayi ba wanda zai taimakeka."
Kifa kanshi yyi a kan sitiyarin motar sai da ya d'auki minti goma a hakan snn ya d'aga kai ya dubeta ya wurga mata wani irin kallo da rinanun idanunsa wanda sai da hantar cikinta ta murd'a ta kasa yin magana ta dinga d'aga hannu alamar yayi hak'uri ta tuba."
Hannu ya d'ora a kan bakinsa alamar tayi shuru🤫."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_ )
_DEDICATED TO MAMAN SADEEQ MARUBUCIYAR MUHIM HAK'IK'A LITTAFIN MUHIM YA NI SHAD'ANTAR YA FAD'AKAR DAMU KINYI NAMIJIN K'OK'ARI WURIN BAJE FASAHARKI DA HIKIMARKI WURIN ZUBA WNN LBR NKI ALLAH YA K'ARA BASIRA DA KWARIN IDO MUNAYINKI IRIN SOSAI D'IN NAN_
*45*
Jiki na rawa ta sanya hannunwanta biyu ta rufe bakinta cike da jin tsoro."
Ido ya kureta dashi, wanda itama shi take kallo, snn yace "bayan matsayinsa na uncle d'inki meye kuma matsayinsa a wurinki?"
Muddun kika kuskura kikayimun k'arya saina tattakaki a wurin nan ba Wanda zai rama maki?"
"Wlh Allah yaya na rantse maka da Allah babu wani abu a tsakaninmu."
Shuru yyi yana kallonta yana karantar gaskiyarta."
Snn yaja dogon nishi tare da mik'a mata handkerchief d'insa fari mai cike da k'amshin turarensa mai sanyin dad'i.
yace "to naji na yarda share hawayen fuskarki, kuma ki natsu magana zanyi da ke."
Amsa tayi da sauri tashiga gogewa, k'amshin turaren ya daki hancinta tayi saurin lumshe ido, tare da sauke ajiyar zuciya."
Ya dubeta yace "Dijamah meyake damunki?"
Da yake sanyaki a damuwa?"
Meyake hanaki bacci?"
Meyake damunki wanda yake sanyaki rama?" Wanda har ciwon zuciya yake Neman kamaki?."
A kwai wanda yake matsa maki a gida ko yake takura maki daga ciki kuwa har da Khalil?"
Ko aure kikeso akwai wanda kikeso wanda bakya iya tunkararsa ki fad'a masa cewa kina sonsa?"
Fad'a munshi kowaye ko mai matsayinsa nayi mki Alk'awarin sai na nemo maki soyayyarsa a duk inda yake domin farin cikinki."
Maganar da yakeyi jitayi kamar ya daka mata mashi a zuciya, idonta ya shiga zubar da hawaye cikin muryar kuka tace " ni bana son kowa bana soyayya da kowa." Tana k'ok'arin bud'e murfin mota ta fita, saboda wani abin datakeji yana taso mata a zuciya."
Da sauri ya rik'o hannunta wanda harta bud'e murfin motar ta zira k'afarta waje zata fita,
wani abin taji ya tsikareta jin hannun yaya mahmud rik'e da hannunta,
Wanda shima hakan yaji wani shocking naratsa shi tun daga saman kanshi har k'asanshi,
Wanda yasanya shi yayi saurin lumshe idonsa,
cikin dasashiyar murya mai cike da kasala yace "karki sake kifita a motar nan."
Jiki ba kwari ta tsaya cak."
daga fitar da zatayi, still hannunsa na cikin hannunta ya kasa sakinta."
Ido ya kureta dashi yana kallonta, yana kuma kallon d'an k'aramin bakinta Wanda taketa faman jujjuyashi tana gunguni, wanda ya kasa jin abinda take fad'a
"Matsa hannunta yayi da k'arfi,
wanda yasa tayi saurin juyowa gaba d'aya ta dubeshi, tana ya mutsa fuska,
"me kike fad'a?" Allah yasa kikeyi mun?."
Ya kuma matse hannun wanda taji zafi sosai tasaki 'yar k'ara tana fad'in "wlh ba Allah ya isa naimaka ba."
"To mekikace?"
turo baki tayi a shagwab'e idonta yana zubar da hawaye tace "bance komai ba."
Baya son ganin hawayenta, ya d'an sassauta rik'on da yayi mata. Tare da janyo fuskarta dai dai saitin fuskarsa karan hancinsa yana gugar karan hancinta, gaba d'aya numfashinsu ya gauraye da na juna,
dukansu sunajin saukar numfashin junansu. Runtse idon tayi tanajin wani abu yana mata yawo tun daga kanta har xuwa k'asanta."
Iska ya dinga hura mata a ido cikin wani salo wanda shima kansa bai San yana yinsaba."
"Daina kuka k'anwata, ya shiga share mata hawaye da d'aya hannunsa, kinsan yayanki mahmud yafi kowa sonki, kuma baya son ganin b'acin ranki."
Bata san lokacin da tasaki murmushi ba tare da sauki ajiyar zuciya. Ta janye fuskarta daga tasa."
Ido ya bita dashi da murmushi a fuskarsa,
Ya kuma gyara zamansa cikin tattausar murya yakira sunanta, "Nana khadija bana son ganinki cikin b'acin rai da damuwa,
Ki cire komai a ranki ki tsaya kiyi karatu, bana son kina kula samari, har sai kin kammala karatunki wanda da zarar kin kammala kin kai matsayin da kikeso ki kai,
ni da kaina zan zab'a maki Mijin aure wanda zai rik'emun ke tsakani da Allah batare da cutarwa ba."
Gabanta ne ya fad'i, ta d'aga kai alamar to."
"Kinyi mun Alk'awari bazaki kula kowa ba bare kuyi soyayya?"
Ta d'aga kai alamar "eh."
"Gud yace tare da kai hannunsa ya Shafa gefen fuskarta yana murmushi "yawwa 'yar k'anwata dan haka nake jidake sosai."
Cikin sigar lallashi yace mekike so na saya maki?" Fad'a mun naji ya kara kunnensa saiti bakinta."
Murmushi tayi ta rufe idonta da tafin hannunta tace "bakomai."
Shima murmushin yakeyi yana kallonta cike da burgewa domin yana son macce mai Alkunya ba kamar Yusra ba."
Tayar da mota yayi ya fara tafiya juyawa yayi ya d'an dubeta still hannunta na kan fuskarta tana murmushi,
kuma burgeshi tayi cikin sigar zolaya yace "oh 'yargidan tsohuwa da jin kunyar yaya mahmud?"
A manta lokacin da aka turomun Buba d'an maigari."
Kuma rufe fuska tayi tana murmushi." Shima murmushin yakeyi yanayi yana kuma kallonta yana tuk'i,
Yau jinsa yakeyi cikin wani yanayi na farin ciki Wanda bai tab"a tsintar kansa cikinsa ba."
Ta wani babban store ya biya da ita, yayi mata siyayyar kayan more rayuwa snn ya suka nufi gida."
****************
Da sallama suka shiga cikin palo gidan,
Wanda gaba d'ayansu suna palon zazzaune harda sulaiman dake zaman jiransa."
tana gaba yana biye da ita a bayansa rik'e da manyan ledodi a hannu."
Ido kowa ya zuba masu yana kallonsu, ganin kowa ya zuba masu ido yasa ,
Dijama tayi sum sum ta shige d'akinsu,
Mahmud ya zagaya kusa da sulaiman ya zauna, ya bashi hannu suka gaisa da yar dariya d'auke a bakinsa,
Snn ya maida kallonsa a wurin Abba da mommy yace "Abba barka da hutawa."
Murmushi Abba yayi yace "yawwa mahmud kundawo?"
Tsohuwa tayi karaf tace " ai mun d'auka a can zaku kwana." Shin wai ma INA kuka tafi."
Kallonta mahmud yayi,
Yayi murmushi yace "meye ruwanki da inda mukatafi tunda kin San ba sayar da ita zanyi ba."
Ya kuma har zuk'a tsohuwa, tashiga masifa tana fad'in aikin banxa aikin wofi, idan kana fad'in abunda ke cikin ranka kafad"a idan kuma baka fad'i zurfin ciki ba inda zai kaika."
Dariya mahmud ya saki mai sauti yace "tsohuwa mai ran k'arfe me kuma zan fad'a?"
"Bansani ba tace had'ida wurga masa harara, ta ci gaba da cin goronta."
Taja bakinta tayi shuru." Gaba d'aya
Palon yayi tsit."
Abba yayi gyaran murya yace "mahmud dama zaman da mukeyi a nan gaba d'ayanmu kai muke jira."
Abba ya dubi sulaiman yace "D'an uwanka sulaiman yanuna yana son k'anwarka,
Ya sameni yayi mun magana yana sonta da aure."
Abba bai rufe bakiba mahmud yace "wacece ko fateema?"
"Ba fateema yakeso ba ummie yakeso, shine nace zanyi maka magana naji ta bakinka."
Juyawa yayi ya Wurgawa sulaiman wani kallo, wanda shi kuma sulaiman ya sakar masa murmushi."
Abba yace "ina sauraronka meye shawararka ko kanada wata magana wanda zakayi a kai."
Cikin wani yanayi na b'acin rai Wanda baya misaltuwa ya dubi Abba yace "indai shawarata ake nema Abba to ban amince da ayiwa dijama aure a yanxun ba domin kuwa karatu zatayi wanda zata tallafi kanta da kuma maraicinta."
Sulaiman yayi karaf yace "na yarda na Amince ko nan da shekara nawa ne bayan ta kammala karatun zan aureta."
Cikin b'acin rai da jin haushi Mahmud yace "ni kuma ban amince ba,
Ban amince ta aureka ba domin kuwa kayi mata tsoha." Dan kuwa dijama bazata auri tsoho kamarka ba mai mata da 'ya'ya."
Tsohuwa tayi karaf tace "idan ka hana ya aureta kai zaka aureta ne?"......
Gabansa ne ya yanke ya fad'i da jin maganar a bazata a bakin tsohuwa."
Mik'ewa tsaye yayi cikin fushi da b'acin rai yace "maganata ta k'arshe ban amince sulaiman ya auri dijama ba, domin kuwa ni na riga da zab'a mata Mijin aure wanda zaiyi dai dai rayuwarta."
Yana kaiwa nan ya d'auki key d'in motar sa ya fita a fusace."
Tsohuwa ta d'aga murya cike da masifa a yanda zai jita tace "zurfin cikin banxa da Wufi anaso ana kaiwa kasuwa dama kafito fili kafad'i abinda ke cikin ranka yafiye maka sauki."
Dariya sulaiman ya saki yace "rabu dashi tsohuwa da bakinsa zaiyi magana a nan gaba."
Dariya shima Abban yakeyi yace "mahmud namijin gaske Wanda da wuya ka gane abinda yakeso da Wanda baya so."
Mommy tace "ai wnn miskilanci ne ke damunsa ba komaiba,
Sulaiman ya kuma sakin dariya yace "Abba kubani nan da wata d'aya mahmud zaiyi magana da bakinsa a kan dijama."
Abba yace "Allah yasa danafi kowa farin ciki domin babban burina d'aya ne a rayuwa na aiwatar da alk'awarin da na d'aukarwa d'an uwana."
ngd sulaiman Allah yayi maku Albarka gaba d'ayanku, aka amsa da Ameen gaba d'aya palon."
_Abin mmki dama sulaiman soyayyar dijama ba da gaske yakeyiba_
_wato had'in baki ne sukayi da Abba domin su fahimci inda mahmud ya dosa a kan dijama wanda har sai yafito ya nunawa duniya cewa yana sonta_
_amma kuma naga mahmud zurfin ciki garesa anya zai iya_
Ina jiran comment dinku masu karatu."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)
*46*
Tuk'i mahmud yakeyi sai jan tsaki yake tare da burzar da iska mai xafi yana share gumi."
Gaba d'aya jinsa yyi baya iya awa d'aya a cikin garin kano, kai tsaye ya d'auki hanyar Abuja, sai gudu yake zubawa."
Yana dafda shiga cikin Abuja dare ya masa dolensa ya nemi wata hotel ya kwana domin tunawa da magar Abba da yake yawan yimasa akan ya daina tuk'in dare."
Juyi yakeyi akan gadon yana hasko fuskar dijama, ya kuma mirginawa zuwa ruf da ciki, maganar Abba ta fad'o masa a rai a kan sulaiman, wani dogon tsaki yaja ya mik'e tsaye ya fad'a toilet yana fad'in Sam baxai yiwoba dijama baxata tab'a auren sulaiman ba."
Wani tafasa yaji zuciyarsa nayi masa Wanda ya rasa dalili,
Ruwan sanyi ya sakarwa kansa yana lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya,
Yusra kuma na ganin dare yayi mahmud baidawoba tashiga tashin hankali,
Tun lokacin da sukayi aure bai tab'a kwana ba a gida ba, ko da dai ba kulata yakeyiba baya son ganinta amma ganinsa da takeyi kullum yana sanyata farin ciki."
Da kyar tasamu safiya ta waye mata, amma ba mahmud babu labarinsa."
Kuka takeyi sosai ta d'auki waya takira Daddy,
Ba sallama bare gaisuwa cikin muryar kuka da tashin hankali tashiga fad'in , "Daddy mahmud bai kwana a gida ba." Nashiga uku daddy kaje kasanya a nemomin Mahmud a duk inda yake, daddy kai kayi mun Alk'awarin duk abinda nakeso zansamu, daddy ina son mahmud amma mahmud baya sona baya kulani baya son ganina a kusa dashi daddy kasanya Mahmoud dole ya soni ya kuma kulani."
Runtse ido yayi yanajin bak'in ciki da k'unci kukan da tilon yarsa takeyi,
Da kyar ya bud'e baki yayi mata magana "shalele daina kuka mahmud lafiyarsa k'alau yaje kano wurin bikin kammala makarantar k'anwarsa dijamah."
Kisanya ido yau mijinki xai dawo gareki, kuma ki kwantar da hankalinki zanyi masa magana dole ya dinga kulaki dole ya soki idan ba hakan ba nasan matakin da zan d'auka daga shi har mahaifin nasa."
Cikin d'aga murya tace "no daddy nasan halinka kana da zafi sosai, nasan KA baka da tausayin nak'asa da kai karkayiwa mijina illah, karka kuri mijina daga aikinsa, idan kuwa ka aikata hakan to kasani nima bazaka sameniba, domin kuwa farin cikin Mahmud shine nawa, tana kaiwa nan takashe wayar tana kuka tare da share hawayen fuskarta."
Shuru tayi tana nazarin maganar daddy dayace mahmud ya tafi kano wurin bikin kammala karatun k'anwarsa dijamah, tashiga maimaita sunanan dijama? To wacece dijama a wurinsa?"
Tabbas tana yawan jin sunan dijama a bakinsa,
Wani lokacin da zarar yashigo gida yana fara'a a waya a kunnensa yana dariya to daga k'arshe zataji yace Cikin sigar zolaya "sai anjima yar k'anwata dijama 'yar gidan tsohuwa, ita kuma tana masa shagwab'a bata son yana kiranta da wnn sunan shi kuma yana dariya."
Tabbas ba iya k'anwarsa kad'ai ta tsayaba akwai wani Abu a tsakaninsu."
Idonta ya kuma yin ja wani sabon kishi taji ya taso mata hawaye na zuba a idonta tashiga fad'in "na rantse da Allah duk macce da tace zata rab'i mijina nayi alk'awarin sai na kasheta da hannuna."
Sallamar Aminiyarta tajiyo a bayanta da gudu ta tashi ta rungumota ta kuma fashewa da wani sabon kuka,
Lubcy ta sanya hannu tashiga share mata hawaye tana fad'in "daina kuka Yusra duk abinda yake faruwa nasani inajin lokacin da kike fad'awa daddy,
Dibeki dan Allah babu abinda kika rasa a duniya kina da kyau kina da kud'i, kina da ilimi,
akwai Alhazai yan gayu masuji da kud'i da k'uruciya wad'anda ke iya biyawa ko wacce irin macce buk'atarta, amma kinzo kin mak'alewa mahmud sai wulak'antaki yakeyi yana juyaki kamar sitiyarin mota."
Wai mekika gani a jikinsa ne kika wani mak'ale masa ne?"
Dan haka ni kika ganni kwata-kwata bana sha'awar aure a rayuwata saboda babu abinda ke cikin rayuwar aure sai bak'in ciki da tashin hankali."
Wani kallo yusra take bin lubcy dashi, duk cikin magagganunta babu Wanda tafi b'ata mata rai kamar metagani ajikin mahmud da tawani likemasa."
D'aga mata hannu tayi tace "Dakata lubcy bana son haka,akwai abinda nagani Kuwa a jikinsa Wanda ke bazaki ganeba."
Snn Kuma bana buk'atar mazan waje mijina nakeso shi kad'ai nakeso na mallaka domin shi nakeso a rayuwata akan komai daga ciki Kuwa har da kaina."
na d'auka zuwa kikayi kibani shawara ta yanda zan mallaki mijina.
a matsayinki na Aminiyata wacce na yarda da ita zuwa kikayi kibani shawara hanyar da zanbi mijina ya soni ya kuladani ya Kuma amince mun, ya yarda dani a kan cewa ni masoyiyarsa ce."
Lubcy taga b'acin rai k'arara a idon Yusra Wanda bata tab'a ganiba,
Tabbas Yusra tayi nisa bata jin kira, ta sauke ajiyar zuciya ta dafata tace "yi hak'uri Yusra na fahimceki, na fahimci yanda kikeji a kan mahmud, zan baki shawara ta yanda zaki mallaki Mahmud ya zama naki Cikin sauki batare da Kinsha wata wahala ba."
Sai a lokacin Yusra ta sauke ajiyar zuciya ta maida hankalinta gaba d'aya wurin lubcy."
Suna cikin sak'awa da kwancewa sukaji tafiyar mutum a bayansu,
Da sauri suka waiga suga mahmud ne ya shigo ko ta inda suke bai kallaba yayi tafiyarsa d'akinsa."
Lubcy ta bishi da ido tana kallonsa, tabbas mahmud namijine, namijin gaske Kuwa, mai razana 'yan maxa bare 'yan mata."
Murmushi Yusra tasaki da taga yanda jikin lubcy ke rawa dataga shigowar mahmud,
Dafata Yusra tayi tana dariya tace "kwantar da hankalinki lubcy ai baiji abinda muke cewa ba, kijirani nashiga wurinsa na fito sai muci gaba da maganarmu."
Lubcy ta zaro ido waje tare da mik'ewa tsaye ta d'auki jakarta da tallakaminta ta kalli Yusra tace "sauran bayani zan kiraki a waya muk'arasa, bata jira abinda Yusra zataceba tayi fice warta gidan."
Kallo Yusra tabita dashi tana murmushi duk rashin kunyar lubcy ganin Mahmud ya firgitata."
Juyawa tayi tanufi d'akin mahmud Wanda tayi sa'a bai sanya key ba,
Koda tashiga yana toilet yana wanka murmushi tayi ta zauna a gefen gadonsa,
Wayarsa ta gani a kan gado ya ajiye ta ta sanya hannu ta d'auka tashiga Gallery tana diba hotona,
Gabanta ne ya yanke ya fad'i da ta dinga ganin hotonan wata kyakkyawar yarinya tana murmushi, can kuma taga wani hoto Wanda sukayi tare da mahmud a motarsa ya d'an sunkuyo kusa da ita suna dariya gaba d'ayansu, aka d'auke hoton
Tashin hankali tashiga Wanda baya misaltuwa tadinga ganin hotonan da sauri da sauri kafin ya fito,
Wani hoto taci karo dashi na wata yarinya 'yar k'auye daga ganin hoton a k'auye aka d'auke shi,
Abin bai kuma d'aga mata hankaliba sai da taka mahmud ya goya yarinyar a bayansa suna dariya aka d'aukesu hoton."
Jawo hoton tayi ta k'urawa yarinyar ido "tabbas wnn itace a cikin hoton farko da tafara gani
"Wnn wacece?" Meye matsayinta a wurinsa?" Daga ganin wa'dan nan hoto nan sun nuna tana da mahimmaci a rayuwarsa, toko itace zab'insa wanda yakeso a ransa?"
Babu wacce ta fad'o mata a rai sai sunan dijama 'yar gidan tsohuwa, tabbas ita ce tashiga furtawa tareda mik'ewa tsaye, tana kallon hoto nan."
Kira ya shigo wayar taga ansayawa number sweet sister ta tabbatarwa kanta dijamar ce ta kira shi"
Sauri tayi ta d'auki wayar tare da karawa a kunnenta tana saurare."
Dijama tana jin an d'auki wayar tafara maganarta mai sanyi cikin shagwab'a "yaya shine kayi tafiyarka ko sallama bamuyi ba,
na ajiye maka wani Abu Wanda idan KA ganshi saikaji dad'i a ranka amma fitowar da zanyi tsohuwa take fad'amun kayi tafiyarka, ko wani abin naimaka pls kayi hakuri kaji yayana."
Dum gaban Yusra ya fad'i jikinta ya soma rawa saboda masifar kishi,
Dijama taji anyi shuru baiyi maganaba ta janye wayar a kunnenta ta kuma kallo ko ya kashe wayar ne,
taga ba kashewa yayi ba,
cikin siririyar murya tace network problum yaya kanajina?"
Yusra tace "karkiga laifin network yanajinki maganace kawai baya iyayi, saboda yana cikin wani sabon network mai wuyar misaltuwa Wanda duk Wanda ya haushi bayaji baya gani har sai lokacin da ya sauka."
Dan haka Wanda kike nema yana kan network baya da lokacin kowa har sai lokacin da ya sauka a kai,
Ta kashe wayar tare da tsurawa wayar ido sautin muryar dijama namata yawo a kai."
Wanda yayi dai dai da fitowar mahmud daga toilet d'aure da towel a jikinsa gaba d'aya gashin jikinsa ya kwanta a kan kyakkyawar farar fatarsa."
Ido ta k'ureshi dashi tana kallon kyakkyawan jikinsa tare da faffad'an k'irjinsa tana lasar baki saikace mayya."
Shi kuma kallon tsana yake mata tareda tambayar ubanme take masa a d'aki,
Idonsa ya d'ora akan wayarsa dake hannunta, zaro ido yayi 😳 alamar kin rainani yayi kanta."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)
*47*
Ya mik'a mata hannu yace "bani waya na."
Faffad'an k'irjinsa take kallo Wanda yacika da gashi a kwance kwanin ban sha'awa,
Wata kalar sha'awarsa ce ta dirar mata,
Tana matuk'ar son mahmud,
Mahmud yayi mata yana d'aya daga cikin kalar mazan da take so jarumai masu iya sarrafa macce kota ina."
Ganin ya nufota gadan-gadan tayi sauri ta tura wayar cikin bra d'inta,
Ko ba komai tasan dole ya sanya hannu a ciki ya d'auko wayarsa."
Mahmud yana ganin hakan ya gane manufarta, hannunsa ya d'aga ya kwad'a mata mari tare da mik'a mata hannunsa yace "bani wayana."
Zabura tayi a gigice tayi cikin jikinsa ta rungumesa tare da d'ora kanta akan k'irjinsa idonta yana zubar da hawaye tana fad'in "ina sonka Mahmud koda zaka kasheni."
Tsaye yayi yana kallonta cike da mamaki ta yanda take kuma tusa kanta a k'irjinsa."
Wani marin ya kuma tsinka mata tare da cireta daga jikinsa yayi jifa da ita a bakin k'ofa."
Wanda yasa tasaki wani kalar kuka mai sauti."
Ya nufeta gadan gadan ya mik'a mata hannu yace "bani wayata."
Jiki na rawa ta ciro wayar a cikin boos d'inta ta mik'a masa tana matsar hawaye."
Karb'a yayi tare da wurga mata wata kalar harara mai cike da tsana,
Yace "bana sonki Yusra bana son ganinki na tsaneki nakasasshiya marar tarbiya."
Tashi kifitarmun daga d'aki jarabbiya babu abinda zanyi da nakasasshin jikinki Wanda kike yiwa duniya talla kowa ya gama gani."
Tunkarota ya kuma yi, zai kuma dukanta
Tana ganin hakan tayi saurin mik'ewa tsaye da sauri ta bud'e k'ofa ta fita waje da gudu
tsaye tayi a bakin k'ofa tana kallonsa wata k'aunarsa takeji tana kuma ratsata, ta sanya hannunta ta shafe hawayen dake mata ambaliya a fuska tace "koda kasheni zakayi bazan gaji da furta maka ina sonka ba, Mahmud ina sonka kuma bazan daina sonka ba,
Nayi Alk'awari sai na mallakeka sai na nuna maka iyakata a gidan nan sai na mallaki abinda nake so daga gareka."
Sai na mallaki zuciyar KA da gangar jikinka ko ta tsiya kota bala'i kota girma kota arzik'i ka saurara KA gani."
Belt d'insa ya lalubo yayo kanta a guje tabar wurin ta nufi d'akinta."
Dogon tsaki yaja ya koma kan kado ya zauna tare da dafe kai🤦🏻♂ shi dai ya rasa yanda xaiyi da yusra."
Wayar sa ya d'auka domin ya kira Khalil akwai sak'on da yakeso ya fad'a masa."
Sunan dijama ya gani alamar takirashi,
minti talatin da suka wuce,
Fasa kiran khalil d'in yayi,
Ya danna number dijama
Yashiga kirata,
duk da dai itama haushinta yakeji yanzun ganin yakeyi harda had'in bakinta sulaiman ya tunkari Abba da zancen aurenta."
Kira uku yayi mata bata d'auka ba, ya
Girgiza kai yace "lallai yarinyar nan sainayi maganin rashin kunyarta."
Ya mik'e tsaye ya sanya kayansa ya nufi masallaci."
Dijama kuma tin lokacin da taji muryar Yusra tashiga cikin damuwa, da tinani
Me Yusra take nufi da yaya mahmud ya hau network d'in da bayajin Kowa a wnn lokacin?"
Tana nufin yana tare da ita a shinfid'a d'aya Kenan?"
Wato yana ganin kiranta kin d'auka yayi, sai dai yabawa matarsa wayar ta d'auka?"
Wato yafi son matarsa akan d'an uwansa, kenan?"
Wani hawayen bak'in ciki yashiga zubar mata, takai kwance rufda ciki tana kuka tana ganin kiran wayarsa yana shigowa a wayarta tak'i d'auka, saima ta kuma fashewa da wani sabon kuka mai sauti."
Wanda yajawo hankali mommy da tsohuwa dake zaune a Palo wuri d'aya."
Da sauri suka mik'e a tare suka nufi d'akin domin ganin lafiyarta."
Kwance suka tarar da ita rufda ciki tana ta faman kuka bata San da shigowar suba."
Mommy takira sunanta "Ummie meyake damunki?" Meyafaru kike kuka?"
A hankali ta mik'e zaune tana goge hawayen fuskarta, tsohowa ta mere baki tace "zancen gizo ai bai wuce na k'ok'i."
Maganar d'ayace wacce muka rasa mafita a kanta,
Tayi ta gumi tace "oh ni Hadiza zamani🤔 ya lalace yaran yanzun inbanda zurfin ciki babu abinda suka ajiye."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)
*48*
Tsohuwa ta kuma mere baki tace "Ke malama ki daina yimana kuka Addu'a ya kamata ki rink'ayi Allah ya yaye maku wnn zurfin cikin dake damunku,
Idan ba hakan ba ninasan mafita."
Ta juya ta fita."
Mommy tabi tsohuwa da kallo tana murmushi, snn ta mayar da kallonta a wurin dijama taje wurinta kan gado ta zauna a kusa da ita,
Tarik'a hannunta takira sunanta a hankali cikin sanyin murya tace "ummie meyake damunki fad'a mun damuwarki,
me kikeyiwa kuka?"
Rausayar da kai tayi cikin muryar tausayi tare da dafe kai🤦♀tace "bakomai mommy kaina ne ya keyi mun ciwo."
"Subahanallahi mommy tace " kinsha magani Kuwa?"
Girgiza kai tayi tace "A'a."
Mik'ewa tsaye mommy tayi cikin hanzari ta d'auko maganin ciwon kai tare da ruwa ta bata tasha."
Tace "Ki daina sanya damuwa a ranki kinsan kina da matsalar ciwon zuciya, ki sanyawa ranki duk abinda kikeso koda baki fad'a mana ba munsanshi kuma zamuyi maki shi kinji ko."
Ta d'aga kai alamar "to."
Snn ta dubi mommy cikin murya k'asa k'asa tace "mommy me tsohuwa take nufi da zurfin ciki mukeyi?" nida waye muke zurfin Cikin?"
Murmushi mommy tayi ta dafa kafad'arta tace "rabu da tsohuwa ummie kinsan halinta abin magana baya mata wuya, ki daina biyewa maganar tsohuwa."
Ki kwanta ki huta kafin fateema ta dawo daga inda na aiketa,
Snn mommy ta mik'e ta fita tareda rufo mata k'ofa."
*****************
Bayan Mahmud ya dawo daga masallaci, still wayar dijama yaketa faman kira tak'i ta d'auka, daga k'arshe sai ma ta kashe wayar gabaki d'aya."
Zaro ido yayi yarik'e. Baki yashiga maganar xuci "to me take nufi?"
Meyake faruwa ne?
Wanda yasa dijama bata d'aukar wayarsa?"
Wayar mommy ya shiga kira itama bata d'aukaba kiran sulaiman ya shigo wayarsa, ya katse masa kiran mommy da yakeyi,
Yana ganin sunan sulaiman a wayarsa yaji wani b'acin rai yazo masa ya harare wayar kamar sulaiman d'in yana ganinsa,
Snn ya d'auki kiran ya kara a kunnensa batare da yayi magana ba."
Dariya sulaiman ya saki yace "haba abokina Allah ya huce zuciyarka duk da bansan laifin da nayi maka ba kakejin zafina."
Mahmud yace "don Allah malam kayi sauri ka fad'i dalilin Kiran nawa a dai dai wnn lokacin saboda ina da abinyi."
Sulaiman yace "to sirikina tuba nakeyi, dama maganar d'aya dai ce ta k'anwarka kuma matata insha Allah,
Yaci gaba da cewa Yaya Mahmud kaina bisa wuya ina Neman izininka da KA amince a sanya mana ranar aurenmu tunda muna son junanmu tsakanina da ita."
Gaban mahmud ya yanke ya fad'i, ya d'an jingina a bango snn yace "wato kana nufin kun kammala komai rana kuke jira a sanya maku?"
Sulaima ya gintse dariyarsa jin muryar mahmud kamar cikin tashin hankali"
Yace "ai nasan kasan da hakan domin nasan Abba zai gaya maka."
Mu yanxun amince warka kawai muke nema abokina."
nasan a duniya babu abinda bazaka iya yimun ba, in har baifi k'arfinka ba."
Mahmud yayi saurin dakatar da maganarsa a fusace yace "banda wnn na rantse da Allah idan har sai na amince snn zaka auri dijama sai dai KA mutu da sonta."
Kai bari makaji dijama baxata aureka ba, nine Wanda zan aurar da dijama ga Wanda nakeso ga Wanda naga dama,
Sam baka cikin tsarin mazan da nake buk'ata dijama tayi rayuwar aure dasu."
Duk wani Abu naka da wasu kayanka wad'anda Abba da mommy suka karb'a gobe zanzo na mayar maka da abinka saboda ba Wanda yakeda hak'in ya zab'awa dijama Mijin aure sai ni, kuma ban zab'eka ba Dan baka d'aya daga cikin,
ya na kaiwa nan ya kashe wayarsa."
Zuciyarsa na tafarfasa ya rasa dalilin da yasa duk sulaiman yayi masa maganar aurensa da dijama jiyakeyi kamar ya had'iye xuciya,,saboda wani zafi da yakeji yana taso masa."
Cikin k'unar zuci ya nufi gida, ya fad'a d'akinsa kai tsaye a kan makeken gadonsa ya fad'a ya kwanta rigingin yana kallon silin tare da tunanin kala kala. Idonsa yayi ja kamar garwashin wuta, yashiga tinanin wato k'arya dijama take masa da tace bata kula kowa?"
Ashe soyayya takeyi da abokinsa har sun tsayar da maganar aure?" Yaushe dijama ta koyi k'arya?"
Wani dogon nishi yaja ya lalubo wayarsa ya danna number ogansu Wanda aka canxa masu."
Ringing biyu wayar tayi oga ya d'auka cike da girmamawa mahmud yake gaidashi tare da bashi girmansa,
Oga ya amsa yana fara'a domin yana matuk'ar son mahmud saboda gaskiyarsa."
Mahmud yashiga gabatar masa da uxirinsa yanaso ya bashi izini zaije kano yayi sati biyu."
Oga yace "mahmud kafi k'arfin komai a wurina, amma kayi hak'uri kabari sai k'arshen wata katafi domin cikin satin nan akwai aikin da zan turaku kuyi mai mahimmaci."
"To Mahmud yace yayi masa sallama ya kashe wayar tareda yin wurgi da wayar gefe d'aya,
Can kuma ko meya tuna yayi saurin mik'a hannunsa ya kuma d'aukar wayar ya shiga kiran number Abba."
Sulaiman kuma duk wayar da sukeyi da Mahmud Abba yana kusa yana saurarensu yana murmushin."
Abba yace Allah ya kaimu goben ai nasan kafin gobe zai kirani a waya."
Ai kuwa bai rufe bakiba sai ga kiran Mahmud ya shigo a wayar Abba,
Abba ya kalli sulaiman suka saki murmushi a tare snn Abba ya d'auki wayar tare da karawa a kunnensa.........."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)
*49*
Sallama mahmud yayiwa Abba cikin ladabi da girmamawa tare da gaidashi."
Abba ya amsa masa tare da tambayarsa ya aikinsa."
"Lafiya lau." yace snn ya d'an nisa yace "Abba naji wata magana a bakin Sulaiman gaskiya ne Kuwa?"
Abba ya kalli sulaiman sukayi murmushi a tare snn yace "wace magana gaji daga cik Kenan?" dan kuwa magagganun yawa garesu."
Gaban mahmud ya yanke ya fad'i yace "Abba wai cewa yayi kungama shirya komai ni kuke jira na amince a sanya ranar aurensa da dijama."
Abba yace "tsohon zance kenan, ai tuni na dad'e da Sanya ranar aurensu wata biyu masu zuwa,
Zan had'asu tare da fateema nayi masu aure na huta, tunda har sun samu wad'anda sukeso."
Zuciyar mahmud tashiga suya, cikin b'acin rai yace "Abba in har inada iko kuma and'aukeni a matsayi Wanda ya isa da dijama Wanda yakeda iko da ita kamar yanda kake cewa a lokacin baya."
Abba Ni dai ban amince dijama ta auri sulaiman ba sam."
Abba yace "saboda me?" Meye dalilinka?"
Shi sulaiman ba mutum bane?"
Shin wai ma tsaya mahmud idan kace baxata auri sulaiman ba kai zata aura?"
Gaban Mahmud ya fad'i.'
Ya rasa amsar da zaiba Abba."
Abba yaci gaba da cewa "ni baxanci gaba da ajiye yara a gabana ba ina kallonsu bayan ko wacce daga cikinsu ta isa aure."
Auren dijama da sulaiman ba fashi nan da wata biyu masu zuwa, ko kashirya ko baka shiryaba."
Abba bai jira amsar da Mahmud zai basaba yayi saurin kashe wayar yana kallon sulaiman suna murmushi,
Sulaiman yace "bantab'a ganin mutum mai zurfin ciki kamar mahmud ba."
Abba yace "Ayya kuwa zai fitar da abinda ke ransa Kuwa?"
Sulaiman yace "xai fitar Abba kabani lokaci ka gani."
Dijama na fitowa taji Abba yana waya da wani yana fad'a masa aurenta da sulaiman nan da wata biyu masu zuwa."
Da baya baya ta koma tana ganin jiri ta fad'a d'akinsu tana sauke numfashi sama sama kamar wacce tayi gudu,
Tunani tashigayi aurenta saura sati biyu?" Kuma da sulaiman?" abokin yaya mahmud?"
Hawaye suka shiga zuba a idonta tana fad'in "ita bata son sulaiman bata tab'a sanyashi a cikin jeren maxan da take so ba."
To ita idan ta auri sulaiman ya zatayi da Anty Fareeda matar da ta d'auketa tamkar k'anwarta ta nuna mata so, babu abinda bata iya mallaka mata a rayuwa
Amma a wayi gari saboda butulci itace Zata auri mijinta."
Sam bazai yiwoba wlh bata son sulaiman bata iya aurinsa."
"To wa kikeso wazaki aure?" Zuciyata ta bata amsar maganrta."
Yaya Mahmud ya fad'o mata a rai ta kai kwance ta saki kuka mai sauti."
Da tuna da kalaman Yusra a lokacin da takira wayarsa."
Shima mahmud ya kasa tsaye ya kasa zaune sai safa da marya yakeyi a tsakar d'aki yana girgiza kai, jinsa yakeyi kamar yayi tsuntsuwa ya dura garin kano,
Amma ina ogo ya hana."
A daren ranar baiyi bacci ba sai sak'awa yakeyi da kwancewa."
Amma muddun yana raye dijama bazata tab'a auren sulaiman ba."
Tambayar Abba ta fad'o masa a rai "kai xaka Aure tane?"
Da fe kai yayi yace "sai dai inje in d'aukota,
Ba wanda ya sani indawo da ita wurina."
*****************
Khalil kuma tun a wurin bikinsu dijama Abba bai kuma sanyashi a idoba yau kwana biyu kenan."
Kwata kwata ya daina kwana a gida hankalin Abba ya tashi yashiga tambayar mommy lafiya Kuwa Khalil yake?"
Mommy tayi murmushi domin tasan halin Khalil sarai, tace "lafiyarsa k'alau kakira wayarsa kaji."
Abba yashiga kiran wayar Khalil dake can kwace tareda budurwasa Ashanty suna holewarsu, dai dai lokacin da ya haye kanta kiran Abba ya shigo wyarsa."
Yana kanta ya mik'a hannu ya d'auki wayar tare da saita natsuwarsa, yayi sallama tare da gaida Abba."
Abba ya amsa yashiga tambayarsa "khalil lafiya k'alau kake kwana biyu baka zo gida ba?"
A ina kake kwana?" Ina kake cin abinci?" Abba yashiga yi masa fad'a kasan bana son shashancin bazan, nawa kake kwata kwata shekarar KA nawa da har zakaje wani wurin ka kwana batare da ka sanar da muba."
Khalil da bakinsa ke cikin bakin Ashanty yana tsotsa hannunsa d'aya yana rik'e da boobs d'inta yana shafa kan yana wasa dashi,
D'aya hannunsa ne yake rik'e da wayar Abba yana saurarensa."
Bakinsa ya cire daga cikin bakinta, dayaji Abba yayi shuru alamar ya gama fad'an kenan."
Yace "Abba kayi hak'uri bawani wajen natafiba ina makaranta jarabawa mukeyi karatu mukeyi sosai da zarar mun kammala zandawo gida Abba KA kwantar da halinka."
Abba yaji dad'i sosai yyi murmushi yayi masa Addu'a Allah yabada sa'a. Ya kashe wayarsa."
Mommy najin yanayin maganar khalil ta fahimci halin da yake ciki sai dai kawai ta girgixa kai tace "Allah ya shirya."
Abba yayi saurin juyowa ya kalli mommy yace "wai meyasa baki yiwa yaron nan kyakkyawar fahimta ne sai na dinga ganin a koda yaushe kina masa kallon rashin yarda nifa bana son haka."
"Yi hak'uri mommy tacewa Abba, fahimta nace har yanzun bakayi ba a kan khalil."
Kuma ai ni yanzun Addu'a ce nayi, masa nace "Allah ya shirya."
"Ameen Abba yace tare da mik'ewa a fusace yayi shigewarsa d'aki."
Kallo mommy tabishi da shi tayi murmushi itama tamik'e ta bishi domin ta lallashesa."
Khalil najin Abba ya tsinke wayar."
Ya saki murmushinsa na yan duniya,
Ya kashe wayar gaba d'aya dan kadda a kuma nemansa yayi jifa da ita gefe d'aya, yaci gaba rabawa Ashanty aiki ba sauk'i."
Saida suka d'auki lokaci mai tsayi suna Abu d'aya snn ya saurara mata koshi ba wai dan yagaji ba sai dai gani da yayi ta bashi tausayi tagaji sosai, Dan baya son yana hutawa da macce d'aya, yafison ya had'asu su biyu ko ukku idan wnn tagaji sai ya juya wurin wnn"
Bayan sunfito daga wanka yana shafa mata mai a jiki, yana kuma k'ara shanshafa, yana matuk'ar son ashanty duk a cikin 'yan matansa ya fisonta a kan kowa saboda tafi gamsar da shi, Kuma ya shaida shi ya fara bud'eta a leda."
Shafata yakeyi tana lumshe idon jin dad'i,
har zuwa wurin k'ugunta zuwa saman cikinta, jiyayi cikinta yayi masa k'arfi ba kamar da ba dayake wasa da cibiyarta a kan taushin cikinta da laushinsa."
Kuma kallon cikinta yayi yaga yad'an taso kamar macce mai ciki."
Hannunsa ya Sanya ya d'an latsa cikin ai Kuwa yajisa da k'arfi ya zira hannunsa a cibiyarta yana wasa da ita kamar yanda ya saba, wani gantsewa tayi saboda zafin da taji cibiyarta nayi mata taja da baya."
Kallo ya bita da shi tabbas Ashanty ciki gareta, sai yanzun ya lura da yanda cikinta ya girma ya fito."
Kallonta yayi da kyau yakira sunanta yace "Aisha watanki nawa bakiyi period ba?"
Murmushi tayi cikin shagwab'a da sakuwa tace "wata bakwai honey."
Wani tabbulan yayi ya fad'o daga kan kujerar jikin madubi
saboda razana da tsoro."
Zaro ido yayi yana kallonsa yace "bakida hankali ne? Kin Kuwa san abinda kike fad'a?"
Turo baki tayi tace "meyafaru honey?"
"OK baki masan abinda yake faruwaba saboda kina dak'ik'iya kidahuma marar hankali so kikeyi kitonamin asiri."
"Nifa bansan abinda kake magana a kansaba kuma ni kadaina kirana dak'ik'iya."
Mik'ewa tsaye yayi zufa na zubo .masa duk da sanyin ac dake d'akin
ya kuma kallonta yace "yo ai har k'ara dak'ik'iyar dake, kina d'auke da ciki harna tsawon wata bakwai baki saniba."
[8/16, 9:12 PM] Mariam Tijjjani Adam: 🌹 *DEEJAMAH* 🌹 ( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Writteng by
*UMMU SAFWAN*
(Fareeda Basheer)
*50*
Murmushi tayi tace "nasani mana sai dai idan kaine baka saniba,
To meye abin d'aga hankali honey dan ina d'auke da cikinka na wata bakwai?"
"Ai ni duk a tunanina idan kasani murna zakayi da farin ciki ka kusan zama Baba zamu haifi d'an so."
Bai san lokacin da ya wanke mata fuska da mariba yace "bakida hankali d'an shege zaki kira da d'an so?' Aisha ashe baki da hankali bakida tunani, so kike ki tonamin asiri a idon duniya."
Da wani ido kikeso na kalli mahaifina Wanda yafi Kowa yarda da dani, ya Amince min d'ari bisa d'ari."
Gabanta ya kai gurfane ya ruk'o hannunta yashiga bata hak'iri
"Pls Aisha ki amince min mutafi asibity a zubar da cikin nan nayi maki alk'awarin bayan an zubar da shi zan aureki."
Kallon cikin idonsa ta shigayi ta kuma tabbatar da cewa da gaske yakeyi,
Tunawa tayi da wata k'awarta suwaiba itama a wurin zubar da cikin tarasa ranta."
Tasan halin Khalil sarai idan tayi masa musu yana iya sanyawa a zubar da cikin kota tsiya kota arziki don ba mutumci garesa ba,
sai dai ita ta rasa ranta."
D'aga masa kai tayi alamar ta amince a zubar da cikin."
Murmushin jin dad'i yayi yace "yanzun ki tashi mutafi asibity nayiwa likita bayani.'
Shafa gefen fuskarsa tayi cikin wani salo na bariki tace "lah honey ai ba sai munje asibity ba,
Bara na koma gida akwai wata k'awata Wanda ta kware sosai a Wnn harkar sai ta fad'a min maganin da zan sha wadda cikin zai zube cikin sauk'i batare da nasha wata wahala ba."
Murmushin jin dad'i yayi yace "gud kinkawo shawara mai kyau,
Yaciro kud'i cikin wata loka dubu d'ari ya mik'a mata yace "idan kina buk'atar wani abin kiyimun magana zankawo maki."
Amsa tayi tana godiya snn ta mik'e tsaye ta sanya kayanta tayi masa sallama ta fita."
Bayan ta fita ya bita da kallo yana dariyar mugunta "ubanwaye zai aureki?"
Allah ya tsareni dana aure macce wacce nagama kwashe rabona akan hanya na kai ta gidana,
da wacce tarbiya zata reni'ya'yana."
Ya saki dariya mugunta yabita da harara kamar tana ganinsa yace "sakarai na dai samu cikin yafita a jikinki,
na barki kuma har abada tunda naga alamar ko zariyar wando ta rab'eki sai kin d'auki ciki."
Itama Ashanty tana fita,
Ta sanya kud'in a jaka tace "baka da hankali khalil kana nufin inje wurin zubar da cikin in mutu kenan, Sam bazan iyaba nafison na barshi duk wata wahala da tsangwama da zansha a gida na yarda kuma na Amince indai har zan tsira da rayuwata da abinda na haifa."
***************
Alhaji Atiku duniya ta juya masa baya yanaji yana gani abinda yafi k'arfinsa a da a yanxun nemansa yakeyi,
'yan mata abokanan holewarsa duk sunja baya garesa dama mafi yawan Matan da yake ma'amala dasu,
Dukansu wasu daga cikiñsu matan yaransa ne,
Wasunsu kuma Matan da suke k'arshinsa ne a wurin aikinsa, yanzun kuma duk sunja baya basa kulashi dama kulashin da sukeyi na dolene saboda suna son aikinsu dan kadda ya koresu."
Juya masa baya da 'yan mata .sukayi
abin yana damunsa ya k'ara sanyashi shiga cikin damuwa."
Zaune yake yana nazarin irin matan da yake ma'amala dasu a rana d'aya amma yanzun ba ko d'aya dukansu sun gujesa."
yau kam ya yanke shawarar zai fita da kansa yaje gidan mata ya nemo wasu sabbin babys wad'anda suka kware a harka."
Hakan Kuwa akayi bayan sallar Isha'i yayi kwalliya cikin manyan kaya kamar wanda zaije wurin d'aurin aure ya fita, kai tsaye ya nufi gidan mata.'
Gidan mata gidane da yayi suna a cikin garin Abuja duk wani shegen namiji mai kud'i ko milki ko wani muk'ami idan yna da buk'atar macce a nan yake zuwa ya zab'i babys wad'anda yakeso masu zafi,
Gasu nan. A azube saika zab'a wacce tayi maka iya kud'inka iya shagalinka barikinka Aljihunka."
Alhaji Atiku yana shiga wurin ido yayi kansa,
mata suna ganin sa,
sai girgiza sukeyi ta d'aukar hankali domin su burgeshi mafi yawansu dagà ciki duk k'awayen Yusra ne, kuma sunsan shi mahaifinta ne,
Amma da yake bariki ce basu damu da hakan ba."
ai kuwa bai kauda idonsa daga gare suba,
abin nema yasamu sai wasar baki yakeyi yana k'arewa ko waccensu kallo, snn ya shiga zab'ar manyan mata guda biyu masu ji da kansu wad'anda komai yaji garesu ya kama d'aki a cikin gidan suka shiga holewarsu."
***************
Mahmud aiki sukeyi gadan gadan, sun samu labarin akwai wani gidan mata da aka bude manya mutane suna zuwa wurin babu abinda ba'ayi a wurin."
Ogansu ya sanya ayi masa bincikin wurin a gano iya abubuwan da akeyi a wurin kafin sufara kame."
amma duk aikin da yakeyi baya cikin kwanciyar hankali idan ya tuna auren sulaiman da dijama Allah Allah yakeyi wata ya k'are lokacin da ogo ya d'ibar masa ya dira garin kano,
Abu d'aya zaiyi shine ya sace dijama ya bar garin da ita yadawo da ita gabansa yaga Wanda zai d'aura mata aure da wani sulaiman can"
****************
Tun ranar da Yusra taci duka a wurin mahmud ta farajin tsoronsa, ta zubar da makaman yak'inta domin ta fahimci mahmud ba irin mazan da ake tilassamawa bane akan dole sai ya so wani abin."
Zama tayi,
tayi naxarin abinda mahmud yakeso a jikin macce meyakeso a rayuwarsa."
Pic d'in dijama ya fad'o mata a rai, gaba d'ayansu ba Wanda take sanye da k'ananun kaya dukansu manyan kayane atamfa da lesi wani harda hijabi."
hakan ta d'aukar wa kanta zata fara shigar manyan kaya indai yin hakan zai sanya mahmud ya sota."
Cikin kwana biyu ta dage da shiga kala kala ta manyan kaya wani lokacin harda hijabi take had'awa."
Duk lokacin da ta kwatanci ya Kusan dawowa gida zata shinfid'a darduma ta dinga Jan carbi" saboda tasan mahmud mutum ne mai son ibada."
duk da dai bata San abinda ake fad'aba idan ana Jan carbin ba."
sai
dai kawai ta dinga motsi da baki."
Amma mahmud ko a jikinsa ko kallo bata ishesaba, wani lokacin idan ya dawo yasameta a hakan yana mmkin canjin da tayi matuk'a sai dai fa bai yarda wai da gaske ta canzaba,
Ita kuma ta dage sai ta sashi ya yarda ta canza ta koma kalar matan da yake so."
Duk wani kalar wulak'anci da yake mata,
Bata tab'a nuna masa ranta ya b'aci ba,
sai dai ta bashi hak'uri cikin k'ask'antar da kai,
a duk lokacin da yake Gida zata dinga yawo da hijabi da carbi a hannunta da zarar ankira sallah zatayi sauri tayi arwala ta haye kan darduma ta dinga jera salloli ba adadi."
ganin baya kulata, duk wata dabara tata da hikima ta k'are,
Ta kan zauna ta kalli madubi ta kalli kanta da kanta ta kuma kallon halittar jikinta ko macce 'yar uwarta idan ta ganta saita kyasa bare mahmud saikace ba namiji ba?"
To shi wani irin mutum ne?"
Kuma lafiyar sa k'alau bashida ko nakasa?"
ko ko tsabar miskilanci ne da jin kai yanuna mata shi namijin gaske ne yana iya controlling sha'awar sa?"
Abin takaici kullum kamar ana k'ara hura mata wutar soyayyar sa da tsananin sha'awarsa a zuciyarta."
Mahmud yana da Duk wani abinda za'a so shi,
Tun daga kan halayyar sa har halittar da Allah yayi masa,
Duk macce da ta mallaki irin mahmud kallonshi kad'ai intayi ya isheta farin ciki da godewa Allah wnn kad'ai ya isheta."
Yusra tana bak'in cikin rashin mallakar mahmud gashi dai mijinta ne sunyi auren amma ya mata nisa yafi k'arfinta duk da kuwa kyaunta kud'inta ilminta maccen da maza ke rububin samun irinsu, amma Mahmud ko kallo bata ishesaba
Yusra dai ta zama macce mai yawan ibada ga kyauta da sadaka duk wnn tanayinsa ne idan mahmud yana gida domin taja ra'ayinsa,
Tafara samun nasararsa domin ta fara gani a fuskarsa ya rage jin zafinta,
Tinda yanzun yana zama a palo yaci abinci Wanda yake sayowa duk safiyar Allah."
Wani dare mahmud ya fito falo zai shiga kicin shan ruwa kamar yanda Al'adarsa take duk daren Allah. Mutum ne shi mai yawan shan ruwa."
Karo yaci da Yusra a kwance a falo kan sallaya sai rawar sanyi takeyi,
Zazzab'i ne ya rufeta."
Ta gefenta ya rab'a ya wuce yashiga kitchen ya sha ruwansa ya fito,
Har zai rab'a ta ya wuce ya kuma dawo domin yaga tana kan ibada ciwo ya sameta bari ya tausaya mata."
Sunanta ya shiga kira "Yusra meyafaru?" Bakida lafiya ne?"
Meke damunki?"
Ya sunkuya yana tambayarta tareda rik'ota ya mik'ar da ita tsaye,
mahmud akwaishi da tausayin mara lafiya."
Tayi saurin k'ank'ameshi "mahmud sanyi lullub'eni zazzab'i ciwon kai."
Mahmud karka gyaleni, karka tafi ka barni."
nan ta dinga cusawa jikinsa tana sauke mai numfashi a fuska da kunnensa cikin salo mai ta da hankali,
Biye mata yayi ya dinga mannata da jikinsa sosai yana goga jikinsa a nata."
Tuni suka fita hayyacinsu duka , Yusra ta gama shigewa jikinsa tare da tsananin murnar yau zata samu nasarar abinda ta dad'e tana nema."
tallabarta yayi cak ya nufi kan kado da ita,
Yashiga sarrafata a hankali cikin kwarewa da gwaninta."
Wani nishi take fitarwa harda 'yar kuwar jin dad'i."
Mahmud ya zura mata ido tare da murmushin mugunta yana k'ara tsumata, sai faman sauke numfashi takeyi gaba d'aya ta cire kayan jikinta, ta rarumoshi idonta a rufe ta fara cire masa botes d'in rigarsa,
Ta tsuma iya tsumuwa mahmud yakai k'ololuwar tayar mata da sha'awa."
Yana ganin ta cire masa riga tana neman zuwa a kan wandonsa ya d'auko wani kyalle ya shak'a mata a hanci cikin minti d'aya bacci mai nauyin gske ya d'auketa."
Ya kalleta yayi
murmushin mugunta yace "Yusra da sauranki ki yaudari Mahmud."
Zan nuna mki a duniya ba komai ake nema a samu ba har Abada bazaki tab'a samun mahmud ba."
Ya maida rigarsa ya sanya ya sauka daga kan gadon yayi Arwala ya nufi masallaci domin gabatar da sallar asuba."
Bayan ya dawo daga masallaci ya d'auki Yusra ya kaita d'akinta ya kwantar da ita bisa gadonta Tare da mata shiri tsab irin na marasa lafiya ya fita ya gyaleta a wurin yatafi wurin exeercise d'insa da yake kullum bayan ya kammala sallar asuba."
Bayan ya gama yayi wanka ya shirya tsab cikin uniform d'insa na soja Wanda yayi matuk'ar yimasa kyau ya dace da hallittarsa da fatarsa, mahmud mutum ne mai kwarjini da farin jini ga al'umma,
Haka nan kawai mutane ke sonshi koda kuwa baka sanshiba kallo d'aya zaka yimasa kaji ya burgeka kana k'aunarshi."
Wayarsa ya d'auka yakira Alhaji Atiku yace "Yusra ba lafiya basuyi bacci ba Daren jiya."
0 comments:
Post a Comment