Yauma tana kwance saman carpet ta kanta bisa pillow kwanciyar rub ciki tayi saboda yadda take jin kan nata kamar zai tarwatse doguwar rigar bacci ce a jikinta iya gwiwa,gashin ta yayi dai dai kan pillow din,idanunta runtse suke ciki n haka ta jiyo sallamarsa,ta kadu sosai wanda hakan ya sake haifar mata da wani ciwon ko motsi ta kasa yi bare tayi yunqurin barin falon,tana jinsa har ya qaraso kanta yana sake maimaita sallamarsa,sai dai dif ta kasa amsawa sai wani bari da jikinta yake yi,yasa qafarsa ya dan bigi gefan pillow din da take kai ga zatonsa bacci take saidai nan ma yaji shiru,hakanne ya danso taba tunaninsa,ya sunkuya a hankali yasa hannayensa biyu ya birkitota gaba daya ta dawo rigingine fuskarta cikin tasa saidai idanunta na runtse don wani tsoron ne ya sake mameyeta,hawaye ya gani sharkaf a fuskarta ga wani dan banzan zafi da jikinta ya yi har haqoranta sun fara haduwa da juna"subhanallah😳"aliyu ya fada,surarta gaba daya ta bayyana har baisan sanda ya fadi hakan ba kyakkyawan gashinta ya sauko ya rufe fiye da rabin fuskarta,sai kuma yadda jikinta yayi zafi da yawa da yadda idanunta suka tasa,ya sunkuceta kamar wanda ya dauki tsinken sakace yana laluben bedroom dinta
Saman gadonta ya ajjiyeta ya zuba hannayensa cikin aljihun wadonsa yana kallonta ya rasa mai ya kamata ya yi mata wane taimako ya kamata ya fara bata,don da gaske tanajin jiki rashin lpyr na damunta,a hankali ya bude labbansa yace"relieve ur self and stop d crying "sai da ya kwashi kusan minti biyar sannan yace"already dama baki da lpy?"ta gyada kai ya sake tambaya"meke damunki?"ta nuna masa kanta,bai sake cewa komai ba ya shiga toilet dinta ya hada mata ruwan wanka mai dumi a bathtub sannan ya fito "kishiga ki shirya kanki likita zata zo"daga haka ya fice,ta daddafa bango ta shiga toilet din ta sabe jikinta ta dawo ta saka doguwar riga ta atamfa mai dogon hannu ta fesa body spray ta hade kanta da band qarami ba tare da ta taje shi ba ta koma ta kwanta,bata dade da kwanciya ba taji ana knocking aliyu ne ya tura ya shigo bai dubeta ba taji yana bada umarnin a shigo
Likitace sanye da kayan aiki,aliyu dama bai lamunci hurda da likita namiji ba akan matsalar iyalinsa tun usuli tun maman iftihal doctor sa'adah itace family doctor dinsa ta qware sosai akan aikinta tasan me take tamakar mayya haka take akan cuta da maganinta,da sallama ta shigo farar macace dirarriya wadda aqalla shekarunta ba zasu haura talatin da biyar zuwa arba'in ba doctor sa'adatu akwai ta da fara'a don.mawuyacine kaga fuskarta babu murmushi yanzun ma da fara'ar a fuskarta suka gaisa da fadila tana mata sannu yayin da Aliyu ya jawo dresaing chair dinta ya zauna hadi da zaro wayarsa ya soma danne danne,doctor sa'adah ta ajjiye kayan aikinta a gefan gadon ta fara fito da su tana tsokanar fadila"Allah dai yasa qaruwa muka samu madam😃"kunya ta kama fadila don a haife doctor ta haifeta,ta dan saci kallonsa sai ta ga ma sam hankalinsa bai kansu
Cikin qwarewa ta soma aikinta tana gwaje gwajen tana hada mata da tambayoyi,tambayoyinta har suka so rikita fadila domin tamakar doctor na son karanto zuciyarta ne ,fadila tayi ajiyar zuciya lkcn da doctor ta tsagaita da tambayoyin ta zauna a gefan gado yadda zata iya fuskantar aliyun sosai tace"gsky a.s maitama damuwa ce fal a zuciyar madam wadda itace musabbabin wannan ciwon nata wanda Allah ya gani da ace tana fa qaramin ciki da tuni tayi miscarriage dinsa,aliyu ya maida wayar sannan ya kalli😒sa'adatu ba tare da yace komai ba tasan bazaiyi maganar ba don ba komai yake bada amsarsa ba saboda haka sai kawai ta dora da bayaninta"ya kamata ka binciki abinda ya sanyata damuwa mai yawa haka,ya dauke idanunsa daga kan likita yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yace"doctor iya sanina bata da wata matsala amma gaki gata ai u can ask her"ya dago kyawawan idanunsa masu tafiya da zuciyoyin miliyoyin 'yammata ya zubesu fes bisa fuskar fadila,tayi gaggawar yin qasa da kanta don kada tana fama da kanta ya baro mata wani aikin,tasan cewar a yadda take jinta dinnan matuqar ta yadda suka hada idanu to la shakka qaryarta ta qare domin daga shi har sa'adah ba zasu sja wahalar gano mai ke dawainiya da zuciyarta ba"meye damuwarki?,ya furta cikin dakakkiyar murya ba tare da ya dauke idonsa a kanta ba ,da zata iya ba shakka da tace masa kaine!,kishinka da qaunarka aliyyu sune damuwata!!!,sai fainkash ko kusa bata jin zata iya,abinda take jin zata iya kuma ahi yafi dacewar tayi din shine shiru kuma shi tayi din
Shiru din kuwa ya ratsa dakin doctor sa'adah tace"mai tama ba haka ake ba,it can be d screat ne she dnt wanna share it with another person so ka bari idan na tafi ta gaya ma a nutse"ta qarasa maganar tana yago pepper daga memonta mai tambarin asibitinta a jiki ta soma rubutu bayan ta kammala ta ajjiye takardar kusa da fadila da har yau kanta ke sunkuye tace"to madam Allah ya qara sauqi but pls kiyi qoqarin rage damuwa"kai ta daga ta mata godiya,sa'adah ta kalli aliyyu tace ga magungunan da za'a siya mata a nemo.yanzu ta soma sha zata samu relief insha Allah amma ta dan ci wani abu before ta sha din,ta miqe tana hada kayanta tqna musu salllama aliyu yace"thanks sa'adah a gaida yara
Mrs muhammad ce
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
▶1⃣7⃣
Fitarta da yan mintina aliyu ya dauki pepper din maganin ya fice ba tare daya ce mata kanzil ba,shima ba dadewa da fitar tasa wayarta dake qarqashin pillow ta dau tsuwwa alamun shigowar kira,a kasalance ta daga wayar tana duba mai kiran sister farida ce ta daga hadi da yin sallama farida tayi dan jim sannan tace sister ya naji muryarki ta canza ne?fadila cikin muryar marasa loy ta masa mata wlh bani da lpy ne farida ya gida ya kuma mubarak?cikin yar qaramar dariya farida tace duk muna lpy sister ko ta samu ne?,samuwa kamarbyaya? Ta tambayeta,farida tayi qasa da murya tace ian nufin fa juna biyu,ta dan basar tace abinda kika bugo ki tambaya kenan?,a'ah anty dama ina ceqa ne gibe ki duba haya ina nan zuwa harda result dinki tun last week ya samu,duk da bata jin da lafiya hakan ya mata dadi sosai har ta nuna zumudi,jin bata da lpy yasa farida qyaleta akan sai tazo goben,ta amsa don dama kantabhar ya soma sarawa ta maida kanta saman pillow ta kwantar tana addu'ar Allah yasa ta samu damar aiki
Ya shigo hannayensa biyu riqe da ledoji ya shigo ya zubesu kan bedside ya maida hannayanaa aljihu kamar kullum,ji tayi kamar ya cika mata dakin wani kwarjininsa ya cika mata gu jikinta yayi sanyi tanajin kamar ko hannuta ba zata iya dagawa ba ta shiga satar kallinsa duk fa batayi niyyar yin hakan ba zuciyarta ce ta tursasata kansa na qasa ne yana kallon carfet kamar mai nazari,sai ya mata kyau sosai fuskarana fes kama ganinta kasan tasan hutu tabbas maza irin aliyu sai ka tara dari zaka samu biyu cikinsu ga tsawo da qaqqarfan gangar jiki mai murdadden damtse mai cike da qarfi faffadan qirji mai cike gargasa wadda ta bayyana har hannayensa yana da jiki amma ba zaka kirashi mai qiba ba domin tsawonsa ya shanye ta,kusan ko yaushe fuskarsa a haka take ba fara'a sam don ita a iya saninta da shi bata taba ganin haqoransa ba,
Saura qiris ya kamata tana satar kallonsa tayi gaggawar janye idanunta daga kanshi a hankali taji yace dazun na tambayeki meye damuwarmk yanzun ma na maimaita karo na biyu"shiru ta sake yi.masa hakan yasa ya kausasa.murya yana sake tambayarta,cikin cool voice dinta tace babu komai,ya dago kamar zai kalleta sai kuma ya lumshe ido ya budesu kan.ledojin da ya shigo da su sannan yace idan tashin hankalinki da damuwarki sun ta'allaqa ne kema kan dawowar maman iftihal to kiyi saurin taimakawa kanki ki nemi sassuci a gun zuciyar ki don zata dawo ne amatsayin mata ta karo na biyu ba wata baquwa bace......sannan ki bawa zuciyar dai taki again shawara da kada ta cika kanta da damuwoyi masu yawa tun yanzun......ya danja fasali sanna ya miqa hannunsa ga wayarta dake gefanta abinka da giant tuni hannun yakai ba tare da ya hau gadon ba ya lallatsa sannan ya ajjiye mata yace"ga abinci nan da magunguna ki sha,then ga number ta if there is any problem contact me"daga haka ya juya ya fita ba tare da Saura ron komai ba
Sai abun ya zamewa fadila wani iri ta jima akwancen kafin ta samu damar miqewa zuciyarta na qarfafa mata gwiwa ta tashi ta taimaki kan nata kamar yadda aliyu ya shawarceta,tq shiga toilet tayi fitsari sannan ta daura alwala wai ko zata ji sauqin zugin dq zuciyarta ke mata,ta dawo bakin gadon ta bude ledojin daya magunguna ne a ciki daya kuma gasashshiya,ta dinga zare tsokar tana ci zuciyar ta dauke da addu'o'in samun sauqin daga quncin zuciya(inda Allah ya taimaki fadila kenan bata mantawa da add'a duk irin situation din da take ciki,muyi koyi da ita yan uwa domin hatta qaddara babu abinda yake tareta sai add'u'a,mu dinga tuna Allah a yayin da muke cikin jin dadi da walwala sai Allah ya tuna da mu lokacin da mu kuma muke cikin qunci da neman taimakonsa wannan fadar annabi ce s.a.w,kai ta addu'a da sannu Allah zai isar maka,take note pls!)jin naman take kamar magani mai daci haka taci gabada dannashi har tqji kamar zata yi amai,ta balli.maganin adadin yadda aka rubuta tasha sanna ta dan zauna na mintina don abincin ya fada mata sanna ta ja pillow ta kwanta,cikin ikon Allah ta dinga jin sassuci a zuciyarta,ta jawo wayarta sai taji tana qamshin aliyu ta soma duba contact dinta taga number din da yace yasa mata ai kuwa a rukunin A taci karo da sunansa full name dinsa ya saka mata ta bude numbers din tana qare musu kallo suma special ne don cikin taqaitattun daqiqu zaka iya haddacesu,(mrs muhammad nace ko na sato muku numbers din A.s maitama ne cikin wayar fadilan?to gasu 0803344.......😜😜 to naqi don naga wata har tana saurin kwafa ba ruwana ku da fadila😜)ta zuba musu ido kamar tana son ganin fuskar mamallakin numbobin da ta gaji da kanta ta rufe wayar ta maida ta qarqashin filon ta lumshe idonta tana maida numfashi cikin zuciyarta ta soma tilawar suratu yusuf tana yi tana bin labarin annabi yusuf din da Allah s.w.a ke bayarwa cikin surar,zuciyarta ta mata sanyi damuwarta ta ragu sosai lallai Allah yayi gaskiya da yace(ala bi zikrillahi tadma'innal qulub/ku saurara da ambaton Allah ne kadai☝🏼 zukata ke samun nutsuwa)
To fa makaranta na labari yanzu muka soma shigarsa kuci gaba da jumurin bina insha Allah zamu cimma gaci😊
Dumbin godiyata a gareku
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻........
[10/16, 12:35 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣8⃣
Washegari misalin sha biyu na rana tana kitchen tana tafasa ruwan lipton so take ta dan sha ko zai warware mata ciki don tun tashinta yau ba abinda ta iya ci,muryar farida taji tana qwali mata kira da gudu ta fito suka rungume juna suna dariyar farincikin ganin juna😄,farida ta dan janye fadila daga jikinta tana cewa sister yi a hankali kada ki mana asarar baby,fadila ta ballamata harara tace"wai ke wa ya baki wannan labarin qanzon kuregen?farida tace bayan mun gama waya jiya da ke da daddare rabi'ah ta kira ni take gayan again,fadila na qoqarin komawa kitchen din tace uhm sai ki zauna ai kiyi ta jiran cikin,farida tayi dariya ta bita,maimakon daba lipton sai ruwan zafin ya koma na girki,suna yi suna casar hira,suka kammala suka zuzzzuba su a warmers suka wanke kwanukan hadi da gyara kitchen din
Wash! Inji farida bayan ta zauna fadila ta kalleta tace kin canza sister fa sosai kinga qibar da kika fara yi?farida tayi murmushi tace ke dai bari ya fadila ina tsammanin ciki ne fa?,fuskarta cike da fara'a 😄tace ke dan Allah,tace wlh da jibi ko gobe mubarak ya matsa sai naje an min test wai kada na jawo masa asara cikin rashin sani ni sai naga kamar ba shi ba,kasala kawai fa nake da yawan bacci,fadila tace,a'ah nima fa ina bayan mubarak sister kije a dubakin meye amfanin zaman haka,kina likita ai kinfi kowa sanin alfanun abin,tace insha Allahu gobe zamu je
Farida ta janyo jakarta ta bude ta miqawa fadila takardunta,cikin zumudi ta buda tana duba result din ba abinda bakinta ke fada sai alhamdulillah,domin kuwa yayi kyau fiye da yadda ta tsammata cikin farinciki tace da farida"burina na gaba farida inga na soma aikin media shine burina tun ina qarama"murmushi ta sakar mata tace"kwantar da hankalinki ya ahmad yana can yana miki wannan aikin don kuwa freedom da express tuni sun karbi takardunki jira yake kawai yaji daga garesu,wani farincikin da qaunar yan uwanta ya sake kamata
Tana toilet tana wanka ta bar farida a afalo tana kallin arewa 24 suna haska maimaicin shirin boyle bitmesin wato kyautata rayuwa da yake jiya tace tayi missing bacci ya dauketa bata kalla ba,ta jiyo hayaniya sama sama ta tsinci dai muryar anty hauwa din haka a gurguje ta gama tana fitowa ta shirya kanta cikin shigar doguwar rigace ta shadda wadda aka mata paint work mai tasadar orange ce akayi mata kwalliyar light blue,body spary kawai ta fesa ta daura dankwalinta ta debo magungunanta wadanda zata sha da rana ta fito falon,rabi'ah ce da sumayya da anty hauwa,cikin fara'a suka gaisa suka mata sannu da jiki"tace ai na samu sauqi ina momy da iftihal mutuniyata,anty hauwa tace suna gida gurin momyn nace ne ba da wanda zanzo duk har su kausar suna gunta muhammad ma tunda ba nono yake sha ba acan na barshi don suna zamu wuce dqga nan wata maqwafciyata ce ta haihu to kuma da yake haihuwar ta danzo da matsala a gidan su take acqn za suyi taron,tace eh Allah ya qara mata lpy,amin inji anty hauwa
Nan suka shiga hira abinsu minti talatin suka miqe suna shirin tafiya fadila dake ta qoqarin zuba musu abincin tace anty ga abinci don Allah ku tsaya kuci,anty hauwa tace bayan lemo da cake da kika cika mana ciki da shi alhamdulillah wlh,rabi'ah tace nikam anti fa na fasa rakiyar nan gidan sunan kuce da maman hidaya ina mata barka na taho anjima farida ta saukeni a hanya,sumayya tace"dama na sani anti ba rakaki zata yi ba ina ji tana cewa yau ana rana da yawa nasan dama daga nan gidan ba inda zata dara"aishikenan muje mu gaisa da samirah sai.mu wuce,inji anty hauwa,sumayya ta coge😒sannan tace a'ah anty nikam zan jiraki cikin mota ki shiga ki fito tayi saurin yin gaba damma kafa antin ta tsayar da ita,fadila tace "baki kyauta ba sumayya idan kika wuce baki gaidata ba"rabi'ah dake zaune tace wlh anty ko nice ba zan je ba,farida dake ta faman cin abincinta abunta tace qyalesu sister mai daki shi yawan inda yake masa yoyo✋🏻,ai kuwa dai sister farida sai.kaje kayi ta bugu taqi budewa gashi fa kana kallo ta tana kalloka qiri qiri,bayan kuma ta bude sai tayi.bake bake a bakin qofa ta tsare ka da ido tana wani ce maka meye?kamar wanda kazo maula gurinta,duk suka kwashe da diyar yadda rabi'ah ta gwada yadda samiran keyi banda fadila da ta dan murmusa gami da girgiza kai tana mamakin halayya irinta samirah
Biyar da rabi farida ta dauki rabi'ah suka tafi suma sashen sai ya dawo sai ita kadai ta so ta yiwa farida zancan dawowar maman iftihal sai kuma taga mai hakan zai dadeta da shi iyaka ta taya ta jimami sai shawara wadda a yanzu ita ma bawa kanta da kanta take,tunanim data fara yin zurfi a ciki ne yasa barin kanta ya soma ciwo bata yada hakan yayi zurfi ba ta tashi ta jona home theatre dinta ta saka cd plate na karatu ya karade falon
Takwas da mu
mintina na dare nasiru ya turo hancin motar ogan nasa cikin gidan,ya samu parking space ya daidaita tsayuwar motar sanna ya kasheta,a hanzarce ya fito ya budewa aliyu shima ya fito sannan ya miqa masa keys din motar yana fadin gashi sir ya amsa yana cewa debo min files din nan na sit din gaba,ya debosu ya bashi sukayi sallama aliyu ya sallameshi,hankalinsa gaba daya ya yi gaba burinsa kawai ya isa sashen nasa ya watsa ruwa a jikinsa ya samu ya kwanta ya huta,ya soma tafiya idanunsa suka kai kan sashen nata babu wadatar haske kamar bangaren samira dake tarwai da haske harda qarar abin kida ya dauke kai ya shige
Yana fitowa daga toilet ya zabi doguwar riga jallabiya fara sol.mai yankakken hannu ya saka ya feshe jikinsa da turarukan baccinsa masu sassanyan qamshi kan sofa ya fada ya miqe qafafunsa sannan ya hardesu ya kansa na kallon sama yasa daya hannun nasa ya shafi cikin sa,yunwa yakeji amma ya rasa inda za shi ya samu abincin da zai gamsar da shi,mutum ne shi.mai tsan tsami ba ko ina yake iya saki jiki ya ci abinscinsu ba sai ya yarda da ingancin tsaftarka hakan ne yasa ya tsani masu aiki hakan yasa tun yana gida ya yi ruwa yayi tsaki ya hana mominsa daukar masu aiki yace meye amfani su sumayya duk da suma bai yarda ko kadan yaci girkinsu sai na mominsa
Ya tashi ya qarasa fridge ya bude ya dauko yoghurt na l&z ya hado da fura ya samu cup ya dama ya sha ,ya sake tashi ya maida cup din kitchen sannan ya qarasa window dinsa yana bude glass din don ya bawa iska daman shigowa duk da iskar a.c da ta mamaye dakin kasancewar mutum ne shi maison natural air,idonsa ya sake fadawa kan bangaren nata duk da yaune ya shigo bashi da niyyar ganin kowa bacci yakeso ya samu isashshe don haka har wayoyinshi ya kashe su gaba daya
Ya saki labulen yana ajiyar zuciya saboda tunawa da yayi haqqine a kansa ya kula da lafiyarta don rabonsa da ita tun jiya da ya batta da magungunan da ya siyo mata ,ya zari keys dinsa ya zura slippers dinsa ya fice
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶1⃣9⃣
Tana kwance a miqe sambal bisa kujera three sitter don tunda tayi sallar isha'i bata tashi ba agun falon tsit yake ba komai sai sanyin na'urar sanyaya daki wanda ta gauraye da qamshin freshner mai dadi idanunta na lumshe ne tamkar mai bacci saidai ba bacci take ba tayi nisa ne a wata duniya mai wuyar fassarawa duk da ciwon da kan yake mata das das das amma hakan bai dameta baqarar bude qofan falon da qamshim mayen turarensa dake rataye da zuciyarta shi ya dawo da ita,ta bude manayan idanunta akansa yayin da shi kuma ke qoqarin tura qofar tayi namijin qoqarin tashi ta zauna kanta na sunkuye a qasa don ba zata iya jurewa kallonsa ba,hannayensa ya goye a bayansa ya qaraso falin yana kallonta da qayatattun idanunsa ya lura kamar ta dan rame duk da ba sanin ainihin kamanninta ya yi ba"ina yini"tace still kanta na qasa,cike da qasaitarsa da izzarsa ya dauke kai ya maida mata gaisuwarta da tambayar jikinta,da sauqi ta fada cikin sassanyar muryarta data sanya yaji wani dan yam ajikinsa
Bata zata ba bata kuma tsammata ba sai jinsa tayi zaune kan kunerar da take kai.kuma dab da ita ya sanya bayan hannunsa a wuyanta da niyyar jin temperatures din jikinta ba komai aransa,sai dai baisan illar da ya sake yiwa fadila ba a zuciya da gangar jikinta ba,kasala mai tsanani tashi guda da kuma wani irin shauqi taji ya saukar mata numfashinta ya tsaya cak na wucin gadi,sam bai kulaa ba yace"still jikinki da ragowar dumi ya kamata ki warke kafin isowar abokiyar zamanku right?ya qare maganar da sigar tambaya,ya.miqe yana cewa babu abinda kike buqata,tamkar ta ce masa"kai nake buqata aliyyu ka qarashe awoyin wannan daren naka tare da ni,maimakon haka sai ta sake gyada masa kai,yace " alright gudnyt"ta bishi da kallo idanunta fal cike da qaunarsa da kewarsa har ya fice daga part din nata ya rufe mata part din,ta koma da baya ta jingina jikinta da kujerar hadi da runtse idanunta hawayen dake maqale a idonta suka gangaro mata wani radadi da zugi zuciyarta ke mata lallai kishi masifa ne
Cikin daren bacci gagararta yayi juyi take kawai akan makeken gadonta cike da sha'awar aliyu tunda take bata taba jin makamanciyar sha'awa arayuwarta irin wannan ba
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Sannu a hankali ta miqa dukkan lamuranta ga Allah cikin ikon sa kuwa ta fara samun sauqinsu saidai fa har yanzu babu sauqi ta bangaren soyayyar Aliyu dake maqare cikin zuciya ,cikin lokacin sam ta daina bari idanunta suga aliyyu duk da tarin zugi da zullo da zuciyar keyi na son ganin nasa amma ta danneta
Cikin lokacin aikinta ya samu freedom da express din duk suka buqaci yin aiki tare da ita,ya ahmad dinne ya kawo.mata da kansa bayan ya sanar da aliyu da kansa ya kuma amince mata da fara aikin nata,tayi murna tayi tsallae tun a gaban ya ahmad din ya sha godiya sosai har da qwallar farinciki saboda yadda take masifar son aikin jarida shikam dariya yayi yace Allah zata godewa,bayan tafiyarsa ta kira farida dake fama da laulayi suka sha murnarsu tare,nan fa ta zauna ta soma tsarawa kanta yadda zata tafi da rayuwar aikinta
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin satin Aliyu ya shirya musu fita wadda ta farko ce agun fadila don bata taba fita ba wani gu da sunan unguwa ba bayan shopping da suke zuwa duka qarshen wata za suje ne gaida hajiyarsa
Tun rana fada ke zumudin fitar tana tunanin mai zata kaiwa momin,akwatunan lefenta dake shaqare da kaya wadanda kamar ba'a taba amfani da komai a ciki ba ta bude ta zabi turarurruka designers guda uku ta warewa abba,ta duba akwatinta da ta adana gift da ta samu na biki ta cirarwa momin atamfofi super Holland da England guda biyu,da kanta ta aiki yaron dake musu gyaran flowers ya samo mata kilishi mai kyau da zuma
Tun magariba ta yi wanka ta shirya kanta cikin atamfa dinkin riga da zani kamar light grean da milk sai ratsin baqi dinkin ya mata cas kamar a jikinta aka qirqireshi yari da sarqa ta saka ma dutse masu kalan milk sai farin agogon hannu tq zuba awarwaro mai 24 farare takalmi da jaka milk sai laffaya data nannade jikinta da ita milk ce mai adon baqi ta debi tsarabarta ta dawo falo ta kunna arewa 24 tana kallon shirin matasa at 360,tayi wani masifar kyau ta fito sosai a babarbariyar ta
Ya qarashe karin hular sa yana daidaita ta a kansa shaddace fara qal a jikinsa dinkin tazarce sai walwali take ta sake fidda sirrin kyawunsa mutum ne shi ma'abocin iya ado ta wannan fannin kam ko mace haka ta ganshi,komai nashi fari ya sanya hatta da agogo,ya sanya glass dinsa sanna fesa turarensa ya rufe sashen
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣0⃣
Bangaren samirah ya nufa wanda sai ta kama dole yake shigar sa,ga mamakinsa aai ya taddata sirshan tana zaune abinta zaninta da rigarta daban daban kanta da ta tsefe shi yana tsaitsaye kamar tabarya😜dama ita ba wani tsawon gashi gareta ba sai qarfi da gashin yake da shi,ba abinda falon keyi saiqarnin kifi sardine ta tara gwangwanayen a gabanta ua daurw yadda qarnin ke bugar hancinsa yana tayar masa da zuciya cikin bacin rai yace mata zaman me kikeyi baki shirya ba tun dazun?ta dan yatsina fuska tace qawatace wlh ta kiarani a waya ta kwasheni da jira ya gyara tsaiwarsa cike da qosawa da azababben qarnin kifin yace mata is ok sai ki nemi wanda zaku tafi tare kinsan bana jira yana kaiwa nan ya sanya kai zai fice yana jan tsaki cike da takaici ,ta yi saurin shan gabansa tana cewa haba sweet kayi haquri mana pls ka bani minti uku kaya kawai zan canza,ya kauce ya fice yana cewa wataqila idan kinyi sauri kin tadda ni kafin in ciro mota is ok,ya barta nan baki a sake ta bishi da kallo sai kuma ta zabura tayi cikin daki don ta shirya
Knocking taji anayi don haka ta zira hill shoes dinta fari ta rataya jakarta ta dauki ledarta don jikinta ya bata aliyu ne shi dinne kam idonsa na bisa screen din wayarsa yana danne danne bai dube ta ba ya juya taja part din nata ta kulle tabi bayansa tana qare masa kallo"ya gaji da haduwa"ta zanta hakan a ranta,tana jingine da rumfar ajiyar motoce har ya gyara parking qa'idarsa ne indai tare zasu fita baya neman driver duk da dama nasiru ne kawai.ke driving dinsa,wanni dogon hirn ya ja da sauri ta daidaita nutsuwarta ta nufo motar tun kafin ta qaraso taji an bangaji kafadarta da mamaki ta dago don ganin waye samirah tana ta zuba sauri zani a hannu tana gyara daurinsa,duk saurin da take gidan gaba aahe takewa,abun ma sai ya baiwa fadila dariya ta saki murmushi😊
Cikin mintuna da basu gaza talatin ba suka qaraso gidan,harabar gidan tsaf kuma fetal da haske ba kowa sai mai gadi shi da wasu mutum biyu zaune kan benci suna sauraron duniya tumbin giwa suna cin gyada jefi jefi suna taba hira,cikin girmamawa ya gaida aliyu sannan ya gaida su fadila ta amsa masa fuska a sake tunda dama da yar sanayya tsakaninsu ya samirabko kallo bai isheta ba bare tasan yana yi,ya dage masa get din ya wuce ya yafitoshi yayi masa ihsani kamar yadda ya saba shi da wadanda ke zaune a gun suka hau zuba godiya abinsa shi kuma baiso
Samira da aliyu suka jera suka fara yin gaba zuwan falon gidan fadila bin bayansu tayi ,sumayya da rabi'ah ne zaune a falin da hijabai ajikinsu da alamar sallar isha'i suka idar,suka juyo suna amsa sallamar sannan suka miqe tsaye cikin farin ciki suna gaida su hankalinsu na kan fadila itama su take kallo suna gaisawa sabanin samirah da ta riqe qugu tana qarewa falon kallo tana yaba tsaruwa da dukiya da ya lashe kamar wadda aka bawa kwangila sannan daga bisani ta zabi kujerar da tayi.mata ta zauna akai,cikin dakiya irin ta babban wa yake tambayarsu ina momy sumayya tace tana sama ya nufi benan taku biyu uku sukayi kacibus da iftihal na saukowa kamar yadda ta saba ta tsugunna ta gaidashi sanna ta daneshi ya sabeta a kafada yana tambayarta momi
Tare suka sauko shi da momin yana take mata baya iftihal na hannunshi ganin fadila ya sata ta zille ta diro ta nufeta a guje cikin murmushi fadilan ta tareta ta dora ta bisa vinyarya dukkaninsu suna dariya ta gaisheta,duskar momi washe da fara'a take.musu barka da isowa samira dake zaune dare dare bisa kujera kamar tata tave yauwa fadila dama.na qasa ne kan carpet ta duqar da kanta qasa tana murmushi cike da kunyar momin,gaisuwa aukai da samirah kamar qawa da qawa yayin da fadila ma ta kasa hada ido da ita a haka suka gaisa,ganin taqi sakin jiki ya sa momyn tace su rabi'ah su kaisu dakinsu itama zata gun abbansu yanzu ya shigo gidan,hira suke abinsu da fasika yayin da samirah ta zaro wayarta ta hau danne danne tana ganin duk ta girmesu tafi qarfin zama cikinsu ai,ga takaicin yadda aujewa fadila haba haba itq aunqi mata haka cikin ranta take cewa hmm dangin miji kenan tsinannu(kunji fa?)
A haka bacci ya dauki iftihal akan cinyar fadila aliyu ne ya leqo hukarsa a hannu yace ke sumayya ku taho dining"samrah ce ta fara miqewa tana cewa dama yunwa nake ji ta fice,qememe iftihal taqi kwanciya dole iftihal na nishi ta sabota a kafada suka fito su sumayya nata dariyar yadda ta dauki ifrihal din da qyar,momy ce da abba sai aliyu bisa dining din kusa da abban abba na dariya yaceyau ban dawo da wuri ba bare a murqushen tsohon
qashi na shine aka rama akanki ko?
Duk sukayi dariya kowanne ya samu kujera daya ya ja ya zauna banda fadila dake tsaye sabe dà iftihal wani baccin nason daukarta amma ta qi yarda tayi don kada a sauketa
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣1⃣
Momy ta kalli aliyyu tace alii rabata da rigi mammiyar yarinyar nan don idan ba kai ba ba wanda zata yarda ya sauketa,ya miqe ya nufesu yanayin yadda ya tsaya gab da ita yana yunqurin karbar iftihal ya haifar mata da wani yanayi cikin jikinta,ya sa hannu zai dauketa cikin rashin sani hannunsa ya shafi qirjinta wani abu taji ya tsirga mata tun daga kanta har tafin qafafunta hakanan shima yaji tsigar jikinsa ta tashi wani shocking yaji kamar an jashi da wutar lantarki,ya sabata a kafadarsa ta miqe zata soma rigima suna hada ido da shi tayi gum da bakinta🤐 ta mayar da kanta kafadarsa ta kwantar ya sauka da ita cikin falom ya kwantar da ita bisa doguwar kujera ya karanta mata addu'o'in bacci na tsari ya tofa mata sannan ya koma
Ta tsugunna ta gaida uncle abba ya amsa mata cikin kulawa yana cewa lpy lau diya ta,sannan ta ja kujera itama ta zauna,sumayya tayi serving din kowa🍽🍴 sannan akai bismillah aka fara ci,kwata kwata kasa sakewa fadila tayi ta kasa kai koda loma guda bakinta sai juya cokalin kawai take a cikin abincin ,amma ga tarin mamakimta sai taga samira ta saki jiki tana ta kaiwa uwar hanjinta🍜 harda tsiyaya lemo 🍹🍾da ruwa da kanta,tayi sakewar da ko ita da uncle abba yake kamar uba a gareta ba zata iya irinta ba
Abinka da mata momi na ankare da yanayin nutsuwar kowaccensu tana kuma sake godiya ga sarki Allah da ya qaddara fadila ta zamo daya daga cikin family dinsu,afakaice rabi'ah ta qarewa samirah kallo uadda take lodar abincinta ko aliyyu da yake dan gida baiyi haka ba,ki saki jiki mana fadilan ummi kici abincin ki mu fa iyayenki ne ko babu aliyu baki ga yadda yar uwarki ya saki jikinta ba?,cewar ummi,samirah ta amshe cikin tabe baki tace momi kinsan wani akwai qauyanci da rashin wayewa atare da shi"sai kowa yayi dif rabi'ah da takaici ya cikata tace ba rashin wayewa bane kowa dai da irin yanayinsa,ta sake tabe baki tace uhmm,ita kuwa fadila dariya ma ta bata sai daga qarshe ne taga kada suji ba dadi ta kurbi lemon da rabi'ah ta zuba mata
Bayan sun kammala momi tasa rabi'ah da sumayya suka gyare gurin suka kwashe kwanukan,suna shirin wucewa don su basu guri momi tace su dau iftihal su wuce da ita,falon yarage daga fadila aliyu samirah sai momi da uncle abba
Abba yayi gyaran murya yayi bismillah sannan ya kirawo sunan aliyu ya amsa masa"naam abba"ya dora "aliyyu girma yanzun ya hau kanka duk da a baya kwatan kwacin wannan girman ya taba hawa kanka kuma kayi namiji qoqari wajen riqeshi yadda ya kamata amma bai kai wannan ba,a yanzu dole na sake jaddada maka saboda zama ne da zaka yishi tsakanin iyalinka har su uku wanda ko ni mahaifinka banyi duk da komai tsarin Allah ne
Daga samirah har fadila babu wadda gabanta bai fadi ba har sai da samiran yabdaga kai ta kalli abban,uncle abba yaci gaba "lamarin mata ali sai da haquri kawaici da kuma jajircewa halitta ce su maau wuyar sha'ani amma idan ka duba Allah sai komai ya zo maka da sauqi ,aliyyu ina horarka da kaji tsoron Allah ka tsaida adalci tsakanin matanka duk wadda ka cuta wlh wlh sai allah ya bi mata haqqinta sai kuma ya tambayeka,kuma ko ni ban lamunci rashin adalci ba acikin gidanka ka riqe Allah ka kuma ji tsoronsa
Ya juyo gunsu fadila da kansu ke qasa kowa da abinda ke cikin zuciyarta yace "dukkaninku ina kallonku ne a matsayin 'ya 'yana na na cikina da na haifa nasihar da zan muku itace kuma ku ji tsoron Allah kuyi zamqn aure a matsayin ibada kuyi biyayya ga mijinku.ku kyautata zamantakewar ku domin kuwa shine muqullinku na shiga aljanna ko wuta idan kuka saba masa Allah ya tsare mu,magana ta biyu kuma na dakatar da shi ne daga gaya muku don inason na gaya muku ni da kaina ta hanyar da ta dace,nasan kowacce mace haka Allah ya halicceta da kishi kuma ba zaku so abokiyar zama ba a yanzu amma ba yanda muka iya da hukuncin ubangiji kuma aure rai ne da shi matuqar bai qare ba komai dadewar zamani sai an dawo anci gaba da yinsa to ina mai baku haquri a madadin aliyyu,mahaifiyar khadija(sunan iftihal na gsky haka abba ke kiranta yawancin lokuta)zata dawo dakun aurenta ina fata zaku hada kanku ku zauna lpy,samirah ta dago kanta a gigice tana fiddo da idanu waje😳tace"abba mai kake fada ne?dama da gaske aliyu yake da yafara zancen?" aliyyu ya juyo ya kalleta wani huci ya saki abba ya lura da yadda yanayinsa ya canza ya san yadda fishin aliyyu yake don haka ya danne shi,cikin tausasawa ya kalli samira yace ki kwantar da hankalinki yata insha Allahu ba zaku fuskanci rashin adalci ba daga gun aliyu ni kaina bazan lamunci hakan ba shiru tayi tana muzurai idonta ya kada yayi ja saboda ganin yadda aliyu ke gasa mata hara ra tamkar zai cinyeta danya,itakam fadila gabq daya jikinta ya saki tunaninta daya ta ina zata samu aliyyu bayan ga wasu na farautarshi ? Jin sunyi shiru dukkaninsu abba yace da momi"kina da magana momin yara?" Ta danyi murmushi tace" aikace komai abban yara,saidai nace aliyu kaji tsoron Allah kamar yadda abbanka yace sannan ku kuma Allah yayi muku albarka kuyi haquri kuma kuyi biyayya sai.kuci riba"suka amsa da amin banda samira da ta kasa furta komai sai tafasa da zuciyarta keyi,abban ya sake basu dama akan idan da mai magana ya yi,ba wadaa tace komai sai aliyu da yace"abba da momi na gode muku kuma insha Allah zaku sameni mai amfani da duk nasihar da kuka yimin zan zamo mai adalci da yardar Allah"Allah ya amince suka ce,fadila ta fito da kayan data taho musu da su ta dorawa abba nasa a gabansa sann ta dorawa momi nata
Duk da ranta babu dadi amma ta ji dadin yadda suka nuna jin dadinsu suka sa mata albarka,aliyyu kansa can qasan zuciyarsa yaji dadin hakan don shi mutum ne mai dake qaunar wanda ke kyatatawa iyayensa,haushi ya sake cika samira tayi dana sanin zuwan ta gidan yafi sau cikin carbi bata son taga wani yana yabo ko son fadila kwata kwata
Cikin mota ma kowa da irin zaren da yakr saqawa zuciyarsa shikam ya dake abinsa kamar bashi ya sanar da mata har biyu zai qara musu abokiyar zama ba tuqinsa kawai yake a nutse,fadila tata saqar na yadda zata juyo da hankalin aliyu take bata so kuma bazata so ace kishiyoyi har biyu su fuskanci raahin qauna da jituwa dake gudana tsakaninta da shi ba,samira kuwa wani mahaukacin kishi ne ke taso mata zuciyarta namata saqa da baqin zare,tana shirya mata irin mummunan matakin da ya kamata ta dauka abu guda ke taka mata burki idan ta tuno yadda aliyyu ya birkice mata da yanayin da ya sameta a daren farkonsu tasan har yanzu dafin na sukar zuciyarsa somin kuwa duk wani tanadin soyayya da sukayi wa juna tn daga ranar ya rushe,duk kuma waa qauna tata dake zuciyarsa wadda ta rage tuni ta rushe
Cikin satin komai ya fara kankama abubuwa suka cedewa baiwar Allah fadila ga zirga zirgar shirye shiryen fara zuwa aikinta ga kuma lamarin na dake mintsinin zuciyarta duk da shiryr shiryenta ya tafi da kaso.mafi tsoka daga damuwar dake cin xuciyarta,tuni tayi waya gidan an ma motocinta service daya tsohuwar tata ce tun ta gida aka sake mata fenti da wasu abubuwa sai ta tashi ta dawo sabuwa dal don tana qaunar motar bata son rabuwa da ita yanzu sai kuma wadda aliyyu ya sa musu a lefe wadda ta sam ira tuni ta dade da cin uban tata ta mora qawaye su ara suma su mora
Kira ta dinga samu daga su anty hauwa anty hafiza har da farida kowannan su nasiha ce da jan hankali ne nasa har farida ta so karayar mata da zuciya saidai tayi qoqari matuqa wajen nuna dakiya da mai da komai ba komai ba
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Wa yasan gobe?
▶2⃣1⃣
Samira kuwa abun nata sai ya zamto tamkar mai qaramin ciwon hauka kamar a kanta aka fara kishiya kasancewar ta samu gudun mawar zuga daga qawaye da yan uwa kala daban daban duk da wasu ba don Allah suke bata basuna baqinciki da rufin asirin kawai da take ciki ne(qalubale a garemu mata sai azo ayita baki shawara akan za'a miki kishiya ko wani harkar wani ahaka kamar mai sonki amma da zaki ga cikin zuciyarsa game da ke tsoronsa ma zaki koma ji,sanin haqiqanin mutum sai Allah,sai ki auna da hankali da Allah ya baki a matsayinki na mutum mai tunani)sai ta sake zama kamar zararriya ita kadai ma abangarenta sai ka jiyota tana bala'i tana zunduma ashariya(wa'iya zu billah)cikin satin baqi ta dinga yi kala daban daban kowanne da tasa guzuri da salon hudubar waccan ta shiga waccar ta fita
Tun Aliyu na zuba mata ido idan tana salon rashin mutuncinta da haukanta har sai da ya zamto idan tazo sai dai ta gajibda bugun sashen nasa ta juya da haukanta ta koma inda ta fito,tuni fadila tabgama tsarawa kanta yadda zata tafiyar da rayuwar aurenta ta gama tanadar komai,tana hango cewar itama fa maca ce tana da duk wani abu da da duk wata ya mave maiji da kanta ke taqamar tana da shi,tana da duk wasu qualities da ake buqatar mace da su kafin ta amsa sunan ta na mace,to me yayi saura banda itama ta shiga fagen a dama da ita?? Me zata jira banda ta shiga ta karbo aliyyunta? Ta gaji kuma lokaci yayi da take ganin ya kamata ace ta kasance da da shi ta gaji da dako da rainon soyayyarsa ita kadai
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Biki ya zamto saura kwana uku wanda yayi dai dai da sauran kwanaki bakwai fadila ta soma zuwa aikinta
A ranar ne bayan sallar magariba aka shigo mata da akwatina set shida masu matuqar kyau maqarenda kaya nasiru yace mata inji maigida,ta jinjina kai ta rufe qofar sashen nata ta koma kan kujera ta zauna daya bayan daya ta budesu ta zubawa kayan ido duk budurin da ake sai yanzu zuciyarta ta tsinke hawaye suka soma zarya a kuncinta a hankali take sa yatsunta tana sharesu tabbasa an jarrabci rayuwarta da jarabta mai girma ta sani cewa son aliyu jarabta ce daga ubangiji acikin jininta yake kuma bata fatan Allah ya dandanawa wata mace kwatankwacin yadda take ji a zuciyarta,nan saman kujerar ta lafe tana hawaye a hankali take furta HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL har taji zuciyarya ta soma sanyi
Haya niya da hargowa take jiyo wa maau qarfi suna karade filin gidan hakan ya sanya kukanta katsewa ta tashi kamar mai sanda ta isa window dinta da yake cikin balcony dinta ta yaye labulen ta riqeshi a hannunta,daga nan tana iya hango dukkq sararin gidan samira ce ke wannan hayaniyar cikin hargowa da babat tanajanyo akwatina irin wanda nasiru ya kawo.mata dazu daga part dinta daya bayan daya tana cillarwa anan tsakiyar filin gidan ko nauyinsu bata ji ,aliyyu na tsaye hannayensa harde a qirji ya zuba mata ido bai ko motsa ba
Sai da ta gama lodesu sanna tayi cikin gidan nata a fusace sai gata da gallon da ashana ta daga tana qoqarin bulbula musu fetur din da yake ciki sai a lokacin aliyyu yasa hannu ya fincikota baya a fusace ya nunata da dan yatsa yana cewa kul kada ki soma,ta dubeshi duk da ta tsorata da yanayinsa amma sai ta dake cikin bala'i take cewa" sai na qona aliyu sai na qona wallahi kayan fadar kishiyan wata tsiya ce,sai dai idan na qona idan ka so nima ka qona ni" ta sake zabura tayi kan kayan da nufin idar da niyyarta cikin qaraji da tsawa ya ambaci sunanta wadda sai da hantar cikinta ta kada amma sai ta waiwayo tace"ko kasheni zakayi ba zan fasa ba" tadai sake nufar kayan cikin azama a karo na uku,cikin fusata yasa hannu ya janyota baya harsai da ta zube warwas a gun tamkar ya bita ya tattaka haka yake ji,don da namiji ne ya masa haka to yanajin ba shakka sai ya nuna masa qwarin qwanjinsa
Ta sani cewa idan taci gaba da abunda take hukuncin da zai yanke mata ba mai sauqi bane hakan yasa tana daga zaunan ta hau borin kunya cikin surutai da maganganu marasa kan gado daga baya ma da taga ya qi kulata sai ta fashe da kuka
Ko kallo bata isheshi ba ya dinga siban akwatunan bibbiyu bibbiyu ya shigewa da au bangarensa yana gamawa ya rufe qofarsa ya barta a nan,data waiga ta waiga taga ba kowa ba wanda ya gansu sai ta goge idonta ta miqe tana kade zaninta tana wa allah godiya da ba wanda yaga abinda ya faru tana yi tana tsinewa hannatu qanwarta gashinan ta jawo mata asarar akwatinan ma dungurun gum dan ita ta bata shawarar tayi haka
A falon sa ya zube ya dafe kansa hannu bibbiyu yana tsananin jimanta al'amarin to haka mata suke ne basu da hangen nesa ya jima a haka sannan ya tuno bai ma shiga bangaren dayar ba kamar yadda yake ce mata a ransa"itama idan ka shiga wataqila haukan da zata yi maka kenan"wata zuciyar ke gaya masa,ba yadda ka iya tunda itama aqarqashinka take kuma ka shigarwa 'yar uwarta indai adalcin kake son yin
Da sallama ya shiga ta amsa a sanyaye tana zaune ne kan kujera hijabin da tasa ta budewa masu shigo da kaya har yanzu shine a jikinta saidai sabanin da yanzu akwatinan a rufe suke,a fakaice yake dan nazarin falon komai tsaf yake cike da tsafta da qamshi hakanan komai a killace yake a muhallinsa da kyawunsa kamar yau aka jerashi sabanin falon samira da komai ya fita hayyacinsa saboda rashin kulawa duk da dama tsadar kayan ma ba daya bane don iyayenta basu da qarfin iyayen fadilan,kanta na qasa ta dam zamo daga kan kujerar tace ina wuni? Duk da bata sa ran masawarsa ba don bai taba amsa gaisuwarta ba ga mamakinta wannan karon sai taji yace "lpy ga kaya nan abinda babu ko baiyi ba sai ki yi maga ko ki rubuta ta girgiza kai tana cewa😔 komai yayi mun gode Allah ya qara arziqi" ya lumshe idanunsa don har zuciyarsa ya ji dadin addu'ar "madalla" yace ya zaro bandir na dubu dubu guda uku ya dora saman akwatinan ya juya ya fice sai yaji wani sauqi na radadin da zuciyarsa ke masa addu'ar ta faranta ransa don tunda yake bai taba samun kwatan kwacin wannan ba daga bakin wani abu wai iyali ba
Muje zuwa yanzu aka soma
Mrs muhammad
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
12:45 pm 03/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣2⃣
Ana ya gobe daurin aure su anty hafiza anty hauwa farida sumayya rabi'ah har da rahama suka zo wa fadila,farida ta zube dinkunan da fadila ta bayar aka mata sunyi matuqar kyau da gaske duk da tana da sababbin din kunan ma da bata taba sa su ba,kala ashirin farida ta zabar mata aka dinko su lace biyar atamfa biyar shadda biyar material ma biyar ne,anty hafiza ce ta taho mata da mai gyaran jiki gashi da lalle takanas sai hade haden magunguna namu irin na mata imgantattun na 'ya'yan itace,anty hauwa sai dariya take tana cewa o'o'o fadila 'yar gata to ai ko kece amaryar sai haka,sai dai tayi dariya ta sunkuyar da kanta qasa cike da kunyarnan ta ta,anty hauwa ta zuge jakarta ya fito da littattafai tace ga saqon momi nan,hannu biyu tasa ta amsa tana godiya litttafai ne kusan goma na addu'o'ine da kuma gyara zamantakewar aure,
Zuwansun ya sake debe mata kewa taji dadi nan suka fara tsara yadda za su gudanar da yinin su na gobe wanda ko wacce mace da za'a qarawa abokiyar zama ke gudanarwa,wuni akai ana qalqale mata jiki yayin da su rabi'ah sumayya da rahama suka zage wajen qal canzawa gidan fasali,sune canza labulaye canza carfet goge goge da ahare share duk da komai na fadila tsaf yake sai abinda ba'a rasa ba,cikin qanqanin lokaci kuwa gidan nata ya canza kamar ba shi ba,hatta qamshinsa sai da aka canza kalarsa ya zama na musamman abinka da diyar bare bari
Rahama ke tambayar fadila samirah fa?fadila tace wlh tun safe dai naji tashin motarta amma ban sani ba ko qunshin itama ta tafi "Allah ya kyauta inji anty hauwa ,bayan isha'i komai ya kammala anty hauwa tace zasu wuce sai gobe kuma idan Allah ya kaimu anty hafiza da yake kwana za suyi ita da farida tace"dama kwanciyar ku muka yi maman kausar wlh ,a'ah hafiza na bar yara su daya a gida daga su sai Abbansu wunin yau fa duka?"anty hafiza tace to don Allah ga laila(mai qunshin da ta dauko)ku sauke min ita a dorayi
Suna kan gado duk su ukun sunyi shirin yin bacci hafiza ta zubawa ido dake qoqarin shafa addu'a tace wai yau wa kuka barwa mijin ne?samira fa bata dawo gidannan ba haka kuke masa?"cikikin son rufe sirrinta da son gyara rayuwar aurenta ba tare da taimakon kowa ba tace "girkin samira ne anty bana son neman rigima da tashin hankali me zani in masa tunda ba girkina bane?salin inje mu raba dai abun fada?"daga haka suka qyale zancan
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Washegarin aka zo akawa salima jeranta da yake aikin maza ne nan da nan yayi sauri amma akwai wasu daga cikin yan uwanta mata da suka zo da su,girkinsu su fadila sukayi sosai suka zuzzuba a manyan warmers suka aikawa yan uwan salima da wani wasu kuma suka barshi nan cikin kitchen dinta saboda mutane yan uwa da maqota da keta zuwa Allah ya sanya alkhairi har a lokacin sashin samira na kuelle ne alamar bata dawo ba kenan hakan yasa kowa ya shigo gun fadila yake yowa idan suka tambayeta samira sai tace ta tafi gidan qunshi
Ba qaramin kyau fadila ta zuba ba tamakar ita ce amaryar daga wayewar garin zuwa yanzu ta sanya kaya kusan kala takwas kenan har harabar gidan jama'ace don babu laifi yan taru duk da ba wanda suka gayyata
💔💔💔💔
Qarfe sha daya da rabi na rana aka daura auren Aliyyu salim maitama da salima tukur Abubakar,kasancewar gidansu salima na na unguwar dake daura da g.r.a ne yasa yanuwan fadila na jiki da suka halacci daurin auren suka dinga zuwa ana gaisawa suna tafiya ciki kuwa harda abbanta da muhammad da ya ahmad taji dadin zuwan hakan kuma ya faranta mata ranta don tun da aka daura aurenta rabonta da taga abban nata kuma shima yaune zuwansa na farko gidan nata,ya mata nasiha sosai da ta qara mata nutsuwa ta kuma sata kuka ta sake tabbatar da cewa ba qaramin zumunci bane tsakanin abban nata da uncle abba mahaifin aliyyu tabbas babu abinda zata wa abban ta aduniyar nan fiye da ta jure zaman aure da aliyyu,anan suka bar mata muhammad zuwa yamma abban zai turo a daukeshi
Qarfe sha biyu da rabi ta sake wanka ta sanya wani Swiss lace pink ne mai dan turuwa kadan sai kore aka masa da ratsin silver din zare sai manyan dutsina masu walqiya sarqarta abun hannu da dankunne mayafi da takalmi duk silver ne dinkin riga da skert aka mata skert din eight pieces ya bude daga qasa sosai ,yayi matuqar karbarta ya haska chaculet din fatarta gashinta mai tsawo da santsi da baqi ya sha parking da pink and green din ribbom sai ya kwanta a bayanta sai sheqi yake tayi daurinta das wanda ya ta qasansa gashin nata ya fito,ta dauki turare tana fesawa taji ana kiranta maqotanta sun shigo kuma wasu na nemanta a harabar gidan saurin da take yasa ta manta bata dauki mayafi ba,suka gaisa da baqin tasa aka kawo.musu abinci sannan ta qarasa harabar gidan, nasiru ne da wasu mutane suke neman gun jibge abincin da ake ta shigowa da su,ta nuna musu store dinsu dake harabar gidan ta farko kusa da parking space
Tana shirin shigewa ciki motocin suka soma danno kai suna parking daya bayan daya,bata fuskanci su waye a ciki ba sai da suka cika harabar gun dukkaninsu cikin fararen kaya suke,Aliyyu ta hango a tsakiyarsu fuskarsa nata fitar da wani annuri cikin wata rantsatstsaiyar shadda babbar riga da yar ciki sai wando zata iua cewa bata taba ganinsa da irin wanna shigar ba ya qara wani kyau da kwarjini sosai ta shagala da kallonsa har suka hada ido
Haushi ne da takaici suka cika shi ganin yadda tayi kwalliya kuma ta fito har kusa da get a haka na tare da tayi lullubi ba,yayi mata kallon nan nasa data tsana wanda ya saba yi mata hakan yasa ta tuna a uadda ta fito fa tayi saurin shigewa cikin jama'a ta bacewa ganinsa
Tana zaune cikin baqinta sumayya ta shigo tace anty kije inji yaya sai taji maganar banbarakwai gabanta kuma ya fadi tace yana ina?yana cikin garden,dakinta ta shiga ta sake fesa turare sannan ta lulluba mayafinta,tunda ta nufo lambun zuciyarta ke dukan uku uku a haka har ta cimmasa,yana tsaye ya goya hannunsa a baya ya juyawa qofar shigowar baya,batasan yadda akayi ya gane ta shigo ba don gurin gaba daya grass carfet ne bare tace yaji takun tafiyarta ne sai ji tayi yayi gayaran murya gayaran muryan sai ya zamo kamar ya mata luguden guduma a qirjinta🔨,me ya fito dake harabar gida babu lullubi?shiru tayi muryarta na dan rawa tace ka.....kay......kayi haquri"ya dan dauke wuta na dan lokaci kana ya juyo da azama kar mai shirin waftar wani abu,hakan ya sa tayi tsammanin duka zai kawo mata tayi baya da sauri cikin tsautsayi ta taka wani dutse sai kuwa ta tadeta tayi baya luuu zuciyarta na bugawa da sauri don ta gama saddaqarwa sai ya sha qasa,sai kuma ta jita jikin mutum aliyu ne ya sa singalalin hannunsa ya tallafeta ta bude idonta data lumshe tana jiran ta jita ta sha qasa sai ga idonta cikin nasa,ya tsuke mata fuska 😠kana yace meye haka tashi" tayi azamar zare jikintata tana cewa kayi haquri,sai ya harde hannunsa aqirji ganin yadda duk tabi ta duburburce yabi gashinta wanda ya bi wuyanta ya dawo kafadar ta ta dama da kallo lace din ya zauanar mata caras cas yabi lafiyayyar fatarta chaculet,ya dan dauke kansa yabi gefansa da kallo yana jan tsaki a fili
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
▶2⃣3⃣
Sai da ya gama shan qamshinsa sannan yace ina da baqi dame dame kuke da shi a kitchen?cikin dai rawar muryar tace akwai sinasir masa funkaso da miya fried rice sai white rice da miya,ya danyi shiru sanna yace cikin sweet a bamu sinasir da masa sai a hado da white rice tace to har ta juya yace hey! Tadan waigo idonta na kallon qasa yace idan min kawo kiyi knocking kawai ki barsu a bakin qofa ta gyada kai ta wuce
Bayan isha'i gidan ua dade ba mowa sai anty hafiza da farida suma suna gama kintsa mata ko ina suka turare shi sannan sukai haramar tafiya,godiya ta musu mai yawa su kuma suka cikata da nasiha ta rakosu tana bawa naty saqo don allah ki kawo min yan biyu tunda kika kaisu gida yaye anty minqi karbosu tace yayanku ma mita yake amma shekaran jiya munyi waya da mama sun kusa dawowa insha allah da haka suka rabu ta dawo ta koma bedroom dinta ta hada ruwan wanka wanda ya wadata da turarukan wanka,bayan ta fito ta shirya kanta ckin wani lafiyayyen material kalar qwanduwar qwai wanda aka masa ado da qyalli silver da ratsin fari kadan kadan ,shima yana daya daga ckikim dinkunan da aka kawo mata jiya riga ne da skert amma wadannan sun kamata sun muma fito da shep din ta sosai,tana gyara kayan kwalliyar dake kan madubin nata ne taji gudar yan kawo amarya jikinta ya saki ta zauna bisa dressing chair
Tana kwance bisa kujerar qaramin falonta agogon bango ya kada qararrwar qarfe goma tayi ajiyar zuciya ta gayar kwanciyarta goma da ashirin da biyu qarar intercome ta tada ita daga bangaren aliyu ne hakan yasa ta fahimci hadasu yake sonyi kamar yadda al'ada ta tanadar gabanta ya tsanata faduwarsa💔,cikin nutsuwa ta sake feshe jikinta da turare turare ta lulluba mayafi a lallausan gashin kanta wanda bata daura dankwali ba
Da sallama ta tura qofar falin nasasu biyun ne suka amsa amaryar na tsaye gaban fridge tana ciro ruwan roba da lemo yayin da gogan ke hakimce bisa kujera two sitter shigar jikinsa ta yanzu ta babbanta da ta dazu duk da dai babbar riga ce yanzu ma a jikinsa ta shadda milk colour ya ajiye babbar rigar a hannun kujerar da yake kai,salima ta dan zubawa fadila ido na yan sakanni sannan ta dauke kai ta dauki plate saman fridge din ta dora kayan fadila ta samu one sitter dake gefansu ta zauna ,saluma ta janyi centre table dan madaidaici gaban aliyun ta dora masata tsiyaya ya masa ta jiye ta koma kusa da shi kan kunerar da yake kai ta zauna,fadila ta saukar da idanunta qasa tana cewa cikin ranta "ni kadaice bani da irin wanna damar me yasa why Aliyu?,na kusa samota na kusa da qarfin zuciyata insha Allah" muryarsa ta jiyo yana fadin kefa mume jira ko?,shiru na yan mintina sanna ya qara cewa"yayi miki kyau" ya ajiye wayar ,saluma tace kawai ka qyale ta ni na gaji bacci nake so nayi,fadila ta dago kai suka hada ido sai kuma kowacce ta dan saki fuskarta fadila tace sannu amaryarmu"itama da dan murmushin a fuskarta tace sannu kuna lpy"a taqaice fadila ta amsa mata da" lau"ta dan saci kallonsa shi lemonsa ma yake kurba idonsa na kan qofa
Banko qofar akayi aka shigo samirah ce sanye da baqar doguwar riga babu ko alamar hida bisa fuskarta sai dan kwalun atamfa da ta dauro a kanta wanda tayi masa daurin ture kaga tsiya,ta kama qugu tana cuno baki gaba tace da aliyu "gani" wani banzan kallo ya jefeta da shi sanna yace "ga gurin zama nan ko ina idan kuma bai miki ba.....ya nuna mata qofa da hannu👉�,sai da ta qarewa ko ina kallo sanna ta nufi kujerar da aliyun ke kai kusa dashi a daya side din ta dora qafa daya kan daya tana girgizata harara salima ta makawa samirah itama kuwa batayi jinkiri gun ramawa ba,taja tsaki sanna taci gaba da jijjiga qafarta,hara rarta aliyu yayi ya kalli qafar da take jijjigawa ta fuskanci abinda yame nufi kuma tasan ba magana zai.mata ba don haka ta sake zumbura bakinta sannan ta sauke qafar tata
Godiya ya far yiwa Allah sanna ya dora dukkaninku a qarqashin iko na kume kuma tsarin Allah ne shi ya tsara hakan kamar yadda yame da ikon tsara rayuwar ko wane bawa nasa to ma gode masa akan duk yadda yayi da tawa rayuwar "daganan ya dora da yi musu gargadi da jan kunne sannan ya tunasar dasu tsarinsa na zama a bangarensa mai girki ta biyoshi"salima ta kanne masa ido tave" dear ani dama na nasan da wanna tsarin naka tuntuni saidai kawai ya zamto kamar tunasarwa a gareni"murmushin shima ya mayar mata yace "yes"
Zuciya ta kawowa samirah iya wuya sai da ta tanka" a banza ai wai talaka ya girmi sarki dolen mutum yanzu shinr qarami ko yaqi ko ya so"cikin fusata salima tace "👉�ke nifa ba dake nake ba,ban gayyatar irinku a zancena don ni idan banda qaddara ba ma baki kai matsayin ma ki zama kishiya ta ba wlh don ko yar wanke wanken gidammu ta fiki kwarjini sai kuwa samira ta nuna ta da yatsa tace"👉�don kutumar uban mutum ya qara gaba mana don ni duwa wuce dole ne a zauna da ni zama daram wlh "sai suka so su kacame
Cikin wata gigitacciyar tsawa aliyu ya dakatar da su sannan yace kowacce ta bace masa agun ba zasu haddasa masa ciwon kai ba haka kawai"salima ta miqe ta shige bedroom dinsa samira kuwa ta fice tana gungunin a qyaleta wlh taci uwar mata,ita kuwa fadila abun nasu tsorata ta yayi don bata taba ganin fadan kishiyoyi ba hasaluma ma ba'a taba yiwa umminta kishiya ba gidansu daga ita sai farida sai muhammad ko a tsakaninsu ba fada suke ba don haka tun ma kafin ya kammala bada umarni su fice din ita tuni ta riga su fita yana juya lamarina ranta
Ransa abace ya shiga dakin duk yadda taso lallashinsa yayi banza da ita ta san halinsa tun ba yau ba kuma bata manta da shi din ba don haka da taga yayi banza da ita yana shirin shiga wankà sai ta qyaleshi sai da ya fito yana shirin kwanciya sanna ta langabe a jikinsa tana bashi haquri,ya dan kalleta ya basar sannan yace matuqar kika ce haka zaki dinga biye mata kunayi a cikin gidana to na rantse babu wadda zan saurarawa acikinku,idan banda raini ma a gabana? Ta sake marairaicewa tana cewa "Allah na lura ita wannan kanta na hayaqi ne da kamar dayar ce da babu ruwana da ita,su auremin mijin kuma suce bazanyi kishi ba" shi sai a lokacinne ma ya tuna da fadila baima san sanda ta fice a dakin ba donsanda yake musu jawabin ka ta na sunkuye ne sai ya tuna rana shigen irin wanna da ya hadasu ita da samirah ba wanda ta kula a ranar ma ahi ko samiran harta wuce" ya kauda wannan yace mata" am telling uh indai kina son zama da ni cikin kwanciyar hankali" "baza'a qara ba dear"
Ganin yadda yaqi sakin jiki da ita yasa ta dinga masa wasu abubuwa wanda suka sa ala dole ya ajjiye fushinsa abinka da dama wanda yake cikin wani hali nan ya bada kai bori ya hau aka tuno da tsohuwar zuma don salima dama idanunta a goge take ta wannnan bangaren to haka shima aliyyun yake dalilin da yasa saliman ma ta kasa auren kowa kenan tayita naci har sai data dawo masa
Mrs muhammad
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?.......
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣4⃣
Cikin kwanakin amarci kawai ake ta ballewa a gidan ,salima wayayyar gaske ce ko da wani lokaci tana manne da A.s maitama samira kuwa ta kasa tsaida hankalinta gu guda,yiwa salima itada da aliyyu labe kuwa ya zamo.mata kamar ibada mintina kadan sai ka hangota tana ta safa da marwa tsakanin sashenta da na Aliyu,fadila baiwar Allah lissafinta yafi ga kwanakin da zata soma shiga office da kuma ranar da zata zamo itace ranar girki a gareta
Kwana uku kenan da tarewar salima fadila ta soma zuwa aikinta ya kama ranar laraba,shiga tayi ta hausawa atamfa ce dinkin riga da zani wadatattu yayin da tayi lullubi har kanta cikin yalwataccen mayafi komai nata cikin kamala yake da nutsuwa haka nan halittarta take kamar wata babbar mace duk da shekarun nata qana na ne,ta bude sabuwar motarta fara qal wadda bata taba shigarta ba saiyau,ta zauna a sit din zaman driver ta kunnata ta wana ta sosai sanna ta sauke hannunta daga kan key din ta hada tafukanta ta soma addu'a🙏🏻,sai da ta gama tana shirin tasar motar ta tuna da hand bag dinta data manto kan gadon ta da sauri ta bude motar ta koma ciki
A hanyar dawowa ne sukayi kacibus da shi kasancewar ta gefansa ne zata wuce din sai tayi tsammanim bai ganta ba don haka ta dauke kanta cikin sauri ta wuce don ta kusa makara ta ajjiye jakar a asit din baya tasa hannu zata kunna motar taji an janye hannun gami da zare key din ta daga kai tq bishi da kallo bai ko kalleta ba ya zagayo sit din mai zaman banza dake kusa da ita ya zauna sosai sannan ya maida qofar ya rufe,ta dan sunkui da kanta😔 ya dan kalleta sannan ya basar don ya lura kamar al'adarta ce hakan,ya tabe baki cikin muryar nan tasa ta isassun maza mai cike da izza ya soma ce mata"ko banza a qarqashin mulki da ikona kike saboda haka u must obeying my statute and order if kina son aikinki,ya dan qara tsuke fuska 😠duk da yawancin lokuta haka fuskar take ya dage kafadunsa sannan yace" I don't know why aka wani tsiri yin aikin bayan ban gaza komai a gidana ba......
Ya dan sha qamshi sannan ya dora firstly ya zama dole kanki shiga ta kamala idan kin tashi fita,sannan ban lamunce da yawace yawace abu na gaba kada ki kuskura na ganki da number din wani qato a waya ko receiving calls ba and d last one kuma mafi girma wanda zai iya causing loosing din aikinki mu'amala da maza,kada ki dauki damar da na baki na fita aiki lasisi ne da na baki da zaki dinga ganin kina da right na yin duk abunda kika ga dama,take note👉,yana qoqarin ficewa tace insha Allahu zan kiyaye"duk da ranta a abace yake da irun dokokim da yake kafa mata da ita a karan kanta ai tasan ya kamata,baice komai ba ya cilla mata key din yaja qofar ya fice ya tafi abunsa,ta miqa hannunta ta rufo qofar sannan tabi bayansa da kallo yanayin yadda yake taku kamar zabar masa inda zai taka ake,ranta babu dadi ta ja motar ta fice a gidan ,yanayin motar yana da dadin tuqi hakan ya taimaka mata wajan dawo mata da walwalarta,a hankali temper dinta take sauka sai ta dora da fadin la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim cikim zuciyarta,da haka har ta qarasa gidan radiyon freedom don can ta tafi sha'awa amma duk da haka akwai wasu privet ayyuka da zata dinga yi da express radio din
Yanayin yadda ta samu karbuwa ya sake sa mata interest akan aikin sosai,su biyu ne kawai a office din ita da wata fauziyya kusan za tayi sa'a da fadilan amma ita nada yarinya daya iman,fauziyya shekararta uku da soma aiki da tashar,sosai fadila taji dadin samun fauziyya da tayi wayayya mai faran faran da son jama'a duk da ita miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma'aikatan tana arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za'a fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu lokacin attachment dinta
Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma takan yi tilawar alqur'ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar
Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida sauran ta rufe sashen nata,
TO FADILA SAI INA?🤔
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣5⃣
Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa qofan,addu'a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa ma na buqatar a kintsashi,ba tare da tsayawa wani dogon nazari ba ta dauko dust bin dake falon ta ajjiye a tsakiyar falon ta zare dan hijabin nata ta jefashi kan kujera ta fara tattare ta fara tattare leda takarda gwangwani da duk wani abu da ya zama datti ne tana jefashi cikin kwandon sharan
Tana tsaka da aikin ne taji ana taba qofar alamar an shigo a tsorace ta dago tana tsammanin aliyu ne sai dai kuma maimakon haka sai taga ashe salima ce tayi tsaye a abayanta tana qare mata kallo ,fadila ta tsani yadda matar me mata naci nkallo haka,dama ita tun da can ta tsani mutum mai azabar kallo,to haka saluma ke mata a duk sanda hanya zata hada su ,abinda ita fadila bata sani ba shine kishine taf cike a zuciyar saliman don so tayi ta samesu gaba daya babu mamora kamar yadda taga samira bata da qira sam,saidai ance gwano baijin warin jikinsa ne ita dinma da tayi dogon nazari da tsinkaye da ta fahimci yadda tata qirar take irin matan nan ne masu azabar tsawo da sirantaka sai wani azababben fari da take da shi irin me gauu din nan to duk da babu laifi tafi samirah amma ko kusa bata kamo qafar fadila ba,tsawonta da azabar sirantaka su suka sata take a miqe kamar number 1 ba wani shape sai tsabar iyayi da yauqi
Ta kau da kai.daga kallon fadilan ta tabe baki sannan tace"oh nayi tsammanin mai gidan ne ya dawo da naga gun a bude" a taqaice fadila ta amsa mata da"A'a" taci gaba da aikinta,sai kawai salima ta bude fridge ta dau maltina hadi da kunna t.v ta nemi gu ta hakimce,sarai ta gano ba abinda yasa saluma zama a gun banda bin qwaqawafin taga me take yi hakan yasa ta sa key ta bude bedroom dinsa ta shige tare da rufe qofar da muqullin ta ciki,salima tabi qofar da kallo cikin takaici don ba haka ta so ba,nan ta zauna tana ci gaba da shan maltinan tana dakon fitowar fadila wadda batasan ma tana jiran ba
Ta qarewa shima bedroom din kallo sannan cikin nutsuwar nan tata ta fare tattare shi shima tana kintsa komai a muhallinsa tanayi tana mamakin kamar babu wasu mata dake kwana a dakin komai a yamutse?towel ne underwear ne comb ne mayuka ne turaruka ne kai tarkace dai wanda da alama a safiyar yau kafin ya fita yayi amfani da su warwatse bisa gadon bedsheet din kansa duk da babu datti amma ya yamutse,kowanne abau ta maidashi inda ya kamata cikin qanqanin lokaci dakin yayi fes komai ya dawo cikin hayyacinsa ta kunna kaskon turaren wuta electric ta zuba irin turaren wutan da take amfani da shi a bangarenta sanna ta wuce toilet
Toilet ne qaton gaske wanda yakai girman ciki da falo na mata da yawa yana dauke da duk wani kayan amfanin toilet na zamani,cikin lokaci qanqani shima ya dau haske komai na cikin sa farine sai da ya dawo daidai tamkar ka zuba abinci a qasan ka ci,sai da komai ya mata yadda take so ya wadatu da sanyayyan qamshi sannan ta bude qofan ta koma falon don ta qarasa aikinsa
Salima ta bar falon saidai ga gwangwani nan da tasha malt cups da qarin ledojin cake da na wasu tarkacen ciye ciyen nata watse a agun da ta tashin,baki ta tabe cikin ranta tana cewa"Allah ya sawwaqe an san yadda za'a bata amma ba'asan yadda za'a gyara ba sai kace ba mata ba,tana wanna zancan zucin tana kammale falin duk da girmansa kuwa,har kitchen bata barshi a baya ba sai da ta gyareshi ,"haba duk kyan abu ai yana buqatar gyara"inji fadila tana riqe da qugunta ta fada bayan ta gama aikin tana qarewa bangaren kallo yadda ya koma tamkar ba shi ba
Aikin ya ja mata lokaci sosai kuma ya gajiyar da ita,tana kimawa bangarenta nan ma dai ba zama din kitchen ta shiga ta kama habarta🤔 cikin tunanin me zata girkawa aliyyu wanda zata iya kammalashi kafin kiran sallar magariba ganin gashi hudu tayi har da rabi,abu mafi muhammancin ma bata san choice din aliyyu ba ,sai ta yanke a ranta bari ta fara gwadashi da tuwo ta gani din ta fuskanci wasu mazan ba sonshi suke ba in yaso idan yayi masa shikenan an wuce gurin
Tuwom shinkafa ta daura miyar danyar kubewa wadda ta dagargaza mata zallar tsokar kaza sanna ta sa tantaqwashi ya wadatu a ciki,misalin qarfe shida komai ya kammala ta soma mulmula tuwon da yayi fari sol cikim farar leda ya tuqu sosai ya hada jikinsa,sababbin warmers masu kyawun tsari ta dauko ta jerashi a ciki,ta gama ta gyara ko ina kamar bata yi aiki a kitchen din ba,ganin tana da ragowar lokaci yasata ta dora farfesun danyan kifi ragon ruwa maimakon zaman jiran dahuwarsa sai ta hada zobo wanda ta markada wadatacciyar abarba ta zuba a ciki ta hada da citta da kanunfari ta dafa,shima ta zubasu a mazubi ta wanke tukwananta,cikin azama ta shiga toilet ta silla wanka
😂😜 na gano su maman sa'ida fa na son jin qwaqwaf an baza👀👂🏻👄 anason aji ya aka kaya ko
To🤔🤔🤔kada dai ku gaji ku biyo safiyya insha Allah don jin kanun labaran
Mrs muhammad dinku ce 07066139278
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:38 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣6⃣
A bakin mudubi ta yada zango ta fara shafe loko da saqo na jikinta da turare dama ta saba da yin hakan kwalliya irin ta zamani mai tsari ta shiryawa fuska fuskarta bata cikata da jagwalgwalo ba ta taje gashinta mai tsaho da sulbi ta daureshi da ribbon ja swiss lace ta saka orange mai adon ja riga da skirt dinkin rafa wanda yayi masifar fito da sharp dinta,ta bata lokaci tana zana dauri a kanta ya zauna gwanin sha'awa fashion ta saka na dutse na sarqa da dan kunne sannan ta cika hannunta da awarwaro irin na india ja mai ashirin da hudu ya ahmad ne ya taho musu da tsarabarsa sati biyu da suka wuce,plate shoe ta saka orange and red ta sake feshe jikinta da turaruka sanna ta kalli kanta a mudubi,masha Allah ta fadi ba tare da tasan ta fadi ba sai murmushi ya subuce mata ita kanta yau ta sake gasgata kyawun da ake fadar tana da shi,kiran sallar magaribar da taji shi ya sata saurin fitowa ta shiga kitchen ta shirya kayan abincin ta kulle sashen nata ta fito tana tunanin qila ma aliyyu har ya dawo,ta cikin balcony din ta ta isa sashen ba alamun ya dawo don haka ta sa key dinta ta bude tana shirin shiga tajiyo alamun tsayuwa mota ta waiwaya sai taga samirah ce ke shirin fitowa daga motar tata wani irin kallo samiran ta watso mata wanda fadila ta gaza gane mai take nufi,dauke kanta tayi abinta ta shige don ba ita bace a gabanta tana mamakin masifaffen yawo irin na samira
Cikin qwarewa ta shirya table din sannan ta sauko cikin falon ta kunna tafkekiyar t.v plasma din dake manne a bango cikin sa'a kuwa malaminta ne ke karatu a saudi qur'an ta dan qaro volume matsakaici ya game falon ta koma gefe ta tada sallarta cikin nutsuwa bayan ta idar ta koma ta zauna tana kallon yadda mahajjata ke dawafi
Mintina biyar da zaman nata taji ana bude get jikinta ya bata Aliyyu ne jikin window taje ya dage labulen tana kallonsa har ya fito daga motar dukkan alamun dake nuna gajiya ga mutum sun bayyana a tare da shi,duk da ya gajin amma a nutsenshi yake kyawunsa na nan saidai fara'a da tasake yiwa fuskarsa qaura hirar da fadila keyi kenan ita da zuciyarta nasiru ne ya kulle motar bayan yafito sanna ya miqa masa kayayyakinsa da muqullan cikin rusunawa kamar ko yaushe aliyu ya karba yana cewa👉kada kowa ya jirani gobe ka sallamesu don bazan fito da wuri ba idan ka sallamesu sai kuci gaba da list din suna yan wadanda suka karbi kayan amma a cire sunan alhaji hamza wannan mun gama da shi✋🏻,nasiru yace ok insha Allahu ya juya yana shirin wucewa yace Allah ya tashe mu lafiya,ameen ya amsa masa
Burinsa ya isa gida yayi wanka ya samu abinda zaici ko da tea ne donshi kam har yau cikin matan gidan babu wadda zai nuna👉�yace girkinta ya masa har gwara salima yakan qoqarta yaci indomie dinta don kore yunwa,yayi mamakin ganin qofar tasa a bude amma sai yayi zaton ko salima ce,ba wani dadi da yaji don ason ransa so yayi ya zauna shi daya ya samu hutu
Saidai yana tura qofan wani daddadan qamshi ya daki hancinsa wanda ya tilasta shi lumshe ido kasancewarsa ma'abocin son qamshi sai ya shiga tunanin inda ya taba jin qamshin amma ya kasa cankowa idanunsa suka sauka a kanta bata anakara da ya shigo bane ko tsorone ya hanata motsi?ya dan tabe bakinsa 😠yana tunanin mai ya kwao ta kuma? Ya qarasa shiga falon yana sallama a nutse ta dago tana amsawa ya dan zubawa fuskarta ido zuciyarsa na son yaba wani abu amma ya rasa meye shi?ita kuwa gabanta ke faduwa cike da fargabar kada ya wulaqanta aniyarta yadda ya saba ganin yaddda ya hade rai kamar ya ga kashi,sai kuma taga ya dauke kansa ya nemi kujera can gefe ya watsar da kayan hannunsa sannan ya zauna har baisan sanda yace wash! ba ya sake lumshe ido yana ci gabada sheqar qamshin da ya ji yayi masa har cikin zuciyarsa ya rasa kuma ta Inda ya samu don dai shi har ya bar falon baiji qamshin ba sai yanzu da ya dawo
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣7⃣
Sannu da zuwa tace cikin cool voice dinta,ya bude idonsa tana durqushe gabansa riqe da cup da jug na glass baice komai ba yabi hannun nata da kallo dake riqe da cup din tana tsiyaya masa lemon zobon dake ta tsatstsafar sanyi da qamshin abarba ta janyo center ta dora a kai sanna ta balle murfin gorar ruwa na c'bon ta cika masa shima cup da shi ta ajjiye masa duk baice komai ba cikin dari darin kada ya gwasaleta ta miqe ta dauki briefcase dinsa safa takalmi key dinsa da duk ya wurgar din ta yi cikin daki da su
Tana shiga tayi maza ta maida qofar ta jingina jikinta ta dafe qirjinta tanajin yadda yake bugawa da sauri da sauri idanunta a lumshe tana dan murmushi☺, cikin zuciyarta tana cewa wai Allah na! Sai da ta dan nutsu sannan ta ajjiye kayan a inda ta tsara musu kai tsaye ta wuce toilet ta kashe makunnin heater din don har jar danja ta kama alamar ruwan ya tafasa ta hada masa ruwan wankan a bathtub ta saisaita shi ya zamo mai dumi sosai yadda zaiyi saurin saukar da gajiya sannan ta zuba masa turarukan wanka a ciki
A hankali yasa hannu ya dauki cup din zobon yana tunanin meye wannan? Ya kai bakinsa da niyyar dandanawa sai gashi ya shanye har da qari sai da yasha cup uku sannan ya saki ajiyar zuciya saboda yadda dadinsa da sanyinsa ya ratsa shi sai yaji kaso goma na gajiya da qishirwarsa har ma yunwar sun fara sakinsa ya samu relief har a qwaqwalwarsa ya jingina bayansa da makarin kujera
Sai a yanzu ne ya lura da canjin da falon ya samu ko ina tsaf tsaf kamar yadda yake so,tunanin wa ye yayi aikin yake don shi kqm daga samira har salima yasan cewa matane masu azabar ganda da ko ruwan sha sai ya tambaya ake iya tashi a dauko masa,ga ruwan wanka can a toilet ko kana da buqatar yin wanka,ya dago da kansa tuni har tayi hanyar kitchen fadila tayi hakanne don gujewa baqar maganarsa ko da ziyi mata ta maqale a window din kitchen tana leqensa
Sai da ya bata lokaci sosai har fadila tayi zaton bazaiyi wankan bane ta soma dana sanin shishshiginta sanna ta hangoshi yana kwance agogon hannunsa hadi da cire suit dinsa ya riqesu a hannu ya shige dakin tabi bayansa da kallo,ta janye idanunta hadi da lumshesu ta dafe goshinta da tafin hannunta tana cewa a can qasan maqoshinta"wo hoho Aliyyu badai miskilanciba?.... sai kuma ta sake sakin murmushi tana cewa"Allah ka mallakamin Aliyyu"tayi saurin dafe bakinta tama zare ido saboda ta fuskanci maganar zuci ce ta fito fili
Sak yayi ya tsaya yana kallon dakin baccin nasa komai kamar yanzu aka jerashi ko tsinke babu a farin tiles din dake mamaye da dakin ya jinjina kai ya ajjiyr kayan hannunsa a gefan gado ya fara binciken inda ya ajjiye rigar wankansa sai ya bude wardrobe donnya dubata a ciki,canji idanunsa suka masa karo da shi,wardrobe ce ta jikin bango mai hangar komai ya canza bangaren shadda daban yadi daban suit dinsa haka kai hatta socks dinsa da handkerchief an masu nasu tsarin bai san sanda ya saki murmushi ba don tsarin ya burgeshi kasancewarsa dan gayu ya tabbatar babu tsarin rigar wankansa a gun don haka ya haqura ya wuce toilet cikin ransa yace wonderful cikin wani glass dake manne a kwanar bandaki ya hango rigunan a tsare jikin hanger bai bata lokaci ba ya shige cikin ruwan wankan duminsa da qamshinsa suka ratsashi sai yaji kamar kada ya fito,ya shafe kusan minti talatin sannan ya sabe jikinsa ya dauraye ya fito bisa gefan gadon ya zauna ya tsane jikinsa ya nemi farar jallabiya yasa don yafi son sata idan ya dawo daga aiki ya taje kansa ya feshe jikinsa da turare sanna ya bude jakar computer dinsa ya cirota yayi waje da niyuar shiga kitchen ya tafasa ko tea ne ya sha
Ganin ya zauna yana aikinsa ya sanyata debo kayan ta shimfida babbar ledar cin abinci a gabansa baisan me takeyi ba sai da yaji qamshin abinci nata shiga hancinsa sanna ya dago kansa ya dubi gabansa ta jera tuwon a farin kyakkyawan plate miyar na wani dan kwano na tangaran shima fari ne tasha man shanu ta cika wani plate din da farfesun ragon ruwan ta zuba ruwa na sha da na wanke hannu ta tsiyaya masa lemo sanna ta janyo tissue box ta ajjiye masa tace bismillah ya kalleta 😠yace " ce miki akayi da yunwa na zo? Ko an baki labari ina buqatar abincinki kinga malama kwashe abincinki ki ban wuri,
Ba qaramin sosa mata zuciya maganganun suka yi ba bata san sanda hawayen da take boyewa suka silalo mata ba😭karo na farko kenan tun sanda ya fara mata cin kashi,batayi qoqarin maidasu ba ta barsu suka ci gaba da zuba
Cikin zuciyarsa addu'a yake allah yasa kada ta kwashe din don tunda yaji qamshin sha'awar cinsa ta kamashi ai kuwa aadu'arsa bata karbu ba don a zuciye ta soma maida abincin cikin warmers din
😜😜😜
Kuyi haquri da wanna yau bani da chargy wadatacce
Mrs muhammad na muku fatan alkhairi👏🏻
📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:39 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Written by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶2⃣8⃣
Sai da yaga da gaske take cikin daurarriyar fuska yace kinga malama zuba kada a qarani gaba ace bani da adalci tunda kin kawo kanki" ya fadi kamar wanda da gasken tilastashi akayin,kalmar tunda kun kawo kankin tayi matuqar bada gudun mawa wajan qona mata rai don haka hawayen da suke zuba suka qara gudu😭
Malmala daya ta saka masa da miya ta miqe wata zuciyar na zugata kiyi tafiyarki kawai wata kuma na lallashinta da hanata tafiya tana gaya mata saurin fushi ba nata bane yanzu da sauran lokaci dai,kujerar da ta tashi a kai can ta koma ta zauna tana qoqarin maida kukanta ta canza tasha zuwa mbc boollywood ta tarar suna film din kuch kuch hotahie tsohon film ne amma bata gajiya da kallonsa
Ta kasa hankalinta kusan gida uku kason farko na kan aliyyu ne da taga ya ci gaba da danne dannensa a computer ya shanya abincin,na biyu na kan matan gidan da ta ga har yanzu ba wadda ta leqo da niyyar yi masa barka da dawowa ashe haka suke masa har ita din?,na uku kuma ta dorashi kacokam ne bisa t.v dake gabanta sai ka rantse da Allah ta bata hankalinta ne gaba daya
Ta gefan ido taci gaba da satar kallo da nazarinsa sanda taga ya rufe computer din ya sauko qasa mamakinta zaman da taga yayi zamane irin wanda annabi yake yayin cin abincinsa mamakinta ya sake qaruwa ne sanda taga yayi bismillah ya sa hannunsa ba tare da ya nemi cokali ba
A hankali taci gaba da bi biyarsa da idanunta,yanayin yadda yake cin abincin a nutse yq burgeta tana ankare da shi har sanda ya cinye ta biyu ya soma cin ta uku,ranta yayi mata dadi ganin yadda yake cin abincin bisa dukkan alamu yayi masa dadi
Hankalinsu dukkansu ya kai bakin qofar jina naturo ta,saluma ce ta shigo da yalwar fara'a a fuskata amma sai taja tayi turus ganin fadila a falon,cikin iya tsabar duniyanci da iya waskewa ta gayyato fara'a fuskarta ta dubi sashen aliyyu tace" a'ah dear inacan ina zullumin yau ka jima baka dawo gida ba"ya miqamata hannu sanda ya sa lomar tuwo a abakinsa yana mata nuni alamar ta taho ,ta taho din kuwa ta zauna kusa da shi sai da ya hadiye sannan yace almost one hour da wani abun da dawowata na gajine shi yasa ba wanda na nema"da ido ta nuna masa fadila tana masa nuni da ita ya akai tasan da dawowarsa har ta rigata zuwa?,dauke kai yayi kamar bai fuskanci abinda take nufi ba don ba'a haka shi da shi,itama tasan hali don haka ta bar maganar
Murya a anarke tace dear dama zancan ankon lubabatu ne qawata da nayi maka,kudin nakeso na karba don banason in zama a qarshe saboda baka fiya samun mai kyau ba"ya gyada mata kai yana ci gaba da cin abincinsa,ta tsare shi da ido ganin baice komai ba bayan gyada kan sai tace sake cewa naji kayi shiru baka"ya dago cikin qosawa yace ba munyi maganar ba tuntuni ba kuma ana amsa miki kuma yanzu baki ga abinci nake ci ba" tace cikin son wayancewa ok takai dubanta ga abincin gaban nasa sannan tace" dear yaushe ka fara cin tuwo?"kai tsaye yace "yau"cikin mamaki ta maimaita yau" ya gyada kai yace "yes"sai kuma tace ammafa nima abincin ya burgeni bari muga"ta tsoma hannu a plate din nasa,aliyu ya tsaida cin abincin ya bata fuska ya dago yana dubanta "repeatedly am telling you duk sanda kika soma cin abinci ba tare da kinyi bismillah ba kina cine tare da shaidan ko?" Ta dan dafe kai tace oh sorry na manta bismillah amma fa abincin nan dear yayi sosai a wane restaurant ka siyo" na gida ne ya bata amsa ya dan dubi sashen fadila wadda idan ka kalleta a zahiri zakayi tsammanin kallin film dinta takeyi haiqan sai dai duk tana jinsu tayi kunnan uwar shegu da su,salima ta fuskanci abinda yake nufi don haka ta tsuke bakinta😷tana da na sanin yabawar da tayi wa abincin din bata yi tsammanin fadilan ce tayi ba
Salima na ta zubawa aliyyu surutu jefi jefi yakan tanka mata har suka kusan tashi da abincin gaba daya har farfesun kifin,suka gama aliyyu ya koma kan computer dinsa ya ci gaba da lissafe lissafensa na kayyayakin dake cikin store da wadanda za'a zuba sababbi da kuma wadanda ya saba rabawa yan kasuwan
Har kusan tara na dare salima na zaune taqi tafiya,cikin haka saiga samira itama ta shigo yanayin samira ne yasa sauran kadan farida ta tuntsure da dariya duk da quncin da zuciyarta ke ciki,nikam safiyya kasa daurewa nayi sai da na dara😂😂 har sai da maman walid ta rufemin baki don kada su ganni
Zanin shadda ne a jikinta rigar atamfa dankwalin material,har abada ba zaka ga kwalliyar samirah cikin gidanta ba idan har kana son ganin kece ado tofa saidai idan fita zatayi cikin qawaye takan ce kada a raina min wayo ina gidan nera dole na dinga keta shiga da kowacce mace zata kiyayi kanta tasan tana tare da matar Aliyyu salim maitama(kunji wata toshewar basira fa)
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
03:15 pm
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?
▶2⃣9⃣
Salam! Samirah tace cikin daga murya tana tafiya tana wani budewa babu wanda ta kalla direct ta wuce gun maigidan hannunta dauke da zungureriyar farar takarda,ya dan bar abinda yake kana ya dubeta yana masawa,ta qaraso inda yake ta zauna hannun damansa yayin da salima ke hannun hagunsa takardar ta miqa masa ya amsa kafin ya duba yace" kada ki sake min irin wannan sallamar da kikamun yanzu don ba sallama bace take note,ok?"ta gyada kai tana buntsuro baki,ya bude takardar yana dubawa,ya qare dubawar sannan ya dago kai yana kallon fuskar samiran idanunsa da alamun neman qarin bayani,ta dan yatsine fuska sannan tace"eh abu uwan amfani ne da suka qare nake da buqatarsu" ya dan gayara zamansa ya jingina da makarin kujerar ya sanya idanunsa sosai cikin nata,sai ta kasa kallonsa ta dan soma rikicewa tana son janye idonta ta kasa tasan shi tamkar maye yake wajen naqaltar mutum tasan yanzun nan ba qaramin aikinsa bane ya harbo jirginta,da zarar aliyyu yayi ma irin wannan kallon yake gamawa da kai,sai da yayi shiru na muntina sannan yace"ina zaton yau ko sati biyu ba'ayi ba na karbi list na dukkan abunda baku da shi na kawo.....ya akqi naki ya riga na kowa qarewa bayan ko sati biyun ma ba'a cika ba?"
Ganin tayi shiru ta kasa bashi amsa yasa ya maida kallinsa ga salima wadda tayi kasaqe tana sauraronsu zuciyarya cike da farinciki tana mai addu'ar Allah yasa a ci mata mutunci"nawa ne kudin naki ankon"tawani yi fari da ido sannan tace😊 atamfa dubu arba'in ne lace dubu sittin aai gudun mawar da zan bata dubu dari"(kunji tsabar rashin hankali irin na wasu matan mutumin da duk qarshen wata yake fita da su suyi siyayyarsu idan akwai abinda sai anshiga kasuwa ake samu zai sa su su rubuta ya bayar a akawo musu haka nan kayan abinci da na ciye ciye zaisa a sabunta miki koda basu qare ba kuwa ruwanki ne kisan yadda zakiyi da su shi dai duk qarshen wata zai miki haka,hakanan zai kawo kudi masu kauri ya baki bayan wanda kullum zai baki koda ba ranar girkinki bace )baiji komai ba kasancewarsa mai hannun kyauta ne koda ba ga iyalinsa ba,amma ya lura barnar ta soma yawa don haka ya sake waiwayawa ga samira yace"uhm....am waiting for d answer
Ta yatsina fuska tace" kasan ni maca ce mai jama'a 'yar dangi kuma duka dangina anan garin suke ba baquwar haure ka auro ba wannan ya shiga ne wannan ya fita"salima tasan da ita take kasancewar iyayenta da danginta ba a garin suke ba a hannun qanwar mamanta take anan kanon amma ba yan garin bane,cikin hasala tace "da uban wa kike?"kamar dama jira samiran kuwa take tace da ubanki nake👉,kinji na kasa da ke ne bare ki dauka banza kawai😙 mtswee!"ai kuwa salima tayo kukan kura tayi kan samira da niyyar shaqota dama da qullin samiran a ranta
Wata gigitacciyar tsawa ali ya daka musu wadda hatta fadila dake gefe sai da ta miqe tsaye saboda razana bare su salima da suka koma sukayi zamqn dirshan ba tare da sun shirya ba,ran 'yan maza ya baci fa zuciyarsa ta tabu take idanunsa suka kada
Cikin tsananin bacin rai ya kallesu "wadanne irin mahaukata ne da baku da burin da ya wuce kuyi kokawa?"salima da ta shaqa da yawa ta nuna kanta👆🏼 tana cewa aliyyu nice mahaukaciya?" Ya dora da cewa "kun
wuce hakanne?bai sauraresu ba ya murza yatsunsa suka ce das das das ya nuna su👉� sannan yace dis is d last worning kunyi na farko kuma kunyi na qarshe dambe a agabana.....☝🏼bazan dauka ba don ni ba shasha sha bane" salima da idonta ya ciko da qwalla😢 tace"amma fa kana gani fa tana shigowa ta hau habaici daga qarshe ta hau zagina.....samirah ta tari numfashinta da cewa"tambaya kimayi na baki amsa daidai da tambayarki" shut up!" Ya sake dakawa samira tsawa ya nuna mata qofa😡👉� sannan yace da ita get out of my room,jiki a salube ta juya zata fita ya ce hey🖐🏽ta juyo ya nuna mata paper dinta👉� take your rubbish neman tashin hankalinki ya siya miki ya bita da "stupid" wani takaici ya sake turnuqeta ai kuwa buguzum buguzum ta qarashe ficewa
Ya dawo da idonsa kan salima yace"ni bani da kunne sanda tayi zagin ba zaki bari kiga hukuncin da zan dauka ba sai ke sarkin iya hukunci?,sai kuma alokacin ta soma shagwabe masa da sunan bashi haquri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu"🖐🏽dont disturb me please leave me alone"ta san bacin ran aliyu bashi da dadi do haka ta ja qafafunta ta fice cikin takaicin asarar da sira ta jawo mata na kudaden da take son karba a gunsa,yaja tsaki mai qarfi cikin ransa yace"silly girl" ya juya a hanzarce ya shige bedroom dinsa
Ransa ya baci sosai mutum ne da baison hayaniya yanzu haka qirjinsa zafi yake haka yake ko hira yayi mai tsaqo yanzu kansa zai fara ciwo shi yasa ko musu bai iya ba,ba ruwanshi da shiga wata harqalla ko abokai bai fiya tarawa ba baifi ka qirge abokansa ba da hannu,to da shi da fadilan bansan wanda yafi wani ba🤔
Mrs muhammad dinku ce
[10/16, 12:39 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Writting by safiyya Abdullahi musa huguma
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣0⃣
Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya canza kayansa zuwa na barci farare ne sol masu taushi mutum ne shi ma'abocin son fararen kayan amfani ya fada bisa gadon yayi rigingine qafafunsa na qasan gadon ranshi a cunkushe yake
Fadila da ke tsaye sai yanzu ta motsa ta saki ajiyar zuciya gami da fadin Allah ya kyauta ya iya mana abinda ba zamu iya da shi ba,ta isa inda suka baje kolin abincinsu suka ci suka tashi bar kwanukan ta tattare su ta gyara gun kamar ba'a yi hada hadar abinci ba agun
Ta isa kitchen ta zubasu cikin sink ta kunna gas ta hada ruwan bununsa wanda ya wadatu da citta kanunfari da lemon grace ta saka lipton daya sannan ta rufe tukunyar,ta koma ta saki fanfo ta wanke duka kwanukan ta adanasu sannan ta juye mishi tea din cikin wani dan qaramin flask mai kyau ta dauki cups guda biyu na tangaran ta dora a saman plate ta hada masa da spoon,ta rufe qofan kitchen din ta doshi bedroom din nasa
Ta tura qofar tana dar dar don tana tsoron kada ya maimaita mat abinda ya mata dazun,ya canza kwanciyar tasa zuwa barin hannun damansa yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,qafarshi da yake dan kadawa kadan kadan shi yasa ta fahimci idanunsa biyu a hankali ta ajjiye tire din a asaman bedside sannan ta koma saman kujerar madubi ta zauna tana fuskantar bayan nasa,dakin ya yi tsit kamar ba wata halitta a dakin sai qarar agogon bango dake maqale a abangom dakin yana ta aikinsa,ita batace komai ba bareshi da tasan dama ba maganar zaiyi ba
Zuwan can ta dan ja numfashi sannan ta tattaro dukka dauriyar da ta rage mata bayan ta gama wassafa da tsara maganar da zata fito a bakinsa,tayi yar gajeriyar gyaran murya a dan tsorace sanann tace" nazo ne baka haquri game da bata maka rai da mukayi dukkaninmu mu ukun,zan ari bakin yan uwana na ci musu albasa ince kayi haquri da mu baki daya,idan ban manta ba haka Abba ya gaya maka a ranar da mukaje masa _lamarin mata sai da haquri da kuma jajircewa halitta ce maau wuyar sha'ani amma idan kasa Allah a gaba sai komai ya zo maka da sauqi_"kayi haquri da mu Allah kuma ya huci zuciyarka😔,ga black tea nan ko kana da buqata sai da safe
Ta miqe tana barin dakin ya dan waiwayo yana dan kallon ta har ta fice,yana cike ne da mamakinta dama tana da saurin sauka a fishi ne?,at least ya samu relief ainun daga damuwarsa,hakan ne ya bashi dama har ya jawo flask din ya murda murfinsa ya bude qamshinsa ya taso ya mamaye hancinsa ya dan lumshe idonsa take kwadayin tea din ya kama shi,yasa kofi ya tsiyaya ya sanya zumarshi ya kurba qamshin cittan da kanunfarin da lemin grace suka hadu a abakinsa suka masa dadi
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tana idar da sallar asuba bayan kammala al'adarta ta kullum wato azkar na sabahi wal masa wanda annabi ya koyar ta koma ta jingina da gefan gadonta idanunta a lumshe ta soma tilawa kamar yadda ta saba cikin sassanyar muryarta,sai da tai izifi biyar sannan tayi addua ta shafa,ta linke sallayarta sannan ta soma gayara bangaran nata duk da ba datti ko kadan sai 'yar qura da ba'a rasa ba wadda hadarin da ake tayi kwana biyu idan ya hado sai kuma ya zama iska mai sanyi wadda ke tashi hade da yar qura,tana kammalawa tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar rigar yan kanti mai roba roba red ce ta sauko mata har qasa ,daga gaban rigar wajen qirji an kamata an mata tattara yayin da ta bude sosai daga qasan aka jera wasu irin dutsuna manya guda uku masu garai garai da qyalli hannun vest ne da ita saboda haka ta sanya long sleeve shirt fara ,tayi rolling da farin mayafi wanda acucin da tayi da gashinta ta mai doughnut ya taimaka wajan qarawa rolling din nata kyau iya kafadunta mayafin ya tsaya,qananun fashion na barima farare ta saka sannan ta jawo takalminta slippers na fata shima fari ne,wayarta ta dauka ta kulle bangaran nata
Yauma da keys dinta tayi amfani ta bude gurin,shiru yake ba motsin komai hakan yasa tayi tsammanin bacci yake,hakanne kuwa ta gani sanda ta leqa bedroom din nasa cikin sanda,yana kwance tsakiyar gadon duqunqune cikin farin lallausan bargo ,gefansa daga qasa dardumarsa ce qur'ani da kuma carbi 📿akai,yayi mata kyau sosai aliyyi gwanin kyau kome yakeyi kyansa fita yake,baccinsa yake verry calmness fuskarsa tayi fresh,sai ta lumshe ido tana tuna da yadda daren jiya tayi nata baccin cike da kewa da azaba,amma shi yanzu gashi yana nasa hankalinsa a kwance har da qarin wani na bayan sallar asuba kenan,ta dauko wayarta ta kashe plasher dinta tayi snapshot din fuskarsa,ai kuwa ta fito shar zara zaran gashin idanunsa sun kwanta luf,tayi kissing din hoton sannan ta juya ta yi kitchen
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
▶3⃣1⃣
Chips ta soya hade da wainar qwai sannan ta dama masa kunun gyada da ya sha madara yayi fari qal sai zuba qamashi yake,sannan ta bare indomie ta yi masa awarar indomie,nan fa qamshin abincin ya karade gaba daya falon har cikin gidan to wani ma yayi rawa bare dan makadi,fadila gwanar girki ce mayyar kitchen ce tun tana gida ma,tana saitin window inda kan famfo yake tana wanke kayan da ta bata ta ke jiyo motsi kadan kadan,windon na cikin lambun bangarenshi da ke bayan part din kowa,tana daga kai ta hangoshi qarfe yake dagawa🏋🏼ya hada gumi sosai,armless riga ce a jikinsa da shortnekeer damtsensa cike da qwanji a murde,ya ajjiye qarfen ya dau dan farin towel dake gefansa yana sharce gumin kana ya dauki bottle na ruwa ya daddaka ya rufe ya koma kan keken training kuma🚵🏻
Ta saki murmushi ta kada kai,da azama ta hada komai ta koma bedroom ta gyara masa ta wanke toilet ta hada masa ruwan wanka,ta budade ko ina da qamshin nan nata sannan ta dawo parlour ta zare rolling din kanta ta fara gyare falon shima ,yana daga can yake jiyo qamshi kala kala na shiga hancinsa da fari qamshin girki ya fara jiyowa ya bude dogon hancinsa yana shaqar sa saboda ya masa dadi daga bisanai kuma ya jiyo wani qamshin qamshin da ya kwana jiya yana sheqa,ya sauka daga kan keken shima ya dauki wayarsa da towel dinsa ya bude qofar bayan ya shigo ta cikin kitchen wanda yasa sauran kadan suyi karo,ta ja baya da sauri tana gaidashi kanta na duqe a qasa kamar kullum bai amsa mata ba dama ta zaci hakan ya dai daga mata hannu🖐🏽ya wuce
A bandaki ya tarar da ruwan wankan nasa,ya dan yi dam domin bai saba ganin hakan ba a tarihin rayuwar aurensa ba ganin tunanin zai bata masa lokaci yasa kai tsaye ya shige cikin ruwan🛀🏼yana sheqar qamshin da yake
Cikim suit ya fito baqaqe masu sheqi sunyi masifar fito da ainihin kyawunsa,takalmi ne half cover dan hasken marun kamar yadda tie dinsa yake marun da jakarsa a hannu fuskarsa saye da fari qal din medicated glass dinsa wanda bai hanawa mutum ganin kyakkyawan qwayar idanunsa,sumarsa a kwance luf baqa sidik sai sheqi take ita ba mai yawa ba kuma ba a aske ba qamshin nan nasa na musamman ke fita a jikinsa,ya dan zauna a hannun kujera yana qarasa taje sumarsa da brush dake hannunsa
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
Afuwa afuwa
Nayi rubutu mai yawa zan turo muku na ajjiye wayar ina dan wani uziri kafin na dawo ya goge,chargy kuma ya riga yayi halinsa,kuyi haquri da wannan ku bini bashi da yardar Allah
Na gode
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:40 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?.....*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣2⃣
Ganin wannan dama ya sanya fadila tayi saurin sauko da kayan breakfast din gabansa duk da cike take da fargabar kada ya gwasaleta,tayi saurin hada masa tea☕ ta daidaita masa zafinsa ta ajjiye masa sannan ta sa masa wainar qwai🍪 da farfesun kayan ciki🍲,taji dadi da baice komai ba ya sauko ya karya,bayan ya kammala ya dauki jakar laptop dinsa💼 ya ciro yan dubu dubu guda uku ya ajjiye mata kamar yadda yake ajjiye wa sauran matan ranar nasu girkin duk da kuwa babu abinda zasu siya komai diba za suyi yana ajjiye,ya yi gaba ta biyoshi a abaya gabanta na dukan uku uku bangaren samira ta ga ya shiga don haka ta ja tunga ta tsaya baifi mintina biyar ba ya fito ya shiga gun salima mintina takwas sai gasu sun fito yana gaba tana biye da shi ganin fadila na tsaye da alamum jiran fitowarsa take sai yanayin fuskarta ya sauya😠 take ta juya ta koma ciki
Har sai da ya shiga mota ya zauna sannan tace a dawo lafiya tayi saurin juyawa ba tare da ta jira cewarsa ba don tasan bazai ce din ba ma idan ma ua fadan to ba mai dadi zata ji ba,tana hango salima da ta yaye labulen falonta tana kallonsu don haka sai fadila ta qorqiro murmushi ta dora bisa fuskarta
Ta rasa hali irin na salimar mutum ce mai tsananin qyashi da hassada ga azabar sa 'ido komai idanunta na kai kamar wadda aka bata aikin yin hakan ita dai samira barta da kishi masifa da tsokalar rigima kuma kana tabata za kuyi uwar watsi agun shikenan duk da haka kishin salima har yafi na samira ita kawai tanada duniyanci da yasa take iya boyeshi ba kamar samira da ba ruwanta ko a gaban uwar waye ayita ta watse ba munafunta
⚜⚜⚜⚜
Haka fadila taci gaba da tsara rayuwarta duk ranar da take da girki zata shiga bangaren ta gyara ko ina da ina,tana kuwa fama da aikin domin tsakanin samira ko salima babu mai iya yin cangal kowacce haka take fita daga girkin ta tabar sashen a ahautsine
Tsakaninta da aliyyu sai girki ta shirya masa daddadan abinci ta zuba masa ya ci idan ya kammala ta kwashe ta wanke kana ta ja qafarta ta bar sashen sai kuma washegari idan ta shigo hada masa breakfast,da zarar kuwa kwanakinta ya qare bata bi ta kan kowa da zarar ta taso a aiki ta shiga sashenta ta qulle qofa tofa sai washegari zata sake fitowa
Wai inji hausawa sunce jiki da jini kuma mutum da zuciya cikin lokacin sai sai qyamar girkin su samira ya fara kama aliyyun ransa ya soma sosuwa da ganin sam gyara bai damesu ba,har gwara ma.salima tunda at least akwaita da son ado da kwalliya zata yi wankanta tayi kwalliyarta hakanan zata qoqarta ta dafa masa koda jallop ce albarkacin masifar son sa da take duk da bata taba girki a gidansu ,amma samira kuwa babu daya qanwar biyu daga ciki
Cikin harshensa da zuciyarsa yana jin dadin girkinta sosai dandanon da bai taba jinsa ba gun kowa ba baya ga mominsa,miskilanci irin nasa yasa ko a fuska bata taba ganin alamun haka ba,takan tattare masa socks singlet handkerchief three quarters da duk inner wears dinsa harda jallabiyoyinsa da yake sawa ta wanke su tas ta goge su sannan ta feshe su ta turare ta jera masa su to ammafa insha Allahu bayan kwana hudu ta karbi girki zata zo ta tarar da su kamar kamar ba su ba komai an hargitsa shi sai ta soma fuskantar wani abu akwai gayya a ciki ta kuma san bazai wuce su salima ba don adawarsu gane da aikin nata a fili yake qara ra wani lokacin takan jiyosu suna yan qana nan maganganu takan sharesu taqi tankawa don basu tari gabanta sun gaya mata ba bare ta kula da shashancinsu
Abu daya ke qona mata rai aishi aliyyun na gani suke batawar shin bazai tsawatar musu ba idan su basu da tunani?
Ga misali a farkon fara aikin nata kafin su soma adawarsu takan tsince kayan aliyyu ne kawai a dakin a watse takan gyara ba tare da ta damu ba tunda tasan aikin ta ne dama,da tafiya ta soma nisa sai suka dinga barin brassiere panties sleeping dress underwear 👙👗musamman salima wadda kullum sai ta tsince nata tunda samira ke fara girki sai ita wanda a qa'ida fadila ce ya kamata ta zamo mai girki a farko amma suka maida ita ta qarshe ta qyalesu duka ta zuba musu ido ,tasan da gayya take zub da kayan,zuciyar fadil na matuqar baci da hakan,a duk lokacin da ta tsinci kayan takan bata lokaci mai yawa tana qissima dalilin barin kayan daga jikin mai su wanda hakan ke qara ta'azzara kishinta ga aliyyu
Wani sabon rainin hankalin kuma sai ta fuskanci ya shigo ta soma gyaran sai ta shigo tace"☺sorry fa don Allah,jiya na mance kayana akan gado wallahi dear ne ya rudani daren jiya shi yasa da safe na manta da su ban dauka ba,kinsan shi akawai nacin abun,sai dai fa ba sauqi shima fa gwani ne😉"wannan ya bata ranta fiye da abinda tayi mata,har ta soma hasashem anya basu da masaniyar babu abinda ya taba gilmawa tsakaninsu?
Akwai lokacin da ta zube har da magungunan mata maau dauke da hotunan banza,wannan fadila maganinta tayi ta dauko mata wasu wanda wata maqociyarsu a acan gida ta bata ita basonsu take bame ma zatayi da su tunda ta bata ta jawo locker ta watsasu sai yau ta tuna da su ta qara mata tace ga wasu sai ki qara naga naki basu kai wadanan tsada ba ni kinsan bana amfani da su halitta ta bata buqatarsu komai nawa yaji ba sai da kwaskwarima ba"jiki a salube ta karba duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi nata kyau to tun daga ranar bata sake bari ba
samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata dauko plates ne🍽 kofuna ne🍶 da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda ce ta chewing gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa babu mai aikin gyara gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta isheta kallo a cikinsu
Su kansun so suke ta kulasun amma ta qi basu wannan dama
Mrs muhammad
📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
01:18 pm 05/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
▶3⃣3⃣
Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga ma'aikata to haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office kuma bata da girki,la'asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga shigar da tafi so kenan ta material ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling dinta kamar yadda ta saba da jan mayafi,takddunta ta diba 📄📉📈 na aikin office da takeson dubawa zata yi wani aiki a kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin matashin kujerarta ta zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira zaune kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima📖 samira kuma na riqe da wayarta📱 tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga zama ta fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara cin karo da baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa ya kalli dan uwansa ba
kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayarta📱taga biyar harda rabi da minti uku bata da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi yayi yawa sanadiyyar hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara tada zafin garin,ga injinsu yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa yana fama da shi kasancewar ba dan qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu heater a.c da sauransu sun riga sun saba da wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri da gada?_,tayi bismillah ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai cika ba da zaman nata samira ta soma receiving call "shegiya kina duniya?......heeeee wlh gamu a cikinsa muna gogawa.......hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba"ta danyi shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace"a haba haba ke sai kace ba nice samira ba?.....k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya sai ta kama gabanta da qafafunta🏃🏽 ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake hannunta tamkar da gsken karatun take tace"qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan kansa,samira ta sake kecewa da dariya "wlh har mai share share da goge goge ita wannan ai ba wahala zata bani ba.....yo hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a gunsa
Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece kuce da wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan tunani sai ji tayi tas!
Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen marin,aikin salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana huci,tuni samira ta katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta dora mata da bayani👉shiru shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki bar ganin kina min kina samun nasara wallahi kin kaini bango nifa ba sa'ar yinki bace don uwarki"tasa yatsanta tan nuna qirjinta👆🏼 tana cewa"ni kika mara?"😁an marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin ma,kina tsammaninke kaďaice tantiriyar karuwa ko?💁🏽to 👆🏼nima karuwace nayi nayi kuma yaqon duniya fiye da naki ke da kika local ma
😳😳mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi yawon karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwomù da har karuwanci ya zama abun ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucenta📝taqi kola kowaccensu tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu cinye junansu 🎭
Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki🔐,ta dago da hazari don ganin mai ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya ahigo kuma baau ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar kaiwa juna duka👊🏻,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa 😢wallahi tallahi ban kulata ba itace ta fara takalatakuma ka tambayi fadila"jin sun sanyo sunanta cikin sha'aninsu ya sanyata azamar taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya kai dubansa😒 gun da fadilan take da salimar ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta ta juya ta shige sashen nata ba tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu ya bita da.kallo👀 karon farko wani abu daga garetà ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta shige ta kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta gudu🏃🏽ta rufe itama qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu😡 a akanta don ta tabbatar In dai ya bincika ya tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan sanyi yake ma hukuncin da zaka raina kankà babu duka ba zàgi bà baqar magana,ya juyo ya dubi saluma da jikinta ke rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa part din
⚜⚜⚜⚜⚜
Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al'adar gidan fita aiyàyya a iřin lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum
Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan
Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta kammalà komai ta kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta jiýo tashin horn ta tabbatar aliyyu ne don bai son jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci gaba da hirarta da ummin tasa daya hannunta dauki jakarta🎒ta sa mèy ta kulle sashin,ta qarasa jikin motar tana sallama da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga salima da samira tamakar an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon fadila tayi azamar matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta🙊 dariya na shirin subuce mata😂,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne
😂😂😂😂😂
Ku biyo *mrs muhammad*
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 12:41 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣4⃣
Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya juyo don ganin meke faruwa haka ake shirin cire masa hannun mota?cikin tsawa musu su matsa masa daga jikin mota,bai wata wata ba ya figi motarsa ya barsu a gun sake da baki😦,gudu yake zubawa abinsa bisa dukkan alamu ransa ya baci,duk sai fadila tayi tsuru-tsuru don da irin wannan gudu da yake zabgawa gwara ya sauketa salun alun ,
Qiiiii...taji ya taka burki,ya gangara gefan titi ya faka motar cikin shaqaqqiyar murya taji yace"fito ki dawo gaba don ni ba driver din gidanku bane😠"bata ce kanzil ba ta dawo gaban
Yanayin zaman yayi wa fadila kusa sosai,mayen turarensa ya soma raba mata hankali,lissafinta ya soma qwacewa take kasala ta saukar mata,wani shauqin aliyyun ya mamayeta duk da azahiri idan ka kalleta zaka yi tsammanin ko inuwar sa bata gabanta
Sun isa shoprite inda suka saba siyayyar duk qarshen watan,ta san tsarinsa bai shiga yana tsayawa ne a waje yayi zamansa cikin mota,da sun gama siyayyar ayi masa total a turo masa list da amount,da yake yana harka da su akwai kamfaninsa dake india wanda akwai hurdar kasuwanci tsakaninsu,"u have twenty minutes idan kima gota haka so sai ki nemi motar mai da ke gida"ta jinjina masa kai duk da idan da sabo yaci ace ta saba don duk sanda ya kawosu mintina ashirin din yake basu basa kuwa darawar domin dukkaninsu sun san halinsa yana iya tafiyarshi
A nutse ta shiga ta duba muhimman abubuwan da take buqata don tana lisaafin jibi ita zata karbi girki duk da ba wani tsiya bane a ciki banda tsabar bauta ta gyare gyare da dafa masa abinci wanda sau da yawa tare suke cinyewa da samira da salima ,sukan daidaici lokacin cin abincinsa ne su shigo da nufin sun zo taya shi hira sai kuma su taya shi lamushe abincin
A gurguje ta kammala zabar duk abinda tasan bata da shi ba wani kaya ne mai yawa ba tunda bata iya gama amfani da siyayyar tsohon wata suke sake sabuwa saidai ma wani abun ta bada shi,sai ta soma dibarwa salima da samira abinda ta lura sunfi siya yawancin lokuta idan suka zo,Allah ya taimaketa minti goma sha takwas ta gama komai,ta riqe leda daya ragowar aka biyo ta da su
Tana fitowa suka yi kacibus da shi yana tsaye a hanyar wucewar tata,shi da wata matashiya ce wadda a qalla shekarunta ba zasu gaza ashirin da shida ba,abunda ya bata mamaki shine ganin hawaye bibbiyu bisa fuskarta😭,ta maida dubanta garesu a karo na biyu daidai lokacin da aliyyun ya nuna ta da yatsansa yana cewa "👉 this is d last warnings da zaki sake bina wani guri ki kama kanki tun kafin ya gudu ya barki and respect ur self"
😳Sai taga kawai ya sa hannu ya rungumota kafadarsa sassanyan qamshinsa ya buwayi hancinta suka bi ta gabanta suka wuce,cikin mamaki fadila ta waiwayo still tana tsaye tana binsu da kallo hawayen na bin fuskarta😭,ta sake fashewa da kuka a guje ta nufi motarta ta fada ciki🚗🏃🏽,
Daf da zasu qarasa cikin motar wadda tuni an kammala zuba kayan taji ya tureta daga jikinsa ,ta tsaya a baya sai da ta bari yayi gaba sannan ta biyoshi,zaman kurame suka sakeyi cikin motar har suka isa gida
Ta kammala shirin baccinta ya sanya night gown sannan ta dora dogon hijabinta mai hannu da ya sauka har saman qafafunta ta sanya sannan ta kwashi ledojin da ta yima su salima ta su siyayyar ta nufi sashensu,saidai ta tarar dukkaninsu basa nan don haka zuciyarta ta bata amsar ba zasu wuce sashen aliyu ba
Can kuwa ta tarar da su kowacce ta debi fushinta akan ya wulaqantata ya tafi ya barta taje masa da shi ,basu san ya fisu fushin ba don haka ci kanki ba wadda ya gaya mawa a cikinsu ya watsar da su a falo ya shige dakin barcinsa ya shiga wanka,sun sani ba wadda tayi gigin binsa ciki tunda suka ga ya musu banza to da tashi da su nan suka jibge a parlour zaman jiran sa,har ya fito ba wadda ya kalla ya haye dining yana fama da girkin salima wanda,farar shi kafa ce tsura babu salad ko cabbage bare akai ga batun nama,cikin qufula ya kira sunan salima da suke zaune suna fama da 'yar harare harare,bisa kansa ta tsaya ita dole wadda akayiwa laifi ce tace gani😼,ya dora gwiwar hannunsa saman table din ya hade yatsunsa cikin juna ya dora habarsa a tsakiya sannan ya kalleta yace"😒 sau nawa nake gaya miki I don't like such cooking?,ko kayan cefanenki sun qare ne?ko sun qare ba zaki iya sanarmun ba kenan?,ta tabe baki ta kawar da kai tace "kayi haquri "ya danyi shiru ya dafe kansa kamar ba zaice komai ba,har ga Allah ba don yunwa ba baiga dalilin da zai sanya shi cin wannan abincin ba,ya shiga tuna irin dandano mai gansarwa da yake samu duk ranar girkinta,ya dago kai yace bude fridge dina ke debi cabbage da cucumber ki yankamin ki hada min da dafaffen qwai tunda yau ban isa naci nama ba"ba tare da ta amsa ba ta juya
Mrs muhammad👑👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
5:44 pm 5/11/1437
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?......*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
▶3⃣5⃣
Da sallamarta ta shigo falon sam bata ma lura da shi ba bisa dining,ta dan dora murmushi bisa fuskarta🙂,salima ce ta masa sallamar itama ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki,ta qaraso gabansu ta direwa ko wacce ledarta🛍 a gabanta tana cewa"sannunku,ga siyayyarku nan Allah yasa na haso muku da abubuwan da kuke buqata " salima shiru tayi saboda tafasa da zuciyarta keyi,yayin da salima yar takife tace" waye ya saki sarauniyar masu shishshigi ,kina murna kina rawar kai an koro mu ke an tafi da ke,shine don digimi da neman gindin zama harda wani yi mana siyayyar kaya ko?to ahir dinki wlh ni ba'a shiga gonata don kiji na gaya miki,har wata fada ce dake a gunsa banda ta shara da zaki mana rawar kai?ko an gaya miki sonki yake?"
"Hmmmm matar cushe kenan"cewar saluma da bata tofa ba sai yanzun,cikin wani irin mamaki da al'ajabi ta dago tana dubansu,meke faruwa?a ina suka san wannan ?haka aliyyu ya gaya musu cewar ba aonta yake ba?,wannan wane irin kwance zani a akasuwa ne?,wanne irin cin kashi ne haka yayi mata?"take idanunta suka sauya launi,wani irin fushi da bata tsammaci tana da shi ba ua sauko mata😡😣,kamar hadin baki suka miqe suna shirin barin dakim don dama haushin kaza ne huce kan dami,tunda sunsan ko giyar wake suka sha basu isa su juye haushinsu ba kan wanda ya musu laifin sai suka juyeshi kanta,suna shirin ficewa suka jiyoshi cikin lion voice dinsa yana kiransu "😠ku kwashe kayan nan daga gun nan ku bace min da gani"kunnen uwar ahegu sukayi niyyar yi a zafafe yace da su"👉�billahil azim duk wadda tabar ledarta a nan tamu ce ni da ita"tilas kowacce ta waiwayo ta dauki tata tabar sashen
Cikin matsanancin bacin rai ta dago kantasai suka hada ido,wani baqinsa ta gani wanda bata taba ganin yayi makamancin haka a idanunta ba,kafin ya janye idanunsa ta fara janye nata tayi azamar juyawa ta bar sashen
Kusan kwanan zaune tayi ,babu abinda ranta bai gaya mata ba,abunda take ta qoqari da fadi tashin bunneshi ashe ya dade da yin tsiro har yqyi yabanya?tabbasa aliyyu ya cutar da zuciyarta ya cutar da zuciya da ke cike da qauna gami da begensa cikin kowanne fitar numfashi na dan adam,tabbas a ayu badon mutum bai da ikon cire son wani daga zuciyarsa ba da itakam ta ciro har zuciyar ta wurgar ta huta ma gaba daya,ranar idanunta basu ga bacci ba sai tunani data takurawa.kanta da shi wanda ya haifar mata da da ciwon kai da zazzafan zazzabi,ba ita ta samu kanta ba sai washegari da la'asar bayan ta takurawa kanta ta cire damuwar ta ajjiyeta gefe
⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin qyanqyami yake shiryawa,gaba daya dakin ya hargitse sun kuma barshi kamar yadfa suka saba,sai dan yakanji relief idan ya tuna zaije ya dawo ya tarar da komai ya zama neat,da hanzari ya kammala ya dauki jakarsa💼 ya fice ba tare da ya saurari breakfast da salima ta hada ba ruwan tea ne fari sol babu citta bare kanunfari sai soyayyen qwai wanda qarninsa ke hanashi hadiyarsa,shi kuma akwai qyanqyami yayin da su kuma basu maida tsafta 💄👠👒💅🏽da gyara wani abu mai muhimmanci ba
Sanda ya dawo ya tarar da sashen nasa yadda ya barshi yayi matuqar mamakin hakan,don bai saba ganin haka ba,yasan ranakun girkinta zai tadda komai a kintse hakanan yaji ransa ya baci da ganin haka,ya zube anan saman kujera yana fitar da iska mai zafi daga bakinsa,ya dubi agogon hannunsa qarfe shida da arba'in har da hudu,mintina qalilan suka rage a shiga masallaci sallar magarib,a kasalance ya duqa yana zare sau cikin qafarsa👞hadi da sabule safar,wata bahaguwar yunwa ke rarakarsa,yinin yau gaba daya ba abinda yaci banda maltina mai sanyi da ruwa da yake ta dirka,saoda yana da yaqinin zuwa ya tadda abinci mai kayau🍛,
Kai tsaye ya shige toilet ya dauro alwala ya dawo falon yana goge ruwan jikinsa da handkerchief,gidan🏛 tsit sai hasken fitilu da ya gauraya da duhu suhun magariba da ya soma kawo kai ,ya dan lumshe idanunsa kewar qanan yara na shigarsa👫,ya tabbata da yana da su da zai dinga jin koda hayaniyarsu ce da gilmawarsu ,ya riga ya saba da tsabar qwarewar.matan gidan wajen iya rashin kula da miji,ya katse tunaninsa sanda ya jiyo kiran salla a masallacin dake can farkon layinsu ya sanya silifas ya fice yana maìmaita abinda liman ke cewa kamar yadda annnabi ya horemu idan munji kiran salla
A can ya zauna ya jira sallar isha'i sannan ya dawo gidan,still gidan dai na nan kamar yadda ya barshi kowa na kulle a sashensa,ya dauki wayarsa ya kira nasiru ya gaya masa inda zaije ya samo masa masa da miyar ganye,cikin lokaci kadan saiga nasirun ya dawo ya amsa ya koma ciki yayi wanka ya sauya kayan bacci,ya zuba masar ya ci sai da ya qoshi sannan ya jawo computer💻 dinsa ya soma shigar da lissafinsa na yau,hankalinsa ya kasu kashi biyu,ko alama zaman gun ya gundireshi sabo da tsaftar gun bata masa ba,shigowar saluma ce ta saka shi tsai da abinda yake ,ba laifi salima indai ta bangaren qalqale jiki ne salima ta iya wannnan kam,yanzun ma ashirye take cikin dinkin lace baqine mai adon ja,ya sauke biron dake hannunsa
0 comments:
Post a Comment