Sadiya ta dafa kadar salima tace to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace ashe dai kin fara gano gaskiya ta🙄"
Sanda ta shiga yana zaune gaban na'urar tafi da gidanka yana qarasa aikin sa da dazun yunwa ta hana shi yi,sallama tayi ya amsa kansa na kan allon computer din,kujerar dake gefansa ta samu ta zauna,kusan mintina sama da ashirin bai ce mata kanzil ba don haka itama ta bude wayarta ta soma register din watsapp saboda yanzu as journalists tana buqatar wadannan kafofin sadarwar,
duk da basu dameta ba don ba yadda farida batayi da ita tun a gida ta bude koda watsapp ne kawai ba amma taqi tafi ganewa karance karancen magazines da wasu rubuce rubucen
Cikin yan mintoci qalilan ta kammala da account dinta na watsapp ta soma qoqarin hada na facebook,falon yayi tsit kowa ya sanya na'ura a gaba,lokaci lokaci takan daga ido ta saci kallonsa,qayatacciyyar fuskarsa da hasken screen ya sake hasketa tayi fresh,ta zubawa hannayensa ido yadda yake sarrafa computer din cikin qwarewa da da gwanancewa typing yake cikin sauri tamkar shi ya qera computer din yasan madannin kowanne abu abun sai ya burgeta sosai
Wayarsa ta soma ringing ya dauke kai daga kallon fuskar computer din ya maidaa idonsa kan wayar ba tare da ya daga ba,baquwar numbace kuma bai dagawa,kira aka ci gabaa da yi akai akai har ya gaji ya danna ok ya dora ta bisa computer ya sanya ta a hands free
Muryar mace ce "hello ranka ya dade" "salamu alaikum wake magana?"ya fada hannayensa na saman laptop dinsa yana aikinsa,"daga daya bangaren aka sake maqe.murya"suna na nadiya ina kiranka ne daga unguwar rijiyar zaki kano"bai maida hankalinsa ba kan wannan yace"me kike nema?"aka danyi jim har yana shirin kashewa sannan akace "don Allah ka rufawa zuciyata asiri kada ka kashemin waya domin kashe wayar tamkar kashe ni ne"ya tsayar da abinda yake sannan yace "uhm go on" aka saki ajiyar zuciya sanna tace "maitama Allah ya jarabceni da tsananin qaunarka wadda tasa na kasa jure hakan cikin zuciyata har sai bakina ya furta maka,ina roqonka don Allah ka taimakeni ka so........" "hey!"ya daka.mata tsawa "stop that,rubbish!"tsit tayi,ya ware idonsa kamar tana gabansa yace"ke baki da ajine irin na mata?" Shiru ba amsa don haka ya dora "let me tell you baki da shi,and inason gargadinki wannan ya zama na qarshe da zaki kira numberta,I hope kin fahimta ko"ya katse kiran hadi da jan tsaki,fadila tayi saurin dauke kanta lokacin da ya dago kansa taga tamkar ita zai kalla zuciyarta na wani irin bugu,kishi ya tokare mata qirji,ta lumshe ido bugun zuciyarta na qara sauri.......
Mrs muhammad dinku ce😘
[8/25, 3:44 PM] +234 812 673 9684: 5:55 pm 16/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*wa yasan gobe?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
3⃣~4⃣
Kusan kimanin minti biyar idanun nata na lumshe ta kasa budesu saboda wani abu da takeji a jikinta wanda tasan baya rasa nasaba da tsan tsar kishi,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya sannan ta bude idonta ta dora su bisa screen din wayarta tana ci gaba da qoqarin kammala bude account nata na Facebook duk da wani bari na zuciyarta na ci gaba da mintsininta,cikin zuciya lallai ta godema Allah da bai qaddara ta zubda ajinta ta bayyana abinda ke zuciyarta ba har ta kai aliyyu ya fuskanta bare ta samu nata kason cin zarafin kwatankwacin wannan wanda it may break her heart
Tabbas ta sake yarda cewa so masifa ne musamman son da hausawa kema laqabi da son maso wani,babu irin baiwar da tabbas bata da ita iya kyau Allah ya mallaka mata shi ilimi hankali da nutsuwa,tasha jin mata yan uwanta da yawa na yaba ta bare tarin maza dake kara kaina a kanta
Ta sake satar kallon nasa wannan karon maimakon ta tadda shi yana aiki kamar dazun yanzun takardun na watse ne a gabansa ya jingina kansa harda bayansa a jikin kujera dukkanin tafin hannunsa ya tallafe bayan kansa da su idanunsa na rufe,gashin idonsa yayi ma idon rumfa tamkar an jera su
"Bani abinci"ya fada idonsa na a rufen,ta miqe ta shirya masa komai still dai idanunsa na arufen har ta gama ta koma ta zauna,a hankali ya bude idonsa ya kalli warmers din"u mean ni zan zuba kenan da kaina?"😒 ta girgiza kai sannan ta taso ta zuba masa white rice ce da miyan kaza sai hadin coleslaw tana kammalawa ta miqe da niyyar fita "ina zaki je?"ya tambayeta cikin izza,ta kawar da kanta sannan tace "sashina zan koma" yaci gaba da cin abincinsa sai da ya mula don kansa sannan yace "ban baki izini ba"cike da haushi da takaicin irin mulkin da yake mata ta koma da baya ta zauna kanta a qas
Cin abincinsa yake with calmness ba abunda ya dameshi ya shanyata abunsa,har ya kammala bai dubi sashenta ba already ta soma gundura da zaman ga bacci ya soma mamayarta ga kuma fita office gobe early,sai da ya kammala duk abinda yake har ayyukan da yake shigarwa cikin laptop dinsa apple sannan ya tattare kayayyakinsa ya maida jakar laptop din yana shirin shiga bedroom dinsa yace da ita"ki hadomin coffee ki kawo min"
Kamar zata fashe da kuka☹ ta shiga kitchen cikin mintina biyar ta hada masa ta juye cikin cikin wani set din butar shayi irin na larabawa na silver da cups dinsu yake hade da tray
Hade da sallama ta shiga dakin yana cikin lallausan bargonsa cikin shirin bacci ba haske a dakin sai na fitilar gefan gado,yana receiving call har ta shigo ta isa bed side ta dora plate din daidai lokacin da ya kammala amsa wayar ya kasheta gaba daya ya cillata bayansa tana tsaye har ya kammala addu'o'in bacci sannan ya juya mata baya yana gyara kwanciyarsa hadi da jan bargonsa "kina iya tafiya" dama a gundire take Allah Allah take ta bar masa dakin ta juya ta fice abinta
Tana shiga bedroom dinta nightgown kawai ta sanya ta fada gadonta tana addu'o'in kadan kadan har ta gama,a hankali ta lumshe idonta tana da muradin yin bacci amma ina sai tunanin da akullum yake zame mata na qarshe a rayuwarta shi ya lullube qwaqwalwarta,duk yadda taso bacci yayi awon gaba da ita abun ya faskara har sai da ta dade tana ninqaya a duniyar qaunar aliyyu haidar sanan baccin yayi awon gaba da ita bacci ne mai cike da mafarke mafarken aliyyun
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Cikin hukuncin ubangiji rayuwar ke tafiya da bawa wani lokaci ta zo maka uadda kake so kake tsammaninta wani lokacin kuma ka samu akasin haka yau fari kenan gobe tsumma jibi nasara gata asara duk cikin hukuncin ubangiji ne da yadda yaso rayuwar bayinsa ta kasance,to bawa mai cike da tauhidi da imani sai ya godewa masa don kamar yadda haka yake ga fadila,shekararta guda kenan cikin igiyar auren aliyyu,shekarar da ta ga abubuwa daban daban ta fuskar qalubale da nasara
Zamu iya cewa babu wani abu da ya sauya dangane da salon mu'amala da alaqa dake gudana tsakaninta da shi baya ga wadda muka riga muka sani,nasara daya ce zata iya daga hannu🙋🏻 ta fadeta cike da alfahari shine duk cikin samira ko salima babu wadda take iya sarrafawa aliyyu girki da tsaftar muhallinsa kamar ita
Abunda suka fi qwarewa ciki sune kowacce ta fito tana tunqaho da hura hancin Aliyyu yafi sonta akan sauran 'yan uwanta,takan kau da kai cike da yakanah tayi kamar bata san abinda suke yi ba,wani lokacin kuma sukan bata dariya har ma ta murmusa takan daukesu ne a matsayin wadanda basu san mai ya kamacesu ba duk da kuwa duk sun bata wasu shekaru sun kuma girmemata sosai tana ganin tutiya bata kamacesu ba a irin wannan rayuwa da suke,ta sanu da gayya suke mata wani abun ganin cewa bata taba daga ido ta kallesu ba bare suyi 'yar tankiya
So suke ta zamo daya daga cikinsu domin kuwa fada tsakaninsu sun koma tamkar 'ya'yam tumaki har bangarenta tana jiyo hayaniyarsu,sukan ji kasiririt ne idan aliyu yana gida don ko giyar wake suka sha a yanzun basu fada gabansa tun tuni yayima tufkar hanci ya kuma tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta kuma ji din saidai su yita 'yan habaice habaice wadanda shi da yake namiji me bai ma fuskantar me suke
Ta riga tuntuni ta saddaqar da cewa soyayayyar aliyyu wani gine ne daga Allah cikin zuciyarta,tayi imani koda bai sonta ba koma zai sota din ba kamar yadda yayi mata tunqaho Allah bazai taba wofintar da ita darajar biyayyar aure da take hidima a gareshi da kayutata gami da girmama buqatunsa,duk da babu wani sauqi da take ganowa a tattare da aliyyun amma har kulluma tana bawa kanta confidence kan hidimar da take masa especially a duk sanda haduwa ta hadasu da uncle abba momi abbanta ko umminta taga yadda suke nuna jin dadinsu har yau da wannan aure nata sai taga zata iya ci gaba da faranta ransu indai hakane
Saidai abinda bata sani ba shi kansa yakan samu kansa cikin nutsuwa a duk ranakun da suka zamo nata ne ko banza ya san yana sakewa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma cike da gamsashshen dan dano irin wanda yake so duk da babu ruwanshi da ita,some times ma kafin ya dawo ta hada duka abinda yake so ta bar masa bangaren,mutum ne aliyyu maciyin abinci bao wasa da cikinsa ko kadan hakanan halittarsa take,duk qwaqwar mutum bai isa yayi indication wasu sign da zai nuna yana jin dadin hidimarta ba
Mrs muhammad dinku ce😘😘😘
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[8/25, 3:45 PM] +234 812 673 9684: 5:08 pm 20/08/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
5⃣~6⃣
Cikin watannin da basu gaza biyar zuwa shida ba fadila ta samu gagarumar nasara ta bangaren aikinta,nasarar da bata taba tsammanin zata sameta in a few months ba,ta soma aikine cikin sa'a,farin jini sosai take da shi,sunanta ya fara fantsama cikin al'umma shirye shiryenta sun samu karbuwa matuqa da gaske,ki ina ka zaga zancan matashiyar 'yar jarida fadila Abbas wakili ake,ita kanta tana mamaki with her few age ta samu daukaka haka,saidai da yake mai hankali ce takan godewa Allah domin tasan babu wanda ya isa yayi mata haka sai Allah,hakan yasa ta sake daura damarar riqo da aikinta cikin qwazo amana da kuma gaskiya da kuma manufa kyakkyawa da zata kawo gyara da ci gaban al'ummarta,bata mantawa da ya ahmad da abbanta wadanda su suka jagoranci samuwar ci gaban nata
Bayan ta kammala duk wasu ayyukanta kamar yadda ta saba,ta shirya masa komai hatta da tissue bata barta ba,sauri take ta yi ta fice daga gun kafin dawowar tasa,saidai kash bata ci nasarar hakan ba don kuwa a bakin qofa suka yi kacibus kadan ne ya rage basu bige juna ba,da sauri taja da baya tana shaqar numfashin ta dake gudu sakamakon tsoratar da tayi,qasa tayi da kanta tana murza tafin hannunta gami da cewa "sannu da zuwa"
Kusan minti biyu taji shiru shi bai wuce ba ba kuma alamun juyawa yayi,ita kuma ya bashi dama ne ya fara wucewa duk da sauri da take ta koma bagarenta ta cire pad din jikinta ta sauya wata,ta dago kanta don taga me yakeyi ne haka yana tsaye hankalinsa kwance kamar bai tsarawa kowa hanya ba don bashi da wani alamu na matsawa hasalima tie dinsa da coart yake cirewa a nutse
Ganin haka yasa ta raba gefansa don ta shige ashe bata sani ba ya sanya mata qafarsa dake saye cikin sau ciki👞sam bata lura ba don hankalinta yayi gaba,luuu tayi baya ya goce sai kuwa ta bugu da qofan falon ,cikin azabar radadi ta dafe gun ta dago a hankali ta kalleshi sai taga tamkar ma baisan mai yayi ba agogon hannunsa na gucci yake cirewa,malolon takaici ya kama mata maqogaro tuni kuka ya kufce mata tasa kai tanashirin bar masa gun tana dafe da goshinta
Ji tayi ya jawota baya ta dawo tayi kamar zata sake faduwa Allah ya taimaketa ta tsaya da qafafunta bayan taga tagar da tayi "sama fa qasa ya kalleta sannan yace "😠baki da kunya ko?,ni zaki buge ki wuce kenan?"tafin hannunta tasa ta kate fuskarta tana ci gaba fa kukanta shi kuwa ya zuba mata ido ba tare da ya sake cewa komai ba, sai da ya gama ikon nasa don kansa ya kauce tare da wucewa ya bar gurin
Da gudu ta fice tana ci gaba da kukan ta wuce bangarenta,dispenser ta kunna tayi heating gurin sannan ta koma bisa gadonta ta kwanta tana maida ajiyar zuciya,me ta masa?ma ta tsare masa banda tsabar cin zali kawai don ta rabe zata wuce sai ya mata wannan muguntar?" Ta danyi qwafa kadan a ranta tana ayyana zata rama
⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Su biyar ne zaune cikin office din fadilan sai fauziyya fa'iza aisha da halima dukkaninsu abokan aikinta ne matasa ne son saidai duk sun girmemata aqalla zasu bata shekaru uku zuwa hudu,amma nutsuwa da kaifin hankalin fadila yasa ta saje cikinsu suna jin dadin zama da ita sosai duk da miskilace saidai akwai karamci da mutunta mutum
Hira suke gaman da zamantakewar aure irin hirarmi dai mata da aka sani wadda matuqar mayan aure suka wuce biyu aka hadu sai an yita,hira ce ta qaruwa ba banzar hira ba wadda bata kamata ba,duk da haka fadila na gefe don bata da abun fadan saidai jifa jifa takan ce wani abu
Hira tayi nisa fa'iza ke basu labarin wata maqociyar yayarta 'yaf nijar dake saida magungunan mata masu kyau na gargajiya wadanda basu cutarwa,dukkansu suka ce ayi kiran matar suna so fadila kawai ta rage,fa'iza ta kalleta"ke ba ki siya fadila wlh maau kyau ne"murmushi tayi tana neman qaryar da zata gilla musu,don ko ta siya me zata yi da su,ta kalli fa'iza "to a hado da ni ga nawa kudin"ta nude zif din jakarta ta fito da kudin,fa'izan ta kuma cewa idan ma bakiso akwai wani hadin tutare mai tada sha'awar mai gida sai a kawo miki shi"cikin basarwa fadila tace"a hadomin duka kawai"(kaji fa mai karatu kamar gasken tana da buqatarsun 😜😜)
Take fa'iza ta kirata ta sanar mata,ta kaahe wayar tana dubansu tace kun taki sa'a don gata nan ma anan kusa don tana ja'en,cikin minti talatin sai gata kowacce ta karbi nata ta sanya ajaka
Qarfe biyar ta soma hada kayayyakinta tana sallama da su zata wuce gida don ta kammala aikinta ,wayarta dake aljihun bayan jakarta ta dauki qara alamun ana nemanta *sister ta* ta gani bisa screen din hakan na nufin farida ke kiranta,da sauri ta daga hadi da yin sallama,"sister ki taho kiga baby girl mai kama da ke kamar copy naki akayi na haihu yanzu haka ina gida"wani tsalle fadila tayi hadi da qaramin ihun farinciki sam ta mance a office take ba a gida ba sai da taga su fauziyya sun taso suna tambayarta mai ya faru sannan ta tuna ta maida wayar tana dariya cikin doki tace junior sister na ce ta haihu wlh"suka mata barka hade da dariya suna cewa saura ke kenan,murmushi 😊kawai ta musu ta saba jakarta tana cewa"Allah ya bamu alkhairi"ta kama kumatun yarinyar fauziyya tana mata wasa har ta fice yarinyar nata kuwa bangala mata dariya don fadila akwai son yara yarinyar ta soma sabo da ita yauma sa'a akaci bata sa kuka ba da zata tafin
Da dokinta ta shiga motarta da niyyar wucewa gidan farida kai tsaye,har ta kunna motar ta tuna cewa sai fa ta sanar da aliyyu,take
murnarta ta ragu tamkar an zare mata laka ta kashe motar,ta jawo hand bag dinya dake kusa da ita ta ciro wayarta ta bude sannan soma searching number'n sa cikin contact dinta wadda yayi mata serving da kansa ranar da bata da lafiya,tayi attempting din kiransa yafi sau goma ta kasa,sai ta fara dialing sai ta katse da kanta,bata san answer da kuma result da zata samu ba
Daga qarshe taga hakan bazaiyi mata amfani ba sai kawai tayi shahada ta kira din,yadda wayar ke qara yin din din haka zuciyarta ke bugu,idanunta a rufe gam tana jiran wayar....
Mrs muhammad dinku ce👑👑👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
7⃣~~8⃣
"Assalamu alaikum" dakakkiyar muryarsa ta doki dodon kunnen fadila,numfashinta ya dan dakata na wucin gadi,komai da ya danganci aliyyi jinsa yake har cikin jininta da bargo komai qanqantarsa kuwa,"hello waye ne?" Ya sake maimaitawa, "idan mai kira baida abun fada zanyi rejecting I have a lot to do"dadi muryar tasa ke mata har can qasan zuciyarta,zata so ta dawwama tana sauraren muryar idan da halin hakan,din din din da taji sau uku shi ya tabbatar mata ya katse wayar kamar yadda ya fada tun farko,ta saki wani dan murmushi da ya tsaya a kuncinta tana kallon fuskar wayar tata,tazarar minti biyar ta bayar sannan ta redial din number tasa
Tana daf da tsinkewa ya daga wannan karon ita ta fara yin sallamar ,yayi dan dum sannan ya masa a daqile sanan ya dora da "who's on d line?"cikin in ina ta soma magana don gaba daya dakiyarsa ta rudata "nice" "kewa"ya maida mata da tambaya,"fad...fadila"ya sake shiru na yan sakanni har tana tsammanin ko baya kan layi ta duba wayar sai ta ga yana nan
"What's going on?"ya sake tambaya,wani abu ya dan taba ranta da gaske bai ganeta ba har sai da yayi analysing a qwaqwalwarsa,"sister farida ce ta haihu" "uhm labari kike ban kenan?"ya fadi cikin watsar da muhimmancin batun a gunta,tambayar ta quleta hakan yasa tayi shiru,"me kike buqata ne ina fa da aikin yi"ta daure tace "baby nake son inje na gani" "ban amince ba"ya fadi kansa tsaye,din din ya katse wayar,wani hawayen takaici ne ya sulmiyo mata,tayi wurgi da wayar kujerar gefenta,cikin takaici ta figi motar sai gida
Danja na tsaida su tana ganin wani wani saurayi dake gefan tata motar yadda ya zuba mata ido da alama yana mamakin me ya sanyata kuka ne,ta kawar da kanta gefe cikin zuciyarta tana ayyana in banda babu kyau fita babu izini tabbas da sai tayi wucewarta gidan farida saidai aliyyu yayi tsirenta,ta share hawayen sanda danja ta sake su ta sake figar motar,tana kallon yadda saurayin ke sa mata signa yana son tsaidata tayi banza da shi ta qarawa motarta speed,ita kanta bata san tayi gudu haka ba sai da ta iso gida agogon wayarta ya harba taga yan taqitattun mintocin da suka kawo ta gida,tana qoqarin shiga gidanne bayan mai jire bakin qaton get din gidan ya dage mata qofa ta soma shiga taji wani horn din,ta glass ta hangota motar samira ce wadda take cin ubanta da hawa ta tabbatar da motar mutum ce da tuni ta dade da guduwa,ba samiran ba hatta qawayenta sai suzo su ari motar su wuni sur suna cin ubanta ko a daddoke mata ita su kuma dawo su yasar mata ita ce mai kudin banza ta gyaro ta zuba musu mai gobe su dawo su sake ara ita kuma ba lissafi ta basu saboda tsabar neman suna irin na samira,shi uasa tayi nacin aliyyu ya canza mata mota qememe yayi buris da ita don yana sane da abinda takewa tatan
Mrs muhammad ce
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
12:36 pm 22/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*PART 2*
9⃣~~1⃣0⃣
Ta ajjiye motar a parking space ta kashe ta tana mai dauke idanunta daga kansu samira zuciyarta na tur da irin halayen mutanen da samiran ke mu'amala da su,hakanan ko yaushe zaka gansu cikin shiga ta banza da rashin da'a,yanzun ma qawayenta ne su uki ta dauko cikin motar kowacce kuma cikin shigar tasu dai ta dabi'ar da suka dorama kansu ,tana jin shewarsu sanda take rufe motarta kasancewar suna bayanta ne tsaye jikin motar samiran su basu shige ba hakanan basu komacikin cikin motar ba,sun saba yi mata haka tun ba yau ba kula su ne sam bata taba yi ba don bata kallonsu ma a matsayin cikakkun masu hankali,tana ganin idan ya kula su ma tamakar ta basu wata martaba da daraja ne,kallon tsiya ma basu isheta ba bare su sa ran wataran zasu samu na arziqi bare fadilan dama miskilar kanta ce sai ka gama cin kashinka a gabanta idan bata ga dama ba quda bazata kore maka ba
Kamar ko yaushe yauma har ta bawa banza ajiyarsu tayi gaba abinta maganar da ta jiyo suna fada ita ta sanyata dawowa da baya ta tabbatar ya zama dole yau ta yiwa tufkar hanci bare yadda take cikin takaicin hanata zuwa gidan farida da aliyyu yayi shewa suka yi sanda take yin gaban sannan daya daga cikinsu tace"badi'a (sunan daya daga cikinsu ta kama)saiki dinga fakewa da fita aiki ana yawo a kwararo
Da baya ta dawo sannan ta fuskancesu,dubansu tayi daya bayan daya up to down ta saki wata 'yar siririyar dariya tace "😏 ai karuwanci iyawa ne kuma karba karba ce,💁🏽wata hajar sai ta qaraci zamanta a kasuwa tasha qura tayi futu futu kullum kuma sai an fito da ita an kasa amma sai kiga ko kallonta al'umma basuyi bare su baqaci siya,kinga kenan inda wani yayi rawa aka bashi kudi wani idan yaje yayi dan banzan duka zaici
Ta sake watsa musu kallon raini sannan ta dora"ku ba abokan yina bane don ban hada sabga da ku ba wannan.....ta nuna samira da key din mota dake hannunta "itace abokiyar yina,ita din ma zata gaya muku inuwarta bata isheni kallo ba bare zahirinta,but.... well zan baku shawara guda daya hade da gargadi mai kama da jan kunne,shawara ta farko itace ku rufawa kanku asiri ku samu ku raba jikinku a dakin aure kafin a rasa mai kwasar ragowarku......😂🙊 au am sorry na manta yanzun ma fa hakance ta faru da ku fa shi yasa kuke gararamba da yawon kwadayi da maula agidajen matan wasu
And gargadina shine kada wadda👉 ta sake bude rubabban bakinta da niyyar shiga gonata don nikam duk cikinku babu wadda tayi isar da zan shiga gonarta,saboda haka nima akiyaye shiga tawa gonar👉"ta kama kunnenta daya da hannunta tace"idan kunne yaji......gangar jiki ta tsira"ta saki hannunta ta juya da niyyar shigewa dukkansu sunyi mutuwar tsaye don nasu taba tsammanin ta iya magana haka ba a yadda samira ke basu labarinta,samiran ce tayi yunqurin nuna jarumtarsu tasha gabanta ta kama qugu tana cewa"ke qaramar 'yar iska mu kike nufin zakiyi wa rashin mutumci?"
Murmushi fadila tayi tace"🤗 a'ah sanin kanki ne fa ni ban iya hayagaga ba ke zaki fara baiwa wanda bai sani ba labari ,to kuwa akan wadancan👈🏼 shashashan bazan fara ba"ta gewayeta tayi wucewarta,tana jiyosu suna ci gaba da kuri da cika baki kala kala akanta har suka wuce sashen samira,cikin ranta take fadi Allah ya bawa daya daga cikinsu sa'a tace zata biyota taga yadda ake rashin albarka
Wanka tayi don taji sanyin zuciyarta tuni ta watsar da batun su samira don basu gabanta hasalima bata daukesu wani abu ba don tasan baya ga tsabar jahilci dake damunsu rashin tarbiyya na bibiyar rayuwarsu,tana mamakin tsarin rayiwa irin tasu sam basu damuwa da yanayin da rayuwarsu ke gudana,falo ta dawo ta hada yoghurt mai sanyi da fura ta dama ta koma saman kujera tana diba da cokali a hankali tana sha zuciyarta sam bata gidan,kira ne na anty hafiza ya soma shigowa wayarta tana neman farida ne tayi ta kiran wayarta busy shine ta kira ko suna tare ta bawa faridan,nan da nan ta tabo mata miki basu gama sallama ba ta kashe wayar don bata son taji kukan da ya qwace mata,kamar kuwa hadin baki yan uwa ke kiranta suna cewa ita zasu yiwa barka itace uwar 'ya,hakan ya raunana zuciyarta sosai tasha kuka,sister faridanta guda amma wai a hanata ganin 'yarsu?
Har magariba jikinta amace yake,sai sannan ta tuna bata kira umminta ta mata barka ba,jin muryar ummin bayan ta daga sai ya karyar mata da zuciya kuka ta saki,a tsorace ummin tace "meye haka lafiyarki kuwa?"cikin kukan tace "ummi ya hanani zuwa ya hana ni inje inga baby ummi"ummin ta saki ajiyar zuciya sannan ta ja tsaki"wlh harkin tayarmin da hankali na zaci wani abune ya faru ko ya sameki?" Ta sake marairaicewa cikin muryar kuka tace "ummi wani abune mana sister farida fa ummi" "to sai me idan baki je din ba?,idan kinje ma me zakiyi mata iyakaci kije kuyi ta surutu,tunda Allah yasa an sauka lpy bashi kenan ba abunda dama ake buqata kenan"ta sake sakin kuka tace "ummi ki masa magana don Allah idan ba haka ba baza ni ba"kama haba ummin tayi kamar fadilan na gabanta tace"🤔lallai bansan haryau quruciya na damunki ba fadila,to ba da ni ba wannan shiriritar,bana som sakarci ki maida hankalinki fadila kada na soma jin wani abu kuna jina ko?" A sanyaye ta gyada kai ta sani ummin bazata so ace bata je ba amma bazata taba bata goyon baya ba,halin ummimsu ne a gidan aure maca ce mai tsananin biyayya ga abbansu ko layi uaja yace kada ta tsallake to insha Allahu ba zata tsallake din ba hakanan kaf yaran babu wanda zata bari ya tsallaka hakan ne yasa har yau har gobe har ma jibi inji shi abban nasu yake alfahari da kuma ji da ita
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar tana jan majina hadi da son maida kukan ta,alwala ta daura tayi sallar magariba ta zauna kan sallayar tana jiran a kira isha,hakanan fadila take tana da kwadayin wannan garabasa da ake samu ga duk wanda ya idar da salla bai kuma tashi daga gurin ba,jira ne baifi na awa daya da rabi ba aka tada isha'i ta gabatar da ita duka harda shafa'i da wutiri sanann ta sake zama ta karanta subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azim,don kanta ta gaji da zaman ta ninke abun sallar ta maida shi muhallinsa ta baro dakin sa hijabinta a jiki don dumin cikin hijabin ya mata dadi
Cartoon ta maida tana kallo kan tashar m.b.c 3,lokaci lokaci tana sakin ajiyar zuciya saboda kukan da tayi,sannu a ahankali ta soma jiyo qamshinsa ,ta daga fararen idanunta ta maida su bakin qofar shigowa falon,cikin nutsuwa da sallama ya shigo yana sanye da jacket black blue sun haska farar fatarsa,sunyi amsarsa matuqa da gaske adorable structure dinsa ta fito sosai,sassanyan kyawunsa din nan ya bayyana cikin kamilalliyar tafiyarsa ya qaraso falon hannayensa sarqe a qirjinsa,can qasan maqoshinta ta amsa sallamar carelessness ya samu hannun daya daga cikin kujerun ya zauna ba tare da ya dubeta ba
With bounded face yace"ki fito na miqaki kiga baby"tamkar tayi banza da shi ko tace ta fasa sai taga idan ma tayi hakan ai kanta ta yimawa ba wani ba don shi kam bashi da asara,ta miqe kamar marar laka ta shige bedroom dinta tana qunquni qasa qasa"sai an ma gama qonawa mutum rai sannan za'a wani tasa shi a gaba akaishi kamar wani dan qanqanin yaro" "idan baki zuwa ba saiki zauna ba ke ya shafa"ya fada a tsawace,baki ta rufe da sauri ta qarasa shigewa bedroom din don batayi tsammanin ya ji ba,lallai shi kuwa wane irin kaifin ji gareshi take mamaki cikin zuciyarta
*NOTE*: assalamu alaikum masoya littafina saqonninku nata isheni da maganganunku game da littafina,duk da cewa na sani nayi muku bayani tun a farko na yadda rubutun zaici gaba da kasancewa sakamakon shirin fitar da shi kasuwa,na dauka tuni mun wuce gun saboda banyi zaton zanci gaba da baku shi littafin ta watsapp bama amma yanayin yadda kuke nuna qauna gameda da shi din yasa naci gaba da rubuta mukun duk da na rage yawansa kamar yadda na fada,
To amma naga rashin fahimta na son shiga ciki,na farko har ga Allah yadda wasunku ke min bana jin dadi yana bata zuciyata,saboda bani da wani uziri da zai taso min a matsayina na yar adam a gunsu abunda kullum suke buqata shine nayi musu kawai typing na turo musu,sannan wasu babu yabawa saidai qorafi da zarar sun gama karanta wanda na samu na turo,hakan da suke yana kashemin gwiwa ne,maimakon suyi abinda zai qarfafa min gwiwa ko saboda gaba kada ku manta hannu ne keyi ba fada muke wayar na rubuta mana,kuma yau da gobe ai sai Allah,ni 'yar adam ce gsky da bana son abinda zai dameni ko ya samun damuwa a zuciyata nakan haqura da abubuwa da dama matuqar zasu jawomin damuwa,don Allah ina roqonki ku tsaya kuyi duba na fahimta game da ni,ni ba budurwa bace matar aure ce ku duba kuga yanayin hidimomin gida na kullum dake kan matar aure baya ga wadanda ka iya taso mata wadanda bata tsara da su ba a rana,ku dinga adalci kuna hukunci na gaskiya,mu fahimci juna don Allah wannan shi zaisa ni daku muci gaba da jin dadin alaqar dake tsakaninmu,wlh akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a rayuwata da nake yi kulluma da kafin fara muku rubutu amma a yanzu sun gagareni yi saboda rubutunku,na sani harka ta mutane sai kayi haquri tunda yadda muka banbanta a halitta haka Allah s.w.a ya ban banta mu a halaye da dabi'u,na gode Allah yasa mu dace👏🏻👏🏻
Na biyu kuma masu ganin abunda aliyyu yake yayi yawa kada kusa gaggawa a lamarinku kuma kada ku manta shi haquri shine jagoran kafatanin lamuran mu na duniya bare haquri ga 'ya mace kuma acikin gidan aurenta hanyar shiga aljannarta riba ce ba kadan ba,ina so ne yan uwana mata muyi koyi da halinta koda cewa ba irin auren ta kikayi ba amma nasan baza'a rasa matsala daya ko biyu da kike iya fuskanta ba daga mai gida wadda shigen halin da aliyyu ya taba nunawa fadila ne to ga yadda ta shanyeta ga kuma ribar da ta samu,na godewa masoyana gana daya ,Allah yayi mana sakamako agidan aljanna ya hadamu dukkanmu a cikinta in kuma ci gaba da zama marubuciyarku ta gidan aljanna 😜😜😀😀👏🏻
Mrs muhammad din[truncated by WhatsApp]
4:50 pm 23/8/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣1⃣&1⃣2⃣
Powder kawai ta shafa a fuskarta ta shafawa kyawawan labbanta lip glosses,atamfa ta zaro cikin kayan nata dinkin doguwar riga ne mai umbrella ta bude sosai an mata dogon hannu simple style ne,ta ware dan madaidaicin mayafinta ta yafa shi har saman kanta kamar yadda ta saba yafenta sannan ta fesa turare ta fito
Yana tsaye a wajen motar yana amsar calling yayin da salima ke tsaye kusa da shi hannunta harde a qirjinta tayi kicin kicin da fusaka,sallama fadila tayi mata sai taga ta dauke kai don haka sai ta ja tunga itama tayi banza da ita,ya gama amsar kiran ya kashe wayar hannunsa na kan mabudin motar salima ta kalleshi tace"please dear"kai ya gyada yana cewa"dont mind" ya bude gidan gaba kusa da kujerar mai tuqi ya zauna ta bude baya itama ta shige,nasiru ya gaida ta cikin girmamawa a mutunce ta amsa sannan ya tada motar suka fice
Tafiya ce kamar ta kurame sai ka rantse bata cikin motar sai shi da nasirunne ke hira jefi jefi galibi ma bai wuce zancan kasuwa,idanunta na kan titi yayin da zuciyarta ta lula duniyar tunani
A bakin get suka dakata bayan mai gadin ya dage masu get aliyyu yasa nasiru yayi masa magana ya rufe ba shigowa za suyi ba,fadila ta tabe baki cikin ranta tana gulmar aliyyun,nasiru ya gyara parking din sannan ya fice daga cikin motar,fadila ta sa hannunta a kan mabudi zata fice "twenty minutes"haka ya fada cikin carelessness,ba abunda tace da shi tayi ficewarta "ko baka gaya min ba ai na sani uban masu tsari da qa'ida na duniya😙"tayi zancan cikin zuciyarta
Da yake takwas na dare ma ta dan gota gidan ya samu sararawa daga cincirundon 'yan barka mutum hudu ta tarar Amina da mariya qannan mubarak ne sai maqociyarta guda daya sai kuma wata dattijuwa inna jummai wadda mahaifiyar mubarak ta kawo mata ita saboda kula da mai jegon da kuma jaririyar,alokacin da ta shiga ma tana kitchen tana kwashe tuwon da ta yiwa faridan,fadila nata qyalqyala dariya ganin inna jummai nata loda tuwon a flask tana ce mata"inna zanso naga dambarwar ku kam da farida don ba abincin da taqi jini irin tuwo,dama dai ni kika baiwa"innan da yake macace mai kirki da saurin sabo da jama'a tace"ai duk qinta kuwa da tuwo yanzu ya zama abokinta dole ta cishi tunda jego ya zo"
Tayi sallama ta shiga falon faridan dukkaninsu suka amsa mata cikin fara'a suna dariyar hirar fadilan da inna jummai,farida kam ture kayan jarirai dake gefanta take tana cewa sister taho nan daya hannun nata kuma cup ne cike da tea tana sha sai hada gumi take inna kuma taqi ma a kunna fanka bare a.c saboda wai jego faridan zatayi irin na da,fadilan ta qaraso tana cewa "🤔sister farida mai tsokana da yawon gidan qawaye yau gata dq baby" dariya ta basu dukkaninsu harda faridan,idanu fadila ta baza tana neman baby tace nifa baku nazo gani ba wlh ina 'yata ku bani ita naji duminta"yarinyar na hannun maqociyar ta ta nannade cikin farin shawul mai taushi ta miqe tana miqawa fadila ita hadi da yi misu sallama ta ajjiyewa faridan 1000 kudin barka ta mata godiya ita kuma ta fice
Ta kammala shanye tea din tas ta dire cup din tana kallon fadila tace "sister da fa har nayi fushi kece ta farko da kika fara sanin haihuwarnan baya ga abbanta amma sai yanzu zaki zo mana tun dazu baby ke son ganin mummynta bata zoba sai da aka rigata gane mata ita" "hmmm lallai yarinyarnan kukan dadi fa kike da yaya yanzun ma ya barni tare ma fa muke"cikin zolaya wadda attitude din farida ne tun usulinta tace "wow kice har an fara boyonki lallai soyayya ruwan zuma"fadila ta harareta tace "wlh badan kin mun abun kaiba kin bani baby mai kama da ni ba da sai na bubbuge bakinki"su amina suka qyalqyale da dariya sannan suka miqe suka ce bari dai mu baku guri kada a buge mana anti a gabammu"dariyar suka bawa fadila su kuma suka fice kitchen gun inna jummai
Fadila ta sake zubawa yarinyar ido tubarkallah masha Allah qatotuwa da ita lallai kam wannan photo copy dinsu ce ta kalli farida tace sister sannu"farida ta ya da kai gefe tana tuno wuyar da ta sha"hmmm ke dai bari sister ansha gwagwarmaya ni kam dan ba qara"fadila ta sake rungume yarinyar a qirjinta tana sake jin qaunarta na shigarta bata qi ace tata bace,ta saki dariya tace "yanzun fa aka fara farida me akai da maza daga ihu daya sai kuma murya ta dashe?😜"ta qarashe ta sigar tsokana yau dai ta maida raddin tarin tsokana irin na farida da take mata ko yaushe,ko da can dama fadila Allah ya zuba mata son yara,sanda suka tashi muhammad ne kawai yaro a gidansu to har gidan maqofta take shiga dauko yara duk da yanayin unguwarsu irin unguwan nin nan ne da ba ruwa na da kai kowa na qulle shi da ahalinsa cikin gida amma haka fadila ke shiga ta taho da su,miskila ce ako ina magana bata dada ta da qasa ba amma banda kan yara hakanan zaka ga ta sasu a gaba suna ta wasansu,farida kam dama idan taga dama idan suka zo neman anty fadila sai ta korasu tace bata nan zasu zo su dameta ne
Farida ta girgiza kai da sauri tana juya ido tace "kai sister is hardly in sake ko zan qara sai after five to ten years,nikam na barmiki ki taba kiji"dariya ma ta bata ganin duk yadda tayi laushi duk rashin tsoro da dakiya irin na farida,murmushi fadila tayi tana ci gaba da kallon yarinyar tayi kissing dinta agoshi,"ina aliyyu ne sister?"🙄af yana waje " farida ta miqe daga kashingidar da tayi tace "kada dai kice mun kuna tare yaushe ya aliyyu boss ya fara kai matarsa unguwa"fadila tace"saboda ya bata min ya fara ta kaina yau kina gani fa kamar gidqn nan yace min wai twenty minutes?"farida tace "wlh am serious ya aliyyu ko salima matarsa ta farko bai taba kaita wata unguwa ba idan ba monthly shopping naku ba(farida ta fi fadila sanin halinsa ne kasancewar tq fita shiga jama'a hakanan ta fita zuwa gidan uncle abba)kuma shine kika barshi a waje ga sitting room nan"fadila ta tabe baki tace "oho masa har get malam salisu ya bude masa yace a maida arufe ba shigowa za su yi ba" "gashi mubarak yanzu ya fita maida hajiyarshi gida da ya shigo da shi"farida ta fada tana lallatsa wayarta,"zancan kike so ki bar mubarak kada ki taso shi idan da rabon zasu hadu zasu hadun don ko mubarak ya zo idan bai ra'ayi ba bazai shigo din ba"
Minti goma sha biyar ta shude suna ta hirarsu farida na cin tuwonta a sake kasancewar su mariya sun bar masu dakin,dahiru yaron dake wa farida aike aike ne ya shigo karbar abincinsa bayan ya miqawa inna jummai kwanon ya tsaya bakim falon faridan yace"anty wai baquwa ta fito za su tafi"fadila ta bata rai don tasan aliyyu ne yayi aiken kuma aqa'ida tana da sauran minti biyar
Ranta a bace bayan ta bude camera din wayarta ta yiwa baby pic ta sake sumbatarta ta ajjiyeta gefan faridan ta dubeta tace sister zan dawo insha Allah me kikeson na kawo miki"murmushi tayi tace"sister fadila nayi missing din wainar shinkafarkin nan da kike mawa dady,idan zan sameta inaso"dariya fadilan tayi saboda ta tuna mata lokacin da suna gidan idan tayi insha Allahu kan ta gama shiryawa Abban a warmer taci na ci kuma ta bi ta har falon abban suci tare da shi tana hara rarta tana komai amma sai tayi biris,"insha Allah kamar kinci waina ta kin gama"sukayi sallama tamkar kada su rabu
Tana fita taga motar mubarak fake kusa da tasu shi dinne kuwa da alam yanzun ya iso don lokacin suke gaisawa da aliyyun ta qaraso suka gaisa ya juya yayi cikin gida yana cewa bari ya dauko ma aliyyun babyn ,hannu biyu yasa ya dauki babin mubarak na gyara masa riqon don da gani bai iya ba,ya riqe ta sosai yana kallinta hadi da fadin"masha Allahu la quwwata illa billah"(yan uwa gaka annabi ya horemu da fada a duk lokacin da muka ga wani abu da ya qayatar da mu to ko kana da kambun baka bazai kama abun ba domin wasu ma auna da shi amma basu san suna da shi din ba,sai kaga abu kayita kodashi ba tare da ka fadi hakan ba daga qarshe sai wani ibtila'i ya saukarwa abun ya lalace don Allah mu kula da wannan)
Fadila na satar kallonsa kadan kadan tana kallon yadda ya zubawa yarinyar ido ya lumshe idanunsa daga baya ya budesu ya sumbaci goshin yarinyar sannan ya miqawa mubarak ita yana sake cewa Allah yayi mata albarka,ya amsheta sukai sallama ya shige gida da babyn
Aliyyu ya yafito qasimu dake fitowa fitowa daga gidan hannunsa da robar abinci qasimu ya qaraso hadi da rusunawa aliyyu ya amshi bandir din kudin dake hannun nasiru ya miqawa qasimu yace ka kaiwa maman baby ya zaro 1000 daga aljuhun trouser dinsa ya bashi ya shige motar yabar qasimu nata zuba godiya yare da komawa cikin gidan don sada saqon aliyyu ya bawa nasiru umarni ya tada motar suka bar layin fadila nata satar kallonsa don kiwa dubu dari ce ya bayar a kaiwa babyn
Mrs muhammad ce 👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
2:08 pm. 24/08/2016
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
WA YASAN GOBE?..
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by masoyiyar buk din wayasan gone..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*Part 2*
1⃣3⃣&1⃣4⃣
Fadila tacigaba da sake2 azuciyarta bata ankaraba taji ana bude get tana dago kaitaga harsun iso gida ashe,parking space ya nufa ya kashe motar,fadila dakekokarin bude motar setaji ya kulle motan ta waiwayo tadubesa suka hada ido tayi saurin dauke kanta zuwa gefe,shiko gogon sebinta ya ke da kallo can yace wai meye kiketa wani bata rai tamasa banza yacigaba damagana ,inatambayarki,kaikidanayine nayi lefi koso kike danabarki kikwana? nan ma shiru yaharzuka cikin tsawa yace wai badakenake maganaba salan wulakanci,
Se asannan fadila tadago kai da fuska cike da hawaye tace wulakanci? wulakanci yawuce wulakantani dakakeyi Wanda haka har matanka suka sami damar gorantamun,Aliyu nayi nadamar aurenka auren bakinciki Inatabbatarma dabadan mahaifinaba dana dade dabarin gidan nan,cikin kuka takemaganar yayin da Aliyun yatsinci kansa da tausayinta Yakuma kasa cewa kome illa binta da kallo.
Fadila tacigaba kodan matanka da ni ba irin su naso nayi kishi dasuba,naso ahadani da wayanda suka San mesukeyi😭 bawadannan da kake kallo amataba nibanga mata anan ba kuma duk ajin naka akan salima da samera yakare ragowar wasu,cikin bacin rai yadakamata tsawa,itako ta dannan motar tabude tafita da gudu tanufi sa shinta,tana shiga tafada kujera setaji ya akayi tayi wadannan magana,setaji kamar bats kyautaba cankuma wani bangaren zuciyarta tacemata garadakika masa haka yasan fa kinsan mekikeyi kuma yasan badan shikike gidanba Dan biyayyar iyayankine,tamike tashiga toilet tayi alwala ta fito ta tada sallar isha dabata samu tayiba.
Can Aliyu kuma kasa futa yayi daga motar jikinsa duk yamutu zuciyarsa ta cunkushe abinda yafi damunsa shine kalmanta datayi kansu samira da salima domin yakaratunawa da yanda yasamu samira adarensu nafarko,sannan Salima bayan rabuwarsu itama ba agida tayi rayuwaba,yadafe kansa karo na farko da naga A S metama na kwalla daya nazurarowa daya bayadaya😰 yace inna lillahi wa inna ilaihirraji un.tabbas jidakai bekama ceniba domin ina tare da wadanda basu cancanci suzama iyayan yayanaba,gashi inakallo se haihuwa ake Wanda akai bikinmu tare duk sun haihu,su naji kowacce tace batashiryaba itakuma wanan yarinyar banashiga harkanta,gashi du k ta gane kome,Aliyu yacigaba da hawaye yana maibakkincikin abubuwa kala kala yadaure ya fita daga mortar jiki akasalance yanufi bangaransa yanashiga ya kulle kofar yabar makullin ajiki sabida bayasan ganin kowa domin koda sunzo sunyi amfani da makullinsu bazebuduba.yashige bedroom yafada gado yacigaba da tunani aranar dai Aliyu beruntsaba Dan maganganun fadila kemasa yawo akwalkwaluwarsa,
Itako fadila cikin nishadi tayi barci domin tafidda wani tabo da kedamun zuciyarta.
*amun afuwa Mrs Muhammad nayi muki shishshigi amma haka mukeson buk yadawo munakara mikamiki godiya dayabawa Allah yakara basira kidora saga inda natsaya domin zansamu goyon bays amma kitambayi friends sunyarda kidora😀*bye nabarki Lfy Wanda sukaji haushi suyafemin kar azagen nima wlh soyayyar buk din yasa nayi👍🏻
Ba Mrs Muhammad bace👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:46 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?..*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣5⃣&1⃣6⃣
Qarfe tara fadila tayi wa iftihal wanka itama ta shirya cikin riga da skert na atamfa a cikin qana nun kayanta ta cirowa iftihal wasu riga da skert dama sun mata kadan jajayene in and top ta raba mata gashinta gida biyu ta tufke mata da ribbon sosai iftihal tayi kyau suka yi break sannan ta soma gyara part dinta kafin ta isa ga na aliyyu don duty dinta ne duk inda ta shiga yarinyar na biye da ita ita ala dole sai ta taya ta aiki sai da fadila ta bata mopping din kayan kallo sanna ta rabu da ita
Fadila ta fito tana goge hannunta da duster bayan ta gama aikin ta iftihal dake ta fama da chocolate tace "anty ina daddy na?"murmushi fadila tayi ta kama kumatunta tace"kwantar da hankalinki 'yar daddy yanzu zaki ga daddy shiga daki bakin gado ki dauko min hijabina"da gudu kuwa ta shiga sai gata da shi a hannu ruwan madara ne iya qugu wanda ya shiga da atamfar jikinta sosai,ta kama hannun iftihal din bayan sun rufe qofan
Tana sa kai falon taji hayaniyar sama sama muryar salima ke a sama,tana tsaye hannayenta harde saman qirji kan aliyyu shi kuma na zaune kan kujera yana sanye da kayan bacci na maza ruwan madara shima hannun nasa harde a qirjinsa😠,shigowar su yasa salima yin dif daga maganar da take yi din gami da sakin fuskarta daga tsukewar da tayi tana dan binsu da kallo(salima akwai duniyanci)sam bata lura da iftihal ba da suka shigo tare sai da yarinyar ta zame hannunta daga na fadila wadda ta shige kitchen ta ruga a guje tayi gun daddynta tana cewa"daddyyyy daddyyyy...."kamar yadda ta saba ta durqusa a agabansa kafin ta haye cinyarsa tana cewa"morning daddy sabahul khair",murmushi ne sosai dauke a fuskarsa wanda bai bayyanar da haqora😊yasa hannu ya dagota yana kallonta yace"sabahun nurrrr my lovely khadija"tayi tsalle ta dane cinyarsa abinta tana wasa da maballan gaban rigar baccinsa tana cewa"daddy tunnjiya nazo da daddare kaqi zuwa na ganka" "wonderful,anan kika kwana ke da wa?""ni da anty fadila tare ma yanzu muka taho"ya daga kansa yana nemanta da idanunsa sai dai tuni ta jima a kitchen bata a gun sai salima dake tsaye ta zubawa 'yar tata ido
Kallonta take tana jin wani alfahari na shigarta tana godewa Allah da bai bata damar rasata ba,wani dadi ne ke cikata ganin gudan jininta ita da halitta mafi soyuwa a gareta wato Aliyyu salim Abdallah maitama,tabbas iftihal abar alfaharinta ce yarinyar bata debo kammaninta ba ko kusa babu wani abu nata data dauko illa farar fata wadda aliyun ma na da ita,kowa ya ganta ya san jinin su ce family din alhaji salim Abdallah maitama ce jininsu ce
Ta dawo daga duniyar tunaninta hadi da miqawa iftihal din hannu alamar ta taho sanda suka hada ido fuskar salima dauke da murmushi,da taga kamar yarinyar bata fahimta ba sai tace"come on baby na come on my dear " yarinyar ta noqe kafada tayi luf jikin mahaifinta kamar mai tsoron ta babu sabo ko kusa tsakaninsu,wani kishi ya kama salima don taga yadda suka shigo da fadila yarinyar a sake take kana ganinsu kasan akwai sabo mai yawa tsakaninsu
Ta sake gwada sa'arta ta miqa mata hannunkaro na biyu tana sake cewa"come on mana mai dear kin manta mominki ne iftihal? Me yasa baki zo guna kin kwana ba ina da chocolate da biscuit da yawa da zan baki"ta sake noqe kafada tace "um um nafison na kwana gun anty fadila she's nice like daddy"sai salima ta maida hannunta ta rungume cikin jin haushi
Aliyyu na ankare amma yayi kamar baiga abinda ke faruwa ba,sai da yaji tana jan qwafa sannan ya tanka mata"duk uwar da bata yi showing mercy akan yaronta ba tayi abandoning duk wasu duty nata akansa no need to deceive her self akan shi zai iya jin qanta ya kuma ji tausayinta"idanunta sun kada sunyi ja kadan take jira ta fara malalar da hawaye tace"aliyyu abinda ya wuce ya riga ya wuce please"ta juya cikin zafin nama ta bar part din nasa kamar zata rushe da kuka
🔱🔱🔱🔱🔱
*TUNA BAYA*👈🏼
🔱🔱🔱🔱🔱
Aliyyu da salima sunyi aure ne irin auren da zaka iya kiransa na soyayya,karatu shi ya fara fitar da aliyyu india cikin garin mumbai dake qasar india,ya karanci fannin kasuwanci da masana'antu ne tun usulinsa,kusan binda ma ya zaunar da shi kenan a qasar bayan kammala karatunsa kafin daga bisani ya soma kai kawo tsakanin nijeria da indian
Tun kafin aliyyu ya kammala degree dinsa na farko yake siyan kaya yana turawa uncle Abba yace a siyar masa tun uncle abban na dariya yana dauka wasa ne abun nasa yakance"alii rigima idan banda abinsa mai ya nema ya rasa da zai takurawa kansa sai ya fara kasuwanci tun kafin ya kammala karatunsa?"shi kama aliyyu ya dage aiko kaya yake tun daga lokacin da uncle abba ya fuskanci son kasuwancin a jininsa yake sai ya qyaleshi ,sai gashi tun kan ya kai ga kammala degree dinsa na biyu ya mallaki kudade masu tarin yawa na qashin kansa tsantsar guminsa,sam yaqi amsar tallafin sisin kwabo dag dukiyar da Allah ya horewa mahaifinsa,kwata kwata aliyyu ba cima zaune bane akwai zuciyar neman na kai tun yana qaraminsa,bai damu da arziqin da mahaifinsa ke da shi ba
Wadannan kudade yaci gaba da juyawa har kawo yanzu matsayin da yake kai na mamallakin companies da share shares a gida nijeria da wadansu maqwaftan qasashen,aliyu ya zamo daya daga cikin matasa masu tarin dukiya mutumne shi da Allah bai bashi dagawar son a san wayeshi ba,yasha gayawa abban nasa tun kafin zuwan wannan lokacin shi yafison yasan ya san zafin neman na kai,sai gashi burinsa ya cika don ya tara dukiyar da shi kansa bai sa ran samun kamarta ba,darajar addu'ar mahaifa riqon gaskiya da amana tausayi da taimakon na qasa su suka kaishi ga wannan matsayin da yake kai
Haduwar su da salima ta kasance ne sanadiyyar hutun qarshen zangon karatu da daliban instute din pashwar suka samu ciki harda,wadanda ba 'yan qasar ba kuma suke da sha'awar zuwa qasashensu hutu nata shirye shiryen zuwa gidan ciki kuwa harda saliman,wasunsu na ahiga kasuwannin dake cikin mumbai don yiwa yan uwa tsaraba
Cikinsu harda salima su hudu ne ita sai wata qawarta 'yar nijeria sa'adiyya abikan karatunta biyu 'yan qasar data nemi rakiyarsu don qasarsu ce sun fita sanin kan farashin kayayyakin shruti da arohi,sun ahiga shagon a sanda aliyyu ke ciki yana zaune kan daya daga cikin kujerun dake ajjiye a shagon suna lissafi ne shi da mai mai shagon kan wasu kaya da aliyyun ya sara a gunsu alokacin tun kafin ya bude kamfaninsa
Abu na farko da ya fara kama jan hankalinta game da aliyyun shine baiwar tsantsar kyau da Allah ya bashi da daddadan sauti ,abu na biyu ya bata mamaki jin yadda yake hira tar tar da indiyanci tamkar haifaffen can,tunda suka shigo shagon daga kallon farko na amsa sallama bai sake duban sashin da suke ba ya mai da kai yaci gaba da abinda ya kawoshi shagon
Ita din ma azahiri idan ka kalleta sai kayi tsammanin hankalinta bai kansa saidai duk siyayyar da take yi kusan qani abun ma bata san me zatayi da shi ba data dauke shi don hankalinta na kan alin
Tuni ya kammala abinda yake yayi sallama da raja ya wuce,sanda yake fita ashagon garin karkatawa ya wuce taga silmiyowar wani abu daga aljihun trouser dinsa ma baya amma bata zaci wani abu mai muhimmanci bane sai da ta sake matsowa ta sa idonta sosai sannan taga ashe wata 'yar kyakkyawar wallet ce ,da sauri tasa hannunta ta bude ciki,rupees(kudin india) ne masu yawa aciki a miqe,sai dan qaramin hotonsa wato passport,sai kuma wasu kati guda uku biyu na wasu shaguna dayan an rubuta *adishwar garment* shagon na cikin *janta cloth market hawkers plaza*ta maida shi ta duba dayan shi kuma na shagon *ajmeri fashion* shagon shi kuma na *hazarat abbas road Samuel street*,duk cikinsu babu shagon da ta taba zuwa tunaninta na kan yadda Atayi masa da wallet da kuma yadda zata sake samun damar hanawa da shi,tana duba kati na uku uku na dauke da sunan hotel din da ya sauka haka jikinta ya bata tunda su muta nene da komai ka siya ko kayi mu'amalar ciniki da shi sai sun baka rasit ko card nasu,tasan hotel din tunda takan ziyarci cikinsa lokaci bayan lokaci nan kusa da makarantarsu yake
Ta maida duka kayan ciki tana sauke ajiyar zuciya,bayan sun kammala siyayyar suka koma cikin makaranta,da daddare ta canza shiga irin tamu ta hausawa atamfa ce saidai dinkin riga da skert ne tayi kwalliya sosai a fuskarta,ba wata tafiya ce mai nisa sosai ba tsakaninsu don haka irin keken nan nasu ta hau ya qarasa da ita,bata sha wahalar samunsa ba saidai da yake hotel ne na manyan mutane akwai tsaro sosai da kuma tsari duk magiyarta basu yarda sun bata number din room din ba sai da sika kirashi suka sanar masa,duk da yayi mamakin mai neman nasa kuma sunce mace yace a bata number din baisan me ya kawota ba ko da taimakon da zai iya bata
Ku biyo
Mrs muhammad👑😘
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:47 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*part 2*
1⃣7⃣&1⃣8⃣
Sai da tayi knocking sama da sau biyar sannan aka bude mata,fuskarta ta wadatu da murmushi😃 yayin da tasa take a tsuke😠 kamar hadari,"sannu ko?"tace da shi cikin fara'a"yauwa sannu" ya fadi adan dake yayi bake bake abakin qofar babu wata hanya bare ta sa ran shiga ciki don ko kalan labulen bakin qofan ba zata tantancewa ba,cikin qosawa ya gyara tsaiwarsa ganin tayi shiru yace "I hope lafiya dai ko?"ta sake yin murmushi a karo na biyu ya zaro wallet din daga cikin yar purse👛 dinta dake damqe a tafin hannunta sannan ta dubeshi tace"wannan ka yar dazun a mall din paras mahal collection"ta miqa masa tana dan murmushi,ya sa hannu ya amsa yana cewa"thank you verry much"ya juya yana qoqarin mai da qofarsa ya rufe
Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar cewa"haaabaaa haabaa malam babu ko goron tsintuwa?😊" a qagauce ya dakata ya juyo yana cewa"nawa kike buqata?"t saki wani mayaudarin murmushi"ba kudi nake so ka bani ba,kawai passport nake so na cikin wallet naka sai kuma phone number dinka shikenan abunda nake buqata🤗"
Girgiza kai yayi hadi"it can't ki zabi wani abun dai daban banda wadannan"ta kanne ido daya😉 tace"ni su din dai nake so"kafewa yayi kai da fata bazai bata ba"i told you ba zaki samu ba"itama kafewa tayi akan shi take so indai alherin da tayi masa yake son rama mata,daya lura tana da yawan taurin kai sai ya bude wallet din ya zaro rupee dubu daya kwatan kwacin kudin nijeria a yanzu naira dubu hamsin ya ajjiye mata saman qafarta ya juya karo na biyu yana shirin sake rufe qofarsa
Ta tabbatar idan ya subuce mata a yanzu mawuya cine ta sake samun dama kwatan kwacin wannan don haka cikin zadin nama ta tattara kalmomin"idan kamin haka baka min adalci ba zaka kashe min gwiwa ne na aikata aikin alkhairi,ni bana buqatar kudinka
Da haka ta kashe masa gwiwa don bazaiso ta zama mara kirki ba ta sanadinsa ya sani idan har hakan ta faru yana da tagomashi a agun Allah,dole ba dan yaso ba ya bude wallet din ya bata passport din hadi da karanto mata numbobinsa ta kwafe tsaf bisa wayarta tayi serving,tun daga lokacin hotonsa shi ya zama abokinta da zarar ta kadaice shi take sawa a gaba tayi ta kallo,kyan Aliyyu na qayatar da salima ya tafi da imaninta 100%
Takan bata lokaci tana gurin kiransa amma ba zai daga ba,ta jure hakan ba tayi zuciya ba tana ci gana da kiransa,yau da gobe tafi qarfin wasa har takai da idan ta kirashi sau goma zaoyi qoqari ya daga mata ko sau daya ne shima daga gaisuwa bai bari a wuce haka,an halicci zuciya abisa son mai kyautata mata to hakan yake don kuwa kulawa sosai salima ke nunawa aliyyun mutum ne dama da bai taba budurwa ba samun hakan yasa ta shiga cusa masa ra'a yinta sannu a hankali har ya minta da ita ya bada amannar zata zama abokiyar rayuwarsa
Asalin salima 'yan katsina ne mahaifanta,yan boko ne na bugawa a jarida irin mutanen nan ne da ake cewa"yan boko aqida"wato ga karatun bokon ga kuma bin duk wasu aqidu nasu, bokon suke da gaske babu sirkin addini ko kada cikin mu'amalar rayuwarsu ta yau da gobe bokon kawai akasa agaba shine madubi,hakan yasa tun a nijeria salima ke alalace don babu kwaba balle hantara da zarar kin kai shekaru goma sha takwas a gidansu to kina da yancin yin komai da kika ga dama,iyayenta na da arziqi daidai gwargwado don su suka dau nauyin karatunta ta fita indian
Mutum daya ne salima ta yarda da shi ta sallama masa jikinta a nijeria suke harkarsu duk da tana bawa wanda taga dama kanta yayi tabe tabensa don a cewarta ita babbar harka take,sai kuma zuwanta india ne wani abokin karatunta rahul,shima din tunda ta hadu da aliyyu tayi mishi fata fata sukayi handing over don kuwa tunda ta ga aliyyun tayi amanna ta samu kalar namijin da take so ya zama miji a gareta ya hada komai hundred percent
Cikin lokaci qanqani salima ta dage a tada maganar aure don kuwa tsoron take kada ta rasa aliyyun saboda tana ganin yadda mata jinsin qabilu kala kala dake indian mazauna can yan asalin indian da kuma baqin haure ke kara kaina akansa abunda ya sauqaqa abun ma babu fara'a ma bisa fuskarsa ko yaushe tana daure ne tamau balle kice zaki kawo masa wargi
Bai damu ba suka koma gida nijeria aka gama komai sannn ya dauko ta suka dawo indian saboda business dinsa ita kuma ta samu ta kammala karatunta,dole salima ta yakice duk wani abokin shashancinta saboda matsananciyar qauna da take ma aliyyun
Ba qaramin tashin hankali aliyun ya shiga ba yadda ya sameta ba budurwa ba duk da bai san ya budurwar take ba hakanan tasha stitches duk don ta matse,yafi aqalla sama da wata abun ma dukansa amma kasancewar sa mutum mai tsananin kishi da baijin zai iya auren mace ya saketa wani ya aureta yasa ya qyaleta,bugu da qari tsantsar qauna da take masa tamkar ta fidda ranta ta bashi,yayi imanin idan ya rabu da ita mawuyaci ne taci gaba da rayuwa parfectly
Cikakkiyar kulawa aliyyu ya dinga samu sosai daga farkon aurensu duk da ya fuskanci qalubale da dama na wasu ayyuka na cikin gida wanda ya zama dole kowacce *cikakkiyar mace* ta iya su,kama da girki zuwa tsaftace gida amma sai yayi haquri da hakan yake koya mata wasu abubuwan da niyyar idan sundawo gida nijeria zai turata makarantar koyon irin wadannan abubuwan
Abu na farko da ya fara kawo babbar baraka a zamantakewarsu wanda shi ya zama sila kuma sanadiyyar barkewar alaqar dake tsakaninsu shine,wata uku da yin aurensu ta soma rashin lpy,tuni suka yiwa mumbai general hospital tsinke sabodancita take sosai ,ba bata lokaci likita ya fara aikinsa cikin dan taqaitaccen lokaci sakamako ya bayyana sun samu qaruwa Allah ya albarkaceta da samun juna biyu
Ba qaramin tashi hankali da razana aliyyu ya tsinkaya ba kan fuskar salima shi da ya tsammaci ganin farinciki,tun acikin asibitin take kuka wi wi har suka iso gida,duk da ya kawo abubuwa da dama cikin ranta game da kukan da take sai dai ya hani zuciyarsa da yanke hukunci bisa zato da zargi,don ya tabbatar ya matsa mata da tambayar mekw faruwa? Bata yi qasa agwiwa ba kuwa budar bakinta tashin farko ta ce masa"gaskiya darling ban shirya haihuwa ba yanzu babu abinda ke cikinta banda wahala da tsofar da mutum,just shekarata ma nawa da zan fara shiga rayuwar raino da wahalar 'ya'ya?,am just 25 fa"ta qaraahe maganar idanunta na malalo da hawaye
Da fari ua dauka rashin fahimta ne saboda boko da ya dabai baye rayuwarsu don haka sai ta ma bashi dariya ya murmusa idanunsa akanta yace"that's my salima,wannan tunanin naki fake ne it's not real,haihuwa ai ni'imace daga Allah wanda kudi ko mulki ko wata isa basu isa su baka ita ba,tsufa kuma ai lokacine,idan yazo babu abinda ke tareshi,bama haka ba idan kika ga haihuwa tasa mace tsufa ya danganta ko daga gareta ne rashin gyara ko kuma daga yanayin kulawar da take samu daga mijinta,ke kam baki da wannan matsalar ko daya,come on baby dont bother your self kinji,I promise I wil be with you cikin ko wanne irin yanayi"
Wannan duk baiwa salima ba tun aliyyu na rarrashinta har ya gaji ya sanya mata idanu,daga qarahe ma ganin ya zuba mata idanu sai tayi tsammanin ko ya haqura ne gaba daya?,sai kuwa ta fito masa da aniyarta na son zub da cikin wai ko don ta samu taci gaba da yin karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tunda tana final year dinta watanni kadan suka rage mata zata fuskanci exams
A ranar taga bacin ran aliyyu irin wanda bata taba ganin irinsa ba,yayi mata kaca kaca ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya mata jan kunne mai zafi akan kada ma ta yarda koda mistake wani abu ya samu cikinsa bazai lamunta ba bare kuma intentionally,ta tsorata ainun amma duk da haka ta kafe ta turje akan bata ga abunda zai sata zam da cikin ba tunda bata so ai ba'a dole shi kuma yace zai mata dolen kuma zata gani,kamar ta haqura amma zugar qawaye na sake tunzurata,cikin rikici ta dinga rainon cikin ji take kamar tasa hannu ta fisgo abinda ke cikin ta jefar ta huta,wani takunkumi ya kafa mata ya hanata fita ko ina hakanan ya hanaduk wani mai zuwa zuwa gurinta,makaranta ma shike daukarta ya kaita ya kuma tsaya a bakin inda da zata dau lecture din har sai ta kammala ya daukota ya maidota gida ya kuma kulleta sannan ya fice sabgoginsa
Da wannan rikici ta kammla karatunta yayi clearing din komai nasa ya dawo Nigeria shi da ita gaba daya sai dai idan wani abu ya kamashi na yaje indian sai ya tasata agaba suje tare su dawo tare don kada ma ya barta tsautsayi ya gifta tayi abinda ranta ke raua mata,don baijin idan ta aikata hakan zai iya qyaleta ko ya daga mata qafa,
Ita kuwa ta samu sake rigima harda mara dalili yinta salima take dom dai taga duk ya dora burinsa kan cikin,ya zuba mata ido ne saboda albarkacin yaronshi da take dauke da shi gashi mai tausayi ne qwarai da gaske kan mace mai ciki,hakanan tsakiyar dare sai ta tashi ta zauna ta kuma taahi aliyyun suyi kwanan zaune ta kuma kwana tana rusa masa kuka da ihu ita wai cikin ya dameta ya hanata sakewa
Cikin haka ne ranar wata juma'a aliyyubya fito a masallaci aka masa waya asibitin doctor sa'adah yazo salima ta haihu,yayi matiqar mamaki don kuwa cikin watansa takwas da sati biyu kuma lafiyar Allah ya fita ya barta a gidan babu wasu alamun naquda tare da ita don baccinta ma take shirga,baiyi qasa agwiwa ba ya isa asibitin cike da murna doki da koma mamaki,yana zuwa ya samu qarin bayanin zuwa tayi aka turo naqudar ta qarfin tsiya wai ta gaji da zaman cikin ajikinta don lafiyarta lau ta iso asibitin,yayi fada sosai don sunga doctor sa'adah bata nan ne da ko bakin salima zai cire don roqo bazata yi mata ba har sai da yarda da kuma izinin aliyyun
Ransa yayi mummunan baci saidai yana yin tozali da santaleliyar baby girl din da Allah yayi masa kyautarsa sai farin ciki ya mamaye gurbin bacin ransa tuni yama mance da abunda ya faru,sak kamammin family dinsu tayo ya rungume yarinyar tsam tsam a qirjinsa qaunarta na mamaye jinin jikinsa,ya dinga kissing din yarinyar da tofeta da addu'o'in tsari kala kala,tuni gidansu ya cika da yan uwa mominsa farin ciki tamkar akan yarinyar ta fara jika,duk wani uatsina da salima keyi da daga kai ita da yam uwanta hakan bai dami yan uwan aliyyu ba domin su gadon arziqi ne ba taka shi sukayi suka haye ba rana tsaka,harkar girma kawai sukeyi
Suna akayi na tserewa sa'a,yarinya tayi albarka sosai don daga salima jar aliyyin babu wanda bai ga hakan ba,khadijatu shine sunan da ya mominsa ta zaba mata don abba ya bawa zabi shi kuma yace ya bawa momin ta zabawa kishiyarta sunan da kanta tayi murmushi tace ta bata khadijatu tana fatan Allah yasa ta yi gadon hali irin na mai asalin sunan,salima dama wannan bai dameta ba ita dama ta rabu da cikin shine agabanta alaqaqai kamar yadda ta laqaba masa
Aka gama wannann ta wuce salima ta sake qirqirar matsala ta biyu wadda ta tunzurashi ta koma jawo igiyar aurensu ta guntule
Mrs muhammad ce👑
📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[10/16, 1:48 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*WA YASAN GOBE?...*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*written by safiyya Abdullahi musa huguma*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*Part 2*
1⃣9⃣&2⃣0⃣
Yadda abun ya faru shine salima sam taqi shayar da iftihal,anty hauwa ita ta gani ta yiwa salima magana cikin nasiha da kuma fadakar da ita illolin dake tattere da qin shayar da yaro nonon uwa indai ba lalura ba mai qarfi wadda zata jawo hakan koda hakan ta faru wasu basu yarda da madarar suna kai dansu ne ga wata wadda suka amincewa halayenta ta shayar musu da yaro balle ita da lafiya lau ne babu wata lalura,qememe salima tayi da ranta taci gaba da dirkawa iftihal baiwar Allah madara ba tare da masaniyar aliyyu ba
Ranar da lamarin ya faru sati biyu ne da yin haihuwar cikin yan suna wata ta sanar da ummi halin da ake ciki don haka ta aiko anty hauwan takanas da roqo da kuma lallashin salima tayi haquri ta shayar da iftihal don abun ya daga hankalin momin tace ko lafiya ce bata da ita tayi magana sai a a samo mata magani cikin tsiwa da rashin kunya salima tace"ita momin ce ta aiko ki?to ki gaya mata babu dan iskan da ya isa ya jawomin abinda zaisa jikina ya lalace lafiyatq qalau saidai tun farko na gayawa ubanta ban shirya haifarta bane,don da na samu dama da tuni tabi rariya ba zata ma zo duniyar ba bare azo ana min iyayin banza da wofi akan...........
Bata qarasa ba taji saukar lafiyayyun mari hagu da dama na kumatunta,da sauri ya daga kai din taga wanda yayi mata irin wannan aika aikar,aliyyu ne tsaye bisa kansa cikin matsanancin fushi fuskarsa tayi jajur😡 abunka da fari huci kawai yake fitarwa kamar wani zaki ya dora da cewa"bansan baki da mutunci ba sai yau ashe ke 'yar iska ce ban sani ba? Mahaifiyata kike fadawa wadannan mugayen kalaman?.....to bari kiji salima.....👉har yau ba'a haifi yarinyar da zata ci mutuncin iyayena ba wallahi duk son da nake mata,yarinyata kuma daga kin bar bata madara indai ni ke aurenki"
Cikin hasala ta miqe tana nuna kanta tace 👆🏼ni ka mara aliyyu?....ni ka mara?,to an fada din yarinya kuma wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata sha min nono ba,ai kana da yan uwa mata kana iya basu ita su shayar maka ko ka samar mata wata uwar ko kuma ka maidata cikinka ka sake haifeta"ya harzuqa matuqa ya daga girarsa yana kallonta "oh haka kika ce! Indai kuwa haka ne baki da wani amfani" "to ba sai ka yiwa tufkar hanci ba"a zafafe ya gyada kai yace "ok,well kije na sake ki saki daya"
Maganar tayi matuqar girgizata tayi zumbur ta miqe ta dangwarar da iftihal da da take riqe a hannunta tace"tafi nono fari ai" ta shige bedroom dinta,yarinyar tamkar kuwa tasan meke faruwa ta tsandare da kuka,ko waiwayo ta bata yi ba,anty hauwa tuni ta qame hannunta aka 🙊🙆🏻saboda sakin da aliyyun yayi
Ta fito dauke da akwati tana shirin fita,sai lokacin anty hauwa ta samu bakin magana "kiyi haquri don Allah ki dauki yarinyar nan"ta juyo a fusace sannan tayi murmushin takaici ta dubi anty hauwa"ai burinku ya cika ko?kuma ina tsammanin kema macace akwai nono a qirjinki kamar nawa to kina iya bata naki"a fusace aliyyu ya sake tasowa da niyyar kai mata wani marin anty hauwa ta tare gabansa
"a'ah aliyyu kada ka sake dole taji haushi its our fault dont beat her again mu lallabata ta dauki yarinyar dai"cikin harzuqa da tsawa wadda baisan yayi ba yace da anty hauwan"ni👆🏼 ni zan lallabata don ta dauki iftihal god forbid anty"ya fada yana kada kai"ko zata nemi hakan ba zata samu ba"bai san ya sake tura ma salima wani baqincikin ba da sauri ta ja akwatinta ta fice,a sanyaye anty hauwa ta juya ta dauki baiwar Allah iftihal dake nannade cikin showel tana ta tsanyara kuka kamar tasan abunda mamanta ke yi ,sanyata tayi a kafada tana jijjigata tana kallon aliyyu dake zaune saman kujera dafe da kansa idanunsa alumshe jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada tasan alamun tsananin fushin aliyyu kenan tun yana yaro ,a hankali tana shafa bayanta har yarinyar ayi shiru da yake mai haquri ce bata da rigimako kadan matuqar ta qoshi
Zaman sukayi tamkar na makoki na kusan minti talatin sanann tace"aliyyu tashi mu wuce gida dole su abba suji irin aika aikar da kayi,ya kada ki bayan ya bude idanunsa da suka koma ja ya kalleta"ban yi laifi ba wannan shine hukunci da yafi dacewa da ita,ni nasan me dame salima ta yimin bayan wannn tun alokacin ta cancan ci narabu da ita amma na daure"ya maida kasa kujera yana maida numfashi ya daga mata hannu alamun ta tafi kawai
Ta girgiza ki tace "a'ah bazaiyi na qyaleka ki kadai ba kana cikin irin wannan mood din"ita tayi driving shi kuma ta bashi iftihal din ya riqe,ido sosai ya zuba yana kallon yarinyar tausayinta matuqa ke shigarsa yana tausaya mata na rashin dacen uwa da bata yiba ya rungumeta tsam tsam a qirjinsa cike da qaunarta
Fa babu irin wanda momi bata yi ba tamkar ta ari bakin wasu,kamin abbansa ya dawo ya dora da nashi,ce masa auke ai haquri shine mafita ba saki ba,shi dai uffan bai ce ba don baijin koda salima ta dawo tofa ta rasa shi shi da 'yarsa har abada
To kuma sai aka taki saa ko rashin saa zance ne?uncle abba me ya nuna dattako da kansa ya taka gidansu salima don yin bikonta,qara ra a gabansa abban ta ya nuna masa shifa ba ruwansa bazai tursasawa 'ya 'yansa ba don suna da 'yancin yin duk abinda suka ga ya dace da rayuwarsu,amma zai kira salima atambayeta idan zata koma to,da yake a cikin zafin kanta take a lokacin bata ji kunyar budar ido tace da uncle abba ba itafa ba zata koma ba"abban nat ya kalleshi yace"to kaji mai zaman tac3 bazata iya ba"abba bai sake tofa kanzil ba ya bashi hannu sukayi musabaha ya dawo gida
Lamarin rayuwar gidan nasu yayi matuqar bawa uncle abba mamaki,rayuwar'yancin kai suke irin ta mai jan kunne?ba rayuwa ba irin ta addininmu wadda fiyayyen halitta ya koyar da mu ba?,wanna wane irin masifane da a yanzu muka qaqabawa kanmi?,bayan ya dawo ya sanar da momin yadda sukayi,ita kanta da ake mace abun ya daure mata kai amma kasancewarsu iyaye masu dattako da basu so dansu yayi saki sai ta nemi izini gun uncle abban akan ita ma zata je ko za'a dace"uncle abba bai hanata ba yadda mai akai da mahaifin salima exactly haka akayi da mahaifiyarta don aqidar duka iri guda ce
Saidai ita an samu dan bambanci kasancewar salima tafara saukowa har ta fara kewar aliyun sai mamarta tace wa momi saidai aliyyun yazo da kansa,nan momi ta saka shi gaba akan lallai lallai ya shirya yaje,shi dai kullum yana binta ne da to don kuwa ya riga ya gama yankewa ransa cewq ko itace autar mata yq haqure mata don gaa daya ta qarasa ficewa fit daga ransa,bata da wani abu a yanzu da zata burgeshi da shi
Ganin momi ta soma tsanantawa a al'amarin sai ya soma shirin komawa indiyarshi ba tare da sanin kowa ba bai so ba ba kuma a son ranshi ba don baiso yayi nisa da yarinyarshi sai da ya kammala ne suka sani,momin taso ta hana abba yayi mata magana aka ta tsagaita hakanan da Maganar dole sai salima ta dawo idan da rabo zaman bai qare ba zata dawo ne,aliyyu mai tsananin biyayya ne bashi da tarin kunne akan duk wani umarni da iyaensa suka bashi,yana dai da zurfin ciki ne da nauyin baki,tun yana yaro idan suk ce yayi abu ya kafe baiyi ba to yanada dalilinsa ne mai qwari wanda sai daga qarshe idan suka bincika sai suga lallai yana da gaskiya
Momi ta gamsu da bayanin abban ta kuma yiwa aliyyun fatan alkhairi da samun dacewa,aliyyu ya bar nijeria 🛫cike da kewa da qaunar 'yar diyar tashi tsoka daya a miya khadijatul iftihal,ya tanadar mata duk wani abu da zata buqata daki guda ya ware mata yajibge mata komai hatta da ruwa da zata sha ya tanadar mata bai bari ya dorawa kowa wahalarta ba harda kayan banza ma da wofi wanda bata buqatarsa,hakanan ya bude mata account duk wata yana saka kudi a ciki yace da momin aje a cira ayi mata abinda tale da buqata,to kawai take cewa kamar yadda uncle abba ya umarceta don shi tuni ya karbe ragamar komai din kudin da aliyyun keta aikin turowa uncle abba yace abarshi cikin account din ta amfanesu idan ta mallaki hankalin kanta
Wata shida kacal salima taji ajikinta qaunar aliyyu da yarinyarta tamkar zata zautata cikin begensu take kwana take tashi,yayin d iftihal ke cikin walwala da samun gamsashshiyar kulawa gata da soyayya ta qannen uba kakanni na gun uba da kuma dangainsa,tayi bulbul abinta madarar dai ita taci gaba da karba don itama taqi nonon kowa zakaran da Allah ya nufa da cara sai gashi cuta mai taba yaro bata taba samun yarinyar ba don ko haqori tashi sukayi suka ganta da shi ya soma fitowa,ga wayo a gunta gane mutane da kaifin basira
Shekara daya da rabi salima ta kasa daurewa,ido ta rufe ta soma neman aliyyun,saidai ya riga ya toshe duk wata kafa da zata sada shi da ita,sai daga baya ta samu labarin ya koma india,ba bata lokaci tayi visa ta bishi don zamanta da aliyyu ta samu dukiya sosai kasancewarsa mai sakin hannu shi yasa hatta zaman gidansu take jin bai mata ba
Acan din ma bata sameshi da wuri ba don ya canza gari ma gaba daya sun zauna a mumbai ne shi kuma ya koma new Delhi taci wuya ka su hadun saidai haduwar tasun mabata haifar mata da d'a mai ido ba,kaca kaca yayi mat irin wanda bata tsammani ba ya kuma jamata kunne da idan har ta sake suka kuma hada hanya sai ya wulaqantata,ta samshi qwarai idan ya fusata baida dadi iya kuma qurewa ta sani ta qureshin don haka bashiri ta tattara ta dawo nijeria ba tare da ta cimma nasara ba
Aliyyu bai waiwayi nijeria ba sai bayn shekaru uku cike da nasarori da budi masu tarin yawa wadanda bai taba tsammatar samunsu ba,company nasa ya bude babba acan hadi da qulla harkokin kasuwanci kala daban daban da wasu manyan kamfanonin,yazoya taras salima naci gaba da bibiyar rayuwarsu shida yarsa taqi aure sam duk wadata tsaya da shi sai taga ba namiji bane ganinsa take kamar mace yar uwarta taqi sauraron kowa da komai,itace kira saqonni na email sms duk wata kafa da ta samu ya rabu da duk wasu layukansa saboda ita amma ya rasa yadda take samun sababbi,sunzo don a basu iftihal yafi sau hamsin tun yana india suke da muradin haka ya gaya masu su da iftihal saidai su ganota daga nesa don bata buqatarsu
🔱 🔱🔱🔱🔱🔱
*samira*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Shekarunsa hudu da dawowa ya hadu da samira gun bikin abokin kasuwancinsa,tunda ta qyalla ido a kansa ta qwallafa ranta,ta rasa ta inda zata samu shiga domin kuwa baida walwala ko sakin fuska shi yasa take fargabar tunkararsa,da yake tare yake ta hidimar bikin abokin nasa da iftihal dinsata lura da yadda yake ta nan nan da yarinyar ta samu kuma information kanncewa 'yarsa ve da yake tsananin qauna sai itama ta jata ajiki sosai tattali take nuna mata kamar babu gobe,shikam mai son wanda ke son iftihal dinsa ne don haka ya sakar ma samira duk da ya ja jikinsa sosai da fari saboda yakan tuna yadda ta kasance masa a baya tsakaninsa da salima
Itama tazo akan gaba don lokacinne tsananin ya sake aure ya masa yawa a gida ahi kuma a zahitin gaskiya a wannan lokacin bai da time na duba mace,ganin ya samu maison iftihal dinsa yasa ya amince daga qarahe ne ma momi ke masa albishir din itafa ba zata bashi iftihal ba donnta riga tazo kenan,ba yadda ya iya duk da son da yake wa yarinyar tasa
Sai da salima ta gasu sosai fiye da tsammaninta wanda tadinga jelen kamun qafa da momi da abban da a baya ta watsawa qasa a ido kullum tana cikin gidantana magiya sannan ta samu dawowa gidanta,gidan da ta tarar ya kubce mata har wasu biyun sun samu mazauni cikinsa,ya ta iya da ranta son da take masa yasa bata ji wani abu ba tayi zamanta duk da a baya tana daga cikin matan dake iqirarin basu ba kishiya don ba zasu iya zama tare da ita ba
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
*_dawowa labari_*
🔱🔱🔱🔱🔱🔱
Washegari tun qarfe tara fadila ke shirin fita suna,tayi wanka ta shirya tsaf cikin shadda dinkin doguwar riga ne yasha aiki daga sama har qasa butter colour ta debi wadanda zata sauya a can kala biyu ne da tayi musu anko ita da faridan zasu sa tare ta shirya iftihal cikin itama doguwar rigar yan kanti wadda ajiya ta bada aka siyo mata hade take da takalminta da ribbons dinta red ce in and top ta tsaya mata iya qauri takalmin boot ne na yara fari qal tayi ma gashin yarinyar ado da fararen ribbon tayi kayu matuqa kasancewar yarinuar mai yalwar gashi mai tsawo da santsi
Hat ta tada motarta iftihal ta hango abban nata ta balle murfin motar ta fice aguje,bayan ta duqa ta gaidashi ya dauketa yana wulla ta a sama shiko nauyi bata yi masa"cewar fadila cikin ranta tana satar kallonsu,tana ganin iftihal na nuno mishi ita,ya juyo ya kalleta suka hada ido tayi maza ta sunkui da kai don kada qwayar idanunsu ta hadu ya saka mata dafin da ya saba jefa maya cikin zuciyarta na qarin qaunarsa,"verry neat ya fada sannan ya dauke kai"iftihal ta leqa fuskarsa "daddy munyi kyau kuwa"yayi kissing kumatunta yace kinyi kyau sosai my dear"tadan bata fuska tace "anty na fa?"yayi yar qaramar murmushi yace "both of you""thank you daddy"ya sauketa bayan ya sake kissing dinta tana daga masa hannu ta zura aguje ta dawo cikin motar tana dariya
0 comments:
Post a Comment