*KARSHEN PAGEN BAYA*
~In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke fuska. Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama~
```»»Tun a mota yar babyn ta fara magana. a cikin wata irin karamar murya. "Sunana safuratu ina tayaki murna da sayana da kikayi". Fatima ta juya domin ganin mai magana bataga kowa ba. tace "abba kaine kayi magana Yanzu?". yace "aa magana kikaji nayi". tace magana naji ko yar babyna ce?. alhj murmushi yayi yace "'yar baby kuma ai ba irin mai magana bace bakiga batada speaker ba...?. Kafin ya rufe baki wata siririyar murya ta kara magana, "Zan dinga saki dariya, zan dinga baki labarai masu dadi, amma ni fa ba'a barina da yunwa, kuma ni kullum sai anyi min wanka an canza min kaya anyi min make-up....." alhj tsurewa yayi domin yaji tabbas yar babyn ce ke magana a tsorace ya fige yar robar yana dudubata wai ko zaiga speaker a jikinta amma bai gani ba. ita kuwa fatima murna kawai take da jindadi yar babynta na magana. alhj yace "fatima 'yar babynki ce fa mai maganar nan to amma ni banga speaker a jikinta ba"
. fatima ta karbe abunta tace "Baba ai itama da baki take yi kamar mu baka gani bane?".
yace "eh ni ban gani ba, amma bari in na koma zan tambayi mai shagon inji ko tana magana. Domin ni ta bani tsoro fa mamana". Haka dai yaci gaba da tuki cike da mamaki har suka karasa gida. fatima ta sauka da gudu tana murna ta nufi cikin gida rungume da yar babynta a parlo ta iske duk yan gidan yara nata rashin ji masu wasa nayi masu rigima ma hk. ai kuwa yan yaran na ganin yar babyn suka yo kan fatima wannan ya karba wannan ya figa wai ko wane yaro sai ya je gurin uwarsa ya kama kuka wai a kwace a bashi. can wasu yara marar ji guda biyu daya ya kama wajen kan yar babyn daya kuma ya kama kafafun sai jayaya suke wannan yana so ya karbe wannan ma yana so ya karbe fatima kuma sai kuka take zasu karya mata yar baby gashi ba dama tayi mgn.
lokacin alhj ya shigo. "kai! kai! ku wane irin mararsa jin magana ne. zaku balla mata abu bata kayanta maza". mika mata sukayi. ta karba ta nufi dakinta asiya ta harare ta tace a zuciyarta "munahika ai alhajin zai tafi zaki ci ubanki". alhj yace "yanzu ku kuna gani a gabanku zasu batawq yarinya abu a gabanku amma ko kuyi magana. haba asiya kece babba fa ko sauran basuyi magana ba ai ya kamata ke kiyi mawa yaran magana". "uhm ai ni kullun a wajenka marar adalci ce to amma yanzu kai ga adalci nan a fili ka nuna mana, tunda ga yara nan da yawa a gida kuma duk yayanka ne amma ace ka ware fatima ita kadai ka saya mata abu. wannan shine adalci ko?". Ran alhj ya bace har zaiyi mgn kuma sai ya fasa ya wuce up stairs. yaje dakinsa ya dauko kudi yq fito yayi tafiyarsa.
su Zuwaira sukayi dariya sukace "aunty asiya kin min daidai ke kadai ce maganin alhj a gidan nan". asiya tace "hmm ku kyale sa ai yau saina toya yar babyn nan muga ta tsiya sai inga me zaiyi haba ya zai dinga fifita wacce kudabukar yarinyar a kan sauran yara bari inje gurinta". su Zuwaira binta kawai sukayi da kallo. ta tashi buzun-buzun ta ta nufi dakin yara. fatima zaune take a kan gadanta ta zaunar da yar babyn tana cin bisket itama tana tura mata a baki. tana ci ci diyata daga bakin. kawai sai taga bakin ya bude. bata wani firgita ba sai ma dadi da taji. ta tura mata bisket din tace "kin koshi.?
lokacin asiya ta karaso gurin ta kama yar babyn da hannu daya ta wullata jikin bango ta fado tim! ta kuma wanke fatima da mari "shegiya yarinya me kike a nan tun dazu ina can ina jiranki zan aike ki kin wani shigo daki kin zauna. dama nasan wannan yar babyn da kika samu ita zata dinga hanaki aiki amma bari ynz in dauke tq in yayankata in toya muga ta tsiya". fatima ta fashe da kuka tana bawa asiya hakuri karta yanka mata ya' abun mamaki fatima na fara kukan suka jiyo kuka a baya. asiya ta juya baya. yar babyn ta gani a zaune tana kuka harda ruwan hawaye
Abunda yayi mutukar tsorata Asiya kenan, da gudu taje ta shige karkashin gado, fatima na ganin haka ta sauko tuni tama bar kukan ta fara dariya, mama asiya ta bata dariya. Zuwa tayi ta dauka yar babyn tana lalashinta. "Yishiru-Yishiru diyata. Mama asiya ce ta taba min ke ko?" Kunnuwan asiya sunji lokacin da yar babyn tace "Eh itace". Cikin wani karamin voice, "To yi shiri bazata sake ba". Asiya a dan tsorace ta fito daga nesa tace "Au! Fatima dama yar tsanar taki tana magana?". "Eh mama asiya ai tun a mota ta fara magana, babama ya dauka bata magana". Asiya tace "to dan kawo ta mu gani". Amsa tayi ta duduba amma bataga speaker ba. "Fatima ina speaker da wajen sa battery?". Mama ai da baki take magana kuma ba'a saka mata battery, yanzu nayi mata wankq bata bushe ba".
Abuda ya fadowa asiya a rai shine. Hawayen da ta gani wato ruwan da fati tayi mata wanka ne. Ai kuwa ta maka diyar da kasa tasa katuwar kafarta ta taka tabi ta samanta ta wuce tana hararen Fatima hade da cewa. "Dauki yar iskar yar tsanar ki, ko dan wannan ai tama wuce yar tsana a girm saidai ace *ALJANAR FATIMA*. Fatima bata tanka mataba da sauri taje ta dauki yarta taci gaba da yin wasa da abunta.
A falo ta iske su Zuwaira suna nan inda suke basu tashi ba. Asiya tana dan dangeshi ta karasa ta zauna ta saki wani gwabran nishi. Wanda yasa su Zuwaira saurin tambayar "Lafiya dai aunty babba, fatan kin yayanka shegiyar yar tsanar nan..." Tarar nunfashinta tayi ta hanyar cewa, "Ina fa 'yar tsana da ta tsoratani. Ashe wai tana magana, ban sani ba ina shiga dakin na karbe ta na maka a bango juyawar da zanyi sai naganta tana kuka harda hawaye. Ai kafin kice me tuni na shige karkashin gado na dauka ai aljana ce, washh! Wllh har yanzu gabana faduwa yake". Su hauwa najin haka suka kwashe da dariya hararar da ta daka musu ita tasa su hadiye dariyar dan dole. "Wai ina su asmart ne ko har yanzu basu dawo daga wajen kitsan ba". Asiya ta tambaya. "Eh wllh kinga har yanzu basu dawo ba, Ni jirama nake su nasan su zasu lalata wannan 'yar tsanar". Zuwaira ta bata amsa. "Ai kinji shiru gidan dake basa nan".
Su Nasmat kuwa na can gidan kitso gaba daya su hudun harda Fiddausi da ameera. Dake mai kitsan tasan halinsu suna zuwa tace su zata fara yiwa su tafi abunsa.kafin a gamawa asmart kitso saida nasmat ta Zubar da duk ruwan gidan, wai wanke kai take daga ta wanke sai ta shinshina tace wari yake. su Fiddausi dama basuyi magana ba dake sunsan halin ta idan ma sukayi mata magana baji zatayi ba. Da sauri mai kitsan ta burbura tayiwa asmart kitson Nasmat duk ta jike kan, Amma a haka mai kitsan tace tazo a mata dake ya dansha iska. Haka itama asmart tata barna kafin a gamawa nasmat saida tasa yara sunfi biyar kuka a ciki harda wanda ta fasawa kai. Jini na zuba yaran tafi ya gayawa uwarsa. Asmart tazo ta kama nasmat kitsan ma ba'a gama ba sauran layi biyu. Amma a haka suka gudu, basu zame ko'ina ba sai gidan aunty Sakina yayar mamar su ce. (Wato mama asiya.)
,
Matar yar lukuta wacce itama jikinta ya kai na mama asiya. Nan ta tashi tana musu sannu da suwa. Bayan sun gaidata. Tace, "Asma'u uwayen rashin ji ziyara aka kawo min yanzu da yamman nan?". Bayan sun kalli junane asmart tace "Eh mama asiya ce tace mu zo kuma ma a nan zamu kwana". Sakina tace to madallah ai naji dadin zuwanku dama ga aiki nan kaca-kaca ya min yawa a gida sai ku dan kama man muyi sauri mu gama kan magariba". Cikin daga murya nasmat tace, "Kutumelesi kiji wannan matar wai mu tayata aiki". "Yaseen ni dai bazanyi ba saidai ke ki tayata". Cewar Asmart "Kutt kinga malama yayar mamar ku ce ba yayar mamana ba. Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata". "A'a wallahi ke dai". Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.....,.............```
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 19-20
NA. 👑 KING BOY ISAH 👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
IN DEDICATION TO YOU
*KHADIJA CANDY* *_ALLAH YA BAR ZUMUNCI, YASA KIFI HAKA NA GODE DA ADDUO'IN DA KIKE MIN. KEMA KUMA ALLAH YA KARQ MIKIN DUMBIN BASIRA DA HIKIMA DA FASAHA, ALLAH YA KARE MANA KE DAGA SHARRIN MAHASSADA DA YAN ADAWA DA MAKIYA. ALLAH YA TSARE MANA KE DAGA SHARRIN DARE. SHARRIN RANA, FATAN KOFOFIN ALKHAIRAI SU BUDE A RAYUWAR KI DUK NA SHARRIN SU GARKAME. AMIN YA ALLAH.*_
_SAM KALAMAN BAKINA SUNYI KADAN DA SU BAYYANA IRIN TSANTSAR FARIN CIKIN DA NAKE JI YAYIN DA NAGA SAKONIN MASOYANA SUN SHIGO WAYATA._
FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata". "A'a wallahi ke dai". Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.~
```»»Aunty Sakina da ta saki baki tana kallansu ita kallansu take abun yaso ma ya bata dariya kuma sai ta basar. Ta cire takalmin ta ta fara kwada musu da sauri suka saki juna. "Kaji yan iskan yara daga zuwa zaku mayar min da gida kamar gidan dambe?, To wallahi bazan iya ba ku tatara ku koma na gode allah ya baku ladan ziyara". Suna jin ta fadi haka sai suka shiga bata hakuri Da rokonta a kan tayi hakuri ta barsu.
Bacin rai tanuna musu sosai ta murtuke fuska tace, wallahi kafin in futo daga dakin nan ku bar gidan nan in kuwa ba haka ba wallahi sai jikin ku ya gaya muku". Tana gama fadar haka ta shige dakin. Su kuwa kofar dakin sukaje duk su biyun sukayi Neldown kamar wasu mutanan kirki.
Sanda tayi kamar mintuna biyar tukun ta fito daga dakin sun bata dariya a yanda ta sansu da rashin ji yau sune roko harda durkusawa. Nan dai tace musu ta hakura amma fa aiki ba'a janyewa'. Da sauri sukace "Mun yarda".
A can kuma gidan mai kitso uwar yaran da aka fasawa kai ce, tazo da wani danta saurayi dauke da wata gora. Da ganin matar kasan jarababa ce, ko yanayin tafiyarta zai iya shedama ba da alkhairi take tafe ba. "Wace yar kutu... Ce ta fasawa yarona kai, ku nuna min ita yanzu itama insa a rotsa mata nata kan". Matar ce ta shigo gidan da wannan furucin lokacin da dan nata kuma ya daga gorar yana shirin makawa duk wacce aka nunu. Da gudu Fiddausi da Ameera suka Ruga dakin mai kitso. Tana shirin binsu Mai kitsan ta shiga gaba ta tare kofar dakin tana "ki saurara basu bane ki saurare ni, kannansu ne basu ba". Tsayawa tayi tana jijiga. "To ai anzo a dai-dai kenan yanzu in nasa aka fasawa daya daga cikin yayyen nasu kai, kinga ai anyi 1-1 ko". Aa dan allah ba haka za'ayi ba kinga nidai kitso suka zo min nan kuma sun tafi gida tun lokacin da sukayi wannan ta'asar. So abunda yafi shine ki bisu can gidan Alhaji salim din".
"Kutumelesi dama yan gidan alhaji salim ne. Kai zo muje ba zama lafiya yau zasu san sun takali wutar dafa kansu". Fuwww!! Ta wuce yaran na binta bayq da kulki a hannu. Tun daga get suka fara rikici da mai gadi, yaki barinta tq wuce, sanda ta shsmmace shi tukun ta ingiza shi ya fadi da sauri suka shiga. "Asiya! Asiya! Asiya!". Da duk illahirin karfin sautinta take kwalla wannan uban kiran. Ta cire gelen dake makale a kafadarta ta daura a ku'gu.
Da sauri su asiya da sauran yan gidan suka fito suna tambaya "lafiya-lafiay". Cikin masifa da tsiwa tace, "Ina fa lafiya ai tunda kuka ganni a haka kunsa ba lafiya ce ta kawo ni ba. Wannan bala'eun 'yaran naku ne suka fasawa dana kai dan haka nazo ko dai a fiddosu insa a fasa musu kai. Ko kuwa kuga tashin hankali". Nan ta fara jijiga tana cewa dan saurayin nan ya matso kusa ya shirya. Asiya tace "Innalilahi yanzu su asmart bazasu barmu mu huta ba, Rikicin nasu ba iya gida ya tsaya ba kenan. Kinga mariya zo muyi wata magana".
Mariya tace itafa ba inda zata sai an fiddo da su asmart ta rama wa yaranta tukun ta tafi daga gidan nan domin har wani hauka-hauka take tana tsalle-tsalle lokacin da Asiyar kecewa suzo su sasanta. Da kyar asiya taja hannunta bayan dakunan su. Basu fi mintuna biyu ba suka fito suna washe hakora. Gaba dayan fishin da Mariya tayi ya zama tarihi ba abunda take sai godiya wa hajiya. Sauran matan sunyi mamaki abun ya daure musu kai. Mariya tayi musu sallama tacewa Dan saurayin "Kai zo mu tafi ai na yafe musu". "Haba mama Najeef fa aka fasa wa kai shikenan munzo a rama kice wai kin yafe". "Kai zanci ubanka fa wai bani nake maka magana ba?". Yana dan gungunin sa ya bita suka fita. Sunje fita mai gadi ya leko ta kofa hade da cewa "Jarababiya kawai allah ya isa turenin da kikayi". Da sauri ta juyo a fusce zatayo kansa "Me kake cewa". Habawa ai da gudu ya shige dakin ya rufo.
Bayan su Asiya sun koma cikin falo Zuwaira tace "wai aunty dukan matar nan kikayi ne ko kusa warning kikayi mata. Naga lokaci daya ta wani saukko". Yar dariya asiyar tayi hade da cewa, "Hmm ba ko daya daga ciki kinsan fa in kikaga mutum na irin haka to in kika bincika harda talauci a ciki, Naira 500N na bata kawai nace taje ayi mishi magani, Shine fa kinji harda su godiya". Dariya sukayi gabaki daya Hauwa'u tace "Gwara da kikayi haka wllh dan da alhaji ya zo ya tarar da ita. Bama su asmart ba mu kanmu bazamuji dadi ba". "Ashe dai kina ganewa gashi yau a dakina yake kinsan yanda muke da shi dama. Ai shiyasa nayi saurin watsawa Wutar nan ruwa".
************
Kwance take a daki ita kadai tana barci. Wata mahaukaciyar dariya mai gigitarwa ce ta daki dodan kunnan ta. Bata shirya ba ta tashi zumbur! A tsorace, tana waige-waige "Alhaji! Alhaji! Dubawa tayi gefan wajen wayam ba alhaji. Hahahahahaha! Dariyar mace ta jiyo kamar a downstairs a dan tsorace ta tashi ta bude kyaure a hankula ta laleka bataga komai ba, hakan yasa ta idasa fitowa. Da fitowarta Kofar dakin ta taji an banko da karfi kamar za'a balla, dan kara tayi ta zabura kuma. Lokaci ta nema bude kofar amma sai taji kamar an Garkameta da kwado. Abunda yayi mutukar girgizata kenan. A saman dakuna ne guda hudu dakinta ne a can karshe sai na Zuwaira sai na Hindu wanda yanzu alhaji ya mayar nasa. Na karshen kuwa na Hauwa'u ne. Dan lungun dakunan a haske yake fes da fararen Gululuka. Lokaci daya tada wutar ta fara farfari. Kwayayen suna wata irin girgiza dariyar Yarinya ne ya biyo baya dariyar marar dadin ji. Ahhh! Ahhh! Da karfe ta fara ihun itama. Ta durkushe a gurin ta sa hannaye ta rurufe kunnuwanta. Hade da runtse idanu. Dif! Taji komai ya tsaya an bar dariyar haka kwayayin sun daina girgiza da farfarin da suka. Mikewa tayi cikin kuka kuka ta fara tura kofa da karfi tana fadin "na shiga uku ni Asiya me ya fito dani. Gashi sai tsorata ni ake yi".
Ta baya taji an tabata wata murya yara taji ance "Mama Aciya juyo cigan ni nayi kyau?". A hankali ta fara juyowa dan ganin mai maganar a tsorace. Koda idanunta sukayi tozali da mai maganar Aljanine yazo mata asuffar Iliyasu babban Dan hauwa. Kanshi a rabe yake gida biyu hayaki ne ke fita da wani turiri a ko wanne bare. Aisiya na ganin haka jikinta ya fara bari ta hau kyarma. Dariya taji ya farayi marar dadin saurare. Ya nufo gunta yana fadin "Nayi Ceau (kyau) kuwa mama aciya(Asiya)?". ta kwada ihu! Ta zuba guje ta nufi Downstairs tsabar firgicewa Bata iya kirga iya matatakalan da take tsallakewa. Sabanin 'da, da in zata sauka da Daya-Daya take yi a hakan ma a hankali.
Tana saukowa tayi wata uwar tirjiya a falo nauyin jikinta da kadan ya rinjayeta ta fadi. Ba wani abu yasa ta tsayawa ba. Sai ganin wata yarinya da ke zaune a Falon cikin wasu fararen kaya masu dauke ido. Yarinyar ta juya bayane bata iya gane ko wacce ce. Hakan yasa ta fara matsowa a hankula tana kiran sunayen yaran gidan wanda take tunanin ko daya daga ciki ne. "Dan ubanki fatima me kike yi ne a nan?. Cikin wannan dare?". Shiru bataji amsa ba hakan ya tabbatar mata da ba fatimar bace. A hankali take tafiya tana nufar wajen da yarinyar take. "Ba fatim bace?. Shimsiya ce? Sa'adatu ce?. Ko dai salma ce?". Sunan jikokin ta take ta jerowa wanda take tunanin ko sune. Lokacin ta karasa wajen mika hannu tayi tana karkarwa kamar ta taba kamar karta taba. Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin..............,......```
TOFA MUJE ZUWA READERS. YANZU ZAMUGA GWANAYEN TSORO. AN FARA KENAN
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 21-22
NA. 👑 KING BOY ISAH 👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
IN DEDICATED TO ALL ZAMANI WRITERS. *ALLAH SARKI YAN UWANA UBAN GIJI ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR MU. A KULLUM GURINA INGA ZAMANI BA'A BARMU A BAYA BA. ALHMDULILAH KULLUM CIGABA MUKE. ALLAH YA KARA BASIRA, YAN UWANA DOMIN NI KAMAR YAYYAI NA NA DAUKE KU. AUTAN KU NE KING NA AUTAR KU QUEEN. ALLAH YA BARMU TARE YA KARA HADIN KAI. AMIN* ♥
.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
_Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin._
»» Aljanar a sufar shamsiya take, jikar Mama asiya hannaye biyu tasa da karfi ta shake wuyan dogayen faracen hannunta masu shegen kaifi. Bakin shamsiya wani bakin abune mai kaure ya fara zuba. Kuma idan ya zubo din a kan mama asiya yake sauka. Mama asiya in banda ihu da neman ceto babu abunda take. Da dai taga ba ko alamun mutane a gida wanda zasu kawo akaji.
Nan ta fara ihu tana kokarin kankare hannun Aljanar da ta makure mata wuya. Aljanar ce ta bude idonu hade da dakawa Mama Asiya tsawa. Ai kuwa fitsari ya fara zubowa harda dan guntun kashi da ya zubo. Fitsarin matseshi take amma zuba yake tsirrr! Duk jikin ta karkarwa yake. Magana na rawa "Haba shamsiya dan allah ki sake ni karki kashe ni me nayi miki ne?, nice fa mahaifiyar babanki". Mama asiya ce ke fadar haka. "Keeeee! Anji ke kika haifi mahaifina to ke kika haife ni ne ni?, Shin a yanzu ni dake waye baba ma?". Muryar mai kamar amsa kuwa aljanar ke magana da shi domin in tana yi dakin har wani jijiga yake yi. "Wallahi kece, kwarai kece baba. Kece uwata ma. Kece ubana, kece yayana, kece yaya ta kece.....". "Keee yimin shiru". Gum Mama asiya tayi ta tsaya da lissafin kafafunta sai rawar karkarwa take fitsari kuwa duk sanda aljanar tayi mata tsawa sai ya subuce ya kwararo. "Hahahhahahjahahhaha!
Aljanar ce ta dake kai sama tana wannan muguwar dariyar. Mama asiya ta dan shammace ta ta ware iya karfin da hannuwa biyu ta tura ta. Can aljanar ta fadi gefe. Tubur-tubur abu ga mai jiki ba gudun kirki, ta nufi hanyar Hawa sama, gaba daya wutar dakin ce ta dauke duf! Mama asiya bata daina gudu ba saida ta hadu da bango kanta ta buda ji kake gum!! Ta kuma zube kasa kamar an yarda buhun gero thom! Kanta ta dafe tana wash! Wash! Aljanar ta gani tazo dai-dai saitin kanta da wata wuka wulshe-shiya a hannunta. "Hahaha- wato ni zaki tserewa ko?. Wukuncin ki kisa ne". Da fadar haka ta daga takobin sama ta caka ma mama asiya a ciki.
Wani Mugun kara ta Saki ta tashi zaune tana nishi daya-daya tana laluba cikin ta jin ko da gaske ne abunda ya faru. Karar da tayi ya tashi alhaji zumbur! Ya fara tambaya "lafiya-lafiya"? Sai yanzu mama asiya ta fahimci cewa mafarki ne take ganin cikinta lafiya lau kuma haka kanta bata jin wani radadi. Alhaji ni kam wallahi bazan yarda ba ashe yarinyar nan mayya ce da wuka fa tazo zata kashe ni a mafarki, wallahi sai na dauki mataki a kanta, to ni kuwa me na tsare mata ne take nema ta cinye kurwata danya". Duk surutun da take alhaji binta yake da tambaya. "Wacece?, wai wace yarinyar". Budar bakin ta tace "Wace yarinya kuwa in ba wannan mayar...". Ta dan dakata tana tunani in fa tace shamsiya abun bazaiyi tsari ba. "Wace"?. "Wannan mayar 'yar taka ce Fatima, duk taimaka mata da nake a rayuwa wai ashe mayya ce ni tazo zata kashe". Tsawa ya daka mata nan da nan ya murtuke fuska, "Asiya bana san iskanci fa, bana san tambadar nan taki, kinje can kin tabo aljanunki sun motso shine zaki likawa marainiya wato. To wallahi kar in sake ji". Gungune kawai tayi, Alhaji kuwa ya kwanta ya juya baya abunsa. Mama asiya na zaune kamar ance ta kalli wajen mirror. Ihu! Ta kwalla ta rukun-kume alhaji kamar wacce zata shige jikinsa. Yarinyar ta gani a cikin mirror tana kiranta. Alhaji yana jinta ya kyale ta, can kuma saj yaji lema a jikinsa wanda yasan wannan ya wuce na gumi.
Tashi yayi yana "Asiya wai miye a jikinki nake ji sharaf!". Har tashin da yayi a rike take gam da shi idanunta a rufe. Wata mahaukaciyar dariya alhaji ya kwashe da ita, Irin wacce ya jima baiyi ba harda kama ciki. Asiya ido a rufe taki budewa tunani take in ta bude zata sake ganin aljanar, Jin dariyar alhajin taki ci taki karewa, yasata bude ido a hankali bata ko kalli wajen mirror ba. "Alhaji ai dole kamin dariya wannan mayar 'yar taka so take sai ta kashe ni ta huta". "Asiya kalli jikinki fitsari ne fa kika sharara duk kin bata gadon, Hahaha wai duk tsoran ne haka harda fitsarin wando?".
Sai lokacin Asiya ta lura da jikinta sharkaf take ta jika kayan barci da fitsari. A kunyace ta tashi da sauri ta nufi bandakin da ke cikin dakin domin tayi wanka. Bayan ta shiga ta juya baya tana kokarin Cire riga sai ji tayi wata kalar muryar 'Yan yara tace "Yauwa Shannunki da Juwa". Da gudu ta fito daga bayan dakin taje ta fada kan alhaji ta shishige mishi. Alhaji na niyar tashi yaje ya canza kaya domin ta jika shi amma sam ta hana ta rufe idanu ko budewa batayi. A haka suka kwanta har safe. Tun da safe taje dakin su fatima ta iske ta ta idar da sallah tana barci, nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne abun................
Ku danyi hakuri da wannan yaseen yau bana jin type din.
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 23-24
NA. 👑 KING BOY ISAH 👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*DEDICATED TO YOU*
QUEEN HAUCY 😘 = *ILLAR BASHI*
BEAUTY QUEEN 😘 = *BADDEEYERH*
UMMU AFNANN = *FATIMAH*
ZUWAIRA MADADA 🍼 = *MATA DA MIJI*
MARYAM 'YAR MAMA = *RAINAN KAUYE*
BEIBOH = *YASMEEN*
😍 _DA KYAU JARUMAI NA ALLAH YA KARA BASIRA_
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne abun.~
Fatima tace tayi sallah amma mama asiya bata barta ba saida tasakata kuka, "Shegiya mayya wato shine jiya kika zo zaki cinye ni ko. Harda wani canza suffofi ko kin dauka bazan gano kece ba". Faddausi ce ta farka jin kukan Fatima, "Mama asiya wallahi tayi sallah ita ta tayar dani ma". Mama asiya tace to uwar iyayi ni ai ba bugwan sallah nake mata ba, wannan yarinyar da kike gani mayyace ban taba sani ba sai jiya nima. A mafarki tazo min tana faman cinye ni, badan Allah yasa kurwata jaruma bace". Fiddausi dai jinta kawai take yi tana mata kallan muguwa azzaluma domin tasan duk maganganun Mama asiya ba gaskiya a ciki. Mama asiya ce ta dankwashi kan Fatima hade da cewa "Yi mana shiru munahika mayya kawai, ai yau sai kinci ubanki a gidan nan bara alhaji ya fita. Kuma yanzu ma ki biyo ni kitchen kina jina?". "Eh gani nan zuwa'. Buzu-buzu mama asiya ta juya ta fita bata jima ba Fatima ta bita baya, Fiddausi tabi bayan Fatima da kallo tace, "Kaico 'yar yarinyar da baki wuce a goya ba amma tun yanzu kin fara shiga kitchen, Allah dai ya kawo miki mafita". "Ameen". Fiddausi taji ance maganar ta fito daga saitin dan karamin gadan fatima ne, ganin ba kowa a gun tsoro ya kamata da sauri taja blanket ta rufe tayi luff!. Kamar kullum yau ma fatima tasha wuya a kitchen bayan irin Aikace-aikacen da tayi ga kuma Mama asiya daga anjima sai ta rankwashi kanta tace "Mayya kawai allah yasa dai karki cinye mana 'ya'ya dan wallahi yarona daya in ya kamu da koda ciwan kaine ke zan bincika".
Dake Mama asiya tabawa sauran kishiyoyin nata labari suma sai suka hau tsangwamar Fatima da dukanta hade da bata aiki mai wahala, Wai suma kashedi suke mata karta kama musu nasu yaran. Ita dai Fatima ba abunda take sai kuka sai in sunyi maganar karta kama musu yara tace "Toh" al halin ita bata ma san miye wata maita ba. Sanda fatima tasha wuya sosai ta kuma yi kuka ba adadi kafin a gama hada breakfast din. Bayan sun sako ta taje ta rungume 'yar tsanarta tana kuka. "baby na kiyi hakuri na barki ke kadai. Wadan can mugayen ne suka ta zalunta na". Yar baby ce ta kama kuka nan Fatima tasa ta a kafada tana jijiga ta tana bata hakuri. "Momy bayi inje in yama miki". Wata siririyar murya ce ta fito daga 'yar tsanar. Fatima bata ji tsoran komai ba. "A'a baby na kinga su manya ne ki kyale su. Allah zai saka mana, naji malamin islamiyar mu yace, duk wanda aka zalunta allah zai saka masa". Yar babyn ce tace "To na fasa zuwa". Yauwa yarinyata muje in miki brush da wanka tukun inzo in miki kwaliya mai kyau". Tana gama fadin haka ta warci 'Yar babyn da hannu daya ta je ban daki. (Wai aka ce 'Kuruci dangin hauka) bayan fatima ta ajiye ta tace. "Haaa, bakinki", nan take bakin 'yar robber ya bude. Hakora ne reras! A jere fatima dake yarinya ce ba ruwanta batayi tunanin wani abuba. Ta sa brush ta fara gurzar bakin. Tana farawa bakin ya fara jini. Fatima na ganin jini ta daka da gurzar bakin ta zuba ruwa ta wanke mata tukun tace, "Gaskiya mai shagon da muka sayo ki baya da mutun ci kuma kazami ne duba fa yanda ya bar miki hakori suka lalace baya miki brush". Aljanar ce tace "Ko sau daya bai taba min ba". Nan dai fatima taci gaba da mata wanka suna hira.
Kyauran ban dakin aka turo da karfi, Ameera ce ta shigo. "wai ke Fatima dan ubanki bana hanaki magana a bandaki ba?. Ko baki san ba kyau ba?". "Yi hakuri aunty wanka nakewa Baby na". "Kutumelesi kaji 'yar banzar yarinya wato barnar ruwa zaki tarkarwa mutane ko, To daga yau sai yau kar in kara ganin kinwa wannan 'yar tsanar wanka kuma ma kawo ta nan, yanzun nan zan kona shegiya kowa ma ya huta, Kawo ta nace magana fa nake miki". Fatima kuka ta kamayi tana boye 'Yar babyn a bayanta tana fadin "Dan allah aunty ki bar min abuna ina santa wallahi". Tsawa ameera ta daka mata wacce tasa saida ta firgita matsowa tayi kamar zata mika mata kuma sai ta sulale da gudu ta ruga waje ai kuwa amira ta bita suka hau tsere. Ameera ta kusan kamata kenan. Fatima tayi wata zilliya ta Bi ta karkashin ameerar ta wuce, sai ji kake ameera Tum! Ameera tasha kasa. (SHI YASA BA'A SO BABBA YABI YARO, BA KYAU DAN IN BA'A CI SA'A BA SAI KA FADI. AKWAI WANI UBA DA YABI DANSA DA GUDU. A LAYI CIKIN JAMA'A YARAN YA KADA SA. YARO DA KAZA DUK KUSAN DAYA NE. WAYO AKE MASA AYI CHARAF A KAMA. IN MA KABI DA GUDU TO KARKA YI GUDU MAI NISa.) Fatima Direct dakin abbanta taje tana kuka yana ganinta ya bar abunda yake ya kamo hannunta. "Mamana zo nan waya taba min ke tun da sanyin safiyar nan?
Cikin kuka Fatima tace "Dady wai aunty ameera ce zata toya min Babyna wai kuma tace kar in kara mata wanka, yanzu ma da gudu ta biyo ni". Ran alhaji ne ya bace. Ya kama hannun Fatima yace muje gunta. A falo suka isketa tana wash-wash.
Alhaji bai bi ta kan wash! Din da take ba ya bal-bale ta da fada hade da mata kashe karta kara shiga sabgar Fatima. Su Asmart ba rabuwar arziki sukayi da Mama sakina ba. Bayan tusar da suka ta banka mata da dare a daki kamar bodarai. Da asuba asmart ta tashi wai tea zata hada. Madarar da suka zuba su biyu ta wuce ka'ida domin saida shayin yayi kauri kamar wani koko. Sakina na ganin haka basu gama sha ba ma ta kora su gida. Da wuri suka je gidan lokacin ba'a kai ga cin abinci ba. Tare da su aka ci sunci Sa'a ba wanda ya gayawa alhaji basu kwana a gida ba. Bayan anci abinci an watse alhaji yayi musu salama ya tafi office. Nan fa mama asiya ta kira Fatima suka mata dan banzan duka ita da sauran matan wai kashe ne karta cinye musu yara Mama asiya kuma na cewa karta sake biyota mafarki. Waje suka korata can Fatima ta koma bayan dakuna ta zaunar da 'Yar tsanar ta facing dinta tana kuka. Yar babyn itama kukan ta fara. Abun ya bawa Fatima dariya itama kuma sai babyn tabar kuka ta fara dariya. Nan dai sukata wasanni.
Su Nasmat da asmart makaranta suka taho basu ma ko tsaya jiran su Fiddausi ba da sauran yara kamar da gaske suka yo sakko, alhalin kowa yasan ba karatun ba suke. A hanya Nasmat ke cewa asmart
"Ni fa wallahi yau mugunta nake ji, Dan haka yau kan mai Tsautsayi". Dariya Asmart tayi tace 'yar iskar karya kawai". Nasmat ta bata rai, "Ke ce dai 'yar iskar karya. Amma ni yau muguntar ce kawai a kai na". "Yauwa yanzu zamu kure mai cika baki". Inji asmart "Ga wani makaho can yana faman tsallaka rami jeki tunkuda shi in da gaske muguntar kike ji". Jakar kur'anin ta tabawa asmart Riko ta nufi dan tshon da aniyar tunkuda shi rami...............
Ni kuwa nace Allah yasa aljani ne 😄😃😃
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 25-26
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
_*IN DEDICATED TO 'YAN BOKO HARAM WA SOYAYYA TA.*_
*SHUGABAR TADA BOMB* 💣 FATIMA. (DAUGHTER)
*MAI BADA UMARNIN KAI HARIN* 💣 Hadiza hadi (Niger) 😡
*'YAR KUNAR BAK'IN WAKE* 👧🏿💣
Zuwaira (madara) 😡😔
_Kunci nasara kai harin da kukayi babban birni zuciya ta, inda kuka kashe mutum uku Biyu kuma na nan suna zubar da jini. Shi yasa ma gaba dayan yau banda sukuni. Kuma yaseen wuta Bal-Bal_ 😡
💦 QUEEN HAUSY💦
I love you too much.
You kill me with you love 😘
*KARSHEN PAGEN BAYA*
_Jakar kur'anin ta tabawa asmart Riko ta nufi dan tshon da aniyar tunkuda shi rami._
»»Irin tsofafin almajiran nan ne, yana yunkurin tsallaka wani rami ya kasa. Nasmat na zuwa kamar wacce zata taimaka mishi dan har magana sai da tayi mishi. Sai da ta duba ko ina taga ba mai kallan ta kawai ta ingiza shi cikin ramin, suka ruga a guje ita da asmart suna waigen sa suna mishi dariya. "Wannan wane irin yara ne da mugun hali haka, yanzu ina fama da kai na ki zo ki hankada ni rami salon in Karashe naka shewa ko, Jeki Allah ya isa. Allah zai hada ki da gaman ki kema". Basu ce mishi komai ba gaba suka kara suna ta jan fada har suka isa makaranta. Malamin na ganin su ya murtuke ya bata fuska, "Kai ku zo nan dan ubanku, yau sai kun gaya min ubanwa ya daure muku gindi, yanzu karfe Goma zaku shigo aji". Gaba dayan su gunguni sukayi, kamar ba su ya kira ba suka nufi bench suka zazauna. Kowa ta fiddo al'qura'ani kamar da gaske karatun zasuyi. "Kai wai ba da ku nake magana ba?". Nan ma basu tanka mishi ba. Abunda ya fusata malam Dalhat kenan, Ya nufo su da zureriyar dorina. Shaf! Shaf! Kake jin karar dorinar da karfi yake dukan su. Bayan yayi wa ko wacce daga cikin su dorina biyu, A ta ukun Nasmat ta Rike bulalar tare da mike wa tsaye. "Malam ya ishe ka haka". Asmart ta fada ido cike da kwalla.
Cikin kuka-kuka Nasmat tace, "Ki kyale sa yaci gaba Wallahi ya sake dukana sai na mishi abunda bai yi zato ba". Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar malam ya saki baki yana kallan su, a zuciya yace, 'Ashe rashin kunyar nan ta su da ake fada har ya kai haka, Ni kuwa zanyi maganin ku". Bulalar ya fizge da karfi ya fara zafga musu kan uwa da wa bi, da gudu suka fita har suna bankade muta ne. Ko laidar Al'quranin ba wanda ya dauko a cikin su. Ko wacce hawaye ne shabe-Shabe a fuskarta Asmart na cewa, "Wallahi bazan yarda ba dole sai na dauki mata ki, chabb! Lalai wannan malamin bai sani ba ne". Nasmat ta ciji labe. "Hmm kyale sa wasa yake damu". Cikin gari suka shiga yawo gida jen kawayen su, sai da suka Dai-Dai ci lokacin tashi a Islamiyya yayi tukun suka koma gida.
Shigar su gidan suka tarar gaba ki daya mutanan gidan sun fito ana faman shiga motoci, da sauri suka karasa suka tamabaya ina za'a je, Mama asiya tace, "'yan gantali har kun gama iskancin kun dawo ko?, nasan dai ba makaranta kuka je ba, kunga Wallahi ku kiyayi rayuwa gwara ku tsaya ku mayar da hankali kuyi karatu, Ni kai na yanzu haushi nake ji da bansan komai ba a karatun Alqur'ani kuma kuma nasan ko Fatiha cikin ku da kyar in da wacce zata iya kai wa dai-dai". Kallan juna sukayi hade da sosai kai Asmart tace, "Mama asiya ina zuwa?". "Au! Har kun manta yau bikin Haleematu?". Wani irin tsalle Asmart tayi "Ashe yau ne". Kokarin shiga mota ta farayi aka hanata, Akace sai taje ta canza kaya. Da gudu taje ta canzo Ko kwalliya batayi ba tazo ta shiga mota. Nasmat kuwa tana guri A tsaye ta wani bata Rai. "Ke bazaki je bane? Kowa na gidan zashi ko har yanzu 'yar banzar gabar nan ta rashin hankali kuna yinta ke da Haleema?". Zuwaira ce tayi wa Nasmat magana. "Allah ya sawa ke inje gurin bikin haleema, Ai ko mafarki nayi naje wajen sai na farka kuma in na farka sai nayi sadaka". Juwaira bata ce mata komai ba t shiga mota. Motoci biyu ne cike. Har sun fara tafiya. Asmart ta leko. "Yauwa nasmat ban gaya miki ba. Wannan tsinaniyar yarinyar tana can tana mana wasa da kayan Makeup wai tana wa 'yar tsanarta kwalliya. Kije kici ubanta dan Allah". Tun asmart bata karasa maganar ba Nasmat ta zungura da gudu ciki gidan.
Direct dakin su ta nufa, tana zuwa ta shako wuyan Fatima ta baya ta fara gallah mata mari. Fatima kuwa ta hau kuka da ihu!, "Wato ke dan ubanki 'yar baby kike wa kwalliya da kayan mu ko". Fatimar hakuri take bata amma taki ji sanda ta mata lilis! Kamar yanda ta fada yau 'yan muguntar ne a kanta. Kunnan Fatima ta kama tana ja. Ba arziki Fatima ta ringa binta tana rike kunnen dan karta ji mata ciwo. Sai da ta kai ta har kofar gida, mai gadi duk da yana tsoran alhaji sai da ya bude kofa domin yasan Bala'in Nasmat Da Asmart. "Dan ubanki bazaki zauna a gidan ba, kuma Wallahi in kika tafi wani waje na fito waje naga bakya nanto kema kin dan sauran". Nasmat ta juya zata shige gidan Fatima ta riko kafarta "Aunty dan Allah ki bani baby na to". Hararen ta tayi ta kuma sa kafa ta haure ta can Fatima ta fadi tana kuka. "Bara inje in yan-yanka babyn dan ubanta itama ke da ganinta sai a lahira in 'yar Tsana na zuwa". Wani kukan Fatima ta ci gaba da bada wa amma Nasmat bata saurare ta ba ta shige cikin gida ta bar Fatima nan tana kuka.
Mai gadin ganin yau gidan ba kowa kuma yana da 'yan uzuririka shima. Fitowa yayi har zai wuce kuma sai ya tuna Fatima na kofa karta shiga, Katan kwado ya koma ya daukko ya zo ya garkame gidan. Yayi tafiyarsa. Nasmat a fusace ta shiga ta daukko 'yar babyn ta nufi kitchen da ita. Wuka ta dauka mai shegen kaifi ta fara dada rawa a jikin Robar amma ko kayan dake jikin babyn sunki ko bancile. Canza wukar taje tayi a cewar ta ba kaifi ne. Fara da dara wukar ta ke da wuya aka fara knock din kofar kitchen din da karfi abun kamar za'a balla. Ta dan tsorata kuma sai ta jure. "Uban waye?". Shiru ba'ayi magana ba. Jin anyi shiru yasa taci gaba da abunda take yi. Ganin wuka taki ta kama babyn ta dauko galan din kalanzir ta ajiye babyn a kasa ta jike ta sharaf! Tukun ta dauko ashana. Zata kyasta kenan. Wani mugub karan buga kofa ya kara dakar mata kunne. Ba tsoran koma Nasmat ta daka ashar, hade da cewa"wane dan ku... Uba ne? Mai gadi nasan kai ne wallahi in na fito ni da kai ne". Bata rufe baki ba aka kara bubugawa wannan karan harda murya ta mai gadi sak! Da yace "Ki buuuudeeee". Abun ya fusata ta jin muryan mai gadi. Ashanar ta kyasta! Ta wula wa yar babyn nan take wuta ta kama ta fara ci. Tana ganin haka farin ciki ya kamata tayi mugunta. Saura kai mai gadi ta fada lokacin da ta nufi kofa rai! A bace domin har yanzu bugawa ake. Tana bude wa taga wayam, bayan kuma yanzu-yanzu ko seconds 4 ba'ayi ba da bugawa. Kofar dakin su tafi an rufo garam. Alamun wani ne ya shiga...............................
🤣🤣🤣 *Yau wata zata ci uban ta. Na tausaya mata.lolz*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 27-28
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
_*IN DEDICATED TO ALL ALJANAR FATIMA FAN'S. INA JINJINA MUKU NA YABA DA IRIN KAUNAR DA KUKE WA BOOK DIN. SANNAN INA BAKU HAKURI MASU KORAFIN PAGE YANA KADAN WALLAHI I'M BUSY. KUCI GABA DA HAKURI. IN DA JIRGIN SAMA YAJE HAWAINIYA MA TAJE IN DAI ZA'A LALA BATA. LOLZ*_
*KARSHEN PAGEN BAYA*
Tana bude wa taga wayam, bayan kuma yanzu-yanzu ko seconds 4 ba'ayi ba da bugawa. Kofar dakin su tafi an rufo garam. Alamun wani ne ya shiga..
»»Kofar dakin ta nufa cikin fushi tafe take da sauri rai a bace, tana zuwa kofar dakin tasa hannu zata bude kenan wani makeken kadangare irin mai jan kan nan ya fado mata a kai. Wani mugun ihu ta saka, ta fara tsalle-tsalle tana zagaye katan falon tana zazage-zazage da Kara duk ta dauka yana jikinta ashe ya fado tun tuni. Ta dade tana yi sai da ta tabbatar baya jikin nata tukun ta dan saki jikinta ta hau dube-dube. Bata hakura ba kofar ta sake tun kara da niyar ta bude wannan karan ma kadangare ne karami ya fado mata wannan karan cikin riga ya shigar mata. Nan ta fara ihu ta fadi kasa tana ta mirgine-mirgine. Kadan garen ya fita. Tashi tayi zaund tana Raraba idanu. A zuciya tace "to wai me ma ya kawo kadangaru falo?".Kuma Wallahi sai na shiga dakin". A fusace ta tashi sanda ta dai-dai ci kofar dakin tukun ta zura a guje. Ta bankade kyauran ta fada karfin gudun nata ya rinjaye ta ta fadi sauran kadan da ta yi karo da katanga.
Suman tsaye tayi a gurin. Dan ganin wani make ken maciji da ya fasa kai yana layi da kai. Nasmat ta san tana matsawa a gurin sai ya sare ta. Karkarwa ta fara yi sai hawaye sharr! Kuka wii! Wii cikin kukan da take tana ihu! "Wayyo mama na na mutu na lalace, dan Allah maciji kayi min rai kayi min aikin gafara, Wallah bazan kara Fashin sallah ba, kuma Wallahi bazan kara fashin zuwa makaran ta ba". Ihun take tana ta zuba Surutai! Da rantse-Rantse macijin ne ya dan kara bude kai nan take yana zaro harshe yana mayarwa. Kara tsurewa tayi da taga macijin yana kara matsowa a hankali. Tsoranta ne ya karu ta fara ihu! Tana karkarwa. Sululu macijin yaje ya fara hawa kafarta. Tana jin haka sai fitsari Sharr! Gaba daya ta jika wajen. Sannan tayi tsaye cik kamar gunki ta rufe ido. Har yanzu dai macijin hawa kanta yake. Jima kadan taji baya nan. Bude ido tayi can ta hange shi ya shige ban daki su. Da gudu tayi waje ta zo dai dai falo kenan wuta gaba daya ta dauke, dama nefa ce. Duk da rana ce amma bata iya ganin gabanta. Juye-juye ta fara yi tama rasa ina zata nufa. Ji tayi an shafe ta ta baya an wuce. Wani razana nan kara ta saki "Wayyo!" Cik kuma ta tsaya waje daya duk da bata gani amma tana jin motsi kamar mutum ya nufo inda take. Abunda ya taho din tana jin karar tafiyan saura kadan ya kara so gurin ta sai aka dawo da wuta. Wani gwabran nun fashi ta sauke nan ta du duba amma ba komai a gun. Kan armchair ta zauna tana nunfashin wuya. "Wash! ni Nasmat yau naga bala'i wannan katan maciji idan ya sare ni ai in ana Wuce lahira ma sai na wuce".
Sukur-sukurtu taji a baya da sauri ta juya Taga ba komai, hahhahahh! Dariya tayi da kanta tukun tace, "Lalai yau na tsorata". Yar baby ta tuno da sauri ta tashi ta nufi kitchen domin gano ko ta idasa kone wa?. Tana bude kyauran Kitchen din tayi tsaye hade da Zurawa guri daya ido, mamaki ne karar ya bayyana a fuskarta. Ganin yar babyn gata nan a kwance inda ta yarda ta amma ko alamar an jika ta da kalanzir babu balle ma Wuta. "Kai!, ban gane ba nafa kona wannan abun kafin in fita. To ko bata jin wuta na?. To amma bari inga a gaba na zan kona ki yar iska". Galan din gas ta dauko a wannan karon ta bul-bulawa yar babyn ta kyasta asha na ta wulla mata. Nan take wuta ta kama bal-bal farin ciki ne ya lulube ta domin yau mugunta ce fal! A ranta. "Kyal-kyal-kyal-kyal, hahahahahahaha, hihihihijijhehehehehrhr". Sautin wata iriyar mahaukaciyar dariya ce da ke fitowa daga falo ya daki dodan kunnan Nasmat da ke tsaye itama tana kallan yar babyn tana dariyar mugunta. Kofar ta bude a hankali ta Leka, fatima ta hanga zaune kan kujera ita ce mai uwar dariyar nan. Nasmat na ganin ita ce sai ta bata rai ta Idasa fitowa..
Ishar ta maka. "Fatima ku....banki". Shiru Fatima tayi ba tare da ta wai-wayo ba, Cikin sauri Nasmat ta karasa gurin tana zuwa kuwa ta Falle Fatima da mari ta baya. Gugur-gugur kai ya fadi kasa ya fara taya jini na fita a jiki. Gangar jikin ma Kasa ta fadi jini ya fara malala. Hannuwa biyu Nasmat ta dora a kai ta maka wani uban kara, Ta nufi gurin gangar jikin fatima ta rugume ta a kirji "Wayyo Allah na na shiga uku na lala ce, Fatima Wallahi ba kashe ki nayi niyar yi ba. Dan Allah ki tashi yanzu in su momy suka zo me zan gaya musu, Yau na shiga uku". Kuka take sosai ba kukan rashin Fatima sai kukan rashin abunda zata ce. "Ai da raina ban mutu ba Sake ni". Gangar jikin Fatima ce ke magana. Shiru Nasmat tayi ta tsurawa Wuyan da har yanzu jini ke zuba ido. Domin taji kamar daga nan taji magana sai dai bata tabbatar ba. "Ni ki sake ni nace". Wata murya ce a shagwabe ta fadi hakan. Kafin a karasa maganar tuni Nasmat tayi wulli da gangar jikin Fatima din tayi hanyar kitchen a guje kamar wacce zata tashi sama. Gangar jikin tsaye ya tashi ya je ya daukko kan ya riko a hannuwa biyu A hakan Fatima ta nufo Nasmat da ke can bakin kofar kitchn tana kokarin bude wa amma kofar ta ki bude wa. Fatimar tana fadin "Aunty nasmat mayar min da kai na- mayar min da kai na". Kuka ne ya subuce wa Nasmat tana tura kufa tana waigen baya tana fadin "Wayyo Allah momy na". Gangar jikin Fatima ya kusan karasowa kenan kofa ta bude. Har Nasmat ta zura kafa zata fada kuma sai taja birki. Yar babyn ta gani ta nufo ta tana kuka ga wuta na cin jikinta kuma hawayen jini ne ke fita a idanun ta. "INNAHU MIN DAUDA WA, INNAHU MIN SULAIMANA, WA BAZAN KARABA NA TUBU KU YAFE NI".Da karfi Nasmat din ke fadar haka tana karkarwa. Da dai taga wannan ba mafita bac...........................
AYI MIN AFUWA BUSY YASEEN
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 29-30
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
PAGEN YAYI MIN DADI SHIYASA NA BAWA BEST FRIENDS NAWA.
Usaini atk 80k
Shamsuu Bin Yerhyer
Mustpha Rogo
Abdul King Article
Musa Umar Abdullahi
Shatu muhammed
Aisha adam
Ahmed tijjaniyu
*HAKIKA KU MASOYA NA NE NA GASKIYA, KUNA A SAHUN GABA CIKIN MASOYA NA. INA GODIYA DA BIBIYAR LITTAFAI NA DA KUKE ALLAH YA BARMI YARE.*
Nasmat a guje ta bar wajen nan suka hau zagaye falo. Gangar jikin fatima dauke da kanta a hannu jini na zuba tana bin nasmat di tana fadin "Auntu dan Allah ki tsaya ki samin kaina". Fadi take tana maimatawa tana biye da nasmat din. Haka itama bangaren yar babyn bin Nasmat take tana fadi "Aunty kashe min wuta wayyo! Wuta na cina". Gaba daya sun zagaye falon sun mishi kaca-kaca da jinin da ke zuba. Nasmat abun ya zame mata biyu ga tsoro ga karfin maganar tasu har cikin kwalwarta, Ta dai fahimci wannan so suke su Haukata ta. Allah ne ya bata sa'a ta ta nufi kofar fita a falo tana kamawa kofar ta bude da sauri ta rufe kofar ta jingina da kofar tana shasheka. Hamdala ta farayi a nufin ta ta rabu da su. "Aunty ki kashe min wutar". Wani uban kara ta daka "waaaaaayyooooo Allah na" ta runtuma a guje tana kiran me gadi. 'Yar babyn ta bita baya Nasmat dakin mai gadi ta leka shiru ba kowa. Nan taje ta fara kokarin Bude kofa taji a garkame da kwado. Juyowa tayi ta zube a kan gwiwoyin ta tana bawa aljanar hakuri.
"Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, daga yau bazan sake takurawa Fatima Allah wallahi tallahi na rantsi da uwata da ubana ku....." "Kheeeeeeeee! Yi min shiru, muguwa kawai azzalumam". Cikin wata iriyar murya mai karsashi da ban tsoro Aljanar ke magana. "Daga yau sai yau idan har na sake ji ko gani kin wa Fatima ko harara, ki san da sani dan Wallahi sai na taba lafiyar jikin ki, kina jina?". Da sauri "Eh naji *ALJANAR FATIMA* daga yau Wallahi na dai na". Wata dariya 'yar tsanar tayi mai ban tsoro wanda kasa kanta girgiza take kamar jirgin dan kara zai tashi. "Oya to dauke ni kije ki min wanka da kwalliya". Zaro ido Nasmat tayi ta kara make wa a jikin gate din dan tsoro. "Keeee! Ba dake nake ba". Jiki na karkarwa Nasmat ta taso kamar bata san tafiya hannun na karkarwa ta dauki 'yar tsanar ta wani mimike hannu kamar wacce ya dauki abun kyama. "Au! Kyamata ma kike oya Rungume ni". Nasmat kamar ta fashe da kuka a mugun tsora ce take. A haka taje tayi wa yar babyn wanka a tsorace Sai da 'yar babyn ta bata wuya sosai a wajen wankan. Domin sai nasmat na mata wanka ta zuro hannu ta kama hancin ta ja da karfi, ko kunne. Nasmat sai dai yi kara kawai. Bayan gama wankan aljanar tasa Nasmat ta zo tayi mata kwalliya ta dauko akwatin ta tasaka mata kaya masu kyau.
"Yanzu abunda nake so shine ki dauke ni ki kaiwa Fatima kice mata dama wanka ne zaki mini, karki yarda kice mata nayi miki wani abun kina jina". Da sauri ta amsa "Eh zanyi hakan aunty aljana". Nasmat ta fada murya na karkarwa. 'Yar tsanar tasa dan guntun hannunta ta wanke Nasmat da mari. Da sauri Nasmat ta dafe kunnu domin zafin marin. Kuka ta fara wii!-wii! Harda hawaye. Tsawa aljanar ta daka mata. " Rufe min baki, Ki kira ni da *SAFURATU* KO *ALJANAR FATIMA* In kuwa ba haka ba zaki san da sani". Gum Nasmat ta kame baki duk da kukan yaci karfin ta sai dai ba yanda zata yi aljana ta saka ta gaba. Hawaye ne kawai ke zuba a idanunta. "Muguwa ashe mugunta ba dadi kuke cutar marainiyar Allah kaf! Gidan nan banda alhaji da fiddausi ba wanda zan saurara wa sai na dauki mumunar mata ki a kanku. Sannan yanzu abunda nake so shine. Bayan kin kaiwa Fatima ni ku wuce gidan baki da ita kina jina"?. "Eh", farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Nasmat domin kuwa abunda take so kenan Taji maganar mugunta. Aljanar tace sai taci uban kowa a gidan. Daukar 'yar babyn Nasmat tayi ta fita da ita anyi sa'a kuwa lokacin mai gadi ya dawo, Wata muguwar harara ta galla mishi lokacin da ta zo giftawa. A zuciya tace "Mugun mai gadi ko hada kai ma aka hada baki, Wai dan kuu... Uba sai yanzu zai dawo bayan na shiga tarkon Aljanah".
Kwance suka Tarar da Fatima a kofar gida sai sharara barci take ta gaji da kuka. Nasmat rike da 'yar tsana a hannnu wacce duk sanda ta kalle ta bata marmarin karawa don irin hararen da take aiko mata. A hankula ta tayar da Fatima ko ita Fatima tayi mamaki abunda bata taba gani a gun aunty nata ba kenan. Ko Nasmat taga mamaki a fuskar Fatima a zuciya yace "Yarinya wuya ce mai saka kafuri sallahr dole". Kallan Fatima tayi Cikin fara'a "Fatima Ga 'Yar babyn ki dama fa wanka ne zanyi mata. Yanzu tashi zakiyi mu tafi gidan biki". Fatima cike da Zumudi ta karba "Na gode aunty na tayi kyau sosai. Amma mama asiya tace baza'a je dani ba". Murmushi Nasmat tayi, "Karki damu baza ta ce komai ba ai dani za'a je". A zuciya kuwa tace "Yarinya ai ko Mama Asiya taga bala'in da na gani dole ta tsure ta amshi duk wani umarni ko da ta san bazai yuyu ba". Fatima tace to "muje muyi wanka ko Ko aunty?". Nasmat kallan Aljanar tayi irin kallan da babyn ta watso mata ya nuna mata alamun bata yarda da wannan ba. "A'a 'yar kanwata ai sai mu makara tashi muje nima ko uniform bazan cire ba". A hakan kuwa Nasmat ta tsayar musu da napep suka hau. Har yanzu jikin Nasmat bai daina Rawa Ba. Allah-Allah take su sauka ta bace musu a gidan biki ta rabu da bala'i. Ba'a jima ba suka isa kofar gidan. Nasmat ta shiga gida kenan domin ta karbo wa mai Napepk kudin sa ta bar fatima nan rugume da babyn ta.
Wasu 'yan mata ne suka zo wuce wa, Idan daya ya kyalla kan yar babyn Fatima hakan yasa tace wa abokiyar tafiya. "Laaaa! Kawata dubi wata 'yar tsan mai kyau muje mu ganata". Suna karasa wa gurin hadiza ta warci yar babyn ta maka ta da kasa tasa kafa ta taka. "Haba kawata wannan gunkin abunda Allah ya tsine wa mala'iku Ma basa zuwa gidan da ke d..,.". Tasss! Tasss, Taji saukar tagwayen marika a kumatun...........................
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 31-32
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
😘 *WANNAN PAGE IN SADAUKAR WA NE GA LITTAFIN👇🏽
🙆🏻♂ *'YAR AIKIN GIDA NA* 🙆🏻♂
*SHAZEE* Allah ya karo basira Aljanar Fatima taji dadin kyautunan pages da kike bata hakan ma yasa ta tasa ni gaba a kan sai na baki wannan. 🙊 Yauwa kuma ina so muyi sirri a bani number hafsat zan aike ta wajen BOKA MAI KWARAN GWAL! 😜 .lolz
👏🏼 *BADA HAKURI* 👏🏼
Masoyan littafin nan ina baku hakuri bisa rashin jina da kuka yi jiya. Naga sakonin ku da masu kira na. Na gode 😍 I luv yhuu All my fans.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Haba kawata wannan gunkin abunda Allah ya tsine wa mala'iku Ma basa zuwa gidan da ke d..,.". Tasss! Tasss, Taji saukar tagwayen marika a kumatun.~
»»Dafe kumatu tayi, "Kai! Kai! Kai! Kut...uba yau za'ayi bala'i a wajen nan wato dan na yarda wannan tsinanar 'yar tsanar shine zaki mare ni ai kuwa bazan taba yarda ba". Kafin kawar tata tayi magana tuni hadizar ta wanka mata mari. Nan fa sukayi hau kunce. Fada ya kace ba. Duk abunda yake faruwa a kan idan Nasmat Ita kuwa tasan abunda ya hada fadan hakan yasa ta kyalkyalewa da dariya harda rike ciki. 'Yar tsanar ce ta mata wata iriyar harara wacce tasa bata shirya ba ta dakata da dariyar. A hankali taje taba wa mai adai-daita kudinsa tace wa Fatima "kinga dauko 'yar babyn ki mu shiga ciki". Da sauri Fatima ta share hawayen da suka fara zubo mata. Ta dauko 'yar Nasmat ta kama hannunta suka shiga ciki. Safuratu ganin sunki rabuwa da fadan ne. Ta zo ta fara kan uwa da wabi. Mari sai dai kaji kara tass! Tass an rasa daga ina yake fitowa. Ba arziki suka rabu da gudu suka bar wajen domin sun maru ba laifi. Da shigar su Nasmat falon. falon suka iske mata ne damkam a ciki su mama asiya suka fara wurgo mata harara,
Umma ce ta taso wacce itace mahaifiyar Haleema da ake wa auren kuma yayar Mama asiya ce. Yanayin jikin su da na asiya duk daya itama yar lukuta ce. "Nasmat ke wacce irin doluwa ce?, Da zaki taho mana da wannan marar jin yarinyar. Ko zaki zo ai bai kamata ki zo mana da wannan ba, Ke kinsan cewa jina na ko kadan bai hadu da wannan kazamar yarinyar ba". Umma ce ke fadar haka. "Umma ni gani nayi an barp ta a gida ita kadai shi yasa ma nace ta taho mu tafi. Mama asiya ce ta taso tubur! Tubur! "Kanwar uwarki ce ita din da zaki ji ba dadi dan an baro ta a gida. Dallah fidda muna ita waje kuna ji daga shigowar ta har ta dumame falon da wari". Umma tace "Zo nan kawo 'yar babyn nan dan ubanki daga yau ta zama ta khaleel". Warce diyar tayi ta mikawa wani marar jin yaron ta dan lukuti. Fatima kuwa ta fashe da kuka ba komai yasa ta kuka ba sai kwace mata 'yar baby da akayi. Wani mugun dadi ne ya ziyarci zuciyar Nasmat ganin abunda su Umma suka aika ta, domin yau cikin mugunta take. Waje Fatima ta koma ta sama wani waje ta zauna ta saka kanta tsaka nin kafafunta tana kuka a hankali. Nasmat kuwa tasan amare suna sama kuma tasan Asmart ma na can amma ta tsaya kawai so take ta ga abunda zai faru. Khaleel ana bashi 'yar tsanar waje yayi da gudu. Wajen wasu marar jin abokan nashi yaje. Suna ganin ta kuwa wani daga cikin su ya rugo da gudu ya dau ki wuka wai yanka ta zasuyi. Sai da aka kwantar kamar dan akuya wukar kawai zasu dora nan take ta fara girma kafin su ankara tuni ta koma make kiya abun tsoro. Rugawa sukayi da gudu khaleel ne rike da wuka sai ya daga kai yake kallanta shi yaki rugawa. "Yanka ni mana khaleel". Abunda take fada tana mai-mai tawa kenan nan take tsoro ya ziyarci khaleel din karkarwa ya fara bai ankara ba yaji saukan bulala.
Gudu yake yana kuka hade da soshe-soshe yana kiran uwarsa. Daga ganin sa kaga wanda ake bi ina zane wa sai dai in ka duba baya babu wani wanda yake biye da shi domin aljanar a bace take. A million ya shigo gidan Nasmat na jin kukan sa a tsorace ta ruga a guje bayan mama Asiya ta wani makal-kale ta. Khaleel ne ya shigo yana kuka Da sauri Umma ta tashi ta tarye shi "Auta na lafiya, auta lafiya". Bayan ta ya boye yana nuna hanyar waje matan da ke falon duk suka dubi gurin ba komai. Da sauri ta juya tana jijiga da gani kasa bala'i ya tashi. "Waya taba min kai auta fada min ko uban waye wallahi sai naje naci mutun cin sa, fada min waye". Cikin kuka yace "Yar babyn Fatima ce". "Kai bana san shirme fada min waya dake ka". Amsar da ya kara basu kenan *"ALJANAR FATIMA* Ce". "Ok kwace ma tayi kenan bari inzo". Buzu-buzu ta fita a waje ta sama Fatima rike da 'yar babyn mari ta wanka mata, "Ke dan ubanki in bawa yaro na abun yayi wasa shine zak kwace, kawo ta dan uban ki" warce wa tayi ta koma ciki Fatima kuwa kuka ta kama yi domin ita dai a iya saninta taga Khaleel ya wuce yana kuka bai dade ba kuma taga ya fito ya kawo mata yar babyn ta da kanshi.
Umma na shiga da 'yar tsanar Nasmat tayi wani mugun tsalle a firgice ta fada bayan kujera A tsorace tayi muky! Tana saurare su. Khaleel na ganin Umma ta shigo da yar babyn ya kara fashewa da kuka ya ruga a guje ya makal-kale Mama asiya kamar zai shige jikinta. "Bana so! Bana so! Karku kawo ta". Abunda khaleel din ke fada kenan ganin uwar tasa bata daina nufo shi da yar tsanar ba ya sa ya tashi ya zuba a guje sama.
Rike baki Umma tayi "Ah! Ashe tsoranta ma yake har na wani bashi. Komawa tayi daga bakin falo ta wurgawa Fatima 'yar tsanar "Dauki tsiyar ki gata nan tsoranta ma yake yi". Fatima cike da farin ciki ta bar kuka ta dauki abunta ta rungume. Masu dafa abinci ne suke ta zuzubawa sun karasa kowa sai dai ya zo ya dauki nasa da na 'ya'yansa Fatima najin yunwa tsoro take taje ta dauka ga abincin a Take away amma tana tsoro a mata fada. Yunwa ta kai mata karo koma taga har yara na zuwa dauka ba'a hana su hakan yasa itama ta tashi dugwi-dugiw ta nufi wajen da aka jera take away din. Tasa hannun zata dauka kenan, taji an daka mata tsawa sai da ta zabura firgi-git "Keeee! Dan ubanki waya baki izinin ki zo nan balle ma har ki dauki abinci?". "Dama-dama yunwa nake ji mama asiya". "Kinci ubanki maza wuce idan anyin sauran abincin shi za'a baki". Magana tayi wa masu dafa abincin tace kar wacce ta yarda ta bawa fatima abincin in kuwa wata ta bata sai ta hadu da fishinta. Tana gama fadar haka ta dauki abincin guda uku ta nufi falo. Gaba daya hudun ta saka gaba da niyar ci. Lomar farko ta na kai wa baki ta zubdo da sauri. Nan take kowa da ya kai abincin baki sai ya zubdo saboda masifafan gishiri da ke cikin abincin duk wanda ya kai baki sai yaji kamar dai gishirin ne yayi loma da shi. Ran jama'a ya baci hakan yasa sukayi tururuwa suka wa masu aikin abincin caaa! Kamar zasu cinye su dan masifa. Mama asiya ce ta juyo ta kalli Fatima mugunta ce ta motso hakan yasa ta dauki abincin daya tana murmushi "Fatima to ga abincin ci ko". Da sauri Fatima ta karba domin masifar yunwa take ji. Loma ta fara kaiwa hannu baka hannu kwarya. Gaba dayan matan gidan kallanta suke suna dariyar mugunta, Ita dai fatima kallansu take ta rasa me yake basu dariya domin kuwa ita lafiya lau take jin abincin da dadinsa. Wata tsohuwa ce ta shigo gidan bara sanye take da bakar hijab doguwa har kasa, fuskarta duk a tatabe.
Bara tayi da farko suka ce hakuri kamar hadin baki. Ta kara nan ma suka bata hakuri. Kamar bata ji ba a karo na uku ta sake yi musu bara. "Masu gida a taimaka min da abinci ko kanzo ne ko saura in sama abunda zan zuba a ciki na rabo na da abinci tun jiya". Sauran muta nan ne suka fara balbale ta da masifa Umma tana murmushin mugunta ta dauko abincin har guda biyu ta sa tsohuwar ta zauna. Ta bata abincin suka koma gefe dan suyi dariyar mugunta. Lomar farko tsohuwar ta zubdo tana kakarin amai.Dariya suka hau kyakyatawa kamar me. "Haba bayin Allah ya zaku bani abincin da zai kashe ni wannan abinci ko gishiri". Asiya ta taso cike da masifa kamar zata hade tsohuwar. "Kinga tsohuwa bama san ciki da rashin mutunci da rai nin wayo, Dan kutu....uba ba sao da aka baki hakuri har sau biyu ba kika ki hakura kuma yanzu an baki shine zaki wa mutane tsiya". Cike da Tsokala da tsiya mama asiya ta juya "Jama'a ku karo mata Takeaways uku ta kara ta kai wa jikokinta". Gaba dayan gidan dariya suka hau yi mama asiya harda dukawa tana Rike ciki. Dagowar da zatayi taji saukar mari ya bada sauti. Tasssss! abunda ya dakatar da dariyar jama'a kenan. Hannu Daya mama asiya tasa ta dafe kumatu, ba abunda ya bata mamaki da tsoro sai ganin ba komai a gurin tsohuwar ta bace.Saukar Bulala taji a bayanta...................
....
Yau wasu sun dauko ruwan dafa kansu.
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 33-34
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
😘 *WANNAN PAGE IN SADAUKAR WA NE GA MOMCY DIN MU. MUNA SANKI MUNA KAUNAR KI. MUNJI SAKON KI A BAKIN 'YAR UWAR MU,
QUEEN MEARYAM ('YAR MAMARMU)*
We love you too♥
BY ALL ZAMANI WRITERS.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Hannu Daya mama asiya tasa ta dafe kumatu, ba abunda ya bata mamaki da tsoro sai ganin ba komai a gurin tsohuwar ta bace.Saukar Bulala taji a bayanta...~
»»Da sauri ta fara so sa baya tana ra raba ido.wata bulalar aka zubga mata wacce tafi ta dazun ma zafi abunda yasa ta rugawa tubur-tubar cikin jama'a tana ihu! Kenan duk. Aljanar binta take tana zane wa tuku ta koma kan uwa da wabi, domin kowa duka take ai kuwa gida ya hargitsa mutum.na tsaye ko yana gudu sai dai yaji saukar bulala. Haka suka fara rantar ta kare suna yin kofa, Nasmat na jin gida ya hargitse ta kwashe da dariyar mugunta domin tasan (A rina, wai an saci zanin mahaukaciya) Wata mata ce aka biyu da gudu ta shigo dakin, karan bugo na tashi amma ba ka ganin mai dukan. Nasmat na ganin haka tayi wani juyin da bata shirya ba. Da gudu ta nufi saman bene (upstairs) ai kuwa matar ta biyo ta tana ihun neman ce to. Nasmat na ganin haka ta kara wuta. Tana karkarwa ta fada dakin da amaren suke ta turo kofa, Tayin saurin Saka kuba. Ta jingina baya tana haki. Gaba dayan 'yan matan ne suka hayaya ko mata kamar zasu cinye ta danya. "Ke wace iriyar ce da zaki shigo wa muta ne ko sallama babu kin tsorata muta ne". Wasu 'yan mata uku ne suka fadi hakan cikin daga murya. "Kuyi shiru Aljanu ne aljanu". Haleema ce ta taso cike da masifa. "Kutumelesi Lalai yau zakiyi bayani wato ke dan rashin kunya har kika iya tako kafarki zuwa wajen biki na oya to wallahi kama hanya in ba so kike yanzu mu kwashi 'yan kallo da ke ba.
Bar ganin ina amarya wallahi sauke gwa-gwaran nan zanyi inci ubanki". Duk da Nasmat taji haushin zancen Amma sai ta basar domin jin Matar nan ta zo bakin kofa sai bubugawa take tana fadin "dan Allah ku ce ce ni ki bude zata kashe ni". Karkar wa Nasmat ta fara yi tsoranta ya karu abun ya zame mata biyu ga masifar haleema ga kuma wacce aljana ta biyu. "Sister Haleema dan Allah kiyi hakuri zan fita, Wallahi nima ba da gangan na shigo ba aljanu ne a gidan yanzu ma aljanace ta biyu mu ni da wata kinji ta nan tana bubugawa". Wani dogwan tsaki amaryar taja tare da kama hannun Nasmat tana kokarin bude kofa ta tura ta. "Aljanu ko to wallahi sai dai su kashe ki amma sai kin fita. Ke sunci kut.....ubansu ma aljanu". Kafin ta rufe baki taji saukar wani lafiyayen mari wani har sai da taga taurari. Juyo wa tayi, "Kai kai kai kika mare ni Nasmat. to wallahi yau banga mai raba ni dake ba a gidan nan". Nasamt kafin ta bude baki ta ce l ba ita ta mare ta ba.
tuni Haleema tayi kukan kura ta kai mata chakuma (kamar zakaru na fada) suka fara bige-bige da naushe-naushen juna su kuwa 'yan matan amaryar sun kai su shabiyar a dakin harda Asnart a ciki amma ba wace tayi yunkurin rabawa. Haka dai suka ci gaba. Saukar bulalin da suka fara ji kamar daga sama yasa suka dan saki juna ko wacce idan ta cike da kwalla. Jin an dakata da dukan nasu kamar hadin baki suka kara cakumar juna. Wani Razana nan kara ne ta cika dakin wanda suka rasa daga ina ya fito. "Kaaaaaa!". Nan fa suka saki juna suka durkushe ko wacce ta rufe kunnuwan ta domin karar yayi yawa. Haka 'yan matan amarya ma gaba dayan su kowa ya rufe kunne suna raraba ido. "Kuuuuu taaaashiiii tsayeee". Wata murya ce wacce in kaji ta kai kanka sai ka firgice gata da karfi ga tsoratar wa. Haleema da Nasmat tsatsaye suka mike ko wacce karkarwa take kamar su ruga su bar dakin. Haka yan matan amarya wasu suka shige cikin (wardrobe) wasu suka haye kan gado suka rufe da blanket kowa dai da wajen da yake nufa neman mafaka. Asmart kuwa kofa ta nufa da gudu nufin ta ta bude ta gudu. Tsawa aka daka mata. "Keeee inaaaa zakijeee". A wajen ta fadi ta fara zubda hawaye "Ba ko ina".
Ta fada murya na karkarwa cike da tsoro. Tana waige-waige saman Silin ta kalla da taga kamar wani baki baki ta wutsiyar ido. Ihuu! Ta kurma hade da Runtse idanu tasa hannaye ta rufe kanta. Kan mace ne a yanke gashi buzu-buzu fuskarta babu kyan gani abun tsoro. Kan reto yake a sama shine ke maganar. Su Nasmat koda suka daga kai suka kalle ta sai tsoran su ta karu ba wacce ta sake yunkurin Motsi da kanta balle ta kalli sama. "Watooo kuuuu waiii gabaaaa kuuuuukeee yiiii tsakaaaa niiiin kuuu koo?". Cikin sauri suka hada baki gurin cewa. "A'ah". Cikin tsawq "Ku rufe min baki marar kirkin banza da akayi kuna 'yan uwan juna kuma ku musulmain ne amma kuke gaba da junan ku. Ku rungumi juna daga yau kar in sake ji. Ko bayan auren haleema ne". Cikin sauri suka Rungumi juna suna karkarwa. Hahahhahhhah! dariya ce mai firgitar wa ta kaura de dakin. "Sauran kuma in sake samun labarin kuna gaba. Sannan Kar wacce ta yarda ta fita daga dakin nan a cikin ku in dai ba lokacin kai amarya ne yayi ba kuna jina?". Wannan karan har 'yan cikin Durowa (wardrobe) sai da suka amsa da karfi "To". Bat! aljanar ta bace.
Tsakar gida gaba daya ya hautsine tun daga farkon layin zaka iya juyo masu ihu nayi masu kuka nayi haka ma masu karatu addu'o'i nayi. Kofar ta kulle har yanzu kuma zanar su ake ba'a dai na ba. Fatima kanta ta tsorata da gudu ta tashi rike da yar babyn ta nufi wani keji ta shige ta boye dan gudun kar a banke ta. Kafin kace me Mata wajen biyar ne suka shiga keji dan ce tan kansu. fatima kam matse ta akayi gam. Macen da ke bakin kofar Kunama ta gallawa cizo ihu ta kwada ta fita a guje tana Soshe-soshe. Gida gaba daya ya hargitse kowa ta kansa yake yi. Abincin ma tuni an zubda shi an tatake. Ga kofa ta kulle taki buduwa. 'Yar tsohuwar nan ce ta bayana a sama kamar tsutsuwa fuska a murtuke. Wata tsawa ta daka wanda tasa gaba ki dayan gidan ya kara hargitse wa. Ba abunda ya kara haddasa cin kosan gidan sai falo da shima yaki buduwa.
Mata kam wasu ban daki suka shige harda masu shiga cikin tukunya dan tsoran bulalar. "Kowa ya tsaya kar ya matsa a inda yake". Aljanar ce tayi magana cikin daga murya abunda ya tsayar da guje-guje da ake faman yi kenan. "Wato ku marar imani ga abinci a gaban ku ba na uwarki ba bana ubanki ba almajira tayi bara harda masu daga sauti gurin bada hakuri. Ke kuma Waccen 'yar lukutar matar (Ta nuna Mama asiya da yatsa) kece muguwa har da bani abinci mai gishi ri nayi magana kika ta so baki ga girma na ba a haka kamar zaki bige ni ko?". Mama asiya jikinta ne ya hau bari murya na rawa "A'a dan Allah kiyi hakuri bansan ke aljana bace, wallahi dama taimaka miki ne zanyi dan na.....". "Rufe min baki, (Aljanar ta daka mata tsawa) Makaryaciyar banza, Ku kuma abunda yasa nayi muku wannan hukuncin dan ku kiyaye gaba ne. Ni Aljana ce ba mutum ba. Da mutum ce da kun wulakanta banza kenan. Wai ace a cikin ku kuna ganin wannan matar zata ci min mutunci ba mai bada hakuri ko dakatar da ita sai ma dariya. Kunci sa'a ni musulmar aljanah ce ba muguwa ba amma da yau sai nayi muku tatas a gidan nan duk da sai na farfasa muku jiki".
Shiru sukayi babu mai ko motsawin kirki kowa a tsora ce yake. "To abunda nake so da ku yanzu shine Ga mai gidan nan da 'yan anguwa a kofar gida sunzo jin me ke faruwa, kar wacce ta yarda ta bude baki ta fadi abunda ya faru, Duk wanda aka tambaya yace ba komai. Sannan baku ba fita daga gidan nan sai bayan an kai amarya. Duk wacce tayi yunkurin fita kuwa zata hadu da fishina". Tana gama fadar haka ta bace bat! Kofar gidan kuwa da su Alhaji ke faman ballawa ta bude wayam. Shigowa sukayi suka ga gidan yayi kaca-kaca nan suka hau tambaya me ya faru kowa sai dai yayi shiru da bakin sa. Masu dan kokari da rashin tsoro ne ma suke cewa babu komai. Nan dai su Alhaji suka gaji da tambaya sukayi fushi suka bar gidan suka koma harkokin su na shirye-shirye daurin aure.
Tsakar gidan tsitt! Kake ji babu mai wani kuzari duk sun jigata marar dauriya ma daga cikin su kuka suke wasu kuma na Soshe-soshen inda suka sha bulala. Wata Yar siririyar mata ce ta mike tana fada. "Wallahi ni sai na fita na tafi gida. Sai dai in kashe ni zata yi ta kashe kawai dan zalunci daga zuwa wajen biki a tsare mu kamar wani gidan maza". Jakar ta ta dauka tasa takalmi ta nufi kofa buzun-buzun da niyar wuce wa. Har ta kusan kai wa kofar gida, taji an kama kafarta ta baya an wani warto....................................
*TASHIN HANKALI*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 35-36
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
DEDICATED TO YOU:
☺ *SISTER NA HAFSAT IBRAHIM* ☺
NAGA DOGON COMMENT, NAJI DADIN ADDU'O'IN KI DA FATAN ALKHARIN DA KIKA MIN. NA GODE KUMA KEMA ALLAH YA BAKI DUK ABUNDA KIKA ROKAR MIN. (Ana tare)
😘 _All my fans thanks 4 You love and supported. Allah ya bar zumuncin. Ina ji da ku sosai da bazar ku nake rawa._😘
🤣😂 _*WATO YAU INA TYPING INA DARIYA BAN TABA DARIYA GURIN TYPING KAMAR NA YAU BA. UHMMM BA SAI NACE KOMAI BA KU KARANTA TUKUN. NAJI DAGA GARE KU MY FRIENDS I LUV U OLL*_ 🤣😂
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
----
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Jakar ta ta dauka tasa takalmi ta nufi kofa buzun-buzun da niyar wuce wa. Har ta kusan kai wa kofar gida, taji an kama kafarta ta baya an wani warto.~
```»» Kafarta ta fadi Janta akayi kiiii! Tana ihu hade da wuntsile-wuntsile, Zaka ga ana janta amma idanunka baza su gano maka mahalukin da ke jan kafar tata ba. Sai da aka kai ta can gaban mutane sannan aka barta, Zaune ta tashi tana kuka tana wage-wage, jama'ar wajen wanda basa da jumurin dariya har sun fara gagaba ta. Suka ji wata tsawa wacce tasa kowa yayi tsi!. Gidan shiru kake ji ko fitsari ba wanda ya yarda ya tashi yara da manya, haka suma can saman beni suna cikin daki sunyi tsi! Sunyi zugum suka ji ana Kwankasa kofar daki. Wasun su tuni sun kankame juna kowa na ihu yana kiran momynsa. Shiru ba wanda ya sama damar bude kofa hannun mace suka gani ya zuro ta jikin kaure ya murda key nan take ya bude. Nan fa tsoran su ya karu ba abunda ya kara tsorata su sai ganin wata kyakyawr zankadediyar budurwa fara ce tas!. Sanye da doguwar farar riga daga ka ganta kaga balarabiya. Wannan ya tabbatar musu da ba mutun bace aljana ce domin basa da alaka da Larabawa. Hannun budurwar rike take da Wani dan karamin akwati mai marika. Nufo su tayi tana murmushi. "Ina Amaryar ta so in miki makeup". Ta fada lokacin da ta durkusa tana kokarin bude dan akwatin. Haleema da Nasmat kamar ba abokan gaba ba domin haleema makal-kale Nasmat tayi Nasmat kuwa kokarin raba ta da jikinta take domin karta jawo mata. Aljanar ta tsaya tana kallan su gaba dayan 'yan matan amaryar kokarin turo haleema suke gaban aljana ita kuwa tana kara make wa. Sakin baki aljanar tayi tana kallan su ganin haleemq bata da alamar tahowa. Tsawa ta yi musu wanda ya rikita dukan su kanta ya fara futar da hayaki. Gaba daya sun firgice jikin halima na rawa ta taho tana wani kwabe fuska jiki na rawa. Daga tayi tako daya sai ta tsaya ta wai waya baya kamar ta ko ma. Aljanar ce ta wani harari kawayen amaryar da idanunta wanda sukq fara komawa ja. Da sauri mutum uku suka turo haleema da karfi. Ta fada jikin Aljanar ta dan rungume ta "Haba 'yar uwa ta ya kike tsoro na bafa cutar da ke zanyi ba". "To", din karfi da yaji Haleema ta fada jiki na bari. Nan Aljanar ta zaunar da ita ta fara Gyara mata fuska. Wasu kayan shafe-shafen ma kai baka taba ganinsu ba. Sai da ta gyara mata fuska ta fito fes! Tayi kyau sosai, Aljanar ce ta juwa musu fuskan Haleema "Tayi kyau kuwa 'yan uwa". Da karfin su kamar hadin baki ba wacce aka bari wajen cewa. "Eh tayi kyau". Duk tsoro suke ji. Sai da Aljanar ta gama gyara ta sosai har gwagwaran sai da ta sake hada mata mai kyau. "Kuta shi mu fita yau kowa sai yawa amaryar nan huduba. Cikin hanzari suka tashi saboda tsabar tsoro. Gaba Aljanar
Amaryar na binta baya sai 'yan matan amarya da suka rufo musu baya. A tsakiyar falo Aljanar ta zaunar da haleema ta ce su dakata ta kira wo muta nan. Ba garda ma duk suka ce "To". Fita tayi waje mutane anyi Tsuru-tsuru kowa sai tunani yake, wannan gidan biki baiyi dadi ba. "Sannun ku da hutawa uwayen amarya ko?, To ban ware kowa ba ku shigo ku mata hudu ba". Kamar daga sama suka jiyo maganar da sauri suka waiga duk wanda ya kalle ta ya san Aljana ce hakan yasa duk a tsorace suka tashi dan bin umarnin ta har rige-rigen shiga daki ake. Kuri sukayi wa amaryar inda ita kuma Aljanar ta tashi sama tana kallan kowa. Jin sunyi shiru sun saka amarya gaba kowa sai raraba idanu yake Ta daka musu tsawa. "Kuyi mata hudu ba nace ba ku sata gaba ku kalla ba". Kafin kace me dakin ya cika da hayaniya kamar makaranta haya-haya wani bai ma san abunda ke fitowa a bakin sa ba, kawai tsabar tsoro ne. Jin sun cika mata kunne ta kara musu wata tsawar wacce tafi ta farkon kara da ban tsoro. Da yawa sun zabura koya ya kama bakinsa yayi tsitt!. "Au! Dama haka ake huduba a garin ku?. Oya daya bayan daya zakuyi" mama asiya ta nuna da doguwar yatsa. "Ke fara". Mama asiya na karkarwa. "To, Amarya kina jina ki bi mijin ki sau da kafa kiyi masa ladabi da biyaya banda Rai ni shi shugaba ne a gare ki. Banda daga mishi murya duk abunda ya saka ki kiyi". Shiru ce ta biyo baya. "Au! Shikenan kin gama?". "Eh, A'ah" ta bada amsa. "To duk ke kina wa mijin ki hakan?". "Eh ina mishi mana". Ta fada tana murmushin dole. "Shikenan zan bibiyi rayuwar ki idan naga akasin haka to ke ma kin san sauran". Cewar Aljanar bata tsaya sauraran amsar ba.cikin daga murya ta nuna Zuwaira Da yatsa ke da kike noke-Noke oya saura ke". Zuwaira a firgice kamar ta saki fitsari ta fara karkarwa tsabar tsoro. "Too too niii dammmaa abuuu!!!...". "Ke ki natsu kiyi mana magana sak!, In ba haka ba yanzu in mayar dake Mage". Hannu zuwaira ta dora a kai. "Na shiga uku dan Allah kiyi hakuri karki mayar ni kyanwa.
Haleema ki tsaya kiyi tunani yanzu kin girma kin zama cikakar mace ki natsu ki zabi kawayen kirki masu nuna miki hanyar tsira karki dauki masu Janki juwa hanyar halaka. Wannan wani zama ni ne ya zo mana wanda shawarar kawaye ke bada babbar gudun muwa wajen kashe aure. Ki tsaya ki natsu ki gane aure shine darajar 'ya mace ki zauna da mijin ki lafiya......". Taf! Taf! Taf! Aljanar ta fara tafawa zuwaira da jin haka sau duk suka dau tafi..Aljanar tace kinyi kokari. A haka aka tayi duk illahirin matan da suke dakin hatta kawayen amarya kowa sai da ya to fa bakin sa ko baka da abun fada sai ka lalibo. In kaki kuwa sai dai kaga ta zuro hannuta tun daga can sama ta wanke ka da mari. Haleema tun tana dauka har ta kai ga sai dai ta ce "Eh", Kawai ko ta daga ma kai.
Wasa- wasa Dai abu har dare yayi anawa amarya nasiha. Dare nayi lokacin kuwa 'yan daukar amarya suka zo ko ta kan Alhji yayi nasiha ba'a bi ba. aka dauka Kowa na zumudin aka basu amaryar su.mata ko daya ba'a sama wacce ta tafi rakiyar amarya ba. Domin duk wacce ta fito daga cikin gidan. Sai tace "Alhmdulilah". Ta ari ta kare ko mai wai-wayen gidan babu. Haka 'yan matan amarya ma duk wacce ta fito sai ta ruga a guje ta nufi hanyar gidan su. Kamar dawa ki haka mata suka cika layin da guje-guje. Ganin za'ayi abun kunya ba 'yan rakiyar amarya yasa mama asiya da umma suka roki su Zuwaira da su taimaka a raka amarya. Su Fiddausi da su nasmat sune a matsayin kawayen amarya su hudun su kuwa su zuwaira a matsayin manyan mata. A tsorace suka kai amrya gidan ta suna kai ta kuwa kowa sauri yake ya fito. Ganin suna shirin tafiya su kyale ta ita kadai gata itama a tsara ce take. Kuka ta saki ta biyo su tace wallahi sai dai a koma tare baza su barta ita ka dai ba. Ganin da gaske take da kyar Fiddausi ta ce tayi hakuri su zauna har angon ya zo. Nan ma da kyar ta yarda. Su mama asiya ansha bulala duk jiki sai radadi. Ana tafiya a mota sai cewa direba (Driver) yayi sauri take. Kowa a tsora ce yake sai da suka karasa gida tukun hankali ya dan kwanta. Su Juwaira a kujerun fali suka zube kowa najin jiki hade da tsinewa gidan bikin. Nasmat da asmart Dakin su suka nufa domin suyi fitsari dan ya matsi ko wacce a ciki. rige-rige suka fara da gudu wajen shiga dakin. Sai da aka . kusan zuwa toilet din Nasmat ta tuno da macijin nan na dazu. Birki taja a gurin tayi baya. Taki fada wa Asmart dan mugunta. Asmart na bude bayin ta kwala uban ihu! Ta juyo a guje. Nasmat na ganin haka itama sai tace kafa me naci ban baki ba. Da gudu suka fita falo. Su mama asiya na ganin su a wannan hali basu tsaya tambaya ba ko wacce ta tashi a guje aka nufi hanyar fita a............................```
0 comments:
Post a Comment