Taki fada wa Asmart dan mugunta. Asmart na bude bayin ta kwala uban ihu! Ta juyo a guje. Nasmat na ganin haka itama sai tace kafa me naci ban baki ba. Da gudu suka fita falo. Su mama asiya na ganin su a wannan hali basu tsaya tambaya ba ko wacce ta tashi a guje aka nufi hanyar fita a.~
»» Su mama asiya Har karo suke yi ita da kishiyoyin ta wajen fita. Har anzo tsakar gida tukun Aamart tace "Nasmat wai miye ake wa gudu?". Tambayar da sukaji Asamart tayi ne yasa duk suka ja birki suka tsaya. Nasmat cike da mamaki tace "Me kika gani a bandaki kika yi ihu!?". Kyankyaso na gani mana, Shine na tsorata ke kuma sai naga kin rugo ai na dauka wani abun ne kika gani". Dogon tsaki sukaja kusan tare, kowa na haki tukun suka fara wa junan su dariyan. "Kaga 'yan iskan yara kun tsorata mu ai mun dauka Aljanar ce ai ta biyu mu har gida". Inji hauwa. Komawa sukayi cikin gidan gaba dayan su a tsorace suke ga barci ga gajiya amma ba wacce take da karfin halin shiga dakin ta ita kadai. fatima ita kam tuni har tabi lafiyar gado tun shogowar su ta farko. Suna nan zaune a falo har alhaji ya dawo. Da ya dawo suka tayar mishi da rikici domin ko wacce sai da ya rakata daki sai ta rufa da bargo tukun yake fitowa. Fiddausi kuwa sai wajen karfe sha daya angon haleema ya zo tukun tace gida zata. Da kyar suka lalaba ta ta yarda zata kwana a dayan dakin sai safe ta tafi.
Yau kusan kwana Biyar da faruwar hakan, kusan kullum sai Nasmat ta hadawa Asmart tarko domin ta taba Aljanar ko fatima amma har yanzu shiru kake ji. Abun na matukar cin ran Nasmat domin tasha zuga Asmart ta ci uban fatima ko kuma ta yiwa 'yar babyn wani abu amma ba abunda yake faruwa. Suna zaune a tsakar gidan kan but din motar baban su Fatima ta zo wuce wa Rike da 'yar tsanar ta. "Ke dan ubanki zo nan". Cewar Asmart, Fatima ta zo. "Muga 'yar babyn nan kullum kina tare da ita kamar mayya". Fatima bata so ba dan gudun kar a dake ta, ta mika wa asmart 'yar tsanar. Nasmat a tsorace take tun da Nasmat ta zo shiyasa ma ko uffan bata ce ba, Yanzu ma badan ta so take zaune a gun ba kawai dan mugunta ne, So take kawai asmart ta tsokalo wa kanta. Asmart na karbar 'yar tsanar ta juya ta ciki da bai, tana kare mata kallo. "Fatima naji ance wai babyn ki na magana ko?". Cikin fara'a Fatima tace "Eh mana tana cin abinci ma kuma idan aka bige ta ko na barta ita kadai har kuka take yi". Asmart ko da jin haka sai ta buga 'yar tsanar da kasa da karfi Tum!. Fatima sai binta kawai tayi da kallo. Asmart ta wani dauke Fatima da mari har sai da ta fadi nan take ta fara kuka. "Shegiya ma karya ciya kince tana kuka idan an dake ta to yanzu me ya hana tayi kuka?". Asmart ce ke fadar haka lokacin ta diro daga kan bayar motan. Taje ta dauki 'baby Doll din ta kama kan ta murda da iya karfin ta, da mugunta so tayi ta cira kan amma yaki cire wa. Fatima kuwa kuka take tana fadin "Aunty dan Allah karki kashe min babyna". Nasmat har yanzu zaune take kan mota sai kallan drama take, Cikin ranta farin ciki cike fal! Dariya ce ta mugunta ta kamata lokaci guda ta fara kyal kyalata. Suna hada ido da 'yar tsanar tayi gum baki. Domin gani tayi kamar hararen ta take.
Asmart kuwa 'yar babyn tayi a kasa ta fara tataka ta tana tsalle tana dira a kanta. "Wato har rai ne da ita da kike cewa karna kashe miki ita kenan, To gashin nan ta mutu". Wani tsalle da tayi gefan takalminta ya dan Daki gefan gashin kan 'yar robar wanda har wani dan guntun gashin ya tsinke daga kan. Fatima na ganin haka ta kara fashewa da kuka. Da sauri taje tana kokarin kwatar 'yar ta tana cewa. "Dan Allah aunty kiyi hakuri kinga har kin fara tsinka mata gashi". Asmart ta sunkuya ta dauki diyar "Au! Ashe fa gashi gare ta aunty yolash! Kenan, amma fa idan aka dan rage wannan gashin zata fi kyau dan haka bari inje in mata aski". Tana fadar haka ta nufi falo da gudu Fatima kuwa ta bita tana kuka tana cewa ta bata diyar ta.
Nasmat na ganin haka ta kyalkyale da dariya harda rike ciki tace "Asmart yau zaki ci ubanki, kin dauki ruwan da zai dafa ki". Haka su asmart suka wuce su mama asiya a falo da gudun tsiya fatima na binta tana kuka. Asmart na shiga dakin tayi sauri ta rufe dakin tana dariya. Fatima nan ta tsaya tana kuka tana faman bu buga kofar. "Ke fati uwarki nace, ko baki ji ba". Hauwa ce ke maganar. "Kaji 'yar iskar yarinya mutane na zaman su suna hutawa zaki zi ki ishe su da kuka". "Mama hauwa aunty Asmart ce ta kwace min babyna". Fatima ta fada tana kara rushewa da kuka. Afusace hauwa tayi kanta tana mata fada har da duka ta kora ta waje. Asmart na shiga dakin ta wullar da 'yar babyn a kasa hade da taka ta ta nufi wajen kayan kwaliyar su tana neman reza ita da gaske iski zatayi wa 'yar tsanar. Wani dan tsalle tayi na jin dadin ganin rezar nan fa ta zo ta zauna ta aske wa
'Yar tsanar kanta tas!. Tana kallanta ta kyalkyale da dariya, "Amma fa kinyi kyau sosai yar yarinyar fatutu, bari in ma kan nan kiss". Ta fada cike da zolaya ta manna wa kan 'yar babyn kiss. Uhhhmmahhh, Ai kuwa taji bakinta da kan kamar ansa gam an like. Jatayi da niyar raba bakin ta da kan 'yar babyn ai kuwa yaki rabuwa bakin nata ya manne Tun tana daukar abun wasa har ta kai ta ga fara kuka tana jan kan ki!ki!-ki!ki! Amma yaki fita. Hawaye shabe-shabe ta tashi ta nufi kofa tana kuka tayi-tayi ta bude kofa taki buduwa. Ihuu! Ta farayi tana neman dauki amma shiru gidan kamar ba kowa.Hannu tasa ta kama gangar jikin 'yar babyn taja da karfi sai ji tayi ta fizge ta. Ai kuwa ta wullar da ita can jikin bango a tsorace tana mai da nunfashi daya-daya. Fitsarin wuya taji da sauri ta shiga ban daki lokacin taji harda kashi ma. Tana tsugune ta fara jin wata 'yar siririyar dariya na fitowa daga dakin. tun anayi a hankali har aka fara da karfi abun yayi matukar tsorata ta domin bata san mai kalar dariyar nan ba a gidan. Wani hayaki kuma taga ya fara shigowa ta kasar kofar toilet din. Bata gama ba ta wanke a hankali ta dan bude kofar a tsora ce. Hayaki ne cike da dakin baka iya ganin na gaban ka ga kuma dariyar har yanzu yi ake. Mamaki da tsoro suka kara ziyartar Asmart a lokaci guda. Wajen da take jin dariyar ta nufa tana tafe a hankali duk da ba wani ganin gabanta take sosai ba. Tana tafiya taji tayi karo da wani abu tana kallan kasa taga wani abu ne lulube da Bakin zani kuma daga ciki dariyar ke fitowa. Karkarwa ta farayi tana tunanin ta daga ko ta barii.......................
*Kuyi hakuri kadan neee*
Ni kuwa Idan nice Asmart sai na daga naga ko ma miye. Kai/ke fa???. Lolz
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 39-40
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*DEDICATED TO YOU, ZAINAB ZEE*
*Hip hip hip hurray, Happy birthday to you*
🍰 *ZAINAB ZEE* 🍰
And
🍰 *BIEBOH* 🍰
*Ina taya ku murnar zagayowar haihuwar ku. Allah ya karo wasu shekarun masu amfani. Ya yafe zunuban da kukayi a shekarun da suka wuce. Ya kuma linka ladar* 😹 It's you day.
~Tana tafiya taji tayi karo da wani abu tana kallan kasa taga wani abu ne lulube da Bakin zani kuma daga ciki dariyar ke fitowa. Karkarwa ta farayi tana tunanin ta daga ko ta barii.~
»»Hannu na karkarwa cike da tsoro ta kama dan bak'in mayafin ta fizge karfi. 'Yar babyn ta gani kwance rufda ciki itace mai dariyar. "Aikin banza ashe wannan abarce ma har na tsorata". Asmart kafa tasa ta dan buge ta abunda ta gani yasa ta fara ja da baya. Idanun 'yar tsanar ne wani irin bak'in jini ke fita a matsayin hawaye ga wasu manyan hakora da suka zazaro waje wani abu take taunawa tana dariyar kamar danyan nama hakan yasa bakin ta shima yayi ja idanunta kuwa sun koma baki da ja. Sabanin bakin da fari. Heheheheheheheh, "Baki san nice ba ko?. To da kin dauka wace a ciki?". 'Yar babyn ce take magana cikin wata 'yar siririyar murya. Nan take jikin asmart ya fara rawa saboda tsoro magana na rawa-rawa, "Dan Allah kiyi hakuri ki rabu dani Wallahi bansan ke aljana bace. Wallahi na dauka diyar roba ce". HahahahHahhha "Wata dariyar mai karfin gaske 'yar robar tayi wacce tasa sai da Asmart ta rufe kunnan ta. "Wato ke azzaluma ko kina zatan zan kyale azzalumai irin ku ne? Muddun da rai! Na da lafiya ta bazan dinga sasauta wa azzalumai irin ku ba. Musamman masu cutar marayu. Yanzu in kina so in hakura ba abu mai wuya bane kawai zo ki dauke ni ki min wanka ki mayar min da gashi na". "To, To". Da sauri asmart ta fada, Lokacin taje da niyar Daukar 'yar babyn amma tayi iya kokarin ta ta raba ta da kasa ma abu ya gagara. Ita kuwa aljanar sai gagaba wata kalar dariya take marar dadin ji. "Oya daga ni mana ko so kike yanzu in fara taba lafiyan jikin ki?". Dan Allah kiyi hakuri *Aljanar fatima,* wallahi nayi-nayi na kasa ne". Hihihihihihh. "To tunda dai kika ce min Aljnar fatima naji dadi kuma na rage miki aiki amma da ko shekara zamuyi baza ki iya rabani da kasa ba. Yanzu abunda nake so jeki ki tsinto gashina ki zo ki mayar min abuna".
Asmart na karkarwa tace, "To ai dakin duk hayaki ne bana ganin gaba na. Tana rufe baki hayakin ya dauke gaba daya taga kamar ba'a taba yinsa bama. Da sauri ta nufi wajen ta fara tsinto gashin da ta aske a kan Aljanar 'yar babyn. Sai da ta tsinto gaba daya tazo ta mikawa aljanar a tsorace tace "To gashi". "Au! Miko min kawai zakiyi? Zo ki mayar min kamar yanda kika aske min in kuwa ba haka ba yanzu kiga karshen mugu". Da sauri Asmart ta matsa kusa ta fara kokarin mayar da gashin da ta aske. Daga ta dora sai taga gashin ya fado, aljanar kuwa sai dariya take. Asmart tuni ta gaji, ta kuma gaya wa aljnar itabkuwa tace dole sai ta mayar mata da gashin ta kamar yanda yake a da. A smart taci gaba. Tana yi ta fashe da kuka da karfi. "Keeeeeeee!!!". Wata muguwar tsawa aljanar tayi wa asmart tana yi kuwa dakin yayi duhu rundum. Asmar bata iya ganin ko tafin hannunta balle aljanar da ke gabanta. A zuciyar ta tace " wannan dama ce ta in tsere dan haka yanzu bari inyi nan nasan ta nan kofar fita take". A hankali ta tashi kamar barauniya take sanda. Kafarta taji tana takawa kamar a cikin hakukuwa. Abun ya bata mamaki ta fara zance a zuci, "To me ya kawo wannan hakukuwan cikin daki kuwa?, dakin da ake share wa kullum. Ahhh! Wayyo Allah kafa ta". Asmart tace yayin da taji ta taka wani abu kamar kaya ya kuma shige mata cikin kasa. Dake har yanzu mugun duhun na nan bata san ko me ta taka ba. Kuka ta fara tana Yarfa hannu tama manta da Aljanar. A wajen ta zauna sai lokacin ta tuno da ashe aljana na kusa. Hakan yasa ta rike baki ta gam. Rintse ido tayi hawaye na zubowa ga radadi zafin da take ji. Bude ido tayi haske fayau sai dai kuma a inda ta tsinci kanta ne abun yayi matukar girgiza ta da bata mamaki. Wani mugun daji mai wasu irin itatuwa wanda bata taba ganin kalarsa ba ko a TV gasu dogaye ga kuma fadi. Duk sunyi inuwa wa waje. Yanayin wajen kadai abun tsoro ne ko kukan tsuntsu babu balle kayi tunanin zaka sama mutum. Wa-waigawa tayi ko ina iya ganinta bata hangi karshen dajin ba. Kuka ta kara fashewa da shi, domin wannan ba karamin tashin hankali bane a gare ta. Sai yanzu idanta ya kai ga kafarta da ke zubda jini ashe kaya ce ta taka. Kara rudewa tayi ganin jinin dake zuba hannu ta dora kai ta fashe da kuka tana surutai na neman taima ko daga uwar ta da dangin ta.Da dai taga kukan baya yi. Sai ta fara kokarin cire kayar, daga ta dan sai ta sai ta saki kara, "Wayyo", Haka dai tatayi. "Kee! me kike a nan". Wata muryar ce katuwa ta fadi hakan, Kamar daga sama Fatima taji maganar
A firgice ta juya firgigit!. Wasu irin mutane ta gani masu mugun abun tsoro. 'yan kanana ne kamar yaro dan shekara 6 haka. Amma kawunan su a mulmule suke kamar kabewa Gasu manyan idanunsu kananu 'yan mitsi-mitsi. Ko wanne daga ciki gashi ne buzu-buzu a kan ba tsari. Asmart ihu ta kurma ta sa hannu ta fizge kayar ta tashi ta ari ta kare. Su ma kuwa sunkai su goma suka rufa mata baya. Sa'arta daya basa da gudu domin kan yake rinjayar su. Suta faduwa. Gudu suke cikin wannan kunkurumin daji asmart duk da tayi musu nisa bata tsayawa wai waye. Sai da tayi gudu sosai tukun ta sama gidin wata bishiya ta jingina tana haki.
Bata fi mintuna biyar ba taji wani irin gurnani a bayanta. A hankali take juyawa a tsorace. Wata bakar damusa ce mai jajayen ido. Sai bude baki take yi tana lasar harshe. Mugun tsurewa asmart tayi, da baya-baya ta fara tafiya damusar na kara matsota. Saurin da damusar ta fara ne yasa asmart ta juya ta runtuma a guje tana ihu! Da musar kuwa tace dake aka hada mu. Gudu take iya karfin ta tana waige. Wani makeken gida taga ya bayyana a gabanta. Batayi wani tunani ba ta Afka! Ciki ta rufo kofar, gida ne makeke mai kayan kwaliya da filawoyi iri-iri sai dai bata ga kowa a cikisa ba. Sannan ba dakuna sai daki daya wani wangame me wanda yake a bude sai wani jan labule dake sanye a kofar dakin shi ya hana aga cikin dakin. Asmart tunani take taje ko kuwa ta tsaya nan. Daga karshe dai ta yanke hukuncin gwara ma taje in ma kashe ta aljanar nan zata yi gwara ta kashe ta ta huta. Gadan gadan ta nufi dakin ta yace labule cike da jarumta tana shigewa Kyauren dakin ya rufe gam. Can Asmart ta hango wata mata tsaye Sanye da riga baka doguwa. Gashin kanta dogo ne shine ya barbazu ya hana q ga fuskarta. Cikin Masifa da daga murya Asmart tace "Ke.............
Yaseen na gaji. Kuyi hakuri da wannan.
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 41-42
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*DEDICATED TO YOU* 😍 👇🏽
*Mzz Dady*
*Rabi'atu Shua'ibu*
*Layuza*
*Phateema*
*Teemah*
*Maimunat (Aunty maimuna)*
*Ummu Azza..*
😍 Thanks d luv an supporting This book❤ Duk masoya na Ana mugun tare 🙋🏻♂
🎤🎼 *YAU TAMBURAN GIRMA NA BUGA DOMIN MASOYA NA,* ☺
🎤🎼 *INA MASOYA NA?. KU FITO* 👯
🎤🎼 *INA MASOYA NA?. KU FITO* 👯
🎤🎼 *INA MASOYA NA?. KU FITO* 👯
🎤🎼 *INA MUKU FATAN ALKHAIRI,* 👏🏼 *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺
🎤🎼 *INA MUKU FATAN ALKHAIRI,* 👏🏼 *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺
🎤🎼 *INA MUKU FATAN ALKHAIRI,* 👏🏼 *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺
👸🏻🎤 Dan Allah masoya Kuyi hakuri
🤴🏻🎤 Dan Allah masoya kuyi hakuri.
M INUWA 2 🤡
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Gashin kanta dogo ne shine ya barbazu ya hana q ga fuskarta. Cikin Masifa da daga murya Asmart tace "Ke....~
"Ke wai wace ce, me kika zo yi gidan mu?, Ke wacce irin muguwa ce?". Cikin karfin hali Asmart ke watsawa matar ta tsaye wacce ta tabbatar da itace Aljanar. Duk yanda ta ci cije ta kafe ta cire tsoro. Dariyar da aljanar nan ta bushe da ita sai da ya tsorata Asmart din dan sai da taji kamar ta ruga. "Keeee!". Aljanar ta fada lokacin da ta dago kai da karfi gashin kanta ne ya wani mi mike tsai-tsaye idanuwanta jajawur Wasu ba kaken abubuwa kamar tsutsotsin suna yawo a ciki. Fuskar tata a tabe take bakin ya wani jirge share gudu, Hancin ta a wani tabe yake. Idan kawa Aljanar nan kallo guda baza kayi marmarin karawa ba. Ko asmart kauce kai tayi da taga hakan. "Lalai samun waje wato kece yau har kike ce min Muguwa ko Asmart?". Da wata iriyar murya Aljanar ke magana wacce tasa Asmart cikin tsoro da fargaba. Duk rawar kan da take da farko yanzu ta daina karkarwa ma ta somayi. "Sunana Safuratu Ko kice *ALJANAR FATIMA* ko kadan bani bari ayi zalunci balle ni inyi. Ko da yake inayin zalunci sosai ma amma fa a kan irin ku azzalumai, Yarinya ce 'Yar karama gaba daya kun fita do wai me ta tsare muku miye abun zaluntar ta in baku taimake ta ba marainiya ce fa". Murya na rawa Asmart ta daga baki da niyar magana. "Baaa.....". Tsawa Aljanar ta daga mata "Me zaki ce min baki da abun cewa Kalmar *YI HAKURI* Kuwa ke ma baki dauke ta a komai ba yayin da kika tashi zaluncin ki, Dan haka nima yanzu dole in zalunce ki ba sani ba sabo". Aljanar na rufe baki ta nuna Asmart da yatsa. Sai gata tayi sama tana ihu! Tana harbe-harben iska Da kafa. "Hahhhahhhhahhahhahah. Yanzu kuma kinsan me zanyi?, Kasa zan sake ki kanki ya daki Dutsen can ya rabe biyu kinga an rage mugun iri". A smart ihu! Ta fara tana bada hakuri hade da rantsuwa baza ta kara zaluntar Fatima ba.
Kafin ta rufe baki tuni Aljanar ta sake ta kasa tayo tana ihu!. Ganin ta kusan zuga kasa gashi saitin dutse ne, Ta rintse idanu ta sadaukar. Ji tayi ta fado a katifar ta. Abunda yayi matukar bata mamaki kenan. Tashi tayi da sauri tana waige-waige cikin dakin abun ya daure mata kai, Tunanin da take wannan mafarki ne ki gaske. Ganin ba kowa a dakin yasa tayi magana a bayyane. "Shegiyar Aljanar muguwa yar...". Kafin ashar din da tayi niyar fada ya karasa fitowa taji wani abu ya diro a kanta ta baya. Ihu ta fara yi "Wayyo Allah na na shiga uku na lalace Dan Allah dan annabi kiyi hakuri Wallahi bazan kara ba". Da karfi Asmart din ke magana. 'Yar babyn ce ta diro gabanta. Tana mata dariya.
Mai wani irin siririn sauti. "Dama zuwa nayi in gaya miki wannan abun da ya faru a tsakanin mu ni dake in kika 'yarda kika fadawa wani Ke ma kinsan sauran". Tana fadar haka ta bace bat!. Asmart na ganin haka ta Tashi ta fito da gudun tsiya daga dakin. Nasmat na zaune a Falo ita da Ameerah suna kallo sukaga Asmart ta wuce a guje tayi waje. Nasmat ta tashi ta bita a guje tana wai-wayen kofar dakin. Haka ameera ma ta biyo su. A tsakar gida Asmart ta tsaya tana Maida nunfashi. "Ke uban miye kika wani rugo da gudu. Kin tsorata mutane". "Kyankyaso ne". Asmart tace wa Ameera. "Asmart Wallahi in kika kara mana wannan iskancin san naci ubanki. Ya zaki ringa fitgita mutane?.
Ameera na fadar haka ta juya ta koma ciki. Asmart tsuke baki tayi tana kwaikwayan maganar Ameera din. Nasmat ce ta Dan dake ta. "Ke gaya min me akayi ni dai nasan yanzu ba kyankyaso bane. Tunda naga baki fito da 'yar babyn ba". Wata muguwar harara asmart ta dakawa Nasmat. "Yar banza ni ai ba ruwa na dake ke dama ashe kinsan abunda ake ciki shine kika min shiru inawa aljanar tambada. Waii!! Ai yau naga ta kai na. Al'quran har na fidda rai!". Labarin abunda ya faru da ita taba wa Nasmat tace harda targa de. Sai dai tana duba wa kuma taga babu. Abun ya bata mamaki matuka. Nasmat ce ta fara gagaba dariya mai makwan taji tausayi dariya harda rike ciki. Sai da taba wa Asmart haushi ta cika tayi fam! Kamar wacce zata fashe tsabar zuciya. Sai da Nasmat tayi dariya mai isarta tukun ta tsagaita ta bawa Asmart labarin abunda ya faru da ita ranar Biki ta kara da cewa "Zuwan da nayi Gidan bikin ba dan Allah bane Aljanar ce ta tilasta ni tasa nayi mata wanka harda kwaliya". Hahahhahhahahhaha Asmart ta fara gagaba dariya ta rike ciki. Nasmat ta bata rai "Bansan iskanci fa Asmart kinsan dai ni yayarki ce". Hhahahhahh "Sorry ni kinsan abunda ya bani dariya ma wau da Kika mari fatima kan ya guntule kuma ta dauko ta biyo ki da shi zan so inga ya kika yi a lokacin.
"Nasmat ta danyi murmushi Sannan tace "Hmm ai ranar naga tashin hankali wallahi. Kai a yanke fa ya biyo ni yana magana". Asamrt tace "Ai kinyi kokari da nice da suma zanyi a gun". Yatsa Asmart ta dora a kan habarta alamun tana tunani. Can kuma sai tace "Nasmat ni kuwa inaga mun sama hanyar da zamu ringa yin mugunta a sauka ke". "Ban gane ba me kike nufi?".
"Yanzu zan fahimtar dake, Sa nin kanki ne gaba daya mutanan gidan nan mugaye ne ga Fatima, abu kada take musu su hauta da duka ko Zagi. To kinga kuma a yanzu daga an taba ta aljanar ke rama mata". Tsallan murna da jin dadi Nasmat tayi"Shegiya Asmart kanki yana ja sosai. Kinma san me na tuno da kika fadi wannan maganar. Wallahi sai na tuno malamin islamiyyar mu shi ya kamata mu danawa bomb". Hahhahaha "Kyale mugu Ai mu shikenan mun sama hanyar mugunta kum....". Fatima ce ta Rugo da gudu hannunta rike da 'yar baby, ta nufo su tana cewa "Aunty 'Ya ta na kuka wai madaya take so". Su kuwa suna ganin ta suka yi waje da gudu..
_____________________
Kullum tunanin su Nasmat a kan yanda zasuyi su hada malamin su da Aljana ne. Yau ma zaune suke su biyu a falo asmart ce tace. "Ni Wallahi bana so mu fara yin muguntar nan a kan kowa sai malam, Wai shi mugu zai ga mugunta ai. Yanzu dai hanyar da zamu bi dan mu hada su fada ya kamata mu nema". Nasmat tayi tsaki, "Ni fa tsoro ma nake aje yafi karfin ta kinsan fa duk karfin aljani malami in dai mai tsoran Allah ne sai yaci ubansa". Hahhaha Asmart tayi dariya "To ai kinji yanda kika ce in mai tsorab Allah ne, kin manta irin zaluncin Malam habib Jifa dan yana san wannan tsigai din duk wanda ya ko harare ta ne sai ya dake sa. Wani lokacin ma fa ba'ayi mata komai ba sai ta hada mutum da malam dan mugunta". Nasmat tace "Zainab ba, Ai ni haushin ta nake ji Allah yasa Aljanar ta hada har ita yanda take 'yar siririyar nan kuwa zatayi gudu". Dariya suka yi gaba daya. Suna cikin dariyar sai ga Ameera ta shigo hannunta rike da leda baka. A yangace ta zo ta zauna a gefe daya ko kallansu batayi ba. Su kuwa tun da ta shigo ledar suke kallo sun san saurayin ta ne ya kawo mata wani abun.
Tana bude ledar kamshin soyayar Kaza ya daki hancin su kamar wanda aka kira suka zo suka zauna a gefanta suna Lasar harshe kamar mayu. Kaza ce dankwaleliya da Robar Madara katuwa mai sanyi. 😒 Muguwar harara Ameera ta wulla musu hade da tsawa. "Nasmat Asmart ku kiyaye ni Wallahi zanci uban yarinya. Kaji yara kamar mayu daga ganin abu sai ku wani taso kamar an kira ku". "Haba auntynmu ai gani mukayi kayan Allah na Annabi ne". Cewar nasamt "Kaji uwar iyayi wato duk zaman mu dake ban isa a ce min aunty ba sai yau dan an ganni da dan abu na ko. To wallahi ba wanda zan bawa". Zumbur Asmart tace "al'quran sai munci".
"Sai kunci saiku.....". Ameera jin wayar ta na kara ta tsaya da maganar da ta dauko, Ta kara wayar a kunne. "Hello Habibina, Ok in fita?. To gani nan. (Just 5mints). Tana fadar haka ta tatara kayanta ta tashi cike da zumudi ta nufi dakin su. Kallo kawai su Nasmat suka bita da shi. Tana shiga dakin taga Fatima a kwance rungume da 'yar ta sai barci take. Da har tayi niyar tayar da ita kuma sai ta fasa a cewar ta idan ta tashe ta Fatima ma cewa zatayi sai ta bata namanta. Bayan ta tabbatar da ba kowa a dakin su nasmat basu biyo ta ba kuma. Karkashin gado ta tura ledar ta lulube da bedsheet ta fita da sauri amsa kiran masoyin ta dake kofa yana jira. Su Asmart kamar jira suke ta fita da gudu har rige-rige suke wajen shiga dakin. Bincike suka farayi da kyar suka gano ledar a karkashin gado. Kamar kazar ta uwarsu ce, Kowa ya ciri cinya daya-daya da sauri suka cinye abu ga marar gaskiya. Yegot din kuwa kowa korba Uku-uku suka yi suka hakura. Dariya Nasmat tayi na mugunta can kuma tace "To yanzu ya zamuyi". Dan jum kadan
Asmart tayi tukun ta kyalkyale da dariya. Nasmat tace "Miye?". "Kinga kalle ni dai kawai samin ido". Inji Asmart tana fadar haka kuwa ta dauki ledar naman taje ta ajiye a kan gadan Fatima da take ta barci ba ruwantan mai ta goga mata a hannayen ta Sannan ta shafa mata abun madara a baki da kagani kace ita tasha. Tana ganin haka ta...................................
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 43-44
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*DEDICATED TO YOU* 😍 👇🏽
*HASSAN ATK TANKO*
*HUSAINI ATK TANKO*
*UMMU BASHIR*
*BEAUTY QUEEN*
*SAMEE KHAIRAH NOVELS*
_Jinku nake a can karkashin Zuciya na_
*PHAREEDA KHAMSHI NOVELS*
_Kuna sani inji kamar ni King din gaske ne_ lolz
*BIGBOY ISAH FANS*
_Kukan na daban ne banda kalaman da zan yabe ko ko gode muku sai dai ince. Allah ya saka muku Allah ya barmu tare_
*KINGBOY ISAH NOVELS*
_Kun riga da kun zama 'yan uwa na jinku nake kusa da Raina. Auntys da sisters king dai na ji daku Allah ya bar zumunci_
😍 Thanks d luv an supporting This book❤ Duk masoya na Ana mugun tare 🙋🏻♂
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Kinga kalle ni dai kawai samin ido". Inji Asmart tana fadar haka kuwa ta dauki ledar naman taje ta ajiye a kan gadan Fatima da take ta barci ba ruwantan mai ta goga mata a hannayen ta Sannan ta shafa mata abun madara a baki da kagani kace ita tasha. Tana ganin haka ta.~
»»Kara bushewa da dariya. Da sauri suka fita daga dakin suka koma falo suka zauna suka ci gaba da tadin su kamar basuje ko'ina ba. Ameera na dawowa dakin ta shiga a bakin kofa tayi birki tana kallan kan gadan Fatima. Murje idanu tayi domin ta tabbatar da abunda idan nata ke hangowa gaskiya ne ko kuwa. "Kutu...". ta kawo ashar ta maka yayin da ta nufi wajen Fatima din a masifance. Dim! Dim! Ta hau ta da kulli baji ba gani, bata ma da kuka ta farka bata sana hawa ba batasan sauka ba sai duka kawai da taji. "Wallahi, yau sai naci ubanki a gidan nan wato har ni zan ajiye abu ke munafuka ki dauko ki ci min". 'Yar babyn ta dauka tayi tulli da ita a bango sannan ta kama Fatima da hannu biyu ta daga chamak!. A falo ta dire ta ta dauki wayar charger ta fara bulala ta. Kuka sosai Fatima tak tana fadin "Aunty me nayi miki?, me nayi miki?". Ita kuwa baji ba gani kawai dukanta take, Fiddausi na kitchen tana jin kukan Fatima ta fito a guje tana zuwa kuwa ta dauke Ameera da mari. Dafe inda aka mare ta din tayi "Kanbuh! Ni kika mara". "An mare ki azzaluma kawai so kike ki kashe wannan yarinyar ne ko dan kinga bata da mai rama mata ne". Safuratu dake gefe wadda su basa ganin ta tace, "Ga mai rama mata nan kuwa". kukan kura Ameera tayi ta cakumi wuyan Fiddausi nan itama kuwa ta kamata suka fara kunce da da naushin juna. Can Allah bawa Fiddausi sa'a ta wulla Ameeera da kadan ta fada kan Asmart t goce tana dariya. Ameera a fusace ta taso ido cike da kwalla ta kara kama Fiddausi. Su Nasmat kam gefe suka koma suna ta kyalkyala dariya suna kuma kara zugawa. Karar dariyar su ce ta fito da mutanan gidan. Fitowar mama asiya tayi dai-dai da kwada Ameera da kasa a karo na biyu. Da gudu ta rugo tubur-tubur tana zuwa kuwa ta nufi Fiddausi ta dauke ta da mari.
Kaji 'yar iskan yarinya mutuniyar banza kawai, kashe ta zakiyi sanin kanki ne kin fita karfi amma ki ke mata irin wannan kadi?". "Ai in ban kashe taba ita zata Fatima". Inji Fiddausi ta fadi tana kara murtuke fuska. Mama asiya ta rike baki cike da mamaki "Innalilahi, Wai dama saboda wannan mayyar yarinyar ne kike nema ki kashe 'yar uwarki. To Wallahi bari kiji daga yau Sai yau kar in sake ganin kunyi fada da 'yar uwarki a kan Waccan tsinanar Fatimar ko kashe ta zata yi ba ruwanki to ta mutu mana miye amfanin ta dama". Fiddausi hararen Ameera tayi da take gefe ido ya kawo kwalla. "Chabb! Wallahi bazai yuyu ba. Taya ina kallo za'ayi zalunci a gaba na Wallahi ko yanzu ta dake ta sai na rama mata. A'ah a kan me". "Haka kika ce, Haka kika ce. Wai ni kam Fiddausi yaushe kika zama marar kunya fitsara ra haka ne. Wai yau har ni kike kallo idona kina mayar min da magana san ranki?". Duk abunda ake Su Zuwaira gefe kallo kawai suke ba wanda yayi magana a cikin su. Mama asiya ta kama hannu Ameera ta tura ta. "Je ki daki Fatima muga a gaba na zata rama mata din ne?". Ameera kuwa ba kunya ta nufi gurin Fatima da sauri da nufin Fatima ta wanke ta da mari da juyowar ta kuwa Fiddausi ta dauke ta itama da mari mama asiya ce ta nufo ta da sauri da nufin ta dake ta. Da sauri zuwaira ta shiga tsakanin su. "A'a Wallahi bazaki dakar min 'ya ba haka kawai. Ai idan ki zo bincike ya kamata ki fara yi ba zartar da hukunci ba".
Mama Asiya tace "Au! Ni zaki wa gorin 'ya zuwaira, To naji malama bari inyi bincike kamar yanda kike so. Amma fa in aka kama Fatima ce da laifi yau ba mai kwatar ta a gidan nan ni da kaina zan ci uwarta". Ta kalli Ameera tace "Ke gaya mana me Fatima tayi miki, Duk da dai nasan kece mai gaskiya amma tunda Su malama Bincikatu ansa mu ai dole muyi bincike". A shagwabe Ameera ta fara magana "Mama wai fa habib ne ya kawo min Kaza da yegot Nazo na zauna kafin in fara ci shine ya kira ni.To dan kar in barwa wadan can jarababun su cinye min shine na tashi naje na kai karkashin gado ashe Fatima na jina shine tayi kamar barci take sai da taga na fita ta dauki ta cinye min cinya biyu Yegot din ma ta kusa shanye wa bari kiga sauran da ta bari". Tana fadar haka ta Nufi daki da sauri domin ta dauko. "To kinji ko?, Kinji ai ke mai Fatima to kinji munafurcin da tayi ko har yanzu kina goyan bayanta?, Bari ta zo da kazar Ai Kinga sai ki biyata tunda har kinda Karfin halin rama mata in an dake ai bazaki Rasa zuciyar biya ba in tayi barna". Mama asiya ce ke kallan Fiddausi tana fadar haka. Fiddausi kam bata ce komai ba amma a zuciyar ta tana shakkar maganganun Ameera. Asmart Rai a bace ta dan matsa wajen kunnan Nasamat tace "Assha abu ya baci fada ya tsaya a kan mutane ni kuwa Wallahi Aljanar na so taci uban Ameera". "Ke dai bari ai nima naji haushi Wallahi, Bomb din nan bai tashi a dai-dai ba".
Ameera na bude kofa taga mage ta kama ledar Kazar da baki ta nufi ban daki da gudu. Ai kuwa ta bita tana "Keeey! Keeey!". Tana wurwurga hannau alamun korarta take. Tuni magen ta Shige Toilet din. "Wallahi sai na amso abuna ba bandaki ba ko cikin kashi zaki shiga. Shegiyar mage ko daga ina ma oho". Ameera ke maganar yayin da ta nufi bandakin da sauri. Tana bude kofar ta Zura kafa sai ji tayi kamar anja kafar ta fadi kasa sharaf!. Magen ce tazo tabi ta kanta da gudu har yanzu da ledar a bakinta. "Wash! Wash!". Ameera ta fada ta kuma tashi cikin karfin hali ta bi magen dake taga karkashin gadan Su Nasmat ta shiga. Zuwa tayi ta durkusa ta tura kai Tana lekawa. Magen taji ta kama hancin ta. Wani mugun ihu! Ameerar tayi. Dan ji tayi kamar zata cire mata hanci da sauri ta fiddo kanta tana laluba hancin ko jini ya fito. Sai da taga babu tukun ta dan sama natsuwa. Kamar daga sama sai jin magen tayi ta duro a kanta ta fara yakushin ta tana karta mata farce a ko'ina Ihu! Ta fara tana faman kaka be ta. Can Allah ya bata sa'a ta yi wurgi da magen. Magen na zuwa kasa sai kuma ta mike da kafa biyu ta fara tafiya irin ta mutana. Murmushi magen ta nufo Ameera tana yi "Kawata ni zaki di ga yiwa iyen wannan?. Ce kace dai baki shan ko ni wacece ba ni ce fa". Magen ke magana wa Ameera maganar irin ta yara. Karkarwa Ameera ta fara. Mugun tsoro ne ya kamata nan take ta fara kuka domin tama rasa abunda zatayi.
Durkushe wa tayi kasa tana bada hakuri hade da cewa magen tayi mata rai!. Wata 'yar siririyar dariya magen tayi lokacin da ta zo tana zagaya Ameera da kafafunta biyu biyun kuwa tana jujuya su kamar hannu. "Haba kawata ni fa ba abunda zan miki ko baki gani ni ba ni ce fa". Aljanar ta fadi haka lokaci da ta tsaya a gaban ameera ta tsura mata idanu da suka juye suka koma Ja Blue. Ameera kallo daya tayi mata ta kara tsoracewa. Domin ko a tarihi bata taba jin mage mai (blue eyes) ba, wannan ya tabbatar mata da cewa aljana ce. "Dan Allah kiyi min rai!. Me nayi miki dan Allah me na tsare miki idan naman kike so ki dauka Wallahi na yafe miki, kuma Wallahi nayi alkawarin zan sayo miki rago dan Allah amma ki kyale ni". Murya na rawa Ameera ke magana haka duk jikinta rawa yake. Magen hannu tasa a bayanta ta fiddo w wani dan bakin glass (ko daga ina oho) makala shi tayi a fuska. "To shikenan tunda kin tsane ni na tafi bazan kara kawo miki ziyara bama". Ameera cike da farin ciki tace "To Mama na Allah ya tsare hanya". Magen ce ta juyo "Au! Na manta ban gaya miki ba na iya kitso ko za'ayi miki?". Da sauri Ameera ta dago "A'a Wallahi na gode jiya aka min". Ta bude kai "kin gani ma". Ta bude kai kafin ta dago taga ba magen sama ko kasa. Tashi tayi cike da tsoro tana waige-waige a dakin. Fitsarin tsoro ne yazo. Da sauri ta nufi ban daki dan ta juye shi. Bude ban dakin tayi hade da ihu!. Itama ta cikin ihu tayi. Ameera ce ba bambanci ko kadan har kayan jikin ta. Baza ka iya banbanta su ba. Kanta ne ya shiga juyawa hannu na karkarwa ta nuna ta cikin da dan yatsa "Ke wace ce ke mai kama dani. Ko Aljana ce?". Ta cikin ce itama ta mai do da shigen tambayar "Wacece ke ko aljana ce?...............................................
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 45-46
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*DEDICATED TO YOU QUEEN HAUSY* 😘
Wannan page kyauta na baki, Ina taya ki murnar kammala littafin ki
💧💦💧💦💦💦💧💦💧💦
*ILLAR BASHI PART 1*
💦💧💦💧💦💧💧💦💦💧
Littafin ya fadakar kuma ya tunatar hade da Tsoratar wa ga masu cin bashi Suki biya. Ina fatan wannan ya zama izina ga masu irin halin Cin bashi Su tuba su Daina In kuwa ba haka ba Suma Zasu iya ciyo bashin Aljana kamar yanda Yake a littafin😘
Mun gode kwarai da gaske Allah ya saka da Alkhairi Allah kuma ya baki hakuri kici gaba suburbudo mana Littafai. Muna jiran Next 😘
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kanta ne ya shiga juyawa hannu na karkarwa ta nuna ta cikin da dan yatsa "Ke wace ce ke mai kama dani. Ko Aljana ce?". Ta cikin ce itama ta mai do da shigen tambayar "Wacece ke ko aljana ce?.~
»»Bangane me kike nufi ba. Ai nice Ameera dama akwai wata Ameera ne mai kama dani komai-da-komai kamai ni?. "Aljanar ce ta kwada ihu! "Wayyo aljana" Ta nufi kofa a guje da ganin haka itama Ameera ta da sauri. Mama asiya a tsaye sai fada take kirtawa Fiddausi ba wanda ya kula ta ihu! Suka ringa ji har na mutum biyu ta cikin dakin. Hakan yasa suka tsare kofa da kallo. Ameera Aljana ce ta fara fitowa a guje tana ihu ta rukunkume Mama asiya da kadan ta kayar da ita. "Miye-miye?". Haka mama Asiya ta fara jero wa Ameera aljana tambaya ita kuwa kofan daki take nuna wa tana fadin "Mama Aljana...". Kafin ta rufe baki sai ga Ameera ta Asali ta fito daga daki sautin Muryar ta da kuma ganin ta da akayi shi ya firgita duk 'yan dakin gaba daya akayo waje da gudu. Ameera kuka ta fashe da shi ta bisu a guje tana fadin "Mama ni ce fa wannan ce aljanar". Mai gadi na dakinsa da jin ihun jama'ar gida da sauri ya dauko Adda ya fito ya nufe su yana kiran "Mine ne-Mine ne?. Nasmat da Asmart sune gaba wajen gudu da su ya fara cin karo basu tsagaita da gudun ba suka bashi amsa "Aljana ce". Da fadar haka ya buga ta kobi a kasa tayi dan kara cike da kuri yace. "Kul!-Ubanta Aljanar". Ya nufi falo a guje Ya kusan isa kofar falo kenan sai ga Ameera ta fito da ganinta yaja wani uban burki ya fadi kasa a tsora ce domin yaga Ameera a cikin 'yan gudu
"Dan Allah Aljana kiyi hakuri ki rufa min asiri na tuba bazan kara ba. Duk abunda na fada Wallahi cika baki ne ban dauka da gaske Aljanar bace". Da sauri Mai gadin ke fadar haka yana jan kugu yana da baya-da baya, Hannu Ameera ta mika mishi "Mai gadi Wallahi nice Ameera. waccan ce Aljanar Wallahi taba ni ka gani". Ai kafin hannuta ya karaso gare shi tuni yayi wani irin juyi Ya tashi ya zabga a guje. Duk uban gudun da su Nasmat suke yi sai da mai gadi y tarar da su har ya wuce su, Bai bi ta kan bude gate ba domin gani yake kamar bata lokaci ne Ta kan Gate din ya haura su Nasmat lokacin suka karaso ganin sunja gate din a kulle yasa suka fara kokarin hawa ta gate suma. Tuni Suka haye Su juwaira mama asiya da hauwa Duk sun tsure Ga Nin Ameera ta nufo su Tana fadar "mama nice Wallahi ta kusa da ku ce Aljanar". Itama kuma Aljanar abunda take fada kenan cikin tsiwa Kara rikita Su mama asiya take da fadin "Gata nana aljana Aljana". Gaba dayan su rudewa suka yi kowa jikinsa rawa yake. Ganin wannan ba mafita bace Juwaira da Hauwa suka fara kokarin Haurawa ta gate din suma. Mama asiya dake tasan jikinta yayi nauyi ko gwada wa batayi ba. Sai bada hakuri wa Ameera take. Juyawa tayi ta kalli su Juwaira da har sun kusa haye wa. Wani mugun bakin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta. Domin taga zasu gudu su barta. Kafafuwan su ta kama da nufin itama ta hau kan gate, Abunka da mai jiki tana kamawa kuwa ta rinjayo su. Da nauyinta suka rikito kasa gaba daya. Ameera Aljana ta faki idanunsu ta mayar da hannunta key ta bude gate din Da gudu ta fita tana "kufito karta cinye ku". Tashi sukayi Kamar ba sune suka fado daga sama ba a million suka fito daga gidan Ihu! Suke da karfi suna fadin jama'a Aljana Ita kuwa Ameera bata dai na binsu ba. Su kuwa su asmart lokacin da suka diro daga gate tuni mai gadi har ya kusan fita daga layin ai kuwa suma suka bishi tuni sun bar layin.
Tafe suke shida amaryarsa A tsakar gida sun nufo wajen mota da alamu fita zaiyi.Dam matashi ne cikin shigar sa ta 'yan sanda ASP Abdul King Article kenan. Ba abunda yake zurarwa amaryar nan sai karya. "Ai in gaya miki Zainab ba karami dace kikayi ba da kika same ni a matsayin miji. Wallahi kin gama dace wa". "Allah mai gida". Amaryar ta fada cikin mamaki. "Allah kuwa. Ke kinsan irin jarumta ta kuwa?. Duk garin nan magana ta ake duk inda kayi sai dai kaji ana maganar Asp Abdul King Article, Irin barayin da nake kamawa da 'yan iska Allah yayi yawa da su. Ke ni fa ko Aljani yayi sata in dai a yanki na ne ina tabbatar miki kafin Gobe sai na shako shi". "Kai mai gida Aljani kuma?, Ni fa gaskiya tsoran Aljanu nake yi". Hahahaha 'yar kuntuwar dariya ya yi "Kamar dai kin manta labarin da na baki ranar nace na kama barawo Aljani kin dauka wasa nake ko?. To ai shekaran jiya ma na kama aljani barawo". Ya fada yana wulwula yar feston din dake hannun sa. "Innalilahi, bani labari mai gida". "Wani dan iskan barawo muka kama a Kasuwa ya saci waya ashe Alja...". Bai karasa maganar ba suka jiyo ihun su mama asiya Ana Aljana-Aljana. Mai gida kamar fa Aljanar nake ji
Ana fada kuma kamar neman taimako suke". "Ai na gaya miki da na damki wuyan barawan nan na fara jibga..." Asp ne yake wannan maganar dan a manta da Zancan. Zainab ta fahimce sa hakan yasa ta takura mishi Sai da ta tursasa shi a kan sai yaje ya gano. Bai so ba cike da tsoro ya nufi gate din tana biye da shi a baya. A hankali ya bude gate din ya dan leka lokacin kuwa yaga su Juwaira a guje sun wuce suna faman ihu ciki har da Ameera ya gani. Juyawa yayi baya dan ganin abunda ke binsu din. Yana ganin wannan ameerar sak! take da ta gaban. Tsoro ne ya kamasa dan yagane alamun wannan ce aljanar. Da karfi ya juya ya banke Amaryar tasa ta fadi kasa bai bi ta kanta ba ya Ruga daki a guje. Itama kuta tashi ta bishi da gudu. Yana zuwa cikin wardrobe ya shike ya rufe duk da a mats........................
Alqur'an Na gaji 🙊 Dama yau bajin type din nake ba.
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 47-48
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
*DEDICATED TO YOU* 😘 ♥♥
Mineert Jibir
Jiddah A Adam
Musa Umar Abdullahi
Bilkisu Yusuf
Ummu Muhsin
Sadiya Bala
Hauwa Agabi
Maryam M Gidado
YearRya Yr Abba
Rabiu Shehu Ps
Jamila Mahmud
Naseer Saleh Babaiye
Sunusi Yusuf Jammo
Yariman Masoya
Maman Kawu
Yusuf Jibril Umar
Aslamiyyat Islam
*HAKIKA KU MASOYA NE. ALLAH YA BAR ZUMUNCI NA KUMA GODE DA ADDU'O'IN KU. HAR KU WANDA BAN AMBATA BA. KUMA RAI NA. A KWANA A TASHI WATA RAN ZAKU GANKU.*
Nasha dariya ba laifi. Saura kuma yanzu zakuyi taku.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Da karfi ya juya ya banke Amaryar tasa ta fadi kasa bai bi ta kanta ba ya Ruga daki a guje. Itama kuta tashi ta bishi da gudu. Yana zuwa cikin wardrobe ya shike ya rufe duk da a matse yake...~
_»»Haka itama Zainab haka Duk da wajen ya matse su Sai da ta kutsa ta shiga. Shiru suka yi na 'yan mintuna. Zainab tace "Mai gida wai miy...". Kafin ta rufe baki yasa hannu ya toshe mata baki. Yana cewa. "Kiyi shiru karta jimu". Ciki rada. Sun kai kusan mintuna 10 a cikin sunyi mukwai. Tukun can Asp ya dan leko dakin ganin ba komai yasa ya karashe fitowa. Kai gado ya fara yana wash! Wash!. "Mai gida gaya min wai me ya tsorata ka haka ne?. Nayi mamaki abunda ya tsorata ka yanda kake jarumin dan sanda mai fada da Aljanu..." Zainab ce ke maganar kafin ta karashe zancen da ta dako. Asp ya katse mata "Keee!. Rufa min asiri wane ni fada da Aljani kinga karki jawo min". "Haba mai gida kamar ba kai ne yanzu ka gama fada ba. Kace kana kama aljanu kana cin...". Nan ma bata karasa zancen ba ya dakatar da ita. "Zainab nafa ce miki ki raba ni da zancen aljanun nan. Ke inda kinga Aljanun da suka biyu wadancan muta nan da daga nan sai dai a dauko ki kinyi dogon suma. Kai!, Ban karashe tabbatar da jarumta ta ba sai yau". Asp ya fada yana kallan Zainab dake tsaye bakin ta dauke yake da uwayan tambayoyi. "Bani labari mai gida dama ba Aljana daya bace, ni ji nayi kamar suna fadar Aljana-Aljana". Asp ya gyara zama tukun yace "Ai in gaya miki ba aljana daya bace. Aljanu ne sunkai dari tun daga farkon layin nan in gaya miki aljanu ne har kofae gida.abunda yasa kuma kika ji su suna fadar Aljana, Ai wata Narkekiyar Aljana ce a gaba. Kingata wata makekiya kamar bishiyar kuka. Idanunta in gaya miki sun kai girman tulu. Ga wasu uwayen hakora Kai fin su da gani sunfi Raiza. Hancin ta kuwa sai a tusa mu mu biyu. Gashi a wani tabe Bama wannan ba wuta ce ke fita ta cikin sa. Kanta kuea wani makeke duk girmansa ba gashi sai wasu kwara uku dogaye wanda suka zubo mata har kusan gwiwa. Gata baki kirin"._
_Karkarwa Zainab ta farayi domin tuni Tsoro ya kamata. "Innalillahi, Mai gida Wallahi har naji mugun tsoro ya kama ni. Da gaskiyar ka da ni ce na ga wannan mugun abu Wallahi da suma zanyi a gun. Na gode Allah ma da yasa ban gani ba". Tana fadar haka ta nufi kofar daki ta garkame cike da tsoro ta dawo ta haye kan gado can ta dukun-kune wai ita da gaske tsoro ya kamata. Dariya yayi, "Hahahhahah kai haba dai Xainab karfa ki bani kunyi. Ba'a san matar dan sanda jarumi irina da tsoro ba, Ai ke baki ma san wani abu ba. In gaya miki lekawar da nayi Wai Aljana nan tayi man nuni da hannu alamun in zo. Ni kuwa naga tama raina min wayo hakan yasa na dalla mata wata muguwar harara irin wacce nake wa kananun aljanu suna zabgawa a guje, nan take itama kannun aljanun da suke tare da ita wajen guda goma suka zube sume.To wai ashe ita har ta ji haushi Nan fa ta fusata ta nufo ni gadan gadan. Abunda fa yasa na rugo da gudu kenan._
_"Lalai mai gida kai sadauki ne kuma jarumi. Ai in da ni ce da sai dai a dauko ni a group". Wani dan kara ne suka ji alamun an dan taba kyaure, Ai kuwa Zainab ta kwadda ihu! Kafin kace kwabo Asp king Abdul tuni har ya haura gado ya Shige blanket. Jin shiru ba abunda ya shigo dakin ne ya sa ya fito nan ya fara kokarin Cire kayan 'yan sanda dake jikinsa. "Yallabai ya naga kana faman cire kaya kai da zaka p
Office?". Zainab ta tambaya, "Amma sai yau na gane bakya kauna ta. In fita wato aljana ta wujijiga ni ko?. To in gaya miki ina nan ba inda zani yaseen yanzu bara in kira Dpo in sheda mishi bani da lafiya"_.
_Asmart da Nasmat tare da mai gadi ashe da suka sha kwana wani waje suka samu suka boye. A cewar mai gadi "Aljana ta fimu gudu duk gudun mu sai ta kamo mu gwara mu labe kawai ta zo ta wuce". Ameera aljana ita ce a gaba wajen gudu sai Zuwaira da Hauwa suna biye da ita. Can baya kuwa Mama asiya ce a tubur-tubur Gudun da take yau bata taba yin kalarsa ba. Ameerar gaskiya tana ce mata "mama ki tsaya ni ce". Duk sanda Ameera ta fadi haka ita kuwa sai taji kamar cewa tayi. Tsaya in yanka ki hakan ke sawa tana kara kaimi a gudun nata duk da ta gaji. Ameera Aljana tsakanin kwana-da-kwana ta bace bat!. Su Zuwaira na shayo kwana suka ga ba mutum. Tsayawa sukayi cik! Suna haki. Su asmart ne suka fito daga inda suke a boye suka fara Wa su Juwaira tambayoyin "Ina Aljana". Juwaira tace "Bakugwa Ameera ta shayo kwana ba?". "Ko daya mu bamu ga wata Ameera ba". Cikin daga murya Hauwa tace "To alqur'an wannan itace Aljanar tunda kuka ga...". Bata karashe magana ba sai ji tayi anyi ciki da ita. Dake bakin kwana take kuma lokacin su Mama asiya suka karaso a guje. Sanda suka wuntsula domin da karfi mama Asiya ta bangaje ta. Ameera na shayo kwana gaba daya suka yi shirin rugawa. "Ku tsaya- Ku tsaya wallahi ni ce Ameera ta gaban ce Aljana wacce ta fara zuwa". Tsayawa suka yi a tsorace suna kare mata kallo. Kallan zargin da suke mata yasa ta miko hannun "Ga hannuna wata ta taba ma taji Wallahi ni ce"._
_Kowa baya-baya ya farayi Hauwa ce ta kama Asmart tana kokarin Turo ta wai ta taba taji. Ita kuwa Asamrt ba abunda take sa kakafe wa tana cijewa, Ihu! Ta fara da taga hauwa ta fara turo ta da karfi ga Ameera na matsowa. "Wayyo Allah uwa ta, wayyo baba wayyo jama'a ku taimako zasu kashe ni". Asamart ce mai fadar haka da karfi. Abun ne ya bawa Juwaira haushi Zuwa tayi ta tunkuda Asmart da karfi. Ta fada jikin Ameera ta rungume ta. da ganin haka sai kowa yayi duk sai suka ji dadi sai yanzu suka 'yarda da Ameerar ta gaskiya ce. Nan fa aka fara tafka mahawara wasu na fadin a koma gida wasu na cewa Wallahi ba abunda zai mayar da su. Har yanzu mai gadi Bai fito ba daga inda yake a Labe domin shi gaba daya kunya ma yake ji. Kamar daga sama suka jiyo maganar alhaji. "Innallilahi Wa'inna illaihir raja'un, Mai zan gani haka". Alhaji ne ya fadi haka lokacin da yake kokarin fitowa daga mota. "Me ya faru Asiya nake ganin ko a Waje Cikin ku ba ko mai gyale?". Mama asiya da take a tsugunne dan tsabar gajiya da tayi ta Dago. "Yo alhaji tunda m ma baka ganmu ba zannuwa ba Ai sai ka gode wa Allah. Aljana ce fa Ta koro mu daga gida". Alhaji ya bata rai yace "Bana san zancen banza Aljana ko dai tsoran ku. Oya kowa ya shiga mota". Yana fadar haka ya juya ya shiga gidan driver ba yanda suka iya domin sun san halin Alhaji dole suka hakura suka shishiga. Sai da suka isa kof Alhaji yata oda a nufinsa mai gadi ya zo ya bude. Sai ma lokacin suka tuno da mai gadi. Fiddausi tace "Baba ai harda mai gadin muka gudu tare ma muka buya da shi". Tsaki alhaji yaja kawai ya fito ya bude Gate din da kansa suka shiga. A falo suka tarar da Fatima tana kallon Tv tana wasa da Babyn ta ba abunda ya dame ta._
_Su mama Asiya jaraba suka bita da shi wai wata kil ma itace aljanar. Alhaji na shigowa duk sukayi tsi! "Gobe zanyi tafiya wajen wani aiki kuma zanyi kwana biyu can, Yanzu ma shirye-shirye na taho in fara domin Tashin asuba zamuyi. Idan da mai matsala zata iya biyo ni ta fada". Yana fadar haka ya kama hannun Fatima yaja ta suka nufi sama. Suna tafiya Mama Asiya tace "Wai baku lura da wani abu kuwa". Gaba daya suka tambaya "Kamar me kenan?". "Wannan yarinyar ni fa ban yarda da ita ba. Dama ban fada muku mayya bace ai inaga itace ta zama Ameera dan ta tsorata mu domin gaba dayan mu mun tsora ta mun gudu amma ita kungo a kanta". Wasu basu yarda ba amma dan mugun ta kawai sai suka amince da hakan. "Mama asiya tace amma ku barni da ita ai gobe alhaji zai tafi zata ci uban......................._
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 49-50
NA. ✍🏼KING BOY ISAH👑
👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽
DEDICATED TO YOU BLOOD ME 😍😘
*TRIPLE QUNEENS*😉
*QUEEN HAUWA HAUSY* 😘👸🏻
*BEAUTY QUEEN* 💋😍
*QUEEN MARYAM 'YAR MAMAR MU* 😍😘
☺ _→ABUNDA YAKE DAINA, ZANA FITAR NA HUCE TAKAI'CI, SOYAYYAR KU A RAI NA ZANA FADA BAZAN BOYE BA←JINKU NAKE A CAN KARKASHIN ZUCIYAN. INA SANKU SOSAI IRIN TOTALLY DIN NAN_ 😁
'YAN UKUN ZAMANI KENAN 😉
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Wasu basu yarda ba amma dan mugun ta kawai sai suka amince da hakan. "Mama asiya tace amma ku barni da ita ai gobe alhaji zai tafi zata ci ubanta…~
_»»Washe gari tun da asuba Alhaji yayi musu bankwana bayan ya bar musu duk abunda zasu buka ta kafin dawowarsa. Mama Asiya kule take da Fatima hakan yasa tun da Asuba taje ta taso ta ta zo ta fara saka ta Aikace-Aikace. Wai sai tayi mopping din gaba daya falo. Har wajen karfe 7 Fatima na fama amma bata gama Ba, lokacin Duk matan gidan sun fito domin yin girki. Juwaira da hauwa ne suka taho a jere. Lokacin Fatima na faman goge TV din da ke makale jikin bango sai dadage take yi domin tsawanta bai karasa wa. Zuwaira ce ta lalabo ta bayanta ta yi mata wani mugun Dundu kamar wacce ta sama sa'arta. Fatima kuka ta kwalla da karfi. Da fara kukanta hauwa ta Wanka mata mari "Ke rufe mana baki dan uwarki ko in kara miki yanzun nan". Fatima ba dan taso ta matse bakin ta da hannu kukan na dan fitowa a hankali. "Shegiya kinibabba uwar iyayi, Yau shine zaki tarki wani goge-goge Na karya wato kinga alhaji baya nan dan kinsan yau dakuwa zaki yi a gidan nan shiyasa kika fara aiki tun yanzu ko?". Inji hauwa, Zuwaira tace "Dubi ma duk kin bata wa mutane waje da jurwayi Baki iya komai ba 'yar iska kawai". Kama kunnan Fatima tayi ta murda. "Fada min Uwarwa ta saka ki mopping kika bata mana Falo...". Maganar Mama Asiya suka ji wacce ta taso yanzu daga barci. "Ni na saka ta domin Yau bata da hutu a gidan nan". Gaba daya suka juya a tare "Au! Aunty babba ke kika saka ta ashe. Af! To ba laifi ai". Lokacin Mama Asiya ta karaso gurun tana murmushi mugun ta tana kare wa Falon kallo. A zuciya tana cewa "Lalai yarinya kin aikatu". A fili kuwa wata muguwar harara ta daka wa Fatima. "Muna fuka kin wani tsare ni da idanu kamar mayya kina wani kukan karya, Maza wuce kitchen". Ta Make ta a kai da hannu. Fatima tana kuka Ta shiga gaba suka bita baya su ukun sai zagin ta suke. Da aka shiga kitchen Fatima ta aikatu sosai. Domin wani abun ma yafi karfin ta kawai saka ta suke. Su ukun ma sun wa aikin yawa amma dan mugunta suka ki barin Fatima ta tafi ta huta. Yau dan wake suke yi da Tea ba'a dauki lokaci ba aka karasa. Zuwaira ce tace wa Fatima ta Tsiyayo man gyada a galan. Duk da tasan Fatima da kyar take iya karka ta galan din. Fatima ba gardama ta dauki mazubi taje ta fara Kokarin bulbulowa. Wani mai ne dan kadan ya Zuba a kasan mama Asiya na juyowa ta gani. Sai ta hau Fatima da duka da kuma masifa haka suma sauran._
_Fatima ta sha wuya gashi sun bige ta sun kuma wanata kuka. Hauwa ce tace, "Munafuka wato kin zubar wa da mutane mai salon yayi saurin kare wa ubanki yazo ya kama mana jaraba yace Ban nata sa muke yi ko. To Wallahi bari kiji Duk yau bake ba abinci a gidan nan". Mama Asiya tace "yauwa kinyi min dai-dai Abunda nake shirin yi kenan. Dan ubanki tunda watan azumi ya kusan kamawa ai dole ki fara koyan azumi. Dama azumi ba sahur yafi lada". Da fadar haka suka bushe da dariyar mugun ta harda tafa hannuwa. Fatima kuwa kuka ta saka domin tasan halin su in suka tashi mugun tarsu har fiye da haka yi mata suke. Aljana Safuratu dake tsaye Tana kallan su duk abunda suke. Itama dariya tayi Tace "Tunda kuka yanke wannan hukuncin. Nima na yanke irinsa a kanku. Ni da ku muga wanda zai cika, Ni nace kune bazaku ci abinci ba sai gobe". Da fada Haka ta sake fashewa da dariya. Duk abunda take kuwa babu mai jinta kuma babu mai ganinta. Mama asiya ce ta Juye dan waken a wata katuwar kulu wanda tasan Fatima baza ta iya dauka ba. Amma tace dole sai ta dauka Ta kai dinner room, Fatima ba gardama taje aka dora mata a kai tana kuka. Tun a nan ta fara Kokarin faduwa. Badan Mama asiya tayi sauri rike wa ba da duk ya zube. Ai kuwa zagi suka bita da shi gaba dayan su. "Tsinanna so tayi ta zubar kowa ya rasa, To Allah baiyi ba". Zuwaira ce ke fadar haka. Oya karbi wannan saura kuma suma ki zubar, Wallahi da sai na daure ki a gidan nan na zane ki. Na kuma sa kowa na gidan nan ya miki bulala Goma-Goma". Mama asiya ta fadi haka lokacin da ta Dorawa Fatima wasu uwayen farantai da Cokula ta kai Dinning. Fatima da kyar ta kai su domin sun mata Nauyi Haka ta dawo ta kuma jidar wasu kayan abincin. Sai da aka shirya komai tsabb! Dan wake kusan cike da wani katuwan kula. Ga kuma tea da bread._
_Mama Asiya ce tace wa Fatima taje ta sako kayan islamiyar ta tazo ta tafi makaranta. To kawai ta fada ta nufi dakin su tana shashekar kuka. Gaba dayan 'yan dakin barci suke sai Asmart da Nasmat Da suke zaune suna tsara wani abun suna dariya da gani kasan ba abun Arziki suke kitsawa ba. Suna ganin Fatima ta shigo suka taso daga inda suke da sauri suka nufe ta ganin tana shirin kuka kuma fuskarta da gani ta sha uban kuka.Nasmat cike da iyayi ta kama Fatima ta dora ta kan gado ta fara share mata hawaye, Tana fadin, "'yar kanwata waya taba muna ke ne kika taho kina kuka?". Tana shashekar kuka tace "Ba su mama asiya bane suka ta saka ni aiki kuma suka ce baza su bani abincin kari ba, Wai sai dai in tafi makaranta a haka". Asmart cike da tausayawa Tace "Ayya 'yar kanwata yi hakuri bar kuka taso muje in miki wanka Kuma in zaki tafi makarantar ma sai in baki Naira Hamsin ki karya". Cike da zumudi Fatima ta Amsa "Toh Aunty Na na gode". Tashi tayi Asmart tayo mata wanka nan suka zi su biyun suke yi mata kwalliya. Ko Fatima kanta da take yarinya abun ya bata mamaki, Sai dai hankalin ta bai ka ta gano akwai wani abu a kasa ba. Asmart ce tace "Fatima daga yau mun daina dukan ki. Kuma mun daina Zagin ki kinji?". Cike da farin ciki Fatima ta Rungumi Asmart "Na gode aunty amma har 'yar baby nama kun dai na Dokanta ko?". Kamar hadin baki da sauri suka ce "Eh daga yau baza mu kara ko taba ta ba". Suna fadar haka suka kalli juna dariya ce ta kusan Kubuce musu jin Sunyi magana a tare. Nasmat ce ta datse dariyar ta kalli Fatima tace, "Wai in tambaye ki, 'yar babyn ki ta iya Karatu?". 'Yar dariya Fatima tayi tace "Sai dai magana ko in dauko ta kiji?". Da sauri Nasamt tace aa ba sai kin dauko ta ba, Abunda nake so dai shine yau mu tafi da ita Islamiyya dan ta koyi karatu, Ai kina so kiji tana yi ko?". Eh fatima tace. "Yauwa yau da ita zamuje Islamiyya ta koyi karatu Daukko ta in goya miki". Cewar Asmart. Da sauri Fatima ta dauko kayanta na islamiyya ta saka. Tukun ta daukko 'yar babyn A tsorace suka goya mata ita._
_Suka saka mata hijab dake hijab din doguwa ce Ta rufe 'yar tsanar ba'a ko ganinta. "Karba kudin, Kije wajen mai.shayin can kice ya baki tea Da bread kinji?. In kinci sai ki tsaya a gun ki jira mu yanzu zamu shirya mu fito kinji?". Fatima tace to ta Nufi hanya ta fita. Da fitar ta su biyun suka fara gagaba dariya. Harda rike ciki Dariyar ce ma ta tashi sauran 'yan uwansu da suke barci. Asmaet ce ta dan tsakaita da dariyar ta kalli Nasmat tace "Kai sister amma kwanyar ki naja ba lalai ba malam ya tsallake wannan target din gaskiya kin iya mugunta". Nasmat tace "Kyale dan iska Nasan yanda ya tsani Diyar roba. Ko 'yar karama ce. Balle wannan katotuwar. Nasan sai yayi boll da ita in ma bai ce zai toyata ba. Kinga kuwa ita Aljanar ba kyale sa zata yi ba. Wata kil tun a gaban mu ta fara cin ubansa". Wafa dariyar suka dora da ita. Hauwa ce ta shigo tayi musu magana tace su fito su ake jira ayi breakfast. To suka ce tukun suka tayar da sauran. Suka je suka yo brush. A falo aka baje kowa yayi Ready Mama Asiya kawai ake jira ta fito. Ba'a jima ba sai gata ta fito. Bayan ta zaun. Kamar yanda aka saba hauwa ce ta tashi da niyar Zuzubawa kowa, Budewar da zatayi taga kular da ke cike da dan waken a wanke ko alamar lema ma babu balle..............._
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 51-52
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
*DEDICATED TO YOU MAH BLOOD NASMAT ('YAR MUTAN ARKILLAH, AUNTY AMA. KU KAM NA DABAN NE A GARE NI* 😍😘
😍 *SO AKAN CE HADI NA RABBAH, ZUCIYA KU TAKE YABAWA. NASMAT HAR DA AUNTY AMA, IN BABU KU SAI DAI A DAKAH GUMBA* 😔 *BAYYANAR SO GA WANDA KAKE SO, YA FI RIBA NI KU NA ZABA* 😘
☺ _KOMAI DADI AI BAYYI ZAMA DA MASOYA BAH. SO YAY MIN RANA DAMA DA BAZARKU NAKE TA RAWA KUMA INA._ ☺
_INAI MAKU FATAN ALKHAIRI. DUK ZAMANI WRITERS KU FITO_ 🙋🏻♂
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~A falo aka baje kowa yayi Ready Mama Asiya kawai ake jira ta fito. Ba'a jima ba sai gata ta fito. Bayan ta zaun. Kamar yanda aka saba hauwa ce ta tashi da niyar Zuzubawa kowa, Budewar da zatayi taga kular da ke cike da dan waken a wanke ko alamar lema ma babu balle.~
_»Kular kamas da ita ko alamar dan wake babu, Domin a bushe ma take, Sakin baki hauwa tayi tana kallan Su Mama asiya, Ganin kallon yayi yawa asiya tace "Ya dai hauwa lafiya kuwa, Ki zuba mana dan wake mana kowa fa ke yake jira". Karkato mata kullar tayi suka ga kular wayam, "Kutu.... Me zan gani haka?, To ina dan waken da yake kusan cike da Kula". Asiya ta karbi kular har shinshinawa tayi taji ko alamun dan wake ma babu. "Kutt! To alquran Wannan ba kular da muka zuba dan wake ce ba. Haba kuji fa ko kamshin dan wake babu a ciki". "Tashin hankali gobarar gemu, To waye zaiyi mana wannan aika-aika ina Fatima?". Zuwaira ke maganar tana kallan su Nasmat da suma sunyi tsuru-tsuru sai kallan iyayen nasu suke. "Fatima ai tun dazun ta tafi makaranta tace mana kunce yau baza ku bata abinci ba". Dajin haka gaba daya hankalin Fiddausi ya tashi Ta bata rai "Haba mama yanzu kun kyauta kenan?. Ya zaku kora yarinya da sanyin safiyar nan makaranta ba tare da ta karya ba. alhalin kuma kunsan ba'a taso wa sai Karfe sha biyu ake tasowa". Gaba dayan su wani mugun kallo suke wa Fiddausin " buhun ubanki Fiddausi ah! Kaji 'yar zamani, Yanzu mu zaki wa wa'azi To abinci dai in gaya miki yau ko kwaya fatima bazata ci ba acikin gidan nan. Bama iya yanzu ba". Cewar Mama asiya, Zuwaira tace 'Kyale 'Yar banza kamar yanda ta tafi da yunwa ke ma haka zaki tafi da ita tunda kinga kular dan waken, Kuma ba mai sani in kuma shiga Kitchen"_
_Gaba daya su Mama asiya ma haka suka fada, "Dan haka kawai Hauwa raba burodin nan kowa ya zuba tea yasha ya hakura". Tashi tayi ta jawo daya daga cikin maka-makan biredin wajen guda takwas. Wuka tasa ta yanka tsakiyar biredin mamaki ne ya bayyana a fuskarta ta tsaya tana kallan biredin Cikinsa yayi baki kirin wasu 'yan kananan kwaruka ne ma a ciki suke yawo. "A'a jiya fa aka sayo wannan biredin bai kamata ace ya lalace yau ba". Asiya ce ta taso daga kan kujerar da take a zaune "Lalacewa kuma kamar ya?". Hauwa ta mika mata biredin tagan shi rube, "Ikon Allah, A inaga wannan shine marar kyau din bara muga". Wani ta dauko ta yanka shima dai haka ba kyau. Gaba daya sai da suka fasa sauran bire din duk Sun lalace daga ciki amma bayan Ko alamar lalacewa babu. Asiya ta hau jaraba. Tana zazagen Gidan biredin. "Wannan ai rainin hankali ne, da zalunci. Ya zasu bawa mutane Rubaben Bread to Wallahi sai na mayar musu anjima". Tsaki Ameera taja. "Mtseewww! Mun kusan makara ga malamin mu bashi da mutunci bari mutum ko tea ne ma yasha". Tashi tayi ta dauki kofi ta karkata wani filas nufin ta ta tsiyayi shayi. "Kan uba!". Abunda ta furta kenan. Gaba daya aka juyo aka zuba mata na mujiya. "Wai ku yau kawai so kuke kuyi mana horo da yunwa kenan. Nan ai ruwa ne zallah ko zafi ma babu". Hauwa tace "mu gani" Ta dauki kofin "lah! Wallahi da gaske take ruwa ne zallah bayan kuma Ni da kai na na zuba tea a cikin nan"._
_Shiru su mama Asiya suka yi ido kawai suke bin Jama'ar gun da shi. "Mtseew To Wallahi ni dai bazan kuma shiga kitchen a yanzu ba. Haba kamar wata jaka?". Cewar Mama Asiya. Zuwaira tace "Wallahi ko ni bazan shiga ba". Fiddausi tace "To mu dai makaranta zamu tafi sai a bamu kudin Break". Dari bi biyu mama asiya ta bisu da shi. Tace "Kowa yaje ya sayi abunda zai ci mu dai ba wanda zai kara koma wa kitchen". Watsewa akayi kowa yaje yayi shirin makaranta. Su mama asiya kuwa mai gadi suka bawa Naira Dubu suka aike shi yaje ya soyo musu Indomie da kwai. Asmart da nasmat a wajen mai shayi suka tarar da Fatima ita har ta karya Tana zaune tana jiransu. Suma kudi suka bayar aka dafa musu indomie tukun suka nufi makaranta._
*______________________*
_Zaune yake yana cin Garau-Garau Yana ci yan girgiza kai daka ganshi kasan yana jin dadin abincin Sai da abincin ya rage baifi Cokali hudu ba ya kare, Mutumin ya Wani murtuke ya bata rai!. "Rafi'at! Rafi'at! Rafy!". Kiran yake kwalla mata da karfi. Ba'a jima ba sai ga wata budurwa ta fito ba laifi tana da kyau dai-dai gwargwado. Gaban shi ta durkushe "Mai gida gani". Mari ya kwada mata wanda har sai da taga Taurari nan fa ta kwada ihu!. "To fa safiyar ai tayi, Ke dai Rafy baki yi dacen miji ba ko kadan Wallahi". "Wai har yanzu Umar bai dai na dukan Rafy ba". Makwabtan su ne ke wannan Hirar. "Ina fa malam ai kullum sai ya dake ta". "Ashsha! Kai amma dai Allah ya shiryi Umar, gashi daga kayi masa magana sai ya hau ka da masifa yace Ai ba matar ka bace". "Ai lamarin sa sai Addu'a, Rafy tana da hakuri"._
_"Cikin bacin Rai da masifa umar yace "Yanzu ke Dan Uwarki kinsan wake bai dawo ba shine zaki kawo min abinci wato inci inshiga mutane Ina tusa ana kallona Ana dariya, Haka kike so ko?". Ya fada yana kallanta. Cikin kuka tace "Mai gida dan Allah kayi hakuri Wallahi na dauka ya dahu ne". Cokali ya dauka ya kara cika shi ya kai baki, Sai da ya kusan hade shi gaba daya ya Furzo!. "Kan uba! Ai banji bama sai yanzu haka kika cika yaji a abincin ashe, Ashe so kike ki kashe ni". Da sauri ya tashi ya nufi daki. Kamar tasan abunda yake shirin yi ta fara fadin "Mai gida dan Allah kayi hakuri bazan kara ba Allah". Fadi take da karfi tana mai-maitawa. Da wani Bakin Belt ya fito yana zuw kuwa ya fara Zane ta. Yana Fadin "Bari ni in illataki kafin ki kashe ni". Ihu! Take tana bashi hakuri amma shi ko kadan baya da alamar Sasautawa balle ma ya kyale ta. Da dai taga yana neman ya hallaka ta sai ta tashi ta ruga da gudu waje, Domin Tasan ba wani wanda zai kawo dauki. Haka yake in yana bugon ta mace ta zo Kwatar ta har ita yake hadawa ya daka. In kuwa namiji ne ya kore shi._
_Fitar ta tayi dai-dai da isowar su Fatima sai tin gidan. Haka ta fito tana kuka shi kuwa ya biyo ta yana fadi "Oya zo wuce ki koma ciki, Ko kuwa Wallahi yau in farfasa miki jiki". Hakuri kawai take bashi tana karawa. Dake tasan halinsa Ba dan ta so ba ta shige gidan a guje. Su Asmart kuwa abun ne ya basu mamaki. Nasmat tace "Kuturun uba!. Lalai akwai masu hakuri yo ai ina kamar wannan Wallahi mutumin nan bai isa ya dake ni in kyale sa ba, Wai dan yana aure na, Haba kamar wani ubana". Dariya Asmart tayi. "Wai ke sai yau kika taba ganin wannan azzalumin kenan. Ranar mu ai har ciki sai da muka shiga ni da Ameera ai kuwa ya biyo mu da kadan y zabga min bulala". Gaba suka yi Aljana Safuratu kuwa tun da taji zancen su nasmat ta fita daga Jikin 'yar tsana,Tace "wannan matar tana bukatar Taimako na, Kuma zan taimaka mata. Cikin gidan ta shiga ta iske su ya zaunar da ita yana fadar, "Yi min shiru muna fuka. Yanzu zan fita kuma ga naira Hamsin can a cikin aljihun rigar da na cire ki dauka ki auno shinkafa kiyi Cefani ki dafa min Farar shinkafa da miyar tumatur (Jar miya). Cikin kuka tace "Haba mai gida naira hamsin ai baza ta isa ko cefane ba". Tsawa ya daka mata hade da daga hannun " Yi min shiru ko in make ki Shegiya ni hka na yi niyar badawa kuma dole kiyi min. Kuma Wallahi idan na dawo na tarar bakiyi ba. Hmm kema kinsan sauran". Yana gama fadar..........................._
*TABB! LALAI ANYI MUGU A NAN*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 53-54
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
😒 *YAU SAI INGA WANDA ZAICE NAYI MINTSILI, (KARAMI) PAGE* 🤔
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
_*WANNAN PAGEN DIN NAKU NE*_
✍🏼 *ZAINUDEEN ZAIN* ✍🏼 😘
✍🏼 *SANAH S. MATAZU* ✍🏼😘
✍🏼 *SANAH SHAHADA* ✍🏼 😘
✍🏼 *RASH KARDAM* ✍🏼 😘
_Malamai kuma abokai a gare ni. Ubangiji Allah ya albarkaci Rayuwar ku, Yasa ku gama da duniya lafiya. Ku Ukun Allah ya baku mazaje na gari wanda zasu zame muku rahama, wanda zasu zare mayafin bakin cikin ku, su lulube ku da na farin ciki. Haka kai ma dan uwa Zainudeen, Allah ya baka Salahar mace mai sanka dan Allah mai hakuri da juriya. wacce zata Zame maka haske ta kore duhu a cikin rayuwarku._ 😎 Ameen Allah ya amsa....
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Yi min shiru ko in make ki Shegiya ni hka na yi niyar badawa kuma dole kiyi min. Kuma Wallahi idan na dawo na tarar bakiyi ba. Hmm kema kinsan sauran". Yana gama fadar.~
_≥»Yana gama fadar haka ya juya ya fice daga gidan. Safuratu tsaye tayi tana tunanin ta ina zata fara ji da wannan matsala, Can kuma sai ta bace bat!. Rafy na zauna sai kuka take abun duniya ya ishe ta ita kam yanzu bata ma san miye abun yi ba. Wata dattijuwa ce tayi salam Rafy cikin Kuka-kuka ta amsa matar ce ta zo daf! Da ita ta sama waje ta zauna Rafy ba abunda take sai binta da idanu wanda sunyi jawor dan tsabar kuka. Matar ce ta danyi gyaran murya tukun ta kalli Rafy cike da tausayawa "Rafy Nasan kina cikin matsanan matsanan ciyar damuwa, Naji labari kullum wannan mugun mijin naki sai ya dake to dan haka ne ma..." Da sauri Rafy ta daga mata hannu "Dakata baiwar Allah naji na gode da tausayawa amma ba ruwan ki wannan Kaddarar rayuwa ta ne, Dan haka dan Allah tashi ki tafi abunki". Matar ta dan muskuta kadan tace, "Haba Rafy ki saurare ni mana ni taimakon ki zan...". CikinTsiwa Rafy tace "Dakata malama nace bana bukata ki tashi ki tafi abunki, Wai ke din wace ce me ruwanki". Rafy ganin matar na neman dauko wani sabon zance ta tashi ta kama hannunta ta jata har waje tana cewa. "Naji na gode da shawara". Tana tura matar waje ta garkame gidan da sakata sama da kasa. Juyowa tayi da wani kukan na Takai'ci A zuciya cewa take "Ba taimakon bane bana so. Amma Nasan bazaki iya taimaka min da komai ba". Daga bayanta taji maganar matar tace "Rafy kiyi hakuri amma fa ni bazan bar gidan nan ba sai na taimaka miki"._
_Rafy na juwa taga Wannan matar ce sai ta kwada ihu! Ta ruga daki a guje nan ma ta rufo dakin._
*__________________*
_Su mama Asiya ne zaune a falo har wajen goma da rabi basu karya ba suna jiran Mai gadi har yanzu bai dawo ba. Mtseeww Mama Asiya tayi tsaki, "Wannan mai gadin sai naci ubansa in yazo Wallahi. Haba wannan ai iskanci ne. Ya zai barmu ko kari babu ya tafi uzurinsa". Tana rufe baki sai gashi ya shigo da sallamar sa. Mama Asiya kular take kallo tana mata fassarori Iri-iri kamar da abu ciki kamar babu. Yana karasowa ya ajiye kular a kasa ta saki sauti Kwangal! Daga ji kasan ba komai a ciki, Gaba daya binsa suke da mugun kallo, Jira suke kawai yace bai samo ba su bal-bale shi da masifa. "Hajiya Wallahi matsala aka samu wajen Mai shaye Biyar naje Duk inda naje sai in samu indomie din ta kare". Zuwaira tace "Kuturun uba!, Amma wallahu kayi mugun rai na mana wayo Akwai mai shayin da za'a je gunsa A rasa Indomie ne?"._
_Haba kyale shi Zuwaira, Inaga dai Wa'adin zamansa a gidan nan ne ya cika. Amma in ba iskanci da rainin wayo ba ya za'ayi ace kamar mu mu aike ka ka dawo mana da kula wai babu". Mai gadi ganin Aikin sa ya fara tangal-tangal yasa shi fara bada hakuri. Yana cewa "Dan Allah kuyi hakuri karku min sanadin aiki na Wallahi in kuna ma so yanzu sai inje in sayo in dafa muku". "Kutumelesi Dallah tashi ka bace mana karka fusata ni yanzu in sallame ka a aiki, Dan ma ka raina mana wayo mune zaka yiwa girki?". Tashi yayi ya fita da sauri ya barsu nan suna tsaki. Hauwa ta kalle su "Ni fa Wallahi bazan iya wannan abun ba, wannan ai cutar kai ce kawai ku tashi muje mu dafa ko indomie ce". Zuwaira tace "Sai dai in ke zaki yi taimako ki dafo min ki kawo min. Amma ni tunda nace bazan shiga kitchen ba to bazan shiga ba sai rana tayi". Mama asiya tace "Wallahi ko ni bazan shiga ba sai dai ki taimaka ki daho ki kawo mana". Mikewa Hauwa tayi zumbur! "Kuturun kare, To alqur'an ba wacce zanje inyi aiki in dafa abu in kawo mata tana nan ta Mimike kafafu a falo tana shakar AC". Mama Asiya ta tashi tana nuna Hauwa da yatsa "Ke karki kuskura, Wallahi karki kuskura ki zage ni". "Ni kam ban zagi wata ba amma dai maganar abinci nace bazan daho in kawowa wani ba". Tana fadar haka ta wuce ta nufi kitchen._
_Inda suke ajiye kayan abinci ta shiga. Tsaye tayi tana kallan dan Sito (store ) Taga wayam ko Kangon buhu babu balle ma asama mai wani abu a ciki. Haka ma kwalilikan indomie babu ko daya. Tsawa tayi cik! A wajen tama rasa abunyi. "Aunty Asiya!, Aunty Asiya!". Tun daga can take kwalla kira Asiya na jinta amma tayi kunnan uwar shegu, ta kyale ta. Sai da ta gaji da kwalla kiran tukun ta fito ta gayawa su mama Asiya abunda ke faruwa. Tubur-tubur ta tashi da sauri ita da zuwairar suka nufi kitchen din hauwa na biye da su. Tsaye sukayi suna kallan Store din suna kallan juna._
*_______________*
_Rafy na daki duk tsoro ya kamata kallan kofar kawai take. Mace ta gani ta ratso ta cikin kofar, Wani mugun kara tayi a tsorace ta haye kan gado ta wani kudun-dune cikin blanket. "Sunana Safuratu ni aljana ce amma ba muguwa bace ni. Dan ni nama tsani mugu, Naga mijin ki kuwa mugu ne shiyasa ma nazo dan in taimake ki. Dan haka ki saki jikin ki karkiji tsoro na". A hankali ta dago tana hada ido da Matar kuma sai ta kara shigar da kanta cikin bargon. Tana magana cikin tsoro, "Dan Allah kiyi hakuri ki tafi na gode amma mijina ba mugu bane dazun ma laifi nayi masa shiyasa ma ya dake n...." Kafin ta rufe baki Aljanar ta daka mata Tsawa wanda sai da ya rikita ta gaba daya. "Bana san iskanci fa, Wato dan kinga ina lalabaki shine kike min wannan kafiyar Yanzun nan zan mayar dake kaza kuma in kashe mijin naki in baki bani hadin kai nayi abunda ya kawo ni Salun alun ba". Dajin haka Rafy tayi sauri ta fito. "Dan Allah kiyi hakuri karki mai dani kaza Wallahi zanyi duk yanda kika ce Aljana". Aljanar ta dan matsa kusa da ita ta zauna. Rafy duk a tsorace take. "To da dai yafi, Kuma ina so ki saki jikin ki ki kaddara a ranki Kamar da mace 'yar uwarki kike magana Ba Aljana ba. Yanzu fara bani tarihin rayuwar Auren ku shin baya sanki ne Yake miki irin wannaj duka ko kuwa?". Hawaye ne yq fara Go slow daya bayan daya a idanunta kafin tayi magana cikin kuka._
*A social net muka hadu da Umar har soyayyar mu ta zama ta zahiri Domin dan anguwar mu ne ban sani ba sai daga baya. muna san juna sosai. Nida umar matsalan da aka samu shine Iyayena masu kudi ne Shi kuwa umar Okada yake da shi yake ciyar da iyayesa ma. Bayan nayi candy sai baba na yace aure zaiyi min kuma auren gida. Wato da dan yayan shi zai hada ni. Ni kuwa na nuna rashin amincewa ta nace umar nake so. Yayan baban nawa dake shi ya kawo shawarar a hadani da dan nasa da yaji nace umar nake so sai ya hakura ya janye. Yace ba laifina bane tunda ba'a tambaye ni wanda nake so ba. Mahaifina kuwa gaba daya ya kasa fahimta. Daga karshe ma cewa yayi zaiyi min Aure da Umar din kuma zai min duk abunda uba kewa 'yarsa amma idan wata matsala ta biyo baya kar in ko nufi hanyar gidansa. Haka na amince domin ji nake bazan iya rayuwa da kowa wanne namiji in ba Umar ba. Haka aka daura auren mahaifina duk a fusace yake dani ko hudubar kirki baiyi min ba. Wannan gidan umar ya kama mana haya muna zaune lafiya lau ba wata matsala kullum sai farantawa juna rai. na tsawan wata biyu, A cikin wata na uku umar ya bullo da wani sabon tsari wanda gaba daya ban sanshi da shi ba. Yau wata na biyu kenan Kusan kullum sai umar ya dake ni. Ba fira mai dadi irin ta ma'aurata. Na kai kararsa gurin iyayensa Suka kira shi a gabana suka mishi tatas, Suka mai fada sosai a nan yace bazai kara ba. Ranar da muka dawo gida Kashe ni ne kawai umar baiyi ba. Gida kuwa sau daya naje da suna yaji Babana ya koro ni yace ma karya kara ganin kafata a gidansa duk abunda ya faru dani ba ruwansa wai ni naja wa kai na. Ranar da Umar yake jin mugunta yasan bani da kudi kuma yasan babu mai bani haka zai dauki Kudi kalilan kamar yanda yayi yau. Yace in mishi wani abincin mai tsada wanda yasan kudin da ya bani bazasu yi ba. Idan ya dawo ya iske banyi ba haka zai same ni yata maka kamar jaka. Nayi kuka na zubda hawaye a kullum kuma addu'a nake Allah ya kawo min mafita Ni kam ba kudi nake so ba. Farin ciki da soyayyar da Umar ke min a da su nake bukata su dawo.*
_Safuratu tayi ajiyar zuciya tukun ta dafa Rafy tace, "Allah sarki haka rayuwar take, wani sai kayi masa tuwan shinkafa idan ya tashi sai kaga ya biya ka da bak'in kanzo. Ina so in miki Albishir da cewa Allah ya amsa addu'ar ki. In sha Allah zan mayar miki da mijin ki kamar da zan sai ta shi. Amma fa sai kin bani hadin kai". Rafy ta kalle ta cikin kuka, "Me zaki mishi, dan Allah karki taba lafiyarsa Wallahi ina sanshi duk abunda yake min ban taba fatan rabuwa da shi ba. Ni kam fata na a gare shi Allah ya shirya min shi". Dan murmushi Safuratu tayi, "Karki damu ba abunda zai same shi nayi miki alkawari, Misali yanzu idan umar zaiyi tafiya na kwana biyu haka, Zai iya kai ki gidan ku yq musu bayani kuma su amince?". Rafy girgiza kai tayi alamun aa. "Sai dai gidan Yayan babana". Aljanar tace "Ok dauko hijab dinki mu tafi can". Tana fadar haka ta tashi ta fito waje. Ita kuwa Rafy ta yi sauri ta dauko hijab da fitowar ta maimakon ta tarar da Safuratu sai Umar ta iske tsaye cikin manyan kaya ya wani bata rai!. Durkusawa tayi tana karkarwa dan tsabar tsoransa da take ji. "Me gida sannu da zuwa, yaushe ka dawo". Cikin fada yace ban sani ba ina abincin da nace kiyi". In-ina ta farayi "Um um, dama-dama.." Harara ya wurga mata. "Dama me?, Shin yanzu da kika sako hijab ina zakije?". Kuka ta fara tana fadin Wallahi ba "Inda zani". Dariya Umar din ya fara yi ita kuwa ta saki baki tana kallansa cikr da mamaki domin rabun ta da ganin umar na dariya Tun baya da wata biyu. "Matsoraciya ashe haka kike mugun tsoran Umar din. To ba Umar bane wannan *ALJANAR FATIMA* ce, Nice nayi sufarsa nayi kyau kuwa?"._
_"Eh kwarai mai gida kayi kyau". Ta fada da sauri Aljanar ta fahimci har yanzu Rafy bata yarda ba shiyasa ma tayi mata Muryanta, Sai a lokacin Rafy ta yarda ta mike tsaye. "Yanzu zuwa zamuyi in kai ki gidan yayan babanki ince masa zan danyi tafiya ne na kwana biyu, Kuma ba dadi a barki a gida ke daya shiyasa ma na kaiki ce, Ni kuma sai in koma sufarki in dawo nan in saita Umar tukun. Kina ganin yayan babankun zai yarda kuwa?". "Eh zai yarda". Inji Rafy "Ok to muje". Fitowa sukayi suka nufi gidan yayan baban nata Safuratu tayi kamar yanda ta tsara suka ci sa'a kuwa ya amince ya karbi Rafi'at. Safuratu kuwa ta fito ta koma gidan a matsayin Rafy din...._
*________________*
_Su Asmart suna ganin an kusa zuwa makaranta sai suka kunce wa Fatima 'yar babyn daga bayanta suka bata a hannu. Nasmat tace "Yauwa 'yar kanwata kinga daga yau 'yar ki zata iya karatu. Yanzu muna shiga cikin makaranta ki Je ki kaiwa malam ita kice karatu za'a koya mata kinji". Murmushi Fatima tayi wanda ya fito da gibinta ya kara bayyana kyawanta. "To aunty Nasmat amma Dai A kusa dani zata ringa zama ko?". Asmart tace "Eh mana ai a ma kan cinyar ki zata ringa yin karatun". Su nasmat Tare suka shiga makarantar. Suna shiga suka jiyo sautin karatun malam din a Aji na 4. Ajin su kenan Asmart tace, "Yauwa Fatima kinji Malam can a jinmu dan tsaya anan ki bari muna shiga muka zauna sai ki kai mai kinji?. "To". Fatima tace nan ta sama waje ta dan zauna. Tana wasa da yarta. Su Asmart gaba suka yi suna dariya harda rike ciki. Nasamt cikin dariya tace "Har naga ana yin sama da malam ana bugawa da kasa, domin nasan sai ya daki Fatima ko yayi wa 'yar babyn wani abu". Asmart tace "wannan ai a zaune take ke dai muyi sauri muje yanzu zaki sha kallo. Bayan sun shiga sun zauna ba'a dade ba sai ga Fatima ta shigo ajin da sallama tana murmushi, hannunta rike da 'yar babyn. Malam ya jawo wata aya yaje rabi kenan ya tsaya cik! Yana kallan Fatimar. Haka gaba dayan 'yan aji zurawa Fatima ido suka yi. Wasu suna tausaya mata domin sunsab yau ta banu tunda ta shigo wa da malam har cikin aji da 'yar tsana. Fatima kuwa tafiya ta fara ta nufi ind.……………………………………………………_
😰 *MUGAYE SUN HADA MATA BOMB. ALLAH YASA MA YA TASHI HAR DA SU.••••*
*DOMIN SAMUN FARKON LABARIN DAMA WASU LITTAFAN. SHIGA CIKI BLUE DIN NAN, KA/KI YI LIKE NA PAGE MU, TUKUN KA/KI DUBA KASA.*
*Fb.me//Zamaniwritesassociation*
Ko nan
*Fb.me//Bigboyisahfans*
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 55-56
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
😎 *WANGA PAGE SADAUKARWA NE GARE KI AUNTY NA. 'YAR MUTAN KATSINAWA.* 😎
🌹 *FATIMA MAMAN ALI* 🌹
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Haka gaba dayan 'yan aji zurawa Fatima ido suka yi. Wasu suna tausaya mata domin sunsab yau ta banu tunda ta shigo wa da malam har cikin aji da 'yar tsana. Fatima kuwa tafiya ta fara ta nufi ind.~
_»»Malamin Fatima ta nufa tana murmushi, sai da taje gabansa tukun ta tsayar da 'yar babyn da kafafun ta ta kalli malam da ya murtuke ya bata Rai yake kallanta. "Ina kwana malam, dama 'yar babyn na kawo a ringa koya mata karatu ta iya Surutu karatu ne kawai bata iya ba. Kuma so nake ta ringa yi". Kafa yasa yayi Ball da 'yar tsanar da karfi ta bigi jikin bango ta fada kasa tum!. A fusace ya juya ya kalli 'yan aji "Ina nasmat da Asmart?". Gamu nan suka fada a tsure. "Oya ku fito nan". Sumi-sumi suka tashi suka je gaban sa suka durkushe. "Kune manya ku zan wa hukunci domin ita yarinya ce bata san komai ba. Me yasa kuka bar Fatima ta taho makaranta da wannan Tsinannan abun?". Cikin hadin baki suka ce "Wallahi Malam ba tare muka zo ba". Karya kuke tare da ita kuka zo mana". Rantse-Rantse suka hau yi wai su alambaran ba tare suka zo da Fatima ba. Da malam yaga suna so su Bata mishi lokaci sai ya juya ya kalli Fatima. "Ke Fatima fada min gaskiya in kuwa kika min karya sai na yanka ki. Tare kuka zo ko A'a?". Su Nasmat ta kalla ko wacce a cikin su Uwar harara yake Tillo mata hade da gatsina duk dan karta fada. "Eh Malam wallahi tare muka zo". A fusace ya juya gare su. "Da Ni zakuyi wa karya ko Dan uban ku?. To ku jira hukunci kar wacce ta motsa daga nan". Hakuri suka shiga bashi shi kuwa bai ko tsaya sauraren su ba. Ya fita waje bai jima ba ya dawo hannunsa da wuka. 'Yar babyn ya dauka a yaje saitin gaban allo, "Kai ina so duk ku saurare ni, daga yau duk wanda ya sake yin ganganci ya shigo cikin makarantar nan da 'yar tsana, Kai bama a makaranta ba Ko a hanya na hadu da mutum da ita wallahi sai jikinsa ya gaya masa._
_Ya kalli su Nasmat tukun yaci gaba da cewa, "Sau nawa ina yi muku bayani ina fada muku Mala'iku na rahama basa zama a wajen da wannan gunkin yake, mu kuwa so muke mu kasance da su a ko da yaushe. Dan haka in kunje gida ku gaya wa babban ku na kwace 'yar babyn Fatima". Yana gama fadar haka ya sa wuka ya yayanka 'yar tsanar har gida shida. Tukun ya kwashe ta ya fitavda ita ya watsa saman soro. Dadi da farin ciki ne suka ziyarci su Nasmat. "Shikenan malam ya jawo wa kansa yau zai gane kurensa". A cewar Asmart, Nasmat tace "Ke ni fa tsoro nake ya zo ya dake mu wallahi". Ya daka din mana ai ba komai ni kam bazan ji zafi ba ko ya bige ni domin kuwa nasan shima yau zai bugu kum...". Bata karashe maganar ba Sai ga malam ya shigo hakan yasa ta garkame bakinta tashi shiru. Yana zuwa kuwa ya dauki bulalar sa sai da yayi musu goma-goma da karfi tukun yace su koma mazaunin su Fatima ma yace ta koma Ajin su. A cikin su Nasmat ba wacce tayi kuka Dan farin ciki ma suke yi wai yau malam ya tabo Alkakai._
*_______________*
_Umar kuwa yana fitowa daga gidan ya nufi gidan iyayensa ya gaida su dauki mashin dinsa ya fito bai zame a ko'ina ba sai wajen abokinsa mujaheed bayan ya parka mashin Ya sauka fuskarsa dauke da murmushi yaje ya mika mashi hannu suka gaisa shima yana kallansa yana 'yar dariya. "Abokina ashe kana gari shiru kamar kayi tafiya baka ko lekowa mi gaisa kai da kake da mashin". Umar sai da ya sama waje ya zauna tukun yace, "Haba mujaheed ya za'ayi in ki zuwa gurin ka da gangan, Wallahi kawai ayyukan ne sai a slow". "Gaskiya ne abokina to me ke Going?. Tun da naga fuskarka dauke da murmushi nasan a kwai labari". Hhhhhhhhh Umar yayi Dariya, "Gaye shiyasa nake san zama dakai Wallahi, domin kai din akwai kwalwa. Gashi dai har ka gano ni". "Eh mana bani nasha". "Kasan dai zance gizo baya wuce na koki, Maganar shawarwarin da kake bani ne kai gaskiya abun nayi min dadi, Yanzu gidana sai abunda nace ayi shi za'ayi Rafy gaba daya tsorona take ji. Yanzu fa idan na ajiye kara baban ta ma ya ajiye mu kowa yace karta tsallaka to Wallahi a yanda take jin tsorona idan nace ta tsallaka na baban ta sai ta tsallaka wallahi"._
_Dariya sosai Umar yayi yace "Gaskiya ne abokina ai nake gaya maka mace kullum kana bude mata hakora kuna wasa da ita wallahi gaba daya raina ka zatayi ta ringa ma abubuwan da taga dama, amma idan ya kasance tana jin tsoran ka, Haba Malam a nan zaka ji dadin rayuwa. kai ni fa yanzu haka maganar nan da muke yi gidan nan haka na fito ban bata ko kwandala ba kuma nace Dambun nama nake so da gasasar kaza. Dan tsabar tsoran da take min har russuna wa take tana godiya tana cewa an gama mai gida. Yanzu nasan ko bata da kudi sai ta ara ko kuma ta sayar da wani abun nata taje ta sayo min kafin in dawo". Duk maganar da yake Umar sakin baki yayi kawai yana kallansa. Dajin yazo karshen zancen umar yace "Kanbuhu! Ashe ni wannan yarinyar rainani tayi. Ni fa nake gaya maka Yanzu Naira Hamsin ne na bata nace ina san shinkafa da miya amma shine ta tsaya tana min surutai wai kudin ko cefane bazai isa ba balle Ma a auno shinkafa ashe kawai dukan da nake mata ne har yanzu bai sa tayi hankali ba". Muhajeed ya kama baki "Kai! Kai! Lalai kuwa bata horu ba. A hakan ma nake gaya maka dan fa baka sakar mata hakoran dariya ne amma da farat! Daya ma cewa zatayi bazata yi ba". Daga jin haka Umar ya mike jikinsa har rawa yake, Muhajeed yace "Abokina naga ka mike ina zaka?"._
_"Hmm, abokina kenan ai mikewar nan da kaga nayi ba inda zani gida kawai zan koma. Domin a yanda ka bani labarin matarka take ma in dai ba haka Rafy ta ringa min ba zuciyata baza tayi sanyi ba. Kuma wallahi in taki min biyayya yau sai na sumar da ita dan ubanta". Yana fadar haka ya mikawa Muhajeed hannu sukayi masabaha ya hau mashin dinsa yayi dogon ja. Mujahedeen na ganin Umar din yayi nisa sai ya kalle shi ya kashe da dariya yace "Banza kawai gara ka hadu da mace mai hakuri sai azbatar da ita kake. Uban waye zai wa matarsa duk abubuwan da nake fada maka in ba irin ku dolaye ba. Shege ni dama KA SAKE TA NA AURA". Umar har ya kusa gida ya sama passenger nan ya tsaya ya dauke sa. Shine ya juya akalarsa i zuwa cikin gari...._
*__________________*
_Mama Asiya, Zuwaira, Da Hauwa babu abunda suke yi in ba uwar hamma ba ta yunwa."mun shiga uku wannan wanne irin bala'i ne to wai me ke faruwa a gidan nan ne. Dazun a gurin kari Munzo mun iske babu Dan wake biredi a rube haka store ba komai. Gashi mun aika Mai gadi sayan indomie babu yanzu mun aike shi sayan abinci Ya dawo nan ma babu. Gashi har Azahar tayi gaskiya ni bazan iya jurewa zama da yunwa ba. Wallahi gidan mu zani ina dalili Azumin dole". Kamar hadin baki suma sauran suka mike "Ai muma bamuga ta zama ba wallahi". Kowa dakinta ta nufa ta daukko hijab kusan tare suka fito. Zuwaira ce a gaba ta nufi kofar fita a falo da niyar bude wa. Tana bude wa ta zura kafa da niyar fita sai ji tayi an hankado ta baya, Haka tayi baya ta fadi Tabar!, Dariya mama Asiya ta kyalkyala, "Saurin me kika haka harda faduwa?". Dan mugunta Zuwaira taki fadawa Mama Asiya turo ta akayi. Ai kuwa Asiya na zura kafarta da niyar fita. Da karfi aka hankado ta baya kamar buhun Hatsi haka tazo kasa Tum!. Badan Zuwaira ta goce ba da a kanta zata fado. Zuwaira da Hauwa me zasuyi in banda dariya, Dariya harda rike ciki Suna cikin Dariya suka ji kofar ta koma ta rufe da kanta da karfi. Hauwa taje tayi-tayi ta bude amma ina..._
*_______________*
_A cikin islamiyya karatu ake amma su Nasmat hankalin su kan malam duk motsin da zaiyi idansu na kanshi. Ko waje ya fita sai sun bishi wai su kawai sai sunga yanda zata kare shi da Aljana. Bayan sun dawo aji an shigo littafan Fiqhu Malam ya kalle Nasmat "Ke Zanyi miki tambaya a cikin littafin.Ahdhari (Ahalari) Minene farkon abunda yake waje ba ga Baligi?". Tsuru Nasmat tayi tana zara idanu ta kalli Asmart cikin Rada "me zance?". "Oho alquran nima ban sani ba". Malam ne ya daka mata tsawa "ke tambayar ki fa nake yi" A zabure tace "Malam abunda ya kamata baligin ya sani shine Mahaifiyar sa da uwayen sa da kannansa da abokansa da makwabtansa". Ta juya ta kalli Asmart "Dan Allah ko ba haka bane". "Haka ne mana" Nasmat ta bata amsa a takai'ce. Gaba dayan ajin suka bushe da dariya. Malamin kansa yaso yayi dariya kuma sai ya bata rai tsabar takai'ci bai kuma ce mata komai ba yace. "Maryam minene farkon abunda ya wajaba baligi?". Mikewa tayi cikin zazakar muryar ta ta fara bayani._
*"Farkon abunda ya wajeba ga baligi ya Inganta imanin sa sannan yasan abunda zai Kyauta farillan Ainihinsa kamar hukunce-hukuncen sallah Dana tsarki da azumi. Yana wajaba a gare shi ya kiyaye hakokin ubangiji, Ya tsaga ga umarnin Allah da hanninsa, Ya tuba ga Allah (SWT), Tun kafin yayi masa azaba".*
_"Attakah biirrr". Malam ya fada gaba daya ajin aka kaurade da fadar "Allahu akbar!". Wajen Nasmat ya zo ya mata bulala biyu, Hade da yi mata fada._
*______________*
_Tunda umar ya shiga gari bai dawo ba sai Wajen magariba. Yana fara'a amma da shigar sa gidan ya wani daure Fuska. "Rafy! Rafy!" Kira ya fara kwallawa sai can tukun ta amsa ta fito Tsaye kerere tayi masa. "Gani". "Ina abincin da na saki kiyi min?". "Banyi ba" ta bashi amsa a hatsale Hannu ya daga da karfi Da niyar kaura mata Mari, Charaf! Ta rike hannu........................._
🤣😂 *Tabb! Ramin mugunta su Nasmat a gina sa gajere*
🙆🏻♂ *Umar kuwai baisan Aljana bace, Pls aci gaba inji ya zasu kare* 😁
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 57-58
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
*DEDICATED TO MY JIGO ZAMANI WRITERS ASSOCIATION * IN san duk masoyan wagga kungiya
✈❤ *JIRGIN ZAMANI* ❤✈
*Mun hau mun shillah Ahhha ha* 😁 *JIRGIN SO ZAYA TASHI KU KADAI MUKE JIRA 'YAN GATA DUNIYAR SO KUNE DA SARAUTA.*
☺ 🎶🎵🎶 _Ku na gano da ku nake san rayuwa._
🎶🎵🎶 _Naga kuna da tausayi kunyi a rayuwa._
🎶🎵🎶 _Zanen dutse hali kuce bashi goguwa._
___
🎶🎵🎶 _Tarbiya ko a harshe ashe akan gane mai itta littafan ku da kansu sun nuna._ 😘
🎶🎵🎶 _Nayi dare ku ban masauki gidan ku in kwana._ 😛 _Kuzo ku shigo har abinci zamu muku kwadan rama_ 🙊 ZAMANI WRITERS ASSOCIATION 😘❤ *WE LOVE U ALL ZAMANI WRITERS FANS*
'YAN PHAREEDAH KHAMSHI NOVELS KUYI HAKURI WALLAHI PAGES DIN NE YAKE TSAYI IDAN NAYI COMMENTED SAI SU NUNA YAYI NAUYI. TO KAFIN RABASHI BIYUN SAI WANI UZURIN YA FIZGE NI. PLS
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kira ya fara kwallawa sai can tukun ta amsa ta fito Tsaye kerere tayi masa. "Gani". "Ina abincin da na saki kiyi min?". "Banyi ba" ta bashi amsa a hatsale Hannu ya daga da karfi Da niyar kaura mata Mari, Charaf! Ta rike hannu.~
_»»Gam ta rike hannun, Umar yaja-yaja ya kasa kwace hannunsa hakan yasa ya kara kai dayan hannun ds karfi da niyar ya dake ta shima rike shi tayi. Yayi juyin duniyar nan ya ware iya karfin sa domin ya kwaci hannun sa amma ya gaza hakan yasa ya bar kokarin kwatar hannun ya wani bata Rai!, "Sakar min hannun" yana fadar haka ta sake shi, Tsayawa yayi a gurin yana kare mata kallo har haske ta yayi da Torch ya tabbatar kums matar shi ce. A zuciya yake fadar "Anya kuwa wannan Rafy ce?. Dama Rafy na da wannan karfin take bari ina jifgarta?". Juyawa yayi ya kara kallan ta. "Bakiyi ba kika ce saboda me to kika ki yi?". A fada ce yake maganar "Saboda baka bar min kudi isasu ba mana". "Au! Kuma dan na baki kudin da basu isa ba shine ke baza ki cika ba kiyi yanda matan Kirki suke yi ko?". Da sauri ta bashi amsa "Sana'ar me nake yi?, ko kuma kana bani kudinka ne?. Kare mata kallo yake sama da kasa Mamaki ne yake karuwa a gare shi. Shi badan ma ya haskata kuma yaji muryar matar shi ce ba da sai yace ba ita bace, Domin yanda yasan Matarshi a kwana nan mugun tsoranshi take yi. Yanzu tsoran dokan ta yake tunda yaji Wani sabon karfi a gunta. Juyawa yayi ya nufi kofa da niyar fita. Ai kuwa ta baya ta kama rigar shi ta jawo shi kamar wani karamin yaro "Ina zaka je baka bani abinci ba?". "Sakar min riga malama masallaci zani". Murmushi tayi tukun tace, "To mai gida a dawo lafiya. Amma maganar abincin dare fa?". Bata rai yayi "zan sayo na kawo". Yana kokarin tafiya tace "To naji amma fa wallahi in ka dade sai na saka hijab na bika na lalubo duk inda kake". Bai ko saurare ta ba ya kada kai yayi gaba Sai sake-sake yake a ranshi._
________________
_Fatima tunda taga an yanka mata 'Yar baby an jefa sama take kuka. Gaba daya yau batayi karatu ba kuka kawai take malamin ajin ya dake ta amma take yin shiru Haka lalabo ma ba wanda baiyi ba. Ita kuwa taki. Ba yanda ya iya dole ya korota waje. Waje ta samu ta sauna ba abunda take sai kuka tana kallan saman soron da aka jefa mata 'yar baby. A haka har aka tashi gaba daya makarantar,Fiddausi ce tazo da kyar taja ta suka tafi gida domin da kiyawa tayi wai ita bazata je ba sai an dauko mata babyn ta. Sai da Fiddausi ta dake ta tukun. Su Nasmat kuwa gaba daya ajin aka watse aka barsu zaune ba abunda suke sai leke wai jira suke malam ya fito su bishi baya suyi ganin kwaf!._
_Nasmat tace "Asmart anya kuwa wannan ya fada tarkon da muka haka mishi?!". Asmart tayi 'yar dariya tace "Haba ke kuwa me kike ci na baka na zuba, Ki jira mana ni nasan bazata taba kya...". Bata karashe maganar ba taga malam ya fita daga makarantar da sauri ta dauki jikar ta ta nufi hanyar fita a ajin. "Yauwa taso, taso gashi can zai fita".Baya suka bishi ba tare da ya sani ba daga Sunga zai waigo sai su labe. haka in suka ga ya tsaya wata majalissa sai su sama waje su labe suna lekensa. Haka dai suka ci gaba da tafiya ba tare da ya gansu ba har ya isa gida. Yana zuwa ya shige gida su kuwa a bakin kofa suka tsaya suna kace-nace. Malam na shiga gidan ya fara jin kauri na tashi. "Masa'auda! Masa'auda!". Ya shiga kwalla wa matarsa kira. Gyaran muryar tayi alamun tana ban daki. Da sauri ya nufi daki domin daga nan kaurin ke tashi. Heater ya iske jone a socket An sata cikin ruwa. tayi daga gani ta dade a jone domin ta kusan tsotse ruwan tayi daga sama kuwa tayi jawur har wayar ta fara narke wa. Cikin hanzari malam ya kai hannun da niyar ya zare ta a jikin socket din, Ai kuwa yana kamawa abun ya hade masa biyu ashe robar ta fara narke wa ga kuma shocking. Wani mugun ihu ya kwada yayo waje a guje yana yarfa hannu yana fadin "Innalillahi!". Su Nasmat da suke kofa kamar jira sukeyi suna jin ihun! Suka afka cikin gidan a guje. A tsakar gidan suka ja burki ganin malam tsaye yana yarfa hannu yana kallansu. Lokacin Masa'uda matar malam ta fito daga ban daki da sauri tana tambaya lafiya. Malam kuwa harara ya watsa wa su Nasmat "Kai uban me ya kawo ku nan?". Kallan juna suka tukun suka juya suka kallesa kamar hadin baki suka ce. "Taimako muka zo yi, (Emergency)". "Taimako to uban waya yace muku ana bukatar taimako a nan". Asmart da sauri tace "Malam munzo wuce wa ne sai mukaji anyi ihu! Shine muka zo dan muga me ke faruwa"._
_"Oh! To daga ina kuke yanzu ko kuna so kuce min da aka tashi daga makarantar ba gida kuka tafi ba yawan ganta kuka fito?". Malam ya fada rai a bace. "Wallahi A'a malam ziyara muka je mu". Malam ya zaro idanu "Ziyara gidan wa a nan layin?. Ba nan layin bane can ne gaba kadan gidan wata kawar momyna ko a gida ka ansan zamu zo". Malam yace "To Shikenan naji kuma Wallahi in gaya muku in na tambayi Fiddausi ko Ameera gobe suka ce min ba haka ba, to jikin ku sai ya gaya muku maza ku wuce gida". Cike da haushi da takai'ci suka juya suka fita a gidan. Tsabar bacin Rai sun dade suna tafiya amma Ko kala ba wanda yace Sai Tsaki kala-kala da yake fitowa a bakunan su. Can asmart ta kalli Nasmat, rai a bace kamar tayi kuka tace "Ashe dai dama Aljanar nan mu ta raina?, kinaga fa duk abunda malam yayi mata ko tsawa batayi mishi ba". Nasmat tace "Ke dai bari abun ya kona min rai, Wai ace duk abunda mukayi munyi a banza malam sai ma kara mana duka da yayi. Amma fa kuma inaga Aljanar ta mutu ne?". Da sauri Asmart ta kalli Nasmat "Haba dai, Dama aljanu suna mutuwa ne?". "Eh mana baki ji malam adamu yace Idan suka rikida suka koma wani abu idan ka kashe abun shikenan ka kashe su ba. Misali idan aljani ya koma maciji in kika kashe macijin shikenan Aljanin zai mutu, To kinga kuma Wannan 'yar tsana ta koma kuma malam ya yayanka 'yar tsanar shikenan ta mutu kenan"._
_Asmart najin haka tayi wani tsallan farin ciki da jin dadi. "Wayyo da kuwa naji dadi Wallahi, Domin da Fatima ta shiga uku kullum da sai na sakata kuka sau uku. Kuma duk dukan da aka mana a Islamiyya sai na rama a kanta". Hhhhhhhhhh Nasmat tayi dariya ta dora da cewa "Ke dai bari mu isa gidan Ai ni kadai nasan abunda zanyi wa Fatima yanda Aljanar ta gasa ni itama sai ta gasu". Suna hirar har suka karasa gidan. Yanayin da suka tarar da gidan yasa basu nema Fatima bama kowa ta kansa yake. Domin Duk wanda ya shigo gidan ba damar fita sai gida ya garkame in kaje da niyar budewa Kuwa kasha mari. Haka suka kwana a ranar su mama asiya ba wanda yasa ko kwayar gero a baka._
_____________________
_Umar ne zaune gurin mai shayi ya saka a dafo mishi Indomie da kwai. Sai washe baki yake ana hira. Bayan wani dan lokaci daban aka miko Mai indomie mai zafi a flat wacce aka lulube da wainar kwai sai tururi Take kamshi na tashi. Karba yayi sai Hadiyar mugun yawu yake. Cokali daya yayi ya kai na biyu ya lumshe ido domin dadin da yake ji na Wainar kwan. Kamar daga sama yaji anyi ciki da Filet din indomie din duk ya warwatse masa a jiki. Da bude idansa da fitowar "Kutumar uba!".Daga bakinsa Duk daya, ba kowa bane Rafy ce tayi kwallo da Farantin indomie din takuma yi tsaye kerere tana hararen sa. "Ke dan iskanci da rainin wayo ni kika biyo har nan kika zubarwa da Abinci?". "Eh an zubar din mugu macuci kawai". Ta bashi amsa a hatsale Hannu ya daga ya kai mata mari cikin hanzari ta Duke. tana dagowa kuwa ta wanka mishi mari Tass!!!....................._
Yaseen na gaji
*Turkash!!!*
0 comments:
Post a Comment