~Ai kafin ta kai aya tuni Umar yayi waje da gudu sakamakon Zumudin da yake na ya fito ashe ya ma manta ko Gajeran wando bai sa ba Tsirara yake. Sai yanzu da ta fada ma ya lura hakan yasa yayi waje a guje.~
_*B*an daki ya koma ya sako kayan shi tukun ya dawo duk kunya ta cika shi. Lokacin da ya dawo tun daga bakin kofa yake jin kamshin abinci. Yana shiga dakin ya iske Rafy zaune tana zuba mishi abinci a plat "Babyna zo zauna in baka a baki". Yana murmushi ya karasa wajen ya zauna. Kallan ta kawai yake yana kara jin santa a ranshi yana tuna rayuwar su ta baya. A baki ta fara bashi abincin kamar yaro. Tana mishi hiraraki masu dadi. Har ya koshi, Tukun ta janye abincin gefe. Shiru ta biyo baya Kafin Umar yace "My wife ban tambaye ki mana?". "Ina jinka Uban 'ya'yana". Umar yace "Dan Allah ina kika samo wannan shinkafar gashi naga miyar harda nama?". Dan murmushi tayi tace "Hmm mai gida kenan. Da kudina na saya kawai dan in faranta maka. Domin nayi miss din dukan ka da zagi". A kunya ce ya sunkuyar da kai. (Kamar wanda yaje kwartanci gidan surikan shi) Rafy tace "Dama ina so in maka wata tambaya in ba damuwa babyna". "Ba damuwa inajinki" ya fada ba tare da ya dago kai ba. "In zaka tuna lokacin da mukayi aure Mu masoya ne na azo a gani. Ko kadan bana san abunda zai bata maka rai. Kullum cikin hidimar ka nake. A kanka har matsala muka samu da iyaye na. Amma Umar wata biyu baya sai ka mayar da gidan nan kamar gidan kaso a guna. Zuciya ta da take cike da farin ciki lokaci guda kasa kafa kayi facali da shi. Fuskar ka da ta zame min abar bege wanda nake kallo ina jin dadi. Sai ka mayar da ita Abar tsoro, abun gudu. Jikina da ya kamata ya sama kyakyawan kulawa daga gare ka. Amma sai ya zama abun duka. Umar mamaki na shine lokaci daya canjin yazo. Meyasa?_
_Umar yaja dogon lumfashi yayi kasa da murya yace "Ba wani abu yasa ba sai ganin lokacin idan na yarda mukaci gaba da zama a haka zaki rainani ki daina jin maganata. Hakan yasa..." "Karya kake Umar ba wannan bane fada min gaskiya in ba haka ba yanz in wuji-jiga ka a anan domin Ni ba Rafy dinka ta gaskiya bace". Cikin wata iriyar murya mai tsoratar wa Sufuratu tayi mishi maganar cikin tsawa. Wani iska kamar doguwar guguwa ya zagaye inda take Sai gani yayi ta canza hallitta zuwa wata dodanuwa mai ban tsoro. Mugun tsoro ne ya ziyarci Umar lokaci guda domin har fitsari ya fara kubce masa. Da baya aya fara ja yana Mata magiya yana cewa "Dan Allah kiyi hakuri Wallahi zan fada miki gaskiya. Zan fada zan fada". Aljanar cikin murya ba dadi tace "Ka sani cewa in ka yarda kayi min karya na kuma bincika na gano haka Wallahi sai ka gane kuren ka". Umar ya fara mata magana wanda bata fahimtar ma abunda yake cewa domin rawar darin da yake saboda tsoro. Tace mishi ya kwantar da hankalin shi ba abunda zata mishi muddun bai yi mata karya ba. Nan ya fara kora mata bayani._
_"Mukhatar dai babban abokina ne tun kafin in auri Rafy muke tare duk wasu abubuwana shi yake ban shawara. To bayan auren mu da wata biyu muna zaman lafiya da matata sosai idan na shigo wasa da dariya irin na masoya abun gwanin sha'awa. To wataran muna hira da Mukhtar sai nake gaya mishi irin zaman mu ni da matata. Ina gama bashi labarin sai ya bushe da dariya yace ashe ni banza ne marar wayo. Na tambaye shi dalili yace min ai wasan nan da muke yi da Rafy shi zai jaho raini a tsakanin mu raini na har abada. Da na musa mishi amma ya cika ni da zance har dai na yarda yace in gwada Murtuke wa. nuna mata wasa ya kare amfanin abun da yake gaya min. Ni kuwa na amince a zuciya nace zan gwada in naga abun baiyi min ba sai in dakata. To washe gari haka na tashi abu kadan idan tayi min sai in kyare ta idan ta nuna wasa take min nan ma in hantare ta. A ranar dai na canza mata sosai kuma tun a ranar ta fara jin tsoro na. Hakan yamin dadi nan na koma na fadawa Mukhtar sai yayi dariya yace Sai ma na ringa hada mata da duka zata na min ladabi kamar babanta. To ni kuwa dake na yarda da shi sosai dan ya fada min cewa shima haka yake wa matar shi.
Da yaga na nuna rashin amincewa washe gari yaja ni gidan nashi. Nan fa naga idan ya mata magana har rawar jiki take. Haka duk abunda za'ayi bata ko iya daga kai ta kalle shi dan tsoro. A gabana ya bata naira Dari yace ta sayo masara da kayan miya da nama tayi musu tuwo da dare. Ko.gardama batayi ba ta amsa tana godiya kamar wacce ya bawa dubu. Nan na tambaye shi nace ya dari zata isa a sayo masara nama da kayan miya. Nace ai ko kayan miya kadai wanda za'a saya sunfi na dari. Yayi dariya yace ai ita zata cika a cikin kudinta. Dake naga tana sana'a shiyasa ban ko musa ba. Kuma abun ya burge ni Kwadayin hakan yasa nima na hau hanya. Wannan shine gaskiyar zance._
_Dajin haka Safuratu ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Ta dade tanayi tukun ta da kalle shi cikin dariya tace, "Amma Wallahi ka bani mamaki wannan ai shirme ne da rashin hankali. Daga baka wannan banzar shawarar dan karta rai naka shikenan sai ka maisheta jaka kata duka Wai ni kuwa kana santa kuwa?". "Da sauri Umar yace sosai ma ina santa Wallahi". Safuratu ta watso mishi wata irin harara da idanuwan ta irin na dodannin wanda in ka kalle su baka shirya ba sai ka sume tsabar tsoro. Da sauri Umar ya kauce kanshi. "Karya kake baka santa Umar. Domin masoyin gaskiya haka kawai bazai ringa azabtar da masoyiyar sa ba. Masoyi kullum burin sa shine yaga masoyin sa cikin farin ciki. Shin kai kuma kayi hakan?. Ai ko kadan ba wanda zai yarda cewa kana san Rafy dan haka ni yanzu zanje in sama iyayen ta in basu hakuri kai kuma maza rubuta mata takardar saki". Durum! Gaban Umar yayi mummunan fada ji yayi kamar jiri na debar shi. Bai san ma yana san Rafy har haka ba. Tunanin irin wulakanci da cin zarafin da yayi mata amma ta jure take zaune da shi haka yayi. Nan ya zube gaban Safuratu magiya da roko ko wanne kala yazo bakin shi fada yake. Yana hadata da Allah ta rufa mishi asiri karta rabashi da matar shi. Safuratu tace "wato ma da ita kaci gaba da jibgarta kana cin zalin ta ko?. To bazai yuyu ba". Kuka Umar ya kama tun karfin shi yana magiya Ita kanta ta tausaya mishi batayi zatan yana san matar tashi har haka ba. Abunda ta lura dashi shine duk abunda yayi bayin kansa bane laifin Mukhtar ne._
_Cewa tayi "Umar bazan rabaka da matar kaba amma in kamin alkawarin bazaka sake mata irin abubuwan da kake mata na wulakanci duka da sauran su a baya". Da sauri Muktar yace ya amince. Safuratu taci gaba da cewa "Sannan kamin alkawarin zaka rabu da Mukhtar domin Mukhtar munafuki ne duk abunda yake gaya ma ba gaskiya bane domin kamar mijin hajiya take tsoran matar shi yake. Duk lokacin da kaje ka iske shi a waje to laifi ya mata ta koro shi wajen". Umar zugun yayi zuciyar shi sam.bata amince da maganar da Safuratu tayi a kan Mukhtar na tsoran matar shi ba. Safuratu tayi wata yar guntuwar dariya tace "Nasan bazaka yarda da zancen da na fada maka ba. Domin ganin yanda matar tashi ke nuna maka idan kuka shiga gidan nunawa take tsoran Mukhtar. take wanda kuma hakan wani plant ne shi Mukhtar din ya hada. Duk wannan zabure-zaburen da yake mata da zarar ka fito a gidan sai ya biya ta kudi dake kasan mayyar kudi ce. Amma abunda nake so dakai yanzu Bari inje in dawo ma da matar ka gobe zan nuna ma a zahirin waye abokin ka". Kafin Umar ya daga baki Safuratu ta bace nan ta barshi sai cicira ido yake. Ita kuwa can taje gidan kawun Rafy a sufar Umar ta dakko Rafy. Da kawun nata yace ta bari sai da safe ta shirya amma taki yarda dake ita kant ta gaji da zaman gidan duk da ba takura amma tafi san gidan mijin ta. Kuma tun da taga Umar tasan Safuratu ce kuma tasan akwai wani abun. Tun a hanya Safuratu ta kwashe labarin duk yanda sukayi har da labarin su sarkin bori ta bawa Rafy. Rafy tayi dariya sosai a zuciyar ta kuwa addu'a take tana fargaba game da Umar. Tare suka shiga har cikin daki Umar ba karamin tsorata yayi ba ganin Safuratu da sufar shi sak! Har kayan jikin sa ba banbanci. Da har ya tashi zai ruga ya boyi Safuratu ta tsayar da shi. Rafy kuwa dariya ma abun ya bata. Domin ita yanzu bata ma tsoran Safuratu ko kadan dan ta gane ba macuciya bace. Safuratu tace kaga malam ga matar ka nan na dawo ma da ita ni na tafi sai da safe gobe ka shirya zamuje gidan Mukhtar ka gane wa idan ka. Da fadar haka ta bace Battt!..............................._
Ganin Safuratu ta bace nima nace bari in gwada bacewar. Batt!! .Lolz
*NA GAIDA SAFURATU. KIN KUSA SAITA NAN GIDAN SAURAN SU MAMA ASIYA*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 79-80
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
😍😘 DEDICATED TO ZAMANI WRITERS. JINKU NAKE KAMAR YAN UWA NA NA JINI. ROKON ALLAH NAKE YA KARA DAUKAKA DA BASIRA. ALLAH YA TSARE MU SHARRIN MAHASSADA. ALLAH YASA ALBARKA A WANNAN KUNGIYA TAMU.
💃🏻 Yanzu halin wasu bakin hanga.. »Baki na hanga...
💃🏻 Basu ganin wani yanada burga...
»Yanada burga...
💃🏻Sai su bi daya biyu su zaga..
» biyar su zaga..
🕺🏻 Munsan arzikin mune.. Zaya bimu...
🕺🏻 Inadai lokacin mune za a jimu...
🕺🏻Kalmomi adansune Tubalin mu...
🕺🏻Harshe zamu tsarkake har ya kaimu.... 💃🏻💃🏻🕺🏻🕺🏻🕺🏻💃🏻🕺🏻💃🏻🕺🏻💃🏻🕺🏻
🕺🏻Kyan lafazinka kwaliyar ka...
🕺🏻Inka biyata sai a dauka...
🕺🏻Sai makiyin ka ma yabika...
🕺🏻Ayita fada dashi a kanka...
💃🏻 Kada harshe ya kai ya barka...
» Yakai ya barka..
💃🏻Yi tunanin amo ka saka...
»Amo ka saka...
💃🏻 Adabi shi ka gyara littafi 😆
» ya gyara littaf...
🕺🏻Nazarin duniya misali....
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Domin ita yanzu bata ma tsoran Safuratu ko kadan dan ta gane ba macuciya bace. Safuratu tace kaga malam ga matar ka nan na dawo ma da ita ni na tafi sai da safe gobe ka shirya zamuje gidan Mukhtar ka gane wa idan ka. Da fadar haka ta bace Battt!.~
_Washe gari da safe bayan su Umar sunyi wanka ya sayo musu abun kari sun karya ya sun zauna suna hira sai gani sukayi Wata yar farar Yarinya ta bayyana a gaban su tana kallan su tana murmushi. Tsorata sukayi dan Umar har zai tashi ya ruga. Yarinyar tace "Nice fa Safuratu *ALJANAR FATIMA".* sai ta yaji haka tukun ya dawo ya zauna suna wa junan su dariya shi da Rafy na tsorata da sukayi. Rafy tace "Kai dai Wallahi raggo ne kamar ba namiji ba. Ace mace ma ta fika rashin tsoro". Umar yayi dariya yace "Ah! Ke kuwa ai da gaskiya ta wa zai tsaya kallan ruwa kwado ya mai kafa". Hhhhh Rafy tayi dariya tace "Ai duk Safurat ta bani labarin ka har da kokowa wajen mai shayi nayi dariya sosai. Ga kuma Sarkin bori mai cire Aljanu". Gaba daya suka kwashe da dariya. Nan dai suka gaisa da Safuratu da take a sufar Yarinya. Tace "To dan Allah Umar ko kai fa. Yanzu zaman a haka ba yafi dadi ba?. Kuna hirq da matar ka kuna dariya. Amma da in ka shigo sai ka wani bata fuska kamar wanda aka kai gaban sarki bai karya ba aka mai bulala dari". Dan murmushi Umar yayi hade da sosai keya yace "In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba. Wancan karon ma sharrin Mukhtar ne". Safuratu tace "Yauwa haka ake so. Amma fa akwai mazan da suke haka wanda a waje_
_Zakaga suna ta bude baki suna wangale hakora kamar wanda aka wa alkawarin Hajji bana. Haka in suna hira suta zuba sai kace Anyiwa waziri aku gorin labari. Amma da zarar sun zo gida shikenan sai kaga sun daure fuska maganar ma sai kaga dakyar suke wa matan kamar wanda aka makure akace suyi dole. Kai wani fa hirar arziki ma bata hada shi da matar shi, balle wasa da Dariya. Wani abu kadan da matar shi tayi masa sai hantara in bata ci sa'a ba harda duka. Kamar dogari a fadar sarki haka suke wa matan da kinyi kuskure kadan. Haba wai su me yasa basa fahimta ne aure fa ana yinshi ne dan cika Umar nin ma'aiki sannan ba'a ce ka auri wacce baka so ba. Wai wasu kamar dai kai yanda ka zaunu a shawarar Mukhtar. Wai suna yin duk hakan ne dan kar matan su raina su. Haba muma matan muna da hankali fa shikenan dan ina wasa da mijina sai in raina shi a kan me?. Raf'iat ko kina ganin zaki iya raina Umar dan wasan da kuke yi". Safuratu ta mayar da kallan ta zuwa ga Rafy shima Umar haka. Rafy tace "Haba-haba ko da wasa Wallahi bazan rainashi ba. Duk abunda kuwa zan mishi cikin wasa ne irin na masoya domin ni tun a waje lokacin ina budurwa na tsara zamana a gidan miji kamar yanda ko wacce mace take tsara nata. Tsarina zan Girmamashi zan kuma maida shi abokin wasa na duk da kuwa nasan cewa shugaba na ne. Amma a nawa tunanin wasa tsakanin ma'aurata na kara dankon soyayya a tsakani. Amma fa ba mugun wasa ba wasa dai irin na masoya. Kamar yanda Addini ya Halarta mana._
_Sannan wasan yana taka muhimmiyar rawa ta bangaren Fushi. Wani abun idan nayi mishi daga naga alamun yayi fushi sai in mayar da abun wasa. Haka wani lokacin ko mun fara cacar baki mun fara fada sanadin wasa da muka sabayi sai kiga abun ya juye ya koma wasa. To ni dai gaskiya bana tunanin zan wasan da muke zaisa in raina shi ko da yaushe zan bawa mijina girmanshi in lokacin wasa ne ayi. In kuwa ba lokacinshi bane a bari". Raf! Raf! Raf! Safuratu ta fara tabi tana kallan Rafy tana murmushi. Shima Umar tafa mata yake. Safuratu tace "gaskiya kin burge ni kuma ni banga kuskure a maganar ki ba. Umar bari muje gidan Mukhtar yau zaka sha mamaki. Karbi wannan abun ka hadiye". Hani farin abu kamar magani ne ta mika masa ba gardama ya karba ya afa baki. Yana hadiyewa ya bace wa Rafy bata ganin shi. A rude ta mike "Innalillahi, Ina Umar din". Umar yana zaune agun yana kallanta amma ita bata ganin shi. Umar da baima san ya bace ba'a ganin shi ba ya kalli Rafy da duk ta rude tana cewa Safuratu ina yake. "Rafy miye haka gani nan a gaban ki ki ringa cewa wai ina nake". Rafy kam bata ji maganar shi ba._
_Dariya Safuratu tayi Ta kalli Umar tace "Ai yanzu ba wanda zai ganka kuma ba wanda zaiji maganar ka daga Allah sai ni. Yanzu haka ka bace Rafy bata ganin ka. Maganar da kayi yanzu ma bata ji ba". Mamaki ne ya kama Umar. Safuratu tace wa Rafy "Ke ma kwantar da hankalin ki ga Umar dinki nan ba sace shi nayi ba. Yanzu zamu tafi gidan Mukhtar ne da shi to har ciki zamu shiga dan haka bazasu gan mu ba. Mun tafi sai mun dawo". Da fadar haka sai suka bace ita da Umar din sai gasu sun bayyana a gidan Mukhtar. Da bullowar su suka ji Murja a daki sai masifa take surfawa Umar hakan yasa Rafy tace su karasa cikin daki. Umar kam duk a tsorace yake dan gani yake kamar Mukhtar zai ganshi. Sai da suka suka shiga dakin ya tabbatar da cewa ba'a ganin shi Nan sukayi tsatsaye suna kallan su Mukhtar din. Mukhtar ne zaune gefan gado Murja matar shi a gefan shi ta rike kugu cikin daga murya da kakatu tace "Kai malam tun dazun magana nake maka amma kayi shiru kamar ina magana da dutse. Kasan dai cewa gidan nan ko kwayar hatsi bama da shi balle kace ayi dan banzan kokon nan da ka saba cewa ayi a karya da shi._
_Dan Wallahi yau bazan karya da koko ba. Duk kayana na saide-saide mun cinye su baka bani kudina ba. Gashi yanzu ina so inje kasuwa inyo sari amma ba kudi a hannuna duk suna gunka. Dan haka tattaro min gaba daya kudina rankatakaf! Ka bani in yaso karka bada kudin Abin karyawa din ma". Duk masifar da take yi Mukhtar yayi shiru bai ce kala ba. Sai yanzu ne ya dago cikin sanyin murya yace "Haba Murja ni fa mijin ki ne ko kin manta ni shugaba ne a gare ki kike daga mun murya haka. Wallahi kiji tsoran Allah Murja". Ya nuna ta da yatsa. Makr yatsar tayi da hannu ta rike baki "Iyeeeh daga bani kudina sai wa'azi?. To Allahu akbar amma fa in kana so wa'azin da kake ya dinga shiga kunnena to a bani kudina". Mukhtar tsabar jin haushi kamar wanda zaiyi kuka yace "Murja ni kike bigewa hannu?". A hatsale tace "Au! Tambaya kake kenan, Baka ma yarda da hakan ya faru ba kenan". Bai bata amsa ba ya tashi da niyar ya fita waje. Ya fara tafiya kenan ta shaki wuyanshi ta baya ta wani jayoshi. "Malam ba inda zaka, Wallahi sai ka biyani kudina". Nan fa Umar ya saki baki yana kallan Muktar a zuciya yana jin haushi abunda ya sashi yayi wa Rafy. Mukhtar da aka shake ma wuya ta baya. Dakyar ya samu ya markayi hannunsa baya ya kwace cikin fushi yace "Cewa nayi bazan baki kudin ki bane?. Inace dai sai naje na samo tukun zan baki?"._
_Murja tace "Kaga malam ni yanzu nake san kudina domin kaji wani yaro can ma yana a bashi mai. Amma babu duk ka cinye min kudi a bashi. Yanzu fa dubu biyar nake binka". Muktar yace "Naji yanzu sakar min riga Yau yau zan biya ki kudin ki in dai huta da jaraba da masifa". Zazaro ido tayi Cikin daga murya tace "Ni kaks cewa masifafiya?. Ni kake cewa jarababiya ko Mukhtar?". "Ni fa ba dake nake ba". Sakar mishi riga tayi hade da cewa. "Jeka ga hanya nan. Kuma Wallahi tallahi yau in baka kawo min kudina ba zaka ga jaraba da masifa da kake fa. Badai ni kake cewa masifafiya ba. Hmm". Mukhtar bai sake magana ba waje kawo yayo. Zuciyar sa sai kuna take._
_Yana fitowa su Safuratu suma suka biyo shi baya. Umar ya girgiza kai yace "Kai amma gaskiya ba karamin rashin hankali nayi ba. Wai ashe haka matar Mukhtar take mishi amma shine har da bani shawara wai kar matata ta rainani. To dan Allah wane raini yafi wannan?. Kai gaskiyar masu iy magana da sukace (RASHIN SANI *YAFI DARE DUHU*). Wallahi zanso inga ya zasu karata in bai biya ta kudinta ba". Safuratu tace "ka dai gani da idanka. Idan kana so kuma ni zan iya hana shi kawo kudin". Uamr yace "Tayaya zaki hanashi". Gaba ta shiga ta fara tafiya. "Muje kaga ta yanda zan hanashi ya kawo kudin". Baya suka bi Umar har wajen ogan su inda yake karbo napepk din. Nan fa Safuratu ta juya zuwa wata jabebiyar mata. Ta shiga yar kurkurar ta zauna gaba daya ta cika kurkurar in aka cire inda umar zai zauna baza'a samu wajen zaman wani ba. tace wa Umar ya shigo. Baiyi gardama ba ya shiga. "To kaga yau a nan zamu ta yawo ba wanda zaima tsayar da shi in yaga mutane a ciki". Umar ya girgiza kai shi dan a tsorace yake. Dan girman matar yayi over. Mukhtar zuwa yayi ya dan kakabe kurar yar kurkurar ya hau ba tare da yasan Su Umar na ciki ba. Haka yata zuba gudu yana bi lungu da sako ko mace daya bata tsayar da shi ba. Tun abun bai damunsa har ya fara damunshi. Domin yaga abun ba kamar yanda ya saba ba._
_Haka ya ringa wuce mutane wanda kuma ya tabbata Napepk suke jira amma da sun ganshin suka hangi Safuratu sai suki tsaida shi. Abun har ta fara bashi haushi ya fara zage-zage. Wasu yan mata ya hanga su biyu sun ci kwaliyya abun su sai kallan hagun da dama na titi suke. Alamu sun nuna cewa abun hawa suke jira. Muktar ya kalle su yace. "Matsala ta da mutane kenan wasu yan rainin wayo ne Wallahi. Yanzu wadancan fa da gani Napepk suke jira amma ina zuwa sai kaga sun ki tsayar dani. Amma bari mu gani". Ta gaban su yaje ya wuce ganin wannan katuwar mata yasa basu tsayar da shi ba. Muktar har yayi gaba kuma cike da takaici yayo baya. Diiiiiit! Ya musu hon hade da cewa "Tafiya ne?". Dayar tace "Eh tafiya ne ya akayi?". Yace ok to ku shiga mujr mana ina za'a kai ku?". Yar siririyar cike da masifa tace "Malam bamasan rainin wayo ya Napepk dinka cike kuma zaka zo kana cewa wai mu hau. To nan ina xamu hau?. Ko kan wanna tikekiyar matar mai kama da giwa zamu hau?". Tana fadar haka suka kwashe da dariya ita da kawqr ta. Safuratu kuwa dajin abunda suka fada sai ya bata mata rai. Kanta ya juye ya koma na giwa. Yan matan nan na ganin kan mata ya koma giwa. Yar karamar ta banke Mai dan jikin ta fadi itana ta wuntsila tsukakun kayan jikin su Bai hana su zabgawa a guje ba. Dan ko tsayawa tata re sket ba wucce tayi. Takalman su kuwa tuni kowacce a ciki ta yi wulli da nata dan tafiya da su bata lokaci ne. Wani gida suka shige a million suka fada daki. Matar gidan na gani haka ta bisu daki itama a guje ta turo kyaure._
_Mukhtar sakin baki yayi yana kallansu. "To su kuma wannan me suke nufi?. Ko dai maciji suka gani a ciki". Juyawa yayi baya ya leka har karkashin kujerar baiga ko kiyashi ba. Bai aminta ba. Ya fito sai da ya zagaye Napepk din ya duduba baiga ko mai ba. Yaja tsaki ya hau Napepk dinshi yayi gaba............................. ... .........._
😰😰😰
TASHIN HANKALI
😰😰😰
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 81-82
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻
GIDAN MARAYU
🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻🙎🏻
_Story&written by✍🏻
Beauty Queen💋💋
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION
*INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIN RAJUN*
KULLUNAFSIN ZA'IKATUL MAUT.
*UMMU RUMMA,* WACCE KUKA FI SANI DA *BEAUTY QUEEN* ALLAH YAYI WA YAYANTA MAI SUNA *ABDURRAHMAN* RASUWA. MUNA ROKON ADDU'A DAGA GARE KU ALLAH YA JIKAN SHI YA MAI RAHAMA. ALLAH YASA ALJANNA CE MAKOMARSA AMIN. SU KUMA ALLAH YA BASU HAKURI DA JURIYAR RASHIN SHI.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Juyawa yayi baya ya leka har karkashin kujerar baiga ko kiyashi ba. Bai aminta ba. Ya fito sai da ya zagaye Napepk din ya duduba baiga ko mai ba. Yaja tsaki ya hau Napepk dinshi yayi gaba.~
_*H*aka yaci gaba da zaga gari amma shiru. Wata mata ce ta tsayar da shi har ya tsaya kuma sai taga su Safuratu tace, "Sannu ko baiwar Allah ai ban ganku ba". Safuratu tace "yauwa sannun ki dai". Mukhtar yace "Yauwa hajiya shiga muje ina za'a kaiki?". Matar a fadace tace "Kan cinyar ka kake so na hau ko ina?. Amma kai dan rainin wayo ne ma wallahi kasan napepk dinka ta cika shine ma har ka tsaya". Muktar juyawa yayi set din baya shi dai ko kwaro bai gani ba. "Kinga malama ba rainin hankali nace kiyi min ba. Kinga mutum ne a ciki da zakice wai a ciki take. Kinga dallah malama ware kama gabanki tunda ba hawa zakiyi ba". Jan Napepk dinshi yayi cike da haushi. Can wani tunanin ya fado mai. Wanda yasa ya juya kan napepk din ya nufi gida. Da isar sa ya sauka ya shiga ciki. Su Umar suka saukko suka bishi. Murja na ganin shi ta haushi da masifa wai ya cika lalaci tun yanzu har ya dawo. Nan yace ta saurare shi dakyar ya samu ta dakata da masifar. Nan ya fada mata cewa tunda ya fita gashi har larfe sha biyu ta kusa amma ko mutum daya baiyi ba. Nan fa ta sake rikicewa wai wannan karyar banza ce yake fada. Ai ba yanda za'ayi yace wai har yanzu bai kama ko biyar ba. Tace "Wannan ai salon munafirci ne. Wato so dai kake ka hanani kudina to wallahi baka isa ba. Tashi ka koma"._
_Mukhtar yayi ajiyar zuciya yace, "Ni fa kinji matsala ta dake kenan. Ke gaba daya baki sasauta mun, Ji yanda kike masifa dan Allah kamar ba da mijin ki kike magana ba. To ni dama ba wani abu ya kawo ni ba. Kamar yanda naji ance idan mutum basuyi rabuwar arziki da matar shi ba idan ya fita kasuwa bata mishi dadi. Shiyasa na dawo domin mu fahimci juna amma kin wani hau masifa". Murja na jijiga kamar wacce aka kunna tace."To wace irin fahimta kuma?. Ai ni in ba kudina ka kawo min ba ba wani zancen fahimta dan ma kaji. Ni in ba Dumus! Naji ba da matsala". Takaici ne ya cika Mukhtar yayi waje ba tare da yace mata uffan! Ba. napepk ya dawo ya shiga yana surutai. "Wai matan yanzu me yasa basu da lura ne. Haba mutum yaje yata fama wani idan yaje neman abincin ma har duka yake shi, Amma daga karshe in ka dawo gidan baza'a kwantar ma da hankali ba. Ji wannan matar wai na dawo mata da laluma amma ta wani dau zafi. Da ace zan samu mata kamar Rafy matar Umar ai Wallahi da yau-yau zan bata takarda". Baki Umar ya rike jin abunda Mukhtar din ya fada. Nan take tsanar sa ta karu a zuciyar sa dan ji yake kamar ya buge sa._
_Mukhtar ya koma ya hau napepk din ya sake dannawa cikin garin. Har wajen karfe daya yana yawo amma ko an tsayar da shi ma sai ace taje abun duniya ya isheshi nan ya sama wata inuwa ya faka hade da cewa "Yin barci na ma yafi mini da inta kone maina a banza. Nan ya fiddo abun sallah ya shimfida ya dan ringesa. Yana ta masifa shi kadai. Bai dade da kwantawar ba barci yayi gaba da shi. Su Safuratu kuwa suna cikin. Wasu gayu ne guda biyu dagani kasan yan shaye-shaye ne. Gudaya ya kalle guda yace "Baabah yau fa nake gaya ma dawa tayi nama. Kalli can". Ya nuna mishi Mukhtar dake kwance yana barci. Dayan yace "Kambuh! Laili yau Allah ya kai damo ga harawa. Kaga zagaya ta can ka dubo mana key nasan yana jikin shi". Wanda ake kira da Muhsan yaje jikin Mukhtar ya fara dube-dube ko zaiga makulle. Can ya hange shi a Karkashin kan Mukhtar a hankali ya zare shi. Ba tare da Mukhtar ya farka ba. Safuratu tace Umar ya sauka ya jire Mukhtar ita zata bi barayin. Da sauri ya sauka. Su kam barayin basa ganin su Umar. Yana ciro makullin ya mikawq abokin nasa wanda shi tuni har ya dare napepk din. Ai kuwa ya tayar yaja ta a guje.
Duk abun da ake Mukhtar ko motsawa baiyi ba. Barci yayi dadi. Da gudun yake jan yar kur-kurar sai da yayi tafiya mai nisa dan har ya fara fit daga garin tukun ya ratse ya sauka daga titi yabi wani jan birji nan ma sai da yayi nisa sosai ya kara kutsa ta cikin daji. Sai da ya shiga cikin wasu bishiyoyi tukun ya tsaya. Kallan juna sukayi kamar hadin baki kuma suka kwashe da dariya. "Kai baabah lalai yau dawa tayi nama yanzu ya kake gani zamuyi?". Dan siririn ya tambaya wanda ya jawo kurkurar. "Ai nake gaya ma abun duk bige ne bari zamuyi kawai dare yayi sai muyi wuf! Mu shiga da ita gari mu shigar da ita". Dan siririn mai suna Rafson yace kai mutumina nake gaya maka in dai muka shigar da wannan. Kaga na daya Zan sayi kwalin sigari giya wiwi Kai Wallahi har koken sai na saya". Muhisan yace "kaji banza gara Kai duk a yan bushe-bushe kawai zaka kare. Ai ni nake gaya ma zuwa zanyi gidan magajiya wuuuuyyif! (Yayi fito) ta dorani a hanya ka dai gane". Ya daga mishi gira. Safuratu kallansu kawai take suna hirar rashin hankali. A zuciya tace yanzu su wannan shikenan fa sun bata rayuwar su da shaye-shaye ga abun har ya kai ga sata. Yanzu haka kuma in ka bincika rashin aikin yi ne ya jefa su".
Sai wajen karfe uku Mukhtar ya farka. A gigice ya tashi ganin ba kekenapepk dinsa............................._
*Ayi Hakuri dan tsito ne*
😳😂😂
Su malam Rafson fa an dauko babban kaya lalai yau dawa tayi nama. Dan kura da kallabin kitse😆
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 83-84
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
😍 DEDICATED TO YOU 👇🏼👇🏼😍
✍🏻 SALMA QUEEN ✍🏻
✍🏻 ZUWAIRA MADARA ✍🏻
✍🏻 ACTION BABY ✍🏻
✍🏻 BEAUTY QUEEN ✍🏻
✍🏻 FATIMA(UMMU BASHIR) ✍🏻
✍🏻 AUNTY MAIMUNA ✍🏻
✍🏻 RABI'AT SHU'AIBU ✍🏻
✍🏻MMN NAJWA✍🏻
☺ NA ROKI ALLAH YA KARA MUKU BASIRA ALLAH YA TSARE MIN KU. ALLAH YA KARA FIKIRA DA FASAHA☺
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~A zuciya tace yanzu su wannan shikenan fa sun bata rayuwar su da shaye-shaye ga abun har ya kai ga sata. Yanzu haka kuma in ka bincika rashin aikin yi ne ya jefa su". Sai wajen karfe uku Mukhtar ya farka. A gigice ya tashi ganin ba kekenapepk dinsa.~
_*G*aba daya a gigice ya tashi nan fa ya dora hannu kamar ya fasa ihu! Waige-waige kawai yake yana rasa abun yi. "Anan fa. A nan nayi parking". Juyawa yayi wajen wani mutum dake taho wa. A rikice ya taryi gabansa "Malam dan Allah baka ga wanda ya daukar min napep ba?". "Ban gani ba wallahi". Cewar mutumin da Mukhtar din ya tambaya. Durkushewa Muktar yayi ya kama kafar mutumin."Dan Allah dan annabi in kaga wanda ya dauka ka taimaka ka gaya min please wallahi ba tawa bace sojan haya na daukko". Mamaki ne ya kama shi. "Kai bawan Allah wai napepk waya ce ko wani karamin abu da za'a sata ba tare da ka gani ba?. Abun naka rainin wayo ne ma". Yana fadar haka ya fizge kafarsa yayi gaba. Mukhtar haka ya ci gaba da taryar mutane yana tambaya amma kowa cewa yake bai gani ba. Duk abunda yake Umar na kallan shi. Amma shi baya ganin Umar din. Mukhtar kamar yayi hauka duk mutumin da ya gani yaro ko babba mace ko namiji sai ya tambaya. Da dai yaga abun bayayi sai kawai ya sama waje ya dora hannuwa a kai ya fashe da kuka. Cikin kuka yake cewa."Yanzu ya zance wa Bash da wanne idanu zan kalle shi ince an satace Napep dinshi tama za'ayi ya yarda". Kara fashewa yayi da kuka. Umar ya tausaya mishi sosai a nan gurin duk da yasa Napep din bazata salwanta ba. Mukhtar nan ya zauna sai kuka yake yana tunani ya saka wannan ya kunce ya saka wannan. Har yamma tayi magariba ta kawo kai suna wajen. Can dai Mukhtar ya mike ya nufi gidan yana tafe yana yan surutai yana zubda hawaye kamar wanda akawa mutuwa. A haka har ya karasa gida sallama ciki-ciki ba'a ko ji yayi. Murja na daki batama ji sallamar sa ba. Waje ya samu ya zauna yayi tagumi. Shi kam tunanin ya zaicewa Bash. (Mai napepk) din yake. Nan fa ya fara zance har yana fitowa. "Yanzu Inje incewa bash duk yau ban yi ko sisi ba kuma ina barci an sace Napep din. Kash! Sam! Bazai yarda ba wallahi"._
_Murja ce ta fito daga daki tana yan wake-wake, Tana ganin Mukhtar tace. "Au! Malam dan karka bani kudina shine kazo ka wani zauna a waje?". Karasawa tayi gaban shi tana zuwa ta wani gyara dan kwali daurin (Ture kaga tsiya) ta rike kugu da hannu daya. Dayan kuwa ta mika wa Mukhtar hade da kauce kanta ga barin kallansa. Alamar ba mutunci. "Malam bani kudina bana san wani waye ya mutu waye ya tashi. Dan Wallahi duk wani plant dinka na gama gane shi". Cike da takaici Mukhtar ya kalle ta a zuciya yace " Wai wannan mata ta ce. Bata ma lura da irin halin da nake ciki ba". Hawaye ne suka gangaro mai a fuska. Murja ganin taji shiru yasa ta kalle tana ganin hawaye a fuskar shi cikin kwaratsi tace. "Dole ka zubda hawaye. Wai ance Saurayin budurwarka ya mutu. Kukan munafurci kenan ma to wallahi baka isa ba malam. Yau naga sadodo wai harda kirkirar hawaye, Eh lalai Malam Mukhtar zaka iya film daga bani kudina sai hawaye to a nufin ka. In durkusa gabanka ina share ma hawayen ina baka hakuri ince kabar kudin ko yaya?. To Wallahi bari kaji yau in baka bani kudina ba bar ganin dare yayi wallahi sai na dauki wani abu naka wanda yayi kudina na sayar na dauki kudina". Mukhtar magana kasa-kasa yace "Haba murja me yasa kike haka ne. Baki san damuwar mutum ba kizo ki kara mai wata damuwa. Ko so kikr hawan jini ya kamani ne in fadi in mutu". "Wannan kuma kai ta shafa. Ni kudina kawai nake bukata in baka bani ba kuma kaga tashin hankali harda rufu'a Wallahi". Muktar yace "Murja An sace napep din da na daukko sojan haya". Murja ta dan sasauta murya kamar abun kirki. "Kaico! Napepk din aka sace ashe ai ni baka gaya min ba tun da wuri in maka jaje. Allah yasa a ganta ya tsare gaba. In ba'a ganta ba Allah yasa mai ita ya maka afuwa". Mukhtar yace "Amin yanzu abun..". Kafin ya karasa ta taryi nunfashin sa. "To an sace napep nayi maka Jaje kumaa gode wa Allah da ba kudina ne a ka sace ba. Da danaji kana zancen sacewa har gabana ya fara dukan uku-uku na dauka kudina aka sace. Tunda basu ne ba Alhmdulilah. bani kudina in adana kar suma garin sakaci irin naka kaje a sace. Atoh! Wanda ya bari aka sace napep ai kudi bazasuyi wahalar sata a gunsa ba. Bani kudina malam"._
_Maganar tayi mugun bata wa Mukhtar rai ji yake kamar ya tashi ya hauta da duka. Matsalar daya yasan ba abunda zai dauka a jikinta. In ma fadan ne bata kashi za'ayi. (Ragas).A zuciyarsa yake tunani cike da tsanar murja "Wannan wai wace irin mata ce. Anya kuwa Murja ba shedaniya ce ba. Kai ai ko shedan ne ke bina kudi na gaya mishi abunda ya faru ya daga min kafa...". Shirun da taji yayi yana tunani ta wani daka mishi tsawa. "Kai malam ka bani kudina wallahi tun muna sheda juna". Nan ma shiru yayi dan yama rasa abunda zaice mata. Kukan kura tayi ta chakumi wuyan rigar sa. Ta fara magana dan masifar kamar mai shirin yin kuka gashi da karfi take maganar. "Mukhtar yau fa ba mutun ci Wallahi sai ka biyani kudina. A take a nan ko kuwa yanzu in maka lahani Wallahi". Mukhtar kokarin kwacewa yake daga shakar da tayi mishi amma ya gaza. Murya a makure yace. "Sakarni ni yanzu ba ko kwandala a jikina in na saaamu zaaan baaki". Maimakon ta sake shi sai ma ta kara shakar shi. Nan shima ya fara kokarin shake nata wuyan jin tana kokarin ta kar shi. Amma ina ya shaketan amma a banza. Ihu! Ya fara kugawa. Wani makwabcin su ne ya shigo sa gudu yazo yaga abunda ke faruwa dakyar ya kankare mukhar a hannun Murja. Nan ya tambayi murja me ke faruwa ta gaya mishi. Tambayarta yayi nawa ne kudin tace dubu biyar. Da sauri Mukhtar yace karya take hudu da dari biyar ne. Ibrahim ya zaro Dubu biyar ya mika mata. Yana bata Mukhar yace "An biya ki kudin ki to na sake ki saki daya. Zama dake ai bala'i ne". Murja cikin nuna rashin damuwa ta wani jujuya kudin dake hannunta tayi guda yiiiriiyirri. "To dan ka sake ni sai me. Kai ne a kasa wallahi domin nice rufin asirin ka kuma dan kaji in gaya ma saki daya ba inda zani. In ka cika dan halak ka karashe biyun". Mukhtar har ya daga baki da sauri Ibrahim ya rufe mishi baki da hannun yaja shi waje. Nan suka bar Murja nata masifa. Duk abunda ya faru Umar na gani sai dai bashi da ikon rabawa ko magana domin yana cikin plan din Aljana._
********************
_Lokacu misalin karfe takwas na dare ne amma shiru kake jin dajin in ba kukan tsuntsaye ba shima ba sosai ba. Kasancewar ba farin wata rudum! Wajen yake duhu in kana tsaye bazaka ga abunda ke kasa ba. Muhisan da rafson ne jingine da yar kurkurar ba abunda suke sai busa sugari. Can kuma Rafson ya kalli Muhisan yace "mu tafi yanzu mana". Muhisan yac "Kai mahaukaci ne naga alama. Yanzu fa dare baiyi ba bar ganin duhun nan sauyin yanayi ne yanzu haka ko tara batayi ba". Shiru Rafson bayi magana ba. Daga cikin Napep din Aka zuro hannu aka dan ja kunnen Muhisan. A fusace ya juya ga Rafson yana mishi jaraba wai ya daina kama mishi kunne. Shi kuwa yace baima san anyi ba. Kafar Rafson yaji anja daga kasar napepk din da sauri ya janye kafar hade da cewa "Baabah akwai matsala fa. Kafata naji ana ja daga karkashin nan". Muhisan yace "Kai dallah can rufe muna baki to me kake nu..". Kafin ya rufe bakin yaji anja tashi kafa"Kuturun uba! Bari inga uban miye ke ja min kafa". Durkusawa yayi da nufin lekawa Wani abun kulli aka mai a duron baya wanda ya bada sauti Dum!. "Kai! Kai! Yau banga mai hanani inci kut... Ubanka ba a jejin nan. Me nayi ma da zaka min dundu"?. Muhisan ne ke fadar haka yana dagowa ya wanka wa Rafson mari shima kuwa ya rama nan fa suka hau kunce. Shuuuuuuuuuu! Sukaji wata irin kara mai karfi ta nufo gunsu. Tsayawa sukayi da kuncen suka fara waige-waige_
_Ji sukayi an watso musu wani abu kamar ruwa. "Kai waye ke watso mana ruwa?". Suka fada cikin hadin baki. Muhisan yaji abun da dan danko hakan yasa ya fiddo leta ya danna. "Jinine yaseen". Abunda ya furta kenan. Da sauri Rafson ya matso kusa. Yana ganin jinin sai suka hau dube-dube wata kururuwa sukaji marar dadin ji a bayan su da sauri suka waiga gefan. Wani katan abune ga dukan alamu baki ne. Idanunsa kawai suke hangowa masu kamar singnonin mashin abun ya durfafo su yana wani irin gunji. Da gudu suka fada napepk nan fa sukayi sukayi ta tashi amma taki. Ga abun na kara kusantowa karar shinna cika musu kunne. Da dai sukaga bazata tashi ba sai gaba daya suka fita suka runtuma a guje._
_Gudu suke sosai a birjin hasken da suka ga ya nufo su a baya yasa su juyawa. Napep din ce ta nufo su ba kowa a ciki. Da ganin haka suka kara kaimi wajen gudu. Basu ankara ba sai gani wannan Bakin Aljanin ya duro a gaban su kamar an cillo shi yana musu wata iriyar dariya mai karfi ga rashin dadin ji a kunne. Wata uwar turjiya suka ja gaba dayan su sai da suka fadi domin tsayuwa ce bata san rai ba. Sunyi yunkurin tashi kenan sai ganin wanna aljani sukayi a gaban su. Abunda ya kara tsoratu su kenan. Cikin murya marar dadin ji yace. "Kuje ku shiga mu tafi". Tashi sukayi suka shiga napepk din jiki na karkarwa. Ba tare da sunga mai tukin ba sukaji anja napep din a guje. Ihu! Suka fara yayin da wata murya ta mace tace "Kuyi mun shiru barayin banza". Shiru sukayi haka napep tata shara gudu har suka kusan isowa gari inda suka tarar da wani gate na yan sanda masu binciken motoci a hanya. Haka suka bi layi ana ta bincike ana zuwa kansu dan sandan yaji ance. "Barayi ne na kawo muku ku hukunta su". Dan sanda ya bata rai hade da cewa su Rafson kai ku fito dan ubanki. Fitowa sukayi ya ja su har wajen ogansu dake can zaune kan benci. "Yallabai ga wasu yan iska nan. Wai mu suke cewa su barayi ne. Wasa suke da hankalin police sir!". Ogan harara ya gallawa su Rafson yace "yan iska dama daga ganin ku yam shaye-shaye ne dan...". "Nice nan na kawo chu bachu chuka kawo kanchu ba". Wata yar Yarinya ce wacce bazata wuce shekara 4 ba ta bayyana a gaban su sanye da bakaken kaya idadun ta manya sun wuce kima. Gata baka. Ai kafin ta rufe baki tuni Ogan yan sanda ya wuntsila daga kan bencin yayi kundunbala ya tashi ya zabga a guje haka suma duk sauran yaran shi da su Rafson kowa ya kama gabansa........................................._
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 85-86
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
😍 DEDICATED TO YOU 👇🏼👇🏼😍
My Dear 💦💧 *Queen Hauwa Haucy* 💧💦
💃🏻 Na yabba da kaunarki gare ni. Bansan da wanne irin kalamai zanyi amfani wajen yaba miki da godiya a gare ki. 🚶🏻
Sai dai ince Allah ya barmu tare Allah kara basira da daukaka na gode matuka da irin Kaunar da kika nuna min. ☺
*A PAGEN DA YA GABATA CIKIN LITTAFIN ALJANAR FATIMA. LOLZ* 😜
~Wata yar Yarinya ce wacce bazata wuce shekara 4 ba ta bayyana a gaban su sanye da bakaken kaya idadun ta manya sun wuce kima. Gata baka. Ai kafin ta rufe baki tuni Ogan yan sanda ya wuntsila daga kan bencin yayi kundunbala ya tashi ya zabga a guje haka suma duk sauran yaran shi da su Rafson kowa ya kama gabansa.~
_*M*ukhtar da Ibrahim suna fitowa Ibrahim ya bada shawarar suje police. Haka suka dunguma suka nufi police din suna cikin tafiya kawai Mukhtar ya hange napepk dinshi anyi parking dinta a gefan tati. Da ganin haka ya ruga da gudu cike da zubudi yaje yana lalekawa yana fadar "Wallahi itace"2×. Umar Safuratu ya ga ta leko daga cikin napep din tace ya shiga. Dajin haka yaje ya shige napepk din. Mukhtar sai murna yake ya shiga gidan baya yana duduba wani abu sai ji yayi anja adai-daitar a guje. Nan ya fara kwalla ihu yana neman agaji. Ba abunda ya kara tsorata shi sai ganin ba driver napep din ita kadai kejan kanta. Ibrahim yayi kokarin ya sama abun hawa ya bisu amma ina. Lokacin da ya samu ya tsayar da wani mashin su tuni har sun bace mai baima san inda sukayi ba. Safuratu bata tsaya da napep din ba sai a kofar gidan Umar da isar su ta sauya zuwa yarinya. Ta kuma bawa Umar wata koya tsanwa yana sha sai gashi ya bayyana. Mukhtar tsoro ne ya kamashi dan ya gane Aljanar gidan Umar ce. Safuratu tace mishi ya fito su shiga daga ciki nan fa ya fara kakafe wa. Umar yayi iya bakin kokarin shi amma Mukhtar yaki yarda ya shiga gida. Abun ne ya bawa Safuratu haushi. Da hannu ta nunashi sai ji yayi an daga shi sama ana nufar kofar gida da shi. Nan fa ya fara ihu yana bada hakuri. Safuratu tace ba komai zasuyi mishi ba amma yaki yin shiru. Daga dayan hannun ta wata wulfefiyar wuka ta fito taje ta tsaya saitin makogwaran Mukhtar Safuratu tace "kayi min shiru ko in umarci wakar nan ta cire ma kai". Shiru yayi ko uffan bai kara cewa ba har suka shiga gidan. Ba nefa gida duk duhu ne Safuratu ta kalle kwan nepar sai wani haske ya fito daga idanun ta ya shige shi nan take gidan yayi hask fayau!._
_Nan suka zaunar da Mukhtar Rafy kam tuni ta gaji da jira har tayi barci. Safuratu tace "Zanyi ma wasu tambayoyi. Amma kasan da sani in ka min karya zan gano ka dan haka gwara ka taimaki kanka a fadan gaskiya". Mukhtar bakin shi na rawa yace "To, To zan fada miki gaskiya". Safuratu ta kalle shi ta nuna Umar "Miyasa ka bawa Umar abokinka shawarwari na banza. Wanda kasan kai ba haka kake wa matar ka ba?". Mukhtar yayi jim! Kadan tukun ya nunfasa yace. "Hakikanin gaskiya na bawa Umar shawarwari na banza ne domin tun muna yara mu abokai ne kuma na riga shi yin aure sai kuma naga ya fini jin dadin auren wannan yasa na kirkiri hanyar da zata dakushe jin dadin nashi shima ya dawo kamar ni. Amma daga karshe nayi nadama". "Karya kake mugu azzalumi macuci'. Umar ya taso mai da fada da niyar ya shake shi. Safuratu ta miko hannunta ya zama xankalele ya shiga tsakanin su. Can Umar ya koma yana hararen Mukhtar yana huci._
_Safuratu ta kalle Umar "Haba kai da nake ganin ka mai hankali shin bakaji abunda Mukhtar din yace bane?. Kai yanzu bazaka tausaya mishi ba. Kalle fuskar shi ka kalle cikin idanunshi kaga cike yake da nadama da tarin dana sani. Umar na kawo shi nan ne dan in muku sasanci ba fada ba dan haka ka saurare mu kawai in bance kayi magana ba karka kara saka baki". Umar jikin shi yayi sanyi da jin haka. Safuratu ta kalli Mukhtar taci gaba da magana, "Mukhtar amma kai miyasa ka auri mata kallar wannan?. Shin auren soyayya ne ko hadi ne". Mukhtar yace "Auren soyayya mukayi da murja sai dai tun tana budurwa ake fada min irin mugayen halayanta. Amma nake kauda kai wasu abokan nawa har rikici muke in suka aibata ta a gabana. Ni a ganina duk rashin kyan halinta ai ni bazata min ba tunda ni mijinta ne. Sai da na aure ta tukun na karyata kai na. Domin kuwa abubuwan da murja take sam basuyi kama da na mai neman gidan aljanna ba ita fa duniya kawai ta saka gaba. Kullum zancen ta kudi-kudi lokacin da mukayi aure idan na bata kudin cefane sai ta murkushe rabi. Idan na auno shinkafa ko Masara sai ta kwashi san ranta taje ta sayar daga nayi magana sai tayi fushi tace wai zarginta nake yi. Da dai naga abun yayi yawa lokacin inada dan arziki na sai na hada yan kudade kusan dubu dari da goma ne. Na bata nace taja jari ni a gani na ai rufin asirin ta nawa ne kuma rufin asirina nata ne._
_Taja jari kuma sana'ar ta karbe ta tana sayar da fulawa. Man kwanti. Shinkafa. Da dai sauran kayan miya. Kwanakin baya sai aka kore ni daga wajen aiki na dawo zaman gida. Duk da ni na bata jari amma kullum bata da abun yi min sai gori wai na zama mijin hajiya ita take cida ni. Da abun ya bani haushi sai naje nace ta bani kudina dubu dari dana bata jari. Nan fa tace ta cinye kai tsaye. Abun yayi kamari har ta kai mu ga dambe. Nayi mamakin karfin murja dan dagani tayi ta ringa nunawa mahalicci tana bugawa da kasa. Da dai naga tana neman jinyata ni sai nace na hakura. Bayan kwana biyu sai na sama wani mashin din ina achaba. Mun dade a haka ina ciyar da ita duk da ta fini samun kudi. To ranar sai mai mashin din ya sayar da shi. Nan na sake komawa gidan jiya kekenapap din nan itace ake bani duk sati to kinga kuwa ko ni kadai ne baxata iya rike ni ba balle ma harda mata ta. Wannan yasa na fara cin bashi a gurin domin ita bazata bada ba sai bashi a haka har na tara kudade da yawa. In kinga irin rashin mutuncin da take min a kansu bazaki taba cewa ni mijin ta bane". Safuratu taja dogon nunfashi tace, "Tabdijam kaga irin abunda ake gaya muku. In kun tashi aure ku nemi mace mai hankali tausayi da sanin ya kamata. Amma sai ku bige da neman mace Fara kyakyawa doguwa. Baku ma damu da kalar tarbiyar ta da halayyarta ba. Hmm in kuwa kuka cigaba da haka lalai zaku ta tsintar kanku cikin irin wannan matsala Mukhtar. Umar abunda nake so daku shine ku yafi juna nasan duk hassadar da yake maka sharrin shedan ne". Umar ya sauke ajiyar zuciya ya kalle Muktar yace "Ba komai abokina na yafe maka Allah ya rabamu da sharrin shedan kuma". "Na gode abokina ameen Allah ya saka da alkhairi". Umar yace mu duka Safuratu ce ya kamata muyi wa godiya. Muna matukar godiya Safuratu. Hakika da za'a samu irin ku a cikin al'umar aljanu da wasu abubuwan sun saitu a cikin mu mutane". Murmushi tayi kafin tace. "A komai ai ana samun na gari ta yuyu bani kadai bace ma. Yanzu Mukhtar ya zakayi da matar ka?". Mukhtar ya bata rai yace "Ni fa na sake ta saki daya. Amma kuma tace bazata bar gidan ba". Dariya Umar da Safuratu sukayi.
Safuratu tace "Ji shegiya kamar gidan ubanta. Bari inje in korar maka ita". Mukhtar yace "Jira bari in karashe sauran saki biyun su zama uku domin na tsani murja gaba ki daya bazan iya zama da ita ba". Takarda aka samo mishi ya idasa sakin Safuratu ta amsa ta bace. A kofar gidan Mukhtar ta bayyana cikin sufar Mukhtar din. Ta shiga gidan bata iske murja a tsakar gida ba hakan yasa ta wuce daki. A zaune fake Mukhtar din ya iske Murja a bakin gado da gani ranta a bace yake. Yana shigowa ta fara binshi da harara. Shima martani yake mayarwa. Takardar ya fiddo daga aljihun shi ya mika mata. "Sauran saki biyun ne wannan ki hada da na farko na sake ki saki da uku". Karbar takardar tayi ta lunkuma a baki ta tataune tukun ta bushe da dariya daga bisani ta bata rai ta tashi cikin tsiwa da bala'i. "Kai Mukhtar To bari kaji karyarka tasha karya wallahi.baka isa ba wannan sakin bai saku ba. Ni da kai mutu ka raba ba inda zanje". Mukhtar yace "Ki tatara ya naki-ya naki kiyi gagawar barin gidan nan tun kafin jikin ki yayi tsami". Yar dariya tayi irn ta raini wayyo hade da cewa, "Ayyiriri iyye nanaye. Kai baka ma ji kunya ba da ka fadi haka?. Waye zai karya ni kai ko kuwa wani?. Na ma ga alamun dukan kake so dan haka bari kaga". Juyawa tayi da sauri waje taje ta daukko tabarya ta nufi Mukhtar tasha mamaki ganin ko motsi baiyi ba duk da kuwa a haukace ta taho da niyar buga mishi. Tana kawo tabaryar yayi charf! Ya rike hade da wanka mata wani wawan mari wanda sai da ta gigice bata ma san lokacin da ta saki tabaryar ba ta fadi kasa. Belt Mukhtar din ya daukko ya fara bulalata tana ihu! Bai sasauta mata ba duk sai da ya farfasa mata jiki tana ihu! Da jan jiki ta fito daga dakin kafin ta tashi ta fita a guje bata ko sake wai-wayo baya ba. Safuratu tace "Yar nema gobe ma ki kara"................................................_
😂 Murja yar masifa yau anji jiki 😜
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 87-88
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
_*THIS PAGE DEDICATED TO ELOQUENCE ASSOCIATION*_
🌟 ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION 🌟
💃🏻😍 *MUSA MELODY, AUTA* 💃🏻😍
_(Autan Eloquence)_
💃🏻😍 *MUHIEVERT INDIA* 💃🏻😍
_ єя ιи∂ια Er love)_
💃🏻😍 *SHAMSIYYA SALIS* 💃🏻😍
_(Autar Eloquence)_
💃🏻😍 *BASIRA N. DABO* 💃🏻😍
_(Basira)_
🤗 Kai dama duk members wanda ban sani ba. Ina muku Fatan alkhairi. Allah ya kara daukaka. Allah ya kara muku basira da Hazaka.
*ZAMANAWA*
Nayi muku fatan alkhairi 💋❤❤
*A PAGEN DA YA GABATA CIKIN LITTAFIN ALJANAR FATIMMA*
~Belt Mukhtar din ya daukko ya fara bulalata tana ihu! Bai sasauta mata ba duk sai da ya farfasa mata jiki tana ihu! Da jan jiki ta fito daga dakin kafin ta tashi ta fita a guje bata ko sake wai-wayo baya ba. Safuratu tace "Yar nema gobe ma ki kara".~
_*S*afuratu ta bayyana gaban su Mukhtar dake zazaune a tsakar gida hannun ta rike da wasu daurinan kudi. "Mukhtar na kori Murja kuma ina kyautata zatan bazata sake ma irin rashin kunyar da take ma da ba". Daurin kudi ta mika wa Umar da Mukhtar kowa daya-daya hannun har karkarwa yake wajen amsa. "Wannan kudin da kuke gani kar kuyi tunanin a banki na sato ko kuma kudin wani. Aa kudina ne mallaki na inada dukiya mai yawa a boye a inda mun biye su ne a wani waje wanda mu biyu kadai muka sani daga ni sai Ummana. Wacce yanzu ita bata raye. Dubu dari-dari ne ku samu koja jari da shi domin neman na kanku. Sallama nake muku sai kuma wani jikon. Umar karka yarda inji ko inga kawa matar ka wani abu makamancin wanda kake mata a baya. Dan in na kama ka da hakan bazaka ji dadi ba. Idan ta tashe kuce mata ni na tafi sai Allah ya sake hada mu". Tana kaiwa nan ta bace bat!. Godiya suka kamayi mata kala-kala suna murna. Mukhtar tunowa yayi bata bashi makulin napep ba. Har ya fara rudewa da tunanin ina zai ganta kuma sai ya hangi keys din a kan tabarma. Da safe da suka gayawa Rafy bata ji dadi ba sosai. Har hawaye tayi tana fadar Safuratu bata kyauta mata ba. Ya zata tafi basuyi bankwana ba. Umar kuwa lalashin ta yake yana cewa ai zata dawo tace......_
______________________
_Gidan shiru kake ji ba hayaniya hakan ya nuna cewa yara sun tafi makaranta kenan. Zaune suke sun tattara hankulan su gaba li daya sun mikawa TV dake makale a bango. Mama Asiya ce ta shigo itama ta sama waje ta zaune hade da cewa "Sannun ku". "Yauwa suka amsa gabaki daya". Kafin Zuwaira tace "Aunty Asiya tun washe garin ranar da abun nan ya faru nake tambayar ki me yasa kika yi duk wannan abubuwan harda goya babyn Fatima amma kinki bamu labari". Asiya ta waiga hagun da dama tace "Yanzu zan fada muku amma abun sirrine dan haka ku dawo nan". Tashi sukayi gaba daya suka koma kan sofa chair din suka hada kai da ganin kasan abun munahinci ne. Mama asiya tayi kasa da murya ciki-ciki tace "Wato ni kaina ina so in sanar daku abunda ke faruwa to sai dai duk lokacin da zan fada muku sai inga wannan shegiyar Fatima. Sai inyi shiru. Shin ko kunsan wannan yar babyn ta hannunta Aljana ce?". Kallan juna Zuwaira da Hauwa sukayi cikin rashin fahimta "Bamu gane ba aljana kamar yaya?". Mama Asiya ta lumfasa tace "Kwarai Aljana nima ban zata ba sai ranar. Duk abubuan nan da kukaga inayi to ita take saka ni. Har bullo min take a cikin wata irin suffa abun tsoro". Kwashewa sukayi da dariya gaba dayan su harda ma rike ciki. Hauwa tana fadin "Wai Aljana sai mu zauna ki mayar damu aljanu ai". Zuwaira tace "Heheheheh!, Kinji fa dama na gaya miki ai motsa jini ne take ba komai ba. Shine zaki bige da ce mana wai Aljana ce..."._
_Asiya ce ta mike a fusace. "Dariyar ta iska haka kuma in kuma mutum bai bari ba Wallahi yanzu zan narki kayan banza. Aa kaji mun yan rainin wayo. Ni dai na gaya muku kuyi hankali da Fatima. Dan yanzu ba ita kadai bace ba kamar da bane da muke mata duk abunda muke so. To yanzu in mutum ya zalunce ta akwai ma rama mata. Dan haka kuyi hankali. In kunne yaji to jiki ya tsira". Tana fadar haka tayi gaba ta nufi dakin ta. "Ni dai cikin abubuwan da nake wa Fatima ba abunda zan fasa sai ma karawa da zanyi Wallahi. Bari ma ta dawo inci ubanta sai muga Aljana. Hhh kawata wai kinji mu za'a mayar Aljana". Zuwaira ce mai wannan maganar. Asiya kam bata ko juyo ta kalle su ba ta shige abunta._
_Safuratu na dawowa gidan taga Fatima bata nan wannan ya tabbatar mata tana makaranta ne. Jikin yar Babyn taje ta shiga. Lokacin tasowa Fatima Nasmat, Da Asmart tare suka shigo gidan sai wasa suke a tsakanin haka ya tabbatar wa da Safuratu cewa Fatima bata cikin wani damuwa._
_Kwana biyu nan Zuwaira da hauwa suna so su taba Fatima su gani kuma suna tsoro. Dan kar suje abunda Asiya ta gaya musu gaskiya ne. Haka shima bangaren abba kullum cikin target yake na yanda zai yiwa Fatima mugunta wacce zai huce haushin marin da mama Asiya tayi mishi a kanta. Safuratu kuwa da taga kwana biyu hankalin Fatima kwance ranar nan tana zaune sai ta tuno da su Kamal da matar sa Khadija hakan yasa tace bari ta nufi can taga irin halin da ake ciki ga Muktar ma._
**************
_Zaune yake a tsakar gidan yana goge takalmin sa da alama fita zaiyi. Yarinyar ce cikin uniform dinta na makaranta tazo ta durkusa ta gaishe shi ciki-ciki ya amsa mata rai a bace. Kamar dai ta bari kuma sai tace "Baba bani naira hamsi". Cike da masifa da hargowa yace "Kinci ubanki ke da hamsin din kaji marar kunya marar tunani yanzu duk halin babu da ake ciki ke baki gani da zaki ce wani wai in baki Hamsun to ko kwandala bazan bayar da. Bace min da gani ko in make ki". Hannu ya daga kamar zai bige ta. Da ganin haka ta tashi ta ruga a guje tana kuka. Ummiey ce ta fito Cikin nuna bacin rai tace "Baban Hawwer gaskiya abun da kake baka kyautawa ko kadan. ko dan kaga Aljanar nan bata dawo shiyasa ka fara wa yarinyar nan rashin mutunci?". Muktar ya dago cikin fushi "Ummiey bana san haka fa. Miye ruwan ki in ma Aljanar ta dawo nasha dai ba wajen ki zata zo ba ko?. Kin anta irin gatan da na nuna wa wannan yarinyar ne?. Ai ko hawwer ban mata abunda na mata ba. Na mata ada lokacin da nake tunanin Aljanar nan zata dawo. Yanzu kuwa tunda naga bazata dawo ba, Ai sai in sakata in wala". Ummiey Tace "To ai ita wannan dukiyar ta ce. Sannan kuma kaga tunda Allah ya karbi Hawwer bai sake bamu wata yar ba. Ya kamata mu rike maryam kamar Yar mu hawwer Domin ni jinta nake sosai a raina kamar yar dana haifa". Mtsww.. Muktar yaja tsaki tare da sa takalman sa yace "Naga alamar maganar kike so to ai ga bango nan sai kiyi da shi. Nasan bazai taba gajiya ba. Ni dai na tafi". "A dawo lafiya". Shine abunda Ummiey ta fada bai ko amsa ba yayi gaba. Safuratu da duk abunda ya faru a gabanta ya faru kai ta girgiza "Lalai wannan ashe bakayi hankali ba. Zamu hadu da kai"._
_Gaba dayan unguwar an taru sai kallan masu jigilar watso kaya waje. Ba mai bada hakuri balle a hana. Wani mutum mai sanye da Jacket ranshi a bace sai cewa yake "Yauwa ku fito da su bana so inga ko cokalin su a gidan nan. Yau yau nake so su tashi su bar gidan nan". Can gefe kamalu ne zaune yayi tagumi yayi wani tsamo-tsamo kamar bera ya fada ruwa an fiddo shi. Gefan shi kuwa Khadija ce ba abunda take sai kuka tana zubar hawaye. Tana tunanin irin wannan bakar rana wai yau sune ake watso musu kaya a kan titi. Kaddara kenan. Safuratu na ganin haka ranta yayi mugun baci. Nan take ta Juye suffarta zuwa wani saurayi mai kwarjini. Tsakiyar mutane ta ratsa ta fara bin masu fiddo kayan tana Fasfaska musu mari tana fadin "Ku mayar da kayan nan kafin Rai ya baci". Ai kuwa basuyi gardama ba suka fara dibar kaya suna mayarwa. Daga baya wannan mai sanye da jacket ya fara bala'i ya nufo Safuratu. Yana zuwa ya duma mata kulli. Da juyowar ta ta shaki kwalarsa da hannu daya ta dage shi sama. Kafafun shi na reto...................................................._
🤔 *NAN FA AKE YINTA*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 88-90
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
🤗 *WANNAN PAGEN NAKU NE MASOYAN LITTAFIN ALJANAR FATIMA A DUK INDA KUKE*
💃🏻 _A KULLUM FARIN CIKINA DA JIN DADI BAYA MISALTUWA IN NA TUNO DA KU MASOYA NA. INA JIN DADIN _COMMENTS NAKU KUNA A RAINA._ COMMENTS NAKU NADA MATUKAR MAHIMMAN CI A GARE NI. KO BA KOMAI ZAN KARA SAMUN KWARIN GWIWA._
😰 _*DAN HAKA YAU DUK WANDA YA KARANTA BAITI COMMENT BA SAI NASA SAFURATU TA SAKO MAI DUTSE A KAI*_ 🙊😜
Luv u oll supporting ❤😍😍😍
🤗 Har Unsupported din ma 😉
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ai kuwa basuyi gardama ba suka fara dibar kaya suna mayarwa. Daga baya wannan mai sanye da jacket ya fara bala'i ya nufo Safuratu. Yana zuwa ya duma mata kulli. Da juyowar ta ta shaki kwalarsa da hannu daya ta dage shi sama. Kafafun shi na reto.~
_*H*arbe-harbe ya kamayi yana neman kubucewa amma ina rikon da tayi mai ba na wasa bane. Wulla shi tayi ya fadi kasa. Da ganin haka wasu yan kallon suka fara sabe wa suna guduwa. Masu fito da kaya kuwa suka kara azama wajen mayar da kayan cikin gida. Mutumin da Safuratu ta koma shi ya nufi Mai jacket din nan a jiki. ya fara da cewa. "Lalai kai ka cika marar imani da tausayi da har zaka sa a watso wa da mutane kayansu tsakiyar titi. Wannan wane irin cin mutunci ne?. A kan kawai basu biya ka kudin hayaba ko mai?. Shin kai baka tunanin in kai ne ake wa hakan baza kaji dadi ba". Mai jacket din ya mike yana kaka be jiki, kafin mutumin ya karaso gare shi ya nuna shi da yatsa. Yace "ba dai ni kawa haka ba a bainar jama'a. to ina tabbatar maka da cewa sai kayi nadamar abunda ka aika ta min. Domin alhaji dayyabu sam! Bazai rabu da kai ba dole ya dau kwakwaran mataki a kanka". Da fadar haka ya juya ya tafi. Safuratu kuwa tace, "Ina nan ba inda zani ina jiran alhji Dayyabun. Ko uban waye yazo inaji dashi. Banza wanda bai san mutuncin dan adam ba". Mai jacket din wanda ake kira da Dan ladi na alhaji Dayyabu. Ya juyo ya kalle Safuratu. "Alhaji kake zagi?. Lalai yau mai kwatar ka a hannun alhaji sai Allah". Juwaya yayi ya hau mashij dinsa ya buga ya tafi a guje._
_Kamalu ne ya taso yana mishi godiya. Safuratu tace "Ba komai ai yi wa kai ne". Kamal fuskar shi cike da damuwa yace "Mun gode da abunda kayi mana, Kuma naga abunda ya faru dan haka nake rokon ka da ka bar gurin nan domin alh. Dayyabun nan da kaji ana fada hatsabibin mutum ne. Yana da kudi sosai shi yasa yake takada duk wanda yaga dama. Yanzu nasan in yazo ya tarar da kai a nan sai ta Allah. Dan Allah ka taimaka ka bar nan". Safuratu dake suffar namiji tace "To wai wannan gidan nashi ne. Haya kuke a ciki ne?". Kamal ya kama hannun mutumin suka shiga daga ciki dan ganin mutane na kallan su. Khadija ma tashi tayi ta bisu. Bayan sun zauna kamal yace, " Wannan da kake gani. Gidana ne kwanakin baya wata kaddara ta fado mana matata ta kamu da wata cuta. Asibiti suka nemi kudi million daya da rabi. Na hada jarina gaba daya Dubu dari hudu ne.Na nemi taimako wajen masu kudi da dangi amma ban samu ba. Gidan nan shi kadai ya rage min. Kuma Allah ya gani a kan matata ba abunda bazan iya yi ba. Da har nayi tunanin sayar wa sai wani abokina ya bani shawara inje wajen Alh. dayyanu yana bada aro amma ya shaida min cewa, Baya ba mutum aran kudi sai ya tabbatar da mutum nada wata kaddarar da tafi abunda ya ara. Yace mutumin baya da mutunci idan kuka sa lokaci baka kai mishi kudin sa ba. To zai zo ya sayi gidan ka ko mota ko wani abun yanda yaga dama ya cika ma kudin ya kuma kore ka. Da naji haka da har nace ban amince ba. Koma sai na canza shawara na amince. Naje na aro million daya da dubu dari na cika da kudin gurina na kai asibiti akayi wa matata aiki. Bayan ta sama lafiya da wata daya alh. Ya fara aiko min dan ladi shine wannan mai jacket din da ka gani._
_Hakan tasa ni dole na saiyar da gidan kuma shi Alh. Dayyabun shi na sayar wa.
Da sukaga watan ya shude ban kai musu kudin su ba shine Alh. Ya turo wasu matasa yan daba suka dauke ni, Suka kai ni wajen sa. Nan yake gaya min tunda naki bayan kudin sa to ya saya gidana. 1.5 million. Yanzu zai cika min dubu dari hudu. Da na nuna rashin amincewa sai yace wa da yan daban nan suta duka na har sai na amince. Nan fa suka fara jifga ta da dai naga suna neman hallakani sai nace na amince. Nan yayi dariya ya kawo dubu dari hudu ya bani. Wannan abun da nake gaya ma ya faru shekaran jiya ne. Yace in tattara kayana in tashi daga gidan in ba haka ba ya min korar kare. Nace to, jiya nayi neman duniya in sama gida ko na hayane in biya shekara amma abun ya gagara. Shine fa yau tun safe ya turo dan ladi da wannan matasan suka zo suka fara watso mana kaya waje. Mutumin ya ja dogon nunfashi yace "Lalai wannan mutumi ya cik...". Hayaniyar da sukaji a kofar gida ce ta tsayar da mutumin bai karashe magana ba. Kamal jiki na rawa yake cewa. "Wallahi Alh. Ne kaga sai da nace ma ka gudu-ka-gudu amma kaki, to yanzu gashi nan ya debo yan daba". Mutumin hankalin shi kwance yace "Abunda nake so da ku yanzu shine kuyi sauri ku shige daki kai da matar ka". Ba gardama kuwa suka shiga suka kulle dakin._
_Alh. Dayyabu Ne a gaba Gefan shi Dan ladi sai kuma wasu garada su hudu Katti ne majiya karfe ko wanne ka kalla fuskar shi zata gaya ma ba imani. Kursiyya tsakar gida ta zo ta yi tsaye ta dan bubuda kafafu ta mayar da hannuwa baya. Irin tsayuwar guards. Alhji ba abunda yake in banda zage-zage. Yana ganin mutumin da tsayuwar sa sai ya tsaya cik! Suma gaba ki daya suka tsaya. Alhj._
_Ya kalle mutumin sama da kasa tukun ya bushe da dariya yace "Kai Amma Dan ladi ban taba sanin kai mashiririci ne ba sai yau. Yanzu dan Allah a kan wannan dan Yarinyar ne ka taso mu ni nama dauka wani jibeben gardi zan gani har na kwaso karti hudu. Hakan ma cewa kake wai na kara wasu. Yo wannan karamin alhakin ko ni ai sai in tumurmusa shi". Dan ladi ya kara matsawa kusa da alhji yayi ya mai rada a kunne. "Alhj bar ganin shi haka kashi daya ne da shi. Da hannu daya fa ya dagani sama". Cikin fada da bacin rai alhaji yace. "Kai rufe min baki matsoraci kawai bari kaga insa ayi min guduwa-guduwa da shi. Tiger Da Musa lion ku kamo min yaran nan yau sai ya gaya min gidan na ubanshi ne da har zan sa a fitar da mutane ya ce a mayar". Rufe bakinsa ke da wuya, Sai kuwa karti biyu suka nufi Safuratu ko wannen su a murmurde yake fuskokin ba annuri. Safuratu Da ganin sun nufo ta sai ta ruga a guje ta shige bandaki. Su tiger suka bita a guje suma. Da zuwa suka tarar da ba kowa a ban dakin sai wata yarinya dake kallan su tana murmushi. Musa Lion ya chakumi rigar ta ta baya ya dage ta sama da hannu daya. A haka suka fito sa ita. Alhaji tun kafin su karasa gurin sa yake cewa. "Kai bana san iskancin banza fa. Ya nace ku kamo min wancan dan Yarinyar zaku kamo min wannan karamar tsakuwar". Tiger ya bude baki maganar shi ita kadai ta isa ta tsorata mutum. "Alhaji ai shine ya koma haka dq alamu yana da layar zana"._
_Alhaji yayi dariya. Hehehehehehe, "Au! Wato shine ya koma wannan Yarinyar nufinshi zamu kyale shi ne". Alhaji ya matsa gaf da Safuratu dake rike a hannun tiger sosai alhaji ya matsa kusa da ita yana mata wani irin kallan raini. har hancin shi na gogar nata. "Wato kana nufin da ka koma wannan Yarinyar muyi hakuri mu kyale ka ko. To kuwa kayi kuskure domin da ka tarye ni fada gwara ka taryi RUNDUNAR SADAUKAI. Domin ni nan da kake gani na nafi kububuwa hadari. Sannan bani da imani ko miskala zarratun, Saboda rashin imanina cinnaka ake cemin baka san na gida ba ciji Jariri in uwar ta motsa in galla ma..." Ai kafin ya rufe baki Safuratu ta cije shi a hanci harda jini. Kafa tasa ta harbi tiger a ciki. Dan zafin da yaji baima san lokacin da ya sake ta ba. Da gudu ta nufi wani bangare na gidan. Alhaji rike da hanci yace "Ku kamomin wannan dan iskan ku cinye shi danye". Da fadar haka su duk hudun suka bi Safuratu da gudu. Kamar biri haka ta kama gini makal-makal ta haye kan soro. Su tiger na zuwa sukayi tsaye suna kallanta. Irin dutsen da ake dorawa a saman kwano gudun kar iska ya dauke ya yace kwano. Shi Safuratu ta dauka ta daga sama alamun jefowa zatayi. Da ganin haka suka tsaya cik suna kallanta. Dariya Safuratu kafin tace "In da mai so ya bakunci lahira a cikin ku ya karaso"._
_Cik! Suka tsaya suna kallan ta domin kuwa sun san cewa duk wanda aka bugawa wannan dutsen ba a kai ba ko a wani bangare na jiki ne ya banu. Ganin sunyi tsaye ba mai niyar zuwa alhji yace, "Tiger dama abunda na daukko ku kuyi kenan?. Bana san iskancin banza fa". Cikin maganar su irin ta yan daba yace "Wannan maganar rai ce fa ake, ahhee Bar gani na a haka daga ta kwada min shi zaka ga na fara ah yane a nan gurin. Allah. Alhaji". Ran alhaji ne ya baci nan ya fara tattare babbar riga "Bari ni inje tunda ku bazaku iya ba". Da sauri dan ladi ya rike shi. "Aa alhaji karkaje wallahi Waccen daga gani ba imani zatayi ba". Safuratu ajiye dutsen tayi ta kalli tiger suna hada ido sai kuwa idanun shi suka koma bakake wul! Ba ko alamar baki a ciki. Da faruwar haka ta diro daga saman Soran. Musa lion da sauran biyun suka nufe ta a guje kafin su karasa sai ganin Tiger sukayi ya shige gaban ta. Da ganin idanuwan shi suka gane ba lafiya ba. "Ku tsaya". Tiger ya fada da karfe muryar kamar wanda yayi magana a Loudspeaker. Cik suka tsaya. Abun mamaki duk wanda suka hada ido da tiger sai shima idanun su koma baki kirin gaba dayan su haka.Alhaji da Dan ladi suna tsaye kallan ikon Allah kawai suke. Da faruwar haka Safuratu tace "Kuje ku daukko min alhaji da yaran sa dan ladi ku kawo min shi gaba na". Gaba daya su hudun suka juya suka nufi alhaji. Da gudu dan ladi ya juya da niyar ya tsere ai kafin ya isa kofa tuni wani yasha gaban shi. A kafada aka sabo su alhaji aka dire a gaban Safuratu. Alhaji na karkarwa yace...........,......................_
🤔 *KAIKAYI YA KOMA KAN MASHEKIYA* 😳
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 91-92
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
😘😘 DEDICATED YOU MY SON *MUBASHSHIR*
HAPPY BIRTHDAY *MUBASHSHIR*
🎂🎂🎂🎂🎂?
💃🏻💃🏻 Allah ya karo shekaru masu albarka
Happy 2+ 😘😘😘
?🎂🎂🎂🎂🎂🎂
💃🏻 *I'M HAPPY* 💃🏻
*HAPPY MAULIDIN NABIYYU SALLALAHU ALAIHI WASALLAM* ☺💃🏻
*Bazamu taba mantawa dake ba ya masoyin Allah.*
*Bamu da kamar ka ya shugaban mu..*
*Mun san cewa duk irin so da kaunar da muke maka bazamu yi rabin san da kake mana ba ya Habibullah*
*Mun gode wa Allah muna kara gode masa a kullum.da ya bamu kai ya Rasulillah.*
*Bamu da komai bamu da kowa sai kai manzan Allah. Ka cece mu ranar da ba mai ceto sai kai. Ba dan matsayin mu ba dan girman Allah ya Rasullillah* 👏🏻💃🏻
Makiyan ka sun tabe. Masoyan ka baza su taba tabe wa ba. Saka mu cikin masoyan ka👏🏻.
Dole muyi murna da zuwan ka ya shugaba. 😟 Wanda basa murn bakin ciki ya kahe su 🤷🏻♂
*YA ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA. AMIN*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
_*"D*an Allah dan annabi kiyi min afuwa ki ceci rayuwa ta wallahi bansan ke din Aljana bace". Safuratu ta harare shi. "To ai yanzu kasan ni Aljanar ce. Naga kamar ka kwaso wadan nan kartin banzan ne domin suzo su tumurmusa ni dan na hana a watsar wa da nayin Allah kayan su ko". Da sauri alh. Yace Aa wallahi sam ba da niyar haka na zo ba. Ni nazo ne ma in c na bar musu gidan su rike. Amma dan Allah karki yi min komai". Kamal da kadija da sukaji shirun yayi yawa basu ji ihun mutumin nan ba. Sai kamal ya taso ya leko. Yana ganin Yarinyar nan kuwa kwalwarsa ta shiga aikin bincike yana kokarin tuna inda ya santa amma hakan ya gagara. Khadija ya kari itama ta leka kamar dai shi. Itama taso ta san Yarinyar amma ta manta a ina._
_Safuratu tace "Aa ka rike gidan ka ai yanzu idan ka basu kyauta. Watakil wata mai tsayuwa zaka zo kace su tashi ka fasa. Dan haka bari a biya ka kudin gidan ka". Bat! Safuratu ta bace. Sai bayan kamar mintuna biyar ta bayyana rike da jaka. Ta mikawa alhj. Dayyabu hannu na karkarwa ya karba. Tace ya daga ya gani. Ya daga kudi ne bandir-bandir na dubu-dubu. Safuratu ta dauki biyu daga ciki tace. "Kudin nan Million daya da dubu dari ne. Ina ce dai sune kudin da ka arawa kamala". Kai ya jijiga alamun eh. "Wannan dubu dari biyu da kaga na dauka kuwa Khadijah zan bawa matar kamala domin ta sasayi duk abunda yaranka suka lalata mata wajen fiddo kaya. Daga yau karka kuma kallan gidan nan balle ma kayi mafarkin zai zama naka". Alhj. Duk a tsorace yake kamar kace arrr! Ya zurq aguje. Yaran shi kuwa sunyi tsaye kem! Kamar wanda aka sasaka. "Kamala! 2×". Safuratu ta kwala mai kira. Da sauri ya amsa suka fito tare da matarshi suma duk tsoro ya kamasu domin idanun su sun gane musu abunda duk ya faru._
_Safuratu tace "Na biya wanna mutumin kudin shi da ya ara maka. Yanzu wannan 400k din dake wajen ka kaja jari ke kuma ga wannan ki saya duk abunda suka lalata miki wajen fito da kaya". Kamal da matar shi mamki suka cika da shi sai godiya suke. Kana kallan fuskokin su kuwa zaka gane akwai alamar tambaya. Tsaya Safuratu ta dakawa alhji. Da yaran shi, tashi yayi ya runtuma a guje haka suma yaran firgigit! Ko wannen su kamar wanda aka tayar daga barci sukayi waje a guje. Safuratu ta mike tace "To ni zan tafi kuma sai wani lokacin. Cikin su ba wanda yace uffan!. Har ta fara tafiya Kamal yace "Dan Allah ke din wace ce?". Jiyowa tayi fuskar ta dauke da murmushi wanda shi ya kara fito da kamanin Yarinyar kwanaki nan take suka gane ta. Safuratu tace "Ni ce Yarinyar da kuka taimaka kwanakin baya. Wannan sakamakon alkhairi ne. Kunsan Allah ma yace . "Shin kyautatawa nada wata sakamako?,Face Kyautatawa".RAHMAN 60 AYA:._
_"Kuyi hakuri wancan karon da na tafi ba tare da nayi muku sallama ba. Ni kaina naji dadin zama daku. kuma zan so ci gaba da zama daku duk da ni ba mutum bace sai dai kuma ayyukan gaba na baza su barni in zauna tare da ku ba shiyasa ma kawai na tafi a lokacin". Hawaye ne ya fara zubowa Khadija. "Shin dan Allah yanzu ma tafiya zaki ki barmu?. Kinsan irin Son da ake miki kuwa. Tun ranar da Kamal ya kawo ki gidan nan ya fada min cewa baki da kowa kuma gaki kurma. Hakan yasa na kamu da tsantsar sanki da kaunar ki dan a lokacin sai naji kamar an yaye min bakin cikin da nake ciki na rashin haihuwa. Kwatsam kuma a daren ranar sai kika gudu kika barni. A ranar ga kamal nan wuni nayi ina kuka domin ji nayi kamar Na haihu 'yar ta mutu ne". Tana zuwq nan ta fashe da kuka Kamal ya kwanto ta jikin shi yana lalashi. Sosai ta bawa Safuratu tausayi domin itama sai da hawayen suka zubo mata. "Khadija kiyi hakuri ki sani cewa aikin da na daukko babban aiki ne bazan iya tsayawa a nan gidan na wasu kwqnaki ba domin in nayi hakan wasu da dama zasu shiga matsala. Zan dai riga zagayo ku in na sama dama in sha Allah. Kuma zan na taya ku addu'a Allah ya baku haihuwa". Da karashe fadar haka Safuratu ta bace._
_Bata bayyana a ko ina ba sai kofar shagon Muktar. Ta bayyana ne a cikin shigar wata tsohuwa almajira fuskar ta duk a yaya mutse, Duk wanda yaga tsohuwar nan sai ya tausaya mata. Faced din shagon matar ta nemi waje ta zauna. Ba abunda take sai kallan Muktar. Duk juyowqr da zaiyi sai yaga sun hada ido da matar a zuciya yace "Waccen fa ina ga yunwa take ji. Kuma yaseen ko mutuwa zakiyi bazan baki komai ba". An kwashi mintuna ya kara juyawa yaga dai again shi take kallo abun ne ya bashi haushi a fusace ya fito daga shagon dan bala'i ko rufe wa baiyi ba kanta yaje ya tsaya yana ta surfa masifa sai kace ya sama sa'ar shi. Ita dai ba abunda tace sai idanu da ta kwalalo mishi ko kiftwa batayi. Daga karshe yace "Kinga malam in ma ke mayya ce wallahi kurwata tafi karfen ki. Haba wannan kallo kamar naci ban biya ba". Ganin taki tankawa ya juya ya koma shago. Abun haushi da takaici har yanzu bata daina kalla shi ba. A zuciya tunanin abunda zai mata yake domin iya bacin rai ranshi ya gama baci. Wai tama rasa wanda zata je ta tsare da kallo duk shagunan makwabtan shi sai shi. A fusace ya kara fita ya koma wajen ta masifa har kamar ya dake ta yake. Mutane na ganin haka suka je suka bashi hakuri hade da tada tsohuwar daga wajen. Can da yamma kuma sai gata hannun ta rike da kwanan bara. "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran"._
_Shiru Mukhtar yayi ba tare ya dago kai ya kalle ta ba. Kamar dazun sake maimaitawa tayi "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran". Dogan tsaki yaja. Tsohuwa bata tafi ba kara fada tayi "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran". A fusace Muktar ya dako "Anki a bada malam dallah ki ware ki ishi mutane". Kara murtuke fuska yayi "Ke wai me zan miki ne tun dazun kin takura min haba malama ni kadai ne mutum a nan ne. Ko kuma sadakar dole sai ni ne zan bayar..." Fada yake surfa mata kamar wanda ya sama diyar shi. Kyalkyale wa tayi da dariyar mugunta. Hannu tasa ta kwaye rabin fatar fuskar ta. Abun da yayi mutukar girgiza Muktar kenan nan take ya kama karkarwa ya zube a wajen yana bata hakuri domin ya gane wace ce._
_Muryar ta ba dadi Tace "Wato dama abunda duk na gaya maka bai shiga kunnen ka ba ko. Naga ma yanzu saura kadan ta rage ma ka fara dukan maryam yarinyar da na baka amana. Da kudin ta fa kake ci kake sha. Amma naira hamsin ka kasa bata". Muktar yama rasa ya zayi yasan dai yanzu bashi da wani abunda zai kare shi. Magiya hadata da Allah da annabi yake. Safuratu ta daka mishi tsawa hade da cewa yanzu zan yi ma hukunci kuma irin shi zanci gaba da yi ma muddun baka dai na abunda kake ba. Zan raba ka da duniyar mutane can zan kaika in da bazaka ga kowa ba sai Dabbobi su kuwa sun fika rashin mutunci, kaga sai ku hadu kutayi in baka ci sa'a bama Kora ko zaki wani ya cinye ka". Tana rufe baki bat! Suka bace yare muktar sai ganin shi yayi a wani kurkurmin daji ba abunda kake ji sai kukan tsuntsaye ga kuma kukan namun jeji. Wata murya da Muktar ya rasa daga ina take fitowa "Muktar wannan shine hukun cin da ya dace da kai zan barka a nan kayi yan kwanaki nasan zaka kara daukan darasin zaman duniya ka gane cewa rayuwa ba komai bace". Hannu muktar ya dora a kai ya fashe da kuka "Dan Allah dan annabi kiyi hakuri wallahi na tuba bazan karaba karki min wannan hukunncin". Shiru yaji ko uffan ba'a ce masa ba. Nan ya durkushe yana ta kuka........................................_
🙆🏻♂😧 *MUKTAR DAGA YAU SAI ASAN MUTUNCIN DAN ADAM. KO YA YAKE BA ABUN A WULAKANTA BANE. BAKA SAN KALAN BAIWAR DA ALLAH YA MASA BA*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 93-94
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
😘😘 *DEDICATED MY ASSOCIATION ZAMANI*
👏🏻😰 ```FATAN ZAKUYI MIN AFUWA. MUNYI BIKI NE BANA SAMUN TYM DIN TYPE. AMMA YANZU IN SHA ALLAH IDAN NA FARA SAI NAJE KARSHE``` 😟
INA ALFAHARI DAKU MASOYA NA 💃🏻 ANA TARE 😘
_Bayan ya gama kukan ya tashi ya hau zagaye dajin, Yayi yawo sosai amma ko alamar gida balle mutum bai gani ba. Safuratu kuwa gida ta koma ta juye zuwa Muktar din. Haka taci gaba da kula da harkokin sa har na tsawon sati guda. Muktar kuwa na can dajin wani lokacin ma abincin da zaici wuya yake masa,_
_Loaci daya rayuwa ta juye mai barci sai dai ya sama wani dan kogun dutse ya shiga ya kudundune. Haka kuma ruwa sai dai yaje wani dan gulbi da yaga ruwa na taruwa yasha. Yayi kuka sosai kuma yayi nadamar abunda ya aikata. A zuciyarsa ya kudurci niyar cewa bazai sake aikatawa Maryam makamancin wannan ba. Yayi kudirin zai rike ta da gaskiya kamar yarsa. Haka kuma kwanakin nan da yayi duk lokacin da yunwa ta takura mishi sai ya dinga tunowa da almajirai masu zuwa wajen shi, Abunda yake zuwa mai a rai shine suma fa haka suke ji yayin da suke jin yunwa. Mukhtar a zuciya yake kudurtar niyar bazai kara hakan ba. Yau aka cike kwanaki bakwai cik! Da kawo Muktar daji. Tun da safe Safuratu ta bayyana mishi nan ta zaunar da shi yana ta tuba yana neman afuwa. Tace "Muktar ya zuciyar taka tayi sanyi ne ko har yanzu cike take da rashin imani da gurin cutar yar da take a matsayin sana'ar ka. Rufin asirin ka". Muktar da yake durkushe gwiwowin sa a kasa. Harda hawaye, Cikin kuka yace, "Dan Allah dan annabi kiyi hakuri dan Allah ki ceci rayuwa ta ki fitar dani daga wannan wahalar._
_Nayi miki alkawarin cewa bama Maryam ba in sha Allah duk wani wanda yake neman taimako zan taimaka masa gwargwadan iyawata". Safuratu tayi mai wani irin kallo na tuguma, Kafin tace "Na saba dajin rantse-rantse daga bakin ire-iren ku na karya. To ka sani cewa in har baka daina cutar da maryam Allah, Allah kaji na rantse ko. To gaba daya sai na amshe duk dukiyar ka ka dawo kamar dai da yanda kake a lokacin da ka karbe musu kudi. Zanje kuma in nemi mutumin kirki in bashi amanar Maryam. Da wannan karon ma abuna nayi niyar yi kenan. Kuma in kana ji wasa to ka sake kwatanta Rashin imanin da kake"._
_Muktar ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na rantse miki har da Allah na canzu zaki same ni ba kamar da ba. Domin wannan horan da kika min ya ankarar dani abubuwa da dama. Dan haka ki taimaka ki mayar dani gida. Nayi kudirin ko da kuwa kin kwace Maryam da dukiyar ta daga hannuna bazan fasa wannan kudirin ba. In sha Allah zan taimaka wa duk wanda ke da bukatar in taimaka wa". Wasu kaya Safuratu ta mika mishi tace yaje ya saka su. Ba dade ba sai gashi ya sanyo su. Makulin shagon ta bashi kafin kiftawar ido sai ganin shi yayi a kofar daki. Dake ya saba da shiru na cikin daji yanzu duk sai yaji hayaniyar nan ba dadi. Bankwana Safuratu tayi mai hade da kara nanata mishi cewa ya kula ya canza hali. Safuratu yau din nan ta tashi ne da tunanin Fatima kuma zuciyar ta na raya mata ba lafiya ba. Hakan yasa ta tashi da niyar komawa bauchi yau._
_____________________
_A bangaren Fatima kuwa bayan kwana biyu da tafiyar Safuratu Zuwaira da Hauwa suka taso ta gaba wai su sai sunga abunda mama Asiya ta gaya musu ko gaskiya ne. Ai kuwa suka fara takura wa Fatima tun suna zaginta har suka fara dankwashi. Ganin ba abunda ya faru ne yasa suka kara kaimi wajen cin zalin ta. Daga karshe ma a gaban jama'a har da kuwa Mama Asiya hauwa da Zuwaira suka karbe yar babyn Fatima sukayi gutsun-gutsun da ita. Nasmat, Asmart, Ameera, da Mama Asiya duk sai suka fara tausaya wa su Zuwaira a kan abunda suka wa yar babyn dan a tunanin su Aljanar in bata kashe su ba sai ta kusa. Su kuwa su Hauwa hankalin su ko tashi baiba._
_Daga karshe ma tatara yar babyn sukayi suka kone ta rumus a tsakar gida. Fatima ta fara kuka ai kuwa suka same ta suka ta narka taci duka har sai da ta gode wa Allah. Bayan kwana daya-biyu su Mama Asiya sunyi mamkin ganin ba abunda ya faru da su Zuwaira gashi kuwa kullum cikin duka da zagin Fatima suke. Hakan yasa suma gaba daya gidan suka koma ruwa. Wato kowa ya koma kamar da zalluncin da ake wa Fatima har ya kusan linka na da ma. Haka abba yanzu kusan kullum sai ya daki fatima ko ya aike ta gu mai nisa. Fatima na shan wuya sosai. Dan ko yau haka ta tafi makaranta ko guntun biredi bata ci ba. Safuratu na isa gidan tace ta duba dakin su Fatima bata ganta ba. Shiyasa tayi tunanin ko tana makaranta ne. Sai dai kuma ta duba inda Fatima ke ajiye babyn ta amma bata ga komai ba. Hanyar makarantar ta nufa. Dan daga nan har sai da ta shiga gidan Umar. Kallo daya tawa Rafy ta gane cewa tana cikin farin ciki. Domin sai aikin gida take hankalin ta kwance tana wake-wake._
_Nan dai ta bayyana suka gaisa take tambayar Rafy ya zama gidan. Rafy tayi mata godiya tace ai yanzu suna zaman lafiya sosai da mijin ta. Hamdalla Safuratu tayi nan dai suka hau hira. Safuratu kam hankalin ta duk yana wajen Fatima. Lokacin ta so su Fatima nayi tayi sallama da Rafy ta fito ta taryi Fatima. Tafe take tana wani rangaji kamar zata fadi, sai zubar hawaye take. Ba komai akayi mata ba yunwar ce kawai ke cinta domin bata saba kai war haka bata ci komai ba. Daga nesa Safuratu ta hange ta. Karasa wa kusa da ita tayi tana kare mata kallo. Irin ramar da Fatima tayi ne abun ya tsorata Safuratu. Domin in ba kayi wa Fatima kwakwaran sani ba. Bazaka iya gane ta ba a yanzu. Dan duk kashin wuyanta ya fito ta rame sosai. Tangal-Tangal din da Fatima keyi har idanta na rufewa hakan ya shedawa Safuratu Fatima najin matsanan ciyar yunwa._
_Sharf! Fatima ta fadi kasa Safuratu na ganin haka tayi sauri ta shiga jikinta. Mutane har sunyo kanta da niyar agaji kuma sai sukaga Yarinya ta mike. Karasowa sukayi wasu na kakabe mata jiki suna mata sannu. Idanun Fatima suka kara zarowa daga ka ganta zaka ga ba kamar da ba. Yar ledar littatafan Fatima ta dauka ta nufi gida. Kwan! Kwan! Kwan! Kwan! Da karfi Fatimar ke buga gida. Mai gadi najin haka ya taso a rikice yana fada yana fadin "Waye wannan yake mana irin wannan buga gida kamar tashin duniya". Buga gidan bana wasa bane domin da karfi Fatima ke bugawa. Har mai gadi yazo yana kokarin budewa amma bata dai na bugawa ba. Yana budewa yaga itace. Ya tsaya tsabar haushi har karkarwa yake. Dan ji yayi kamar ya mare ta duk da tana yar gidan. Fatima ganin mai gadi baya da niyar matsawa. Fuuu! Ta bangaje shi ta wuce can ya fadi kasa a gigice. Domin irin bangajewar da Fatima tayi mishi ba karamin kato bane zai yi masa ita har ya fadi. Yayi mamaki sosai. Tashi ya kakabe jiki ya juya yana kallan Fatimar domin ya kara tabbatar da ita din ce ko wata.
_"Tabbas Fatima ce, to amma ina ta sama wannan karfi haka". Shi kadai yake kallan ta yana magana shi daya. Kofar falo Fatima ta ja da karfi kamar zata ballata. Yanayin yace labulan kadai kai in ka gani kasan bana arziki ba. Hauwa ce kadai a dan ringeshe kan sofa tana tauna Cingum tana daddana waya. Tana jin shigowar Fatima ta tashi zaune. Ita Fatimar ta nufo. Ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Fatima da shi mai dauke da harara._
_"To shegiya har an taso daga makaranta wato za'a zo a ishi mutane da kuka. To kafin ki fara komai ajiye kayan makarantar ki shiga dakina kiyi mopping dinshi ki gyara komai kafin kizo in fada miki next work naki". Fatima kam tsaye take ta kafe Hauwa da ido bata ko giftawa. Hauwa ganin Fatima taki wuce wa tayi abunda tasaka ta tace. "Ke dan uwarki ba kiji abunda nace kije kiyi ba. Yar buhun uba kin wani tsare ni da wannan shegun idanun naki. Ko dai na jaki kike so yan...". "Ina abincina?". Shine abunda Fatima ta fada hakan yasa Hauwa bata karashe maganar da ta fara ba. "Iyee Fatima ni zaki wa rashin kunya?. To bari kiji dan ubanki ko langen taliya bazaki ciba yau a gidan nan. Oh! Baki ji abunda aunty zuwaira tace ba ken...". Cikin tsawa da kagara Fatima ta kara fadar, "Ina abincina na ce?". Abun ne ya fusata Hauwa hakan yasa ta daga hannu da zafin ta da niyar wanka wa Fatima lafiyayan mari. Charf! Fatima ta rike hannun hade da Wanka wa Hauwa mari da dayan hannun ta................................._
0 comments:
Post a Comment