~Cikin tsawa da kagara Fatima ta kara fadar, "Ina abincina na ce?". Abun ne ya fusata Hauwa hakan yasa ta daga hannu da zafin ta da niyar wanka wa Fatima lafiyayan mari. Charf! Fatima ta rike hannun hade da Wanka wa Hauwa mari da dayan hannun ta.~
_*G*alala Hauwa ta saki baki tana kallan Fatima cingum din da take ci ma bata san lokacin da ya fado ba. Rike kunci tayi tana jin radadi a zuciyar ta tana fadar "Anya wannan Fatima ce?". Hannu Fatima ta sake dagawa da nufi mari "Ina abincina nace?". Da sauri Hauwa tace "Bari in daukko bari in daukko miki". A tsorace ta mike ta nufi kitchen din Fatima na binta da wani malalacin kallo._
_Hauwa taje ta zubo mata abincin ta kawo. "Yauwa Fatima ga abincin". Ta mika hannun ta na dan karkarwa. Fatima na amsa ta zauna a nan ta fara cin abincin hannun baka-hannu kwarya. Juyawa Hauwa tayi da nufin haurawa upstair dakin ta. "Ina kuma zaki je dawo ki zauna". Fatima ta fada ba tare da ta dago kai ta kalle Hauwa ba. "Umm umm da... Da.. Ma zanje ina... Jin fitsari nee". Hauwa tayi maganar murya na karkarwa. Dan duk ta tsorata da Fatima tasan ba ita kadai bace, Akwai lauje cikin nadi. "To ba yanzu ba dawo ki zauna". Fatima tace ba tare da ta kalle ta ba. Hauwa har zatayi magana. Fatimar ta daka mata tsawa hakan yasa ta gimtse bakin ta. Sumi-sumi ta zo ta zauna. Sai kallan Fatimar take wanda sai cin abincin take kamar wacce tayi shekara bata ci ba. "Innalilahiwa'inailaihirraji'un 2×, Me zan gani haka". Zuwaira ce ka fadar haka lokacin da take saukko daga kan matakalar tayo kasa._
_Da sauri ta karaso gurin ta tsaya kan Fatima tana zazaga masifa. "Hauwa haka mukayi dake wato in kafa doka har kin isa kisa kafa ki shure ko?. Wato wuyanki yayi kwari, Ni dake waya fara shigowa gidan nan ko da baki min biyayya a matsayin ki na kanwata wacce nafi shekaru ba. Ai ya kamata kiyi min biyayya a matsayina na wacce ta riga ki shigowa gidan nan". Hauwa kallan Zuwaira kawai take tana kallan Fatima dake faman dibar Shinkafa fara da miya. batace ko kala ba. Zuwaira taci gaba da cewa "Sanin kanki ne nace yau yarinyar nan bazata ci ko kwayar shinkafa ba a gidan nan amma gashi nan kin dauka kin bata. Wato ke uwar tausayi. Zanyi maganin ki kuwa". Hauwa kallan Zuwaira kawai take tana mata wani kalan uku goma hudu shabiyar. Kasan ranta kuwa addu'a take Allah ya kai damo ga harawa._
_Fatima ce ta mike rike da filet din abincin. Kamar jira take Zuwaira na juyawa kuwa ta yaba mata shi a fuska. Bata jira komai ba ta juya ta nufi dakin su. Hauwa na ganin abunda ya faru ta kwashe da dariya harda rike ciki. Zuwaira kuwa cik ta tsaya kamar wacce suka gasar tsayu ita da gunki. Haushi ya kule ta can kasar ranta tunanin abunda zatayi wa Fatima take. Dan kakabe jikin ta tayi miya duk ya bata mata kaya. In ka ganta sai ka rantse wasa da miya tayi. "Ni ni ni Fatima tayi wa haka,_
_Lalai Yarinyar daga ni kuwa bazaki kara ba. Yau ko makiyin ki sai ta tausaya miki Fatima". A fusace tayi waje, Nan take zuciyoyi suka shiga aikin bata shawarwari na mugunta wanda zatayi wa Fatima. Dakin mai gadi ta zarce. "Fito-fito mai gadi, Ina wannan dorinar taka mai baki biyu?". "Tana daki Hajiya". Har dan jijiga take yi dan kaguwa "Bani aranta yi sauri dan Allah". Kallan ta ya tsaya yana yi "Hajiya wa kuma za'a daka da ita. Naga yaran duk suna makaranta?". Tsawa ta daka mai, Nan da nan ya zabura ya shiga daki ya daukko mata. Yana bata ta nufi wajen tankin ruwa ta debi ruwa a irin yan kananun bokitin nan. Ta nufi falo da shi. Fridge ta nufa da sauri ta daukko kankara ta zuba a ciki tukun ta shiga tsiyayya ruwan sanyi. Ita kadai take magana. "Dan ubanki ai yau kin shiga uku sai na jikaki da ruwan sanyin nan tukun in miki dukan kawo wuka. Badai ni kika wa wannan wulakancin ba". Tana gana matse pure water mai sanyi ta dauki dorinar da bokitin ruwan wanda zuwa yanzu tuni ruwan yayi mugun sanyi. Ta nufi dakin su Fatima. Hauwa dai na zaune a falo ido kawai take binta da shi._
_"Ayi dai mu gani in tusa tana hura wuta". Inji Hauwa ta fada da dan karfi. Zuwaira taji ta amma bata kula ta ba. Dashigar ta dakin ta fara kwallawa Fatima kira. "Fatima! Fatima! Fito dan kut...uban ki. Yau ai sai kin raina kanki". Shiru bata ji ko motsi ba. A tunanin ta Fatimar na ban daki. "Ki fito na gaya miki dan Wallahi in na iskeki a bandakin nan bazamu kwasheta da kyau ba. Sai nayi miki jini da majina Wallahi". Nan ma shiru bata ji an tanka ba. Bulala da bokitin ruwa ta dauka buzun-buzun ta nufi ban dakin da zuwa tasa kafa ta haura kofar da karfi. Kofa na budewa taga wayam. "Shegiya asbe ta gudu daga dakin". Falo ta fito "Hauwa ina wannan shegiyar Yarinyar ta nufa da ta fito?". Hauwa ta kalli Zuwaira Mamaki karara a fuskanta. "Au! Fatiman fitowa tayi ne?". "Kina nufin baki ma ga wucewar ta ba?. Fatima zaki gama guje-gujen ki kidawo ki iske ni har gida". Zuwaira ta fadi haka ta ajiye bokitin da bulalar a gurin, ta nufi Upstair da niyar taje dakin ta canja kaya._
_Da bude daki ta tsaya cik! Tana karewa tsakar dakin kallo Fatima ce gaba daya ta bince ke wardrobe din da su kabbet duk ta wurwatsa kaya a tsakar daki. Yanzu ma sai bincike take tana bubude lokoki. "Aunty Zuwaira jan baki nake ta nema tun dazun a ina kika ajiye shi". Wani kululun bakin ciki ne yazo wa Zuwaira makogoro. Nan take ta kai dubanta Mirror ta hangi duk kayan kwaliyar ta har da jan bakin ma a wajen, "Wai amma dan rainin wayo wannan yarinyar tace wai jan baki take nema. Kai kawo dai wani tashen iskanci da rainin wayo ne. Amma bari inyi maganin ki yanzu". Jawo dakin tayi da sauri ta koma falo da gudu ta daukko bokitin ruwa da bulala. Tana dawowo ta bude daki kuma sai gani tayi wayam! Ba kowai sai tilin barnar da Fatima tayi mata. Domin shirya kayan da Fatima ta warwatsa kadai jarabar duniya ne. Gashi wasu kayan a goge ma suka amma Fatima ta kara tattake su. Hauwa na zaune a falo taga Fatima ta fito daga saman beni bayan ita kuma bata ga fitowar ta daga dakin su bama. Abun ne ya kulle mata kai. Fatimar tafe take hannun ta rike da dan karamin mirror na kallan fuska dayan hannun kuma jan bakine da take ta faman Gogawa a lips inta. Tsaye taje tayi a kusa da Hauwa tana shafa jan bakin. Zuwaira tun daga sama kake iya jiyo jarabar ta. "Yarinyar kamar Aljana,yanzu nan fa na baro ta a dakin nan wai amma bata nan. Hmm dani kike zancen Fatima._
_Ai Wallahi in dai kere na yawo zabo na yawo wataran a hadu. Wai ni ta...". Bata karashe fadin abunda tayi niya ba hango Fatima da tayi a falo. Nan take ta fara sauri tana kokarin sakkowa. Fatima hanyar dakin su ta nufa. Zuwaira dake rike da bokiti da bulala a hannu da gudy taje tasha gaban Fatima. "Ina zaki munafuka Allah ya kama ki. Yanzu zan chaskwala ki". "Bani waje in wuce". Fatima ta fada cikin kagara. "Iyeee! Lalai Fatima arzikin rashin kunya yaci uban na da.Har ni zaki iya kallan kwayar idona kice wai in matsa ki wuce. Bari ki karbi hukunci tukun sai ki wuce ko da jan gindi ne". Kokarin ajiye ruwan take. Ai kafin ta ajiye wata irin bangaza da Fatima tayi wa Zuwaira can ta fadi kasa bokitin ruwan yayi sama ya fado duk ya jijika Zuwaira da Carpet din falon. Wata mahaukaciyar dariya hauwa ta kwashe da ita. Har da rike ciki hade da hawayen dariya._
_Zuwaira tace "Hauwa wai Giwa ce ta bangaje ni ko Saniya ko Rakumi?". Hauqa kara kwashewa tayi da Dariya. Cikin matsanan ciyar dariya tace, "Duk ba ko daya a ciki". "To dan Allah jirgin kasa ne ko mota._
_Domin kuguna ji nake kamar ya karye bani iya tashi yanzu". Hhhhhhhhhhhhhhh Dariya kamar zata kashe ta. Karar dariyar ta ne ya tashi Mama Asiya dake can sama tana barci. Da sauri tayo Downstairs tana "Lafiya-lafita mi yake faruwa ne?". Falan taga kaca-kaca Can an watsar da shinkafa da miya. Nan an kwarayar da ruwa. Hauwa ta kalla dake ta faman Dariya. "Ke kuma wanne irin iskanci ne zaki bata mana falo haka. Nan fa ba falon ki bane ke kadai balle kiyi mana kazanta". Hauwa ta dan rage dariyar kadan tace "Aunty Asiya Wallahi bani bace aikin Fatima ne". "Kuturun kareee! Wace Fatimar?". "Fatima tamu ta nan gidan mana". Cikin fusata Mama Asiya ta nufi dakin su Fatima tana fadar. "Ina take dan ubanta Wallahi sai ta gyara dakin nan tsaf!"................................................_
🤣😂 *Wayyo cikina* _HAUWA DOLE IN TAYA KI DARIYA. SU ZUWAIRA MADARA ANJI JIKI, SAI KUMA A TASHI AJE AYI JINYA_ 🤧
_*KU BIYO NI ZAI-ZAI DAN WANNAN KARAN WANDA AKAYI BABU SHI BAI MORI LITTAFIN BA*_ 🤝
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 97-98
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
DAN KADAN NE DAI. KUNSAN ANCE *"DA BABU GWAMMA BA DADI".*
*DEDICATED TO* 👇🏼👇🏼
😍😍
*BIGBOY ISAH FANS*
😍😍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
😍😍
*GIDAN MARAYU FANS CLUB*
😍😍
*3STAR HAUSA NOVELS* 💃🏻
😘 GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU TARE DA FATAN ALKHAIRI. BANI DA KALAMAI KO AZANCI DA ZAN IYA MUKU GODIYA DA SHI. SAI DAI KAWAI ALLAH YA BAR MU TARE.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~MUN TSAYA A INDA HAUWA TACE, "Aunty Asiya Wallahi bani bace aikin Fatima ne". "Kuturun kareee! Wace Fatimar?". "Fatima tamu ta nan gidan mana". Cikin fusata Mama Asiya ta nufi dakin su Fatima tana fadar. "Ina take dan ubanta Wallahi sai ta gyara dakin nan tsaf!".~
_Mama Asiya na shiga ta iske Fatima zaune a gefan gado ta juya mata baya. "Fatima! Fatima!2×". Shiru fatima ko waigowa batayi ba. Kara matsawa wajen ta tayi "Ke dan iskanci da rainin wayo kinaji ina kwala miki kira amma kikayi banza dani. Zonan dan ubanki". Gashin kan Fatima ta kama ta jawo ta kiiii! Har cikin falo, "Maza jeki daukko kayan mopping kizo ki tattara shinkafar nan da kika zubar ki wanke wajen miyar nan da kika zubda. Sannan in kin gama ki daukko tsumma kizo ki matse wannan carpet din da kika zubda ruwa a kai". Harara kawai Fatima ke binta da shi. Hauwa da Zuwaira dake zaune kan armchair tana wash-wash ba abunda suke sai kallan Mama Asiya da fatima. Zuwaira fatan da take shins Allah yasa Mama Asiya tayi ganganci wa Fatima._
_Duk maganar da Mama Asiya take Fatima ba abunda take mata sai mugun kallo. Mama Asiya da ta gama jawabin nata ta juyo taga Fatima na hararen cikin fada tace "Ke Fatima ba magana nake miki ba. Wallahi tallahi in raina ya baci bazaki ji dadi ba. Dan ba wanda ya isa ya kwace ki a gidan nan...". Duka ta kaiwa Fatima dim! "Ni kike wa gatsine da uban ki. Bari ki gani". Juyawa tayi ta dakko dorinar wajen Zuwaira. Fatima na ganin haka ta kyalkyale da dariya lokci daya kuma sai ta hade girar kasa da ta sama. "Zaki iya duka na da bulala. Na baki offer nan. Amma ki sani cewa duk bulala daya idan kika min ni goma zan miki". Mama asiya bata dakata ba ta nufo Fatima tana zuwa ta lafta mata balula. "Wuce kiyi abunda na saki". Wani malalacin kallo Fatima tsare mama Asiya da shi. Dan bulalar da aka mata sai ka rantse ba jiki aka daka ba domin kuwa ko motsi batayi ba. Mama Asiya ta kara buga mata bulalar tana nuna mata hanya da hannu._
_}"Ki wuce kiyi abunda na saki nace ko?". Zata kara mata ne Fatima ta rike bulalar. "Bulala ashirin ya ishe ki dan wannan jikin naki ba lalai ya dauki talatin ba". Tunanii mama Asiya ta shiga yi nazari take akan maganar da Fatima ta fada. Domin ita bata gane nufin ta ba. Tana tsakar tunani sai ji tayi Fatima ta fisge bulalar daga hannun ta ta Zura mata._
_"Wai-wai wai.. Fatima ni kika dak..". Ai kafin ta rufe baki ta kara jin saukar wata bulalar. Hakan yasa ta nufi Fatima da nufin ta kwace bulalar. Da gudu ta shige ta. Hakan yasa Fatima tayi saurin gocewa kuma tasawa Asiya kafa. Rigijimmm! Kake ji ta Fatima. Su Zuwaira in banda dariyau ba abunda suke yi. Sai dai kuma daga Fatima ta harare su sai kowacce ta matse bakin ta. Fatima kan Mama Asiya taje tana Maka mata bulala tana kirge. "3..4..5..6..". Mama Asiya na tashi ta kara nufar Fatima a fusace. Tana Zuwa kusan ta Fatima ta kara sa kafa ta hangiza ta baya._
_Tagal-tagal ta tafi zata fada kan Coffee tabal din dake tsakar falo. Ganin in ta fada kanshi ya gama aiki dake na Glass ne da sauri Fatima ta rike hannun ta. Ta mike tsaya. Ko da taga ta mike sai taci gaba da dukan ta. Wannan karan Asiya da gudu ta hau zagaye falon tana neman dauki. Fatima na binta tana zana. Duk wacce mama Asiya ta nufa. Hauwa ko Zuwaira sai su arce a guje. Sai da Fatima tayi mata bulala ashirin cik!. Tukun ta zauna kan kujera tasa Mama Asiya tayi Kneltdown a gabanta. Dage kai tayi gefe ta fara wa mama Asiya magana kamar yanda tayi mata dazun._
_Cikin gadara fatima tace, "Maza jeki daukko kayan mopping kizo ki tattara shinkafar nan da na zubar, ki wanke wajen miyar nan da kika zubda. Sannan in kin gama ki daukko tsumma kizo ki matse wannan carpet din da kika zubda ruwa a kai". Jikin Asiya har yana rawa tace "To to an gama ranki shi dade". Zuwaira da Hauwa sun jin haka suka nufi Hanya zasu tsere._
_Kan Fatima a kasa ba tare da ta dago ba tace, "Ku muna fukai na baku damar tafiya ne?". Tsaye cik! Sukayi suna kallan juna. "Ku dawo nan ku tayata wannan aiki. Bari inje in siyo halawa. Kuma saura inzo inga wata bata abun da na sata. Uhmmm Wallahi da jaki ma sai ya tausaya mata". Fatima na fadar haka ta mike har ta nufi kofa kuma ta juyo. "Au! Ashe ba kudi a guna". Kallan su tayi daya-bayan-daya Suma ita suka kwalalowa ido kamar wasu mujiyoyi. "Mai nera dari ta bani kun wani kwalalo min idanu. To tubarkallah kuci kanku". Dajin haka suka shiga raba idanu, Suna kallan junan su. "Kaaaaaaaaaaaaaa! Daku fa nake". Wannan muguwar kuwwar ta daka musu wanda yasa duk sao da suka rufe kunnuwa. Dajin haka har rige-rige suke wajen daukko kudin._
_Zuwaira ce ta fara kawo mata. Hannu na karkarwa kamar wacce ke rawar sanyi ta mika mata hade da cewa "Gashi dari biyar ne ba canji". Wata muguwar harara Fatima ta bita da shi tukun ta karbi kudin fuuuuuu! Ta wuce. Dai-dai lokacin Mama Asiya da Hauwa suka fito da sauri ko wanne rike da kudi. Zuwaira ta juyo "kudin ku sun huta. ta ai ta tafi". Mama Asiya tayi ajiyar zuciya hade da kallan su gaba daya "Shin mai kuka fahimta game da lamarin nan". Kamar hadin baki su hauwa sukace. "Aljanar ce ta shige ta ba wani abu ba". Mama Asiya tace. "Haba nima nayi tunanin haka. Ji yanda Yarinyar ta juye lokaci guda ta zama abar tsoro. Ai kuwa sai munyi taka tsantsan domin Wallahi wannan zata iya sabauta mutum". "Ahh! Ni Zuwaira yau naga tashin hankali. Gaskiya dole mu dauki matakin gagawa". Hauwa ce tace "Kunga Wallahi gwara muyi abunda tace kafin tazo ta fatatake mu". Mama Asiya ce ta koma kan kujera ta zauna._
_Da ganin haka itama Zuwaira ta je ta zauna. Hauwa tayi musu wani irin kallo a gantsare tace "Shin me hakan ke nufi?. Ko kuna nufin bazakuyi aikin bane?". Su Mama Asiya kallo kawai suke binta da shi. "Chabb! In kuwa haka ne Wallahi nima bazan yi ba. Gwara in Aljanar ta dawo tayi mana koma miye a tare". Hauwa na fadar haka ta nufi wajen su ta nemi waje itama tayi zamant...................................................._
😰👏🏻 Kuyi hakuri da wannan kuyi min afuwa. Wallahi sai da karume-karume nayi type din nan. 😆 Sai na fara sai kawai wani uzurin ya zo. Yanzu haka wani abokina ne ya kawo min ziyara. I'm busy 😰
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 99-100
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏼 *®Z.W.A*
_*WANNAN PAGEN NAKA NE AUTAN ELOQUENCE. ALEWAR KANKANA MELODY*_
_Ku bani kidan birthday a sama._
💃🏻💃🏻 Autan- Eloquence, Kuce min Auta Eloquence Today is u birthday 💃🏻 Today is you birthday 💃🏻💃🏻.
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*HAPPY BIRTHDAY MUSA MELODY AUTAN ELOQUENCE*
🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰🍰
_Happy birthday Melody wish you many more Albarkakun years head_ 😍😘
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
Allah ya yafe maka zunubanka na shekarun da suka wuce. Kuma allah ya baka wasu shekarun Masu albarka 💃🏻💃🏻
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Chabb! In kuwa haka ne Wallahi nima bazan yi ba. Gwara in Aljanar ta dawo tayi mana koma miye a tare". Hauwa na fadar haka ta nufi wajen su ta nemi waje itama tayi zamant.~
_*M*ama Asiya na ganin hauwa ta zauna sai tace, "Haba hauwa wai ke a zatan ki bazamuyi aikin bane?. Haba mu mun isa. waya isa yaki yi aljana ta zo ta karyashi. Kinga dama ni jira nake ki daukko kayan ne fa". "Yauwa nima abunda na gani kenan". Cewar Zuwaira. Hauwa tace "To ai da na dauka nufin ku bazakuyi ba ne". Fita tayi ta kwaso kayan mopping Har su tsintsiya da abun kwashe shara. "To ku tashi gashi na daukko". Mika mama Asiya tayi "Wayyy! Wallahi ni kam duk na gaji please dan fara. Kafin in taso". Zuwaira tace, "Ashe bani kadai ba gajiyar nan. Kinji kuwa yanda kuguna yake kamar zai balle"._
_Cikin hantara "Dallah yi min shiru muguwa kawai. Ai ban taba sanin ku mugaye bane azzalumai yan bakin ciki sai yau". Kallo suka tsare ta da shi, Yayin da ita kuma taci gaba da magana. "In ba zalinci ba kunsan cewa Yarinyar nan Fatima ba lafiya lau take ba, Kuna ganin zan mata ba dai-dai ba amma kuka ki dakatar dani...". Tun kafin ta krasa maganar Zuwaira ta karbe ta da cewa "Wannan kuma Hauwa zaki cewa muguwa. Domin tun farko ita tasan cewa Aljanu sun shiga jikin Fatima amma taki wa mutane magana".Yar dariya Hauwa tayi hade da cewa, "Daga baya kenan. Ku tashi muyi aikin nan tun wuri Wallahi". Ganin basu da alamar tashi ita ma hauwan ta zauna hade da cewa "Wallahi bazanyi sharar nan ni kadai ba. Gwara in ta zo ko kashe wa zatayi ta kashe mu tare"._
_"Kanki ake ji". Cewar Zuwaira. Zaune suke kowa da tsoro a zuciyar shi, amma cikin su ba mai so a gane yana jin tsoran. Karar bude kofa sukaji. Ai kafin kace kwabo, Tuni ko wacce daga cikin su ta tashi da sauri ta dauki abun ta fara aiki. Su Asmart ne suka shigo gidan. Su mama Asiya na ganin su. Kowacce ta yarda abun hannun ta ta koma ta zauna. Mtsweeee! Mtsewwww! Mtsewww Sautin tsaki kawai kake ji yana tashi. Su Nasmat kuwa mamaki ne ya cika su. Daga shigowar su sunji an tarye su da tsaki. Har sun nufi dakin su Zuwaira ta kira su. "Kuyi sauri ku cire uniform din islamiyar nan kuzo ku share gurin nan". To suka ce ciki-ciki suka wuce suna gun-guni. Bayan sun fito ne suka kama aiki, Fuskar su ba mai annuri kamar ta shanu sai gunguni suke. "Wai daga dawowar mutum daga makaranta ko hutawa baiba a saka shi wani shar...". Shigowar Fatima ya hana Asmart karashe maganar zucin da take._
_Lollipop ne a bakin ta yana tsotsa ga wani biscuit a hannunta. Su mama Asiya gaba daya sun tsorace dan Zuwaira har yar karkarwa take. Nasmat tace "Wannan Yarinyar kuma uwar wa ta bata kudi har ta sayi wannan katan biscuit din?". "Uwarki ce ta bata". Zuwaira ta bata amsa. Shiru tayi tana kallan uwar tata da duk ta lura da yanayin ta a tsorace take. Asmart tace "Ke Fatima zo nan dan ubanki ki share wajen nan kal!, ki goge". Da sauri Mama Asiya tace "Sai dai ni uwar ki in share". Da fadar haka su Asmart suka fara tunanin akwai lauje cikin nadi. Fati dake bin su Zuwaira daya bayan daya da harara sai yanzu tayi magana tace wa su Asiya "Ku ku tashi ku tafi abun ku". Har rige-rige suke wajen tashi. Zuwaira har ta kusan zuwa Stairs ta juyo. "Uhmmm! Fatima chanji na fa". Cikin gadara Fatima tace, "Na bawa almajirai sadaka. Ko da magana?". "Aa"._
_Zuwaira tace ta wuce sama da sauri Fatima rufe ido tayi kamar me gyangyadi. Cikin tsawa Asmart tayi magana "Ke Fatima in kika yarda na karaso wajen ki wallahi sai kin raina kanki". Shiru bata bude ido ba balle tayi magana. Nasmat dake kallan tace, "Ke wai ba magana ake yi miki ba?. Kin wani rufe ido kamar kazar dake gwaida". A fusace Asmart tayo kanta da nufin ta dake ta._
_Fatima na bude ido tayi turus! Asmart taja birki tayi baya a guje. Haka itama Nasmt bata san lokacin da ta tsallake kojera ba ta wuce. Kofar dakin su sukaje zasu shiga kenan sukaji an turo kofar da karfe. Ba komai ne ya tsorata su ba. Idanun Fatima ne suka koma baki kirin gashin kanta ya wani mimike tsaye. "Ku dawo ku share gun nan. Ina zaku?". Suna karkarwa hade da kankame juna suka juyo. "ba inda zamu". Cikin tsawa tace suzo su share gun. Da sauri suka taho suka hau aiki. Rufe ido Fatima tayi ta sake bude wa nan take kuma idanun ta suka dawo Normal. Su Asmart sai shara suke suna goge carpet ita kuwa Fatima ta mike kan Sofa Sweet take sha abunta tana wasa da Biscuit dinta. Abba ne ya shigo yana jin waka._
_Ganin su Asmart na aiki Fatima a kwance ya daka mata tsawa wai ta tashi ta taya su aikin. Fatima ko kallon shi batayi ba. Su Asmart ne suka ce yaje ba komai zasu karasa aikin. Washe gari da safe. An zuba wa kowa abun kari Indomie da biredi sai tea. Asmart da Fatima gefan su guda. Fiddausi da amira ma. Haka suma yan kanana yaran. Sai abba da ya dawo falo ya zauna a nan yake break din. Fatima ce ta fito daga dakin su ta nufi Dinner. Bata wani tambayi ina abincin ta ba taje ta dauke Tea da indomie na gaban Mama Asiya. Da ganin haka Abba ya daka mata tsawa. "Ke dan ubanki sa'ar kice da zaki daukar mata abinci". Wata muguwar harara ta watsa mishi. Hade da murguda baki "Nata nake so kuma shi zanci in ka isa ka hana. Kuma ko da naka naga damar ci shi zanci". Fatima ke kallan shi tana maganar. Tashi yayi ya nufi dinner din a fusace._
_Mama Asiya kamar ta dakatar da shi kuma wata zuciyar sai ta bata shawarar cewq ta barshi watakil Aljanun Fatima mata kawai suka raina. Abba yana zuwa ya daga hannu ya kai mata mari, cikin hanzari ta goce. Duka ya kara kai mata da kafa. Nan ma ta goce tana binshi da wani shu'umin kallo tana murmushi. Mama Asiya da ta lura d Fatima da sauri ta zo ta janye danta dan kar a sabauta mata shi. Shi kuwa tuni ya hau daukin zuciya sai huci yake. Yana hararen Fatima da ita kuwa ko kula da shi batayi ba taje kusa da Fiddausi ta zauna tana shan tea. Tana gamawa ta tashi zata fita waje. "Ke dan uwar ki dawo kije kiyi shirin makaranta". Cewar Abba. Ficewa tayi ba tare da tace mushi komai ba. Abba yace_
_"Fatima ina tausaya miki. Dan Wallahi in na kamaki daga ni sai ke sai nayi miki fata-fata, Dan yau naga kin tashi da wani sabon salon iskancin". "Ko?". Fatima ma juyo tace mishi. Kofin shayin dake hannun shi ya wulla mata. Ba abunda ya bashi mamaki sai ganin da yayi kofin yayi Kwana ya nufi wani wajen. Bayan ya gama shan shayin ya tashi ya nufi dakin shi domin yaje ya huta. Yana shiga kafin ma ya bude kofa yaje kofar ta rufe kanta da karfki. Tsuru Abba ya tsaya yana kallan Kan bad dinshi wani abu ne cikin Blanket dinshi Yana gurnani marar dadi yana kuma mamotsawa._
_A hankali Abba ya nufi wajen hannun shi har karkarwa yake. Duk ya gama tsoracewa domin shi bai bar kowa a dakin ba. Kuma baima taba jin gurnani kalar wannan ba. Zuciyoyin suka shiga bashi shawara wata zuciyar na cewa ya bude yaga miyr wata zuciyar kuma na cewa ya fita ya gayawa su Mama Asiya. Ta wani fannin kuma ceqa yake "inje in sanar da su kamar dai ni din va namiji bane. Bari kawai in bude inga miye. Hannun na karkarwa sai ya kusa kama bargon kawai sai yaja baya a tsorace. Kusan sau biyar yana yin haka. A na shida ne ya daure ya kama bargon yaja da karfi. Ahhhhhhhhhhhhhh! Ya sakk ihu!............................?.....?......._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 101-102
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ta wani fannin kuma ceqa yake "inje in sanar da su kamar dai ni din va namiji bane. Bari kawai in bude inga miye. Hannun na karkarwa sai ya kusa kama bargon kawai sai yaja baya a tsorace. Kusan sau biyar yana yin haka. A na shida ne ya daure ya kama bargon yaja da karfi. Ahhhhhhhhhhhhhh! Ya sakk ihu!.~
_*I*tama ihun ta kwada. Yana ganin Fatima ce sai ya bata rai hade da watsa mata harara. "Ke uban me kike a nan dakin?. Wa yace ki shigo min daki?". Shiru tayi tana kallan shi ba tare da ta bashi amsa ba. Dube-dube ya shiga yi yana neman abun da zai dake ta. Ganin ba bulala ko wani mabugi a wajen ne yasa shi tsawa yana mata mugun kallo. "Oya tashi ki bar dakin nan ko inyi kasa-kasa dake a nan wajen". "Bazan tafi ba din yau a nan xan wuni". "Ke ni kike gaya wa wannan maganar?". Ya nufo wajen ta ya daga hannu zai mare ta yaji hannun ya tsaya cik! a lankwashe. Hahahaha ta kwashe da dariya. Abba kuwa fama yake ya mike hannun shi amma ina abun ya gagara. Ga Fatima sai Dariya take mai. Abun ya kara fusata shi nan take ya kara daga dayan hannu da nufin ya wanka mata mari. nan ma hannun ya tsaya cik! Duk hannuwan nashi biyu suka makale suka tsaya a lank'washe. Fatima da ganin hakan ta tashi ta fita daga dakin a guje tana Dariya. Su mama Asiya lokacin sun gama cin abinci yara kuma duk sun tafi makaranta. Sai su uku zaune a falo suna tadi._
_Fatima suka gani ta zo ta wuce a guje tana dariya. Zuwaira da Hauwa har yun kura zasu tsere suma a tsorace sukaji Abba a daki sai kwalla kira yake. "Mama! Mama!". Da sauri suka nufi dakin nashi a hanya sukayi kicibus. Hannuwan shi biyun duk a lankwashe. Ya rasa yanda zaiyi har ya fara zubar hawaye. Su duk ukun tambayar shi suke me ya faru. Cikin kuka ya fada musu duk abunda ya faru. Da jin haka mama Asiya tana jin haka tac "Kaico! Wai kai Abba me yasa baka gane wa ne. Yarinyar nan tunda kaga ina raga mata ai ya kamata kasan cewa akwai lauje cikin nadi. Aljanu ne suka shiga jikin Fatima. sau tari ina nuna maka ba ruwanka da ita amma kaki yanzu gashi ka jawo mana bala'i. Dama yanzu nake so in zo in gaya maka cewa ka fita harkar ta kar ta sabauta min kai. Ban sani ba ashe har ta faru ta kare". Ta kalli su Zuwaira tukun taci gaba da magana. "Dan Allah yanzu miye abun yi?. Kunga ta mayar min da da Masaki"._
_Jugum! Su Zuwaira sukayi suna nazari can Zuwaira tace, "Wannan abun ba wani abu ne ya jawo shi ba sai rashin sani wanda kuwa kowa yasan cewa *YAFI DARE DUHU*. To amma yanzu abun da ya dace shine muje mu roki Fatima ta taimaka ta mikar mishi da hannun shi. Tunda durkusa wa wada ba gajiya wa bane in dai za'a sama biyan bukata". Gaba daya suka aminta da shawarar Zuwaira. Kofar dakin su Fatima suka nufo tun daga nesa suka jin sautin dariyar ta. Mama Asiya tace "A gaskiya gidan nan ba lafiya. Aljanun jikin fatima rikakkun gardawa ne. In bamuyi a hankali ba duk sai sun babala mu. Kuma ya kama ta mu sanar da alhaji ya tafi wannan shegen aikin nashi ga gida yana so ya fi karfin mu". Hauwa tace, "Gaskiya ne amma ai naji yace ya ran Friday zai dawo". Zuwaira tura kofar tayi taji a rufe gam! kwankwasa kofar ta shiga yi tana fadar "Fatima! Fatima!. Dan Allah ki bude mana. Ba dan halin mu ba dan Allah". Shiru fatima taki bude wa. Sun dade a wajen kowa na tofa albarkacin bakin sa na magiya. Abba ma cikin kuka yake rokon ta ta bude ta mikar mai da hannun shi. Domin yaga wanki hulana neman kai shi dare. Fatima ta bude kofar cikin uniform dinta na islamiya rai a bace tace,_
_"Ku gafa in wuce ko in hangiza ku gaba daya kuma ko mutum ya karyw ba abun da yasha ruwana". Ta make kafada alamun ko Oho. Mama Asiya da Abba lokaci daya suka zube kan gwiwoyin su suna magiya. Fatima ta kwashe da yar banzan Dariya. Wai yau su Mama Asiya ce da durkusawa gaban Fati ana bada hakuri. Sai da Fatima tayi dariya mai isar ta cikin isa da iko ta kalli asiya tace, "In kina so in mikar mai da hannu sai kinyi tsallan kwado". Tsuru! Suka zazaro ido gaba dayan su. Hauwa da Zuwaira kamar su kwashe da dariya. Zuwaira da san gulma ta wa Hauwa rada a kunne. "Yau zamu ga tsallan kwado a gun Asiya. Tubur-tuburtu kenan". Wata muguwar dariya ce ta zo wa hauwa. Da kyar ta iya samu ta matse bakinta. Asiya tayi misisi da ido ta marairaice, "Haba Fatima kiyi hakuri mana ni yanzu ina zan iya tsallan kwado?". Fatima tayi hanyar wajen "Bakya so hannun danki ya mike ashe?"._
_Da sauri Asiya ta mike ta shiga gaban Fatima, "Yi hakuri dan Allah karki tafi ki bar Abba na a cikin wannan yanayin". "To maza ina jiranki fara". Mama Asiya ta tsuguna. Juyawa tayi ta kalli Su Zuwaira dariya suke mata sosai amma ciki-ciki ba yanda Fatima zata ji ba. tsalle mama Asiya taso tayi amma ko rabuwa da kasa kafafunbatayi ba saboda nauyi da jikin ta yayi. Hahhahhahah Fatima ta kwashe da dariya, "Malama kiyi sauri kiyi ina jira kinga dai na makara makaranta". "To....To. Bari in kokarta". Tsalle mama Asiya tayi niyar yi a karo ma biyu. Akayi rashin sa'a kuwa kafarta bata zo a dai-dai ba. Sai ji kake rigijif! Ta fadi._
_Fatima ta tuntsite da dariya. Haka ma su Zuwaira. Sai da Fatima tayi dariya har tana rike ciki. Tace, Kin fadi jarabawa amma tun da dai kin sani dariya Abba mike hannun ka na dama". Tana fadar haka ta juya ta wuce, Kamar wasa Abba ya mike hannun shi na dama yaka ya mike lafiya lau kamar bai taba lankwashe wa ba. Yayi murna sosai sai dai kuma hannun hagun har yanzu a lankwashe yake. Tun daga tsakar gida Fatima ke kwalawa Mai gadi kira yazo ya bude mata. Da sauri ya fito yana ganin Fatimar ce yayi tsaki. "Wai ke wannan yarinyar yaushe kika koma haka ne?. Ina tarbiyar ki take. Wato naga kwana biyun nan tashen rashin kunya kikeyi". Gatsine da harara kawai take binshi da shi. Haushi abun ya bashi ya nufo ta zai daga. "Wallahi kana dukana kayi ta aikin ka. Sanin kanka ne Alhaji baya san abunda zai taba ni kuma ran Friday zai dawo". Yanq ji ta fadi haka sai jikin shi yayi sanyi. Tsaki yaja yaje ya bude mata kofar._
_"Zo ki wuce jarababa kawai. Ke ma dai su Asmart sun koya miki wannan masifar ashe". Bata tanka mishi ba dungwai-dungwai ta wuce har makaranta. Makaranta ta cika makil! Sai karatu ake Fatima ba tare da wani fargaba ba ta shiga ajinsu. Malamin su na ganin ta ya fara binta da harara. Ita kuwa ko a kwalarta. Domin yunkurin wucewa ta zauna ma take yi. Malam yace, "Ke gidan ku, Ina zaki ko baki san kin makara bane?". "Ayi hakuri malam, na tsaya yin wani abu ne". "Kaniyar ki. Zo nan". ba gardaa taje. Tana zuwa kuwa ya fara zafga mata bulala. Sai da yayi mata uku. Yace "Oya maza wuce ki nema waje ki zauna". Tsaye tayi ta kafe shi da ido tana hararen shi. Tsawa ya kara daka mata amma taki tafiya. Hakan yasa ya kara juyowa yaci gaba da dukan ta abun yayi matukar tsorata malam yanda yasan Fatima da shegen kuka bulala daya ko biyu yake mata ta fashe da kuka yau kuwa gata sai duka yake amma ta kafe shi da ido tana harara ko kwalla babu. Sai da ya gaji da dukan dan kanshi ya barta yaje yaci gaba da darasi yace, "In kinga dama ki kwana a nan tunda bazaki je ki zauna ba. Da fadar haka Fatima ta wuce ta zauna. Abun ya daure wa Malam kai a zuciya yake saka "Anya kuwa wannan Fatima ce?"._
_Basarwa yayi yaci gaba da darasi. "Yara yau zamu ga mai tsantsar hazaka daga cikin ku. Idan baku manta ba kwanaki munyi bayanin taimama a cikin littafin ahdari. Sanan kuma mun kwana biyu munayi wanda sai da na tabbatar kun hardace tukun na daina biya muku. Dan haka yanzu ina bukatar Dalibin da zai tashi ya mai-maita mana. Kuma zan bawa duk wanda ya karanta min dai-dai kyauta. Yara biyu ne suka tashi daya mace daya namiji sai duk sai sun fara sai su kakare. Fatima ce ta mike. "Ni zan karanta kuma bana bukatar kyautar". Malam kallo kawai ya bita da shi. Nan take ta fara_
_*"Tafiyar da bata sabon Allah ba. Da marar lafiya, (Wanda yaji ciwo ko kuma dai yaa jin matsanan cin sanyi, Yana iya Taimama). Sallar farillah ko ta nafila. Mazaunin gida lafiyayye. yana iya Taimama dan Gudun fital lokacin sallah. FARILLAN TAIMAMA: Niya da bigiri (waje) mai tsarki. Shafar fuska, da shafar hannuwa zuwa dantse. Da bugun kasa na farko da gagautawa. Shigar lokaci da sadar da ita zuwa sallah. BIGIRE: (WAJE) Wajen da ya hallata ayi taimama a shi. Turbaya tubali. Da dutse da kankara da waje mai danshi da makamantan su. Taimama bata halatta da suminti ko abun dafawa. Ko kan tabarma. Da itace da ciyayyi.*_
_*Anyi rangwami ga marar lafiya ya shafi bango in dai bai sama wanda zai samo mishi kasa ba. SUNNONIN TA: Sabun ta bugun bigiri wajen shafar hannuwansa da shafar abunda ke tsakani Ku'i biyu da dantsen sa. Da jerantawa. MUSATAHBBANTA: Yin bisimillah, Gabatar da Zhirin Zura'i (Tsuntsuyar hannu). A bisa badinin sa. Farkon sa a bisa majinkircinsa. MASU WARWARE TAIMAMA: Masu warware ta daya suke da masu warware alwala. Ba'a yin sallar nafila biyu da taimam daya. Wanda yayi taimama domin yin Sallar farillah ya halatta a gare shin yin farillah bayan ya gama. Ya halatta ka taba Alqurani dawafi, da Tilawa. Da sadar da ita kafin fitar lokaci. Ya halatta ayi duk abunda aka ambata da taimama. Wanda yayi taimama yayi sallar isha'i yayi sha'i da wuturi, ba tare da ya jinkirta ba. Wanda yayi taimama yana da janaba. Babu makawa sai yayi niyar ta".*_
_Tana kaiwa nan ta koma ta zauna abunta. Malam kuwa tun da ta fara kallan ta kawai yake yana kada kai da alamun mamaki. Bai san lokacin da bakin sa ya furta. "Attakabir" Ba. Yara suka kwasa. ",Allahu akbar". Har aka tashi daga islamiyya malam na mamakin Fatima yau gaba daya ta canza. Fatima tunda aka tashi daga makaranta ta tafi gidan Rafy. Rafy kuwa dake tasan halin Safuratu sai tayi tunanin ko itace tayo sufar fatin. Nan sukata hira Fatima na taya ta wasu aikin gida. Bayan la'asar Fatima ta koma gida. Yau ma kamar yanda ta sabawa mai gadi haka tata buga get din da karfi. Wannan karan yana budewa ta bangaje shi ya fadi can gefe ta wuc fuuuu! Abunta. Asmart Nasmat Ameerah da Fiddausi dake gefe tana karanta novel a Facebook. Sune a falon. Suna kallon Mtv. Fatima na shigowa ta nemo remote ta rasa. Kawai sai zare Socket din tayi. Asmart na ganin haka tayo kanta da masifa........................................._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 103-104
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
📚 _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
👏🏻 *MASOYA AYI HAKURI DANI. WALLAHI KWANA BIYU INA BUSY NE BANA SAMUN TIME DIN TYPE* 😒😏 *MASU CEWA JAN AJI NE. DUK SAI NA HADAKU DA ALJANU* 🤧
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Asmart Nasmat Ameerah da Fiddausi dake gefe tana karanta novel a Facebook. Sune a falon. Suna kallon Mtv. Fatima na shigowa ta nemo remote ta rasa. Kawai sai zare Socket din tayi. Asmart na ganin haka tayo kanta da masifa.~
_"Ke Fatima bana san iskanci da tambada mayar mana da socket ko in lakada ki yanzun nan Wallahi". "Baza'a mayar ba". Asmart da taga Fatimar bata da alamun mayar da socket din dai ta nufo ta a fusace, Kafin ta karasa wajen ta. "Kai! kai! kai!._
_Rufa mana asiri in ba sokikr mu shiga uku ba yanzu". Hauwa ce ta fadi haka lokacin da ta fito daga kitchen. Asmart dakata wa tayi tana kallan Hauwa'u. Fatima tace, "Duk wanda ya kunna tv din nan yau ni da shi ne a cikin gidan nan". Da fadar haka ta juya ta wuce daki. Asmart tace, "Me ke faru Aunty Hauwa?". Hauwa tace. "Wato ku duk baku san me ke faruwa a gidan nan ba kenan?. Ai tun jiya Aljanu sun shiga jikin Fatima su suke sakata duk wani iskanci da take. Kuma gasu da shegen karfi. Kai dazun ma Abba da yaje dukan ta Wallahi hannun shi tsayawa yayi a lankwashe, Da kyar muka samu ta mikar mai da hannun daya, Dayan kuma taki mikar mishi wai sai Aunty Asiya tayi tsallan kwadi". Hhhhhhhhhh Nasmat tayi dariya, "Lalai Aunty Hauwa kin iya tatsuniya. Wai yanzu kina nufin daga naje dukan Fatima kawai dai hannuna ya makale". Hauwa tace, "Kwarai in kuwa baki yarda ba gaki gata. Inda ba kasa nan ake gardamar kokowa". Asmart tace, "Kai nima dai ban yarda da wannan jawabin ba. Haba dai yo ai ni ko a Tv ban taba gani ba. Kuma wallahi yanzu zan kuna TV din tayi abunda zatayi". Hauwa tace, "To marar kunya wato duk da ina auren baban ku matsayina bai haura karyatawa kai tsaye ba. To shikenan ni na barku lafiya. Ba dani ba raban fadan Zakuna. Wanda baiji bari ba yaji hoho, Ni kunga tafiya ta". Hauwa na fadar haka ta haura sama abunda. Asmart tsaye tayi abun nayi mata yawo a kwakwalwa. Tunani take ta Mayar da socket din ko ta fasa. Nasmat ganin asmart ta kasa kunna tv yasa ta tashi ta nufi wajen "Dallah matsoraciya matsa ni in jona in ke tsoro kike. Abunda dama wannan 'yar tsanar ce Aljanar kuma an toyata"._
_Asmart na jin haka tace "Kuma fa haka ne". Nan suka fara rige-rigen mayar da socket din. Fiddausi na jinsu duk abunda suke ko uffan bata ce musu ba. Ta dukufa wajen karatun novel da take a waya. Ameera kuwa game take a waya sai ihu! Take kamar zautacciya. Nasmat da Asmart daga wannan taje saka socket din sai dayar ta ture ta. Wai kowa na fadin shi zai mayar. Da suka dade suna haka sai kuma suka tsaya suka sasanta a kan a kama a saka a tare. Da mayar da socket din da dauke war wutar dakin duk daya. Juye-juye suka shigayi. Fiddausi da ameera su kansu sai da suka dakata da abun da suke. Gam! Gam! Gam! Windows din falon ne suke rufe kansu da karfi. Duk da rana ce a lokacin amma sai falon ya zama duhu rudum, kamar tsakar daren da ba farin wata. "Nasmat!, Fiddausi!, Ameera!. Kuna ina?"._
_Suma din gabaki daya a rikice suke sai kiraye-kirayen juna suke. Domin duhun yayi yawa ko tafin hannun ka baka iya gani. Fiddausi ji tayi kawai anyi sama da ita ana ja kamar wacce iska ke tafe da ita. Ihu! Take tun karfen ta hakan yasa su Nasmat suka kara rikicewa suma. Kofar falo ta bude Fiddausi sai ji tayi an watso ta waje. Mai gadi ne yayo kanta yana tambaya "Lafiya-lafiya me ke faruwa". "Aljanu ne". ta fada tana nuna mishi falo yayin da take kokarin tashi. Tana tashi ta zangara a guje. Mai gadi ma da gudu ya koma daki ya garkame kanshi. Su Asmart da sukaji ihun! Fiddausi ya lafa sai suka shiga kiranta. A hankali Asmart ke fadar "Aunty Fiddausi! Aunty Fiddausi!". Shiru bata ji an amsa ba. A tafiyar da take tana lalube irin na makafi sai taji hannuwanta sunci karo da mutum. Nan take ta fara lalubata tana kiran sunayen su. "Nasmat ce?, Ko aunty Ameerah ce?. Fiddausi ce?. Yi magana mana". Shiru bata ji yarinyar tayi magana ba. "Wai Fatima ce?". Ta kuma tambaya tana shafa fuskar. Tana zuwa saitin bakin sai ji tayi an gallara mata cizo. Ahhhhhhhhh!. Ta saki ihu! Abunda ya kara dugunzuma su Nasmat kenan suma suka rikice. Gudu suka ringa yi ba tare da sun san ina suka nufa ba. Bango birki. Nasmat na tafe a cikin duhu taji tayi karo da mutum. Tunani ta Asmart ce. Cewa tayi "Asmart wai duhun miye wannan?". Shiru bataji tayi magana ba._
_Lalube ta kamayi kuma sai taji ai yarinya ce taci karo da ita din. "Fatima! Fatima!". Wata irin walkiya suka gani kamar an kawo nepa an dauke. Nan take suka kara dimaucewa. Hahahahhaha gaba dayan dakin ya kwashi dariya, Zuwa can kuma sai wani ja haske ya cika dakin gaba daya. Nan take suka ga junan su bayan sun hadu waje daya ne suka kuma jin wata irin dariya kamar ta yara a bayansu. Ahhhhh! Suka fasa ihu a tare. Ba komai bane suka gani sai kan Fatima na tafe q kan iska wuyan wani irin jini ne mai kauri ga danko yake zuba kasa. A bakin ta kuwa wani danyan nama ne take ci duk jini na zuba. Ga kuma gashin kanta da ya koma wasu murda-murda ba kyan gani sai motsin yake da kanshi kamar macizai. al'amarin duk wanda yaga abun dole ya tsere in ba'aci sa'q bama mutum sai ya suma. Wannan kan na Fatima mai shegen abun tsoro n ya nufi su Asmart su kuwa kamar wanda aka rike wa kafafu sun kasa guduwa. Suna nan tsaye sai tsala ihu! Suke. Kan na zuwq saitin Ya wangare baki ya wani kara fadi. Kamar zai hade su baki daya. Luuuw! Suka ringa zubewa sumammu. Kafin kiftawar ido falo ya dawo yanda yake. Su Mama Asiya duk ihun da ake baya zuwa wajen su hakan ne ma yasa basuji ba. Zuwaira ce ta sakko daukan wani abu. Tana ganin su Nasmat a shimfide ta rude nan-da-nan ta fara kwallawa su Mama asiya kira. Suma da gudu suka sakko downstairs din suna tambayar me akayi.Zuwaira ta nuna musu Asmart da yatsa. Ai da sauri hauwa ta dakko ruwa mai sanyi aka fara yayafa musu._
_Duk wacce ta farfado sai ta kankame ta kusa da ita a firgice suna sambatu da ambatan sunan Fatima. Mama Asiya da duk ta rude take tamabay me akayi. Hauwa tace, "Ni dai dazun na barsu nan lokacin Asmart zata daki Fatima shine na dakatar da ita na fada musu cewa Fatima nada aljanu. Shine har suke karyata ni. Sannan kuma Fatima ta zare socket tace duk wanda ya mayar zatayi maganin sa". Hauwa ta kalle gurin socket din taga an mayar, "Af! Socket din suka mayar ai yanzu gashi sun jawa kansu". Mama Asiya cikin masifa ta fara magana. "To Wallahi bazai yuyu ba. Dole a dauki mataki Wallahi ko in bar gidan nan yau. Haba ya zan tsaya ina kallo aljanun Fatima su kashe min yara. Bari in kira alhajin shima da yaje yayi zaman shi a kasar mutane kamar can aka yanke mai cibi". Da sauri ta koma daki ta daukko wayar ta kira Alhaji. Ko gaisawa basuyi ba ta fara binshi da masifa take gaya mishi duk abunda ke faru. Alhaji kuwa wufantar da zancen yayi. Yake cewa. "Wato Asiya kuma ta nan zaki bullo wa Yarinyar nan ashe har yanxu wannan zaluncin da kike wa Fatima baki daina ba. In banda karya da sharri ya zaki ce wai Fatima ta addabi gida kaza-da-kaza?". Mama Asiya cikin masifa ta kara kai'mi. "Au! Abun da zaka ce kenan. To Wallahi in haka ne zan tatara yarana in tafi da su gidan mu. Haba ina dalili yaseen bazan yarda Aljanu su kashe min yara ba. Yanzu haka ga su Asmart nan rai hannu Allah Aljanu sun dadake su duk sun ji musu ciwo". Daga can alhaji yayi magana da alamun shima ya fusata. "To naji zaki iya tafiyar ki amma karki sake ki fitar min da yaro ko daya. Ke in ban isa inyi iko dake ba ai na isa inyi da yara na. Kuma in sha Allah wannan juma'ar zan dawo sauran inga kuma ba dai-dai ba. Ko inji Fatima tace min zalumtar ta kuke. Wallahi da sai na dau kwakwaran mataki wanda bazai miki dadi ba". Yana fadar haka ya kashe wayar._
_Tsaki mama Asiya taja, "Wato kai kana can ka bar mu da Aljana na neman sabautamu". Haka dai gidan ya wuni cikin dar-dar, Fatima kam ta zama abar tsoro dan in tazo waje gaba daya sai suyi tsit. Da dare da kyar suka yarda da su kwanta a dakinsu. Wajen karfe 11 na dare Fatima ta tashi ta tafi sama mama Asiya na barci taji ana tashin ta. Tana farkawa kuwa taga Fatima. "Fatima me akayi kike tayar dani tsakar daren nan?". Mama Asiya take maganar cike da tsoro. "Murya na fitowa biyu-biyu Fatima tace, "A nan zan kwana dan haka ki tashi ki koma falo ki kwanta". Mama Asiya na karkarwa ta tashi ta yayimi bargo ta fita a dakin. Tun kafin ta sakko daga kan matakalar ta hangi mutum a zaune a falo mace ce kin bakaken kaya. Ta juya mata baya........................................._
🏃🏻🏃🏻🏃🏻🏃🏻🏃🏻 A dakace ni yaseen na gaji🙊
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 105-106
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
📚 _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*DEDICATED TO YOU* 😁
QUEEN HAUCY
MINEERT
AMÆL
SALMAH
MINEERT
QUEEN MEIMIE
PHATEEMA
MARYAMU 🙊
MUHIEVER INDIA
❤ KUNA A RAINA KU DIN NA DABAN NE A HEAR DIN KIN. 💃🏻 INA SANKU MASOYANA. ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Mama Asiya na karkarwa ta tashi ta yayimi bargo ta fita a dakin. Tun kafin ta sakko daga kan matakalar ta hangi mutum a zaune a falo mace ce kin bakaken kaya. Ta juya mata baya.~
_Cikin muryar tsoro mama Asiya ke magana. "Wacece?. Waye a nan?". Shiru bata amsa ba. Kara matsawa tayi tsoran ta na dada karuwa. Sai tambya take amma anyi mata shiru. Nan ta tsaya tana sake-saken ta juya ko kuwa ta karasa. Zuciyar ta ce ta bata shawarar cewa taje ta gane wa idan ta waye a zaune. Gwara nan da can din wajen Fatima. Cikin Kwarin gwiwa ta nufi wajen matar ta dan kauda tsoran ranta. "Waye-waye". Ta kara tambaya firgigit matar ta juyo Hauwa ce, da alamu gyan-gyadi take. Mama Asiya na ganin Hauwa ce tace, "Hauwa wannan wane irin kaniya ce. Kina ji ina miki magana kika share ni, Wallahi har kin bani tsoro". Hauwq na murza ido tace, "Ni wallahi cikin barci ne ma naji kiran ki". Mama asiya tac, "To ke kuma wace uwar ta dawo dake falo ga dakin ki can kin baro?". Hauwa ta waiga baya alamun marar gaskiya. Murya kasa-kasa tace "Wallahi Fatima ce ta bini daki ta koro ni wai in dawo falo ita zata kwanta a dakin". Zagayawa mama Asiya tayi ta zauna._
_Cikin rada mama Asiya tace, "Taf! Di jam, Kika ce Fatima ce ta koro ki". "Eh Wallahi ita ce, Yanzu haka tana can saman gado na tayi kwanciyar ta". "To Fatima aljanun nata ko har sun fara raba ta gida biyu ne?. Domin yanzu ta koro ni fa daga daki na wai...". Sautin saukkowar da suka ji daga stairs ne ysa mama Asiya bata karashe maganar da ta fara ba. Suka juya su biyun suka zura wa wajen ido dan ganin wanda zai sakko. Ba kowa bane Zuwaira ce itama rike da bargon ta a hannu kamar almajirin da ya fito rani. Mamaki ne ya kama ta ganin su Asiya a falo. "Aunty Asiya, Me kuma kuke yi a falo". Zuwaira ke tambay. Asiya tace, "Ai ke ya kamata mu tambayi me ya fito dake daga dakin ki da tsakar daran nan harda kwaso blanket". Zuwaira ta juya baya tukun tayi kasa da murya tace, "Aljanun Fatima ne suka koro ni. Wai fa dan daukar alhaki ina kwance abuna sai ji nayi ana tayar dani, Bayan na bude ido naga Fatima ce, Kar kuso kuji cikin irin muryar da take magana. Da shi abar tsoro shine ta koro ni falo". Su mama asiya suka ce ai sai kizo ki hau layi domin muma nan da kike gani ita ta koro mu". Zuwaira tace, "A gaskiya ya kamata mu dauki mataki haba Aljanu ma ai suna da maganin". Asiya tace, "Rage murya kar su jiki, Dan Wallahi yanzu zakiji ana gaura miki mari". Da sauri Zuwaira ta matse bakin ta da hannaye. Bayan sun baje a falo. mama asiya tace, "Nasan matakin da zan dauka. Ku bari gobe zan gaya muku"._
_Washe gari tun da asuba kafin su mama Asiya su tashi daga barci, Fatima taje ta debo ruwa a waje mai shegen sanyi. Nan tazo ta fara kwara musu. Gaba daya a gigice suka ringa tashi. Suna tashi suka ganta zaune kan 3Stars tana musu dariyar mugunta. Daga bisani ta bata rai tace, "Maza ku tashi aje ayi sallah sannan a zo a shiga kitchen". Suna rawar dari suka tashi ko wacce ta nufi dakin ta dan yin sallah. Fatima ta tashi ta shiga dakin su, Nasmat, Ameera da sauran yaran sai barci suke abun su. Fiddausi ce kadai ta tarar kan sallaya tana karatu. Da sauri Fatima ta koma ta kara debo ruwa ta zo ta dingi watsa musu tana tashin su suje suyi sallah. Ameera watsa mata ruwan da akayi, abun yayi matukar bata mata rai. A fusace ta nufi Fatima, Batayi wata-wata ba ta kwasa mata mari. Sannan ta dora da fada, Yayin da ita kuma Fatima ta sadda kai kasa. "Ke Fatima bar ganin ana cewa wani kina da Aljanu. Wallahi ni ba raga miki zan ba. Aljanun banza, Shikenan dan kina da Aljanu sai kita takura wa mutane. Miye zaki wani watsa wa mutane ruwan sanyi da safiyar nan. Anki ayi sallahr". Firgigita Fatima ta dago kai. Dagowar da tayi idanun ta sun koma kamar garwashi har wani tartsatsin wuta ke fita a idan. Gabaki daya mutanan dakin sai da suka tsorata. Su Asmart kam kankame juna sukayi hade da runtse idanu. Fiddausi kanta da take karatu abun ya firgitata. Nan take ta fara karatun da karfi tana tofawa saitin Fatima. Fatima bata kula ba. Hannu ta mika saitin Ameera dake baya-baya a tsorace kamar tayi kuka. Ameera sai ji tayi an shake mata wuya. An dage ta sama ba tare da subga wanda ya daga tan ba. Sai da aka wul-wulata kafin aka mako ta kasa._
_Sa'arta daya kan katifa ta fado. Fatima cikin wata murya mai zaburar wa tace, "Maza kafin in kirga goma kowa yaje yayi alwala,.....1....2..". Ai da gudu aka ringa rige-rigen shiga ban daki dan yo alwala. Bayan sun yo alwalar sun fito kuma sai sukaga fatiman bata nan. Daki-daki.Fatima tabi ta tattaro su mama Asiya aka shiga kitchen domin hada abun kari. Tukun taje dakin Abba ta tayar da shi shima yayi sallah. Har ya fara mata magiya a kan ta mikar mai da dayan hannun shi, Ta daka mai tsawa hakan yasa ya kyale ta. Su mama Asiya sunji jiki sosai yau a Kitchen, Domin kamar yanda suke wa Fatima. "Dake wannan kul-kula wancan kwashe can gyara nan", A da. Haka itama Fatima yau ta ringa juyasu, kamar ta sama bayin ta. Haka wajen cin abinci ta ringa bada doka. Domin ko katuwar loka taga mutum yayi sai ta kwala mishi Cokali. Gaba dayan gidan kuwa tsoranta karuwa yake a gare su. Ana gama cin abinci Fatima tace to masu zuwa islamiyya a tashi ayi shiru, Ku kuma matan gida a gyara gida shara wanke-wanke da goge-goge. Tana fadar haka ta wuce daki. Yayin da suma masu zuwa islamiyyar tuni sun fece sun bar wajen. Mama Asiya ta rike baki alamun mamaki "Oh! Duniya kowa ya sama waje sai kiga ya baje kolin shi. Yanzu dai ga Fatima aljanu sun sata tana mana iskancin yanda taga dama kamar mu yaranta ne"._
_"Ke dai bari wannan abun takaici. Ya muka iya haka zamuyi hakuri mu jure har Alh. Ya dawo muga irin matakin da zai dauka". Cewar Zuwaira. Asiya ce ta katse mata hanzari ta hanyar cewa. "Kai aradu bazamu jira har sai ya dawo ba. Yau fa laraba kuma shi yace sai ya kai juma'a tukun zai zo, Dan haka yau zamuyi maganin abun ku dai bari wannan aljanar ta tafi makaranta tukun". Nan suka fara share-share suna kakauda kayan da suka ci abincin. Ba'a jima ba sai ga fiddausi da Fatima sun fito cikin uniform din islamiyya. Wani dan iskan kallo fatima ta jefa wa su mama Asiya kafin tace, "Ai na dauka da bazakuyi abun da na saka ku ba"._
_Tana fadar haka bata ko jira sun tanka ba ta kama hannun Fiddausi suka fita. Ita dai Fiddausi duk a tsorace take da Fatima gudu take cutar da ita. Bayan yara duk sun tafi makaranta su mama asiya suka shirya mama asiya tace musu malami zasu je su samo yayi masu Ruqiya ya fitar da aljanun. Gaba daya suka amince da haka. Ga motar alhaji amma suka fita a kasa. Kasancewar a cikin su ba wacce ta iya mota. Suna tafe har sun kusan barin layin sukayi kicibus da wata mata da alamu yar anguwar su ce, Tafe take tana rausaya kamar wata budurawa, Ba hijab bane a jikin ta gyale ne ta dan yafa a kafada. Fuskar tasha hudar wacce zan iya ce muku har taso tayi yawa. Cingum ne a bakin ta tana tauna lips din yasha jan baki. Da gani kasan yar duniya ce. "Asiya Anguwa za'a fita, Da safiyar nan?". Washe baki su Asiya sukayi "Eh wllh Nafisa daga ina haka". Asiya ta fada. Matar tace Wallahi naje sayo abu ne. Ina zaku je haka". Asiya ta kwashe duk abunda ke faruwa ta fada mata. Rike baki nafisar tayi hade da cewa "Aljana fa kika ce?. Tabb! To yanzu ina zaku sama malami". Mama asiya tace "Aa gamu dai mun fito da wajen limamin masallacin jama'a zamuje watakil a dace". Nafisa ta roke baki "ah! Liman to bari kuji in gaya liman ba abunda zai muku. Sai dai yace kuje kuci gaba da addu'a. Amma akwai wani malami da na sani ya kware wajen fitar da aljanu, In kun amince na hutar daku ni zanje in kawo muku shi har gida"................................._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 107-108
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
📚 _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
SAI NA AURE TA
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
ωяιттєи ву:
shamsia salis
Eloquence Writers Association
____________________________________
Na tayaki murnar Autar Eloquence. Allah ya kara basira. Allah yasa mu amfana da darrusan cikin littafin amin
____________________________________
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Amma akwai wani malami da na sani ya kware wajen fitar da aljanu, In kun amince na hutar daku ni zanje in kawo muku shi har gida".~
_Su Zuwaira sukace "ba dai boka ne ba ko?". Nafisat tace "Aa ko daya wannan shahararren malami ne. In kun amince yanzu ma daga nan bazan karasa gida ba sai in juya in daukko muku shi". Mama Asiya tace "To shikenan je sanar wa mai gidan ki to sai kizo ki karba kudin mota, ko kusa ne?". "Aa Wallahi can wani kauye ne kudin motar mutum biyu Dubu daya ne. Dubu biyu zuwa da dawowo. Batun mai gida kuma da kike. Dallah rabu dashi miye na sai naje na gaya mishi". Hauwa da Zuwaira tabe baki sukayi suna kallan Nafisa din. Asiya bata ce komai ba ta fiddo dubu uku a handbag dinta ta bawa Nafisa "Gashi kije ki daukko shi muna jiranshi. Mu in dai zai cire mana wannan Aljanar to ko nawa ne zamu iya bashi". Ta juya ta kalle su Zuwaira "Ko ya kukace yan uwa". Da sauri suka ce "Kwarai kuwa ko nawa ne zamu iya badawa mu dai gurin mu ta bar gidan". Nafisa tace "Karku damu aikin wannan malamin sha yanzu magani yanzu ne". Su Asiya suka juyo suka koma gida inda ita kuma Nafisa ta tsayar da napep ta hau tace a kai ta Sabon layi, Daga anguwar su nan naira saba'in ne. Tana sauka ta nufi wata kofar gida wanda kofar gidan wasu samari ne ke zaune ba abunda suke sai busa sigari da gulmar masu wucewa kan hanya. "Sannun ku dai dan Allah Aliyu ko ta bare yana gida". Gudan ya kalle ta yace "wani abu yayi mike ne?. Ko dai yayi tsiyar ne". Nafisat tace "Ba abunda ya min ni dai kawai ina neman shi ne in yana nan". Dayan yace mata "Yaje can sama wajen wata cuwa-cuwar sa amma yanzu zakigan shi ya dawo". "To na gode". Nafisat tace ta koma gife tana jiran Ko ta bare. (Sunan da ake kiran aliyu kenan). Bata jima a wajen ba ta hange shi ya taho, Duk da kasancewar shi dattijo hakan bazai hana ka gane cewa dan duniya bane. Yana hango nafisat ya fara wasa ta yana mata kirari.
"Kaga shegiyar uwa mai saka 'ya'ya biyayyar dole, Kaga kaska rabi mai jini wanda ke da dan kadan ma abishi a tsotse. Ke ba maciji ba kinfi macijin dafi. Da ganin nasan bakin ki a kwai batu. Dan banza bata kai zomo kasuwa._
_Kuma Wallahi da kaga kura ta ba nama ka tabbata ba dan Allah ta barshi ba. Yanzu dai miye labari ne". Nafisa kam kallo kawai take binshi da shi tana murmushi domin ita da shi kar ta san kar ne. Daya baya neman daya sai za'a aikata wani mugun abun wanda za'a dan fizgi wani abu a ciki. Tana yar dariya tace "Shege Ko ta bare, Wato ka san dai in ka ganni gidan ka ba banza ba". Yace "Eh mana ai nasan bazaki taba wanke kafafun ki takasan ki kawo min ziyara ba. Da gani nasan akwai wata harkar ne". "Tabbas kuwa akwai babbar harkar. Wacce in dai ka yarda zakayi nake gaya ma zamu sma kudi sosai". Aliyun yace "Gaya min mana kinsan fa ni dan kasada ne bakiji suna na bama. Ai kawai ko miye na zanyi in dai za'a sama yan karafa". Nafisat tace "Yauwa mutumina. To dama can wasu makwabtan mu ne suka neman za'a fitar musu da aljanu, kuma gidan masu kudi ne. Watakil ma ba wani Aljani kawai firgitane suke. Shine wai na hadi da su a hanya zasu je neman malami mai fidda Aljanu to kawqi ganin za'a sama wani abu shiyasa ma wannan shawarar ta zo mun". Tsuru ya tsare ta da ido yana mata kallan yan iska. Lura da hakan yasa tace "Kai malam bana san wulakanci ya zaka wani zura mun na mujiya. Ko naci ban biya bane".
A fusace yace,"Ina fa kika biya, ai bansan dan banza kika dauke ni ba sai yau". Cikin rashin fahimat da neman karin haske tace, "Ban gane na dauke ka dan iska ba?". "Kwarai kin dauke ni dan iska tunda. Har wai ni zaki ce naje na cire Aljanu. Yo na cire Aljani ko kuma Aljani ya cire ni". Kwashewa da dariya Nafisa tayi, Zuwa can kuma ta dan tsakaita hade da cewa,"Ko ta bare, wallahi ban taba sanin kai mugun matsoraci ne ba sai yau". "Aa ba tsoro bane, ai gaskiya ne. Duk iskancina ai bazanyi wa Aljani ba.kinsan ance aikin guguwa ta dau kara da karmami, bata shiga rumbu ta dauko dammunan hatsi". Nafisat tace, "To kwantar da hankalin ka. Wannan kar ya dame ka, dan bana tunanin aljanun gaske ne. Ni ina tunanin ma kag'e ne sukeyi mata". Aliyu ko ta bare yace,"Au! Kina tunanin ba aljanun bane". Nafisa tace,"Kwarai ba Aljanu bane iskancin sune kawo irin na masu kudi". Ko ta bare yace, "To in dai haka ne na amince". "Yauwa ko kai fa. To yanzu abunda za ayi shine, ka shiga gida ka sako fararen kaya sababbi, masu babbar riga da katan charbi sannan ka fito muga ko kayi kama da malami. Dan in bakayi kama da malami ba wallahi wani zan nema in sashi wannan aikin". Gemun shi yaja hade da cewa,"Haba ai ni din nan da kike gani in nasha manyan kaya bazaki iya banbanta mu da limamin anguwar ku ba. Yanzu bari in sako kayan sallah na". Ciki ya shiga ya sako shadda ce fara kal har dauka ido take, yasha malum-malum ga hula zannah. Matsalar daya baya da charbi. Nafisat na ganin shi tace komai yayi. Nan yake gaya mata cewa bashi da charbi. Nafisat tace ba komai suje kasuwA._„
_Nan take suka nufi kasuwa ta sayo mai katan charbi hade da wasu turaruka. Ya fashe jikin sa sai kanshi yake kamar sabon ango. Sun taho a hanya Nafisa ke tsara mishi yanda zaiyi take fada mai sunce Yarinya ce karama mai aljanun dan haka abunda zaiyi shine yace a saka su daki daya su kwana idan yaga asuba ta kusa kawai sai ya shake yarinyar ta suma. In yaso da asuba sai yace ya gama fitar da aljanun a sallame shi sai ya gudu. Fashewa yayi da dariya yace ya fahimta. Bayan sun kamalla duk shirin su suka nufi gidan. Nafisa ta fara shiga ta sanar musu gashi ta zo da malamin, Su mama Asiya suka ce ta shigo da shi ciki. Makeken carbi ne a hannun shi yana ja bakin shi na motsi ka rantse da Allah kace tasbihi yake, Alhalin shi kanshi bai san abunda yake fada ba kawai motsa bakin ne. Da shigowar shi falon ya kwashi kamshi. Su Asiya na ganin shi suka zube kasa cikin ladabi da girmamawa. Nafisa a ladabce ta nuna mishi 1star tace ya zauna. Da bismillah ya zauna nan take su Mama Asiya suka fara kwasar gaisuwa. bayan ya gama gaisawa yayi hamdala tukun ya fara daga kai yana kare wa falon kallo sama da kasa yana jijiga kai alamun a kwai magana. Cikin ladabi Nafisat tace "Malam me ke faruwa?. ko aljanun ne". Gyaran murya yayi tukun ya kalli mama Asiya yake cewa sunyi sakaci da har suka bari Aljanu suka cika musu gida haka. Cikin hanzari ya nuna wani bangare a falo, kunga ga fatalwa can ma ta fito daga dakin can zata gudu. Kunsan fa aljanu ko fatalwu basa yarda su hada wajen zama dani in dai ba masu shegen taurin kai ba. Su Mama Asiya kallan wajen da ya nuna sukayi wayam ba kowa, Zuwaira tace,"Allah shi gafarta malam fatalwar da ta gudu yanzu mace ce ko namiji?". "Mace ce gata can fara ce kuma siririya". Sallalami suka fara gabaki dayan su. Nafisat ta tambaya me suke wa sallalami, mama Asiya tace, "Kin manta kishiyar mu uwar Fatima wacce ta mutu". Nafisat tace "Na tuna ta, ko kuna tunanin itac fatalwar?". Zuwaira tace, "Kwarai ita muke zargi domin aljanun ma duk a kan yarta Fatima suka tare". Aliyu yace, "Ba mamaki itace, Domin kuwa nayi mamakin ganin gadajen Aljanu ba adadi a tsakar gidan nan. Wannan ke tabbatar min da cewa Aljanu da yawa ne ke rayuwa a gidan nan". Asiya ta kalle shi hade da cewa, "To yanzu malam miye abun yi"._
_"Karku daga hankulan ku tunda dai gani nan na zo yau-yau sai na kore duk aljanun gidan nan. Dan haka yanzu ku kawo min yarinyar mai suna Fatima da kuke zargin ko yar fatalwar can ce". "Ai suna makaranta. Amma sun kusan dawowa". Inji Hauwa da sai yanzu tayi magana. Aliyu tace, "To ai shikenan bari mu jira ta ta dawo. Dan in san ta inda zan faro". Mama asiya tace, "Yauwa Allah shi gafarta malam, Akwai wani dana mai suna Abba da Fatima ta lankwasar mishi da hannu. Munyi-munyi taki ta mikar mishi da hannun". Aliyu yace,"Ina yake ku kawo shi inga". Hauwa ta tashi da sauri ta nufi dakin Abba ta kirawo shi. Yana zuwq ya zube gaban malam yayi gaisuwa. Bayan Aliyu ya amsa, yace Abba ya miko mai makalallen hannu. Ba gardama Abba ya mika mishi. Malam Aliyu ya ware karfin shi yasa hannaye biyu yaja hannun da niyar ya mikar da shi ta karfi. Ihu! Abba ya kwada hade da cewa. "Wayyo zai karya min hannu". Malam na jin haka yayi saurin sakin shi. Ana cikin haka sai ga Fatima da Fiddausi sun dawo daga islamiyya. Da shigowar su falon, Fatima ta fara hararen malam aliyu ko ta bare.......…………………………………………………………_
🤔 Lalai Malam Aliyu cire Aljanu da kyau 😂😂😂
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
Page 109-110
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
📚 _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*KARSHEN PAGEN BAYA*
"Wayyo zai karya min hannu". Malam na jin haka yayi saurin sakin shi. Ana cikin haka sai ga Fatima da Fiddausi sun dawo daga islamiyya. Da shigowar su falon, Fatima ta fara hararen malam aliyu ko ta bare.~
_Tunda yaga tana zare mai ido ya gane cewa itace Fatima hakan yasa yayi saurin mikewa tsaye yana kallanta yana tofe-tofe. Su Zuwaira sukayi saurin mikewa suma. suna cewa, "Yauwa malam itace wannan din". Malam yace ai ba sai kun gaya min ba. Domin tana shigowa naga Aljanu da ifiritai kusan million a tare da ita. Amma ni naga ma kokarin ku da har kuke iya kwana a gidan nan. Shin wai basa baku tsoro ne". Zuwaira tayi sauri tace,"Ai ba tsoro kadai bama har da duka. Mu dai malam ka taimaka". Aliyu yace,"Karku damu, Yau bazan bar Aljani ko daya ba a gidan nan. Amma aikin ku fa nada wahala sosai gaskiya domin ma yau ta kama dole ma sai na kwana a gidan nan". Gaba saya suka ce ba damuwa su dai gurin su a fitar da aljanu. Nafisat kallo kawai take bin Aliyu da shi.Yanda ya takarkare yana zuga karya wa su mama Asiya. Kamar wani malamin kwarai._
_Fatima da Fiddausi basu wani tsaya sauraren su ba. Kai tsaye dakin su suka wuce. Malam na kiran Fatima! Fatima! Ko wai-wayen shi batayi ba. Balle ya sa ran zata juyo. Zaunawa yayi yace da su mama asiya yana bukatar kayan aiki. Domin yanzu zai fara. Su mama Asiya suka tambaye shi dame-dame yake bukata. Nan yake gaya musu cewa Yanzu dai yana bukatar daki guda. Sannan a sayo soyayyun kaji amma a tabbatar da farare ne.yaci gaba sa ce musu a samo abinci kamar fillet biyar pure water leda daya. Domin ina so zan kafawa Aljanun gidan nan tarko ne dan akwai masu shegen gudu. Wanda zan kama ta dalilin abincin nan. Sai da ya gama lissafin shi su mama asiya suka tura mai gadi yaje ya hado duk abuda malam ya bukata. Dakin da aka ware mai yace a kai kayayyakin. Sannan ya tashi ya shiga dakin hade da ce musu yana zuwa. Wani mugun kallo Nafisa tabi shi da shi. Wato sai yanzu ta idasa gano tantirancin Ko ta bare. Asiya tace "Mu ko nawa ne zamu iya kashewa, in dai za'a fitar da Aljanun nan"._
_Nafisa tace,"Karku damu ai in dai wannan malamin ne bani da shakka a kanshi. Aikin shi kenan kama Aljanu". Su mama asiya sukace Allah yasa su fita domin kuwa yan taurin kai ne. Aliyu na shiga dakin ya fara debar girki sanda yaci abinci sosai yaci ya koshi yaci nama san ranshi tukun ya sha ruwa ya goge bakin shi. Filet biyu ko wanne da kaza a kai ya fito da su yana tofe a ciki. Kamar mai addu'a da gaske. Yace wa su mama asiya su sa a daukko sauran abincin da naman a kai bayan dakunan amma a rufe. Yake cewa yasan aljanu da shegen kwadayi suna zuwa dauka zasu makale. Dan karfin addu'ar da yayi a ciki. Su mama asiya da kansu suka shiga suka dakko sauran abincin sunyi mamakin ganin anci abincin har hauwa ta kasa daure wa da ta tambaye shi. Sai yace Aljana ce taci lokacin da mai gadi ya kai su. Wai kafin ya karasa Aljanar taci kuma ma wai ya kashe ta._
_Haka dai suka raraba abin cin nan harda ruwan. Duk abunda suke mai gadi na kallan su ga muguwar yunwa da yake ji. Nafisa kuwa banda harara ba abunda take aikawa Aliyu. Waje ya samu ya zauna a falo aka kunna fanka aka kawo gaban shi aka kuma kawo abinci da lemu. Malam yace ai shi ya koshi domin Aljanu ke kawo mishi abinci duk lokacin da ya bukata. Baici ba sai Nafisa aka bawa ta cinye. Yana nan gidan har dare yayi ita kuwa Nafisa sallama tayi musu a kan cewa gobe zata dawo.Aliyu Da yaga ish'i tayi sai ya faki idanun mutane ya zagaya bayan daki wajen abincin nan yana zuwa yaga duk an cicinye naman nan haka abincin ma duk an babata gun. Daga can yaga wani flat din wanda ba'a taba ba. Sai da yaci ya koshi tukun ya goge bakin shi yaje yace wa su mama asiya suzo su gani. Suna zuwa sukaga duk anci abincin nan an rage wani wajen an fara cin cinya an yar. Ruwan ma duk an fafasa anyi wasa da shi. Tambayar shi sukayi a kan waya ci abincin. Nan ya karkace hula ya fara zabga musu karya wai ai Aljanu ne sukaci addu'ar da yayi ne ya manta baiyi bismillah ba shiyasa wai Aljanun da suma zo ci basu makale ba. Su Asmart najin haka suka kyal-kyale da Dariya. Su mama Asiya suka tambaya me suke wa Dariya. Basu bada amsa ba suka ci gaba da dariyar hakan yasa Zuwaira taji haushi ta kora su da gudu suka koma falo suna daria. Nasmat taks cewa Asmart ita gaskiya bata yarda da mutumin nan ba.wai tana zargin ko ba malamin gaske bane. Asmart kam cewa tayi, "Au ke ashe zargi ma kike?. Kina gani fa gashi kiri-kiri ya maka karya. Wai yace Aljanu sukaci abincin bayan kuma mu muka ci". Nasmat ta kyalkyale da Dariya Dariya tace,"Watakil mune aljanun". Asamrt tace,"Yanzu mu rufa mishi asiri ne ko kuwa?". "Kyale shi muga iya gudun ruwanshi tukun. Ba dai yace zai cire Aljanun Fatima ba yau". Dariya Asmart tayi hade da cewa."Ai kuwa dai mu rufa mai asiri zuwa goben mu gani"._
_Acan kuwa su amam asiya suka cewa malam ya yake ganin za'ayi. Ce musu yayi shi yasan yanda zaiyi wai in ya kama aljanun Fatima zasu kawo mai sauran. Falo suka dawo aka kawo mishi abinci nan ma yace ya koshi wai Aljana ta kawo mishi yaci. Fatima yasa aka kawo mai gaban shi nan yata tofe ta da miyau kallan shi kawai take yi tana hararen shi ba tare da tayi magana ba. Da abun ya bashi haushi sai ya fara kashe ta da mari yan cewa tayi magana. Su mama asiya suke cewa mai yasa yake dukan ta. Sai yace musu ba ita yake duka ba Aljanun ne wai dama yasan sai sun mishi garda. Nan yata jifgar Fatima amma taki cewa ko uffan!. Wajejan karfe goma na dare Aliyu yace a kai Fatima daki domin a can zaiyi aikin kuma yace a daren duk tauri kan aljanun sai ya cire su. Daki aka kai ta ya shiga ya kulle bayan yace wa kowa ya shiga daki ya rufe. Bayan Ya musu gargadin kar wanda ya fito ko da fitsari ne. Gado ya dale abu shi ya kalle Fatima dake tsaye tana zare mai idanu yake ce mata in kinga dama ki zauna ko ki kwana a tsaye ma ni ba ruwa na. Barci yake abun shi har da munshari. Can cikin barci yayi mafarkin wasu mugayen halitu masu ban tsoro gasu da girma sukata tsorata shi suna firgiya shi daga karshe suka kai shi wajen wata yarinya da ba kai a jikinta sai iya gangar jikin. Hannun ta rike da wuka._
_Ko da yaga haka sai tsoro ya kara kama shi. Wannan halittun suka kai shi gaban ta bata jira komai ba ta daga takobin ta jaka mai a ciki. Da cakawa ya farka firgigita. Ya tashi da ihu mai makon yayi addu'a. Fatima ya gani tsaye yanda ya barta lokacin da ya kwanta har yanzu haka take bata ko motsa ba. Kasancewar dakin da hasken dake akwai nepa. Ya kalli agogon dake makale a bangon dakin yaga karfe biyu. Ya juya gax. Fatima da niyar yi mata magana. Wayam yaga wajen ba kowa. Dube-dube ya kamayi. Ya sakko kasa yan kiran sunanta dake yaji an fada mai. Ya duduba duk inda yake tunani bai ganta ba. Sai karkashin gado. Yana lekawa da nufin yaga ko ta na nan yaji an rike mishi kai. Ihu! Ya farayi yana neman agaji. Jan kan nashi ake shima yana iya kokarin shi yana neman ya kwace amma ya gaza. Sai da yasha wuya sosai tukun aka sake shi. Da sauri ya yashi ya koma kan gado ya lulube da bargo yana lumfashi day-day. Dif! Yaga wutar dakin ta dauke. Nan take kuma yaji dakin ya gauraye da wata ibilishiyar dariya wacce kunnuwanka bazasu iya sanar da kai inda take fitowa ba. Domin in kaji Dariyar sai kace gaba daya ma dakin ne da kanshi yake dariyar. Ga dariyar ba dadin saurare. Aliyu yasa hannuwa ya toshe kunnuwa hade da kara dukun-kunewa. Kiii! Yaji an kama kafar shi an jawo shi kasa cikin duhu ya mike tsaye yana lalube-lalube. Can yaji ya dafo wani abu kamar mutum mari aka dauke shi da shi wanda karfin marin yasa har sai da ya wuntsila. Ihu! Ya kwalla mai uban kara ya fara bada hakuri. Wata dariyar ta kara kaurade dakin. Ba tare da hasken dakin ya dawo ba ya kara mike wa tsaye. Kamar iska ya kwashe shi yaji an maka shi da bango. Kafin ya yunkura ya dawo yaji an kara fisgar shi an maka da kasa. Ji yayi kamar bayanshi ya karye. Ihu ya fara kwallawa va kaf!-kaftawa su Zuwaira na dakunan su sai da karar ihun ya tashe su. Su kuwa basu kawo a ransu cewa malam ne ke ihu ba. Su wai zatan su aljanu ne. Hakan yasa suke kara dukunkunewa.........................................................._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
*Before last Page 112-113*
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
📚 _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
❤ DEDICATED TO MASOYAN LABARIN *ALJANAR FATIMA* ❤
🤗 Kun taka rawar gani a yaba ba kadan ba. Masu bibiyar labarin nan. Dole nayi jinjina na kuma yi muki fatan alkhairi masoya na. Hakika in baku bazan iya ba. Allah shi bar kauna. Safuratu na bankwana *HAUSAWA NA CEWA A JURI ZUWA RAFI. WATARAN TULU YA FASHE.* 🌝
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ihu ya fara kwallawa va kaf!-kaftawa su Zuwaira na dakunan su sai da karar ihun ya tashe su. Su kuwa basu kawo a ransu cewa malam ne ke ihu ba. Su wai zatan su aljanu ne. Hakan yasa suke kara dukunkunewa.~
_Haka Fatima taci gaba da tsorata malam Aliyu tana bashi wahala. Kafin safe sai da ta sumar da shi.Har Waje-jen karfe bakwai su mama Asiya basuga malam ya fito ba balle suji ya akayi. Nan wasu ke cewa aje a bude a gani. wasu kuwa cewa suke abar shi watakil aikin ne bai gama ba. Suna zazane a falo bayan sun karya sai ganin Fatima sukayi ta fito daga dakin ranta a bace. Fuskar ba wal-wala. Batayi wa kowa magana ba. haka kuma ba wanda yayi mata magana, Taje ta shiga dakin su jimawa kadan sai ta fito. Tana zuwa ta makore wuyan mama Asiya da karfe. Ba tare da tace mata komai ba. Mama Asiya tayi iya kar kokarin ta ta kasa kwabcewa. Sai da ta nemi agaji tukun da kyar sauran jama'ar suka kwace ta. Ana kankare ta daga nan ta sake shake wuyan Hauwa nan ma da kyar aka kwace ta. Nan fa ta shiga layi daga an rabata da wannan sai ta malale wa wannan. Kuma shakar da take bana wasa ba._
_Dan ji zakayi kamar wani Rikakken gardi ne ya shake ka. Kuma kafin a kwace kaji jiki. Da gudu su nasmat suka fita waje aka nemo mutane. Aka daure Fatima da kyar. Domin su kansu masu daure tan sunji jiki. Wasu duk tajiji musu ciwo. A nan falo aka hadata da karfen jikin Matatakala (Stairs) aka daure ta. "Duk sai na kashe ku ranar da na kunci". Abunda ke fita daga bakin Fatima kenan. Bayan hankalin yan gidan ya dan kwanta ne. Su mama Asiya suka tuna da aliyu. Da sauri suka nufi dakin kwance suka tarar da shi har lokacin a sume. Aka kawo ruwa aka yayafa mishi a firgice ya tashi yana raraba ido. Yana mikewa ya zabga a guje Kamar wani sabon mahaukaci. Ana kiran shi ko waigowa baiba. Da ya isa falo yaga Fatima a daure na hararen shi sai ya kara kaimi wajen guduwa. Asmart da Nasmat dariya kawai suke su. Zuwaira ta daka musu tsawa take tambayar su miye na dariya. Nan suke gaya wa mutane cewa Da gani Aliyu malamin karya ne. Nan suke fadar cewa su suka ci abincin da Aliyu yace Aljanu ne suka ci. Sallalami su Asiya suka kwasa. Zuwaira ke cewa in kuwa haka ne sai sunyi maganin Nafisa. Asiya tace "Ai ba wani ba wata zuwa zamuyi ta biya mu duk kudin da muka kashe kawai"._
_Zuwa sukayi suka same ta da masifa. Da kyar suka kankaro dubu uku a gunta. Haka Fatima ta kasance a gun a daure abinci ma hanata suka ringa yi sai dai fiddausi ta bata a sace. Abba kuwa har yanzu hannnun shi daya a makale. Sunyi-sunyi Fatima taki gyara mai hannu. Su Asiya duk a tsorace suke kullum fargabar kar Fatima ta kunce suke. Dan suna shan barazana da kashe di a gunta. Domin cewa take in dai aka kunce ta sai ta kashe mama Asiya Zuwaira da Hauwa. Hakan yasa ma suka gagauta kiran alhaji. Cewa yayi sharri suke mata. Hankalin shi bai tashi ba yaji ya matso ya dawo gida sai da yaji sunce sun daure Fatima. A lokacin ne yaje ba abunda yake so sai gida. Yau take juma'a ranar da Alhaji zai dawo. Tun da safe akata shirye-shirye aka gyara gidan tsaf!. Safiyanu da matar shi da yaran su uku sunzo. Haka ma Yusuf shida matar shi. Kowa yaci kwalliya in banda Fatima dake daure. Su Safiyanu da basu san me ke faruwa ba sai a lokacin suka tambaya mama asiya ta zauna ta shirya musu karya da gaskiya._
_Abba murna yake sosai domin yasan in dadyn su yazo dole Fatima ta mikar mai da hannu. Tun wajen sha biyu su Safiyanu suka yafi airport domin tarbo Alhaji. Sai wajen karfe uku jirgin su ya karaso. Suka runkuto a mota suka taho gida. Ba abunda yake tambaya sai Fatima. Haka da suka shigo gida duk iyalai sun fito kofar gida cik da farin ciki. Shi kanshi yaji dadin irin taryar da aka mai a tafiyar yan watanni kamar yaje yayi wani shekaru. Abunda ya rage mai farinciki shine kawai da baiga Fatima ba. Aliyu da Abdul suka shiga jidar kayan da Alhaji ya kawo suna shiga da ita. Alhaji na shiga falo sukayi ido hudu da Fatima dake daure jikin karfe. Ta fashe da kuka hade da fadin "Dady kaga yanda suka daure ni ko?". Hankalin shi a tashe ya nufe ta tausayi ya kama shi kamar ya fashe da kuka. Nan take yaji wani irin haushin su Mama Asiya. Kunce ta yaje ya farayi. Mama Asiya Zuwaira da Hauwa. Hankalin su yayi matukar tashi ganin abunda Alhajin ke shirin yi. Asiya da sauri tanufo shi tana hada shi da Allah karya kunce Fatima. Tsawa ya daka musu hade da cewa "mutanan banza marar tausayi. Wato abun naku har ya kai ku daure ta dan kunga uwar ta ta mutu ko?". Zuwaira da hauwa suma magiya suke binshi da shi akan ya hakura karya kunce Fatima ya saurare su amma. Yaki. Yana kunce Fatima ya warware mata igiyar dake jikin ta. Nan take suka rungume juna. Alhaji Salim tsabar tausayi sai da ya zubar da hawaye. Safuratu na ganin an kunce Fatimar sai ta koma jikinta. lokaci daya Alhaji yaji Fatima ta zabura ta kwace jikinta daga jikin shi kamar wacce aka tsinkula. Nan take idanunta sukayi jajur kamar wacce ta kwana tana kuka. Da gudu ta nufi kitchen kamar wata mahaukaciya. Bata jima ba akaga ta fito hannunta rike da wukA._
_Da gudu ta nufi su mama Asiya. Sa ganin haka sukayi waje da gudu. Fatima ta bisu. Alhaji Safiyanu da yusuf da sauran matasan da gudu aka bi su. Sai da kyar aka samu aka rike Fatima su mama Asiya kam har sun kusa fita daga layin sai da sukaga lala-lalai an rike ta an kwace wukar tukun suka juyo. Kusan karti biyar ne ke rike da Fatima amma sai juyasu take kamar wanda suka rike giwa. Hankalin Alhaji a tashe yasa aka nemo masu Ruq'yah. Bai wani bata lokaci ba malamin mai suna Bashir Halilu Tabiyyah. Ya karaso. Yana shiga ya tarar sai fama ake da Fatima ana rirrike ta. Kai tsaye ya nufi gunta ya tofa mata wasu addu'o'i. Yace su sake ta. Ba tare da gardama ba suka sake ta. Sunyi mamakin ganin ta tsaya cik ta natsu. lokacin su mama Asiya suka shigo. Kukan kura tayi ta warci wuka ta nufe............................................,..................._
🌝 Komai yayi farko zaiyi karshe 🤹🏻♂🤹🏽♂
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA. SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
👺👽👽👽👽👽👽👺
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
👺👽👽👽👽👽👽👺
*THE END*
©🤴🏻 *KING BOY ISAH* ✍🏼
👑
. 👩🏻💻👨🏻💻 .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍🏼 *®Z.W.A* .
. 📝 .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
📚 _*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 _*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*JIJINAR BAN GIRMA GA MAKARANTA LABARIN NAN. KAMAR YAU NE NA FARA DA ONE PAGE YAU DAI GANI A END*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ba tare da gardama ba suka sake ta. Sunyi mamakin ganin ta tsaya cik ta natsu. lokacin su mama Asiya suka shigo. Kukan kura tayi ta warci wuka ta nufe.~
_Su Mama Asiya. Da gudu suka koma. Malam yayi caraf! Da Fatima. Nan take ya fara tofa mata wasu addu'o'i shiru tayi tana kallan mutane. Malam ya mata karatu cikin kunnenta na hagun. Tukun ya dafa kirjinta yaci gaba da karanta ayoyin ruk'yah. Ji sukayi ance "Dakata malam ni ba azzaluma bace". Cikin bacin rai malam yace, "Ke kuwa ce azzaluma tunda gashi kin shiga jikin yar karamar yarinya kina kuma yunkurin kashe wasu". Aljanar tace, "Kwarai na shiga jikin Yarinya kuma hakan kariya ne daga wadancan azzaluman matan ubanta. Domin in ban kashe su ba su zasu iya kashe ta ita". Tsuru aka zurawa Fatima ido da bakinta ne kawai ke motsi amma ba ita ke maganar ba. Alhaji har rawar jiki yake domin sosai yake san Fatima. Nan malam yasa aka kirawo su Asiya a tsoarace suka zo suna baya-baya da Fatima wacce sai hararen su take kamar idanun zasu fado kasa. Malam yace wa Safuratu me su Asiya sukayi wa Fatimar na zallunci. Bata boye komai ba duk ta kwashe abubuwan da su Asiya da 'yav'yan sukayi wa Fatima ta fada. Malam ya juya gare su ya tambaya haka ne. Jiki a sanyaye ta amsa cewa eh duk abunda ta fada gaskiya ne. Alhaji a zuciye ya nufi Asiya da niyar ya dake ta yana fadin "Amma Asiya kin cika macuciya maciya amana. Amanar ma ta marainiya kuma yarinya". Ba dan malam ya dakatar da shi ba kuma ta gudu da sai ya ji mata ciwo. Nan malam ya kwantar mishi da hankali ya kuma ga Safuratu yake tambayar ta ta yaya akayi ta zo gidan har take taimakawa Fatimar. Bata boye musu komai ba ta sheda musu cewa wannan aikinta ne. Ta dade tana irin taimakon nan da sasanta matsalolin ma'aurata. Gaba dayan falon sunyi mamaki malam yake tambaya. Shin a kwai irinta ne dama a cikin Aljanu. Tace ita dai bata sani ba amma tasan cewa. Ba duka aka zama daya ba._
_Malam ya tambaye ta a kan me yasa take irin wannan taimakon. Tace "Dogon labari ne amma dai bari in baku shi a gajarce yanda kuma zaku fahimata. Uwata da ubana mutanen kirki ne a cikin mu aljanu tun kafin a haife ni a kasarsu wani babba daga cikin aljanun shi ne abun bautar su. Wata rana sai sani Aljani wanda shi ya kasance musilmi ne. Yaje garin bisa batan hanya. Da yaje kasar kuma mahaifina ne mutum na farko da suka fara haduwa da shi. Kuma shi ya sauke shi a agidan shi. Ko da lokacin sallah yayi. Ya tashi yayi su sai suna kallanshi ba tare da sun ma san ko me yake ba. Bayan ya gama sallar yaga sun tsura mai ido basu tashi sukayi sallah ba. Da ya tambaye su sai suka nuna basu ma san me yayi ba. Nan suke fada mai su ai shugaban su suke bautawa. Natsuwa yayi ya musu bayanin Islam sosai kuma suka fahimata suka gane. A kwana a tashi iyayena da wannan bakoj aljanin suka ta zagaye gari suna shedawa mutane addinin da suke ba na gaskiya bane. Muslinci shine addini gaskiya suna amfani da hujjoji kwarara wanna yasa aljanu da dama suke aminta su karbi muslinci. Ana haka har magana ta kai ga wannan shugaba nashi. Nan take ya bada umarnin duk wanda aka kama a kashe shi daga iyayen nawa har wanda suka karbi muslinci. An kama wasu an kashe wasu kuma sun tsira. Cikin wanda aka kashe harda mahaifina. Mahaifiyata da wannan bakon aljanin da kyar suka sha. A ranar suka bar kasar. Suna fitowa daga kasar mu aka ci sa a ya gano hanyar kasar su. Suka nifi can shi da uwata. In takaice muku labari a can garin mahaifiyata ta haife ni. Ta haife ni da kwana daya tace ga garin ku nan. A hannun matar wannan aljanin na taso labarin irin wuyar da nasha a gunta da 'ya'yan ta nada tsayi. Da naga dai abun yayi yawa suna neman sabautani saboda sunga ni marainiya ce bani da kowa. Sai na gudu. Garin yawo na har na iso kasashen mutane. Lokacin ban taba ganin dan adam ba. Wacce na fara gani kuma yarinya ce yar karama. A wani daji_
_Ta jifgo itace da yawa a kanta. Da kyar take tafiya. Al'ajabi da mamakin ya cika ni. Hakan yasa na bita a baya ba mukata tafiya domin lokacin na lura da bata gani na. Sai da muka kusan zuwa gari na ringa hangen mutane kalar yarinyar. Da muka shiga nata ganin su kala-kala fari da baki. Ban daina bin Yarinyar ba dai da mukaje har gidan su. Nasha mamaki ganin yanda mater wacce da farko nayi zatan uwarta ce. Tata dukan Yarinyar wai ta debo itace kadan. Sannan ta sake sata wani aiki. Haka dai naci gaba da bibiyar ta har dare. Abun ya bani mamaki sosai ganin ni irin abunda matar wancan Aljanin da yaranta suke min. Haka itama wannan Yarinyar matar nan da Yaranta suke azabtar da ita. Da na tsananta bincike sai na gano cewa ashe ita din marainiyace bata da uwa. Ubanta kuwa baya cewa komai ko a gabanshi aka mata abu. Hakan yasa ni kuwa nayi amfani da damata nata taimakon Yarinyar nan ina rama mata duk abunda aka mata. Dan dole suka shafa mata lafiya. Daga karshe na bayyana a gabansu na tsoratasu a karsu kara cutar da ita. Kuma nayi musu kwakwarar kashe di. Sai da na tabbatar sun daina mata duk abunda suke mata sannan na rabu da su. Da nayo gaba a garin da na iske still na sake iske wata marainiyar haka dai naci gaba dayi zuwa yanzu bansan yarinya nawa da mata nawa na gyara wa rayuwa ba. Bana barin azzalumi. Kuma ni bana kisa. sai dai in wahalar. Ko su Asiya ma kawai ina musu barazana ne. Wannan shine takaitaccen labarina". Ko da Safuratu. ta zo nan a zancen ta kusan mutum biyar sukayi ajiyar zuciya a lokaci daya. Nan malam da sauran mutane suka jinjinawa Safuratu hade da karfafa mata gwiwa. Su mama Asiya nadama ce karara shimfide a fuskokin su. Malam yayi musu nasiha mai ratsa jiki. Ya kuma fadi musu illolin cutar da maraya da zaluntar sa. Da kuma irin ladar da mai kyautatawa maraya yake sama a gurin Allah. Sosai sun ji wa'azin dan wasu daga cikin su harda hawaye. Nan suka dauki alkawari cewa bazasu sake musgunawa Fatima ba. Suka kuma nemi gafara gun Safuratu. Tace ita ba ita sukawa laifi ba Fatima ce. Ta kara da cewa kyautata mata da yi mata alkhairi shine zai tabbatar mana da kun daina abunda kuke kun tuba. Sannan ku sani zan dawo ko ba yau ba. Da fadsr haka sukaji Fatima na attishawa. Daga bisani wani farin hayaki ya fito daga bakin ta. Nan da nan gumi ya jike ta sharaf! Ba'q jima ba sai barci. Su mama Asiya har rige-rigen daukar ta akata daki ake. Alhaji shi kam baic komai ba. A zuciya yake addu'ar Allah yasa su Asiya su cika alkawari._
_Alhmdulilah kwana biyu gidan ya canza kowa san Fatima yake. Dan a cikin su Asiya har rasa wanda yafi san Fatima Alhaji yake. Haka bangaren yara ma. Su Nasmat duk inda zasu sai suja Fatima. Godiya Alhaji yayi wa Allah. Domin Allah shine mai saita komai. Gashi a lokaci daya Allah ya shirye matanshi sun gane gaskiya._
A nan nima nake cewa.
TAMMAT BIHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN 📿🕋
```A nan na kawo karshe labarin Aljanar Fatima. A yanda na tsara littafin yafi haka. Saboda wasu dalilai yasa na yanke shi. Ina rokon Allah ka kurakuran dake cikin littafin nan wanda nayi da sani da wanda nayi ba da sani na ba. Ya Allah ubangiji ka yafe min. Allah kasan kudurina a kan littafin nan nayi shi ne dan fadakarwa Allah ka shiryar da masu irin halin nan ta Dalilin littafi na. Domin kai ne mai shiryarwa.```
0 comments:
Post a Comment