Wayar Ma'u dake kan bed din ya fara ringing, har wayar ya tsinke bbu wadda ya kula daga Ma'u har Nature, kiran wayar aka sakeyi, nan ne Bature ya dawo hayyacinsa ya tsagaita abunda yake ya mirgine ya kwanta gefe yana sauke numfashi a hankali
Cikin kunya da jin nauyi Ma'u taja blanket ta rufe jikinta kan ta jayo wayarta
Anty Jidda ce manne a screen din, Ma'u na picking Bature ya mike a hankali yabar dakin cike da jin haushin Kansa yadda ya xage yake kokarin xubda girmansa a wajen Ma'u
Direct bedroom dinsa ya wuce ko takan abincin baiyiba, sanda ya kuma wani wankar, jallabiya yasa ya dawo kan dinning din yayi serving kansa ya fara cin abincin, yana taunawa yana murmushi don daxun shiyasan meyaji
"Kina inane nayita kiranki bakya dauka ko salon iskancin nakine ya motsa"
A dayan bangaren Jidda tayi magana a xafafe
Harara Ma'u tayiwa wayar kamar Anty jiddance
"Ina wankane yanxun na fito"
"Ya Bature ya shigo dakin kine?
Jidda tayi tambayar bbu wasa
Daria ma tambayar tabawa Ma'u a xucia tace "kujimin matarnan da gulma ita ina kiranta na tambayeta Ya Balarabe ya shigo dakinta ne"
Shirun datayi yasa jidda daka mata tsawa
"Bake nake tambayaba"
"Mexai kawoshi dakina, ai baya xuwa dakina"
Ma'u tayi maganar tana tura bakinta
"To ki bude kunnenki ki jini da kyau, idan Ya Bature ya xo dakinki ko ya kiraki dakinsa kada ki kuskura ki bashi hadin kai, idan kikaga xai dakeki ki ce mishi kina period, kuma ki dinga sa kananan kayanda na tsaya mikin nan idan yana gida, kina dinga giftawa ta gabansa kuma ki rage jin tsoronsa"
Jidda tayi maganar cikin muryan gargadi
Baki Ma'u ta tabe tace
"Toh Anty"
Itama jiddan tabe bakin tayi tace
"Hadda wani toh kamar kin dauka, idan ma baki daukaba ma ruwanki kexaki bonu nan gaba"
Katse kiran Ma'u tayi tace
"Lallai kam idan na mishi gardama yaci uwar ubana kina can bbu ruwanki, duk abunda ya nema bashi xanyi ji yadda daxun ya jiyar dani dadi"
Murmushi tayi ta mike taci gaba da shirinta tana mitan maganar Jidda
Night gown tasa iya gwiwa ta bude kofa ta leka, ganinsa a dinning ne yasata komawa dakin tana mita
"Toh uban me ya xaunar dashi a dining din, so yake naje ya nemo laifina ya dakani gashi bbu mai karbata, wlh baxan fitaba sai yabar wajen sai dai yunwa ya kasheni"
Ganin batada niyar fitowane yasa Bature tashi ya shige bedroom dinsa ya kwanta, yanason jin dumin Ma'u amma gudun reni yasashi yin ta maxa har bacci ya daukesa
Ma'u najin Bature ya shiga ta fito taci abincinta isheshshe ta koma bedroom dinta, ta kwanta tunanin abunda ya faru tsakaninta da Bature ta hau murmushi da haka bacci ya dauketa
Bature Estate
Zahra ce xaune a dinning space ta xuba tagumi, duk jerin abincin dake gabanta ta gagara cin komai
Ummi dake xaune cikin falo ta lura da yanayinda Zahra ki ciki tace
"Zahra me nake gani haka, kada tun yanxu kin fara tunanin Bature, idan ma shi kike tun wuri ki fitar a ranki, kuma kiyi maxa ki dibi abincin nan kici tun kan na saba miki"
Ajiyar xucia Zahra tayi tace
"Ummi ni tunani nake kada Ya Bature ya kusanci Ma'u"
Tsaki Ummi tayi tace
"Shi Baturen mahaukaciyace ta renesa da xai kusanci Ma'u don Allah ci abincinki kibar tunanin wata banxa wai ita Ma'u, nasan ko kallo bata ishe shiba"
Diba abincin Zahra tayi ta fara ci amma har yanxu hankalinta bai kwantaba don tasa; halin abunta
Waya Ummi ta dauka ta kira Abdallah
Ruwan wanka Batool ta hadawa Abdallah ta fito toilet din daure da towel, kan stool ta xauna cikin batsarwa tace
"Ya Abdallah tashi ka shiga wanka"
Abdallah dake xaune bakin bed ya harareta yace
"Dacan ke kike sani wanka"
Murmushi tayi tace
"Dacan baka biya sadaki bane shiyasa bana saka amma yanxu daka biya dole na saka don kaci sadainka da tsinke"
"Ai sai kixo muje kimin wankan don cika ladanki"
Abdallah yayi maganar yana cire jallabiyar dake jikinsa
Murmushi Batool tayi tace
"Ai ba maganar lada bane maganar sadakice"
Murmushi kawai Abdallah yayi don Batool ta fishi iya xare xance, mikewa yayi ya shige toilet
Batool tabi bayansa da kallo tana murmushi tana dada godewa Allah
Kwaliyya Batool ta caba tasa Ankara gown mai matukar kyau, tana kokarin daura dankwali wayar Abdallah yafara ringing
Tashi tayi taje ta daga wayar ganin Ummi yasa picking call din da fara'arta ta gaida Ummi
A dakile Ummi ta amsa
"Ina mai wayar yake"
"Yana wanka"
Tabe baki Ummi tayi a dayan bangaren tace
"Idan ya fito kice inason ganinshi yanxu yanxu"
Jiki a sanyaye Batool tace
,"Toh"
Katse wayar Ummi tayi
Baki Batool ta tabe tace
"Wata sabuwa inji dan caca"
Tanajin Abdallah na kokarin fitowa tayi saurin barin bedroom din kan yace xai sa kaya a gabanta don xai aikata
Dinning space ta nufa ta xauna tana jiran fitowarshi
Kamshin turarensa ne ya tabbatar mata yana nufo dinning space din
Abdallah na isowa yaja kujerar gefenta ya xauna, murmushi tayi masa tace
"Kayi kyau Ya Abdllah kamar sabon ango"
Martanin murmushin Abdallah ya mayar mata yace
"Nagode dear, amma na wuce kamar sabon angon aini angone"
Baki Batool ta tabe tana kokarin serving dinsu tace
" angon waye kenan"
Kama hannunta yayi yana matsawa yace
"Ina wata bayan Batool Matata"
Sosai Batool taji dadin kalamansa, amma sai tayi fuskar tausayi tace
"A'a Ya Abdallah abunda bakason Batool"
Cikin sanyin murya yace
"Pls Batool ki daina cewa haka wlh ina miki son 'yanuwantaka kuma nasa soon zai koma so da kauna, ina fatan yafima yadda nakeson Ma'u"
Take hawaye ya fara ambaliya a fuskar Batool
Share mata ya shiga yi a hankalinta yace
"Haba Batool tawa kada ki xama ragguwa mana, ya kamata ki xama jaruma kan naxo amsar hakkina"
Kwace hannunta tayi ta rufe fuskarta tana murmushi kasa kasa
Bayan sun gama cin abincine ta sanar masa sakon Ummi
Peck ya mata a kuncinta yace
"Bari naje su Abba ma nason ganina"
A dawo lfy taiyi masa lokacinda ta rakashi bakin kofa
Bayan wata daya
Zahra ce kwance akan bed duk abun dunia ya mata xafi, kewar mijinta na damunta ssai, ga xaman gidan ba dadinsa takeji ba kowa ya juya mata baya Ummi da Mami ne ke sauraranta bayansu duk mutanen gidan bbu mai mata magana kotaje gaida su Abba ma bbu mai.amsawa ga Ummi tace idan ta yadda ta koma gidan Bature xasu raba gari, ssai ta rame ta koma kalar tausayi
Wayarta taja tayi dialling number Jidda don ta tallafa mata ringing uku yayi Jidda ta daga, suka gaisa a mutunce
Zahra tace cikin sanyi
"Don Allah sis kiyi hakuri nasan ban kyauta ba kuma banyi daidaiba, pls ki taimake ina cikin matsala dunia tamin xafi"
Ta karashe tana kuka
"Pls Sis ki bar kuka king a ranar danake guje miki gashi tun kan aje ko'ina taxo, kin bi son xucia da xugar Ummi kin ki bin Ya Bature gashi yanxu kina danasani"
Jidda ta fada a dayan bangaren
"Nasan komai Sis kuma na amshi laifi na, yanxu mafita nake nema"
Zahra tayi maganar tana gyara kwanciyarta
A dayan bangaren Jidda tace
"Mafita shine ki kira Ya Bature ki bashi hakuri, sai ki koma wajensu Abba da Ammi suma ki basu hakuri"
Ajiyar xucia Zahra tayi tace
"To Ummi fa ya xanyi da ita, tace idan har na koma gidan Ya Bature bbu ni bbu ita"
Baki Jidda ta tabe tace
"Kibi ta Ummi ta kashe miki aure, kin san Ya Bature bai sha mishi kaiba kiga sakon takardar sakinki"
Ido Zahra ta ware kamar Jidda na gabanta tace
"Saki fa kikace Jidda? Kina ganin Ya Bature xai iya sakeni"
Daria Jidda tasa hadda Shewa tace
"Iyeeeh Sarauniyar mata Zahra ke wacece da baxai iya sakekiba, kina ganin ya samu dalleliyar yarinya kice baxai sakekiba, ina ganin kina hauka"
Take kuka ya tasoma Zahra ta shiga rera
Sosai Jidda ta tausaya mata tace
"Ba kuka xakiyiba hanxartawa xakiyi ki kira Ya Bature"
"Nagode Jidda Allah yabar kauna, bantaba tunanin xaki tsaya ki saurareni har da bani shawara ba, insha Allah xanyi yadda kikace"
Murmushi Jidda tayi tace
"Bbu komai Sis ana tare"
Yake Zahra tayi tace
"Ki shafamin kan Amal dita"
"Gata nan ma tana gaisuwa, ga kuma na ciki na daga hannu"
Cike da mamaki Zahra tace
"Kada kicemin cikine dake"
Murmushi Jidda tayi tace
"Daman baki saniba ai naxata kin lura lokacin bikin nan"
"A'a ban luraba kin san lokacin hankalina baya jikina, Allah ya sauke lfy, Allah ya samu a danshinku"
"Ameen"
Jidda tace ta katse wayar
Bbu bata lokaci Zahra tayi dialling number Bature
Gidan Bature
Tun ranar bbu abunda ya sake hada Bature da Ma'u sai gaisuwa, yayi kokari matuka wajen danne sha'awarsa don bayason ta renashi
Ssai Ma'u ta gaji da xaman gidan daga bedroom sai falo ko kitchen bata lekawa, tanason xuwa gidan Anty Falmata amma tsoro na hanata tambaya
Yau ta dau aniyar xata cire duk tsoron datakeji taje ta tambayeshi xuwa gidan Anty Falmata
Sanda ta gama shirinta tsaf cikin riga da sikat na atamfa, ya amshi jikinta ssai ta fito sharr da ita
Direct bedroom din Bature ta nufa xuciarta na dukan uku uku
Da sallama ta bude kofar ta shiga, bata sameshi ba karar ruwar datajine ya bata tabbacin yana wanka, xama tayi gefen bed din ta kurawa hotonshi dake gefen bed din ido yayi matsifar kyau ssai
Tsintar kanta tayi da Murmushi tana jin dadin kallonsa
Wayarsa dake gefentane ya fara ringing takai dubanta kan wayan
Tsaki taja dataga My Zahra manne a screen din wayar
Ssai haushi ya kamata
"Idan ba karuwanciba mena kiransa tunda kinki dawowa, wlh irinsu nema kesa maxa su raina mata, bari xanyi maganinki"
Picking na call din tayi
A dayan bangaren dadi ssai ya kama Zahra Bature ya dau wayarta, cikin kissa da kisisina tace
"Amincin Allah ya tabbata a gareka Mijina"
Baki Ma'u ta tabe ta make murya kamar wadda ta tashi daga bacci tace
"Yana wankan farilla"
Kadan ya rage Zahra ta kurma ihu don tsabagen takaici ga wani mugun kishi ya taso mata wai Ma'u ce kece mata Baturenta yaje wankan farilla, lallai kam ta bawa yarinyar nan wuri, amma xata magantata
Shirun da Ma'u taji yasa jin dadi don tasan ko ba komai ta kona ran Zahra
"Idan bakida sako xan katse wayar don na gaji ssai wlh ashe haka Ya Bature yake da jarab........... "
A harxuke Zahra ta katseta
"Ke kucaka rufewa mutane baki ina abunda Mijina xai dauka a jikinki, wlh karya kike Ya Bature baxai taba hada daki dakeba balle kuma ya hada jiki dake k........ "
Ssai maganar ya konawa Ma'u rai tace
"Hada jiki dani na nawa kuma wai ancewa kuturu Allah ya la'anceka, hada jiki kam sai dai kada a kuma, and pls banason daga murya don kada babyna ta samu matsala kin san mu masu ciki munason lallabawa"
Bata jira jin abunda Zahra xata ceba ta katse wayar tana daria
Dago kanta daxatayi taga Bature tsaye a bakin kofar toilet ya kama kugunsa yana mata duban "kin isa"
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
Fans ina godia da soyayyarku gareni
Allah yabar xumuncin kauna
Son So
Batool Adam Jatco (Amfanin Soyayya)
Mrs Adam
SadNaf (Makobtan Juna)
BeeBie Isa ( Dan Makaho)
Batool Mamman
Lamtana
Phertymerh (Yusrah)
Pherty Zahra (El-Mustapha)
Sameena Aliyu (A Duniarmu)
Zainab Makawa (Tarko)
1⃣8⃣
Ihu mai karfin gaske Zahra ta saka tayi hurgi da wayarta jikin bango sanda ya fashe, kuka mai cin rai ta shigayi tana cewa
"Wayyo Allahna Ummi kin kasheni, na mutu na lalace wayyoni Zahra shikenan tawa ta kare Ma'u ta kwacemin miji"
Ummi na kwance a bedroom dinta tana tufka da warwara yadda xata shawo kan komai, taji ihun Zahra kamar daga sama, da hanxari ta mike ta nufi bedroom na Zahra
Da mugun mamaki take kallon Zahra data burkice ta fice hayyacinta ta xama tamkar sabon kamun hauka
"Ke me haka?, meya saneki? Me akayi miki"
Kukanta Zahra taci gaba dayi don yanxu haushin Ummi takeji matuka tana ganin duk abunda ya sameta Ummimce sila
Cikin kuka Zahra tace
"Ummi kin cuceni, Ummi kin rabani da farin cikina"
Hannu Ummi ta dafe a kirji tace
"Ni Hawwa ni na cuceka Zahra? Uban me na miki dana cuceki"
"Yanxu na kira Ya Bature Ma'u ta dauka tana cemin wai yana wankan farilla, kuma tanada ciki"
Tsaki Ummi taja tace
" Allah ya tsinewa wayonki Zahra ace wai Ma'u ce xata fada miki magana ki dauka, kishine kawai ya rufe miki ido har kika yadda da shirmen Ma'u, da bakuwarkice Ma'un sai ki yadda, kilama barin wayar yayi a falo ta samu ta shirya miki.iskancinta, ke kuma kishi ya rufe miki ido kika manta wacece Ma'u kika hau kika xauna"
Sai yanxu Zahra ta tuna wacece Ma'u wannan kadane daga aikinta, amma duk da haka hankalin Zahra bai kwanta ba, kilan maganar Ma'u gaskia ko kuma maganar Ummi ce gaskia
Tsagaita kukan tayi tayi kalar tausayi tace
"Pls Ummi ki barni na koma gidana naje na koyawa Ma'u hankali, na fiddata a gidan da karfin kissata na maidata kamar baxawara"
Murmushi mugunta Ummi tayi ta xauna bakin bed tace
"Kin kawo xance mai ma'ana tabbas wannan babban dabarane, insha Allah next week xaki koma dakinki, Kuma ki tabbatar naga Ma'u a gidan nan"
Itama Zahra murmushi koba komai ta samu taji sauki a ranta
Gidan Bature
A hankali Bature ya fara takowa bakin bed da Ma'u ke xaune, fuskarsa dauke da killer smile
Duk wani tsoron duniar nan Ma'u ta jishi, jikinta har rawa yake ta gama tsorota sai raba ido take
Xama Bature yayi kusa da ita ya juyo da ita tana fuskantarsa
"Madam Ma'u, ashe bayan fitsara da rashin kunya tare da ta'asa hadda ta'addanci Ashe kin iya sharara karya haka, banaso abubuwan su miki yawa don haka xan tabbatar da duk abunda kika cewa Zahra"
A raxane Ma'u ta dago tana kallonshi
Dage mata gera yayi yana murmushi mai dauke da mugunta
Tare hawaye ya shiga ambaliya a fuskar Ma'u
Harshenshi Bature yasa ya fara lashe hawayen dake ambaliyar, baki Ma'u ta bude da shirin magana, take Bature ya hade bakinsu ya shiga sotse bakin Ma'u kamar Meerna Parrot ta sami sweet
Cikin dabara Bature ya raba Ma'u da kayanta ya xama daga ita sai pant don ya rabata da bra ma
Xafafan sakonni masu rikitarwa Bature ya shiga aikawa Ma'u, yana bin kowani sassa na jikinta yana sarrafa cikin kwarewa
A hankali Ma'u ke nishi dadi don ssai take amsar sakonnin sai wani cije lips dinta take tana kara bankaro masa kirjinta dayake sotsewa tana mimmike kafa
Sun dau lokaci a haka, ko wanne na Jin ddin abundake faruwa duk sun mance duniar da suke sai nishi dadi kawai ke tashi a dakin
Cikin shauki Bature ya gangara xuwa cibin Ma'u ya shiga lashewa yana mata tafiar Susa da harshenta
Ihu Ma'u tasa tareda cusa hannayenta cikin lallausar gashin kan Bature tana cakudawa
A hankali Bature ya dinga tafia da harshensa har saman maran Ma'u, sambatu Ma'u ta shigayi
"Pls kada ka bari, idan ka bari xan mutu, ka cika gaba Baby ( hmmmm yau su Bature ne Baby, wani abu sai an shiga turaka, tsula tsiya inji Mrs Adam )"
Xame pant din Bature yayi ya shiga sucking din Ma'u, haukane ya rage Ma'u tayi, tayi kukan dadi har muryanta ya dishe, bbu irin sambatun da batayiba
Ganin ta gama macewane yasa Bature mikewa ya gyara mata kwanciya yadda xaiyi komai zam zam, nan take ya afka mata
Wayyo Ma'u daga kukan dadi ta koma kukan axaba, ihun ceto ta shigayi, ganin bashine mafitaba yasa dukanshi da iya karfinta hadda cixo
Amma san Bature bai san ma tanayiba , don ya lula duniar dadi sai shawagi yake, kwasar gara yake bbu kakkautawa
"Wayyo Ammi, Wayyo Mami, Ku taimakeni xai kasheni, Anty Jidda na mutu, wlh Ya Bature xakayi kisan kai, Allah ya isana ban yafe ba axxalumi kawai"
Tun Ma'u na iya yin tsiwa da Allah ya Isa har bakinta ya mutu murus ta dawo sai ido kawai don ta axabtu ba dan kadanba
Sau hudu Bature ya sadu da Ma'u, badon ya gajiba tausayine yasa ya dakata don yaga numfashinta har ya fara sama
Hada mata ruwa mai dumi yayi, ya dagata kamar yar doli ya direta cikin ruwan xafin
Ihu mai baraxanar illata kunne tasa bbu shiri bature ya toshe kunnensa
Zafi mai ratsa gabban jiki Ma'u takeji kuka tasa gwanin ban tausayi
"Ka taimakeni ka cireni wlh xan mutu, Wayyo bayana, wayyo marata"
Tunda Bature yake bai taba tausayawa Ma'u ba sai yau, yasan ta axabtu iya axabtuwa
Mikewa yayi a sanyaye yace
"Pls Asma'u kada ki fita cikin ruwan nan"
Karon farko da Bature yacewa Ma'u pls kuma har da sanyaya mata murya
Duk radadin datakeji bai hanata mishi duban mamaki ba
Bedroom ya koma ya janye Bedsheet da jini ya bata, ya dauko wani ya shimfida, ya koma toilet da wadda ya cire a washing machine yasa ya dauke
Duk Ma'u na kallonsa tana mamakinsa sai murmushi yake kamar Angon kare
Sanda ya kintsa komai ya daukowa Ma'u gown a bedroom dinta kan yaxo ya fidda daga cikin ruwan ya sauya wani ruwa ya mata wankan farilla injita da fade ya nadeta a towel kamar jaririya ya direta kan bed
Da kansa ya shiryata, ya balla pain killer ya bata tasha ya gyara mata kwanciyarta ha lullubeta da blanket
Itada dai Ma'u da ido kawai take binsa don gani take kamar ba Ya Baturen data sani bane, don bata taba sammanin haka daga garesa ba
Shigewa Bature yayi toilet ya sake wanka hade da wankan farilla ya fito ya shirya tsaf a kakinsa na Air force, ssai ya amsheshi
A karo na farko daya burge Ma'u ta kuma jinjina kyaunsa, wani abu dabata san menene ba ya shiga taso mata
"Zan wuce wajen aiki, idan kinada bukatar wani abu ki kirani, pls ki kula da kanki banda yarinta"
Bature ya fadi hakan daidai kunnen Ma'u
Peck ya mata a goshi ya tattari keys dinsa da wayoyinsa ya fice
Ma'u kam ta kasa gaskata sauyin datake gani gun Oga Turawa
A wajen aiki anga sauyi wajen Bature, fuskarsa dauke da annashuwa sabanin yadda ke a hade kamar hadari
Haka Bature ya kasance ranar cikin farin ciki da annashuwa tareda jin dadi
Yanason kiran ma'u yaji ya ta kasance abun haushin shine baida numberta kuma abun ashsha ne ya kira a tura masa, haka yanaji yana kallo ya gagara samunta
Excuse ya dauka ya nufo gida tun lokacin tashinsa baiyiba
Ssai Ma'u tasha tarairaya da tattali gun Bature, a Baturensa yake a fuska amma gangar jikinsa sun bauta mata ssai ya shiga mata hidima
Misalin 9:30 na dare Bature ya gama shirin kwanciyarsa, yaxo ya rumgume Ma'unsa tsam a jikinsa yana shakar kamshinta mai rikita masa tunani, shiru yayi kamar yayi bacci yana shakar kamshin a hankali
Ma'u najin Bature yayi shiru, ita a ganinta bacci yayi ta janye jikinta daga garesa ta sauko a kan bed din a hankali, wai don kada ta tadashi, tayi hanyar barin falon don tana tsoron kada dare yayi dare Bature ya maimaita abunda yayi daxun
Tana gab da kama handle din kofar Bature daya kyaleta yaga iya gudun ruwanta yace
"Xanyi mutukar saba miki idan kika fice daga dakin nan"
Rintse ido Ma'u tayi cike da tsoro ta dawo ta kwanta nesa da Bature
A limshe da ido Bature yace
"Idan kika bari na biki inda kike abunda na miki daxun nafila ne"
Bbu shiri Ma'u ta mirgino ta shige jikinsa xuciarta na dukan uku uku
Bayan Sati Daya
Ssai Zahra ta shirya kanta tayi gyara na musamman ta fito fess
Ana washegari xata koma Abuja aka rangada mata kitso da lalle masu daukar hankali
Gun su Abba taje ta nemi afuwarsu kuma ta sheda musu gobe xata koma dakinta fatan alkhairi suka mata
Dataje gun Ammi kam cewa tayi
"Idan don Allah xaki koma Allah ya hada kanku xaina lfy, idan kuma wani sharrin xai kaiki Allah yasa kaikayi ya koma kan mashekiya"
Gidan Bature
Tun daga ranar da Bature ya kwashi gara, bbu abunda ya sake shiga tsakaninsa da Ma'u sai dai idan ya dibo xafi ya sauke da romance
Ssai Ma'u tanajin dadin kasancewa da Bature don ya gama tsayan xuciarta da xafafan romance dayake mata masu birkita mata lissafi
Sonshi ya mata mugun kamu, har addu'a take kada Allah yasa Zahra ta dawo sai dai kawai a tura mata takardan sakinta (kujimin Ma'u da bushewar ido)
Shiko Goga Bature ya mance da kowa da komai sai som Ma'u dake kara ninkuwa a xuciarsa, ssai yake kokarin koyawa Ma'u sonsa da kuma rage mata tsoronsa, kuma yana ganin ci gaba ssai don yanxu tana iya xama gefenshi ta sake sosai
Half gown ne a jikin Ma'u, ta tufke gashinta tana tsaye a jikin madubi tana ma kanta Murmushi
Da mamaki taje bakin window tana duba wayene yaxo don taji karar tsayuwar mota
Gabantane ya shiga dukan uku uku lokacinda taga Zahra ta fito daga motar tayi wani kyaun ban mamaki
Take Ma'u taji kuka yaxo mata
"Kukan uban me xakiyi? Xuwa xakiyi kisata kuka bawai ki tsaya kina mata kukaba, nuna mata xakiyi kin rigada kin rushe gomnatinta"
Xuciar Ma'u ya sanar da ita
Da sauri Ma'u ta fice xuwa main palo, xama tayi akan cushion kafart daya nakan daya ta dau wayarta ta kara a kunne
Tanajin motsin shigowar Zahra, duk da xuciarta ya tsinke amma ta dake tace
"Baby kenan kasan bbu abunda xan ajje maka sama da abunda kafi so, kaga yadda bakin abun dadinka suka kumbura suna jiranka kaxo ka sotsesu yadda ka saba"
Rashin jin takun Zahra ne yasa ci gaba da bayani don tasan Tarkonta ya kama kucciya
A shagwabe tace
"Amma Sweety a hankali xakayi ko, don wlh ban gama wartsekewa ba da na jiya"
Shiru tayi kamar mai sauraran bayani daga dayan bangare, daga bisani tace
"Toh Honey, bari naje bedroom sai muyi video call din na nuna maka kayan dadinka"
Mikewa Ma'u tayi tana kada jikinta ta nufi Bedroom dinta
Kukan kura Zahra dake tsaye saura kiris xuciarta ta buga don bakin kishi tayi ta nufi kan Ma'u gadan gadan
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
1⃣9⃣
Jin hucin Zahra da Ma'u tayi a bayanta shi yasata rugawa da gudu ta shige dakinta tayi masa key
Bugun kufar Zahra take da karfi
"Don ubanki ki bude kofar nan, Ashe ke kamar' yar iskace da kin tsaya dana nuna miki yadda ake iskanci, bari Ya Baturen ya dawo yau xai xaba koni ko ke"
Sanda Zahra ta gaji don kanta ta wuce dakinta ta nata bambami
Haye kan bed dinta Ma'u tayi tana daria
"Hoohooohoo ni Ma'u, haka kawai xata sakamin hawan jini gwara na fara saka mata"
8pm Bature ya sauko palon cikin takunsa na katsaita, wuce Zahra dake xaune a falo taci kwalliya na alfarma yayi ya nufi dinning space
Kamar Zahra xatayi kuka ta mike ta bishi dinning space din
Kujera dake kallon nashi taja ta xauna ta marairace fuska tare da kissa tace
"Don Allah Sweety kayi hakuri, nasan ban kyauta ba wlh baxan sakeba"
Ko kallon inda take Bature baiyiba sai ma ci gaba da latsa wayarsa dayaci gaba
Daman tasan xa'a rina kukan kissa tasa
"Pls mana Dear, Allah baxan sake ba"
"Hakurin me kike bani? Me kikamin?"
Bature yayi maganar yana dialing number Ma'u
Ringing biyu yayi ta daga
"Sai naxo na daukoki"
Yana fadar haka ya katse wayar
Kishi ne ya turnuke Zahra
"Na maka laifi mana naki biyoka lokacinda ka nemi na biyoka"
Baki ya tabe yace
" kanki kikawa ba niba, kinga kanki xaki bawa hakuri "
Jin takun Ma'u ne ya hana Zahra magana
Black jeans da red bodyhug Ma'u tasa, sunyi matukar amsarta, daure gashinta tayi da black ribborn, fuskarta bbu wani kwalliya amma tayi kyau ssai
Cikin takun Jan hankali ta iso dinning space din, kujerar dake gefen Bature taja ta xauna
Satan kallon Zahra tayi taga tana mata mugun kallon, murmushi kasa kasa Ma'u tayi tace
"Ashe kin dawo Anty Zahra, Sannu da dawowa"
Mugun harara Zahra ta wurga mata
Baki Ma'u ta tabe ta shiga serving nasu
Wani kasada ta gwadayi na hada abincinta da Bature, addu'a take Allah yasa kada ya kobsata
Zahra ko ido ta xuba tana kallon ikon Allah, ita dai iya saninta tunda take bata taba cin abinci a plate daya da Bature ba, abun bakin ciki sai ga Ma'u xataci plate daya da Bature, kukane yaxo mata mai karfi, dakyar tayi jarumta ta danne kukan
Shima Baturen Mamaki ssai hakan ya bashi, amma da shike shi namijin dunia ne sai ya boye mamakinsa, yana jin jina wayo irin na Ma'u, mace komin kankantarta akwai kisisina da kissa a tare da ita
Karar spoons kawai ke tashi a dinning space din, bbu mai cewa uffan
Zahra dai jagwal gwala abincin kawai take don ta kasa kai ko loma daya bakinta tsabagen kishin dake cinta
Lura da haka da Ma'u tayi tace
"Anty Zahra ya bakya cin abincin, ko kin koshine"
Murmushi tayi tacigaba
"Kodashike ma yadda Ummi ke son kin nan nasan ta cika miki ciki kanki taho"
Ba karamin namijin kokari Zahra tayi ba wajen danne xuciarta kada ta biyewa Ma'u don ta fahimci Ma'u so take tayi double offense, dabara ne ya fado mata ta maidawa Ma'u murmushi tace
"Nadanci abincin ai, banaso naci dayawane na kasa farantawa Sweetyna rai anjima, don kin san ya jima da samun nutsuwa"
Kadan ya rage Ma'u tasa kuka, ita tai maganar kuma ita ya dama don ssai martanin Zahra ya bugeta
Ikon Allah Bature ya tsaya kallo da Ma'u da Zahra duk mamaki suke bashi, kunne kawai ya baxa musu amma idanunshi yana kan plate kamar baisan me suke cewaba
Shiru wajen yayi Ma'u na naxarin wani irin martani xata maidawa Zahra, Sam kishin dake cinta ya hanata tunanin komai haka ta hakura da tafarfasar xucia suka kammala cin abincin
Bature ne ya fara barin dinning space din yana murmushi kasa kasa
Zahra na ganin ya haura ta dubi Ma'u irin kallon gargardin nan tace
"Wlh Ma'u ki fice idona, ke har Yaushe kikasan dadin miji daxaki budi baki kimin fitsara, keda kike matar hadi, idan ma badon kaddara ba ina Ya Bature ina ke, kuma ina mai miki lalbishir daga yau kin bar kwanan dakin Ya Bature idan ma kina kwana"
Ganin Bature baya nan kuma idan ta kuskura ta tanka mugun duka xatasha gun Zahra yasa Ma'u mikewa a hankali ta nufi bedroom dinta, daidai xata shiga bedroom din ta daga murya inda Zahra xata jita tace
"Ma'u batasan dadin mujiba sai dai mijine yasan dadin Ma'u don yadda yake ihu da sambatu ya nuna baya samu wannan dadin gun muna mata sai mace, kuma batun matar hadi inaga kin manta bara na tuna miki, Zahra ma Matar hadice bata soyayya ba, maganar kwanan daki kuma yanxu Ma'u ta fara sula tsiya a turaka"
Bata jira komai ba ta shige bedroom dinta ta banko kofa
Yatsa Zahra ta ciza ta kada kai irin xan kamakin nan ta bar dinning space din itama ta haura
Kwance Bature yake kan gadonsa na alfarma sai murmushi yake don yanada tabbacin wannan salon na matansa zai sanya kusanci ssai tsakaninsa da Ma'u ya samu yadda yake so
A hankali Zahra ta turo kofar ta shigo bedroom din, xuwa tayi ta durkusa gaban bed
"Pls Honey ka taimakamin wlh na gane kuskurena, Allah baxan kara maimaita hakanba"
Kamar mai bacci Bature yayi banxa da ita
Ssai Zahra tayi ta masa magiya hadda kukanta, amma Bature yaki kulata
Daga karshema cewa yayi
"Idan kin gama kije ki kiramin Ma'u mu kwanta"
Ihu Zahra tasa
"Wayyo Allah na shiga ukuna don Allah Sweety ka rufamin asiri ka barni ni kwana a da kin nan wlh ina bukatarka"
Dakyar dai ta shawo kanshi sanda ta hada da maganar rashin haihuwarta kan ya saurareta
"Shikenan Zahra ya wuce, amma kuma ki sani idan kika kuma aikata haka sai dai ki tsinci takaddar sakinki a hannunki"
Share hawayenta Zahra tayi ta haye kan bed dinta ta rumgume Bature
"Nagode ssai Dear, insha Allah baxan kuma hakanba"
Su Bature daman ana hannu take ya baxama duniar Ma'aurata ya shiga sula tsiya
Sam bacci ya kauracewa Ma'u sai juyi take, don tayi mugun sabo da romancing dinta da Bature keyi, kuka tayi ssai dakyar da sudin goshi bacci yayi gaba da ita
Washegari kin fitowa breakfast Ma'u tayi, Babu kuma wadda ya nemeta hakan kuwa ba karamin dadi yama Zahraba don a ganinta ta fara maganin Ma'u
Sai 10 Ma'u ta fito cikin shirinta na fita anguwa tea kawai ta hada tadanyi sipping tayi dialling number Bature
Sanda ya kusan katsewa kan ya dauka
"Ina kwana"
Ta fada a sanyaye
"Lfy"
Ya amsa a takaice
"Daman so nake xanje wajen Anty Falmata"
A dayan bangaren Bature yace
"Na mantama ban sanar dakeba ta haihu yau kwana hudu"
Ido Ma'u ta zare tace
"Meta samu"
"Idan kikaje xaki gani, kuma kada ki jima"
Bai jira cewarta ba ya katse wayar
Bakaramin amfani xuwan Ma'u gidan Falmata yayi mata ba, don taje ta samu 'yan uwan Falmata sunxo daga Maiduguri sun bata lacca ssai baida kayan gyaran jiki data samu
Lokacin dinner ne Bature ya sanar dasu ya raba musu kwana bibbiyu
Bayan kwana biyu
Bbu abunda ke shiga tsakanin Ma'u da Zahra sai harara da habaici tun ba Zahra ba ta dau abin da zafi, ssai take nuna kishinta a fili
Yau Ma'u xata amshi girki, xuwa tayi kitchen ta kori cookernsu, ta xage ta rangada girki mai rai da lfy don cikin laccan hadda yima miji girki aka shaida mata
"Gaskia yau girkin Samuel yayi dadi ssai, Honey ka turashi course ne"
Zahra tayi maganar lokacinda take kokarin kai spoon din meat love rice bakinta
"Ai basai ya tura Samuel course ba tunda ya auro wadda ta iya girki"
Cewar Ma'u tana sipping Ginger juice datayi
Daga Zahra har Bature mamaki ta basu, aina suke lokacinda ta koyi girki har ta iya haka
Harara Zahra ta hurga mata tace
"Kinga Ma'u kada ki kuskura kice xaki raina ni don kaddara ta saki auren mijina, ko bbu komai na girmeki balle kuma idan aka duba dangantakarmu"
Marairaice fuska tayi abin tausayi tace
"Pls Honey ka shiga tsakanina da Ma'u don wlh xan iya babbalata wani sa'in"
Mugun kallo ya jefa musu kowa ya shiga taitayinsa, amma kasa kasa Zahra ke harar Ma'u
Koda lokacin kwanciya yayi, wanka da Humra Ma'u tayi ta nufi turaka
Waya ta samu Bature nayi da Balarabe, gefenshi ta xauna akan bed tana jira ya gama wayar
Katse wayar Bature yayi ya juyo yana duban Ma'u
"Wayayi girkin daxun"
Ya jefa mata tambaya
A shagwabe tace
"Ni nayi"
Shagwabar tata ta burge Bature ssai
Rumgumeta yayi a jikin shi
"Idan kuma na samu bakye kikayiba sai na sassaba miki"
Wasa ta shigayi da gashin dake kwance a kirjinshi tace
"Meyasa baka shaving gashin nan?"
Tayi tambayar cikin salon Jan hankali
Ido Bature ya xuba Mata nadan lokaci yana naxarin yadda batajin tsoronshi yanxu idan har akaxo fagen nan, kanshi ya kada daya tuna jaraba gareta
"Kinaso inyi shaving wajen ne?
Ya tambayeta yana shimshina gashin kanta dayasha gyara ssai ga kamshi
Tura bakinta tayi tace
" banason kayi shaving yafi kyau haka, kaga Babyn Anty Falmata kyakyawa dashi kamar na sato na gudu"
Ta canxa topic din
Daria ta bawa Bature amma sai yayi murmushi yace
" kinason Babyne?"
Kai Ma'u ta kada alamar "eh"
Janyota yayi jikinsa ya fara kissing dinta a kasalance yace
"Insha Allah yau xan miki ajiyar Baby"
Ma'u da babu baki shiru tayi tana karbar sakonni, ssai ta dage wajen mayar mishi da raddi
Jaraba plus jaraba abun ba magana ssai suka mori juna, sai yanxu Bature yasan yayi aure yana gamsu yadda ya kamata ba kamar Zahra yanxu yanxu tace ta gajiba
Asuba ta gari Ma'uBature
Hu6a Mubi LGA Adamawa State
Durkushe Hajiya Turai take itada Ummi da Lubna gaban boka a cikin wani bukka mai duhu
Hajiya Turai ce ta xayyanawa boka bukatarsu, daria bokan ya kece dashi yace
"Hajajo mutan Makkah, kisa ranki a inuwa indai wannan itace kawai bukatan angama, naga yanada mata ita matar ya xa'ayi da ita"
"Ya saketa kawai boka"
Lubna ta fada kaitsaye
Kai Hajiya Turai ta girgixa
"Ai idan ya saketa anci bulus, kada ya saketa ya dai tsaneta yayita gana mata axaba, yadda Ammi ta bakanta mana rai muma sai mun bakanta mata"
Lubna tace
"A'a Anty bakya ganin xai shafi auren Shukrah ko Zahra"
Gyara xama Ummi tayi tace
"Baxai shafi ko dayaba idan ma shafarne Zahra ce kuma xuwa na gaba akan Bature xa'a mana aiki"
Boka dai da ido yake binsu yana murmushi yana kada kai
Sanda ya tabbata sun gama maganarsu ya dauki kullin magani ya bawa Ummi yace
"Wannan a saka mishi a cikin abinci da xarar yaci shikenan aiki ya gama kyau"
Cika boka sukayi da kudi suka mike suka fice
Ransu fari kal
Ummu Subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
JINJINA
Mahmu Gee
Habiba Mohammed (Sahra)
Afrah Bhai
2⃣0⃣
Yau asabar tun safe Abdallah da Batool dukaxo gida, suna xuwa bai kai minti biyar ba saiga Hisham da Shukrah, duk a falon Ammi suka hada xango bayan sun gaisa da iyayensu
Tunda Ummi taga Abdallah ta shiga kitchen da manta don hada masa favorite dinsa jallof na couscous
Hira suke ssai sai daria suke da shewa abun gwanin ban sha'awa
Ammi tace
"Ja'iri lokacin da aka aura maka ita ba har xaxxabi kayiba"
Batool tayi sauri tace
"To Ammi hada wuri ana xaman lfy xaki bata, xaxxabin ma ai naso ne koh Baby"
Ta karashe maganar tana dagewa Abdallah Gera
Murmushi Abdallah yayi yace
"Ssai kuwa xaxxabin sone"
Baki Ammi ta tabe tace
"Xakuji da gulmarku"
Hisham yasa daria bbu kakkautawa
Duk suka xuba masa ido
Ammi tace
"Kai kuma me haka kamar sabon kamu"
Tsaigaita dariar yayi yace
"Ina tuna yadda al'amura xasu wakana a gidan Ya Baturene, ga Ma'u ga Ya Bature ga kuma Zahra, xanso naga wannan dramar"
Duk daria sukasa Shukrah tace
"Ai kuwa ba karamin drama akayiba, don dukkansu bbu tayan baya"
Kasa kasa da Murya Batool tayi tace
"Sis ya kamar akwai ajiyar Babynmu ne"
Murmushi Shukrah tayi tace
"Kai Sis wlh kin fiya gulma ya akayi kika gane"
Itama Batool murmushi tayi tace
"Nima inadashine shiyasa na gane"
"Haba dai Sis"
Shukrah ta fada da dan karfi
Duk suka juyo suna kallonta
Jan hannunta Batool tayi suka mike suka nufi bedroom din Ammi
Harara Ammi ta bisu dashi tace
"Sai manyance kama uwayen mata"
Daria Hisham da Abdallah sukayi
Warmer mai kyau Ummi ta dauka tasakawa Abdallah abincin a ciki ta barbada garin maganin da boka ya bata a ciki ta juya ssai maganin yabi jikin abincin, ta bari a kitchen ta nufi bedroom dinta tayi wanka kan ta kirasa yaxo yaci
Hira Batool keyi da Shukrah kowa na bada lbrn yadda take xaune da mijinta cikin jin dadi
Wayar Shukrah ne ya hau ringing, Honey ne manne screen din tayi picking cikin sauri
"Assalamu Alaikum Honey"
Amsa sallamar Hisham yayi yace
"Sweery pls samomin abinda xanci kixo kiyi feeding na, part din Mami"
"Toh Honey gani nan tafe"
Ta katse wayar ta mike
"Sis bara na kaiwa Honey na abinci"
Kai kawai Batool ta gyada mata don bacci ya fara Kamata
Direct part din Ummi Shukrah ta nufa, kitchen kai tsaye Shukrah ta nufa
Tana shiga kitchen din idonta ya sauka kan warmer da Ummi tasa abinci, bude warmer tayi taga abunda ke ciki
Murmushi Shukrah tayi ta dauki plate ta dibi abincin, har xata fita taga ya kamata ta kara abincin kada nasu Abbu ne, konawa kitchen din tayi ta bude tukunya ta kara abincin a warmer ta fice
Kamar yadda Hisham ya fada mata a falon Mami ta sameshi takai mishi abincin, take Hisham yaci abincin don shima yanason couscous
Tusa Abdallah a gaba Ummi tayi sai yaci abincin
Plate Abdallah ya dauka ya dibi kadan na sama yaci don ya rigada ya cika cikinsa kan suxo
Gidan Bature
Tun safe Ma'u na kwance a dakinta tana fama da masanancin xaxxabi, ko breakfast bata fita tayiba ga Bature baya gari ya tafi port court
Rashin ganin Ma'u ya damu Zahra amma tana tsoron shiga dakin Ma'u kada wani Kissa ta shirya, shiyasa Zahra tayi xamanta a falo tana jiran dawowar Bature don ranar xai dawo
Dakyar Ma'u ta lallaba ta janyo wayar ta tayi dialling number Bature, hawayene ya shiga bin kuncinta dataji number switch off, tana tsoron kiran Zahra kada ta mata wulakanci
Bature na dawowa Zahra ta karbesa hannu bibbiyu da taimakonsa ya kintsa
Suka fito falo tare, a cushion suka xauna
"Sweety baxaka ci abinci bane"
Zahra ta tambayi Bature cikin kissa
Kwantar da kansa Bature yayi a jikin Zahra ya limshe idonsa, Ma'u kawai yakeson sanyawa a idonsa
"Ma'u fah?"
Yayi tambayar cikin ko in kula
Bata rai Zahra tayi tace
"Tana dakinta"
Ta bashi amsa a takaice cike da kishi
Mikewa Bature yayi ya nufi bedroom din Ma'u
Kuka mara sauti Zahra tasa tanajin tsanar Ma'u ssai
Ssai xaxxabin yaci karfin Ma'u, bugu daya ta fice hayyacinta, tayi amai ssai
Bature na bude kofar dakin idonsa yakai kanta, da gudu ya karasa dakin ya dagota, ya mannata da jikinsa bai damu da Ammi daya bata mata jikiba
"Lfy HUSNA meya sameki"
Duk da Ma'u na cikin matsanancin hali vai hanata jin dadin sunanba
Daukarta yayi ya shige da ita toilet ya mata wanka, shiryata yayi cikin dogon Riga yasa mata hijab ya fice da ita
Zahra na xaune sai kallonsu tayi, mikewa taxo jikinta har rawa yake tace
"Lfy Sweety? Meya sameta?"
Mugun kallo ya hurga mata
"Bani waje na shige, kina gidan nan batada lfy amma kikayi zamanki koki lekata"
Baki Zahra ta bude xatai magana, yadan hankade ya shige
Kamar xatai kuka ta koma ta xauna
Da isarsu Hospital cikin kankanin lokaci aka tabbatarwa Bature Ma'u nada ciki sati biyar
Ssai Bature yayi murna hadda bawa Doctor tukwici, daga bisani kuma tausayin Zahrarsa ya kamasa
Ma'u naji tanada ciki tayi murmushin mugunta a xuciar ta tace
"An bani lasisin sheke ayata yadda ya kamata, Anty Zahra kin bonu"
Tun a hanyarsu ta dawowa Ma'u ta shiga shagwabewa Bature, shi kuma yana biye mata
Fargaban wani Irin hali Zahra xata shiga ya hana Bature sanar da ita Ma'u nada ciki
Fitowa falo ma'u tayi tana chart a WhatsApp
Kujerar dake fuskantar wadda Zahra ke xaune ta xauna, tana murmushi da Batool ta sanar mata tanada ciki kuma take tambayarta idan Anty Jidda ta haihu xataje suna
Voice note Ma'u ta shigawa Batool
"Da wuya naje Sis, kin san Ya Bature bayason nayi nesa dashi, amma xan lallabasa yabarni naje"
Tana gamawa tayi sending
Baki Zahra ta tabe tace
"Makaryaci dai bai ji dadiba wlh"
Murmushin mugunta Ma'u tayi amma bata tanka ba, dialling na number Bature tayi, yana picking a shagwabe tace
"Sweetheart wlh tun daxun miyau na sai tsinkewa yake"
Daga dayan bangaren Bature yace
"Mekikeso Husna"
Sake shagwabewa tayi tace
"Gwaiba nakeso naci"
"To bbu damuwa xan turo akawo miki"
Yayi maganar tare da katse wayar
Mikewa Ma'u tayi tana daria kasa kasa
Shan gabanta Zahra tayi
"Ke rainin sense dinki ya isheni haka, idan kika kuma wlh sai nayi kasa kasa dake"
A tsiwace Ma'u tace
"Da kuwa an daureki har igiya ya saura don wlh Ya Bature baxai barki kimai asarar baby ba yabarki"
Zaro ido Zahra tayi hadeda dafe kirji
"Kina nufin kinada ciki"
Kada kai Ma'u tayi tace
"Confirm, congratulation kin kusa xama yadikko"
Jimamine ya hana Zahra cewa komai ta wuce Ma'u jiki a sanyaye ta haura dakinta
Ganin yanayinta yasa Ma'u tausaya mata tayi danasanin fada mata maganar, itama Ma'u jiki a sanyaye ta wuce bedroom dinta
Banko kofa Zahra tayi ta fada kan bed tasa kuka mai cin rai ta janyo wayarta tayi dialling Number Ummi
Gidan Bature
Waya Ummi take da Hajiya Turai, korafi Hajiya Turai take mata
"Anya Hawwa kin bawa yaron nan maganin nan yaci kuwa"
"Wlh Anty na bashi kuma a idona yaci"
Ummi tayi maganar tana rage muryan Tv
"Gaskia yaci muga result don Zee ta matugar daga min hankali kwanarnan"
Shigowar Shukrah cikin kukane yasa Ummi ba shiri ta katse wayar
"Mexan gani Shukrah? Me aka miki"
Xubewa a jikinta Shukrah tayi tana kuma mai cin rai tace
"Ummi na shiga uku, Ya Hisham xai kasheni, yau da safe shegen duka yamin kuma yace shi Yanxu Zee yakeso"
Wani jirine ya fara dibar Ummi tace
"Ke banason shirma wata zeen yakeso"
"Zeen Anty Turai, hadda daukar numberta a wayata ya kirata"
Hannu Ummi ta dora a ka tasa kuka tace
"Wayyo Allah menakeji haka, don Allah Shukrah kicemin karya kike"
Kara volume na kukanta Shukrah tayi tace
"Wlh gaskia ne Ummi, Ya Hisham ya tsaneni"
Wayar Ummine ya shiga ringing, batayi kukorin daina kukarba ta picking call din
Zuciarta ce ta fara dukan uku uku dataji kukan Zahra
"Wayyo Ummi na shiga Tara, Ma'u nada ciki, pls Ummi kiyi wani abu"
Kuka mai karfi Ummi tasa, tanayi Shukrah nayi ga kuma Zahra itama tanayi abundai babu dadin gani
Da gudu Zee ta sauko daga staircase taxo ta fada kan cinyar Hajiya Turai
"Mom daxun Ya Hisham ya kirani yanatamin xantukan soyayya hadda cemin idan bai aureniba xai iya rasa ransa"
Murmushi Hajia Turai tayi tace
"Kujimin jibebbiya Abdallah ya kiraki ko Hisham"
Gyara kwanciyarta Zee tayi kan cinyar Hajia Turai tace
"A'a Mom Ya Hisham ne Mijin Shukrah"
Da mamaki Hajiya Turai tace
"Hisham kuma garin yaya haka, naga kina murna ina Abdallah kike so"
A shagwabe Zee tace
"Ai da babu gwara ba dadi, kuma ni ina tsoron Batool nan gwara Shukrah xan iya duk yadda naso, bakiga ranar danaje ina yimasa wasaba sai hararata take kamar xata doken, nidai nafison ya Hisham yanxu"
Kada kai Hajiya Turai tace
"Shikenan ni farin cikinki nakeso, tunda Hisham din kikeso hakan xa'ayi"
"To Mom bakya ganin xamu samu matsala da Anty Hawwa"
Baki Hajiya Turai ta tabe
"Idan xaki samu farin ciki ko Mijin Hawwa xaki aura ina bayanki, matsala kuma ita ya shafa"
Rumgumeta Zee tayi tace
"Proudly Mom, love you much"
Daria Hajiya Turai tayi tace
"Love you much more Zee"
Ummu subay'a❤
[23/10, 01:09] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝🏻
GODIA DUBU
Pherty Zahra (Jiddatul Musty)
Son so
Ummu Subay'a Fans❤
2⃣1⃣
"Wlh banga mahalukin da zai hana auren Zee da Hisham, tunda tace tanaso, ai ba akanmu aka fara hada 'yan pendoni gida daya"
Cewar Hajiya Turai tana kada jikinta
Salle Ummi tayi ta dire tace
"Billahillaxi baxai yiyuba, karyanki tasha karya Zee baxata tabs auremin Mijin diyaba, tunda Zee tasako kanta cikin familyn mu komai ya dinga tabarbaremin"
Lubna data xuba musu ido tace
"Kinga Anty Hawwa duk fa Abunda ya faru laifinkine, maimakon ki bawa Abdallah magani kikaje kika bawa Hisham"
Harara Ummi ta gallawa Lubna tace
"Zan ci ubanki idan baki rufemin bakiba, na dau asara wancan karon amma wannan karon bbu ni bbu asara ko mutuwa Zee zatayi baxata auri Hisham ba"
Dariar Boss Hajiya Turai tayi tace
"Nima Turai baxan dau asara ba dolen dole sai Zee ta auri Hisham, ita Shukrah idan taga dama ta hadiye rai ta mutu asarar kuce ba tawa ba"
Daria harda Shewa Ummi tayi tace
"Turai naga alamun bakida imani kuma bakida mutunci, tunda haka kikaga ya dace to xan nuna miki ni Hawwa wlh nafi karfinki, idan har ina numfashi kai ko a kabari nake Zee baxata taba auren Hisham ba Zeee baxata taba shiga Bature Family ba don yafi karfinta, Hisham Mijin mace dayace "
Itama Hajiya Turai Shewa ta buga tace
"Nagode Allah.da kika furta hakan da bakinki Hisham Mijin mace dayace, tabbas Mijin Mace dayace don Zee na aurensa xatayi waje da Shukrah, Gidan Bature kuwa sai sun samu jika da Zee and kuma da kikace xaki hana auren ko kina kabari wlh karyanki baki Isa ki hanaba idan nima ina raye, ko yawo tsirara xanyi don inga diyata ya samu Abunda take so, ina mai baki shawara ki dauke idonki daga kan auren Hisham da Zee ki koma can kan Zahra ki kwata nata 'yancinta, Abunda baxai yiyuba ai gwara mai yiyuwa"
Ihu Ummi ta saka tace
"Mu xuba mugani shege ka fasa dan halak sai yanka"
"Haba jama'a mun xo nefa don Neman mafita ba kace naceba, don Allah kuyi hakuri Ku xauna a sasanta a samo mafita ko so kuke yan uba sujimu su mana daria"
Lubna fa fada tana duban Ummi
Gyara Gyalanta Ummi tayi ta sabi Jakarta tace
"Bbu xaman mafita dukkanku munafukai ne, ai bbu 'yan uba kamanku, kuma wlh nafi karfinku"
Bata tsaya dauraran xaginda Hajiya Turai ke mata ba ta fice daga falon a harxuke
Kwance Shukrah take tasa kanta a cinyar Mami tana kuka mai cin rai
"Don Allah Shukrah kukan nan ya Isa haka, daxayi maganin komai da tun jiya yayi maganin, ki daure kiyita addu'a insha Allah komai xaixo daidai"
Cikin kuka Shukrah tace
"Mami ki barni nayi kukata, kina ganin fa yadda Ya Hisham ya shafawa idonsa tuka a gabanku ya nuna baya sona ya tsaneni shi Zee yakeso, Mami ya xanyi da raina, gani nake asiri Zee ta mishi don taxo gidanmu bai kai satiba hakan ya faru kuma hadda cewa wai Ya Hisham na burgeta ya iya soyayya"
"Auxubillah kada na kara jin haka daga bakinki, wannan xatone kawai muci gaba da addu'a bbu Abunda ya gagari Allah"
Mami ta fada tana shafa kan Shukrah
"Hakane Mami Allah ya amsa mana Addu'armu, komai ya daidaita cikin kankanin lokaci"
"Ameen"
Ssai tausayinta ya kama Mami itama kamar ta fashe da kuka tace
Kuka Batool tashigayi kamar ranta xai fita bayan ta gama waya da Shukrah ta shaida mata dukkan abunda ya faru
Abdallah da fitowarshi wanka kenan ya tsaya yana kalkonta da mamaki daga bisani ya karasa kusa da ita ya xauna ya janyota jikin shi yace
"Madam me kuma ya faru"
Cikin kuka Batool tace
"Daman abunda ya faru daxun a gida kenan kace bbu komai, meyasa ka boyemin Dear?"
"Ohh so sorry dear banason ki daga hankalinki insha Allah very soon komai xai daidaita akasine kawai aka samu"
Dubanshi tayi tace
"Akasi? Wannan yafi akasi wannan kaddarace take shirin faruwa"
Murmushi Abdallah yayi yace
"Come on Dear insha Allah bbu abunda xai faru sai alkhairi kawai fadan masoyane"
Kada kai kawai Batool tayi ta lafe a jikin sa
Gidan Bature
Xaune a falo Ma'u take tayi cross leg tana kallon Indian series tana dan daukar strawberry tana ci hankalinta kwance
Cikin katsaita Bature ya sauko daga staircase, yaxo ya xauna kusa da ita, ya janyota jikinsa ta kwanta luf
"Baby kinajin dadinki fa kinga yadda kikayi fresh kamar na hadiyeki"
Daria Ma'u ta kyalkyale dashi tace
"To ai kai kake sani nake fresh, tunda duk abunda nakeso kanamini"
Murmushi Bature yayi ya shiga shinshina gefen wuyarta
A kasalance Ma'u tace
"Pls ka bari Baby, kagafa jiya dakyar na samu kuguna yabarmin ciwo"
Dubanta yayi cikin shauki yace
"Kene ai kin cika Sweet dayawa, muje na gaisa da Babynmu don inaso na ficene, kinga yau da asubama kin hanamu gaisawa"
A shagwabe Ma'u tace
"Muje Baby amma guda daya xamuyi don kada mu bama babynmu wahala"
Murmushi Bature yayi ya dagata sama kamar 'yar tsana, ya haura da ita bedroom dinsa
( wai jama'a daman Bature ya iya soyayyane, yaki nunawa Zahra, gaskia Team ZahraBature kukai shi kara kotun Soyayya😜)
Makale da hannun juna Bature suka sauko shida Ma'u, sunyi kyau ssai sun kuma dace
Jin takunsu yasa Zahra dake xaune a falon dago ido ta dubesu, kadan ya rage xuciarta yayi bindiga
Kasa da kanta tayi don idan taci gaba da kallonsu xata iya komai don kishi
A sanyaye tace
"a dawo lfy Honey"
Sake Hannun Ma'u yayi yaxo ya mata peck a goshi, suka wuce har bakin kofar palon Ma' u ta rakashi sanda ya mata peck kan ya fice
Takun isa da katsaita "irin na cikan nan" taxo xata shige gaban Zahra
Cikin fushi Zahra ta fincikota
"Ke don ubanki waye kikewa wannan katsaita, yau sai na kowa miki hankali a Gidan nan"
Ido Ma'u ta shiga rabawa kamar an tare kwarto don ta tabbatar yau Zahra baxata barta ta tarata dayawa
Duk da tana cike da tsoro bai hanata tsiwaba
"Malama sakeni ko ki janyowa kanki bala'i, don wlh kina tabani kin taba igiyar auren ki, idan Ya Bature bai sakeki donniba ai xai sake ki don Babynsa"
A sanyaye Zahra ta sake Ma'u tasa kuka mai karfi ta haura dakinta
Baki Ma'u ta tabe tace
"Kujimin munafuka idan anyi maganar Baby sai tasa kuka"
Wucewa tayi dakinta tana murmushi
Bayan wata Biyar
Duk yadda kowa ya dau maganar Hisham da Shukrah abun ya wuce haka
Hisham ya shafe idonsa da tuka yace sai Zee kuma baxai saki Shukrah ba
Duk wani baraxana da Ammi dasu.Abba suka mishi amma ko a jikinshi haka suka hakura suka xuba mishi ido
Shukrah kam ta fama fita hayyacinta duk ta xabge ta koma kashi da rai ga cikinta dayaketa girma, duk rashin imaninka idan ka ganta sai kayi kuka, ta tattara ta koma part na Mami don ita ke kwantar mata da hankali, Batool na yawan xuwa tadan debe mata kewa
Koda Zahra ta sanarda Bature ya dau xafi sosai yaxo har Kaduna amma abun shima ya gagareshi ya koma
Bbu inda Ummi bata shigaba don wargaxa auren amma kamar karawa wutar petur take, tayi kuka har ta gaji ga Zahra kullum sai ta kirata ta sanar da ita bakin cikin da Ma'u ke kunsa mata
Ummi da diyoyinta sun dawo abun tausayi
Saurin Sati daya auren Hisham da Zee Abbu ya matsa dole Shukrah ta koma gidanta, Ummi kuma ta dire tace baxai yiyuba, ssai akayi rigima a karshe dai Ammi ta balbale Ummi haka Ummi badon tasoba ta hakura Shukrah ta koma, tana gudun kada ta xurfafa Ammi ta zargeta
Jidda ta Haihu ta samu baby boy akasa mishi Sunan Bature wato Muhammad ana kiransa junior
A yau aka daura auren Hisham da Zainab inda Abbu ya tsaya cukucuku akan auren ya marawa Hisham baya
Biki ssai akayi inda Hajiya Turai ta tsaya tayi barin kudi yadda ranta yakeso, tayi biki na alfarma da kyece raini
Family Bature kam bbu wadda ya hallaci bikin, har aka kammala
Tunda Zee ta tako gidan wahala da ukuba suka taru akan Shukrah, itake musu abinci wataran idan tsiyan Zee ya tashi hadda wanki, ga babban ciki abun bbu magana
Shukrah ta xama kamar 'yar aiki ta kode ta jeme ssai
Sallama Batool ta shiga kwadawa a main palon gidan Hisham, bakinta kusan biyar bbu wadda ya amsa, can sai ga 'yar aiki ta fito gaida Batool tayi
"Ina matan gidan"
Batool ta tambaya
"Hajiya Amarya ta fitaHajiya Uwargida kuma tana wanki a garden"
Ido Batool ta xaro tace
"What? Shukrah kuma da wanki da tsohon cikintan nan"
Bata jira Cewar 'yar aikin ba ta wuce garden kai tsaye
Shukrah na kallon Batool ta shiga murmusawa
"Mama kwalla barka da xuwa"
Gefenta Batool ta xauna tace
"Yawwa Sis, keko mai ya hadaki da wanki a yadda kiken nan"
Yake Shukrah tayi tace
"Wlh ina exercises ne kawai na dibo ina wankewa"
Baki Batool ta tabe tace
"Hanyar exercise na dayawa ba sai wankiba, ki nemi wani abun kiyi"
"Gashi na kusan gamawa, kawai bari na gama"
Shukrah ta fada tana dan yatsene don ta gaji ssai
Bin igiyoyin Batool tayi da kallo da mamaki tace
"Kada kicemin kekayi duk wankin nan"
Kai Shukrah ta girgixa
"Bani bace Zee ce tayi"
Baki Batool ta tabe tace
"Ke kika santa"
Tun safe sai bayan la'asar Abdallah ya bugawa Batool xaixo ya dauketa
Bayan Batool ta shirya suka fito Shukrah na rakata
A Main Palo sukaci karo da Zee ta fito daga yawon gantalinta, ko kallo bata ishe Batool ba, Batool ta wuceta gefenta
Cikin fitsara Zee ta janyo Batool gabanta tace
"Ke ba'a koya miki gaida manya bane"
Kallon lallai kin Isa Batool kewa Zee
"Don Ubanki ki sakeni ko nayi kasa kasa dake, na miki kallan sa'arki"
"Ke Batool Ashe bakida kunya, matatace fah Oyo gaidata"
Cewar Hisham data shigo falon
Daria Batool tasa hadda Shewa tace
"And so what idan matarkace, wlh baxan gaidata ba ko uwartace baxan gaidaba"
A harxuke Hisham yayo kan Batool gadangadan, da sauri Shukrah ta taresa
"Don Allah kayi hakuri kada kayi ta'asa cikine da ita"
Hangade Shukrah Hisham yayi taje ta bugu da center table
Ta kwallah kara mai rikitarwa, nan take sai ga jini na bin kasanta
Hakan kuwa yayi daidai da shigowar Abdallah falon
0 comments:
Post a Comment