Hannunta ri'ke da bindiga ta seta shi akan rawanin dake kan waliyyin da ke shirin d'aura auren mijinta da wata macen tana mai cewa "wallahi tallahi ka kuskura ka d'aura wannan auren, sai na d'aura Auren Ranka da Mutuwa"!
Cikin murya mai d'auke da tsawa mijinta ya mi'ke yana cewa "ke menene haka kin haukace ne?
To mah meye kawo ki nan gurin? wannan ai dabbanci ne". A zafafe ta katseshi ta hanyar cewa "idan akan soyayyarka ne na cancanci in amsa sunan dabba
Domin kwa bana gani bana ji kuma bani da hankali, akan sonka ina iya aikata komai ko da kuwa d'aukar rai ne, bana 'kaunar ko wacce mace ta ra6eka ko da kuwa ta kasance muharramarka ce,
Dan ina kishinka mijina, kishina ya bambanta da kishin da ka sani ina maka kishin da bana kaunar ko da jaririyace tayi maka murmushi ka maida mata martani, mijina me ka nema ka rasa a guna da kake shirin kulla alaka irin tamu ni da kai da wata?
Duk wani kyautatawa da kulawa da mace ta ke wa mijinta ina yi maka, ta ina na tauyeka a zaman aure na da kai? a zamana da kai sai dana tabbatar na maye maka duk wani gurbi a zuciyarka, me ka nema ka rasa a guna? ta ina na gaza?".
Ta tambayeshi idanunta na zubar hawaye cike da bacin rai yace "ra'ayi! domin ni ban shirya zama da mace d'aya tilo ba, ra'ayina ne kawai in 'kara aure, saboda Allah da manzonsa s.a.w basu haramta ba!''
Ya bata amsa A fusace, ta maida bindigar kan goshinsa tana cewa "ra'ayi ko dai JARABA irin taku ta maza?
Hmm toh wallahi tallahi idan har ba'a fasa d'aura auren nan ba sai na kasheka, inya so ni da ita mu rasa ka Idan kai JARABA ce tasaka ka har zaka 'kara aure
Toh ni zanyi amfani da JARABABBEN KISHINA da nakeyi akan ka in da'kushe duk wani tasirin JARABAR dake d'awainiya da kai".
"Keeee dakata nagaji dajin munanan kalamanki akaina SUHAYR me ne yasa kika dau kishi kumallonki bayan kinsan irin soyayyar dake tsakaninmu?".
"SAHEEB bakada abunda zaka iya gamsar dani a halin yanzu, amma naci alwashin ruguza auren nan inko ba haka ba yanzu za'a haifi dan daba idoo".
Tuni waliyyi da sauran jama'a suka arce 🏃 don baza su yarda ayi musu sawarwarin rayuwarsu ba. To amma Nikam ko a jikina dan kwa in na fece to ba me dauko rohoton shi yasa nayi ta Maza lol 😜
Asalin Labarin
Suhayr takasance ya ta biyar daga cikin yayyinta maza da take bi daga ita sai autan su, a wajen iyayenta Alhaji kabir sulaiman da kuma hajiya ikilima Mahaifinta yakasance hamshakin mai arziki kuma babban dan siyasa da'ake damawa dasu acikin gwamnati mai ci,
Hmm suhayr ta kasance yar gaban goshi sannan duk abunda zata yi a wajen mahaifinta dai-dai ne, Bayason ganin bacin ranta hasali ma da yaga bacin ranta gwara a kunduma mishi ashar,
Kuma hakan yasamo asali ne sabo da ita kadai ce yarsa mace amma kuma takasance mai ladabi ga duk wanda ya girme mata atakaice zamuce tanada ladabi da biyayya gana gaba da ita.
Wata asabar ne sakaliya suhayr ta tashi da dokin zuwa bikin kawarta wacce sukayi Hassan Gwarzo tare, ta shirya tsaf ta shiga dakin mummy don tayi mata sallama, tace "Mummy yakika gani ,shigan nan tayi kyau kwa ?"
Ta fadi tana fari da ido, hjy ikilima murmushi tayi tace "my beautiful daughter you are such a pretty damsel,
Allah ya azurtaki da miji nagari wanda zai kula da surar da Allah ya azurtaki da ita," Tsalle tayi tace "Mummy kina fasa mun kai sai naji duk duniya babu wata ya mace datakaini kyau Hhhhh lol 😂".
Mummy tace "tabbas hakane babu koda ita ai kam sai an samu banbanci ko wajen shafa jambaki, Maza yata Allah ya tsare ga wasu yan kudi kibiya koda shop rite ne ki siyamata gift Wanda zaki kaimata"
Ta amsa tare da cewa "toh na gode umma Allah yakara girma da tsawon kwana da daukaka" "Amin!"
Tuni aka wanke motar da zata fita da ita tana baya direba na tuki a gaba saida sukayi siyayya sanan suka wuce GOLDEN DRAGON dake hanyan nasarawa G.R.A inda ake friends Eve din
Tun a waje taga wani gaye Wanda kunnenta yajiyo mata sunansa SAHEEB dagani ba tambaya kanwarsa ya rako wajen, tuni taji ya shiga ranta yadda bazata iya rayuwa inba dashi ba.
Wucewa tazo yi tace "hey" ko kallonta baiyi ba saboda bawata mace a gabansa inba HUMAIRAH ba wacce aski yariga yazo gaban goshi bikinsa saura wata biyu.
Rashin amsatan da baiyi ba bai wani bata mata rai ba illah wani sonsa dataji yake shiganta kaman yanda iska ke ratsa mutun idan yana bakin rafi.
Da shigarta tanata ware ido don ta hango kanwarsa ta zauna kusa da ita don dai kwai akwai tambayoyi data tanada zatayi mata akan SAHEEB.
Can ta hangota kusada amarya maryam wadda suna ganin juna sukayi wani irin shewa aka tuno da school life, janta tayi gefe tace "ke waccan yarinyar kawarkice?"
"Eh" maryam tace, Suhayr tace "wallahi wani na ganta dashi kaman dan uwanta wallahi am in love, pls help me kin sanni idan ina son abu gaba daya nake ruftawa".
Maryam tace "Kash suhayr ai kinyi latti inajin bikinsa bai wuce saura wata biyu ba,"
Suhayr ta cigaba da cewa "Pls maryam just tell me u r joking ?"
Maryam tace "haba suhayr yaushe muka fara yar wannan dake kinsan cewa I can't lie or tell you a joke,it's the truth u better accept it or leave
"Ohsshh' suhayr ta furta sannan tace "ya zanyi kenan?" daidai da zuwan wasu friends din maryam hakan yasa ta dubi suhayr Tace "am coming nayi baki"
H'm suhayr kujera ta samu ta zauna saboda kafafuwan ta suna Neman kasa daukanta, dafa kanta tayi gaba daya taji ranta yabaci wani irin kishine ke bijiro mata,
Wanda bashida maraba da leben wuta A haka aka fara event amma gaba daya hankalin ta da tunaninta yana wajen Saheeb wanda yaketa zuba love acikin waya shida masoyiyarsa Humairah,
In yana tare da ita gaba daya jinsa yake kaman ba'a duniyaba, saboda dadadan kalaman da Humairah take tanada kullum don ganin farin cikin hubbinta.
Daga ciki suhayr tana kallonsa daga waje yadda farinciki da annashuwa yake dawainiya dashi. "Oh ni suhayr mezanyi ganin na lalata alakar dake tsakanin sa da wadda ake ikirarin zai aurah?".
Tambayar da takewa kanta kenan agun. "yes!!" tuni wata dabara tazo mata direbanta ta kira tace yadan zagaya tunda bayanxu zasu gamaba.
Bayan yan mintuna ta fita harabar waje bata nufi ko inaba sai wajen da Saheeb ke tsaye jikin wata mota,
"Salamu alaikum!" tace amma ina yayi nisa, ta kara masa sallama shiru har saida ta buga saman motan sannan ya juyo.
"Yi hakuri gimbiya zankiraki yanzu", yana juyowa sai yakasa koda motsi saboda kyawun sura da Allah yayi mata, amma ina is too late to cry went the head it cut off.
"Yah lafiya ?" Ya jefe ta da tambaya, Tace "wallahi nayi running out of battery ne inaso inkira direbana ne, daga yaje yadawo amma shiru" suhayr ta maida martani.
"Okay ba damuwa gashi ki kira" saheeb ya fadi tare da mika mata wayarsa.
Wani murmushi tayi wanda bashi da maraba da dana mugunta, a zuci tace "ina matukar kishin wanda nake so don haka kana bani tausayi don saina rabaka da ita aure kuwa sai an fasa" kuma sai na...................tab-din sai tayi me,??
[7/18, 9:57 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/19, 9:08 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (2) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Matsawa tayi daga gun tare da fara yin wayar bogi, bayan ta gama wayar bogin sai ta juyo ganin hankalinsa ba ya kanta hakan yasa ta yi flashin layinta da wayarsa,
sannan tadau number Humairah a recoeved calls dinsa, sannan ta juya ta bashi wayar sannan tace "gashi ngd Allah yasaka da alkhairi"
sai kuma tace "dan Allah in bazaka damuba inason sanin sunanka" cike da rashin damuwa yace " Okay sunana SAHEEB kefa ?"
Da sauri ta amsa da cewa "sunana suhayr kabeer sulaiman", "wow Nice name" suhayr tayi murmushi tace"in bazaka damuba zanso muzama abokai" tare da kallonsa ido cikin ido
Saheeb yace "badamuwa nagode" domin yasan cewa fadi take kawai ,ina ma zata ganshi har suyi wata abota!
A wannan lokacin tafi kowa farinciki domin plans dinta sunkusa fara aiki, a ranta tace "saina rabaka da duk wata ya mace ,hatta uwar data haifeka, balle kuma kanwa ko yaya indai mace ce,
To kwa bakai ba ita, a ranar anyi shagali ,nan ta samu shiga wajen nimrah kanwar saheeb sabo da ta dinga jin duk wani details, Har wajen mota ta raka nimrah
Sannan kuma sai tace "ki gaida su mummy dan Allah insha Allah zan kawo miki ziyara kamar yadda kikamin kwatance" dariya nimrah tayi tace "Allah ya kawoki "
Sai suhayr tace "amin" har suka bar harabar wajen tana daga ma nimrah hannu wanda ba nimrah takema ba da Saheeb take wanda baima San tana yi ba.
Mota tashiga cike da damuwa, direba ya bata wuta. Saheeb yana tuki yace "Nimrah ina kika jajibo waccen yarinyar? karfa ki hada kanki da ita yar gidan masu kumban susa ce kuma kin san hudubar da baba yake mana,
Wato na cewa mutsaya a matsayin da Allah ya ajiye mu don mu tsira da mutuncinmu". nimrah ta dube shi tare da cewa' Na sani yaya Saheeb amma itace ta bukaci hakan daga gareni
To kaga kuma bai kamata na wulakanta taba tunda acikin mutane muke" saheeb ya katseta da cewa
"Okay naji, amma nidai na gaya miki waccan yarinyar ta wuce ajinki". nimrah ta bata fuska tare da cewa"
"Toh nace naji yaya shikenan" saheeb ya dan dubeta tare da kai hannunsa kan fuskanta yace, "haba my sweet sister don't be upset with me".
SAHEEB shine da na farko a wajen iyayen shi sai kanninsa sai kuma mata su uku, gaba daya su biyar ne wajen iyayen Nasu,
Alhaji Garba dan'kolii shine mahaifin Saheeb bawani mai arziki bane amma yana da rufin asiri gakuma wadatar zuciya, dan kasuwa ne a cikin kasuwar sabon gari dake kano rufuna gareshi wanda yake saida kayan yaji
Ita ko mahaifiyar shi kuwa zaman gida take yi bata sana'an komai. Yan dangine don zuri'ar dan koli tanada yawa sannan sun kware a fannin auren zumunchi wanda hakan yasa yan garinsu ke tsegumi akan cewa iya su-isu tsakanin su suke
Dan kwa ba ashiga ba'a fita. sabo da basu yarda bare yazo Neman auren yayan su ba, shi yasa ma aka hadashi aure da Humairah yar gidan wan babansa,
Kuma ikon Allah hadin yayi daidai saboda suna kaunar junansu!
Suhayr tunda ta koma gida takasa cin abinchi sai tunani gaba daya yan uwanta sun shiga damuwa ganinta cikin wannan halin,
Hmm shiko mahaifinta daya dawo daga Abuja ya shiga rudanin ganin halinda take ciki. ganin sun isheta da tambaya sai kawai ta amsa musu da cewa "da tambayoyin nan dakuke mun kawai ku tayani da Addu'a don a yanzu ita kadai nake bukata daga gareku"
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yayin da suhayr bata da aikin yi illa a kullum ta kira Humairah da boyayyen number tana yi mata barazanar saduwa da mutuwarta in har matukar bata fasa auren Saheeb ba.
A bangaren Humairah tana ganin abun kamar wasan kwaikwayo amma daga baya taga abun yana Neman fin karfinta, ganin a kullum in ta fita sai suhayr ta bugo tace mata ta ganta waje kaza.
Hakan yasa bashiri tasawa iyayenta kuka tana cewa ita gaskiya bazata auri saheeb ba saboda ana baraxanan kasheta. Mahaifinta ransa a bace yace "Baki isa ba domin ba'a taba yar da taki auren dan'uwanta a danginmu ba
To kuma baza'a fara a kanki ba" Kwatsam sai ga wayar humairah na kara ,jikinta na rawa ta dayka tare da cewa" hello" a tsorace
A daya bangaren muryar suhayr ce take cewa "kin janye, ko kuwa saina karar da danginku daya bayan daya sannan in nannadeki, sanin kanki ne cewa saheeb baxai aureki da munin halitta".
Ai kwa humaira bata san lokacin da bakinta ya fara fadin "wallahi na hakura na rabu da shi koda kuwa shine autan maza" da yake a loudspeaker tasa kuma iyayenta sunji komai, hankalinsu ya tashi,
Ba tareda bata lokaci ba, aka hada family meeting aka raba saheeb da humairah, ba tare da dayan su naso ba.
Tun daga ranar da suhayr ta je gidansu saheeb, nimra take bata labarin abin da ya faru, shikenan ta fara nuna masa kulawa,tausayawa da kuma uwa uba , soyayya mai tsafta wanda ba gauraye aciki.
Kamar wasa suhayr da saheeb suka zama addicted da juna, sai dai kuma tsantsar kishin da take nunawa a kullum, wanda yin hakan yake damun saheeb,
Ana cikin haka ne har ya kasa hakuri yayi mata magana yace "Gaskiya suhayr ya kamata ki sani nifa ba d'an kowa bane asalima banda wata Sana'a dana dogara dashi sai na mahaifina,
Sannan kinga da, da wacce zan aura amma aka fasa kuma bana so na yaudareki, kin fini komai suhayr me zai hana ki nemi wani dai-dai dake baniba???
Sannan kuma gashi yanzu haka an kara yimun baiko da yar uwata Salma bani da bakin dazan musawa mahaifina sabo da haka ne tsarin family dinmu Suhayr ina sonki amma gani nake kwarya tabi kwarya, niba abokin burinki bane.
" Zancen saheeb ga suhayr ya katse ne dalilin zuwan wata wacce sukayi makaranta da ita, "saheeb barka da rana!" kamar daga sama kalamanta suka dirgo,
Sai suhayr ta ware ido tayi tsalle ta watsa mata wani mahaukacin mari tare da nuna ta da yatsa tana cewa "karki kuskura ki sake yiwa mijina magana inba hakaba, zanyi Ajalinki hhhh lol 😜
Tace Ni wallahi na rasa me yasa wasu matan suke shiga hurumin daba nasuba" Oh! suhayr ta furta tare dan jan hannun saheeb, ko ta bari ya yi wa budurwar magana taki balle kuma harya bata hakuri,
Hmm ita kuwa cool baby Abun ya daure mata kai don a iya saninta saheeb baida mata baiyi aure ba amma hakan yasa ta tambayi kanta da cewa "ita wannan din wacece?" Hhhhh lol 😜 Nidai cewa nayi dadai kin tafi karki fiye kallonsu takara watsa miki wasu tafin lol 😂
To Nima ganin irin wannan marine yasa Na feceee dan kar nima nasha ban shirya ba ehe ------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/19, 9:08 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/20, 8:12 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (3) **★**
Ci gaban labarin
Cike da damuwa saheeb ya fisge hannunsa tare da cewa "For God sake suhayr me yasa kike son ganin bacin raina? Yar class dinmu ce fa, gashi kin mareta ba tare da ta saan hawa ba balle sauka kuma kin hanani in bata hakuri "
Ai a fusace suhayr ta amsa da cewa "Saheeb nifa gaskiya in har zaka dinga yiwa yan mata magana gaskiya zan nisanceka, saboda zan iya kashe ko ma wacece
Sabo da JARABABBEN KISHIN dana ke akanka...." saheeb ya katseta ta hanyar cewa " Go ahead suhayr go ahead ki sani in dai kika aikata kisan kai, hukuma bazata barki da rai ba"
Sai suhayr tace "Who cares? suwaye hukumar in bamu ba, so I can do anything and I see no reason da wani zai dakatar dani". saheeb yace" Okay haka kikace?,
Toh shikenan suhayr bana Son ki kuma inhar kin saurari kalamaina a baya ya isa ki gane komai, Inada wacce nake so kuma .......",
H'm ai bata bari ya karasaba ta juya a fusace ta shiga mota ta tayar tare da barin gun a fusace. Gudu take batare da tana cikin hayyaci ba,
Ikon Allah ne kadai ya kawota gida ba mutum ba, da kuka ta shiga gida tana cewa "Mummy yace baya sona mumy baya sona ya zanyi?" sai Mumyn tata ta tare da tambayar "wai waye?"
Suhayr ta amsa da cewa "Saheeb yace baya sona mummy mutuwa zanyi bazan iya rayuwa in bada saheeb ba Mummy wai auren zumunchi za'a mishi"
Mummy tace "Ki kwantar da hankalinki insha Allah zaki aureshi" Tun daga ranar suhayr tafara ciwo wanda aka rasa meke damunta baci basha, Anje asibiti amma sun kasa gane musabbabin ciwonta,
Hakan yasa mummy ta bugawa daddyn suhayr waya ta gayamai halin da yarsa take ciki kasancewar baya gari. A daren ya baro Abuja, yana isowa ko ruwa baisha ba,
Kebewa yayi da suhayr don jin damuwar ta. "Abba cewa yayi baya sona wai auren zumunchi za ayi mishi." wasu zafafan hawayene suka fito daga idanunta. A fusace daddyn yace "Wayeshi ?
Kuma waye ubansa a garinnan? Kisa ranki a inuwa insha Allah sai ya zama mallakinki ke kadai" sannan kuma yace" Amma fa nasanki da mugun kishi maybe shiyasa yace baya sonki?
Ai kwa da sauri tace "No daddy watace tayi mai magana ni kuma na gaura mata mari shikenan fa,
Pls Abba muje in bashi hkuru shine farin cikina, banida wani burin wanda ya wuce in farantawa saheeb rai." Washe gari su daddy da direbansa sukayi samnako zuwa gidan su saheeb.
Sallama akayi da Alh Garba, yafito dayake mahaifin suhayr sananne ne ko'a TV, hakan yasa ba shiri mahaifin saheeb ya saukeshi a falonsa, bayan sun gaisa sai daddy ya fara magana kamar haka
"Daman nazo ne akan dan wajenka yata daya tilo tana gida rai a hannun Allah duk ta dalilin danka mai suna saheeb ka taimakemu yadda Allah ya taimaken ,
Farincikin suhayr shine nawa, banida katabus indai tana cikin wani hali, kuma Na dade da sanin tradition din family dinku amma dan Allah akan yata a sassauta mana
Ni dai nasan saheeb na kaunar suhayr amma shi gani yake tamkar tafi karfin sa kuma yata ba haka na tarbiyantar da itaba
Da amai arziki da talaka duk daya suke a gun Allah" Mahaifin saheeb ya bude baki yace "amma fah maganar da muke anyi mishi baiko da yar kanwata salma".
Sai daddy ya katseshi da cewa "malam kayi mana wannan taimakon suhayr tana can kwance ba lafya"
Sai mahaifin saheeb yayi jim sannan yace "A gaskiya saina tuntubi yan uwana zan nemeku nan da satii daya" Alhj kabir sulaiman yayi godiya.
Ankai ruwa rana, anyi dauki ba dadi a family din dan'koli'. Saheeb yace shifa mace guda bazata kawo rarrabuwan kawuna a cikin family dinsu ba kawai shi ya hakura .
Kuma ya fadi hakan ne cike da damuwa a fuskansa. '"Itako suhayr ta nace babu wanda takeso saishi cutafa ta karu bawani sauki.
Amma daga bisani dole suka hakura, sabo da halin da take ciki kowa cikin family dinsu saheeb ya tausayawa Suhayr, ciki harda Alhaji sanusi wanda ya tsaya kaida fata cewa saheeb bazai auro wacce ba yar dangiba,
Daman saheeb yana kaunanta amma gani yake yar manyace mezatayi dashi cima zaune. "Yakaiga duk yar da saheeb zai Neman sai anyi baraxanar kashe yarinyan shiyasa yazama bora,
Dan kwa babu yarinyar datake kulashi daman abunda suhayr takeso kenan. "Soyayya sukeyi ba dare ba rana ji sukeyi kaman su Cinye kansu,
Abu daya kesawa ajisu shine inya fiye kallon mata masu wucewa, shi yasa suka koma zance acikin gida. Wata rana ne sun fita yawon bude ido shida suhayr.
Sai wata tace ma kawarta "kinga wani gaye mai kyau wallahi harnaji sonsa acikin raina". 'Karaf sai a kunnen suhayr kukan kura tayi tayi kan budurwar cike da jin kishin Saheeb,
Kuma ta cakumi wuyanta ta tsinka mata mari, idonta duk ya rufe tsabar bakin kishin da take ji. Janyota saheeb yayi yace "ke wace irin macece?
Meye gaminki dasu,? kinga suhayr indai abunda zaki dinga yi kena inmun fita toh gaskiya zansa doka kowa ya fita batareda wani ya raka kowa ba" Jinsa kawai take amma idanunta sun kada sunyi jajir kamar garwashi.
Suhayr ta rike k'ugu tana huci tace, "daga yau koda a dakinki kika ganshi zaki kiyayeshi mayya kawai Ina ruwanki da kyawunsa kekika yishi?
Masu shegen surutun tsiya da kalle kallen tsiya ke ana babbakan giwa waxai jiyo kamshin Giwa? Toh ki kula mahauniyarki ta kiyayi ramata Kadan namiki nagobe saiyafi na yau idan kika sake mun katsalandan".
Tsaki tayi tace "banza kawai juyowan da zatayi, ta nemi saheeb ta rasa, sai neme neme takeyi amma bata ganshi ba! Sabo da bakin ciki batasan lokacin da wasu hawaye suka kwaranyo daga idanunta ba,
Da sauri ta ruga cikin mota ta kafa kai da sitiyari, jitayi an ruko hannunta a tsorace tace "Ya salam"!
",Karkiji tsoro suhayr saheeb ne masoyinki," Tuni taji dadii acikin ranta, "Meyasa kike kishina dayawa?
Ni nakine suhayr karkiji komai" suhayr tace "saheeb zan iya rasa rayuwata ganin kanawa mata magana Toh kaga da in rasa raina indaina ganinka ai is better inne mawa kaina yanci tafadi tana kallonsa cikeda soyayya amma damuwarta bata boye ba.
Saheeb yace "Amma suhayr, "sheet!! tace mai tasa hannu a lebensa, "don't say a word saheeb...." "You deserve more than dis from me, look right into my eyes what can you see?"
"Kura mata ido yayi yace mata " JARAB EL GHIRA Flames of jealousy" 'Tabbas ba karya saheeb ,"abunda kafadi daidai ne" suhayr ta kalleshi tace say a word dat will make me to be happy now"
"Saheeb yace I LOVE YOU wholeheartedly"," Suhayr taji dadi kwarai. "toh yakake gani Saheeb bazan iya komai a kanka ba?"
Yace "Zaki iya amma kuma ya kamata ki sassauta saboda nifa mijin mace hudu ne??" Zare Ido! Suhayr tayi tace "karka kuskura inba hakaba zaka iya rasani sannan zan iya amfani da jarababen kishina in katse duk wata halaka dake tsakaninka da wata mace"
"Look" Saheeb yace "abar maganan" muje ki kaini gida kinsan yau saboda ke banje kasuwaba" "Toh" tace suka kama hanya waka takemai da harshen larabci.
"Kaine masoyina na gaskiya mijina kuma uban yayana Zanyi fito nafito da duk wata mace datake Neman ruguza alakata dakai" dan sai na------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/20, 8:13 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/21, 6:38 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (4) **★**
Ci gaban labarin
Kallonta kawai yakeyi Azuciyarsa yace tabbas akwai aiki a gabana nida Nake da burin auren mata hudu? Ni maison tara zuri'a mai yawa gashi suhayr batason taga nayi alaka da wata ya mace.
Suhayr ce taji Shurun yayi yawa, ta juya tana kallonsa amma baisan Abunda ke faruwa ba burki taja wanda yayi saurin dawo dashi daga dogon tunanin da yake yi, "suhayr da lafiyanki kuwa"?
"Hmm" murmushi tayi cike da takaici Suhayr tace "kai ya kamata in yiwa wannan tambayan saboda da alamu kaine mara lafya kusan minti goma kana tunani bayan gani a kusa dakai,
Me kanema ka rasa da zaka dinga tunanin wata?". Saheeb zare Ido yayi "suhayr wallahi ba tunanin komai nakeba illah tunanin rayuwa mai daukeda so da kauna da zamuyi in munyi AURE, Narasa ta yadda zan nuna miki yadda nakeji".
Hhhhh lol 😜 murmushi kawai suhayr tayi don tasan kawai kwaskwarima ce yayiwa kala mansa bawai gaskiya bane amma ta basar, Itadai burinta ya cika ta mallakeshi a matsayin mijinta daga nan sai tasa kafar yaki da duk wata mace koda kuwa yau aka haifeta,
Nace hmm shi yasa fatanta akoda yaushe Allah yabata yaya maza, sabo da mugun kishin da take dashi akan diya mace. Nikam nace To Allah ya rabamu da irin wannan JARABABBEN KISHIN
Sannan kuma Nace suhayr kin manta Allah keyi ba mutunba, kana naka babatun Allah na can na shirya maka nasa tanadin, wanda inya baka bakada bakin kin amsa, inko har kace bai iyaba lokacin zai nuna maka ikonsa"
Ansa ranan aurensu wata biyu, amma fa daqyar Baban Saheeb ya shawo kan danginsu suka amince. Kowa a dangi ya sanda bikin saboda bikine na yar gata ya daya tilo
Amma saidai kash daidai sa second daya suhayr bata samu kar buwaba wajen mahaifiyar Saheeb ba. 'Saboda tace duk itace silar rusa mishi aure shida yan uwansa, gashi tana Neman ta rabashi da yan uwansa mata tunkafin tashigo cikin family dinsu.
Ita kanta suhayr tasan cewa mahaifiyar saheeb bata kaunanta amma koh a bakin gyalenta, don cewa take wata ranama saikin so ganinsa in hanashi.
Biki yanata matsowa anfara shiri gadan gadan Amma babu gidan da za'a sa suhayr , gidane saheeb yasamu ciki da falo wanda a kalla mutanen gdan da yara sunkai dari
Tuni suhayr ta kai kukanta wajen mahaifinta ya basu gidanshi dake zooo road, gidane wanda ya amsa sunansa gida. Saidai mahaifiyar saheeb tace Sam bata yarda da wannan tsari ba saboda gudun gori,
'Danta bazai zauna a gidan surukai ba, tasan cewa ai talakane ta Nace tana sonsa. Indai bazata zauna a gidan daya kamaba saidai afasa wannan auren haka umman saheeb tace tun lokacin data samu labarin cewa anbasu gida.
Suhayr tashiga tashin hankali dajin wannan sako daga wajen umman saheeb Tace lallai ne ma zanyi maganin wannan shu'umar tsohuwar cije labe tayi tace yayanta ya rakata gidansu taje da kissa tana bata hakuri harda kuka
"Wallahi umma duk abunda kike tunani ba haka nakeba, inason saheeb bazanso bacin ransa ba, umma kiyi hakuri muzauna a gidan da abbana ya mallaka mana"
Umma tace" bazan taba rabuwa da saheeb ba soyayyarsa nake so ba kudinsa ba, indon kudi nake son sa wallahi bashi da abun da zai mallakamun".
Nan tayi-tayi mata magiya da kyar dasa bakin yan uwa umma ta aminche. Biki saura sati daya Anje an fara shirya gida da kayan alatu,
Ankawo akwati guda biyu a wulakance tirmin zani hudune kuma duka super print ne sai takalmi kafa daya sai gyale guda daya shima. Shiyasa komai Umman suhayr taki basu koh ruwa,
Amma duk suhayr bataji komaiba, saima boye kaya da akayi don kar ya zama abun zunde a cikin danginsu. Sadaki kuwa dubu goma sha biyar suka kawo sai kace wata bazawara, duk don suhayr tace tafasa amma ina sonsa dada karuwa yakeyi acikin zuciyarta.
Biki ya rage saura satii daya ne suhayr sunje kasuwa sukayi batan hanya, sukabi ta layinda runfunan su saheeb suke.
Mace tagani tana mai magana tuni taji numfashinta na Neman daukewa zuciyarta na bugawa uku uku! da sauri taja kawarta suka fita daga kasuwar. waya ta dauka ta kira saheeb tace "ina kasuwa ka fito bakin titi zaka ganni
H'm ai kwa Jikinsa na rawa yafito daman angaya masa anganta a layinsu, Yana isa Suhayr ta balla masa wani irin harara wanda sai daya shiga taitayinsa,
"Saheeb abunda bazan taba lamuncewa ba kenan yin sana'ar dazaka dunga mu'amala da mata, dole ka canza Sana'a wanda maza ne abokan cinikin ka dole kayi nesa da duk wata mace hatta yan uwanka mata sabo da kwanciyan hankalin mu baki daya".
Saheeb kallonta ya tsaya yi cikin tsananin damuwa sannan cikin bacin rai yace "bantaba Sanin cewa Suhayr ke mahaukaciya bace sai yau? kina ganin zan bar sana'ar mahaifina ne inyi wata daban?
Kinsan cewa Sana'ar koli ita muka gada mukeyi tun iyaye da kakanni, Oh suhayr meyasa kika shigo rayuwata? For the first place am not in love with you amma saboda kaunar da naga kike nuna mun ne yasa kika ga na amince miki har kika fara shiga zuciyana a hankali Amma shine zakizo ki ruguzamun rayuwa?
Toh ki sani baki isaba Saidai ki mutu! kokuma Abu mafi sauki ki rabu dani auren afasa banayi" Saheeb ya qarasa maganar cikin hargowa.
Suhayr Ji tayi kalaman saheeb na Neman haukatata me yasa Saheeb zaiyi mata haka? Bayan yasan zata iya mutuwa akansa,
Gashi talaka mafi kaskanci a idanunta amma takasa ganin wayannan bayaga soo da kaunansa dake dawainiya da ita. dishi dishi kawai ta fara gani ta zube a wajen a sume
. "Na shiga uku" saheeb yafadi cikin tashin hankali, wasu mutane suka taimaka masa suka sata cikin mota itada kawarta, sai asibiti.
Bayan awa uku ta farfado da sunan Saheeb acikin bakinta, "saheeb karka juyamun baya kishinka wajibine a gareni zan iya jure komai amma banda ganin kanayin mu'amala da mata"
Tuni saheeb yafara zubarda hawaye wanda shikansa besan dalilinsa na zubdasu ba. Ni kwa nace "sone saheeb ka kamu da son suhayr baka saniba"
Rike mata hannu yayi yace "suhayr tabbas ke macece wacce kowani da namiji zaiso samu matsayin mata Bakida wani aibu a tattare dake,
Ki share hawayenki nime kaunarkine," 'Shuru tayi lokaci guda taji ta warke tashi tayi tace "pls and pls saheeb in zaka mun magana ka dunga sassauta kalamanka a gareni".
"Karki damu bazan karaba". Saheeb yafadi hakane don ya faranta mata rai" 'dariya tayi can ta lura da kallon da Noor take musu tuni tace "maza ki fita ki bacewa ganina kafin inyi takanki kallon me kike mai?
Karki sake zuwa inda nake, tunda naga take takenki so kike ki fara shiga hurumin daba nakiba".
Haka nan Noor ta fita don tasan halin kawartata. Shuru shuru zasu dawo ina basu dawoba, gashi zaa fara mata gyran jiki,
Hajiya rahmatu Maiduguri aka kira tazo ta gyra suhayr umma ce ta dau waya ta kirata tace "suhayr me yasa kika dade? Bayan kinsan schedule din mu na yau?"
"Umma gani nan tahowa, in the next few minutes," Ta fada. Umma tace "Toh tace saikin dawo".
Ta kalli Saheeb, kallon da suhayr tayi masa yasa saheeb jin wani yanayi ajikinsa, Suhayr tace "Yauwa saheeb da akwai wasu dinkuna da nayima sannan daddy ya siyo ma wasu takalma daga England, dan.........h'm Asuba ta gari in sha'allah -----------------------------
------------------------------
----------- ---------------
0 comments:
Post a Comment