Sai tace to muje inna saukeka sai in baka, sannan ga wasu yan kudi kayi amfani dasu nasan kanada hidima". Qin karba yayi sai da ta nuna bacin ranta sannan ya karba.
Har kofar gida takaishi inda umman saheeb ta leko ta taga'. $uhayr tagani sanye da kaya tsadaddu ta dannan wani Abu boot din mota ya bude. wasu Abu ta dauko a Leda "saheeb gashi zan tafi" ya karba,
Ai da sauri ta shiga mota ta figi mota kaman zata tashi sama, Shiko tsayawa yayi yana kallonta harta bacewa ganin sa sannan ya shiga cikin gida
Ai kwa sai ji yayi ana cewa angon suhayr, bai tanka su ba ya shiga cikin daki Ya zauna akan katifarsa, "da akwai aiki agabana, gaskiya suhayr inna ce bazan miki kishiyaba na munafunceki"
Banida burin zama da mace daya". Hahahh lol 😂 Nace Toh pa kace akwai budiri a gidan Suhayr da Saheeb, hmm fans muje zuwa dai
Ayau Sha Tara ga watan November wanda yayi dai-dai da ranan asabar ne, dubban Mutane ciki har da "senator na kano central", suka halacci daurin auren Suhayr kabir sulaiman da Angonta
Saheeb Garba Dan'koli
Bikine na manya bikine
wanda ya amsa sunansa biki. Ba ai wani event ba sabo da suhayr tace bata iya jure kallon da yan
mata zasuyi wa mijinta ba, walima kawai akayi bayan daurin aure.
Suhayr tayi kyau duk da ba
wata kyakkyawa bace amma da yake ance ko amaryar Buzuzu ce ranan bikinta kyau takeyi, lol 😜
Badon farar fataba inajin da sai dai akai kasuwa,
Suhayr gajerace badai sosai ba sannan tana da idanu wanda zamu iya kiransu da sexy eyes, bakinta dan karami dan das, tana da jiki wanda ba zamu iya kiranta da siririya ba, sai kuma hanci kwarai batada hanci lollzzzzzzz 😝
Da misalin karfe Tara na darene yan daukan amarya
suka hallaro domin daukar amaryarsu, motaci uku ne Golf guda biyu sai wata space wagon
guda daya.
Ga kuma dunbin jama'a yan rakiyar amarya kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake Ita ko suhayr fada ake mata sosai wanda ko wacce uwa take yiwa yarta in zata kaita gidan miji.
Ciki harda fada akan jarabebben kishin data sawa kanta, "Hjy ikilima ce ke magana da kakkausar murya: "suhayr kishi a jininmu yake kuma Allah
ne ke halittan kowani bawa da dashi,
To amma sai yasa nawani yafi na wani Karki kasance me
nuna kishinki a fili yata ki sassauta kishinki, don kishi ba hauka bane wallahi indai kikayi koyi dani toh tabbas suhayr zaki zama yar gaban goshi a
gidan saheeb".
Kuka suhayr keyi wanda saida tasa kowa na wajen kuka wanda zan iya cewa kukan yazame ma kowacce amarya al'ada,
Dan kwa dazaran za'a kaita gidan miji sai ta dinga kuka saboda tunanin ta rabu da gida da kuma yan uwa da Abokan arziki, kenan sai dai ziyara
Mahaifinta shima yayi mata fada kwarai me shiga jiki. An fito za'a sata a mota bawata mota mai tsada tanajin abun da ake cewa Amma bataji komaiba illah kosawa da tayi akaita gidan saheeb, Acikin daya daga acikin golf din akasa suhayr
Sai yan uwan hjy ikilima, dana mahaifinta suka cika sauran motacin biyu don ba kawa ko daya data shiga
motar kai Amarya daman tun asalinta suhayr daman ba mai jaye jaye bace.
Ankaita gidan ta dake zooo road kowa sun watse sabo da mahaifinta ya bada umurnin kar wanda ya kwana," daga suhayr sai saheeb aka bari acikin gdansu
A daren yau hankali ya kwanta, suhayr ta zama mallakin saheeb, "Suhayr ayaune zamu kafa tarihi a rayuwar mu, yaune muka kasance ma'aurata," kunyarsa suhayr keji wanda abaya ba haka takeji akansa ba. "Tashi muyi sallah ko?" Cewar saheeb wanda farin cikinsa yakasa boyuwa,
"Toh" tace. Alwala suka dauro suka gabatar da sallah da godiya ga mahaliccin su, wanda ya kawosu zuwa wannan lokacin. Sun danyi ciye ciye daga bisani Suhayr ta tashi tahau gado ta kwanta a tsorace don tasan daren yau shine daren farko da zata kwanta gata ga namiji wanda a yanzu shine annurin zuciyarta.
Tuni bacci yayi awon gaba da ita, saida saheeb ya kammala ya tashi ya matsa kusa da ita yana mata rada a kunne "cutey kitashi ki cire wannan kayan kin san suna da nauyi zasu hanaki bacci".
Tashi tayi tana cewa "Umma dan Allah ki kyaleni kin sanfa nagaji dayawa," tana bude Ido sai taga Ashe saheeb ne sai ya mata murmushi rungumeta yayi yace "yar umma daga yau kin daina kwana da umma", dariya tayi tace "hakane saheeb sabo ne kawai kasan bana iya bacci sai da umma,"
Saheeb yace "gashi yau za kiyi bacci ba tare da umman ba" dariya sukayi duka, tashi tayi ta dauko kayan bacci tasa amma fah saidata shiga cikin toilet saboda kunyarsa data keji.
A daren yau saidai muce Alhamdulillah saboda saheeb ya cimma burinsa akan masoyiyar shi, ya maida mugun yawunsa "Assalatun farko saheeb yatashi yayi wanka
Sai ya fita zuwa masallacin dake kusa dasu, bayan ya dawo ne ya tadda Suhayr kwance sai faman kuka takeyi, wanda hakan yaba saheeb tausayi, sabo da yasan cewa yayi laifi.
Amma kuma ai hakuri ya zama wajibi daman haka auren ya gada, haka ko wacce mace tayi going through. daukanta yayi cik ya kaita toilet ya hada mata ruwan zafi, ya taimaka mata ta gyara kanta, ta gabatar da sallah.
Sai suka koma suka kwanta farkawa tayi ta shiga kitchen don ganin abun da zata iya dafa musu, amma taga wayam hakan bai bata mamakiba sabo da tasan mijinta bashi gareshi ba. wani corner ta leka taga kayan garanta daki guda nan tafara tunanin abunda zata sarrafa amma babu kayan hadi,
Tana cikin wannan nazarin ne taji ana knocking kofa, Budewa taje tayi Ali direba tagani yace ina "kwana uwar dakina ya bakon waje?," "Lafya" tace, yace "Daman hjy ce tace in kawo muku abinchi". Tace "shiga dashi mana," Coolers ne na abinchi ya shiga dasu ciki ya ajiye a falon.
Juyowa yayi yace "sannan tace kiyi min lissafin abubuwan da kike da bukata yanzu kasuwa nayi" tace "toh" sannan ta lissafa komai a littafi ta rubuta ta mika mai ya tafii.
Tsayawa tayi tana tunanin irin sonda iyayenta ke mata, abun da iyayen saheeb ne yaka mata suyi mana wannan hidimar amma sai gashi umma ce dakanta,
Duk yanayin da suhayr take ciki saheeb na kallonta ji tayi an dafata da sauri ta juyo tace "my life sannu da tashi".
Sam bata nuna mishi a wane hali takeba, "Suhayr tunanin me kikeyi?" Ya fada yana kallonta. Tayi saurin cewa "Lah my life ba komai kawai tunanin yadda zan faranta maka rai nakeyi".
H'm dariya yayi don yasan kwaskwarima tayiwa kalamanta, tace "kaji mijina muje dinning kaga abun da umma ta aiko mana dashi tace muhuta karmu dafa komai".
Daukanta yayi suna dariya cikin nishadii da kaunan juna, Sunci sunyi kat suka koma falo suna kallon Indian film Bayan wata biyu, suhayr ta kasance mace mai kiyaye duk wani hakkokin mijinta
Babu abin da ya nema ya rasa daga gareta, matsalarta daya a duniya kishi bata son kishiiya kuma bata kaunar duk wata mace ta rabeshi hakan yasa ta roki alfarmar mahaifinta ya bashi kudi ya ja jari ya bude shagon sai da hula da agogon maza,
Domin bata son yayi "white collar job" da hakan zai kawo cudanyrsa da mata ko da kuwa yan uwanta ne bare kuma nashi. kyawawan dabiunta da kuma son da ta ke masa yasa ta samu love dinsa 100pecent domin duk wuya duk dadi tana jurar yi masa komai, dan har sai da takai cewa ko......H'm friedns Barkanku da sapiya----------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 11:57 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 11:58 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (6) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Asslm friends da fatan kuna cikin koshin lafiya, wato naga Alamar bakwa son littafin nan, h'm to ai shikenan tinda bakwa so din, sai ku fada min wanda kuke so, in kuma bani da shi to Nifa Allah ya hutar da nine ehe.!!
Watarana Suhayr tana zaune a falo sai taji ana knocking sai ta mike taje ta bude kofar taga wasu yan mata kyawawa, sunsha mai da foundation, kallonsu takeyi shekeke wanda hakan yaba nimrah haushi tace wai ko baki ganeni bane?".
Suhayr balla ma nimrah harara tayi tace "me kikazo yi gida na da wayannan masu kama da aljanun?" Suhayr ce ke magana cike da isa da fankama. "kut gaskiya nimrah matar wannan naki batada mutunci mune ma masu kamada Aljannu?"
Suhailah ce ke magana tana taunan cingam. "Suhayr magana muke kina kallonmu", dariya tayi tace "ina jiran inji duka ne sabo da Nace muku masu kama da mami water".
"Ke!" Nimrah ce ta dakawa suhayr tsawa "da kata kiji karki ga kina yima sauran mutane in sun zo gidanki kice zaki mun, dan ni nafi karfin yinki wallahi sai dai in nayi da gyatumin ki". what.!!?
Suhayr ce tace "Habawa Nimrah kinso ki tafka babban kuskure wajen taba mun iyaye wanda nasan sunfi-min naki iyayen sau miliyan, ai kin san bakin rijiya ba gurin gadar makaho bane,
Nimrah kafin in bude idona in rufe ki fitar min da wayannan masu kamada yan ruwan inba hakaba I will surely sure you gals mah true colour".
Nimrah tace "Aikam da wuya yau inba'a haifi da marar Ido ba" inji nimrah wanda ta runtse Ido bataji bata gani, don tsabar takaicin abin da Suhayr tayi musu. "
Mai gadii John" Yayi saurin shigowa yana cewa "yes hjy lafya irin wannan kira". cikin bacin rai Suhayr tace "How many times have I warn you that I don't want to see any lady in dis house apart from my mum? Haven't I warn you?"
John jiki na rawa yace "yes mah," "oya before the count of three I don't want to see any of this things infront of me".
Hhhh ai kwa da duka john ya rakasu amma fah Nimrah baki yaki mutuwa "cewa tayi "yau kin nuna min gida nakine Suhayr amma sai kinyi nadamar cimun mutunci shegiya yar matsiyata." Ciki ta koma ta harde kafa
Ashe saheeb na nan suhayr ke cima nimrah da friends dinta mutunci, "Hayaniyyan me nake ji suhayr?" shuru tayi kaman bada ita yakeba
Sai can ta dago ta kalleshi tare da cewa "Pls saheeb ka gayawa kanwarka, nasa mata boundary da gidan nan". Shima cikin bacin ran yace "kozaki iya gaya min dalili?".
Sai tace "dalili shine zan iya raunatata inta kara shigo min da kawayenta, masu suffan jinnu gidan nan, Akan mema sai tazo gidan nan
Kai nifa bana son shisshigi ka gaya mata," Saheeb ne ke zaune kusa da ita yace "suhayr Nimrah kanwata ce kiyi hakuri da abun da zan fadi
Nimrah nada ryt din zuwa inda nake". Tayi saurin dakatar dashi da cewa "dakata Saheeb ina da kishi da bana so kayi tozali dawata mace inba niba, don haka ta kiyayi gidan nan, don ko jaririyace ina matukar kayi mata murmushi bare baliga kaman nimrah."
Yace "Amma dai kinsan nimrah muharramata ce?". Tace "Koma me cece na gama magana" tashi tayi ta shiga daki. A ranan ya shiga wani hali ummansa ce ta kirashi ta cimai mutunci, sannan da sharadin saiya kara aure ko yana so ko baya so.
Tunani mai zurfi ya shiga amma bashi da yadda zaiyi, Suhayr ta hanashi mu'amala da mata harma da yan uwansa, Gashi saheeb yana matukar kaunar matarsa baya son yaganta cikin damuwa, baya son ganin bacin ranta,
Amma kuma yana mamakin kishi irin nata, inda za'a bashi littafi da Biro tsaf saiya rubuta kishin suhayr gaba daya.
Saheeb Ya kama sana'a ba kama hannun yaro acikin manyan plaza dake kan hanyan Hotoro. da yake wajen center ne inda manyan mutane ke wucewa, gaba daya kayansa na wajene saidai kayan gida kaman su shadda, huluna, da dai sauran su.
Amma fah koda yaushe akan waya sukeyi da sahibar tasa wato suhayr, arana saita kirashi fiye da sau talatin, sabo da kishi dake dawainiya da ita Amma hakan bai hanashi yin budurwaba, lol 😜
Daman masu iya magana na cewa duk wayon amarya sai ansha manta, haka shure shure baya hana mutuwa.
Rannan ya tashi da wuri daga shago ya kashe wayansa, sabo da yana so yaje family house dinsu ance ana Neman sa, don ya san inya gayawa suhayr sai tasan yadda tayi ta hanashi zuwa,
Adaidaita yahau sai dorayi, yana shiga aka yi mishi cha mijin hajiya! Mijin hajiya!! Mijin hajiya!!!. ya danji kunya kwarai amma ya maze yaga dangi kowa ya hallara abun yayi matukar razana shi, zama yayi sannan ya gaida su,
"Yauwa saheeb abun da ya taramu anan shine game da matarka suhayr data hanaka sakat sabo da kana zaune a gidan su sannan kuma ta baka jari". Inna larai ke magana shuru yayi baice kala ba sabo da yasan daman za'a Rina, "dalilin taruwar mu shine muna so ka kara aure".
Zare Ido yayi yace "aurefa kukace? dan Allah kar kuyi min haka dududu watanmu nawa da aure za'a kawo min zancen wani aure yanzu Haba dan Allah ku canza wata shawarar amma ba wannan ba".
Ummansa dake gefe tace "dole kayi aure don samun kwanciyan hankali". Bashi da yadda zai yi dole ya amsa masu ba don zuciyarsa na so ba, a haka ya koma gida cike da tunani iri daban daban, ta ina ma zai fara sanar da Suhayr wannan zancen?.
Da shigarsa yaji kakarin amai da sauri ya yadda ledojin dake hannunsa, da gudu ya shiga toilet suhayr ya gani tafita hayyacinta. "Subhanallah cutie meke damunki haka"?
Bata iya bashi amsaba, illah hawaye dake tsirarowa daga idanunta "Saheeb zan mutu ka kaini asibiti".
Mota ya dauko ya sata suka wuce asibiti. Likitane yace ashiga da ita, amma suhayr dukda ciwon da take bata sassauta kishinta ba, gam ta rike hannun saheeb tare suka shiga Hhhh lol 😂
Anyi mata test kusan kala uku, " congratulations yallaboi madam tana dauke da ciki wata biyar". Saheeb yayi saurin cewa "Likita wata biyar fa kace ya akayi bata saniba kuma nima haka?"
Likita yace "Tana iya yuwuwa inna farine bazata ganeba, haka kaima, amma ya kamata a kula da ita sosai
Musamman ma abinchi, tadinga cin kayan marmari irin su zogale dama dai sauran kayan Karin jini A yanzu bata bukatar motsa jiki sabo da dan bai riga da yayi kwari ba".
Murna wajen saheeb sai wanda yagani don ji yake kamar ya hadiyeta don murna. Nima sai na sami kaina ina yin murnar Hhhhh lol 😜
An sallamesu, hjy ikilima musamman tazo don ganin yar tata, Sunsha fira tsakanin ya da uwa tuni aka fara siyayyan kayan ahaihuwa.
BAYAN WATA UKU
Lokacin cikin Suhayr yana wata na takwas, dangi fah sun tashi haikan ganin saheeb ya kara aure, domin sun ce suhayr tayi musu kane kane gashi yanzu arziki yaci uban Nada, sai a cika gida da iyali,
Saheeb ya fara Neman aure gadan gadan, amma duk abun da yakeyi suhayr bata saniba, Har ansa ranan wata uku duk ya maidata biri-boko, Hhhh lol 😜 makota tashi ga saiga wata mata ta shigo, tana cewa, "ke ummu aiman Ashe makocinki aure zaiyi?
Duk kishin da ake cewa matarsa na dashi". Ummu aiman sai siginal takewa indo amma itako sai zuba takeyi, Sai da ta gama tsaf suhayr taji wani irin ciwo na neman cin karfin ta tace,"Baiwar Allah ko zaki min kwatancen gidan su yarinyar?". "kwarai mai zai hana". Inji indo. Nanfa indo tayi ta mata kwatance har ta gane.
"Nagode" tace tashi tayi taje gida, tace "yau sai ya gane cewa, ruwa ba sa'an kwando bane, sai ya gane shayi ruwa ne sai na nunawa saheeb cewa yayi kuskure namiji munafiki, ni zai munafurta? ya kara aure? kabashi dukkan yardarka yacima amana".
Gyale kawai ta chanja ta nufi Gidansu yarinyar tayi sallama da uban yarinyar, cike da mamaki ya fito yana kallon Suhayr. tace "naji labarin cewa, zaka aurawa mijina yarka? Ina tabbatar maka da cewa sai-----------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 11:58 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 11:59 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (7) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Sai tace to amman kasani yarka zatayi kwanan prison matukar tace zatayi kishi dani, don saina aikata inda bazata kara jin kamshin mijina ba,
Sannan inkun shirya yarku tazo gidana, toh ku kawota da likafali, don sai nayi ajalinta". Uban yarinya yace "aikin banza, kewacece?
Aikam sai munyi Shari'a dake har yaumut-tanadi". Suhayr tace "Mune gwamnati kaje ka tambaya waye Alhj kabir sulaiman ina jin kasanshi, toh nice diyarsa daya tilo, In yazo shi mijin nawa kace yaci gaba da Neman aure ni kuma, inci gaba da rusamai tsari".
Tura cikinta tayi ta shige mota ta badamai kura, Uban yarinya yace "tab ai kwa aurennan anfasa, bazai iya da wannan jarabar ba da ganinta zata aikata duk abun da tace. Hhhh lol 😂 Saheeb yaje zance uban yarinyar Yace "karya sake zuwa mai gida sabo da matarsa tazo tayi barazanar kashe musu ya". gida ya dawo cikin bacin rai ya iske Suhayr
Sai yace "Suhayr hankalinki ya kwanta kin raba abun da Allah ya hada, tun kafin muyi aure kike abu daya haryanzu kinki ki daina". tana daga zaune tace "kamanta dakwai ranan danace ka kalli kwayar idona? nace ma mai ka gani"?
Kace mun JARAB EL GHIRA? Flames of jealousy? Toh I can do more than wat you are thinking saheeb, Bantaba Sanin cewa kai munafiki bane sai yau butulu kawai wanda ke manta Alkhairi, Badan so baya dubi da nasaba da chanchanta, Yaushe zan aureka Saheeb?
Amma shine zaka zaga bayana kaci amanata? kayi hakuri da kalamaina, nasan kai mijinane, dole infadi Nasan duk umma ce ke sawa ka kara aure, kuma wallahi Allah ya saukeni lafiya, sai naje har gidan ta gaya mun dalili, Inace ita kadaice wajen mahaifinka?
Ohh shine sabo da kiyyaya zatasa ka kara aure toh zan gani, ga fili gamai doki Saura sukuwa". Mari taji ya sauka a kuncinta,
"Karki sake yima mahaifiyata cin zarafi a gabana inke baki san darajar iyayeba toh ni na sani kuma aure ba fashi sai nayi kuma ra'ayinane, bana umma ko Abba ba, Saina cika gidan nan da zuri'a mai yawa, sai dai ki mutu.
Kuncinta ta rike tana mai kallon saheeb Ido cikin Ido, Cike da takaici tace "tabbas saheeb sai kayi nadaman marina saika san cewa ka mareni Akan wata yar iska? Kayi kuskure wannan So ne ko kuma kiyayya,?
Saheeb magana nakeyi kana jina, aikam inhar ina numfashi bakai ba kara aure acikin gdannan, Na yima rana shine zakamun dare"?
Wasu zafafan hawaye ne suke kwaranya a cikin idanun ta, amma saheeb koh kallonta baiyi ba, bare kuma ya tausaya mata ko dan sabo da abun da take dauke dashi a cikinta.
Fuu Saheeb ya wuce kaman zai tashi sama kuka suhayr keyi tana cije baki sabo da wani ciwo datakeji, Tana cikin wannan halinne taji sallama ashe kawartace tashi tayi ta bude kofa "ah ah maraba da mutanen jigawa saukan yaushe ina yaran da oga?".
Qawar tace "tab suhayr uwar biyu kenan wannan ciki naki da akwai bayani". dariya suhayr tayi a falo suka zauna tasa mai aikin ta takowowa bakuwa Abinchi da Abunsha, "kawata naji dadin zuwanki wallahi, inada damuwa sosai", tas ta kwashe komai ta gayawa kawarta.
Qawar tace "tabbas suhayr keme lefi ce ya zaki dinga yin Abu irin wannan? Bayan kinsan halin maza in suka so Abu sai sunyi ko'a boyene?
Tunda nake da baban hydar ban taba cewa bazan zauna da kishiya ba, dama zai kara auren wallahi Nina shige mai gaba don ganin yayi auren kuma gashi muna zaune lafya". Suhayr tace
"Tab aini Jarababben kishi na bazai barniba, Akan saheeb zan iya rasa raina". Ummu hydar tace "Tab bari kiji kadan daga cikin wani littafi na matan aure dana taba karantawa," kila ya miki amfani don bance dole ba".
" Idan har kika yarda da cewa namiji ba zai qara aure ba suhayr to wllh kinyi wauta domin basu da tabbas a cikin wannan bangaren, karki yarda namiji yayi miki alqawarin baxai miki kishiya ba, shi kanshi ai bai san me yake gaba ba, idan Allah ya rubuta sai yayi auren nan to fa ya xama dole yayi shi".
Ta cigaba da cewa "Idan kuma kika ce ba zaki rike dan Mijinki ba, dan Kishiya Nan ma kin tafka shashanci babba, don Idan kin haifi naki 'Ya'yan babu tabbacin cewa xaki dauwama a gidan ba
Ko a cikin duniyar ma, Idan kuwa kika ce namiji ba dan goyo bane kin zama sakarya, domin kin mance da cewa ai kece baki Iya yanda ake goyon namijin ba" Idan kuma kika ce Kishiya ba abokiyar zama bace ba, mijinki baxai qaro wata matar ba toh ke naki 'Ya"yan Idan kin haifa jere za kiyi dasu a dakin ki?
Karki raina uwar mijinki domin tamkar uwa take a gurin ki..........ta dan numfasa snnan ta cigaba "Idan kina wulakanta dangin mijinki, toh naki dangin waye zai girmamasu? Idan kika ce ke bakya son kishiya toh sauran Yan mata da zawarawan gari suyi yaya?.
Suhayr tabbas yaka mata kifarka daga nannauyan baccin dake dibanki Suhayr shuru tayi don tasan dakaman wuya gurguwa da auren nesa, yadda take da kishinnan aikam bazai taba yuwuwa ba,
Ummu hydar taci gaba da cewa, "Idan kika ce ke bakya son kishiya toh kisani, da yiwuwar ayi miki kishiyar waje wacce Idan akayi rashin sa'a kishiyar nan taki ta waje ta aiko miki da "SAKON MUTUWA" HIV hhhhhh tab-din lalle kam
SUBHANALLAH, Suhayr meyasa baza kiyi amfani da wannan hudubar ba ki gyra, lahiranki?". "tabbas ummu hydar da kishiyar gida tabbas na kwammace ta waje Inta tashi ta kashemu mu duka".
Ummu hydar tace "kash yayan da kika Haifa kuma fa?". Cewar ummu hydar. Suhayr kai tsaye tace "Suzama marayu" Ni kam dai Nace Suhayr kin fara bani tsoro lol 😜😜 Fans ku kawo min agaji,
Duk abunda kawar suhayr ke fade duk a kunnen saheeb, Hannu yadaga sama yace "Allah kasa suhayr tayi amfani da wayannan fatawa" amma me
Ai sai yaji akasin haka. a ranan ummu hydar ta tafi tabar suhayr da dumbin tunani. Shi kuma saheeb ya rasa yadda zaiyi, akullun yana da shaawar ganin ya tara mata domin ya tara yaya masu yawa.
A haka suhayr taci gaba da tsula tsiyarta, duk inda taji yaje neman aure saida taje ta wargaza, sai da tayi sanandin lalacewar auren daya nema guda 7. danginsa suma sun bashi mata duk yadda akayi da boyewa sai da ranar daurin aure taje da bindinga tasawa waliyyin a goshi yana daurawa zata aika dan banza lahira.
Ci gaban labarin
Nan yan'uwa aka fara cece kuce akan saheeb lallai suhayr tafi karfin shi, harta isa ta hanashi qara aure?. Saheeb ne ya juyo cikeda bakin ciki, dajin kunya ga dubban abokansa harda abokan cini kayyanshi Yace "suhayr am disappointed in you, you disgrace me in public? Had I know zaki zaman mu matsala a rayuwana, tabbas daban au........"
"Saheeb dakata" wata murya yaji kakkausa da alamu babu wasa acikin muryan. Juyowan da Saheeb yayi mahaifinsa yagani, Mahaifin nashi yace
"Tabbas auren ka da suhayr alkhairi ne, Sannan bakada wata kallaman dazaka aibanci suhayr, tacika mace jaruma, sannan wallahi tayi ma komai duk abun da ake so mace ta dunga yiwa mijin ta to ai ka samu". Hhhhhh tab-din Anya kwa.!!!?
Shidai Saheeb bakin ciki ne ya isheshi, yarasa makemai dadii yaci gaba da cewa" kaida kanka Saheeb duk randa zan tambayeka cewa ya zaman takewanka da Suhayr? kakan cemun babu wata matsala,
Toh banga dalilin ka na kara aure ba tunda bata gaza wajen kyautata maka ba". "Amma Abba".... "Bansanjin wani kalma daga bakinka ku tafi gida kawai". Habawa ai kwa sai......"
Kai kai kai tab-din Naga Suhayr tana hararata kar nima nasha Bindiga dan haka Nayi 👉 nan aguje 🏃 h'm sai tomorrow kuma in sha'allah ----------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 11:59 AM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 12:00 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (8) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Sun koma gida ba wanda yace ma kowa kanzil, Ahaka suka cigaba da rayuwa har Suhayr ta haihu
Amman baice da ita komai ba, ko barka bare kuma ya dauki da yayi masa huduba tun daga asibiti daya kaita bai kara hada Ido da itaba.
Bayan mahaifin Saheeb yazone ta gayamai halin da ake ciki, ya yiwa da huduba yasa masa sunan mahaifinta wato kabir wanda tayi mai lakabi na NOOR wato haske
Murna a wajen Suhayr bai misaltuwa. Suhayr ta hana kowa zuwa mata barka daga danginta har na mijin, Sannan ta fada ma ummanta baza tayi suna ba kuma bazat a koma gida wankaba,
Abunda ya daurewa umman ta kai shine yadda Suhayr take yin magana ba koh alamar shakka, ta kaleta tace "Suhayr meye dalilinki na cewa baza kiyi sunaba? sannan kuma kinsan yin suna yazaman mana al'ada"
Tace "Umma nace Bazan yi sunaba' sabo da bazan juri ganin mata acikin gidana ba Sannan meye abun doki dahar sai anyi suna bayan uban d'an baya maraba da zuwansa duniya" tana magana tana zubda hawaye wanda duk wanda ya kalleta sai yasan cewa Rashin kulatan da Saheeb bayayi yana cimata tuwo a kwarya.
Umma tace "Suhayr hakanan Saheeb bazai juya miki bayaba saidai inkin yimai laifi" Suhayr tace "wani laifine umma nayi banda ya wuce naje na wargaza mai auren da yake shirin karawa? Nibanyi fushiba daya munafunce ni bai sanar dani cewan zai'yi aureba sai shine zai yi ?
Nikuma nayi amfani da kishina wanda bashi da maraba da leban wuta na ruguza komai, kishiya a gidan Saheeb sai dai ko bayan raina".
Umman Suhayr ce tace "kull inba hakaba zaki tafka kuskuren da sai kinyi dana sani, wannan maganar in kikayi wasa yan Ameen suka amsa toh wallahi zaki mutu kuma yakara aure ke har hudu sai yayi".
"Umma bazan iya jure jin kalamanki ba, Maiyasa bazaki bani goyon bayan yaki da kishiya ba? Wallahi umma kishiya ba abokiyar zama bace" Suhayr ke maganar cikin muryar kuka. Umma tace "Tabbas suhayr kishiya abokiyar zamace idan kikayi dace"
Tayi saurin cewa "Umma kiji kalamanki? cewa kikayi idan nayi dace? Nikam kishiya ba kwai bace umma bare in kwankwasa ta inji irinta, Umma idan kishiya abunyi ce mai yasa ban tashi na ganta a cikin gidan mu ba?
Idan kishiya dadii ce maiyasa bakice Abba yakara aureba? Idan kishiya dadii ce meyasa Yawancin marubuta na duniyar yanar gizo ke fada mana illolinsu? Lol😜😜😜 aa pah tam.!!!
Umma tace "Suhayr karki zurfafa kishi don koba jima koba dade namiji mai son aure sai yayi, Allah ya hadaki da miji jarababbe sai dai kiyi hakuri " tayi saurin cewa
"Hakuri Umma? Nikam zanyi amfani da jarabata da jarababben kishina inci gaba da wargaza mai tsari" Itadai umman Suhayr cewa tayi "Allah ya ganar dake hanya madaidai ciya,
Amma duk abunda kike na kyautatawa, tabbas kici gaba karki fasa namiji wawa ne. Hhhhh lol 😂 Aradu banda Ni Nikam Rass nake Man.Bash An hado mata sha Tara na arziki harda k'yautan mota tsalleliya daga mahaifinta,
Akwati biyar nata' uku na jariri NOOR, Sannan ga kudi masu yawan gaske. Rago biyu Saheeb ya yankawa yaro, mai aikice tayi gyran nama ta soyashi tsaf makota kawai tamikama suma ba dukaba, dangin Saheeb sunyi tsaigumin Rashin kawo musu naman dabatayi ba
Saheeb yafara sauyawa, ya daina fushi da ita Sun koma kamar da amma fa burinsa yana nan na kara aure. wata safiyane aka buga kofa, direban gidansu tagani, "lafiya naganka da sanyin Safiya?". driver yace "eh Alhaji ne yace in sanar miki da cewa kishirya wani sati ansama miki makaranta a *NORTH WEST UNIVERSITY*"
"Dan Allah pah?". Tayi murna sosai, saboda murna saida tabashi tukwaici. Saheeb na shigowa ta karbi ledar dake hannun sa, tayi mishi maraba yayi wanka ya gabatar da sallah sannan take gayamai cewa an sama mata makaranta, yaji dadi kwarai yace Allah ya bata sa'a Shiri suhayr take yi zata gidan su tun Asuba ake dauki
Tare suka fita ita da Saheeb ta saukeshi a shago ita kuma ta wuce da alkawarin inzata dawo zata biyo ta daukeshi, " I love you Saheeb" tace tana mai kallonshi, yayi murmushi yace "your love to me is like a priceless Gold"
Sai itama ta mayar masa da cewa "You are expensive in my life Saheeb I can go on without you in my world". dariya yayi yace, "Suhayr kenan duk abunda kika fadi nima haka nakeji a zuciyana".
Kissing dinta yayi ya shafa kan Noor yace "ka gaida grany da takwara" Har yayi nisa ta kirashi "pls Saheeb banda kalle kalle". Hancinta ya lakuta yace "I promise you dat my love". Akan hanya ta sauka tayiwa Umma siyayya, tufa ta saimata da kayan marmari.
Rike take da Noor saiga wata mata daganinta bazawara ce don bazaka kirata budurwa ba duk'da ba abun mamaki bane samun babban mace kamarta batayi aure ba.
Kusa da Suhayr ta matso tace "Sannu fah inason yaronki". washe baki tayi abunka da mai yaro wawa, Okay to Nifa ban da Aure mah balle yaro kuma daga nan kuma in zama WAWAN lol 😜
"Tnx alot kin ganshi duk ya kosa yaje yaga grany". Matar tace "Ah in bazaki damuba dan Allah meye sunansa dake kanki". Suhyr tace "Sunansa NOOR ni kuma Suhayr". daidai da an miko mata kayan data siya na kayan marmari.
Tace "dan Allah bawan Allah biyoni dashi". bayan boot ta bude ta zubasu. tuni suhayr ta manta da wannan matar, motar ta ta shige don Suhayr batason zakewa.
"Baiwar Allah tsaya".......Ina tuni suhayr ta figi mota tana isa bakin gate tayi horn aka bude mata, Packing loge Ta nufa ta jera tata motar da sauran. waya ta dauka don ta sanar ma Saheeb ta isa amma akasamu akasi yana waya kasar waje, don yayi odan kaya Ta kirashi yafi sau tulin gashin tinkiya amma shuru"
Tuni zuciyarta tafara tafarfasa, cewa Saheeb da mace yake waya. K'ara k'ira tayi aka samu ak'asin a 'network' kiran yashiga wayar wata..... Bugu daya aka dauka Ba jira Suhayr ta fara bala'i ta inda take shiga batanan take fitaba "ka tuna Saheeb you promise me cewa baza kayi waya da wata mace ba pls Saheeb kasan ko yadda nakeji yanzu?.
Shuru taji Suhayr tace "mijina abun alfahari answer me pls" "Hello kiyi hkr ba mijinki bane" damm! taji zuciyarta ta buga jin muryar mace da yake shu'uma tasamu dukda bata Santa ba amma tana bakin cikin ganin mace ta hana mijinta sake wa koh kuma mace mai shegen kishin tsiya.
"Kinyi shuru nace ke wacece?" cikin zafin rai Suhayr take magana. "Islam ce Kuma ni budurwan mijinki ce, gashi kusa dani yana bacci daya tashi wanka zaiyi yayi sallah don bashida cikakken tsarki saimu wuce juffatu muyi shopping". Jiri Suhayr take gani idonta na juyawa hhh lol 😭
Ai karfin hali tayi tace "baki isaba yar iskama irinki harkin isa mijina yaxama abokin iskan cewar ki? Karyarki tasha karya wallahi kin gamu da ajalinki in dai nice yar iska marar mutunci marar Sanin ciwon kai must"
Tsaki tayi tace "kinibibi sakarya indai mijinki ne ke kadai sai ingani. katse wayan tayi. Mai gadi taba NOOR ya shiga dashi tace tana zuwa Mota ta shiga Shagonsa ta nufa cikin ikon Allah yana ciki yana ta sallaman customers. Saida tabari ya sallami kowa
Sannan tace "Saheeb kataimakeni ina cikin rudani wacece kaba wayanka?" Saheeb dafe kirji yayi yace "No Suhayr you most be dreaming tunda na shigo shago wallahi ko waje ban lekaba"
Mamaki duk ya cikata Kira wayar kiji cikin ikon Allah ta kira yadauka taji gashi dai muryan mijinta ne duk sai taji kunyan ta kamata "Saheeb kayi hakuri "
"Shhhhh Karkiban hakuri abun da nake so dake shine kizama mai yi mun kyakkyawan zato, kiyarda dani Suhayr" sai tace-----------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
0 comments:
Post a Comment