Cike da jin kunya Suhayr tace "Saheeb kayi hakuri amma kaji na rantse maka mace tadau wayanka". Saheeb yace
"Haba Suhayr ana samun matsala daga network In mutun yakasa samun ka kawai sai suyi Diverting Call dinka saiya shiga wayar wani Inkuma dashi wacce ta dauka in ta duba baza taga lambar ba" Tashi tayi tace "natafi don koh umma bata ganni ba"
Saheeb yace "Ok love you " kallonta Saheeb keyi kaunar matarsa kawai yakeyi a ransa. gida ta wuce ummanta tagani rikeda Noor sai kuka yakeyi "Oyoyo umma"
Umma ta tarbeta da cewa "dakata Suhayr Na rasa gane miki, wannan kishin ina rabaki dashi amma kinkiji." Suhayr tace "Umma me nayi kuma" Suhayr tabata rai
Umma tace "inajin duk Abunda ke faruwa shine kikaje shagonsa koh? kitada mai da hankali ? In baki ba mijinki farinciki ba Suhayr me zaki bashi? nidai ina baki shaawara ki daina don bashida amfani, Amsheshi kibashi madara yasha".
Haka sukayita hira har yamma gashi Abbanta bai dawo ba, tabar sallahu cewa tana gaida shi zata dawo kafin ya koma. saida tabiya ta shago ta daukeshi, Suna isa nimrah suka gani a bakin gate Sai cin magani take tana cika tana batsewa. Mai gadine ya bude gate suka shigo,
Fitowa Saheeb yayi rikeda Noor a hannun shi, ya kalli Nimrah yace "Nimrah lafiya kike kuwa? Baki iya ki gaidani ba?" Nimrah tace "dan Allah yaya kasan tun yaushe nazo gidan nan?
Sannan kuma umma tace karna dawo saina ganka". Zaro Ido yayi yace "lafya?" Nimrah tace "Inafah kusan sati umma batada lafya ba kazo ka gaidata ba koh kiranka akayi baka son dauka". Nimrah ta tabe baki ganin Suhayr tazo wajen Saheeb yace
"Nidai banga kiranku ba gaskiya" Suhayr tace "nicenan nake kashewa, saboda muna cikin jin dadi ba wanda ya isa ya hanamu sukuni" "keh Suhayr kin san koh uwa tawuce gaban wasa? Yanxu da mutuwa tayifa? Saheeb ke magana cikin bacin rai. Suhayr tace "Dana shiga uku".
Nimrah dake tsaye tana ballama suhayr harara , tace "kuma umma tace inna ganka mutaho tare". Suhayr tayi saurin cewa "Ba inda zashi sai gari ya waye" Nimrah tace "Aikam kinyi kadan inace kema wajen naki uwar kikaje? kuma sai naga bai hanaki ba". Suhayr tace "ai uwata ce" Nimrah tace "shima Uwarsa ce"
Kallonsu kawai yakeyi yana kallon son zuciya irinna Suhayr..... Baice da ita komai ba hannun Nimrah ya rike taji kaman ta kurma ihu, tace "Saheeb ina kake shirin zuwa?" shuru yayi Nimrah tace "gurin ummansa zashi" tafadi tana mata gwalo.
Hmm ciki Suhayr ta shiga tace "lallai sai nayi maganin Nimrah Saina nuna mata cewa ita karamar yar iskace", Kwafa tayi, hmm Sallah ta farayi Sannan ta shiga kitchen tafara girki. Taliya ce da macaroni ta dafa wanda yaji kayan lambu" wanda ya hada da carrot, pea, harma da cabbage, Ga hanta Sai ta danyi pineapple juice dan daidai.
Farfesu tayi musu na kafan sa Tajerasu a dinning. Jikin mahaifiyar shi ya tsananta, Tuni yashiga rudu asibiti aka wuce da ita, Ruwa aka Samata. da yake kusa da zoo road ne "Bari naje gida" yacewa kanninsa ya kawo musu abinchi Yana isa gidan ya shiga Suhayr yake kwalawa kira
Fitowa tayi cikin wasu yan iskan kaya wanda bashi da maraba da ace tsirara take. Bata nuna mai wani abu ba, Saima murmushi da take tana taku daya kan daya, wanda tuni Saheeb yaji gaba daya jikinsa ya gama mutuwa,
Kusa dashi ta matso "wani irin kamshi yaji tuni ya sunkuceta ta sai daki kan gado ya ajeta. yafara.
"Lafiya yaya bai dawo ba har yanzu?" Cewar Sarah mai bima nimrah. "hmm inkika bibiya wannan yar'iskan matar tasa ta hanashi ya fito" cewar Nimrah Amrah dake zaune tana kallonsu Batace dasu uffan ba don arayuwarta ta tsani ayita cece kuce don ita tace Suhayr bata kai matsayin dazata dinga maganarta ba.
Amrah hatsabibiya ce rigimanma don tace Nimrah batai komai ba. Nimrah tace "Amma bari na fita waje inje in siyo mana koda dankaline muci". Nimrah ce ke magana daga ganin fuskanta kasan cewa akwai damuwa kwarai. wata budurwace da ganinta kasan tasha boko ta koshi tajiyo duk hirarsu.
Tace daga gani da matar wansu suke Amma kuma sunban tausayi. Tashi tayi ta dafa kafadan Amrah tace "beautiful ya naga kin bata fuska? Kina neman ki bata kyawunki?"
Amrah tace "Kamar yadda kika gani mahaifiyar muce ba lafya kuma da yayanmu mukazo yaje ya kawo mana abinchi kinga bashi ba labarin sa kuma baya rasa nasaba da matarsa don taki jinin mu balantana kuma umman mu kila ita ta hanashi dawowa, yadda kikasan tayimai asiri".
"Karki damu ya mai jinkin" ta cewa Nimrah. Nimrah tace "Da sauki bacci takeyi". "Ok bari ina zuwa" flask taje ta dauko makare da abinchi ta kawo gabansu tare da cewa "Pls kannina kuci abinchi idan umma ta tashi kubata taci".
Mamakin kirki irin nata sukeyi Sarah tace "inba zaki damuba inason Sanin sunanki". Budurwar tace "Ni sunana Atika". "Suna mai dadi" cewar Amrah. Har dare ya tsala Saheeb bashi ba alamansa,
Haka suka kwanta a kujera sukasa kansu a gefen gadon da ummansu take kwance. washe gari kaman a mafarki Saheeb ya tashi, sai a lokacin yake tunawa da ummansa harma da kanninsa, tagumi yayi kawai sai hawaye wanda nima bansan kona meye ba. lol 😜
Nashiga uku kallon Suhayr yakeyi wacce batasan me duniya take ciki ba duka ya dada mata ji kake tas!! "tashi tabbas Suhayr zaki iya halakar dani bansan cewa kin kware a yaudara ba, bansan cewa bakida imani ba" Saheeb ke maganar cike da takaici. "Saheeb wat is the matter?
You wake me up and you're insulting me? For goodness sake wat have I dont?". Suhayr ta fada itama da bacin rai. Saheeb yace "Ai daman bazaki saniba tunda kinyi succeeding nabar mahaifiyata da kannaina da yunwa bayan nagaya miki cewa ummata tana asibiti kizuba abinci inkai musu".
"Yanzu mekakeso kace Saheeb? Nabar mahaifiyarka da yunwa? Toh you are wrong saboda hakkina dake kanka ka sauke, so i don't care". Ta fada tana mai niyyar komawa ta kwanta.
Cikin bacin rai yace "Suhayr kafin in irga uku ki tashi kishiga kitchen kidafama umma abinci ki hadamun inkai musu inba haka ba Zan nuna miki true color na". Ya qarshe da tsawa. Haka Suhayr ta tashi Minti arba'in yayi yawa ta kammala. Ya dauki hanya sai asibiti, Yanata tunanin wace karya zaiyi ya gamsar da kanninsa?
Yana shiga cikin asibiti wata ya hango ba wata bace Abeeda ce take ba ummansa abinchi a baki. Lokaci guda yaji sonta yashiga cikin zuciyarsa, "Inama Suhayr ce takewa umman sa haka da yaji dadii" Abinda yake fada kenan a cikin zuciyarshi.
Karasawa yayi yace "umma Ina kwana" koh kallonsa batayi ba Kanninsa ma kowa ya bata rai. "pls my sisters kuyi hakuri wallahi........" Bai karasaba nimrah tace "nasan yaya tunkafin kazo nan kashirya irin karyar dazaka sharara mana dan haka bamu da bukatar jin wani Abu daga bakinka"
Umma dake kwance tace "kinyimun daidai Nimrah kai dai kam kaji kunya wllh". Tsayawa yayi jikinsa duk yayi sanyi kunya duk tabi ta isheshi. "umma kiyi hakuri tunda yasan yayi kuskure" Abeeda ke magana cikeda ladabi.
"Umma albarkarku itace kadai ke tasiri a rayuwar mu kisa mishi albarka sannan ki dinga mishi Adu'a Allah ya tsare shi daga kaidin mace",
Takarasa tareda kallon Saheeb wanda yayi nisa a fagen son Abeeda Hhhhh tab-din lalle fah to nifa zan feceee dan Nikam tsoron Suhayr nake yi ehe dan kar tami irin------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 12:01 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 12:03 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (10) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Tir kashi Abeeda dai kawar Suhayr ce amma batasan cewa saheeb mijin Suhayr bane kubiyoni donjin yanda zata kaya kwanan su biyu a asibiti Amma ba suhayr ba labarin ta,
A gaskiya fah abun yana damun Saheeb amma bashi da yadda zaiyi, washe garin ranan da zaa sallame su Saheeb yace "suhayr bakije kin gaida umma ba gashi har za'a sallamesu"
Koh kallonsa batayiba tace "pls Saheeb kadameni wai shin ina ruwana da Rashin lafiyarta? Koh inada matsala da hakanne? Pls Saheeb ka kyaleni, ask you can see am ready to school So inkaje ka gaidata ga abinchi a dinning bissimilah".
Koh kallonta baiyiba yace "kitashi kidauko cooler kisamun nawa abincin zankai musu asibiti". "aah-ah Saheeb wai meye amfanin su nimrah da bazasu gda su daho abinci ba Tika-tika dasu?". Inji Suhayr
"Ba matsalanki bane inkinji toh kitashi inkuma bakijiba Zan fita can waje insiya musu". Suhayr tace "Tafi nono fari Kasan da hakan ka tsaya jaka ta dafa ka kai musu?".
Tashi yayi don yanajin inya cigaba dajin munanan kalaman ta zasu tarwatsa zuciyarsa. Akan hanyansa na zuwa ne yayi musu odar abinchi sunci sun sha daga bisani ne kuma aka sallamesu, adaidaita suka hau har gida.
Abeeda tayi missing dinsu amma batada yadda zatayi Sunyi exchange na number, domin sudinga gaisawa, itama Abeeda takamu da son Saheeb. A hanya suhayr ta hadu da Abeeda tana tafiya tana yanga Packing tayi tace "yanmata ran gari Takawarki lafya".
Dariya Abeeda tayi tace " wata sabon gani suhayr". Suhayr tace "Shigo mana kinsan mun tsaya akan titine". Abéeda ta shiga sannan tace "suhayr yaushe kikayi aure?" Suhayr tace "Hmm last year badai ke kintsaya ruwan Ido ba?
kinganni harda dana Noor" "wow Nice name" inji Abeeda. Suhayr tace "Northwest University nake zuwa kefah" Abeeda tace "Aini poly nakeyi, Ina HND ne".
"To Allah ya taimake mu "Yasu hjy lapiyarsu kalau Abeeda na dade ina son ganinki Ina so ki rakani wajen wannan malamin hajyan Akwai Matsala". Abeeda tace "Suhayr matsalar me daga yin auren ki koh 2yrs bakiyiba?".
Suhayr tace "Abeeda kinsan koh kishin da nake akan saheeb? Kinsan irin taaddancin dana dinga yi? Akan yana so ya kara aure? Kafin aurena sai da na rabashi da yan mata sun kai biyar, bayan auren mu kuwa bakwai na lalata, Ke har wajen daurin aure"
"Wat!" zare Ido Abeeda tayi tace "tab Suhayr ke shu'umace". Ta tabe baki tare da cewa "ai nafi haka ke Niko uwarsa bata zuwa gidana bare kuma kannin sa koh yan uwansa" Abeeda tace "tirkashi Ashe dakwai bikin zuwa babu zane"
A zuciyarta tafadi "tabbas Saheeb yayan Amrah shine mijin Suhayr" "Oh my God Suhayr kin kade sai kinyi da kinsanin fada mun sirrinki, saina shigo rayuwar Saheeb Na hanaki sakat" A baki tace "Okay zan rakaki amma yaushe kika shirya?".
Ta danyi jim tana nazari sai kuma tace "ummmm Abeeda mu barshi weekend kinga am free ba school". Abeeda tace "Haka zaayi". Ahaka sukayita hiran har takai Abeeda bakin poly sannan ta wuce nata makarantar.
Cikeda farin ciki Suhayr tace "Saheeb bakaiba kara aure, Sai anyi mun maganinka Saheeb bawai muzgunama nake so nayi ba sonka nakeyi Banaso wata ta rabeka ne Sabi da kishi
Abeeda na isa gida tace da hajiya "Hjy kinsan meya faru yau Suhayr nagani Har tayi aure kinsan harta haihu?". "Iyeeh tabdi jam" inji hjy saude. Abeeda tace "Hjy ina wanda nake baki labarin Rashin kirkinta ?" Hjy saude tace "eh" "Toh Ashe Suhayr ce Hajya duk yadda za'ayi inshiga gidan saina shiga koh ta halin kaka".
Hjy saude tace "Yauwa yata haka nakesonki da jarumta, Karki sake ki karaya". Abeeda tayi dariya tare da cewa "Bakiji ba wai zan rakata gurin Malam ai kibari hjy tsuntsu Biyu zan jeho da dutse daya Itace sakarya hjy"
"Yauwa yata" hjy ta rungumo Abeeda tace", "Yar hjy, uwar hjy, yar lelen hjy, yar gaban goshin hjy, Kishiga ya auro hudu kuma ki zauna dasu, indai kisssace yanzu kai ya waye ba boka ba Malam iya ruwa fidda kai wanda ya iya allonsa ya wanke".
"Hjy yanzu zan kira Malam inyimai bayanin komai, yafara aiki tunda nasan a irin kallon da yakemun, hjy dakwai so a ciki" Malam suka kira tayimai bayani yace angama cikin kankanin lokaci zaki zama halak malak dinsa ammafa Saikinci damaran zama a gidan Saboda matar shu'umace duk yadda kike tunani tafiki
Sannan ta mamayeshi kwarai Saboda yana masifan sonta Sannan gdan da suke ciki mallakin mahaifinta ne ke harta kasuwancin dayake kudinta ne". "Malam ai wannan duk ba wata matsala bace Masifa kuma ai saimuyita gwabzawa Mekarfi ya kwaci kansa".
Malam yace "Angama" Washe gari tun safe Suhayr ta kammala aikinta, Saheeb yana zaune Tunanin Abeeda kawai yakeyi, duk Suhayr tana kallonsa da yanayinsa. Mai aikinta ta goge ko'ina Sun kammala. kusa dashi tazo ta haye kan kafarsa tace "Nurul-Q'alby Lafiyarka kuwa gaba daya ka canza? Kodai akwai matsalane a kasuwa?"
Rungumeshi tayi har sunajin numfashin juna. "Talk to me Saheeb Your silence it wat I hate". Dagota yayi yace "my blood ba abunda ke damuna Saidai har yau nakasa cikama zuciyana burinta" "Zare Ido tayi tace "buri kuma?
Wani burine wanda ya wuce mu karasa rayuwar mu nidakai da yayana har abada?" murmushi yayi Amma na ciki na ciki yace "Hakane Suhayr Allah yabarmu tare" "Amin" tace "inaso zanje unguwa Amma bawani dadewa zanyiba Sannan a gida zan bar Noor".
Saheeb yace "Amma Suhayr dakin tafi dashi inajin da hankalina yafi kwanciya" "Toh" tace tana dariya tace "your wish is my command". A hanya suka hadu da Abeeda, suka kama hanya sai wani kauye can gaban dawanau Gaban "kwa" in an wuce "Dungurawa" Wato "Doruwar shehu"
Cikin unguwan suka shiga sai gasu a kofar gidan Malam din, Sunyi mishi bayani yace dubu talatinne ba yawa da sauri Suhayr tafito da kudi zunzurutun kudin ta bayar. Fans kun san me to fah ai Nine akaba kudin Na yita mata tsayuwar dare hhhh lollzzzzz 😜
Abeeda tace "Malam kar ayi sanya" yace "karki damu" Kallon suhayr takeyi tace "sai kinyi dakin sani don saina maye gurbin duk abinda kika kasa Hakan zaisa nasamu matsayi a birnin zuciyan Saheeb" to amma kuma fah duk Acikin zuciyarta take zancen.
Sun kama hanya kowa da abunda yake sakawa Bayan sati hudu wata guda kenan, Saheeb yarasa sukuni har saida ya binciko gidansu Abeeda, daga zuwansa yace aure yake so nanda wata guda Sannan baya so kowa yasani sabo da karya koma kunnen matar sa.
Soyayya mai ma'ana ce tashiga tsakanin su Baya iya barci sai yaji muryanta, kullun saisun gaisa da yan uwansa, harma da umma lokaci guda ta asirce zuciyansu da alkhairai. Shiko kanin Saheeb ba wadda yaki jini irin Abeeda, don yace batai masa ba gwara Suhayr sau miliyan, So gamon jini"
Kwatsam mustapha yaji ana zancen yayansa zaiyi aure kuma a boye musty yace "shikam bazai yarda a munafunce Suhayr ba," Gidansu Abeeda anata shiri biki saura satii biyu.
Shiri akeyi gadan gadan, akalla saida Saheeb yayiwa Abeeda akwati biyar harda kit, Sadakinsa naira dubu hamsin Yabada komai na kawayen amarya. Sannan Nima aka bani Nawa dan naji dadin ci gaba da labarin ehe------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
[7/23, 12:03 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[7/23, 12:16 PM] 🅰 " 🅰 " D, 🅱⭕Y: _______JARABABEN*KISHI______
_______________________________
------ Littafi --- Na daya ------
----- 🔛-----
**★** PART (11) **★**
Post
By :----Man Bash ----
.
.
Saheeb ne tsaye yace "Abeeda daga yau bazaki sake ganina ba, sai ranan daurin aure". bata rai tayi "saboda me my Blood?" Yace "Sa boda banaso Suhayr ta gane komai saboda tafara mun complain cewa Bata gane yanayina ba kinga karta dagoni"
Rikicin duniya damai rai akeyinsa "hakane Amma dai zakazo dinner koh?" Cewar Abeeda. Yace "Eh zanzo karki damu" "Toh" tace ta juya tana jujjuya sassan jikinta komai na kadawa, Saheeb ya bita da ido har ta bace ma ganinsa. Shiko musty nazarin yadda zaayi a Raguza aurennen yake, Gashi kuma yakasa zuwa ya sanar da suhayr,
Kwatsam saijin labarin dinner da aka shirya yayi sai yace "toh koh saina sanar da suhayr Kartace na munafunceta" Ayau ne daurin aure tun safe Saheeb ke shiri ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Suhayr duk tana kallonsa daga bisani tace "oh my God dan Allah Saheeb safa da marwan me kakeyi? Sai kace wani Marar gaskiya?" da sauri ya juyo yace "suhayr kaman ya wane irin zancene wannan"
Cewa tayi gulty conscious" I dole in tambaya sai wani rawan jiki kake kaman me shirin yin sabuwar amarya?".
Dam gabansa ya fadi "Yauwa inaso ka kaini gdansu Abeeda kawata inyi mata godiya". "Godiyan me ?" Ya fada a dan tsorace, sai kuma ya maze ya ce "Look suhayr yawonki yafara over fah kiyi hakuri next week kyaje" sai tace "Allah yakaimu",
Yana fita daga shi sai boxer, daki ta nufa wata tsaleliyar shadda tagani bugagga Ga wata hula mai shegen tsada. mamaki ne duk ya cikata ina Saheeb zashi? Tab yau akeyinta Rakumi da kayan tanka hhh 😂
"Saiko na hanashi zuwa koh ina falo ta dawo ta kalmashe kafa, Yazo ya wuce yasa shaddar sa fara kal, kitchen ta nufa da sauri ta debo miyar datayi na manja, fitowa yayi yana duba irin kyan da yayi Baiyi auneba ta taho da sauri daidai da saheeb ya dago Gaba daya miyar ta kwaremai Gashi miyar da zafi".
"Subhanallah!" ta fadi tareda da cewa "swthrt am sorry it's a mistake " Kallonta yakeyi kaman yasa hannu aka yayi ta ihu!!!! "Suhayr kin kyauta kwarai" a zuciyarsa yace "Amma daga gobe zaki gane kurenki". daki ya wuce baice da ita uffan ba. wata shadda yasa tsohuwa sawa daya Yasa hula ya fita, Abokinsa Marwan ne ya zo ya daukeshi a mota.
Saheeb yace "My guy kaga abunda suhayr tayi mun? Miya ta watsamun a kaya" marwan yace "Mutumina gaskiya saika zama namiji inba hakaba Suhayr saita zamema annoba Saukinta ma Abeeda itama A ce". Andaura Aure kowa ya shaida,
Abeeda kwa sai murna take umman saheeb sai godiya take ga Allah, yan uwa kowa sai barka yake mata. Musty ne Yakama hanyan zuwa wajen Suhayr don ya sanar da ita, sabo da sauri takalmi daban daban yasa Rigarsa a baibai. Niko me zanyi banda dariya lol 😂
H'm take ya fada koh sallama babu "lafiya musty na ganka hajaran majaran???". Musty yace "Ina lafya maye ya cinye amarya". zare Ido Suhayr tayi tace "a ina? Hhh 😂
Musty yace "Aunty bafa nufina meye ya cinye Amarya bane Yaya Saheeb yayi aure". "What???" batasan lokacin data mike tsaye ba, tace "musty kana nufin Saheeb dina yayi aure?" Musty yace "Kwarai aunty har an daura ma nima dazu nakeji". Suhayr tace "Tabbas Saheeb yayi kuskuren boyemun komai, amma kuma ban makara ba Naji ma zaayi reception".
Ah to aina? musty ya gaya mata shiri ta tashi yayi tana zubda hawaye, a gida tabar Noor wajen mai mata aiki. "Musty zo muje" motarta ta dauka ta dauki madoki abunyin golf tasaka a bayan boot. Nace hmm
Gudu takeyi har suka isa wajen da ake partyn da yake tinted glass ne babu wanda ya gane ta, tace "musty kazauna a cikin motan karka damu bari na shiga don banaso afara komai". Ta fita ta shiga ciki Saheeb ta hango yanata washe baki, Wato yayi amarya, chan ta hango kawarta Abeeda bakaramin razana Suhayr tayi ba, " what! ai Abeeda itace ta auri Saheeb din?"
Take tambayan kanta amma idanunta kodai gizo suke mata. "No in mafarki nake yi ya kamata in tashi, No dis won't be possible". ji tayi ankira Saheeb da, amaryar sa Abeeda Hhhh lol 😜 ai sakato tayi Basu ankaraba duka suka faraji tako ina da sandar golf,
Sannan kuma gata da bindiga kowa ya kasa tunkarar ta, tuni Saheeb ya fadi sumanme, itako Abeeda tuni kamanninta suka canza, baki ya kumbura amma Suhayr duka takeyi baji ba gani.
Hhh saida tayi nasaran sumar da Abeeda Hjy saude lbr ya risketa tuni ta tsure. Loudspeaker ta dauka Tace "ina ma kowa murnan zuwa gaggarumin bakin biki wannan da kuke gani maciya amana ne, Abeeda kawata ce wadda na yarda da ita amma shine taci amanata,
Shikuma wannan da kuke gani ba kowa bane illah mijina kuma uban yayana, nasan dayawa mutane zasu kirani da mahaukaciya tabbas basuyi karya ba, Indai akan miji nane. wutan kishi na damuna kwarai Bansan wace jaraba bace kecin sa yayi mun kishiya kuma kawata?,
Kadan kuka gani". ta fadi tana kallonsu koh motsi basayi. Tiryan-tiryan ta sakko tana taku daya bayan daya tace "kafin in irga uku kowa ya bace" ta nuna bindiga,
Habawa kan kace me kaman anyi ruwa an dauke. ta tsallake su tayi waje, ta shiga mota suka koma gda. Suhayr tayi kuka kaman ranta zai fita amma duk abunda tayi tace bata huce ba.
Ambulan ce aka kawo aka kai Saheeb da Abeeda asibiti Hankalin kowa sai da ya tashi ciki harda umman saheeb. Abbansa yace "duk abunda ya faru Halima kece sila kuma ina gaya miki kisa kafar zuwa kashe gobarar da kika hada da hannun ki kuma a gidan danki
Don ni ba abunda ya dameni wallahi " Shuru umman saheeb tayi, batace dashi uffan ba, Fuuuuu tafita Suhayr ce tace "musty muje gidan naku".
Hanya suka kama sai dorayi suna tafe kowa ba baka sai kunne A kan kwana ta ajiye shi Sabi da kar ace tare suke, koh Sallama babu Suhayr ta fada dakin umman Saheeb. "Ban taba Sanin cewa ke gurmi bace mai hada guri,
To amma umma innace miki uwar banza nasan wallahi banyi laifi ba, Umma tabbas kin saiwa kanki fetir din da sai ya kona ki, kin ziga Saheeb yayi aure don farin cikinki Bakisan akasin haka zaki samu ba, Zama da kishiya bazan iyaba sai dai yau in zaki tashi daga dakin nan kibasu su zauna,
Sannan kuma ki ciyar dasu Amma bada kudin ubana ba." Shuru umma tayi ta rasa bakin magana. Suhayr tace "Dole kiyi shuru sabo da kin san baki shuka alkhairi ba Munafukar tsohuwa". "tub" tayi ta watsawa umma miyau tace "kadan kika gani saikinzo zaman makoki
Sannan ne to zaki gara ganewa idonki, zaki san yadda zafin kishi yake." kai tasa zata fita kawai taci karo da Abeeda tsaye tace h'm sai tace "zafin kishi koh hauka?
Tambayanki nake?" Suhayr dago jajayen idonta tayi ta hankada Abeeda sai da ta fadi. Suhayr ta taka wuyanta tace "ke in baki san cewa ni yar taaddan mijina bace yau zaki sani,
Kinyi gangancin shigowa hurumin daba nakiba, Saheeb is mine Abeeda mine alone" Kakari Abeeda keyi kaman zata mutu. Nimrah ce tace "tabbas baki san darajar taki uwarba, dabaki zo har cikin gidan mu kinciwa uwarmu mutunci ba"
A fisace Suhayr ta juyo tace "Nimrah dake nake wayasa bakinki a ciki, oh baki sanni ba amma yau zaki sani dan ni din nan bana daukan raini a wajen kowa bare ke"
Wanka ma nimrah mari tayi tace " Say a word again and I will show you the other meeee" tub tayi ta watsawa nimrah miyau kai kai kai tab-din lalle kam abin nayi ne to nima ganin haka ne ya sani fecewa lol 😜------------------------------
------------------------------
----------- ---------------
----
0 comments:
Post a Comment