Safiyar ranar Asabar garin kano ya kasance cikin shiru dan mutane ma jefi jefi kake ganinsu a waje kasancewar Asabar d'in k'arshen wata ne,ranar _Sanitation_ kenan....
A wannan rana da yawa daga cikin mutane basa fitowa daga gidajensu sai k'arfe sha d'aya,lokacin an saki titi kenan kowa sai ya fita yayi uzurinsa masu ababen hawa kenan,wanda basu dashi ma sukan zauna suyi hira da iyalinsu kasancewar ranar garin yakanyi tsit babu hayaniya sosai saboda yawancin mutane suna gida tare da iyalinsa...
Sumayya tana d'aya daga cikin mutanen dake cikin nishad'i a wannan ranar,yanayin garin yazo da wata iska mai dad'i da take kad'awa..
A tsakar gida suka baje tabarma suna shan iska, Sumayya ta kalli yayarta Nasiba tace "yaya kinsan me?" kai Nasiba ta gyad'a alamar a'a,Fatima tayi saurin matsowa tace "Aunty bamu musha"
harara Sumayya ta yi mata sannan tace "babu ruwanki uwar gulma" ta juya ta kalli Nasiba tace "irin wannan yanayi yana saka saurayi da budurwa cikin nishad'i yayinda suke zance a irin wannan yanayi zasuji sun k'ara son junansu,haka zalika uwa zataji dad'in kasancewa da 'ya'yanta,kai hatta gidan marayu a wannan yanayin sukan samu kansu cikin nishad'i,haka mata da miji ma"tana kaiwa nan ta mik'e tsaye...
"mu kuma a wannan yanayin sai muka k'are a b'arar gyad'a ko karin kumallo bamuyi ba,bara ina zuwa"
"ina zakije" Farida da tun da aka fara maganar bata ce komai ba sai yanzu tayi tambayar...
"ku zuba ido ku gani" Sumayya ta fad'a lokacin da ta zira silifas d'inta..
"Karki je ko ina" Nasiba ta daka mata tsawa..
kallonta sumayya tayi a shek'e sannan tace "wlh sai naje kiyi hkri kawai" ta wuce k'ofar d'akin Aunty Hadiza( _step mum_ d'insu).
bugun k'ofar take da k'arfi,su Nasiba suna hango ta daga inda suke zaune...
bud'e k'ofar Aunty Hadiza tayi tare da lek'o kai,idanunta a lumshe da alamun bugun k'ofarne ya tashe ta daga bacci,
"lafiya kike buga mana k'ofa haka?"
K'ugu Sumayya ta kama irin mai shirin yin dambe ta b'ata rai tace "ina son magana da baba"
"to mai baba sai ki bari ya tashi daga bacci ko"
ta tab'e baki tare da kallon sama "yanzu nake son magana dashi"
"to bazaki ganshi yanzu ba"
"idan kuma na kusa kaina na shiga d'akin fa?"
cikin b'acin rai Aunty hadiza tace "saiki shiga in gani idan d'akin uwarkine"
da sauri sumayya ta kalleta tace "kema aiba na ubanki yakubu bane tunda babu sisinsa ciki hatta kayan d'........bata k'arasa magana ba taji Aunty hadiza ta wanke ta da mari,hannu ta d'aga zata rama,caraffff baba ya rik'e tare da angaza ta gefe..
"amma fa kana gani mari na tayi"
"ta mareki d'in marar kunya kawai,kin bi kin addabi mutane,ko masifa anan ta ganki ta k'yale sumayya"
Cikin zafin rai ta matso tace "amma baba kasan a irin wannan yanayi 'ya'ya suna so su kasance tare da iyayensu domin su fad'a masu damuwarsu su kuma su share masu hawaye,amma mu antule mana damin gyad'a mu tsinke mu b'are mu markad'a sannan mu dama kunun da zamuyi karin kumallo?ku kuma kai da wannan kusha shayi?"
ta d'anyi shiru sannan ta cigaba da fad'in "watan matar nan d'aya a gidannan ka kori ummarmu ta tafi gidansu yau wata biyu kenan shiru babu ita,gaskiya ana d'aukar hak'k'inmu dan ko abinci ba isarmu yake a gidannan ba"
kallonta yake ransa a b'ace sai da ta gama sannan yace "ki jira in fito daga d'aki baki bar nan ba in nuna miki k'arshen rashin kunya"
yana shiga d'akin ita kuma ta damk'o Aunty Hadiza suka fara kokowa "wlh sai kin barmu mun ji dad'i a gidan ubanmu..
Nasiba ta taso da gudu tana kacaniyar rabasu sai jin saukar dorina sukai a jikinsu tuni sumayya tabar fad'an ta na neman guduwa,ya tare ta kuwa ya fara jibga,da k'yar ta samu ta fita waje a guje...
"Zo nan! zo nan! idan kika fita wlh ranki sai ya b'aci"
Sum sum ta dawo ta sungunna gabansa,farida da su fatima sun kafa ido suna kallo kawai...
"ke kika goyawa Sumayya baya ta mana rashin kunya?"
a tsorace ta girgiza kai..
"kiyi magana munafuka gayyar 'ya'ya mata duk kun cika min gida kun isheni yanxu idan na mutu babu wanda zai gaje ni ina amfanin tara 'ya'ya mata??babu wata rana da zan moreku a rayuwa, shine na kawo wadda zata haifamin kuke so ku b'arar da cikin?"
"a'a baba kayi hkri"
"ki fad'awa sumayya kar ta dawo min gida"
duka suka taso suna bashi hak'uri amma baibi ta kansu ba ya shige d'aki shida matarsa suka rufo k'ofar...
suka gaji da tsayuwa a gurin suka koma kan tabarmarsu....
Tana tafiya tana goge hawayen takaici ta rasa wce irin rayuwa ce wannan...
zata koma inda za'a share mata hawayenta..
Hango shi tayi zaune ya tara duwatsu a gabansa ga tarkacen tsunmukaransa yana ta jefe jefe da duwatsun..
Ta k'arasa gurin ta samu dutse dake kusa dashi ta zauna
"Gentle,(shine sunan da take kiransa dashi kasancewarshi nutsatstsen mahaukaci)"ta kira sunanshi rai a b'ace...
Cigaba yayi da jefe jefensa da alama ma bai san tanayi ba..
kuka ta fara yi cikin bak'in ciki,a hankali ya juyo ya kalleta..
"an b'ata min rai a gida naxo ka sharemin hawaye kaima ka nuna halin ko in kula a gareni"
Ta gyara zama cikin kuka ta cigaba da fad'in "gentle duk da nasan baka magana baka komai amma idan ina magana dakai kakan sani a gaba kana kallona da alama kana jin abinda nake fad'a duk da bai zama dole ace ka fahimta ba,gentle me nayi maka yau?a irin wannan yanayin kowa yana cikin nishad'i hakane?"kallonsa ta tsaya tanayi yayinda shima idonsa na kanta...
hmmmm "gentle kasan me?"ta fad'a ba tare da ta kallesa ba...
"gentle babanmu baya k'aunarmu kasancewarmu 'ya'ya mata amma meyasa baya duba wa cewa muma 'ya'ya mata muna da rana,idan ma ba haka ba ai sai ya duba cewa ba mu mukayo kanmu ba Allah ne ya halicce mu kuma ya bashi mu amana,kullun sai yayi wq ummanmu gorin rashin haihuwar d'a namiji shine ya auro wata mata 'ya'yanta biyu duk maza,wai dan shima ya samu 'ya'ya maza,wlh an kusa nemata a rasa ina dalili za'a baba da kansa y...................jifanta taji yayi a gefen kunne....
Kallonsa tayi tare da rik'e gurin cikin jin azabar ciwo....
Shiru tayi dan tasan idan tana magana gentle ya jefeta to yana so tayi shiru ne saboda mgnar bata da fa'ida ko kuma bata dace ba,amma yau kam taji zafin abin...
"bazai yuwu ba ka rik'a jifana haka kurum ka kurmanta ni baka da kaico"
Ta mik'e tsaye ranta a b'ace ta wuce sa tare da jan dogon tsoki.
ji tayi ya sake jifanta a gadon bayanta tayi saurin juyowa tare da d'aukar dutse ta[Truncated by whatsapp].
_Nafsal 07038363997_
*4 more details*
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
*_E-D-I-T-I-N-G_*✍
_WRITTEN BY_
*_SaNaz deeyah_*
*_&_*
_*Nafisa S Adamu*_
5⃣▶6⃣
_Dedicated to 💖_*beebah luv*_💖
Harara ta dalla masa "bara na tafi karma kamin rauni dan naga yanxu ka tashi daga gentle ka koma gang"
Mtswww! Tayi gajeran tsoki tare da barin gurin....
Ranar dai a titi ta yini tana bulayi,ta tsokani wannan ta zagi wancan Ba babba Ba yaro bata d'agawa kowa k'afa ba.
Sai daf da magrib ta koma gida sbda yunwar da ke cinta...
A tsakar gida ta tarar da baba zaune kan tabarma,hadiza na kusa dashi.
Da farko kamar karta shiga amma da taga babu sarki sai Allah,sai ta daure ta Shiga...
"Zo nan" baba ya kirata cikin fad'a...
Har k'asa ta sunkuya a gabansa....
"Meyasa baki da mutunci?baki da d'a'a?"
"Baba kayi hkri"
"Inyi hkri kika ce?"
"Eh"
Janyota yayi ya jibga ya jibga har sai da ya gaji sannan ya k'yaleta,ko k'walla babu bare hawaye a fuskarta...
"Goggo Zatazo gobe saboda na gaji da halinki,Sati guda na baki ki fitar da miji Idan Ba haka Ba zan aurar dake ga duk Wanda naso"
"Kuma baba baka aurar da yaya Nasiba Ba sai ni" ta fad'a tana zumb'urar baki.
"Wlh ko kina tsafi da jar jab'a sai kin bar min gida kije can gidan miji kiyi rashin kunyar miji ya jibgeki"
Dariya tayi sannan ta zauna kusa dashi cikin barkwanci tace "baba gobe idan inna zata zo tare da umma zatazo?wlh so nake umma ta dawo"
"Gafara can banza shashasha kawai"
Sum sum ta tashi ta shige d'aki...
Su fatima,Farida,ihsan suna kwance, Nasiba na zaune tayi tagumi....
Jikinta Sumayya ta fad'a tana kuka "na shiga uku yaya Nasiba wlh guduwa zanyi"
"Ki gudu kije ina Sumayya?ai na fad'a miki ki daina rashin kunya bakya ji sam"
Ta goge guntun hawayenta tace "ai Ba mu muka halicci kanmu Ba da baba zai tsanemu kawai dan Allah ya yimu a 'ya'ya mata,wani ma haihuwar yake nema Allah bai bashi ba,dan haka wlh sai nasan abinyi" ta tashi ta koma gefen su farida ta kwanta...
Ita dai Nasiba Binta tayi da kallo...
*_10:57:43 pm_*
"Wallahi yau koni ko ita" abinda kunnen sumayya ya juyo mata hadiza na fad'a...
Ta k'ara runtse idonta ita a dole bacci take.
Bankad'o k'ofar d'akin nasu akayi...
Baba da ita hadizar suka shigo.
"Ina Sumayya?"baba ya fad'a rai a b'ace
Nasiba tace "Sunyi Bacci"
"Ai wlh dole ta tashi a Nuna mata kuskurenta ni zata watsawa uwata ruwan kwata?cab lallai wuyanki yayi kauri" hadiza ta fad'a tare da k'arasawa gurinta ta d'uma mata duka, a sukwane ta mik'e dan dukan ya shigeta....
Tana mik'ewa tsaye ta kama hadiza suka kaure da fad'a...
Da k'yar baba ya samu sumayyar ya hankad'ata tsakar gida...
"Allah wadaran naka ya lalace"
"Ki fita kibar gidannan yanzunnan kafin na illata ki"
"Baba dan Allah kayi hak'uri yanzu fa sha d'aya ta wuce"
Farida ta fad'a cikin sanyin muryarta...
Duk Wanda ya k'ara magana saina tsine masa...
Ita kuma taurin kai ya hanata bashi hak'uri...
Takalminta ta Saka ta fita,'yan uwanta suna ta kuka...
Tayi nisa da tafiya dan har ta wuce unguwarsu,ta gaji sosai ga bacci ga gajiya,garin yayi tsit bakajin komai sai kukan karnuka...
Ta jingina jikin wani kango dan ta huta ga tsoro ya mamayeta,kamar a mafarki taga ana hasketa cike da tsoro ta bud'e ido taga mutane kusan biyar tsaye a kanta...
Da gudu ta tashi ta yanki tsakiyarsu ta wuce..
Suka rufa mata baya tana gudu suna Binta...
Kuka sosai take tana fad'ar "Allah ka ceceni daga hannun azzalumai".
Gajiya ta fara zuwar mata gashi basu daina Binta Ba,ta fad'i ta tashi haka ta cigaba da gudu...
Tana shan wata kwana taji an rik'o hannunta tare da shigewa cikin wani k'aton rami,ta bud'e baki zata zunduma ihu t[Truncated by Whatsapp].
_Sadeey_😘 _07035111671_
_&_
_Nafsal_💄 _07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
3⃣ñ4⃣
'Daga dutsen tayi zata jefeshi kawai ta fasa ta ajje....
Kallonsa take cike da jin haushinsa lallai ya manna mata hauka ma da har zai jefeta, dole ta nuna masa cewa zuwa gurinsa da takeyi taimakonsa takeyi da kuma tausayinsa bazai yuwa ya mayar da ita sauna ba ko kuma mahaukaciya kamarsa..
Cigaba yake da wasansa hankali kwance ya ma manta da wace iskar ta kawota..
Cikin zafin rai ta k'arasa gurinsa tare da yin ball da kayan dake gabansa,still bai kalleta ba...
"Kai dalla Malam bakaji ne"tayi masa maganar cikin tsawa...
"Lallai ka rainawa kanka hankali,ka kalleni, gentle wlh idan na daina zuwa gurinka sai kayi kewata duk da ba hankali ka cika ba"tana fad'ar haka kuwa yayi saurin d'agowa ya kalleta...
Ta had'e ranta sosai tayi masa tsoki ta wuce…
Ranta a b'ace ta koma gida cikin takaici da Dana sanin fitar da tayi,an b'ata mata rai a gida ta fito dan taji dad'i gentle ya raina mata wayo ...
A zaure taci karo da Nasiba,had'e rai ta k'arayi dan ma karta kowa mata maganar baba,abinda tak'i kuwa shine ya faru...
"Baba yace karki shigo masa gida"
"Karna shigo masa gida?" Sumayya ta maimaita Kalmar....
"Haka yace na sanar dake"
"Cabbb to yaya Nasiba ina zanje idanba nan ba?"
"Shawara d'aya ne, ki bari ya fita sannan ki shigo,idan ya dawo sai muje mu bashi hak'uri"
Kamar ta fad'i abin tsoro haka sumayya ta zare ido ta kalleta tare da fad'in "akan waccan 'Yar iskar?wlh sai na shiga sai dai ya yanka ni"
"Rashin kunyar nan babu inda zata kaiki sumayya"
"Rashin kunya ita ke ceto na daga gurin waccan azzalumar" ta fad'a tare da shigewa ciki...
A tsagar gida ta had'u da baba yana alwallah da alama sallar walha zaiyi,kanta a k'asa zata shige d'aki.
"Kulll....kada ki sake ki shiga ki koma inda kika fito"ya fad'a ransa a b'ace..
Nasiba ta kalla sannan ta kalli baba "baba sags Ina na fito idan ba nan ba?"
"Karki min rashin kunya sumayya"
Rai ta had'e ta kuma tsaya cak a gurin har ya idar da alwallahr..
"Ba cewa nayi ki fita ba?"
d'an kwali ta cugi ta fara magana cikin fad'a-fad'a "wlh babu inda zani, nan gidan ubana ne zama daram,sai ka bari idan k'auye naje gidan baffa gidanku kenan to sai ka hanani shiga"
"Ni kike fad'awa haka?"
Shiru tayi tana kallonsa...
"Sumayya baba ne fa,mahaifinmu"Nasiba ta fad'a cike da mamakin sumyn..
"Ahhh!nasan da baba nake magana amma ai gaskiya na fad'a,zama daram a gidan nan,saboda nan gidan ubana ne".
"Jirani in fito" ya fad'a tare da shigewa d'aki..
Cikin d'aga murya take fad'in "wlh baxanje ko ina ba,ka kashe baba amma Kafin nan wlh indai Ina raye SAI NAGA K'ARSHEN........bata k'arasa maganar ba taga ya fito da sharb'eb'iyar wuk'a..
Da gudu ta fita ya bita.
******
Tana tafiya tana surutai kamar wadda ta zare ..
"Baba kayi hak'uri dani duk abin nan da nake inayi dan na nemo mana 'yancin mu,ka yafe min baba"
Cigaba tayi da tafiyar har takai gidan da take son zuwa..
'Dan kwali ta cire ta gyara d'orinta tayi masa turo kaga tsiya sannan ta Shiga cikin gidan ...
"Salamu alaikum!a inda bai dace ba" ta fad'a tana yatsina fuska"
Bilki dake zaune a tsakar gidan tayi saurin mik'e wa "me kike nufi da zaki zo har gidan mu ki nemi zaginmu?"
Kallon sama da k'asa tayi mata sannan tace "to algunguma,ohhhh su cin dank'o harda kaza? ni kuma ince me da aka hanani zaman lfya a gidan ubana?"
Inna ce ta fito daga d'aki tana tambayar ko lfya take jin hayaniya....
"Barka da fitowa, wadda ta raba kan 'ya da mahaifi,hankalinku ya kwanta ai,wlh tunda kuka had'a munafurci Nima sai na rama"
Ta d'an yi shiru sannan ta cigaba da fad'in...
"Yadda hadiza tace sai taga k'arshena to Nima SAI NAGA K'ARSHENTA zan nuna mata true face d'ina ranar zaKu fahimci ko wacece sumayya"
Ta juya zata fita taji bilki tace "ai yanzu ya kamata ki nuna mana koke wacece"
Wani cup ta d'akko a gefe cikin zafin nama ta d'ebo ruwan kwata ta watsawa innarsu "kad'an daga aikina" ta fad'a tare da bawa rigarta iska....
A gaban gentle ta dira tare da zama,sai ajiyar zuciya take...
Shikam kallonta kawai yake...
Cikin nishi da gajiyar gudan da tayi ta kalleshi "mtswwww!,kai idan na baka lbrima jifana kake meyasa ma na dawo gurinka?"
Tashi tayi ta koma can nesa dashi ta zauna,ga mamakinta taga ya taso ya[Truncated by whatsapp]
_Sadeey & Nafsal_
_07038363997_
4 more details
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA?*🍁
🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
🍁🍁
🍁
_WRITTEN BY_
*_Nafisa S Adamu_*
_&_
*_SaNaz deeyah_*
*_Dedicated 2 beebah luv💞 & Munay💕_*
7⃣ñ8⃣
Taji an toshe mata baki,tayi shiru sai ajiyar zuciya take cike da tsoro da fargaba tare da nadama...
Kusan awa d'aya suna cikin ramin,sai da sukaji babu motsin mutane ko kad'an sannan aka janye hannun da aka toshe mata bakin...
A tsorace ta juyo ta kalli Wanda ya toshe mata bakin,ta dai San namiji ne amma bazata ce ga yadda fuskarshi take Ba,kasancewar duhun darene Wanda babu hasken farin wata...
Tashi taga yayi ya fita,ita ma a tsorace ta fito ta tsaya gabansa....
Kuka ta farayi cike da tsoro..
"Dan Allah ka taimake ni idan ka barni anan dawowa zasuyi su cuceni"
Baice komai Ba illa juyawa da yayi ya cigaba da tafiya,tayi saurin shan gabansa, "bawon Allah kaji tausayi na wlh ji nake kamar hanjin cikina zasu fito saboda tsoro"
Ga mamakinta taga ya cigaba da tafiya babu alamun tausaya mata da yayi...
_wlh ko kasheni zakayi saina bika_ ta fad'a a ranta sannan ta cigaba da binsa...
Sunyi tafiya mai nisa ne ta fara ganewa unguwarsu yake maida ita.
Zuciyarta ta cigaba da bugawa, _kardai ace aljani ne, tayaya yasan unguwarmu_ ta fad'a a zuciyarta tare da jin fargabarta ya k'aru.
A k'ofar gidansu taga ya tsaya tare da bubbuga k'ofar gidan…
Jikin bango ta lafe ta runtse idonta tare da jin wani guntun hawaye a Idonta...
Maganar baba ce ta fargar da ita "kai waye da tsohon darennan"
Shiru baiyi magana ba illa knocking daya cigaba dayi…
A hankali Sumayya ta k'arasa jikin k'ofar tace "baba nice"
"Ke wa?"
"Sumayya ce"
" 'Yar kare me kika dawo yi gidana,ai ki koma inda kika fito"
Cikin tsoro tace "baba dan Allah kayi hkri ka bud'e min wlh bazan sake ba na yarda ka aura min duk Wanda kake so"
"Kin d'auki alkhawari ko?dan wlh kin isheni na gaji da ganinki a gidana"
"Na d'auka baba"...
Yana bud'ewa ya haskesu da touchlight Dama kawai so take taga fuskar Wanda ya kawota gidansu...
"Waye kuma wannan?"
Baba ya tambaya yana dallewa gentle ido.
A tsorace tayi baya "gentle???? Dama Kaine?"
"Taya akai kasan baba ya koroni daga gida?"
Ba magana yake ba bare ya bata amsa...
Juyawa yayi zai bar gurin tayi saurin shan gabansa "gentle ina zaka tafi a darennan,ka dawo ka kwana ko a soro ne"
"Soron ina?ai sai dai in rufe gidana Ku kwana a waje tunda kema kin zama mahaukaciya kamarshi" baba ya fad'a cikin b'acin rai
Ta kallesa ta marairaice tace "baba dan Allah ka tausaya masa,wlh akwai 'yan fashi a unguwarnan karsu cutar dashi"
"To to to marar kunya" ya fad'a tare da hankad'ata cikin gida,ya kuma kulle...
Tana shiga d'aki ta tarar da Nasiba da farida zaune kan sallaya da alama sallah suka idar...
Sauran kuma sunyi bacci...
Tana shiga taji wani bak'in ciki ya turnik'eta sai kuka...
Haushi yasa Nasiba ta kasa ce mata komai,
Tayi kukanta ta k'oshi sannan ta nemu guri ta kwanta.
_Washe Gari_
Tunda Sassafe Sumayya ta fita ta siyo gasara mai d'an yawa tare da taliyar Hausa da 'yan kayan miya na naira hamsin…
Koko mai kauri ta dama sannan ta dafa taliyar.
'Daki takai tà ajje masu nasu ta d'auki sauran a kwano da koko a jug zata fita...
"Ina kuma zaki?" Nasiba ta tambaya..
"Kedai Ido ne naki" ta fad'a Ba tare da ta kalleta Ba..
"Sarkin mararsa kunya".
Itama bata tanka mata Ba ta fice...
Bata zarce ko ina Ba sai inda gentle ke zama..
Tun daga nesa ta hango tarkacensa amma babu s[Truncated by Whatsapp].
_Sadeey_ _07035111671_
_&_ _Nafsal_ _07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *_MENE AIBUNA_* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
_Written by_
*_Nafisa S Adamu_*
&
*_SaNaz deeyah_*
_Dedicated to beebah luv💞 & Munay💘_
9⃣▶1⃣0⃣
Ba shiri ta ajje kwanukan hannunta ta k'arasa gurin...
"Gentle" ta kira sunansa da k'arfi...
Shiru babu alamun zaizo ko yana gurin...
"Na shiga uku ina zanga gentle?"
Duddubawa tayi amma babu shi babu alamunsa...
Ta gaji da dubawa ta koma gida cike da damuwar rashin gentle....
Yinin ranar kuwa da bak'in ciki ta yisa dan ko abinci ta kasa ci.
Da yamma goggo ta iso gidan...
Bayan ta huta ne tasa hadiza ta kirawo mata sumayya....
"Idan kinga dama kizo inji goggo"
"Anje anyi min sharri Ba"
"Karki min rashin kunya"
Mtswww "idan kina da kunyar Ba" ta fad'a tare fita.
"Karshen rashin kunyarki yazo dai" hadiza ta fad'a tare da bin bayanta...
Tana durk'ushe gaban goggo da,,sai fad'a take mata....
"Idan uwarki ce ai bazaki mata rashin kunyar nan Ba,wlh ki kiyayeni matar babanki ai mahaifiyarki ce"
Ranta a b'ace tace "amma goggo wannan ai zagina kike a fakaice"
"Goggon ma halin naki zaki gwada mata?"
"Ka k'yaleta dani take zancen"
Ta b'ata rai ta kalli baba "na janyo auren Sumayya nan da kwana hud'u,ka fad'a a Masallachi duk mai so ya fito,naga Wanda kika yiwa rashin kunya katifa ma wlh baza'a siya miki Ba tabarma ta isheki,kaji na fad'a maka ko?"
"Naji goggo"
"Inga k'arshen rashin kunyar a gidan mijin da aka bashi sadakarki".
Tana kwance kan cinyar Nasiba sai kuka take ita yanzu ina zata tsoma ranta?....
"Kinga k'arshen rashin kunya Sumayya?ai na fad'a miki babu inda zata miki rana"
"Na shiga uku ni sumayya ya zanyi?dawa za'a had'ani?wa zai cigaba da kula da gentle? Ya rayuwata zata kasance a gidan mijin da ban sanshi Ba?"
Lallashinta Nasiba ta cigaba dayi yayinda ita kuma tak'i daina kukan.
******************
Yana zaune a parlour gaban momma yana rok'onta....
"Momma ki taimaka min ki taimaka mata"
"Arish ya kake so nayi?kasan halin babanka fa"
Arish ya kalli momma yace "momma na fad'a miki komai game da kulawar da yarinyar nan take min?momma idan nayi sake bansan wa za'a bata ba,mahaifinsu baya sonsu,sati guda ya bata ta fidda miji"
"nasan komai Arish amma ina tsoron na tunkari dadynku da maganar"
"Momma kidai gwada sa'ar ki,nima zanje na samu abba Bashir na sanar dashi komai"
"Arish kabi a hankali dai,kayi komai cikin nutsuwarka"
"Insha Allahu momma" ya fad'a tare da barin gurin...
Momma ta bishi da kallo tare da yi masa fatan Alkhairi a rayuw[Truncated by Whatsapp].
_Nafsal and Sadeey_
_07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
_Dedicated to beebahluv💞& Munay💕_
1⃣1⃣▶1⃣2⃣
Tana zaune tayi shiru tunanin irin wannan tashin hankali da ake neman turata take..
Nasiba ce ta shigo cikin sallama ta samu guri kusa da Sumayya ta zauna...
"Zuwa jibi ya war haka kin zama matar wani"
Sumayya tayi saurin kallonta cikin tashin hankali...
Nasiba ta cigaba da fad'in "ina amfanin rashin kunya Sumayya?yanzu kalli yadda za'a d'ora miki aure da wani Wanda har yanzu baki San ko waye ba?kinga k'arshen rashin kunya ko?mu kanmu zamu d'auki darasi akanki"
Baki ta tab'e cikin tsiwa tace "nifa ko a jikina dan Za'a yi min aure,damuwa ta d'aya shine ina zanga gentle?ina ya shigane?ina son fad'a masa wannan breaking news d'in,waini za'a bada sadakata,wlh goggo muguwa ce"
"Ke! Sumayya" Nasiba tayi maganar a tsorace...
Tashi tsaye tayi cikin takaici ta fara fad'in "wlh bazai tab'a yuwuwa ba za'ai bikina a k'i sanar da mahaifiyata"
Kamar an ingiza ta tayi saurin fita tsakar gidan ta tsaya...
Cikin d'aga murya ta fara fad'a...
"Ke wa kike fad'awa haka?"
Cikin rashin kunya ta kalli goggo tace "ga duk Wanda ya tsargu to dashi nake"
Mari baba ya wanke ta dashi cikin b'acin rai yace "Ashe baki da mutunci?rashin mutuncin har yakai kiyiwa uwa ta?"
"Kayi hkri baba,amma ai uwa bata fi uwa ba,kamar yadda kaji haushin maganar dana gaya mata haka nake jin haushi idan kunyiwa umma" ta fad'a tana kuka.....
"Eh lallai ka haifi fitsararru tabbatattu"goggo tayi maganar cikin b'acin rai..
"Hmmm goggo ai sun raina uban nasu,ranar nan haka sumayya tace masa idan taje gidanki sai ya koreta amma nan gidan ubanta ne Ba inda zata" hadiza ta fad'a cikin zuga…
"Eyeh lallai ne gimbiyar Mara sa kunya" ta fad'a tare da kallon baba "yau zakayi sanarwa a Masallachi,inaso gobe e yanzu an d'aura aurenta koma da mahaukaci ne" goggo ta fad'a tare da barin gurin.....
Ta rab'e jikin bango tan ruzgar kuka..
"Wannan wace irin tsana ce?wace irin rayuwa ce wannan?za'a min aure mahaifiyata na raye amma bata san komai ba?na shiga uku niya zanyi da wannan k'addarar?"😭.
A hankali ta zari takalminta zata bar gidan "ina zakije?"
Gabanta yayi mummunan fad'uwa,
"Wlh kin tsorata ni Fatima"
"Ba dole ki tsorata ba tunda baki da gaskiya"
"Hmmmm dole ne na tsorata sbda yanzu am not in d mood"
"Hmm yanzu ina zakije?"
"Neman gentle" ta fad'a tare da saurin fita dan kar fatima ta tsayar da ita.
A zaune ta tarar dashi gaban kayansa...
Cike da mamaki ta k'arasa gurinsa...
"Gentle ina ka shiga kwana2?"
Ya zuba mata idanunsa kawai...
Kuka ya kubce mata a gurin,sai da tayi mai isarta sannan ta d'ago kai ta kallesa
"Gobe e yanzu na zama matar wani"
Kallon mamaki ya bita dashi,dan ya nuna ya tsorata a fili..
Ta cigaba da fad'in "nasan dole ka tausaya min gentle, bansan ya zanyi Ba banma San wa za'a had'ani dashi Ba,zanyi missing d'inka gentle, Allah ya tsaremin kai daga sharrin mugayan mutane"..
Ta tashi cikin kuka tabar gurin...
**********************
Kamar Wanda aka hankad'o haka ya shigo d'akin a gigice
"momma na shiga uku"
Ya fad'a tare da zubewa kan kujera.
Arish l[Truncated by Whatsapp]
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁🍁
_Written by_
*_Nafisa S. Adamu_*
_&_
*_SaNaz deeyah_*
_Dedicated to beebahluv💞& Munay💕_
1⃣3⃣▶1⃣4⃣
"Lafiya Arish?kasan me kake fad'a kuwa?"
Ya dafe kansa yace "momma baban yarinyar yace gobe gobe zai d'aura mata aure koma da wane,momma ya kukayi da daddy?momma please ki taimaka min"
Ajiyar zuciya tayi dan ta rasa menene mafita...
"Momma kinyi shiru please ki fad'a min yadda kukayi da daddy?"
Ta kalleshi cikin kulawa ta fara magana...
"Arish inaso ka dubeni kuma ka fahimceni,tun a jiya na samu daddynku na fad'a masa amma yak'i saurarawa ya fahimceni ma,yace shi 'ya'yansa baza su auri talaka ba,bare su nasu yau kafi yau baka,na rasa meye mafita wlh"
"Momma wlh bazan iya hkri inga an aurar da ita ga wani Ba,momma bazan iya jure ganinta a gidan wani bani ba,bazan so ganinta cikin wahala ba"
Tausayinsa momma take saboda tasan tunda ya fad'i maganar bazai iya jurewar ba sbda tasan Arish yana da kunyar yayi wasu maganganu a gabanta...
"Arish hkri zakayi kasawa zuciyarka dangana"
Shiru kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai Ba.
Hajiya karima ce ta fito ita da Zahra da Asiya....
Suka watso ma momma kallon banza tare da shek'ewa da dariya..
Cikin zafin rai Arish ya tashi ya kwad'awa Asiya mari tare da fad'in "ke wace irin mahaukaciya ce da zaki kalle mu kiyi dariya?"
Haj karima ta d'aga hannu zata ramawa Asiya,Zahra tayi saurin rik'e hannunta "Ummi kiyi hkri kinga mune bamu da gaskiya tunda mu mukayi masu dariya"....
"Ai da kin k'yaleni na ga da Wanda yake tak'ama"
Tayi tsaki ta wuce,Zahra ta Mara mata baya...
Asiya na rik'e da kuncinta ta kalleshi "wlh kayi da 'Yar halak bani ka Mara Ba to ka sani bashi ka d'auka nd u will pay 4 it" ta wuce ta barshi a tsaye...
"Momma wace irin rayuwa ce wannan?"
"Karka damu watarana sai labari"
"Momma wlh zan iya ajje aikina in dawo gidannan in zauna naga Wanda ya Isa ya b'ata miki rai tunda shi *Aryaan* yayi zamansa a turai yak'i dawowa shi ko missing d'inmu bayayi"
"Komai zai wuce *Arish* karka damu".
*******************
Tana k'udundune a bargo tana ta karkarwar sanyi hawaye sai zuba yake a idonta...
Fatima,Nasiba,farida suka shigo d'akin tare da Umma...
"Sumy ki tashi ga Umma" farida ta fad'a cikin jindad'i..
Kukanta ta cigaba dayi a cikin bargo dan tasan ba abinda zai kawo umma gidan....
Umma ta matsa kusa da ita tare da tab'a goshinta....
Zafi taji jikin nata..
A hankali ta bud'e ido ta kalli umma...
Zubur ta mik'e Tare rungume Umma....
"umma na shiga uku mutuwa zanyi"
"Bazaki mutu ba Sumayya"
Nasiba ta k'arasa kusa da umma ta zauna "umma wlh sumayya ita ta jawa kanta,rashin kunyarta tayi yawa bata d'agawa kowa k'afa ba,goggo ma so tayi ta mata rashin kunyar ita kuwa tace aure zata mata yaune fa?bama musan wa za'a bata Ba"
"Ba komai akwai Allah,ki tashi kiyi wanka kafin mutane su fara zuwa,ni mai 'ya'ya mata dama ban zauna ba komai da mahaifiya ya kamata tayi nayi muku Ku duka"
Kuka kawai Sumayya keyi tare da tausayin kanta wace irin rayuwa zatayi shin wazata aura ayau?.
**************
Tana jingine da bishiyar gidan tana k'ara yiwa Malam bayani.
"Malam wlh Arish ya shiga cikin damuwa bansan meye mafita Ba sai wannan,banason gañiñshi cikin b'acin rai...
"Hafsatu kina ganin Ba matsala?kinsan halin mahaifin yaron nan?"
Momma ta gyara zama tace "adai d'aura masu auren sai acewa mahaifinta yayi hkri za'a d'auki amarya zuwa k'arshen mako ni kuma zan San abinyi Kafin lokacin....
Ta bud'e jaka ta fiddo kud'i..
"Malam ga dubu d'ari nan a matsayin sàdakinta"
Yasa hànnu ya karb'a, tayi godiya ta k'ara da cewa "Malam a basu hkri sbda ango bazai samu damar zuwa Ba ayyuka sun yi masa yawa".
"Bara mu k'ok'arta mu tafi kafin wasu su rigamu"
Kuka momma ta fara,inna ta dafata tare fad'in "karkiji komai hafsatu ke tamu ce zamu yi miki duk abinda baifi k'arfinmu ba"
"Nagode ma Allah daya bani Ku a matsayin Wanda suka màye gurbin iyayena,tabbas kun rik'e amanar baffa"
"Da akwai abindà yafi rik'oma da zan yiwa mahaifinki sbda kowà ya San shi mutumin kirki ne,fatan Allah ya jik'ansu ya musu ràhma"
momma ta amsa da "Amin".
_Sadeey & Nafsal_
_07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S. Adamu_*
*Dedicated to beebahluv💖 & Munay💕*
1⃣5⃣▶1⃣6⃣
Tana kwance kan katifa duk ta dunk'ule jikinta sai rawar d'ari takeyi...
Zazzab'ine sosai a jikin....
"Kina inane ki fito ga surukanki sunzo"
Gabanta yayi mummunar fad'uwa,yanzu har an d'aura aurenta da wani Wanda bata sani ba?
Hawaye wani na bin wani,haka suka rik'a kwaranya a idanunta....
Umma ce ta shigo d'akin ta d'agota tare da jan hannunta zuwa d'akin baba...
Kanta a k'asa dan bata son kallon wad'anda take gani a matsayin mak'iyanta...
Gefe ta samu ta zauna har suka gama bayaninsu umma bata ce uffan ba....
Baba ya gyara zama ya fara magana "a gskya mu a tamu al'adar ana d'aurawa yarinya aure ake kaita d'akinta,amma zan iya yi muku alfarma nan da kwana biyu a kaita d'akinta.
Waya Malam ya fiddo ya kira momma yayi mata bayani...
Bayan ya katse wayar ya kalli baba yace "babu damuwa za'a iya kaita a yau ma,wad'anda zasu rakata sai su shirya mu tafi dan kar muyi dare"
Da sauri sumayya ta d'ago kai ta kallesu cikin tsananin fargaba.
Suka tashi suka fita dan su basu guri su tattauna...
"Babu wata nasiha da zan miki dan kuwa bajinta kike ba,Abu d'aya ne zan sanar miki, rashin kunyar da kika shuka anan ita zakije ki girbe a gidan miji,sa'ar ki d'aya kin samu gidan Hutu dan bansan ya akai ma hakan ta faru ba, Sai Abu na k'arshe shine _kada 'ya'yanki su zo min gida dan kuwa ba gidan ubansu bane kece gidan ubanki dan haka idan zakizo to kizo ke kad'ai_ na gama magana ta zaki iya tafiya"
kalaman data fad'a kwanaki sune suka dawo Mata a rai...
_baba nan gidanmu ne Ba Wanda zài hanañi zama a ciki,sai ka bari idañ naje gidanku ka koreni amma nan gidan babana ne_
Maganar ta dawo mata a rai..
Cikin kuka ta juyo ta kalli baba "baba dan Allah ka yafe min"
Ta juya ta kalli hadiza "hankalinki ya kwanta kinyi abinda kike so amma ki sani baki rabani da gidannan Ba har abada" ta fita tana kukan takaici...
Gashi bata wani jindad'in jikinta.
"Oho dai d'ana har ya fito duniya cikin kwanciyar hankali,ina dalilin wannan irin masifa taki".
Tana zaune gaban umma sai kuka take,umma na yi mata nasiha....
Su farida ma kuka suke tayata na tausayin irin rayuwar da zatayi acan,Aure sai kace na babyn roba.
********************
"Malam ban fahimta ba naji kace da *Aryaan* aka d'aura auren bada *Arish* ba?" Momma ta fad'a cikin firgici da tashin hankali...
Arish dake gefen momma ji yayi kamar an soka masa mashi a k'irji..
A gigice ya mik'e cikin rud'u da fargaba.
Malam ya gyara zama sannan yace "Wannan wata dubara ce mukayi sbda mahaifinsu,Auren ñañ da Arish aka d'aura sunañ Aryaan dai mukàyi amfani dashi,saboda tun farko an cewa Alh..
Arish zaiyi aure ya nuñà rashin amincewarsa...
Yanzu kawai za'a cewa Alh. Aryaàn ne yace ayi masa àure sbda yànà soñ ya dawo gida,kinga riba biyu kenan,ga dawowar d'anki ga savng d'in d'anki".
"to Allah yasa mu dàçe" momma ta fad'a cikin jindàd'i..
"Amin" suka amsa...
Arish dai tsarin baiyi masa ba sbda yana tsoron Abinda zaije ya dawo.
Kamar yayi màgàñà sai kuma ya tuna Ba hurumiñsa bane ya shiga maganar manya..
Tashi yayi ya fita yana ta juya maganar Malam a cikin zuciyarsa.
Yanzu shikenan baya da right d'in ya kira sumàyya a matsayin matàrsa yana ji yana gani...
Shin a wane matsayi daddy zài d'auki maganar auren dà aka jonama Aryaan?
Fargabarsa d'aya ce,kada daddy yaçe a turawa Aryaan matarsa can...
Idan kuwa hakan ta kasançe lallai asiri zai tonu kuma ran mommà zai b'aci..
Fargaba yake lokacin daya hango matsaloli dà dama...
Bai gama tunanin ba momma tà k'atseshi da fad'in "Arish muje sbda har án rigà àn kàwo amarya nasàn ñi ake jira"
Key d'in motar ya mik'a mata a sànyaye yac[Truncated by whatsapp].
*dis ix jst d beginning*
💫💫💫💫💫💫
_Sadeey & Nafsal_✍
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S. Adamu_*
_dedicated to beebahluv💖 & Munay💕_
1⃣7⃣▶1⃣8⃣
"Ya ka mik'o min key d'in mota?" Momma ta tambaya..
"Momma ai babu damar naje Sumayya ta ganni"
"Hakane Arish" ta fad'a tana murmushi.
Haka momma taja motar yanaji yana gani.
*****************
A falon gidansu Arish,
Asiya ce zaune kan kujera ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya sai masifa take yiwa Sumayya...
Kuka kawai takey saboda yau babu mai cetonta sai Allah yau k'arshen rashin kunyarta yazo Wanda ada take ik'irarin *Sai taga k'arshen rashin kunyar Hadiza*...
'Yan kaita tuni an juya dasu sai ita d'aya k'wal da aka barta a kan carpet kamar marar galihu....
Haj karima ce ta fito rik'e da cup da kuma kwalin lemo ta ajje kan d'an k'aramin center table dake kusa da daddy....
Samun kujera tayi ta zauna "wai wannan yarinyar bazata daina kukannan ba?duk ta cikawa mutane gida" mtswww....
Taja tsoki,daddy da tunda akace amaryar gidannan ce bai sake cewa komai ba sai lokacin
"Ki barni dasu,jira nake ita Hajia habiban tazo naji wane ya yi aure bada izini na ba a matsayina na waliyyin 'ya'yana?"
"Gskya kam Alh tayi mugun raina maka hankali sai kace ba kai ka haifi *Aryaan* da *Arish* ba?ni yanzu 'ya'yana daga mazan har matan waya Isa ya tsallake dokarka"
Ya bud'e baki zaiyi magana momma ta shigo cikin sallama....
"Sannu da zuwa" daddy ya fad'a,a yadda yayi maganar sai da tasha jinin jikinta....
Cikin falon ta k'araso tare da d'ago Sumayya "tashi daga k'asa 'yata"
"Dakata habiba" daddy ya tsayar da ita cikin tsawa...
Ya mik'e tsaye cikin fad'a ya fara magana "me kike nufi ne?wane irin uba kika maidani ga 'ya'yanki?taya za'ace anyiwa wani a cikin 'ya'yana aure ba da Sanina ba"
Cikin sanyi murya tace "anyi maka laifi Amma kayi hkri nasan idan nace d'anka na son aure ba yarda zakayi ba,shiyasa muka yanke hukuncin idan anyi auren ka Sani"
Kai ya girgiza tare da fad'in "lallai kin isa da yawa"
"Kayi hkri"
"Sorry for urself Dan kuwa kinsan bakiyi min in k'yale ko?darajar 'ya'yanki ne yasa kike zaune a nan da tuni na sender ki Inda kika fito"
Bugun k'irjin Sumayya ya k'aru yayinda Dana Sani ya yawaita a zuciyarta....
_wannan masifa da mai tayi kama?Ashe ba umma ce kad'ai taga a k'ubar aure ba_ ta fad'a cikin zuciyarta....
"Wanene a cikinsu yayi aure?"
*"Aryaan* ne"
*"Aryaan*?" Daddy ya maimata maganar tare da zaunawa...
Wayarsa ya fara latsawa tare da karawa a kunne...
"Kada kace min komai bana buk'atar gaisuwarka,duk Inda kake kayi booking jirgi gobe gobe ka dawo ka had'o kayanka duka Dan kabar zaman k'asarnan" ya katse wayar tare da kallon momma wadda har a lokacin gabanta na fad'uwa.....
*"Aryaan* aure yafi tsaron kamfanin ubansa da yake yi ko?to ya dawo Nigeria yaci aure ga Matar nan ai,shi *Arish* da yake jin magana ta sai ya koma can idan lokacin auren yayi mu Tura masa mata inya samu acan kuma shikenan,ai shima *Aryaan* haka na masa alk'awari Amma ya tsallake magana ta"
A yanzu bugun zuciyarta momma ya k'aru Ashe plan d'in da suka had'a ba mai d'orewa bane,yanzu ya zat.........bata gama tunanin ba daddy ya katseta...
"Sai kuje kukai amaryar part d'inta kafin a gama gininsu nacan waje"
"Alh ina da magana?"
"Bana buk'atarta a yanzu" ya fad'a tare da barin falon....
Part ne babba flat mai d'auke da d'akuna biyar parlour 2 bedrooms 3,Wanda dama tuni daddy ya gama tanadarwa 'ya'yansa maza su Biyar *Aryaan,Arish,Ashaq,Asrar,Ashaz*, part d'in *Sumayya da Aryaan* yayi matuk'ar kyau da tsaruwa...
'Daya daga ciki Lemon green parlour ne d'ayan kuma gaba d'ayansa light purple ne,yayinda bedrooms d'in ya kasance pusher pink,golding,dark blue....
Ko wane d'aki kalar kayan d'akin kalar paint d'in d'akin....
Tana zaune gefen gadon d'aya daga cikin bedrooms d'in,momma na tsaye tana ta yi mata nasiha kamar ba Surakarta ba,tayi mata a matsayin nasihar uwa ga 'yarta lokacin aurenta....
Har lokacin Sumayya kuka take wannan wace irin k'addararriyar Rayuwa ce Wai mijin da aka d'aura masu aure Bayama k'asar,shin zaman dad'i kuwa zai k'ara ziyartar ta?...
Kuka sosai ta cigaba dayi a cikin mayafin da aka lullub'a mata Dan ko momma bazata ce ga kamannin Sumayya ba sai dai kawai tasan *Arish* bazaiyo zab'en da bai dace dashi ba...
Zahra ce ta shigo d'akin da gudu "ina amaryar tamu?"
Momma tayi murmushin jindad'i lokacin da Zahra ta zauna kusa da Sumayya tare da rungumeta...
Cikin jindad'i tace "yanzun na dawo daga saloon akace min anyi amarya a gidannan kinga ko jaka ban ajje ba na juyo,Auntynmu bud'e fuskarki mu ganki nasan *Yaya Aryaan* yayi dace"
Duk lokacin da aka ambaci *Aryaan* a matsayin mijin *Sumayya* sai momma taji fad'uwar gaba....
"Yawwa Zahra bara na barku da ita naje nad'an kimtsa"
"To momma" ta fad'a tana dariya...
Ita ma momma cikin jindad'i ta fita Dan ganin *Zahra* ce kad'ai a gidan take son farin cikinsu...
Tana rik'e da waya ta gama bawa Aryaan labarin abinda ke faruwa....
"Amma momma daddy kinsan laifina zai gani?k'ila ma ya daina min magana"
"Aryaan a hankali daddynku zai fahimci gaskiya,fisabilillahi so yake Ku lalace idan bai bari kunyi aure a wannan lokacin ba"
"Hakane momma Amma gskya banji dad'i ba shima Arish da rigama yake"
"Kai dai idan ka dawo zan warware maka komai"
"Amma kuma momma taya zan rik'e Matar da ba tawa ba a matsayin matata?momma kinsan nifa bani da hkri Dan wlh zan iya mata duka idan ta min gadara"
Hmmmmmm "kasa Allah a ranka Aryaan,ba matarka bace baka da right d'in tab'ata bare duka,zakayiwa d'an uwanka alfarma kafin mu samu mafita Dan kuwa Arish baya da d'an uwa kamar kai"
"Shikenan momma zan rufa masa asari har lokacin da komai zai warware"
"Ni zaka rufawa domin nice a cikin matsala"
Murmushi yayi sannan yace "Allah dai ya kaimu goben danni tuni na gama shirya komai"
"Amin,Allah muku albarka"
"Amin momma"
Sukayi Sallama suka katse wayar.
_Nafsal 07036383997_
_Sadeey 07035111671_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_Nafisa S. Adamu_*
_&_
*_SaNaz deeyah_*
_dedicated to beebahluv💖 & Munay💕_
1⃣9⃣➡2⃣0⃣
*WAYE ARISH?*
Alh Muhammad Imamu hafaffan d'an garin Zaria ne,anan yayi primary and secondary skul d'insa......
Ya taso cikin gata da soyayya ta iyaye...
Yana level 2 a Ahmadu bello university babansa yayi masa auren gata...
Domin Matar ma babansa ne ya zab'a masa a d'aya daga cikin 'ya'yan aminansa ....
A lokacin yana soyayya da karimatu wadda ta kasance tana diploma anan A.b.u d'in tana karanta mass comm yayinda shi kuma yake karatun business administration....
Kwatsam yaji anyi masa aure,kasancewarshi mai biyayya ga iyayensa yasa bai nuna rashin jindad'insa ba...
A haka suka zauna da Habiba tana gaba mata azaba Amma ta shanye bata tab'a nuna hakan ba...
Har ya gama karatunsa ya samu aiki a Kaduna suka koma can da zama.
*Aryaan* shine d'ansu na fari Wanda Alh Imamu da kansa ya zab'a masa sunan.....
Ya d'auki son duniya ya d'ora akan *Aryan* komai nasa *Aryaan*....
*Aryaan* yana shekara 8 a duniya haj habiba ta haifo d'anta namiji...
Tun daga lokacin Alh Imamu ya ajje komai ya fara tattalin matarsa tare da nuna kulawa a gareta....
Da kanshi ya bata zab'i akan sunan jariri...
*_Arish:-the brave Soldier_* shine sunan da ta zab'a masa kasancewar tanason ya zama soldier....
Kamar wasa shekaran *Arish* 10 a duniya lokacin *Aryaan* yanada sha takwas ya gama sec skul yayinda *Arish* yake a js3 kwasam Alh ya auro tsohuwar budurwarshi haj Karima Wanda a lokacin 'ya'yanta hud'u suka rabu da mijinta....
Tun daga ranar momma(haj habiba) tayi bankwana da farin ciki,ga haihuwa ta tsaya mata cak...
Ta rungumi 'ya'yanta Wanda a lokacin Alh Imamu yaja baya dasu..
Haihuwar fari haj Karima ta haifo maza uku.....
Bidirin bakin sunan Wanda ba'a yisa ba ko a haihuwar *Aryaan* shi akayi a gidan....
Party kala kala yara sunga gata...
Aka sa masu suna *Ashaq,Asrar* da kuma *Ashaz*,
shekararsu Biyar a duniya aka haifi *Asiya* tana da shekara biyu aka haifi *Zahra* wadda itace autar gidan a halin yanzu tana Ss2,Asiya Ss3, triple kuma suna karatu a Australia....
Yayinda *Aryaan* yake director na kamfanonin mahaifinsa dake Span....
Arish kuma SSS ne yana aiki a jahar kano....
*Wannan shine tak'aitaccen labarin Arish*
_Cigaba_
Kiran Sallahr farko na assalatu Sumayya ta mik'e zaune tare da sakin ajiyar zuciya Dan ko runtsawa batayi ba,tsoro takeji ga motsi da takeji kamar za'a shigo,ga sanyin AC ga kwa nan kad'aici,ga ciwon kai......
Duk ita kad'ai...
A hankali ta sakko daga kan gadon tare da k'arewa d'akin kallo....
_"na shiga uku,Allah kasa ba gidan 'yan yankan kai aka kawoni ba,gidannan yafi k'arfina"_ ta fad'a a hankali yayinda hawaye ya zubo a fuskarta...
Da k'yar ta gane Inda zata kunna tap tayi alwallah....
Tana kan sallaya har gari yayi haske sosai..
Ta zari wayarta ta fito parlour...
Dank'ari! Ni wa? A gidannan duk nawa ne?shin wane irin millionaire na aura?waye shi?
Haka ta gama zaga ko ina sannan ta shiga wani side...
Long corridor ne kamar yadda hanyar bedrooms d'inta suke....
A kitchen ta ganta....
"Nan kitchen ne?ko d'akinmu bai kai girmansa ba" ta fad'a cike da tsoro...
Pusher pink bedroom ta koma Wanda dama can momma ta kaita...
Bedsheet d'in ta gyara ta kakkab'e komai,a kan mirror taga room freshener ta feshe ko ina a d'akin tabi duk gidan ta feshe sannan ta shiga toilet...
Inda Allah ya taimaketa tana da tsabta gashi tasan rayuwar gidan masu kud'i a novels da take karantawa jefi jefi....
Tasan komai na tsabta da zaman aure da yadda zaka tafiyar da rayuwarka cikin jindad'i a gidan miji...
A bakin wardrobe ta tsaya cak lokacin da ta ganta cike da kaya Dan bata Masan me xata d'auka ba...
A sanyaye ta janyo wata gown light blue ce atamfa ta saka ta, komawa jikin mirror tayi ta janyo drower gurin fashions birjik ribbons,bangles,da tarkacen k'alek'alen...
Ta gama shirinta cikin blue and pink sai zuba k'amshi take tare da fargabar wane irin miji ta aura waye mahaifinsa, da komai akayi mata kamar d'iyar President...
Tana zaune a purple parlour tana duba agogo jefi jefi ga yunwa na cinta......
K'arfe sha d'aya agogon dake manne a bango ya nuna,tsab ta mik'e tare da yafa mayafinta aka....
Ta rufe part d'in da key ta nufi part d'in momma Dan ta gaidata...
Tana ta fargaba a haka ta Tura k'ofar falon..
*Arish* ya fito daga side d'insa yayi daidai da shigowar Sumayya part d'in.
_Tofa......Fans ya ya take ne?_😳🤔
_Ku biyo Sadeey da Nafsal danjin yadda zata kaya_...!
_Sadeey 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍂 *MENE AIBUNA* 🍂
🍂🍂🍂🍂🍂🍂
🍂🍂🍂🍂
_WRITTEN BY_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adam*_
*dedicated to beebahluv💖 & Munay💕*
2⃣1⃣▶2⃣2⃣
*I dedicate dis page to u my Aunty(Aishat A Muh'd)u'ar such luving nd caring Aunt@luv u alot*
Da sauri ya koma baya tare da b'uya a jikin bene...
A parlourn ta tsaya kasancewar shiru babu motsin kowa gashi batasan ina zatayi Ba tunda jiya aka kawota kuma bstasan ko Ina na gidan Ba.
Kamar momma tasam zata shigo sai gata ta fito daga side d'inta....
Sumayyar na tana zube kan carpet, duk da bata San fuskarta Ba amma ta gane itace...
Da sauri ta k'arasa gurinta tace "a'a 'yata yaushe kika shigo?meyasa kika Zauna a k'asa?"
Bata ce komai ba illa k'ara durk'ushewa da tayi ta gaida momma.....
Janyo ta tayi tare da fadin tashi mu shiga d'akin,fitowar da nayi breakfast zan had'a a kai miki dan nasan kina jin yunwa. .
Idonta ya kai kan *Arish* dake lab'e jikin bene,tayi nurmushi tare da jan Sumayya cikin d'akinta....
Sai lokacin *Arish* ya samu damar fitowa
daga inda ya b'uya,
Da saurinsa ya fita tare da shigewa cikin mota...
Tana zaune gefen gadon Momma,Sai janta take da hira,itakam tayi k'asa da kai saboda tsananin kunya..
Turo k'ofar Akai aka shigo,Zahra ce da saurinta ta k'arasa ta gaida momma sannan ta zauna kusa da Sumayya...
Auntynmu jiya kin b'oye mana fuskarki yau dai gashi na ganki..
Ta d'ago kai ta kalli momma tace "Momma wlh yaya *Aryaan* yayi dace kuma ya iya zab'e"
Shiru momma tayi dan bata da tacewa.
*******************
Kowa dake gidan ya halarci taron da daddy ya buk'ata idan ka d'auke *Arish* da baya gidanma tun fitarsa da Safe...
Daddy yayi gyaran murya ya fara magana,
Na d'auka na isa da kai *Aryaan* na d'auka duk dokar dana shimfid'a maka bazaka tsallake ba Ashe ni *KALLON KITSE NAKE YI WA ROGO*(Littafin Autar hijia).
*Aryaan* dai yana kusa da momma yayi shiru dan bak'in ciki da takaici..
Daddy ya cigaba da fad'in,Aure ka zab'a ko?to ga matar nan ankawo maka har gidanku...
Ya nuna Sumayya dake takure a k'asan tiles..
Kasan meye dokokina akan aurenku?..
Da sauri *Aryaan* ya d'ago kai a kid'ime Dan yasan daddy zai iya yanke babban hukunci akanshi..
Daddy Dan Allah kayi hkri nasan nayi laifi amma ina Neman afuwarka...
Hmmm *Aryaan* kenan! meka maidani ne?
Banzan uba?Wanda baya da iko akan 'ya'yanshi?to k'arya ne...
Hukuncin dana yanke a kanku kaida matarka shine,
Bana buk'atar Ku Sake gaidani kai kaida ita,sannan Iran ina guri banason ganinku a gurin.....
Babu shiri *Aryaan* mik'e tsaye, Daddy hukuncin nan yayi min tsauri.........!,
Dakata *Aryaan*! Ya katse shi cikin tsawa..
Bana buk'atar maganar ka a halin yanzu ka rik'e kayanka,kuma ka zauna in gama fad'a maka dokokina..
Cikin rashin gwarin jiki *Aryaan* ya zauna...
Kuma duk 'yan aikin gidannan mata zan sallamesu,daga yau Habiba ce zata rik'a duk wani aikin da Sukeyi,rangwame d'aya zan maka shine kasa matarka tayi replacing idan ta amince ruwanku...
Wannan shine hukunci na farko da na yanke miki sauran kuma ba saina fad'e su ba...
Ina *Arish* yake?...
Tun Safe ya fita,momma ta fad'a cikin Sanyin Murya...
Ki sanar dashi ya zauna cikin shiri dan Zan masa visa ya tafi a satin nan....
Daddy aikinshi fa?,Zahra tayi maganar itama cikin rashin jindad'i...
Aikinsa ai bazaisa Ya tsallake dokar ubansa ba kamar yadda d'an uwansa yayi...
Ai wannan yarinyar bata da kishin iyayenta sam..
Asiya ta tab'e baki tace,daddy nifa 'yan aikine suke gyaramin d'aki na...
Yanzun ma ai bata b'aci ba habiba zatayi muku duk abinda masu aiki keyi,tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka...
ya mik'e tsaye tare da kallon haj karima,triple sai upper week zasu dawo ko?..
Eh da yardar Allah..
'Dakinsu yana buk'atar gyara...
Ya fice yabar falon...
Itama haj karima cikin annashuwa tace ma 'ya'yanta ku tashi mu tafi...
Zahra da kamar bazata tashi ba,haka nan ta tashi suka bar falon...
A hankali Sumayya ta d'ago kai dan ganin wane irin miji aka aura mata...
Idonta ya sauka a fuskarsa,kallon tsana taga yana yi mata k'arara..
Babu shiri ta maida k'wayar Idonta k'asa...
Kallon tsana yake min,to meyasa Ya aureni idan baya sona..
Gabanta yayi mummunar fad'uwa lokacin da zuciyarta tace mata _Kodai Momma ce ta had'a auran_…
Na shiga uku Ya rayuwata zata kasance tare da mijin da baya sona.
0 comments:
Post a Comment