Karka damu *Aryaan* zanyi komai kamar yadda ya fad'a,komai zai wuce insha Allahu...
Da Sauri Sumayya ta k'arasa gaban Momma tare da ajje gwiwo yinta a k'asa...
"A'a nice ya dace nayi bakya ba,dan Allah ki barni zanyi duk abinda masu aikin gidannan keyi…
Cikin k'arfin hali Momma ta dafa kan Sumayya tare da fad'in…
Karki damu 'yata,aikin gidannan ya miki yawa…
Baiyi min yawa ba,inayin fiye da Wanda ya fisa ma...
Kiyi hak'uri 'yata bazan iya bari kiyi ba,ba aiki aka auro ki kiyi a gidannan Ba...
Ta fad'a tare da barin falon...
Bayanta *Aryaan* ya bi,aka bar Sumayya ita kad'ai a falo..
_Allah Sarki gentle ko a wane hali yake yanzu,ko me su Yaya Nasiba suke yanzu?nasan anacan ana gana musu azaba,nima gani zanga k'arshen rashin kunyata a gidannan,an kawoni inda ba Wanda na sani ko ya sanni babu ko wayar da zan kirawo inji lafiyar 'yan uwana wannan wace irin rayuwa ce?_…
Yana zaune a gefen momma tana yi masa nasiha *"Aryaan* ina k'ara jaddada maka kaji tsoron Allah ka guji fad'awa ga halaka,wannan yarinyar Ba matarka bace ka sani dan Allah ka kiyaye ka rik'ewa d'an uwanka amanarsa na fad'a maka komai,kada ka hantareta kada ka yarda Ku kwana d'aki d'aya"..
Insha Allahu zan kiyaye Momma…
******
Tana zaune a gefen gado shi kuma yana tsaye jikin mirror,Zuciyarsa zafi take gaba d'aya haushinta yake ji da tsanarta..
Mtsww yaja gajeran tsoki tare da fad'in "zan shimfid'a miki dokokina,na farko na bar miki wannan bedroom d'in da d'ayan golden sune naki kada ki sake ki shiga nawa,falo kuwa babu inda Bazan zauna Ba idan naso…
Duk abinda kike buk'ata ki rubuta a paper ki ajjemin kan center table zan gani....
Kuma kema duk abinda kike buk'ata zan ajje miki a falo inda zaki gani…
Kada ki yarda Ina zaune a falo kema ki zauna babu wannan…
Kallon banza ya bita dashi tare da barin d'akin,a zuciyarshi yake fad'in _me *Arish* ya gani a jikin wannan 'Yar k'auyen?ita Ba fara ba,mtswww kodan ni na saba ganin farar fata_
*SUMAYYA*
*Chocolate colour ce,doguwa ce babu laifi fuskarta ma doguwa ne,tana da hanci dogo,bakinta d'an k'arami ne mai d'auke da peach lips,tana da idanu masha Allahu,gashi kam akwai shi kasancewar ummarsu buzuwa ce*......
*dz Sumy's personality*...
Da ido kawai ta bishi tana tunanin rayuwa irin Ta gidansu…
_insha Allahu da kanka sai ka dawo gareni,bazai yuwu ace banji dad'in zaman gidan ubana ba kuma zaman gidan miji Ya gagareni_...
Ta furta a hankali tare da kallon k'ofa...
_shin ta ina zan fara?yayi zaman turai,tabbb da aiki a gabana_…
Kamar magana take jiyowa daga falo,da sauri ta yafa gyalenta ta fita...
Sannunku da zuwa…
Sumayya ta fad'a dan bata sansu ba.
Yawwa sannu...
Cikin bak'unta suka gaisa…
Ta tashi ta shiga kitchen ta d'ebo kayan biki a plate ta kawo musu tare da lemo…
matar tayi murmushi tace "baki Sanni Ba ko?"
"Eh gskya ban sanki ba"
"Ayya! Sunana Rabi'atu ni 'Yar gombe ce,aure ne ya kawoni Kaduna yau watana d'aya a garinnan ni neighbor d'inki ce,wannan k'anwata ce ta kawo min ziyara shine nazo mu gaisa"
Cikin jindad'i Sumayya tace "amma na gode kuma naji dad'in zuwanki dama nima bansan kowa Ba a........
Bata k'arasa maganar ba taji an daka mata tsawa……
Waya baki izinin tarar bak'i a gidana?
Ko gidanki ne?
Tayi k'yam a tsaye tana kallonsa cike da mamaki…
Tsaki yaja tare da fita waj[truncated by whatsapp].
_Sadeey_ _07035111671_
_Nafsal_
_07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_Nafisa S. Adamu_*
_&_
*_SaNaz deeyah_*
*Dedicated to beebahluv💖 & Munay💕*
2⃣5⃣▶2⃣6⃣
Tana nan tsaye ta kasa ko motsawa daga gurin...
Har sai da Rabi'at ta kama hannunta ta zaunar da ita…
Karki damu 'Yar uwa sai hak'uri...
Zaunawa sumayya tayi tare da dafe goshinta...
Kasa jurewa tayi dan haka ta bawa Rabi'atu labarin komai...
Hawaye ta goge saboda takaici...
Karki damu 'Yar uwa,gaskiya kina cikin tsanani,dole kina buk'atar taimako…
Ta kalli k'anwarta tace "farha ungo key d'in ki jirani ganinan zuwa...
Bayan tafiyar farha,Rabi'at ta juyo ta kalli Sumayya tace "me kika tanada 'Yar uwa?wlh karkiyi wasa da damarki idan Ba haka Ba zaki iya rasa aurenki a yadda naga mijinki Nada zafi".
Murmushin takaici Sumayya tayi sannan tace "Nafi k'aunar ya sakeni in koma garinmu in cigaba da rayuwata cikin kula da gentle"
"Gentle?"
Eh gentle wani mahaukaci ne a unguwarmu Wanda baya duka baya zagi ko magana bayayi hakance yasa nake kiranshi da gentle...
Hmmmm ki ajje maganar gentle Sumayya ki fuskanci Alk'iblarki abinda ke damunki shi zamu samu mu warware...
Ki zamo mai Saka k'ananun kaya a gidanki,ki kasance cikin tsafta,kwalliya...
Uwa uba girki,idan kin iya girki kin gama komai...
Sannan da yace ki daina yi masa magana kar kiyi amfani da maganarsa ki yi masa magana a duk lokacin da kika so mijinki ne babu wani Wanda zai miki shamaki...
Girki shine babban matsala dan wlh bansan yadda zanyi amfani da kayan kitchen d'ina Ba ni ban saba Ba kullun da itace muke aiki,nad'an iya snacks kad'an,kamar meat pie,cincin,...
Hmmm sister wannan ai normal snacks ne zan kowa miki wasu harda juice juice ma...
Taso muje na nuna miki Idan yaso daga baya sai mu Fara practicing,yanxu dai zan nuna miki yadda zakiyi amfani da gas,rice cooker,micro wave,da sauransu...
Haka suka shiga kitchen ta nuna mata abubuwa da dama nan harta fara koya mata wasu daga cikin snacks,anan tayi sallahr Azhar..
Sai wajen k'arfe hud'u sannan ta tafi tare da alk'awarin gobe zata dawo.
*****************
Kana jin abinda na fad'a maka ko?…
*Arish* yayi shiru Ba tare da yace komai ba,
Asiya ta gyara zama tace "hmmm ni ranar nan har mari nasha wlh gwara ya bar k'asar ma".
Yanzu yaushe zaka gama aikin da kukeyi?,
Eh har anyi arresting d'in su anma shigar da k'ara kotu...
Hmmm ai k'wara ka tafi ma amma ina amfanin kai ta zama a matsayin mahaukaci ina amfani...
Daddy ai haka sha'anin aikin namu yake..
mik'ewa yayi tare da fad'in "ka zamana cikin shiri" ya fad'a tare da ficewa..
A bedroom d'in momma, *Arish* yana zaune kan sofa,yayinda momma take zaune a gefen gado *Aryaan* yana gefenta...
Momma yanzu mene mafita?gaskiya bazan iya zuwa Ba saboda Abu biyu..
Na farko bazan iya zuwa ba saboda banason in barki haka ana wulak’anta ki a gidannan..
Na biyu kuma matata momma ya za'ai na tafi na barta anan?
Uhmm! *Arish* ya zama dole ka tafi ka barmu saboda rashin tafiyarka wlh zai iya haifar da Dana sani...
Ka tafi idan komai ya lafa sai ka dawo,matarka kuma is Safe zan kula da ita domin Amanarka ce ko ince *AMANARMU* ce,insha Allahu komai zai zama normal...
Momma tayi maganar cikin kwantar masa da rai.
Haka *Arish* ya danne zuciyarshi ya fara shirye shiryen tafiya..
Kwana hud'u tsakani jirgin su *Arish* ya d'aga yanaji yana gani,bayada ikon ganin Sumayya bare tafiya da ita..
Ita kuwa Sumayya ta dage da koyon duk wani abinda tasan zai jawo hankalin mijinta ya dawo gare ta,dan haka ta dage inyau tana gidan Rabi'at gobe Rabi'at na gidanta,sun zama aminan junu.
*Bara mu waiwaya gidansu Sumayya*
Fatima ce ta shigo da gudu,Nasiba ta tare ta a tsakar gida "kee lfya?"
Ta tsaya tana haki ta kalli Nasiba tace "kinsan meya faru yaya?gentle d'in yaya Sumayya Ashe Ba mahaukaci bane d'an sanda ne,sun Kama Alh Salisu d’an kwangila".
Nasiba ta zaro ido tace "dagaske kike"
Farida ta fito daga d'aki ta k'araso gurinsu..
"Yaya Nasiba wallahi da gaske ne,ita Fatima labarin taji ni kuma da idona na ganshi..
Ya bani takarda yace na baki na manta wallahi bara na d'akko miki…
Ta shiga d'aki ta d'akko takardar ta fito da ita tare da mik'awa Nasiba...
Cheque ne na 100k,Nasiba ta fad'a cike da mamaki...
Wallahi na manta yau kwana shidda da bani,sun kama Alh sani.
Aikuwa kuje banki a karb'o yau ko abincin ci dama bamu dashi, kuje keda Fatima ni zan zauna kar baba da hadiza su dawo bama nan kinsan hadiza da k'age.
Hakane bara muyi sauri muje mu dawo naso ace Sumayya tazo taga gentle d'inta da tayi murn[Truncated by Whatsapp].
_Sadeey 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_Nafisa S. Adamu_*
&
*_SaNaz deeyah_*
*Dedicated to beebahluv💖 & Munay💞*
2⃣9⃣▶3⃣0⃣
Sai da tasha kukanta ta k'oshi sannan ta mik'e ta shiga bedroom d'inta...
Toilet ta fad'a ta sake yin wanka..
Ta gama shiryawa tsaf sannan ta koma d'akin *Aryaan* d'in...
Kayan abinci ta kwashe takai kitchen sannan ta dawo ta gyara d'akin fes ta feshesa da turarukan k'amshi...
Tana kwance akan gadonta hawaye yanata bin kuncinta tana gogewa...
_Allah sarki gida,da yanzu duk tsiya rashin kunyata zata k'waceni da yanxu na kaiwa gentle abincinshi,da yanzu ina tare da 'yan uwana muna hira_…
Ta sake goge hawayen sannan ta tashi ta d'auki hijab d'inta ta fita...
A falo ta ganshi zaune yana kallon news ta wuce ba tare da ta tanka masa Ba shima bai mata magana Ba...
Tana fita yaja dogon tsaki..
_an had'ani da k'ajaga kawai,wani da aure nida kular masa da mata gaskiya an had'ani da wahala_…
Ita kam Sumayya direct part d'in momma ta wuce,a falonta ta sameta zaune ita da wata suna hira...
Yawwa gatanan ma saiku gaisa,momma ta fad'a lokacin da Sumayya ta k'arasa gurin...
Gaidasu tayi kanta a k'asa tana murmushi....
Matar ta janyo ta cikin wasa tace "ah gaskiya d'ana yayi zab'e"
Momma tayi murmushi tace "shi kuwa miskilin ai ya biyewa ubansa baya ko maganar aure"
"Zaiyi insha Allahu shima"
Momma tace "hmmm to Allah ya kawo lokacin".
Ta d'an kalli Sumayya sannan tace "zo nan 'yata me nake gani a kuncinki?...
Ta d'an shafa gurin kanta a k'asa tace "babu komai nazo shiga d'aki na buge da k'ofa"
Haj Falmata gane min dan Allah nifa kamar sawun mari nake gani a fuskar yarinyarnan...
Shine mana wlh mari ne...
*Aryaan* ne ya mareki ko?a wane dalili?...
A'a.......a'a..
Ta rasa me zata ce ma..
Cikin b'acin rai momma ta kira *Aryaan* a waya tace yazo ya sameta a falonta...
Sumayya na zaune tayi shiru tana tunanin hukuncin da *Aryaan* zai d'auka a kanta tunda tasan cewa zaiyi ita ta kawo k'ararshi...
Cikin sallama ya shigo ya zauna gefen kujera sannan yace "momma ga ni"
"Ai na ganka d'in"
Ashe ban isa na saka ko na hanaka ba?yaushe ka fara musa maganata *Aryaan*?,duk maganar dana gaya maka akan Sumayya ta tashi a banza?....
Ya d'ago kai yace "momma 4 wat reason zata yi min rashin kunya na k'yaleta,idan na barta wlh zata yi abinda yafi haka"...
Ai ba fad'a zakayi ba a zaune sai ka tashi ka dake ni shiyafi dacewa...
A'a hajia kuyi hkri abi abin a hankali...
Taya zan bi abinnan a hankali hajja falmi,kina ganin yadda yake min magana kamar zai dake ni...
To wallahi bari kaji idan ka k'ara yi mata koda kallon banza ne wlh sai na b'ata maka,haba da Allah kaiko tausayinta bakaji?tayi aikin gidannan tayi na nata side d'in,duk bautar da takeyi a gidannan baka gani,ai ba aiki aka auro ta tayi Ba amma tazo tana taimakon mahaifiyarka kai kuma kana muzanta mata,to wlh nayi muku Katanga daga yau,ka kuma tashi ka bani wuri...
Cikin b'acin rai ya tashi ya fita....
*12:45pm*
Tana kwance kan gado tayi rufda ciki hankalinta gaba d'aya a tashe yake....
A hankali ta sakko daga kan gadonta ta koma falo ta zauna...
Minti kad'an ta kalli agogo amma shiru babu *Aryaan*...
_Allah kada ka kamani da laifin da ban aikata Ba,Allah ka sani kuma kana gani banyi niyyar na b'ata wa Mijina rai Ba_.
Wani guntun hawaye ta goge tare da mik'ewa tsaye lokacin da taji horn d'in mota dan kuwa ta tabbatar shine....
Tana nan tsaye ya turo k'ofa ya shigo....
Cikin kid'ima da firgici da mugun tashin hankali ta ja da baya tare da fad'in "yaya *Aryaan* me zan gani?hasbunallahu wa n'imal wakil"
*_Uhmmmmmm✍_*
_By Sadeey&Nafsal_
_07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S. Adamu_*
*Dedicated to beebahluv💖& Munay*
2⃣7⃣▶2⃣8⃣
Basu dad'e da fita ba,su baba suka shigo...
Farida ce kad'ai zaune a tsakar gidan tana karatun Ahlari...
Ina sauran 'yan uwanki,
Sun je nema mana abinda zamuci,
Da izinin wa suka fita?,
Farida ta b'ata rai ta kalli baba, kai kace yau sai dai mu nemo abinda zamu ci fa...
Baba dan Allah meyasa baka k'aunarmu?mu 'ya'yankane da Allah ya baka baba idan bakayi mana ba shin wa zai mana?ka tsanemu kasancewarmu 'ya'ya mata baba kada ka manta zamu iya zama wasu a nan gaba,na tabbatar a wannan lokacin zaka so taimakonmu saboda lokacin tsufa yazo maka,dan Allah kaji tausayinmu ka mana adalci.
Kingama ko akwai sauran magana a bakinki?
Nace kingama ko akwai sauran magana ne?, ya fad'a cikin tsawa..
Ta tsorata dashi sosai,dan haka tayi shiru bata ce komai ba...
Hadiza ta d'an dafa ciki tace "wash ni wlh hayaniyar yarannan sai ta sa nayi b'ari...
Ta fad'a tana ya tsina fuska..
Ki barni dasu duk zanyi maganinsu,dani suke zancen ai sunga yadda na yankewa sumayya hukunci to wallahi idan sukai wasa abokaina zan aura musu...
Yo Maigida sai kace kana tsoronsu wallahi duk ka sallama su ko ma samu mu sake a gidannan...
Uhmmm _Saniya da ciki ba'asan abinda zata haifa ba_ …
Sumayya ta fad'a..
Kan uba! Me kike nufi da hakan..
Ina nufin keda kike proud da cikin ki bakisan abinda Allah yayi ba...
Maigida kanaji ko?kaga bak'in ciki k'arara...
Zo nan! Ya kirata cikin b'acin rai yace "wallahi duk abinda ya samu cikin nan ke zan tuhuma keda Sumayya..
Kizo nace!,
Kuka ta fara tare da fad'in wallahi bazan zo ba ka dokeni...
Ta ruga da gudu ta fita..
Tananan tsaye jikin layinsu har su Nasiba Suka dawo,ta tare su tana kuka ta basu labari...
Nasiba tace "kinga kud'in da yawa a jakata,na yanke hukuncin mu gudu mu tafi gombe gurin umma dan ni yanxu ko gida bazan shiga ba karya ganni da jaka ya kirani ya karb'e..
Sunfi awa biyu anan Kafin Fatima taje tayi sand'a ta shiga ta janyo musu k'atuwar bakkon kayansu.
*****************
Ta gama gyara gidan gaba d'aya komai neat,kitchen ta shiga ta d'ebo kayan abincin ta jera a dinning table...
Jollof d'in cous-cous tayi Wanda yasha lawashin albasa da kifi,sai sinasir da miyar ganye...
Sannan tayi musu _Cucumber juice_…
Wannan duk Rabi'at ce ta koya mata..
Gidan gaba d'aya ya game da k'amshin abinci dana turarukan wuta da freshner ..
Sanye take da doguwar riga ta atamfa lemon green,vlisco Holland, fitted gown ce d'inkin yayi kyau yayi matuk'ar karb'arta...
Makeup tayi sosai jiran dawowar mijinta kawai take dan yanzu ta d'an fitar da tsoro yadda Rabi'at ta bata shawara...
Tana zaune akan kujera ta saje da falon kasancewar falon ma duk abinda ke cikinsa lemon green ne...
Horn d'in motarsa taji lokacin taji wani mugun bugun zuciya...
Minti biyar sai gashi ya shigo falon hannunsa rik'e da brief case rantsa a had'e..
Da sauri ta mik'e ta k'arasa gurin..
"Sannu da zuwa" ta fad'a tare da mik'a hannu zata karb'i briefcase d'in...
Ke wace irin dak'ik'iya ce? Ya fad'a tare da hankad'ata da brief case d'in..
Tayi baya dan saura kad'an ta fad'i...
I warned u na fad'a Miki ki daina zuwa inda nake ke mayya ce wai?
Mayya kuma?
Mtswww yayi tsaki ya wuce..
Kan kujera ta zauna tare da dafe kanta...
Shawarar Rabi'at ce ta fad'o mata _karki damu da duk wulak'ancin da zai miki wlh duk zai daina indai kinbi shawarana_…
Murmushi tayi ta d'auki kayan abincin ta bishi bedrum d'insa...
A tsorace ta tura k'ofar ta shiga,yana zaune kan Sofa ya dafe kanshi...
Ga abincinka nan ko sai kayi wanka?..
Cike da mamaki ya d'ago kai Ya kalleta dan baima ji shigowarta ba,
Janyo flask d'in yayi ya bud'e cous-cous d'in..
Dad'i taji sosai dan ganin zaici abincinta..
Bata ankara ba kawai jin saukar abincin tayi gaba d'aya a jikin ta..
Ta d'ago kai zatayi magana kawai taji saukar ruwan lemo a fuskarta...
Da sauri tasa hannu ta rufe fuskarta...
Idan kika k'ara shigowa d'akina wallahi sai kin raina kanki banza dak'ik'iya Mara hankali da tunani...
Cikin kuka ta mik'e tsaye tace "Kaine Mara hankali kaida bakasan darajar aure ba bakasan yadda zaka tattali matarka ba....
Mari ya wanke ta dashi tare da hankad'a ta,fad'uwa k'asa tayi ta bugu sosai....
ya b'ata rai yace idan kin d‘aukeni sakaran miji to ki ajje wannan a ranki.
Ya fice ya barta anan tana kuka.
Sadeey&Nafsal
07038363997
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S. Adamu_*
*Dedicated to beebahluv💖 & Munay💞*
3⃣1⃣▶3⃣2⃣
Me zan gani?,ta fad'a tana ja da baya..
Dama d'an giya aka aura min d'an shaye shaye...
A buge yake kallonta cikin maye yace "ke ni kike cewa d'an giya?to wallahi sai kin gane kurenki" biyota yayi cikin tangal tangal kamar zai fad'i, da gudu ta bar falon ta shige bedroom d'inta ta turo k'ofa..
Stool ta janyo ta zauna tare da dafe goshi..
Wannan wane irin bala'i ne, dama baba yasan d'an shaye2 ne ya aura min?
Shin meyasa baba ya tsani 'ya'ya mata dan Allah ya yomu a mata sai kuma ya tsangwame mu?to idan mazan ya haifa mene fa................Saukar duka taji a jikinta zubur ta mik'e tsaye..
Wa kike cewa d'an giya? A tsorace ta kalleshi dan ya bugu sosai...
Ta matsa da baya tace "dan Allah kayi hak'uri wallahi bada kai nake Ba" ya za'ai nace maka d'an giya?..
A hankali ta matsa ta kama k'ofa zata fita tajita a rufe gam..
Jikinta ya fara rawa a tsorace ta kallesa tace "yaya *Aryaan* dan Allah kayi hak'uri"
Zaginta ya fara ta uwa ta uba,abinka da mutum a buge...
Hannunta tasa ta rufe bakinta a kid'ime ta fara matsawa da niyyar ta shiga toilet ta rufe...
Ko bakin k'ofar bata bari Ba ya janyo ta ya fara duka da wayar wuta..
Ihu salatin magiya babu Wanda batayi Ba amma a banza...
Yayi mata lilis sannan ya zube anan ya kyalaya amai mai shegen wari dan zai iya Saka mutum amai...
Anan ya barta cikin maye ya fice ya shiga d'akinsa...
Tafi awa a kwance a k'asa tana kuka,duk rashin kunyar da tayi a baya bata tab'a yin nadama Ba sai yau..
A hankali ta tashi zaune kawai ganin jini tayi yana zubowa daga fuskarta,tayi saurin tab'a goshinta taji wani azababben zafi.....
'Dan kwalinta tasa ta d'aure goshin danta tsayar da zubar jinin...
Jikinta duk ciwo yake mata ga sawun dukannan duk ya tashi a jikinta guraren duk sunyi jajir...
Cikin dauriya ta tashi a daren nan ta wanke inda yayi amai ta goge Allah ya taimaka bai tab'o mata carpet ba...
Bin d'akin tayi da turaruka ta feshe...
A hankali taja k'afarta ta bar d'akin duk da batajin k'arfin jikinta..
'Dakinsa ta shiga cikin tsoro da fargaba,can tsakiyar gado ta hangoshi ya gudundune jikinsa yana bacci,blanket ta janyo ta lullub'eshi sannan ta kashe wuta taja masa k'ofar..
Tana shiga d'akinta itama ta kwanta,sai me?
Zazzab'i rum ya rufeta ga ciwon kai kamar zai tsage...
Har akai kiran sallar asuba idonta biyu,
Da rarrafe ta shiga toilet tayo alwallah tayi sallah,ta san *Aryaan* bai tashi ba amma ciwon da takeji bazai barta ta tab'uka komai ba.
*_08:55am_*
Mik'a ya farayi sannan Yayi addu'ar tashi daga bacci Ya tashi zaune tare da kallon agogo...
"Subhanallah" ya fad'a yana mamakin makarar da yayi cikin sauri ya sauka daga kan gadon tare da shigewa toilet...
Bayan ya gabatar da sallah yana cikin addu'oi hankalinsa ya kai kan blanket d'in dake kan gadon...
_bayan nayi bacci yarinyar nan ta shigo ta lullub'e ni_
Yayi murmushi sannan kuma yayi shiru tare da recalling duk abubuwan da suka faru a daren jiya..
"Wat a caring wife" ya fad'a a fili yana murmushi...
Gaskiya *Arish* yayi dace a rashin hankali da shishshigi irin na yarinyar nan sai kace Mara zuciya..
Ya fad'a lokacin da yake nad'e sallaya...
K'ofar d'akinta ya turo,ya hangota lullub'e da bargo...
Keeee!me kike nufi da kika zauna kina shak'ar bacci kina nufin uwatace zatayi aikace aikacen can part d'in?
Daga cikin bargon hawaye duk ya jik'a filon da take kwance a kai karkarwa kawai take cikin jin zafin ciwon jikinta..
Magana fa nake miki bazaki tashi Ba?..
A hankali ta zame bargon ta tashi zaune,idonta a rufe amma hawaye ne ke zuba, a hankali tace "yaya zazzab'i nake kayi hak'uri"
Cak ya tsaya lokacin da yaga d'ankwalin da ta k'ulle goshinta dashi guri d'aya duk ya jik'e da jini...
Dukan da yayi mata jiya ya tuno,
_idan momma ta gani na shiga uku_ ya fad'a a zuciyarsa tare da barin d'akin..
Itama kwantawa tayi ta cigaba da kukanta....
Da first aid box ya dawo d'akin ya hayo kan gadon tare da cire blanket d'in dake jikinta...
Tsigar jikinta duk ya tashi ta Saka hannu tana k'ok'arin janyo blanket d'in,shi kuma yayi saurin matsar dashi gefe..
A hankali ya d'agota ya jingina ta da fuskar gadon ya fara treating d'in ciwon,tana kuka tana goggocewa ya rik'eta gam a jikinshi ya wanke mata ciwon da auduga da spirit sannan ya nad'eshi da bandage...
Da kansa yaje ya had'o mata tea mai kauri,sai da ya tsareta ta shanye sannan ya bata magungunan
zazzab'i dana ciwon jiki..
Ya kwantar da ita amma ya hana ta lullub'a dan zazzab'in ya sauka...
Yana nan tsaye ya kafa mata idanu ita kuwa a kwance take tana karkarwar sanyi ga zazzab'i jikinta kamar garwashin wuta...
Yau ce rana ta farko daya fara tausayinta da kuma jin tsananin sonta a zuciyarshi...
Sai yau ne yake ji a jikinsa inama Sumayya matarsa ce, ayau kam ya yarda *Arish* yayi dacen mata...
Da sauri ya fita daga d'akin yaja mata k'ofa dan kar shaid'an yayi masa hud'uba akan matar k'aninsa.
*Ku biyo mu*✍
_Sadeey 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S. Adamu_*
*Dedicated to beebahluv💖 & Munay💕*
3⃣3⃣▶3⃣4⃣
Wanka yaje yayi sannan ya shirya,sai da ya gama komai sannan ya dawo d'akin Sumayya ya tsaya kanta lokacin har tayi bacci ga gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta da alama zazzab'in ya fara sauka..
Murmushi yayi sannan ya fita..
A hanyarsa ta zuwa office yana tafiya yana tunanin Sumayya ya kasa tantancewa tsakanin *SO KO TAUSAYI*nta yake?
Har ya k'arasa office babu kuzari a jikinsa..
*12:00pm*
Tun daga k'ofar falo Zahra ke sallama amma shiru babu amsa...
kanta tsaye ta shiga bedroom d'in Sumayya,
A kwance ta ganta ta gudundune jikin ta ga zuffa duk ta had'a..
Zama tayi a gefen gadon ta d'anyi shiru sannan tace "bara na k'yaleki tunda bacci kike yi na dawo anjima".
*01:11pm*
Ta farka daga baccin,cikin hanzari ta shiga toilet tayi alwallah ta gabatar da sallahr Azhar sannan ta shiga kitchen dan ta had'awa *Aryaan* lunch duk da tasan baya cin abincinta..
jollof d'in macaroni tayi Wanda yaji kifi da hanta tare da vegetable,sannan ta d'akko coconut a fridge ta fasa tayi coconut juice Wanda yaji liquid milk da vanilla…
Komai nata cikin Sauri takeyi kasancewar lokaci ya k'ure mata..
Sai k'arfe 02:56pm sannan ta gama,ta had'a komai akan dinning table.
Gaba d'aya gidan tabi ta share tayi mopping ko ina sannan tabi gidan da turaren wuta d'an Maiduguri Wanda Rabi'at ta bata..
Ana kiran sallahr la'asar ta shiga wanka.
Ta fito Sanye da riga da skirt na swiss lace,blue green ne mai ratsin golding a jikinsa,ta d'auki necklace da earring had'i da bangle duk golding ta Saka a jikinta...
Tayi kyau sosai kyaunta ya k'ara bayyana kana ganinta kaga *Black Beauty*..
Ko ina k'amshine ke tashi a gidan.
Sai da tayi sallahr la'asar sannan ta nufi part d'in momma dan yau throughout bata lek'a ba..
Zuro hijabin nata tayi ya rufe mata bandage d'in dake nad'e a goshinta dan kar momma ta ganota..
Aikuwa bata gane ba kasancewar momma ba ta fiya kallonta ba,Zahra ce ma taso ta gano ta saboda yadda ta lullub'e kanta,Asiya kam ko kallo bata isheta ba.
Ta fito zata koma part d'inta taci karo dashi shima yana fitowa daga mota...
Da sauri ta k'arasa gurinsa ta saka hannu ta karb'i manya manyan ledojin da suke hannunsa..
Ga mamakinta sai taga ya sakar mata yana murmushi..
Cikin k'warin gwiwar data samu tace "Sannu da zuwa"
"Yawwa sumayyah ya gidan"
"Lafiya lau" ta amsa tare da wucewa ciki cike da mamaki..
Kan kujera ya zauna tare da sakin ajiyar zuciya,ajje kayan tayi akan center table sannan ta zauna k'asa ta sake cewa "sannu da zuwa"
'Dagowa yayi ya kalleta sannan yace "ya jikinki?"
Kanta a k'asa tace "jiki da sauk'i na warware ai"
"Kinsha magani?"
"A'a"
Cikin kulawa yace "banajin kinci abinci ma,bara na d'akko miki magani"
Har ya tashi,tayi saurin tashi ta tare shi da hannunta kamin tace "yaya *Aryaan* kayi wanka kaci abinci tukunna"
Kallonta kawai ya tsaya yi yayinda yaji bugun zuciyarshi na k'aruwa...
Ya kauda kai gefe yace"idan kinsha maganin sai na ci abinci saboda yanzu lafiyarki ce tafi damuna"
"Ai nima banci abinci ba yaya,kayi wanka sai muci sannan nasha maganin"
"Okay" ya fad'a tare da shigewa side d'insa.
Yana zaune kan dinning ya zuba mata ido tana had'a masa abinci sai da ta gama ta tura masa,ya kalleta yace "nida wa wannan?"
"Kai kad'ai"
Nida ke dai ai wannan ya min yawa..
Duka zaka cinye fa,ta fad'a cikin jin dad'i..
Ta zuba d'an kad'an sannan ta zauna..
Yana ci yana kallonta cike da mamakin yadda ta iya girki haka,
_gaskiya *Arish* yayi sa'ar mace dama nine na samu mata irin Sumayya_,
_Dole ne na rage shiga harkarta dan gudun karna fad'a tarkon shaid'an_…
Yaya *Aryaan* ya naji kayi shiru?ko girkin nawa baiyi maka dad'i ba?..
Ta fad'a cikin tsokana.
Tura abincin gefe yayi ya b'ata rai tare da jan tsoki ya tashi ya bar gurin...
Cike da mamaki ta bishi da ido.
*Tofaaaaaaaaaaa*✍
_Sadeey 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: [3:52PM, 1/28/2017] Nazly baby:🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisah S Adam_*
*Dedicated to beebahluv & Munay*
3⃣5⃣▶3⃣6⃣
Har sai da ya shiga side d'insa sannan ta d'auke idonta daga kansa,
Wasu hawayen takaici ne suka zubo daga fuskarta,tasa hannunta ta goge sannan ta sake kallon abincin daya fara ci ko spoon uku baiyi ba ya ajjeshi,tashi tayi ta tattara komai ta kai kitchen sannan ta fito ta zauna kan kujera tare da fashewa da kuka mara sauti..
_15 minutes later_
Daga d'akinsa ya fito cikin shirinsa da alama fita zaiyi,har ya wuce ta sannan ya dawo ya ajje mata leda akan center table d'in "ga maganinki ki daure kisha yanxu cox anjima ma zakisha"
Ta d'ago kai ta kalleshi muryarta na rawa tace "bazan sha ba gwara na mutu,kuma kafin ka dawo zaka tarar da gawata"
Ta ruga da gudu cikin kuka tayi side d'inta..
Da sauri ya bita cikin tsananin mamakin kalamanta,
Yana tura k'ofar yajita a kulle..
"Ki bud'e Sumayya dan Allah"
Shiru tayi tana saurarensa wannan ce rana ta farko data fara jin ya kirawo sunanta..
"Kiyi hak'uri ki bud'e pls" yana fad'a yana jijjiga k'ofar..
"Ka kyauta *Aryaan*" kamar daga sama yaji muryar momma..
Da sauri ya juya ya kalleta a tsorace,
"Me kayi mata?"
Bakinsa na d'an rawa yace "momma babu abinda nayi mata"
Cikin b'acin rai ta k'arasa jikin k'ofar tayi knocking tace "bud'e 'yata nice"
Jin muryar momma yasa tayi saurin bud'e k'ofar..
Fuskarta sharkaf da hawaye, "me akayi mini?dukanki yayi?"
Kai ta girgiza alamar a'a..
"Meye a goshinki to?"
Da sauri ta dafe gurin dan har ta manta akwai ciwo ma..
"Bigewa nayi d'azu da safe"
Kai kawai ta girgiza tare da jan hannun sumayya suka bar gurin..
Har bakin mota ta jata,kamar ta tambayi momma ina zata kaita amma sai tayi shiru dai..
Haka momma ta shiga mota ta jasu,
A k'ofar wani gida suka tsaya,ginin gidan ginin k'asa ne madaidaici.
Sallama suka shiga cikin gidan kai tsaye suka zarce har d'akin,momma na rik'e da hannunta kamar zata gudu inta saki.
"A'a habiba kece yau a gidan"matar dake kwance kan darduma tayi maganar lokacin data tashi zaune..
"Wlh inna nice"
"To ku shigo maraba maraba".
Bayan sun gaisa ne inna ta kalli sumayya tace wannan itace amaryar *Arish* d'in"
Gaban momma yayi mugun fad'uwa da sauri tace "a'a matar *Aryaan* ce"
"Af na manta ne,ai baku tab'a kawo mana ita mun gaisa ba"
"Wlh inna ina ta son samun lokaci in kawota to Allah baiyi Ba"
"Allah sarki sannunki amarya" kanta a k'asa a hankali ta furta "yawwa"
Momma ta gyara zama tace "inna gurin Malam nazo dan ya warware mana matsala tsakanin *Aryaan* da ita"
"Yana d'aki bari nayi masa magana.
Ta tashi ta fita..
Tare da Malam suka shigo,ya zauna gefen gado sannan yace "ai banji shigowarku ba"
"Malam ina yini" momma ta gaidasa cikin girmamawa,sumayya ma ta gaidasa.
Shiru sukayi na wani lokaci sannan momma ta fara kuka..
Abin ya bawa Sumayya mamaki ainun,
"Meye faru ne wai?"
Malam ya tambaya cikin mamaki,momma ta goge hawaye ta kallesa sannan tace "malam na gaji da abinda *Aryaan* yake ma yarinyar nan duba kaga yanxu yadda yayi mata duka kalli fuskarta,na tabbatar jikinta ma ya fashe"
"Me tayi masa haka"
"Tak'i ta fad'a min gaskiya"
Tashi yayi sannan ya kalleta yace "ki biyoni"
Babu musu momma ta bishi sumayya na nan zaune itada inna.
Suna tsaye a zaure Malam na yi mata bayanin yadda za'ai,
"Ki daure kusan yadda za'a gayama mahaifinsu gaskiyar cewar ba *Aryaan* bane mijinta *Arish* ne saboda gudun kar wani abu ya faru azo ana dana sani"
Cikin nutsuwa momma ta kallesa tace "Malam wlh aurena zai iya mutuwa Idan har na fad'awa Alh cewar Sumayya matar *Arish* ce,zai ce nayi wasa da hankalinsa,kuma *Aryaan* duk kwanan duniya sai nayi masa nasiha akan yaji tsoron Allah ya rik'e amanar k'aninsa tunda yasan cewa Ba matarsa bace ita kuma tana tunanin shine mijinta,baya da hujja da zai koda tab' a yatsarta bare har Ya doketa amma ya nuna min ban isa dashi Ba"
Malam yace "ki barni dashi,yanxu abinda za'ayi shine ki bar yarinyar anan zuwa wani lokaci,idan maigidan naki ya tambaya kice tana nan saboda *Aryaan* yana cin zalinta kuma shi babu matakin dazai d'auka idan ma kin gaya masa tunda shi a nashi al'adar babu auren talaka babu k'aunar talaka a ransa to ki barta a nan har *Arish* ya dawo,shi kuma ai baya da damar ya tambayi inda take tunda yasan Ba mallakinsa bace"
"Hakane Malam,dama mahaifinsu bazai tambaya Ba tunda bayason ganinta ma,yanxu idan na koma zan aiko da kayanta nagode Malam Allah yayi jagora"
Ta k'arasa maganar tana hawaye..
"Ki daina kuka habiba insha Allahu komai zai zama daidai".
Har bakin mota suka raka momma sai da Sumayya taga dagaske momma barinta zatayi sai ta fara hawaye,
Cike da mamaki momma ta juyo tana kallonta.
_by_
_Sadeey & Nafsal✍_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: [9:50AM, 2/4/2017] SaNaz deeyah:
🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_WRITTEN BY_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S. Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
3⃣7⃣▶3⃣8⃣
Cikin tsoro momma ta dawo kusa da sumayya ta fara jijjigata tana fad'in "mene kike kuka?ko dai ya miki wani abune?ki fad'amin me ya miki?"
A lokacin ne kukanta ya k'aru ta cigaba dayi Ba tare da tace komai Ba,momma kam ta tsorata sosai da ganin yanayin sumayya dan haka ta kalli Malam tace "Malam ka gafarceni zanje nayi bincike akanta dan wallahi na tsorata da lamarin"
"Ban amince ki tafi da ita ba ki barta a nan kome ke faruwa kimin waya"
Jikinta ba gwari ta shiga mota ta tafi su kuma suka koma gida dan har a lokacin Sumayya kuka take...
A bakin gate ta ganshi zaune kan plastic chair duk ya duburbuce daya ganta,kana kallonsa zaka hango tsantsar damuwa a tare dashi...
Cikin hanzari tayi parking ta fito fuskarta babu annuri take kallonshi,shima a sanyaye ya taso ya k'araso gurinta.
"Me kayiwa Sumayya da har take kuka saboda na rabata da kai?" Abinda ta fad'a kenan cikin b'acin rai,sai da gabansa ya fad'i sannan ya kalleta ya juyarda kansa gefe yace "babu abinda nayi mata"
"Kaji tsoron Allah *Aryaan* idan kasan kayi mata wani abu ka sanar min muyi wa tufk'ar hanci"
Cikin damuwa yace "momma idan nayi mata wani abu Allah ya k'onani,idan baki yarda Ba zan dafa miki al'k'ur'ani"
Kallonsa kawai take cike da b'acin rai ta sake fad'in "bakai ba ita daga yau na rabaku bazaka sake ganinta ba har sai mijinta ya dawo" gabansa Ba k'aramar fad'uwa yayi ba, sai dai kawai bashi da damar cewa komai..
Motarta ta koma taja tare da shigewa cikin gidan…
*```NIGHT ```*
A daidai inda ake parking motoci yayi parking tasa motar,babu b'ata lokaci ya fito ya nufi k'ofar da zata sadashi da gurin...
Club ne Wanda ya tara 'yan mata da samari mararsa kamun kai,ko wanne da irin shigarsa dan Idan kaga wata sai ka rantse Ba musulma bace,
But a hakan sun amsa sunan musulmai kuma yawancinsu hausawa da Fulani ne...
Wasunsu suna filin rawa ko wacce da saurayinta tanayi,wasu sunsha sun bugu wasu suna gefe rungume da samarinsu suna alfasha wasu suna zaune suna hira yayinda wasu anjasu d'aki,kowa da abinda yakeyi..
Empty table ya nufa yaja kujera ya zauna tare da Kiran number *Samon*(frnd d'insa ne) 'yan mata kala2 sun kawo Kansu amma ya wulak'antasu dan yanxu baya cikin mood d'in..
Babu jimawa samon ya iso gurinsa shima yaja kujera ya zauna tare da kallon *Aryaan* "lafiya naga duk ka sauya Aryaan?" Ajiyar zuciya yayi sannan ya fara magana "kasan komai akan auran k'anina *Arish* kasan matarsa ni nake rik'onta amma babu abinda ya tab'a shiga tsakaninmu"
"Nasan komai *Aryaan* to meya faru ne?"
"Suleman na kamu da son Sumayya har inaji a jikina bazan iya rabuwa da itaba kona awa d'ayane,bakaji yadda zuciyata ke harbawa ba,momma ta d'auketa ta rabamu da ita saboda tana tunanin ina cutarta ko kuma zan iya mata wani abu na rasa mafita wallahi bacci ma ya gagareni"
Dariya samon ya shek'e da ita sosai sai da yayi mai isarsa sannan ya kalleshi ya sakeyin dariya yace "sai da na fad'a nace sai kazo kanason sumayya amma kak'i yarda wai kai ka tsaneta,to yanxu ina tsanar?mace ce fa kissosunsu yawa ne dasu aboki"
"Yanxu mafita nake nema samon inason a maida aurenta dani tunda Dama da sunana aka aura mata *Arish*,kuma tana sona sosai sannan Muna waya da *Arish* but bai tab'a tambayata ita ba ina tunanin ya samu 'yan matan turai"
Murmushin mugunta samon yayi sannan yace "wannan ai abune mai sauk'i idan kaje gurinta a matsayin mijinta Kayi amfani da ita babu Wanda ya sani tunda ita ta d'auka Kaine mijinta I thought ka biya buk'antunka da ita Ashe kai kananan kana gadi"
*Aryaan* ya numfasa yace "hakan ma za'ayi tunda na lura tana sona nasan zata amince a duk lokacin Dana buk'aci ta bani kanta *MENE AIBUNA* dan nayi amfani da macen da aka aurawa k'anina amma da sunana akayi amfani dubunnan jama'a sun shaida Sumayya matar *Aryaan* ce hatta mahaifinta da nawa,momma dasu malam ne kawai suke cewa *Arish* mijin Sumayya,daga yanzu na soke *Arish* babu mahaluk'in daya Isa rabani da ita zan Nuna mata soyayyar da bata tab'a gani a rayuwarta Ba"
Yana gama fad'a ya mik'e tare da shirin barin gurin..
Suleiman ya rik'o hannunsa yace "ina zuwa kuma?"
"Zanje nayi fighting akan a dawo min da matata"
"Hahahah gaskiya abokina wato har ta zama taka"
K'warai kuwa"
"Yau bazaka d'auki beb ba?"
"No need" ya fad'a tare da barin gurin.
Nafsal
07038363997
Comments only👌
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: [4:58PM, 5/5/2017] SaNaz: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_Nafisah S. Adamu_*
*&*
*_SaNaz deeyah_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
3⃣9⃣▶4⃣0⃣
Ranar kasa bacci yayi daga ya kunce wannan sai ya d'aura wannan ya rasa mafita,ya kasa samun hanyar da zai bi dan dawo da Sumayya gidanshi..
Washe gari misalin k'arfe goma na safe ya shirya tsab' sannan ya nufi part d'in su momma....
A falo ya tarar da ita tana goge2 Randa Ba k'aramin b'aci yayi ba,ya kalli Asiya dake zaune kan dining table tana ta lallatsa waya ya daka mata tsawa tayi saurin mik'ewa a raxane.
Cikin b'acin rai ya kalleta ya cigaba da fad'in "Ashe baki da d'a'a baki da mutumci?kina ganin momma na aiki bazaki karb'a kiyi ba?haka kika Zahra nayi?wato k'anwarki ma ta fiki hankali ko?"
Dayake tana tsoronshi sosai dan haka tayi shiru tana kallonshi, "ki karb'a ki cigaba kafin na sab'a kamanninki" da sauri ta nufi gurin momma ta k'arb'i towel d'im tana gunguni.
"Me kike cewa?"
"Ni babu abinda na ce!"
Yayi tsoki sannan ya kalli momma "magana nake son yi dake momma"
"Okay muje d'aki"
Babu musu ya bita it's kuma Asiya ta bishi da rakiyar harara.
Yana zaune k'asan carpet momma kuma tana zaune kan sofa,duk Kansu sunyi shiru can *Aryaan* yayi k'arfin hali yace "Momma maganar Sumayya kina ganin hakan da kikayi daddy bazai fahimci wani abu ba"
Ta kallesa sannan tace "koma zaiyi bazan dawo da ita Ba ka lahanta ta saboda amanarmu ce *Arish* idan yaxo ya sameta a haka bazai tab'a jindad'i Ba"
"Momma Baran sake b'ata mata rai Ba insha Allah bazan sake shiga harkarta ba ni kawai banaso daddy yazo yayi ta miki fad'a"
"Kai ka zab'i haka ai kai kaso ayimin tunda harka kasa bin umarni na"
"Am so sowie momma wlh Baran sake Ba" ya marairaice sosai yana rok'onta..
Tayi smiling tace "shikenan zan dawo da ita ka guji sab'ama alk'awari"
"To momma insha Allahu".
A ranar momma taje ta dawo da sumayya domin itama tana son zama da ita,nasihohi sosai tayi masu akan su zauna lafiya sannan ta barsu tayi part d'inta..
Kusa da ita *Aryaan* ya dawo tare da rik'e hannun Sumayya "ki yafema mijinki ki gafarceni nayi alk'awarin bazan sake b'ata miki rai ba zan nuna miki son da ban tab'a nuna wa wata 'ya mace ba"
Jikinta na karkarwa a ranta ta furta _zan zauna dakai a duk yadda kake *Aryaan* zan koyawa zuciya ta sonka fiya da Wanda take yi maka ada xan hanaka shaye2 kamar yadda ko wace mace ke gyara mijinta_ tuni hawaye ya siyayo daga idonta,a rud'e *Aryaan* ya rungumeta tare da goge hawayenta...
A lokacin yayi mata alk'awari kala kala na kasancewa da ita har k'arshen rayuwarsu
Haka suka yini suna yima junansu alk'awarin rik'e junansu cikin aminci da k'aunar juna...
Tana kwance kan gadonta tana jiran dawowar *Aryaan* yace mata ta jirashi yanxu zai dawo yana son yayi surprising nata,a zuciyarta tanata sak'e2 abinda zai kawo mata na surprise kawai *gentle* ya fad'o mata a rai..
_Allah sarki gentle ko a wane hali yake yanxu?ko su Fatima na kular min dashi?_
Hmmmm tayi ajiyar zuciya sannan ta cigaba da sak'e sak'enta, _Ashe wahalar da xansha a gidan miji ba mai d'orewa bace,Ashe *Aryaan* xai dawo da bakinsa ya furta kalmar so a gareni,Allah sarki umma tayi hak'urin zaman gidanmu amma duk da haka har yau tana shan wahala_
_Saboda ta haifemu a 'ya'ya mata,ko sai yaushe baba zai fara k'aunarmu har yanxu bama rayuwa da dad'i har sai baba ya fara sonmu muma my zama masoya ga iyayenmu_…
A haka har *Aryaan* yazo ya sameta "baby xo muje falo kiga wani abu" babu musu ta sakko daga gado yaja hannunta suka fita falo,
trolley har biyu manya manya ta gani a ajje,da sauri ta d'aga kai ta kallesa yayi murmushi yace "duk nakine baby,muje ki gani"
Jikinta babu k'wari ya janyo hannunta ya zaunar da ita Ya bud'e ya fara nuna mata "English wears ne masu kyaun gaske tare da sleeping dress kala kala,sai turaruka masu k'amshi,
Bayan ya gama nuna mata sannan ya rufe ya bar guda d'aya a waje..
Ya juyo ya kalleta a hankali ya fara magana "baby wannan ita nake son kimin kwalliya da ita yau domin mu raya darenmu na farko a yau ko dan Neman d'orewar zaman lfyar mu fatan zaki bani had'in kai"
Kanta a k'asa ita kunyarsa ma duk ta mamayeta a haka ya gama surutansa ya barta ba tare da ta bashi amsa ba.
*11:38pm*
Ta gama feshe jikinta da turaruka ta mulka mai a gashinta sai shek'i yake ta janyo rigar da *Aryaan* ya bata ta bud'e,kunya ce ta kamata har sai da ta rufe ido..
_gashi tun 10 *Aryaan* yamin waya yana jirana gaskiya inajin kunyar inje masa a haka duk da mijina ne shi._
wata shawara ce tazo mata a ranta Dan haka ta d'auki rigar ta Saka sannan ta zura dogon hijabi..
A hankali take tafiya tana jin d'an fad'uwar gaba tana tunanin yadda zata kaya a darenta na farko da mijinta..
Har zata tura k'ofar d'akinsa kawai taji maganarsa k'asa2 tayi saurin kara kunnenta a gurin..
_yes insha Allahu yau xan cika burina babu mahaluk'in daya isa ya hanani yaune ranar da take tunanin zai kasance Daren aurena da ita na farko_…
wani jirine ya fara d'aukarta da k'yar ta tsayar da hankalinta ta cigaba da sauraren maganganun *Aryaan* Wanda suka xo mata kamar a mafarki..
_shi kansa *Arish* bai tab'a tambayana ina Sumayya ba duk wayar da muke dashi it means bai damu da ita ba ko kuma ya daina sonta ne ya samu wata a turai bayan yasan irin case d'in da akasha akan auransa da ita Dan daddy ma bai Sani ba sai matar kawai ya gani shine momma ta b'oye tace masa matata ce........_
_Kai bakaga yadda daddy ya zageni ba ni bansa kan zance ba yace na bar outside har abada,ya mayar da *Arish* can ga momma ta Riga tace Sumayya matata ce dole aka hak'uri *Arish* ya koma can shi kad'ai ni kuma kullun cikin nasiha ake min inji tsoron Allah in guji sharrin shad'an kar wani Abu ya had'ani da ita matar k'anina ce in rik'e masa ita amana kafin asan yadda za'a gayawa daddy gaskiya_………
_Kuma kasan me?da sunana aka d'aura auren amma dai a matsayin matar *Arish* kaga har danginta duk ni suke gani a matsayin mijinta_…
_yanxu sonta nake Dan ganinake nafi *Arish* sonta duk da lokacin da yaga daddy ya hana auren ance kusan hauka yayi saboda yana mutuwar sonta dan momma tace a yadda ta ganshi tabbas idan ya rasata zai shiga matsala.._
_Wlh I.b nima ban Sani ba ko son shawa'ane kona gaske nidai nasan a da ko ganinta bana son yi amma a yanxu kam babu mai rabamu sai Allah saina dage akan ita matata ce kuma babu Wanda zai rabamu idan nace ni mijinta ne domin daddy ma haka aka ce masa kuma daddy kaifi d'ayane_…………
_I.b momma sai dai ta yafemin zaman zina kuma ba akaina aka fara ba,nikam idona ya rufe bana ganin kowa sai Sumayya d......................._
Ta kasa k'arasa jin labarin dan jikinta gaba d'aya tsuma yake da k'yar ta iya d'aukar k'afafunta ta koma d'aki,tana shiga ta Saka key tare da fad'awa kan gado tana kuka Mara sauti kuka na takaici tare da dana Sani...
Haka ta rik'a jin bugun k'ofarta yana tayi yana cewa ta bud'e har ya gaji ya bari..
Haka ta kwana tana kukan takaici bacci kam sai dai b'arawo tayi ta farka.
*_Muje dai my readers_*✍
_Sadeey S 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: [8:18PM, 5/6/2017] SaNaz:🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
4⃣1⃣-4⃣2⃣
Da asuba da k'yar ta samu tayi sallah tayi addu'oi da azkar data saba amma yau kam bazata samu damar yin tilawa ba saboda idan tanayi zai dunga katsewa cox tana cikin damuwa..
*06:00am*
Tana zaune kan gado hawaye nata zuba daga idonta duk da idon ya k'ank'ance saboda kuka amma ta kasa daina wa,
_ya zanyi yanxu?idan ya ganni tabbas zai iya tab'ani tunda shi gani yake babu_ _matsala,meyasa baya tunanin lahirarsa?shin meye mafita?_
Sak'e2 take tayi a zuciyarta amma ta kasa samun mafita ita tsoron fita ma take daga d'akin dan yanxu bata k'aunar ganin *Aryaan*
Shin Waye *ARISH?*,Meyasa ya aureni bayan baya sona?
Tayi maganar a fili tare goge hawayenta...
```lokacin dayaga daddy ya hana auren kusan hauka yayi don yana mutuwar sonta.......```
Maganar *Aryaan* ta jiya ce ta fad'o mata a rai..
_yana sona meyasa ya tafi ya barni baya ko nemana?ko dai ya daina sona kamar yadda *Aryaan* ya fad'a ko kuma ni d'in ba type d'insa bace?shin meyesa ko maganarshi ba'a tab'a yi min ba?to shi d'in waye shi dolene insan w......._
Bugun k'ofar da akayi ne yasa ta saurin kallon k'ofar a tsorace dan ta san ko wane ke bugun,
"Sumayya wlh idan baki bud'e k'ofar ba zan b'allata" taji yayi maganar da k'arfi a tsorace ta sakko daga kan gadon a hankali ta furta "na shiga uku" sannan ta matsa jikin wardrobe ta janyo doguwar rigar atamfa ta Saka sannan tasa hijabi da sauri ta k'arasa jikin k'ofar kasancewar mugun bugu da taji yana yi...
Tana bud'e wa suka had'a ido yayinda taji wani mugun bugun zuciya, "meya sameki naga idonki ya kumbura?"
Tayi shiru ba tare da tace komai ba "kuka kikayi ko?" Da sauri ta girgiza kai,sai kuma hawaye ya zubo mata bata san lokacin da tace "umma da 'yan uwana na tuna" sai wani kukan ya sake kubce mata..
ya rungumeta a jikinsa tare da dafe goshinta "haba baby ni kuma ai kin sakani a damuwa tun jiya nake tunani ko laifi na miki nazo nayi knocking kika k'i bud'ewa pls karki sake azabtar da mijinki nayi alk'awarin zan kaiki kiga umma kinji"
Ita kam a tsorace take a ranta sai fad'i take
_kaji tsoron Allah yaya *Aryaan*_
Gashi ya matse tsam ta kasa k'watar kanta,sai da kanshi ya lura bata so ya cikata,
"Me zaki yi mana na break fast?ko tare zamu shiga kitchen d'in" jikinta na tsuma tace "zanyi komai" smiling yayi a zuciyar ya furta _wata rana ke zaki kawo kanki_,
Ya fita ya barta a tsaye anan..
_Meyasa Arish?meyasa ka bar matarka a hannun mazinaci Wanda kake tunanin zai rik'eta amma yanason cin amanarka tabbas ka tabka *babban kuskure* bakasan wannan abin hatsari bane,insha Allahu daga yau bazan k'ara bari mijin da ba nawa ba ya kusance zan Kare mutuncin aurena har ranar da zan karb'i takardar saki a hannun *Arish* koma waye shi_…
Hawaye sosai yake bin kuncinta tana gogewa,
tana nan tsaye ta kasa tab'uka komai har takwas tayi sannan ta nufi gidan Rabi'at...
A tsakar gida ta had'u da ita tayi saurin tararta tare da fad'in "lfya sumayya?meya sameki na ganki a haka?"
Kuka sosai Sumayya ta fara hakan yasa Rabi'at tayi saurin janta d'aki ta zaunar da ita gefen gado,ta zura mata ido tana ta kuka dan mai kuka ba'a fiya rarrashinsa ba dan kukan k'ilan yasa shi jin sanyi a zuciyarshi..
Sai da tayi mai isarta sannan ta goge hawayenta ta kalli Rabi'at "ina dab da fad'awa halaka Rabi'at"
"Halaka?a wane dalili?"
Hmmm Sumayya tayi ajiyar zuciya ta sauke k'wayar idonta k'asa, "ke kad'ai zan iya fad'awa sirrina domin a yanxu kin tashi daga k'awa kin zama 'Yar Uwa" ta d'anyi shiru har sai da Rabi'at tace "inajinki Sumayya"
_meyasa zaki bayyana sirrinki Wanda bai kamata ace kin tonashi yanxu ba domin in har kika fad'awa Rabi'at tabbas bazata iya b'oyewa mijinta ba_ zuciyarta ce ta ayyana mata haka...
Da sauri kuwa ta juya akalar maganar da fad'in "Rabi'at wlh ina tunanin halin da 'yan uwana suke ciki dan babana bai wani damu damu ba"
"Allah sarki Sumayya ki daina fad'in haka maybe commitment ya masa yawa sai kuke tunanin rashin damuwa ne,dama wannan abinne ya sakaki kuka kika zama wata wujigaga dake"
d'aga kai tayi alamar eh,Rabi'at tayi dariya tace " *Aryaan* da *Arish* suce me su da suke 'ya'ya maza kuma baki ga abinda mahaifinsu ke masu ba kema shaida ce suna shan wahala dagasu har momma"
Da sauri Sumayya ta kalleta tace "waye *Arish* kuma?"
Cike da mamaki rabi'at take kallonta "kina nufin kice baki sanshi ba?"
"Wlh ban sanshi ba"
"Ko *Aryaan* bai tab'a gaya miki shi kuma koda a waya baku tab'a gaisawa ba?"
"To wai meye na mamakin?"
"Dole nayi mamaki mana k'anin *Aryaan* mai Uwa d'aya haka uba ma,bayan bikinki da sati d'aya aka maidashi can turai kamfanin babansu amma ai kinsan case d'inma ko?"
"Eh na Sani amma no ban tab'a ganinshi ba"
"Gaskiya nayi mamaki da *Arish* baixo kun gaisa kafin ya tafi ba kodan yanajin haushin *Aryaan* ne sanadin barin aikinsa dan wlh baiso tafiyar ba amma baxai iya musawa umarnin babznsa ba haka ya fad'awa mijina".
Har kusan k'arfe 10 Sumayya na zaune a gidan tanajin labarin *Arish* da irin hak'urinsa sai da taga mijin Rabi'at neman fita sannan ta tafi.
Wanna tayi ta shirya cikin lace green mai ratsin silver ta yafa mayafi silver tayi part d'in momma,a falonta ta tarar da ita tana breakfast ta samu kujera ta zauna suka gaisa sannan momma tace "bara a mik'o maki abin break ki karya ko"
"A'a wlh a k'oshe nake"
Ta d'anyi Shiru sannan tace "momma dan Allah wayarki zaki aramin xan kira nasiba"
"Ohh har yanxu *Aryaan* bai siya miki ba?"
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba..
"Ki gama wayar yanxu zan kirashi ya kawo miki kuwa" ta fad'a tare da mik'a mata wayar...
Contacts kawai ta shiga ta fara searching number *Arish* tayi s'a ta gani guda uku biyu na 9ja 1 ta outside tayi saurin kara wayar a kunne kamar mai kira ta tashi ta fita,da sauri tayi part d'inta idonta na kan number tana haddacewa aka bata Ankara ba taji tayi karo da mutum,wayar ta fad'i k'asa da sauri yasa hannu zai d'auka a tsorace t...............[Truncated by whatsapp]
*4 more details contact us*✍
_Sadeey S 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: [11:00AM, 5/7/2017] SaNaz: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
*_SaNaz deeyah_*
_&_
*_Nafisa S Adamu_*
```Dedicated to beebahluv & Munay```
4⃣3⃣-4⃣4⃣
"Yaya *Aryaan*" tayi saurin kiran sunanshi,ya juyo ya kalleta..
Cikin zafin nama ta Saka hannu ta d'auki wayar tare da maida hannunta baya,
Cikin tuhuma yace "muga wayar hannunki" jikinta sai tsuma yake cikin dakiya tace "yaya *Aryaan* kayi hkri nayi maka laifi"
Shima sai da yaji bugun zuciya a ransa..
_kardai zargin da nakewa yarinyar nan ya fara tabbata_...
"Bazaki ban wayar ba kenan?"
"Yaya......"
Sai kuma tayi shiru hawaye ya fara zuba a idonta,
"Baki da gaskiya ko?"
Ta girgiza kai alamar a'a
"To meyasa bazaki ban wayar na nagani ba"
"Nasiba zan kira kuma kace karna kirawo shiyasa nake kunyar na maka k'arya"
Ya bud'e baki zaiyi magana wayarsa ta fara ringing, yana d'agawa tayi saurin rab'awa ta gefe ta shige cikin gidan..
Bata tsaya ko ina ba cikin bedroom d'inta ta rufe k'ofa tana numfashi d'ai2...
Sai da nutsuwarta ta dawo mata sannan ta janyo memo ta rubuta numbers d'in *Arish* ta turasu can k'asan wardrobe sannan ta zauna ta kira Nasiba number ma a kashe,dan haka ta d'auki wayar ta maidawa momma.
A zaune ta tarar dashi gaban momma da alama fad'a take masa saboda ransa a b'ace yake,ta samu gefe ta zauna sannan ta mik'awa momma wayar..
"Kin gama abinda zakiyi da wayar?"
"Eh" ta amsa cikin sanyin murya, "to tashi mu tafi" tayi mamakin maganar amma dai ta tashi ta gyara mayafinta.
Basu zame ko ina ba sai sai wani babban shopping mall,har lokacin baice uffan ba sai dai idan momma tace kaje gu kaza sai ya nufi gurin,a haka suka isa gurin wayoyi,momma ta kalleta tace "ki zab'i wacca kikeso" bakinta na rawa tace "ko wacce aka bani tayi min"
Momma da kanta ta zab'ar mata wata techno l8 silver color mai kyaun gaske..
Haka sukaje sumayya ta zab'i sim card guda biyu airtel da mtn,sukayi 'yan siyayya suka dawo gida,
Yana ajjesu ya juya ya fita ya bar gidan momma ta bishi da kallo "yaro ba'a isa ayi maka fad'a ba sai ka hau fushi d'an uwanka ba haka yake ba salihi ne ba ruwansa da fushi sai anyi masa babban laifi"
Ji tayi gabanta ya fad'i lokacin da momma ke maganar,
Momma ta nuna mata duk yadda zatayi amfani da wayar daki2.
*08:13pm*
Tana zaune kan sallaya tana lazumi,ya turo k'ofa cikin sallama ya shigo...
Kanta a k'asa tana ta karanto addu'o'in neman tsari daga sharrin shad'an,shi kuwa sofa ya samu ya zauna ya zura mata ido tana ta adduanta,da taga bayada niyyar fita kawai ta shafa ta kallesa "sannu da dawowa"
Bai ce komai ba illa kallonta da ya cigaba dayi Wanda har sai data tsargu,
"Kin kyauta ko?"
Bata ce komai ba sai fad'uwar gaba da takeyi kawai, ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna tare da tallabo hab'arta "baby kinason mijinki yayi ta shiga damuwa sanadinki?kinfi so naje na nemo mace a waje na biya buk'ata ta ko?"
Hannu tasa ta janye hannunsa daga jikin hab'arta a zuciyarta ta furta
_macuci ko kunya bakaji kana kirana da matarka_
A fili kuma tace "yaya *Aryaan* kayi hkri ka tafi d'akinka yanxu zan biyoka da abincinka"
"Okay korata ma kikeyi"
_idan har ya san kinji maganarnan zai iya miki koma menene ki bi a hankali dashi_
Zuciyarta ta bata shawarar dan haka tayi saurin had'e hannunta sannan tace "yaya ka gafarceni zan maka duk abinda kakeso na daina b'ata maka rai"
Murmushi yayi tare da rik'o hannunta "sure?"
Ta d'aga kai alamar eh,
"Okay! Ina jiran abincina had'e dake gaba d'aya Dan idan kika kawo abincin bazaki fita ba sai da safe kin amince?"
"Na amince"
Haka ya fita yana murnar yau zai kasance cikin farin ciki zai cika kudirinsa,ita kam yana fita ta rakashi da harara...
Kusan minti ashirin da fitarsa tanata zagaye d'akin ta rasa yadda zata yi ga tana tsoron karya zo ya ritsata a d'akin tana nan tsaye kawai wata shawara ta zo mata..
Ta fizge mayafin jikinta ta d'auki wayarta ta rik'e ,ko takalmi babu a k'afarta ta fita,bata zame ko ina ba sai part d'in momma,tun a main parlour ta had'u da Zahra da Asiya zasu fito da sauri Zahra ta rik'ota tace "lfya Aunty?"
Bata San lokacin da hawaye ya zubo mata ba ta durk'ushe a gurin ta rik'e cikinta tana kuka "meya sameki?" Zahra ta fad'a a rud'e
"Zahra zan mutu cikina,wayyo Allah umma"
A kid'ime Zahra ta kalli Asiya pls kirawo momma, harara Asiya ta bita da ita sannan tayi tsaki tace "ni 'yar aikinta ce" ta sake jan tsaki ta fice..
A waya zahra ta kira momma tazo,suka kama Sumayya suka kaita bedroom d'in momma..
"Zahra kira Dr yanxu yazo kar abin yayi k'arfi" itama Zahra a rud'e take da sauri takeyin komai,sumayya kam sai juye2 take a dole ciwon ciki takeyi..
Bayan Dr ya dubata yace masu maybe wani abin taci Wanda cikinta bayaso, ya rubuta magani a lokacin momma ta hau mota ta siyo ta dawo aka bawa Sumayya tasha....
*01:12am*
Ta bud'e idonta ta ganta akan tafkeken gadon momma ita kad'ai d'akin ba wani haske sai dmp lyt,ta mik'e zaune ta kalli ko ina a zuciyarta tace
_ya Allah nagode maka yanxu da banyi haka ba da tuni an kawar min da budurcina ta hanyar haram,Allah ka k'ara kareni,gobe kuma ko wace k'arya zanyi gskya *Arish* ka cuceni da kabarni da igiyar aurenka ba tare da kasan ko wane irin hali zan shiga ba_
Wayarta dake gefe ta janyo ta rubuta numbershi ta outside dan tasan da ita zaiyi amfani "A" kawai tayi saving a number sannan ta bud'e data..
A daren tayi downloading whatsapp ta shiga..
Ba k'aramin haushi taji ba lokacin da taga last seen d'insa baifi minti 2 da sauka ba cikin jin haushi ta fara masa typing.......
_hmmm ka bar matarka a gida ka zauna chatting har dare bakayi bacci ba kana chat da wasu matan_…
Kamar jira yake tayi sending tanayi taga ya dawo online kuma ya fara yi mata typing....
*Alk'alamin mu✍*
_Sadeey S 07035111671_
_Nafsal 07038363997_
[9/23, 7:22 PM] Nafsal: [9:23PM, 5/9/2017] Nafsal: 🍁 *MENE AIBUNA* 🍁
🍁🍁🍁🍁🍁🍁
🍁🍁🍁
_Written by_
_*SaNaz deeyah*_
_&_
_*Nafisa S Adamu*_
```Dedicated to beebahluv & Munay```
4⃣5⃣↗4⃣6⃣
_babu sallama ba introducing kawai sai tuhuma?hala kai journalist ne Dan nasan sune suke tambaya kai tsaye_😊
Ranta ba k'aramin b'aci yayi ba cikin jin haushinsa ta rubuta....
_*Arish* banason wasa_
Shima ya rubuta...
_pls wanene dan Allah nima ka fad'a min ko waye kai,cox ya kamata ace nasan dawa nake chat ko_
Tana karantawa tayi shiru na d'an wani lokacin sannan dabara ta fad'o mata,cikin jindad'i ta fara typing....
_Sunana Nadia Muh'd ni 'Yar gombe ce na samu numberka a wajen wani abokinka inaso mu zama friends idan babu damuwa please_
Tana turawa taga ya fara typing,gabanta sai fad'uwa yake tana sauraren abinda zai ce mata..
_Nadia meyasa kike chatting a wannan lokacin a matsayinki na mace ya kamata ace a wannan lokacin bacci kike ko nafila_
_kaima meyasa kake chatting a wannan lokacin ya kamata ace bacci kake ko nafila_
_lol to aini namiji ne ke kuma kinga macece_
_baka da mata ne da kake chatting a darennan_
😊 _u ar very funny,tym d'inmu ba d'aya bane ni yanxu anan k'arfe 9 na safe_
_ni zaka maida yarinya ko_
_wallahi da gaske make_
_to na yarda yanxu ya maganar friendship namu_
_ki kwanta dai da safe zamuyi maganar_
_ni banajin bacci kona sauka bayi zanyi ba_
_okay meye fa'idar frndship tsakanin mace da namiji?_
_ban gane me kake nufi ba_
_I mean idan Mace da namiji na abota meye ribarsa?_
_riba sosai kuwa_
_ko zaki iya fad'amin kad'an daga ciki_
_idan mun zama abokai zaka gane da kanka_
_kiyi hak'uri Nadia ni a tsarin rayuwa na babu frndship da wata mace,matata ta isheni itace komai nawa itace abokiyar rayuwata,tunda na aureta nayi alk'awarin bazan sake kula wata mace ba,itama nasan tana can tana karemin kanta_
Wani dad'i taji sosai ko babu komai tasan *Arish* har yanxu yana sonta,yanxu kam taji sonshi ya ratsa jinin jikinta duk da bata San ko waye shi ba..
tana murmushi tana yi masa typing...
_a'a ban gane ba ina matar taka?_
_tana nan Nigeria cikin garin Kaduna_
_amma meyasa ka barta baka tafi da ita ba?_
_hmmm kinata Jana ina Baki labari ko?_
_a'a_
_sha'anin aiki mana ai bani kad'ai na baro matata nazo aiki ba_
_hakane_
'Dif taga ya sauka,sai taji babu dad'i domin hirar tayi mata dad'i.. gyara zama tayi ta saka wayar a gaba tana hawaye...
_mijina ka yafe min nayi abinda Allah ya hana,nayi shigar da bata dace ace nayiwa kowa ba in ba mijina ba_…
_Allah ka yafe min nayi komai a rashin Sani amma kome zai faru bazan k'ara bari *Aryaan* yana min abinda bai dace ba_
Da wannan tunanin dashi tayi bacci.
Washe gari tun k'arfe 6 na Safe ta fara jiyo hayaniyar 'yan gidan,ta mik'e ta fita a falo ta tarar da momma na lazimi,ta duk'a ta gaidata cikin girmamawa
"Kin tashi kenan,ko hayaniyace ta tayar dake" kanta a k'asa tace "a'a dama na tashi tun d'azu"
"Ya k'arfin jikinki?"
"Alhamdulillah na warware"
"To Allah ya k'ara sauk'i"
"Amin ya rabbi" ta d'anyi jim sannan tace wa momma zataje ta gyara part d'inta ta tashi ta fita..
A harabar gidan suka had'u da Zahra da sauri ta k'arasa gurinta tana dariya tace "Aunty ya k'arfin jikin?"
"Da sauk'i Zahra"
"Yanxu nake shirin zuwa dubaki wlh aiki muke tayi kinsan yau munada manyan bak'i daga turai"
Gabanta yayi mummunar fad'uwa bakinta har rawa yake wajen tambayar waye zai dawo..
"Triple d'inmu ne xasu xo yau" ajiyar zuciya tayi sannan tace "bara na gyara part d'ina na tayaku aiki"
"Haba Aunty ki huta keda baki da lfya"
"Na samu sauki ai,bara na dawo" ta wuce itama Zahra ta shiga part d'insu tana murmushi..
A falo ta tarar da *Aryaan* zaune yana shan ruwan Lipton,suna had'a ido taga ya d'auke kai ransa a had'e...
_tafi nono fari_
Ta fad'a a ranta sannan ta wuce d'akinta,wanka ta shiga tayi sannan ta fito ta shirya cikin wani cotton lace blue black,gown ce tayi mata kyau sosai,simple makeup tayi sannan ta haye gado ta janyo wayarta..
Whatsapp ta shiga ta duba ko *Arish* yana online duk da cewar bata da chaji sosai amma tanason tayi magana dashi dama shi kad'aine friend d'inta...
_okay_
Kawai taga ya rubuta kuma still yana online, murmushi tayi ta fara rubuta..
_kawai ina tashi daga bacci naji inason chatting dak_.......
Bata k'arasa ba kawai taji an fizge wayar,da sauri ta kalleshi ta mik'e tsaye a tsorace tace
"Bani wayata" ta mik'a hannu ranta a b'ace,shima cikin b'acin rai yayi wurgi da wayar tare da fard'o ta zuwa k'irjinsa...
A gigice take ta k'ok'arin kwatar kanta shi kuma ya rik'e ta gam idonsa a rufe ya fara mata magana a kunne..
"Kiji tausayina baby kinfi so ki sakani cikin tashin hankali baby kinkuwa san irin son da nake miki,meyasa bazaki bawa mijinki hak'k'in aurensa ba?" Jin kalamin daya fad'ane yasa ta fara dukansa tun k'arfinta batasan lokacin da tace "k'arya kake macuci kai ba mijina bane kanason yaudarata ne, na Sani na San *Arish* ne mijina ba kai ba wlh idan baka cikani ba zan maka ihu"
Cikin tsananin firgici ya saketa yana mata kallon mamaki,
Kuka sosai ta farayi cikin tsananin nadama tace "ka cuceni kana amfani da son zuciya kanason cutar d'an uwanka,ni *Amanarka* ce an damk'a ni a hannunka amma ka yaudareni kace ni matarkace" ta sa hannu tana goge hawayenta ta nufi bakin k'ofa tajita a rufe,juyowa tayi ta kalleshi "bani key d'in"
"Bazan baki ba"
"Wlh idan baka bani ba sainayi ihu kuma na fad'awa kowa abinda kake k'ok'arin aikatawa"
Shima cikin zafin rai ya k'araso gurinta yace "ki fad'a mana sai me?idan kin fad'a momma kika tonawa asiri matar data fiddo ki daga cikin k'angi,ku talakawa haka kuke baku san a taimakeku ba"
Ta d'an ja da baya daga wajensa sannan tace "nagodewa Allah ni ba fasik'a bace"
Dariya yayi wadda har saida ta bata tsoro ya matso gurinta yace "ni ba fasik'i bane so ne ya jawo hakan *MENE AIBUNA* Dan na so matar da aka d'aura aurenta da sunana?wlh babu Wanda ya isa ya rabani dake inasonki so Mara misaltuwa kuma babu Wanda ya isa ya hanani cimma burina a yau d'innan kuma a yanxu ko da kinyi ihu babu mai jinki domin duk 'yan gidannan sun tafi airport taro triple" a tsorace taja da baya tare da fad'in "kaji tsoron Allah"
Dariya ya sakeyi ya Ciro key d'in ya wulla kan gadon tare da nufowa inda take gadan2.
0 comments:
Post a Comment